Share this page
sauyin ruwa suka haɗu suka sa ta ɗan fara kukan ciwo , Sai dai kasancewar nan Amurka ba kamar ƙasashen Africa da basu cigaba bane ta fuskar kula da lafiyar ɗan Adam . Cikin ƙanƙanin lokaci a rana ɗaya aka bata magunguna tare da duk wani taimakon da ya dace a ƙarshe likitan ya gargaɗe su akan kiyayeta daga wannan sanyin mai tsanani , dan haka ciwon bai tsananta ba ya lafa  . Kwanaki biyu Biyamuradi yayi yana tsara abunda ya dace na daga sabon kuɗirin sa , da tunda ya samu gamsassun bayanai daga bakin likitan Mama , Ya dangana da nema mata lafiya a yanzu domin babu damar yi mata dashen ɓargo ko juyen jini da zai iya bata waraka , dole zasu cigaba da haƙuri tare da kula da ita , tana shan magungunan ta har zuwa wasu shekaru nan gaba da za'a samu wani cikin 'yan'uwan ta da zai isa sadauƙar mata da ɓargon sa .   Tun a washegarin ranar ya koma asibiti ɗauke da sabon ƙudirin sa bayan dogon nazari tare da kai komo a ƙarshe zuciyar sa ta amince ya haƙiƙance cewa zai kai Falmata ga Manyan likitocin ido dake Mayo clinic su duba ta , idan tana da rabon gani shi zai yi iyakar ƙoƙarin sa wajen biyan kuɗaɗen da za'a buƙata domin yi mata aiki zuwa kan magunguna domin  samun warakar ta . Babu shakka Falmata ta cancanci duk wata kulawar sa duba da yadda take nuna ƙauna ta haƙiƙa ga gudan jinin sa da yake da tabbacin ko mahaifiyar Mama baza ta so ta sama da son da Falmata take yi mata ba , Sannan akwai wani abu da shi yake ji game da Fatima da ya kasa fasaltawa a zuciyar sa sai dai yana yawan sakawa a ransa cewa saboda irin kulawar da take yiwa 'yarsa ne. Bayan haka Halin mutum yana zama tsani wajen samarwa da mutum Alkairi ko akasin sa , halayen Fatima mafi yawansu masu kyau ne , ƙwari yake yabawa da Yakanah tare da Nagartar dake gare ta .    **** Yau ne Alƙawarin sa da Sabon likitan da zai Fara duba Falmata wacce bata kai ga sanin ƙudirin sa ba , domin bai kai ga sanar da ita ba . Kasancewar ƙarfe uku na yamma shine lokacin da zasu ga likitan hakan ya sa shi fita sayo musu hot chocolate Su sha kafin fitar su domin zai taimaka wajen rage musu jin matsanancin sanyi . Da Sallama ya tura 'yar ƙofar ya shiga inda ya tarar da su a zaune yadda ya fita ya bar su , da ɗan gudu Mama ta taho gurin sa ",Bienvenue Papa, que m'as-tu apporté?  (sannu da zouwa Papa me ka kawo min ?) Rungumar ta yayi suka ƙarasa kan doguwar kujerar da Falmata ke zaune fuskar ta ɗauke da siririn murmushi , ", Sannu da dawowa Baban Mama ,   "Sannu da hutawa Maman Mama , yace da sigar zolaya yana kallon fuskar ta      Hot Chocolate ɗin ya ciro musu gami da sanya 'yan chokula ya sakawa  Falmata nata a hannu, Ya ɗauki Mama ya ɗora a cinyar sa ya shiga bata a baki tana kurɓa a hankali Shiru ne ya biyo baya , ɗumin shayin da aka yi shi da garin koko ( cocoa ) da damammiyar  Madara mai zafi yana ratsa sassan jikin su daɗin sa kuma yana basu nishaɗi , da yasa Falmata bata farga da tayi shan haɗama ba sai da ta ji 'yar robar hannun ta sakayau , ta kai chokalin baki , taji bata ɗebo kome ba . Biyamuradi Youssouf wanda duk idanun sa ke kan ta ya ga irin shan da tayiwa chakulan ɗin, ya kai hannu a hankali ya zare robar daga hannun ta tare da musanya mata da nashi wanda bai kai ga fara sha ba , ", Fatima bois ça aussi ( ki sha wannan ma )   " Baban Mama na ƙoshi fa , nagode .    Ta furta hakan tana jin kunya na taso mata , Murmushi mai sauti yayi , ganin yadda gefen bakin ta ya ɓaci , ya kai hannun sa kusa da fuskar ta , hannun sa na sauƙa a jikinta ta jaa baya da sauri tare da ajiye robar hannun ta ,    "Dakata Fatima , repérer zan ɗagga miki daga fuskar ki ,     Babban ɗan yatsan sa ya kai gami da goge mata gefen bakinta inda hot chocolate ɗin ya sauƙa bata sani ba . Kanta a ƙasa tace   "Nagode . bai amsa ba illa ɗibar chakulan ɗin da yayi ya kai bakin ta ,   " amshi lait au chocolat chaud , buɗe bakin ta tayi cike da kunya ta karɓa , "zan iya sha da kaina . tace masa muryarta can ƙasa , yayi kamar bai ji ta ba ,  tare da cigaba da bata a lokaci guda shima yana sha , bata sha dayawa ba tace da shi ta ƙoshi , cikin nishaɗi ya shanye sauran , yana ƙurewa fuskar ta kallo da take sumul babu ɗigon ƙwalliya , Bayan sun gama , yace mata   "Fatima zamou fita zouwa hospitalisé ku shirya yanzou ,   " Baban Mama zamu sake ganin wani likita daban ko ? Wannan bai ƙware ba sosai ya zai ce cutar Mama bata warkewa bace ? akwai ciwon da bashi da magani ne ?   da wani irin yanayi yake dubanta yadda take maganar cike da son samun warakar Mama ya taɓa ransa , ita bata da wani sauran buri ne a rayuwa da ya wuce lafiya tare da walwalar Mama ? Bata yiwa kanta wani shiri ko tanadi ? Bata da wani buri ne na gina tata rayuwar ? " Doctorat gasskiya ya faɗi Fatima , cutar Mama batta maganin waraka a yanzou sai fa kou ɗaya bissa hanyoyin da ya faɗi da kouma babu dama a yanzou , ba bissa lafiyar Mama zamou tafi hospitalisé ba , Shiru tayi ranta babu daɗi , yaya zai ce babu hanyar samun warakar Mama , shi baya irin tunanin da ita take yi ne  ? Meyasa bazai yi wani yunƙuri ba domin taimakawa gurin samar da yadda zasu yi su tsaretar da Mama daga wannan ciwon me azabtarwa , ?    So take tace masa akwai hanya mana ,  sai dai tana cike da tsoro , da jin nawi tare da zargin ko matsayin da take da shi a wajen sa bai kai wannan matakin ba , mafi girman lamarin ya tambayeta ƙarin bayani , to tace da shi me ? Ko a mafarki bata jin ta san amsar da zata iya ba shi . Cikin sanyin jiki ta tashi , da gudu mama ta sauƙa daga jikin Baban ta ta zo ta kama hannun Falmata , sannu kan hankali tayi mata jagora zuwa ɗaki  , Ajiyar zuciya ya sauƙe bayan shigewar su ɗaki , bai ji daɗin sanyin da jikinta yayi ba kan amsar da ya bata , Mayo clinic Doctor Omer Berat ɗan asalin ƙasar turkiyya ( Turkey ) da aiki ya kawo shi Amurka , shine ƙwararren likitan ido da zai duba lafiyar Idon Falmata , Bayan sun shiga wajen sa tare da taimakon na'urar fassara yare suka gaisa , Babu ɓata lokaci ya nemi da ya fara zantawa da marar lafiyar sa , A hankali Youssouf ya kamo hannun Falmata da take zaune a kujerar da take fuskantar ta shi yace ,   "Fatima ki saurara da kyau likita ke son yin magana da ke kan lafiyar ki . " Lafiya ta ko ta Mama ? "Lafiyar idon ki Fatima . Ya amsa yana sake tabbatar mata , Mayar da hankali tayi ga likitan lokacin da ta ji ya ƙira sunan ta , Ta amsa , tana mamaki daman ita ya kawo asibitin a yau ? Tambayoyi ne sosai Likitan yake yi mata da mafi yawan su Falmata bata da takamai-mai amsar su domin tambayoyin sun shafi asalin dalilin sumuwar rashin lafiyar idon nata da ita bata sani ba , amsar da ta bashi a ƙarshe ita ce   " Je ne sais pas, je viens de vivre dans la cécité , mes parents sont morts sans me dire à quel point j'étais aveugle . ( nima ban sani ba kawai na tsinci kaina cikin rayuwar makanta kuma iyayena sun mutu ba tare da sun bani labarin yadda makanta ta ta samo asali ba . )   Biyamuradi Youssouf da amsar ta ta taɓa masa zuciya , ya sake runtse hannun ta cikin nashi , yana jin yadda tausayin ta ya kawo masa . bayan ɗan guntun rubutun da likitan yayi ya umarci Falmata da ta zo kan ɗan wani gado da yake daga gefe a ofishin ya duba idanun nata , Har bakin gadon Biyamuradi ya kama hannun ta , ya kaita tare da kama mata ta hau gadon ta kwanta  , Doctor Omer ya haska ƙwarar idanun nata da penlight , ya ɗora da tambayar ta ko ta ga haske ? Tace ita bata ganin kome , Cigaba yayi da haska idon yana dubawa , a ƙarshe ya kunna slit-lamp ya dallare mata ido da haske , Wani irin kaifi ta ji ya soki idanun ta da ya sata kifta idanun da sauri tare da kai hannu biyu ta riƙe kanta da ya sara mata , "washh kaina . " Sannu ', ita ce kalmar da Youssouf ya furta da sauri yana riƙo hannuwan nata ya sauƙe daga kan ta ,   Bata amsa ba illa riƙe hannun sa da tayi saboda yadda har yanzu take ji ba dai-dai ba a ƙwarar idanun ta .   Bayan likita ya gama dube-dube a ainashin cikin ƙwarar idanun ta , Biyamuradi Youssouf ya kamata suka dawo wajen zaman su suna fuskantar likitan da yake rubuce-rubucen sa cikin kwamfiyuta , Turo ƙofar ofishin akayi wata mace ta shigo , babu ɓata lokaci ta jagoranci su Youssouf zuwa wani sashi na daban inda aka yiwa Falmata hoton ƙwarar ido aka tura ga sakamakon ga Likitan ta ta kwamfiyuta kamar yadda ya turo musu da bayanan irin hoton da yake so su yi mata ta kwamfiyuta . Kafin isowar su hoto tare da bayanan da duk suka dace sun riga sun iso masa , dan haka bayan ya kammala binciken sa  , ya zunkuɗa yana mai gyara zaman gilashin idon sa , ya shiga yi musu bayani dalla-dallah cikin turancin sa yayin da su kuma pilot-in-ear yake fassara musu cikin faransanci , Iritis shine ciwon da ya haddasawa Falmata matsalar idanu da har ya kai ga ta rasa ganinta , shi iritis wata cuta ce da take samun ƙwayar baƙi/brown na tsakiyar idon ɗan adam , da take kumbura ƙwayar idon , sa ciwon ƙwayar idon da disashe gani ,gaza ɗaukar haske da sauran matsaltsalu da dama , wanda ake iya samun sa ta hanyoyin da suka haɗa da ƙwayoyin cutar maɗamfari ( infection ) , jin ciwo kai tsaye ga cikin ido , kamar bugu zuwa ƙwarar ido na daga kowanne irin abu , da kuma cutar da take kama ƙwayoyin halitta na jini tana kashe su. Bayan dogon bayanin da likitan yayi musu ya ɗora musu da bayani kan matakin da cutar ta kai ga idon na Falmata wanda rashin samun maganungunan da suka kamata a kuma lokacin da ya dace , ya kai ga ta rasa ganin ta na tsawon wasu shekaru  sakamakon mutuwa da wasu daga cikin jijiyoyin ƙwarar idon suka yi . kai tsaye bazai yuwu ba ganin ta ya dawo kamar na sauran mutane masu lafiya , duk da cewa akwai yuwuwar kaso ɗaya bisa uku na ganin nata ya dawo tare da taimakon magunguna da allurai zuwa kan aiki na musamman da za'a iya yi mata a idon idan har magunguna da alluran basu taimaka yadda yakamata ba , wanda zai ɗora ta akai da zarar ya kammala binciken sa a yau . Cigaba yayi da yi musu bayani har zuwa lokacin da ya tabbatar sun samu gamsuwa sun kuma fahimci duk bayanan da yayi musu , da kan shi ya jaa jinin Falmata ya fita da shi zuwa ɗakin gwaji saboda ya auna ya san irin magunguna da alluran da suka dace yayi mata bisa ga mataki na farko . Basu bar asibitin ba sai da aka mata allurai biyu ta babbar jijiyar hannun ta tare da yi mata ɗaya a jijiyar da take daf da idonta na dama , Ba ƙaramar juriya ta nuna ba wajen tsayuwa da tayi cikin nutsuwa aka huda mata jikinta babu zilliya bare ihu da hatta shida kansa likitan sai da ta burge shi sanin da yayi allurar gefen idon tana da zafi  ,        Ya dube ta bayan ya ƙare mata allurar gefen idon ,  " sorry It'll hurt but just for a few minutes .    Gyaɗa kai tayi tana jin yadda idanun nata suka yi nawi ga wani irin yanayi marar daɗi da take ji a idon , " Baban Mama , ta ƙira sunan sa tana lalubar hannun sa ,   Da sauri ya riƙo ta " Na'am Fatima , sannu kina jin ciwou ? comment vous sentez-vous en général ? ( How are you feeling overall ? ) "  Idona yayi jini ne ? "bai yi jini ba Fatima , sannu  .    **** Misalin ƙarfe tara na dare suka bar asibitin bayan sun ci abinci sama-sama daga kitchen ɗin cikin asibiti . Suka yi bankwana da likita omer bisa ga yarjejeniyar sake dawowa asibitin nan da kwanaki huɗu masu zuwa , bayan ya haɗasu da mugunguna ɗore da dokoki da sharuɗɗan da ya gindaya musu  . Baki ɗayan su sun gaji Mama tayi bacci a jikin Babanta , Falmata kuwa tsukun da idanunta ke yi yana damunta wanda yake ta zubar hawaye , gaba ɗaya bata jin daɗin kome , damuwarta ta tayar da Hankalin Youssouf da yake amfani da kalmomin rarrashi iri-iri yana jera mata sannu , har suka dawo gida , kai tsaye ya zarce da mama ɗakin baccin su ya kwantar da ita ya lulluɓa mata bargo tare da kunna hutar ɗumama daki ya fito falo inda ya tarar da Falmata ta rufe fuskarta da hannu biyu , ta jingina kanta da jikin kujerar da take A sanyaye ya ƙaraso wajen fuskar sa na nuna damuwa ƙarara  , Zama yayi a kusa da ita jikin sa na gogar nata , ya kai hannu a hankali ya sauke hannun ta daga fuskar , Hawayen da idanun ke yi ya goge da hankicif ɗin da ya zaro a aljihunsa , "Fatima yaya ne ? Ciwo ne har yanzou ? Kou zamou koma ga doctorat ? " Baban Mama idanuna ciwo suke kamar zasu fita , idona bai taɓa ciwo haka ba , bazan warke ba kar kayi asarar kuɗi dayawa , lafiyar Mama yafi samun lafiyar idona muhimmanci kuma .. "  Shittt , yace yana kai hannun sa kan ɗan bakin ta .   " Fatima baki ji abounda Doctorat ya faɗi ba ? Zaki warke ko ba du ba , waye ya faɗi miki zata zam asara doumun nayi jinyar ki daga jakka ta ? " kiyi ta addu'a Allah shi sa a cimma nasara bissa ga neman lafiyar ki kin ji kou  ? Shiru tayi , ita ganin zancen likitan take soki-burutsu tayaya idanun ta zasu fara gani ? Bayan a iya sanin ta bata taɓa ganin hasken duniya ba . Muryar sa ta katse tunaninta " Kou baki so watarana ki ga fuskar mijinki ? Kou baki so watarana ki ga fuskar ɗiyar ki Mama tare da 'ɗiyan da zaki haifa nan gaba ? Jin ya sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi sai ta ɗago kanta , ' " inaso , amma nafi son na samu ɗa domin ya sadauƙar da ɓargon sa ga Mama , ta warke kamar yadda likita ya faɗa ,   Sai yayi shiru yana kallon ta da taimakon hasken da bai cika yawa ba da ya hasko daga jikin ƙwan fitilan dake ajiye saman teburin gaban su , zancen ta ya zo masa a bazata , ya ratsa ƙwaƙwalwar sa a jirkitatcen yanayi da ya kasa tantancewa . Ita ma shiru tayi cike da fargabar kasassaɓar da tayi , kada dai tayi masa laifi ? Ko dai zantukanta basu dace ba ? Tayi masa tsaurin ido ko ? Sauƙar hannun sa cikin nata ya katse mata tunanin zucin da take yi  , "Fatima mu tafi muyi sallar isha'i kiyi kwana (bacci ) dare yayi ," A sanyaye ta amsa da "To, Har suka kwanta bacci babu wanda ya kuma magana kowanne a tsakanin su yana tunani, Wayar sa ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira , da azama ya ɗauka ganin wacce ke ƙiransa ya sanya shi miƙewa a hankali ya nufi ƙofar ɗakin , ya zo fita ya juya gami da kai kallon sa kanta da tayi lamo cikin bargo kamar mai bacci , ajiyar zuciya ya sauƙe ransa cike da tunaninnika barkatai ya fita gami da jaa musu ƙofar , Falmata wacce duk motsinsa a kunnen ta , ta miƙe zaune gami da yaye bargon , cikin ranta sam babu daɗi gani take kamar ta ɓata masa rai da maganganun ta tunda gashi daga lokacin bai sake cewa da ita kome ba , ko fushi yayi ?  Tashin muryar sa da yake magana kamar a gabanta "kasantuwar ta mai buɗaɗɗen kunne " ya sa ta saurarawa  zagayayyar fuskarta na bayyana wani yanayi irin na wanda aka shammata lokacin da taji yana cewa , "bonjour ma princesse comment allez-vous aujourd'hui mon amour? ( Alo gimbiyata yaya kike yau masoyiya ? ) Cigaba yayi da cewa "Je vais très bien et tu me manques aussi , ( ina lafiya lau nima nayi ƙewar ki )   Ƴar dariyar nishaɗi yayi , kana ya cigaba da cewa , " wannan kalma ke kin ka faɗe ta , ni kouwa gurina ba haka ne ba , duk wani bigeren da babu ke cikin sa wajena daɗin sa ragagge ne , babu kome anan sai matsanancin sanyi tafe da tarin nawi da wahalwalu bisa kaina ,   Murmushi yayi mai sauti , " a gida nake Yarima , ga gurin aikina kuma Mai muƙamin Major , nan kuwa ai ban wucce matsayin bawa dake hidima ga wassu rayukan ba , Gicciyewa yayi ya kishingiɗa yana me cigaba da sauraron ta , " ba domin yanayi da bashi yiwuwa na taho da ke ba, kin sani ban iya tafiya ga nissan duniya batare da ke gefena ba maimounatu ke ai sashi ce daga jikina , Falmata da take sauraran sa , sai ta koma ta kwanta tare da lulluɓuwa ta cure jikinta guri ɗaya ga barin sauraran zantukan sa , zuciyarta ke wani irin bugu da yake tafe da zallar tashin hankali ,   Sunan wacce aka ƙira da Maimounatu tare da irin Kalmomi masu daraja da aka mallaka mata , sun gaftare tare da ruguza duk wani ɗan guntun tunanin banza da ta fara yi ,"Ah to na banza mana , tunda 'yar kulawar da yake bata ya sa ta hasashen hawa wani matsayi da bata kai shi ba a wajen sa ashe ita ɗin ba kome bace face tarin nawi da wahalhalu  . Hawaye masu ɗumi suka gangaro daga idanunta suna ɗiga bisa hular sanyin kan Mama . Maiduguri Nigeria Tun ranar da Doctor Hamza ya gargaɗi Yakaka akan kada ya sake ganin fuskarta bata sake bari sun haɗu ba , Ko muryar sa ta ji yayi Sallama da shi bai cika shigowa ma sashin nasu ba , da sauri zata nemi gurin ɓuya , duk cewa tun daga ranar duk lokacin da ya buƙaci abinci daga Rahima ita take girka masa , sai ita kuma Rahima ta kai masa . Yau Asabar ya shigo gidan da safe misalin ƙarfe tara shirye yake tsaf cikin shirin sa na zuwa ɗaurin auren ƙanin Abokin sa . Yana yin Sallama , Yakaka da take goge Falon bayan ta gama sharewa tayi saurin ajiye moper ( mofi ) ta tsallaka da ɗan gudu ta shige ɗaki ta rufo ƙofar , Hajja da take zaune a gefe tana karin kumallo ta harari bayanta ta wutsiyar ido kafin ta taɓe baki , " Ni hauwa'u naga abunda yafi ƙarfi na , ke kenan kullum a tsalle-tsalle da guje-guje ? Uwa wata tunkiyar da take rawar turke ? Allah ya kyauta . Washe baki tayi tana dariya ,lokacin da Doctor Hamza ya shigo " a ah kaga manya ɗiban farko ,  Babban likita , Fuskar sa ɗauke da murmushi suka gaisa , ba tare da ya zauna ba yace   "Hajja ina Rahima ?   " Yanzu ta hau sama , a ƙira ta ne ? " a ah yi zaman ki Hajja idan dai ta fito ace ta min girki kafin dawowata ta kai min ɗakina . " To babu laifi zan faɗa mata .   " Nagode Hajja . Ya juyawa da nufin fita idanun sa suka sauƙa kan Hoton Mama da tun ranar da ya fara ganin hoton yake son tambayar Rahima 'yar waye ? Ƙwarai hoton yarinyar yake fusgar hankalin sa , Dan haka ya dawo da baya yana tambayar Hajja , " Hajja wannan 'yar waye haka aka samu kyakkyawa  ? Da dariya Hajja ta amsa masa " 'yar wajen Fatima ce ,  Mama sunan ta ai sun ma yi tafiya ne can Amurka ita da iyayen nata . "Fatima ? Ya maimaita , " wacce Fatima Hajja ?  " Ƙanwar wannan yarinyar Yakaka take ko wa ?   'okay , Ya amsa yana barin wajen ba domin ya gane wacce ake nufi ba kai tsaye sai dan ƙiran sunan Yakaka da Hajja tayi . ƙarfe biyu na rana suka shirya tafiya gidan Amne su Uku Rahima , Yakaka da kuma Hajja da itama tace zata je . Shatar shatar adai-daita Rahima ta ɗaukar musu wanda ya tokare daga bakin hanya yaƙi gangarawa kwarin unguwar a cewar sa gargadar cikin unguwar zai ɓata masa mashin , dan haka dolen su suka sauƙa Rahima tana ta mitar wahalar tafiyar da zasu yi a ƙafa kafin isar su gidan . Da wani tasowar sabon yanayi a zuciyar Yakaka take bin unguwar da kallo , unguwar da ta zama tushe na hargitswar rayuwar ta da bata tsinci kome a ciki ba illa wahalhalu da tarin abubuwan ƙi , unguwar da suka sha gwagwarmaya a cikin ta ita da ƙanwar ta da ƙawarta Yagana ko ina yagana take a halin yanzu ? Wataƙila ita rayuwa tayi mata kyau , tayi aure ta fara ginin rayuwar 'ya'yan ta . tunaninta ya katse lokacin da Rahima ke cewa su gangara , Tana bin layin tana tuno da haɗuwar su da Doctor Hamza a bakin layin ana ruwan sama ,taimakon da yayi mata a ranar da ba domin shi ba da ta faɗa babbar kwatar taji mummunan ciwo ko ma ta rasa ranta , "Allah sarki yaya dakta , Ta furta hakan daga ƙasan ranta lokacin da suke miƙawa cikin layin . Daga nesa ta fara jiyo hargowar sa muryar sa a sama yana rantse-rantse , domin ta tabbatar da shi ɗin ne ? Tayi saurin ɗaga idonta ta ɗora a kan sa shi da wata matar da kallo guda tayi mata ta gane yanayinta na matan banza , Da sauri ta ɗauke kai tana ɗan jawo hijabinta gaba kaɗan , zuciyarta cike da fatan Allah ya rufe masa ido ya wuce bai ganta ba bare ya gane ta. cikin rashin sa'a hasken da take da shi ya riga ya ɗau hankalinsa kasancewar sa kawali idanun sa koyaushe akan wankakkiyar mace yake babu ruwansa da matsayinta na matar aure ko akasinta . Sun ƙaraso gaf da juna ya jaa ya tsaya , kafin ya ɗau salatin da Hajja ta ƙarasar masa , Sauri yayi ya zagaya ta sashin ta ya dogare , yana kallon fuskar ta da taƙi yadda su haɗa ido , Dariya ya kwashe da ita yana tafa hannuwan sa alamun mamaki yace , "Ahayye nanaye ke duniya mai abun mamaki ? Yanzu duniya da gaskiya Yaks kƴa ga Ɗanliti ki ɗauke ido ki kawar da kai ? Lalle Yaks kin zama kaza ci ki goge bakin ki , Ko da yake ai kome kika yi ba mamaki tunda baki da shayin kowa . Yakaka ta saci kallon Hajja wacce tayi saƙare tana bin Ɗanliti da kallon banza , " Ɗan-Ɗan

Chapter 59 of 103