hannun sa ,
Cikin Falmata ya bada wani sautin ƙululu lokacin da ta ga an miƙo masa bindiga ya zura harsashin a ciki , wani irin tsoro mai girma ya ziyarceta , meye yaje shirin faruwa da ita ? aina ma wai take ?
Magana suka fara yi bayan sun ɗan yi gaba kaɗan da inda take tsugunne ba tare da wani ya kulata ba daga cikin su ,
Tsantsar tsoro yasa ta daina fahimtar me suke cewa duk kuwa da cewa da yaren da tafi fahimtar sa bisa ga sauran yaruka suke magana , idanunta sun fir-fito , bindigogin hannuwansu kawai take bi da kallo da zuwa lokacin ta lura fiye da rabinsu suna riƙe da bindiga .
Da ɗaya-ɗaya suka jide kwalayen , tana ganin lokacin da suka ɗaga kujerar da take baya suka maida wata jakar bacco gurbin da suka cire kwalayen ,daga haka ta ga sunyi musabaha tsakanin Ahmadou Gayu da wasu daga cikin tawagar ,
Da gudu-gudu suka hau bayan motocin su ,suka tada tare da nausawa cikin daji .
Amadou gayu ya ƙaraso kanta lokacin da yake cewa ,
" 'yar dindimi sai ki tasso mu tai na sauƙe ki daga bakin hanya inda zaki iya samun motar da zatta sada ki da cikin garin Maiduguri ni iyakatai bakin daji kome da kin ka ji motsi nai anan ki manta da sautin anan muddin kin biɗarwa kan ki lahia , kin ji kou ?
Gyaɗa kai Tayi da sauri , ta shiga motar suka sake nitsawa cikin daji , sai lokacin ta lura babu kowa a motar sai su biyu , ko ina sauran mutane huɗu na bayan motar ? Ta tambayi kan ta .
**
Ƙarfe sha ɗaya na safe yayi mata a cikin babbar tashar garin Maiduguri , bayan Ahmadou gayu ya sanya ta a mota daga ƙaramar hukumar Mobar da ta kawo ta cikin garin .
Duk tayi busu-busu da ita ta fita hayyacinta , yunwa da firgici sun maida ita firka-firka , amma duk da haka .
Hamdala ta dunga yi lokacin da ta samu tabbacin tana cikin garin Maiduguri ne ta samu ƙubuta daga hannun mutanen da tun-tuni ta fahimci ko su waye su .
tunanin inda zata dosa kuma ya rufe ta , domin ita dai bata san takamai-mai sunan unguwar gidan Prof ba , duk rayuwar ta cikin garin ta yi ne a halin tana makauniya ,
Wata rumfa ta hango ana tuyar doya da ƙwai a bakinta, ta ƙarasa ta zauna daga ƙasa tana kallom mutanen wajen da fiye da rabin su maza ne hatta mai tuyar da mai rabawar duk samari ne ,
Da zamanta a wajen , wani matashi da ya ciko ɗan farantin roban hannunsa da soyayyar doya mai kwai , ya mata duban ƙasƙanci , kafin ya ajiyewa wani mutum doyar a teburin gaban sa , ya ƙaraso inda take
"Ke baiwar Allah ki tashi daga nan , idan bara za kiyi ki shiga cikin tasha ko kuwa ki nemi wani wajen amma ba nan ba wajen sana'ar mutane .
'kayi haƙuri dan Allah hutawa nake yi , ga kuɗina ka bani abunda kuke sayarwa na duka ,
Ta miƙa masa kuɗaɗen da bata san adadinsu ba da ta zaro daga cikin jakar hannunta ,
Kallon kuɗaɗen da bana Nigeria bane ya yi , kafin yace
"waɗannan takaddun fa ? Kuɗin ina ne ?
Kafin ya rufe baki ubangidansa ya ƙwalla masa ƙira
" Bashari wai kana ina ne ?wannan wanne irin tsagoron zunzurutun walaƙanci ne zaka tafi hirar banza ka barni da ayyuka , to wallahi idan har ƙazar nan ta ƙone a mai , na rantse sai ka biya ni dan ni da asara kullum saɓani muke .
Da sauri Bashari ya bar kan Falmata ba tare da ya karɓi kuɗin da take miƙa masa ba ,
Ya ƙarasa da gudu wajen ogan sa ,
"kayi haƙuri oga wata mata ce kamar mahaukaciya dai haka ta zo da wasu kuɗaɗe kamar na landan a hannunta wallahi oga wai ta miƙa min su na bata doya , kuma kuɗin dayawa oga
Da sauri Ɗanliti ya saki matsamin da yake hannunsa acikin mai ba tare da ya tsame doyar ba ,
"kai Bashari na fa sanka da sakin ƙwai , kuɗin landan fa kace ? Dala fa kenan ? Yau a masu sayen doyar tawa har da masu Dala ? Ina take ? Nuna min matar ?
Nuno masa Falmata yayi da har lokacin take takure a zaune ,
Cikin ƴar marairaicewa Ɗanliti ya kwararo mata sallama , da sauri ta ɗago kanta jin muryar wanda ta taɓa sani a baya ,
Suka yi arba da fuskokin juna, shirun ƴan wasu daƙiƙoƙi suka gifta kafin Falmata ta miƙe tsaye da sauri tunowa da tayi da ko wanene Ɗanliti.
' wa nake gani haka kamar un-un Ɗankachallari ? Wai kece ko kuwa kamanni ne ? Ah ai babu zancen kamanni ma ga ƙwala-ƙwalan idanun nan daga ina kike ƴarkachallari haka kamar 'yar bina ?
Muryar ta na ɗan rawa , tace
" Ba sunana ba kenan , sunana Falmata ,
' haka fa ashe sunan ki kenan , to dawo daga nan a kawo miki doya ki ci ki sha ruwa ko kya samu nutsuwa , na ga yunwa na tanɗar bakin ƙirshirwa a fuskar ki .
A ɗarare ta zauna a inda yake nuna mata kan wani benci , aka kawo mata zazzafar doya da ƙwai har da dafaffen ƙwai guda biyu da aka soya su da ƙwai ,
Tas ta cinye ta sha ruwan leda biyu , tayi hamdala
Ɗanliti da yake gurin suyar sa ya bari tare da sake dawowa yana sake tambayar ta daga ina take ?
A takaice ta faɗa masa daga inda take , daga haka tayi shiru
Ɗan jimm yayi yana kallon ta , kafin yace
" wai , tabɗi yanzu nan daga Niger kike ? shiyasa mana na ga kin koma busu-busu , ashe rairayin hamada ne ya turbuɗe ki , ai kin ma kaima barka da sahara bata haɗiye motar ta ku ba kamar yadda nake ji ana labari wai-wai , koda yake da kuma kun yi mutuwar shahadar nan da kowa ke nema ,
" nima kin ga ai yanzu duk na tuba na daina abunda yake jawo min tsinuwa , na kama ƴar sana'ata da nake rufawa kaina asiri da ita , aure ma nake shirin yi , O ni Ɗanliti mutuwar Saly Fara ta zamanto min alherin da na samu shiriya a domin ta ,
Ya ɗaga hannun biyu sama , yana ƙara cewa
"Allah na ƙara gode maka da ka kashe Saly Fara ni kuma ka shiryar da ni .
Shiru Falmata tayi tana sauraren bayanin da bata nemi jinsa ba , ji tayi ya cigaba da cewa ,
" ai ƴar danginku ma zan aura wallahi kuwa ,
Ɗago kanta tayi ta dube shi ,
"ƴar dangin mu ? Tambaye shi da mamaki ,
" eh Ƴar uwarku Yagana ba , ni kuwa ina Yakaka wallahi habibiya tana nemanta ruwa a jallo tace tayi ta zuwa gidan da kuke bata samun ku , can gidan wani mutum mai kuɗi wai a Danboa road ko ina ?
Da sauri Falmata tace ,
"Ina Yagana take ? ta san gidan Prof ? Ka kaini wajenta ta kaini gidan Prof ,
Kwantar da hankalin ki indai habibiya kike nema kin same ta tunda kika ganni , nan da mintoci talatin ma zaki ganta anan ta zo , ai tare muke sana'ar mu , ita take yi mana wanke-wanken farantan kayan sana'a , kinsa rayuwar nan cuɗanni na cuɗeka ne .
****
Yagana ita ta sada Falmata da gidan Prof da misalin ƙarfe biyu na rana , har falon prof ta so shiga da ita sai dai aka hana su saboda yana tare da baƙi , amma an musu iznin shiga ciki sashin matar gidan domin su jira shi .
"Falmata ai tunda na kawo ki ni zan iya tafiya ko ?
Yagana take neman iznin Falmata bayan sun kawo ƙofar sashin su Rahima ,
"Yagana , Nagode , Nagode zaki iya tafiya ,
"Babu kome Falmata ai mun zama ƴan uwa banda sharrin shaiɗan da ya rinjayeni a baya na aikata kuskure , Dan Allah idan Yakaka ta dawo zan zo na nemu gafararta ta yafe min .
Nan suka yi sallama ,ba tare da Falmata tasan wanne kuskure Yagana ta aikata ba da take neman yafiyar Yakaka ,
Jikinta babu ƙarfi ta nufi cikin gidan , a zuciyarta tana saƙa yadda zata yi ta tunkari Prof da zancen ya raba aurenta da Youssouf batare da ta bayyana mummunan laifin da suka aikata ba shi da Yakaka ,
Saboda bata so wasu su dubi Yakaka da wannan mummunan laifin , zata zama abun aibatawa a wajen Al'umma ,
A hankali ta tura ƙofar falon ta shiga sanyi da ƙamshi mai daɗi ya buso ta , daga ciki kaɗan ta tsaya tayi sallama da zazzaƙar muryarta ,
Cikin nutsuwa matar da take zaune a kan ɗaya daga cikin sabbin kujerun falon tana saƙa da zaren ul da kwarashi, ta ɗago kanta , idanun ta suka sauƙa akan Falmata da itama take iya hango alamun farar fatar ta daga inda take ,
Muryarta bata fita sosai ta amsa sallamar ,
Su dukkanin su shiru suka yi suna kallon juna ,
Cikin sanyin jiki falmata ta kalato murmushi ta ɗora bisa fuskar ta, zuciyar ta na bata cewa Rahima ce wannan take hangowa A hankali tace
"Rahima ni ce fa, ni ce Falmata ƙanwar Yakaka baki gane ni bane ?
Kwarashin hannun Khaalty Rahima ya faɗi ƙasa bata kula ba ta miƙe tsaye ta nufi inda Falmata take , zuciyarta na bata tabbacin cewa mafarki take , wataƙila kuma gizo take yi mata ,
Tana zuwa ta miƙa tafukanta biyu ta dafa kafaɗun Falmata idanunta suna jiran ɓacewar ta daga ganinsu ,
Ƴar dariya Falmata tayi , kafin tace ,
"Rahima kina mamakin gani na ko ? Yakaka ma ai tana zuwa wataƙila gobe zata iso ba tare muka zo ba Rahima....
Hannun Rahima da taji yana tattaɓa mata fuska , yasa ta haɗiye sauran kalmomin ta , ta riƙe hannuwan tana ƙoƙarin sauƙe su daga fuskarta , da wani irin sauti ƙasa-ƙasa , Khaalty Rahima tace
"Falmatana ke ce ? Ke ce wannan Falmata ? Ke ce ? Ina Yakakana ?
Rungumo ta tayi gaba ɗaya zuwa cikin jikinta tana fashewa da kuka mai sauti ...
Assalamu Alaikum masu karatu .
Da fatan duk kuna lafiya ??
Ina mai baku haƙurin ji na shiru da kuka yi wasu hidindumu ne suka sha kaina , da fatan kun min uzuri ? ❤
Nagode .
[12/16, 1:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
45
Da rashin yadda a fuskar Falmata , ta ɓanɓare jikinta daga na khaalty Rahima , Muryar ta na ɗan ƙyarma tace ,
"wacece ? Rahima kece ?
Zuwa lokacin Murmushi Khaalty Rahima take , murmushin da har ya bayyana haƙoranta , sake riƙe hannun Falmata tayi , da sautin muryar ta mai ɗan ƙarfi tace , "Falmatana ni ce Mamar ku , ni ce , ashe kuna raye Falmata , ina Yakaka ?
Da wani irin yanayi Falmata take sake wara idanunta tana ganin dusu-dusun fuskar matar da take gabanta , tana jin wani irin bugu da zuciyarta ta sauya a take da ziyarta ruɗani a tare da ita tace, "Mama na ? Ke ce Maman mu ?
Sai tayi baya da sauri kamar zata gudu , ta waiga dama da hagunta , da wani sauti tace , "Yakaka ina kike ? Kina ina ? Ki zo ki ganta wai wannan Maman mu ce ? Wai da gaske ita ce ?
Murmushin fuskar Khaalty Rahima bai ɗauke ba lokacin da hawayen fuskarta suke cigaba da sauƙa ta matsa tana sake kusantar ta , sai ta miƙa hannu ta jaa hancin Falmata da bai wani ciƙa tsayi ba , ta zarce da riƙe kumatunta duk biyu da hannuwanta , sannan ta haɗa goshin su guri guda , tana sake cewa ,"Ni ce Mamanku Faɗimah-Zahra ni ce Ina Amina ?
Wani irin yanayi ne na zallar Farin-ciki mai tafe da sanyi mai samar da nutsuwa , taji yana bin duk wata jijiyar jikinta , a sanyaye ta karkata kanta , muryarta da rangwamen sauti tace ," Maman mu ke ce ? Ke ce Mama da gaske ba mafarki ko gizo ba ? Mama daman kina Raye ? Mamana .
Bata jira ta amsa mata ba ta zarce da rungumeta ,tana sakin kuka da ƙaramin sauti , irin kukan da Ɗa yake irin sa a lokacin da ya tsinci kansa a gaban Mahaifiyar sa bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana haɗiyar baƙin-ciki cikin kewar ta .
Khaalty Rahima ta sa hannu biyu ta rumgumeta , tana jin wani irin tarin farin-ciki marar misaltuwa , ashe daman rayuwa zata sake iya yi mata sauyi mai tattare da farin-ciki irin wanda ta fidda rai da samun sa , ashe watarana zata zo da zata sake ganin ƴa'ƴan ta ? Allah abin godiya .
Sauƙowar Amnee daga Sama ita ta jaa hankalinta, da mamaki ta ƙaraso tana kallon su , da har zuwa lokaci , Falmata take kwakume da Mamanta bata bar kuka ba , da alamar tambaya a muryarta tace
"Ukhtee Rahima me ya faru ? wacece wannan ?
, jin sautin muryarta yasa Falmata ɗago kanta , kafin ta bi bayan Khaalty Rahima da take riƙe da hannunta , suka ƙarasa gaban Amnee , da murmushi Khaalty Rahima ta haɗa hannun Falmata da na Amnee , tana cewa
" wannan ita ce 'Ya ta Falmata da na baku labarin su ina zaton sun mutu ita da yayar ta mai sunanki Amina da ake mata laƙabi da Yakaka , ikon Allah da girma sai ga shi ya kawo min ita har gabana .
Sai ta waiga ga Falmata , tare da cigaba da cewa , "Fatima ya akayi kika san ina nan ?
Da bayyanuwar murna Amnee ta zarce da rungume Falmata , kafin ta ɗora da cewa , Alhamdulillah , Alhamdulillah , ashe ba haka nan ba na so yaran nan tun a rana ta farko da na fara ganin su , ace 'ya'ya nane , jini na , 'ya'yan 'yar'uwa ta , Ukhtee Rahima ai nasan Fatima da Yakaka tun shekarun baya suke rayuwa tare da 'yan uwansu a gidan nan ba tare da sun san dangantakar su da juna ba , kai Alhamdulillah .
Saman kujerun wajen suka zauna ,suna sanya Falmata a tsakiyar su , khaalty Rahima ta ce ,
"Ikon Allah Ukhtee ashe ma kun san su ? Ashe suna hannun ku ?
" ƙwarai na san su , ai yayan Zainab ( Doctor Hamza ) shine ya kawo su gidan nan a matsayin ƴan gudun Hijira , a gidan nan suke tsawon shekaru kusan biyar zuwa shidda , ikon Allah kenan ai kuwa ko zuwan Yakaka na kwanan nan taje har wajena ta gaishe ni , ai itace wacce kika ji na tambayi Rahima shekaranjiya kan ina take ta shaida min ta tafi Niger wajen Ƙanwar ta da 'yar ta , Allah ya saɓa haɗuwar ku ai da gidan nan zaki tarar da ita .
"Ikon Allah , to Alhamdulillah , Alhamdulillah , sune kalmomin da Khaalty Rahima take faɗi farin-ciki na sake gauraya ta , ji da tayi ashe ma 'ya'yan ta gida suka dawo , ashe ma tare suke da yayun su , ƙarƙashin kulawar mutumin da yake mazaunin Uba a wajenta , Babu shakka tare da dukkanin tsanani akwai sauƙi , kuma ba'a fidda rai daga Rahamar Ubangiji .
A kusan tare suka jefawa Falmata tambaya ,
"Fatima ina Amina da 'yar ta ?
Shiru Falmata tayi da famin raunin cikin ranta , a hankali ta ce da su ,
"Allah ya yiwa Mama rasuwa kwanaki huɗu da suka wuce ,
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon, Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon," suka haɗa baki wajen cewa , shiru kuma ya gifta tsakanin su cike da jimamin rashin jikar su da basu kai ga samun damar ko da ganin fuskarta ba a zahiri , babu shakka Allah baya barin wani domin wani ya ji daɗi .
" Ina Maisunan Ukhtee ita kuma ? Ba wajen ki ta tafi ba ?
Ƙhaalty Rahima ta sake tambayar Falmata ,
Shiru Falmata tayi tana sunkuyar da kanta ,
Wani busasshen yawu Khaalty Rahima ta haɗiye tana jin tashin hankalin da yake farmata , kada dai ace wani mummunan lamari ne ya afku ga ɗiyar ta mafi soyuwa gareta ?
Matsa hannun Falmata dake cikin nata tayi da ɗan ƙarfi , ta ɗan ɗaga sauti tana sake maimaita tambayar " Falmata ina kika baro Yakaka ??
***
A Niamey tunda Yakaka ta dawo daga tasha , bayan samun tabbacin Falmata ta riga ta tafi Nigeria ta wannan mummunar hanyar mai cike da hatsarin ƴan kungiyar Boko Haram ,
bayan kuka babu abunda take yi , gabadaya ta ɗora laifin gudun Falmata akanta , tayi danasanin zuwanta ƙasar baki ɗaya yafi a ƙirga , ganinta da ace bata zo ba da Falmata bata gudu ba , sai ta ji inama da ta zauna akan batun Youssouf da yace su rufa asirin tsakanin su kada Falmata ta sani a tun farko , ƙila da suna da damar da zasu haɗu ita da Youssouf su wanke kansu a wajen Falmata bayan sun ƙaryata ƴan uwansa a gabanta , da kuma lamarin bai kwaɓe ya haka ba ,
Ganin kuka ba zai mata magani ba yasa ta miƙe tsaye ɗauke da jakar kayanta , Hajja wacce take zaune zugum ta dube ta tare da cewa ,
"Babba uwar Mama ke kuma ina za ki ? Kadda kice min kema gudun fanfalaƙin za kiyi ? Kiyi wa Allah ƴar nan ki tsaya mu ji da damuwa ɗaya kadda ki ɓaro mana wata sabuwa , guje-gujen nan ba kana bane , 'ya'yan nan ai ƙwarya ta gari tana ragaya , kamar yadda darajar ɗiya mace ɗakin Mijinta kar ki tafi ko'ina Dan Allah ,
Ba tare da Yakaka ta dubi Hajja ba tana share hawayenta da gefen hijabinta tace ,
"Hajja gara na tafi saboda Falmata fa ko da taje Maiduguri lafiya , bata fa san hanyar gidan Baa prof ba, kuma bata san kowa ba a garin bayan shi , dole zanyi hanzarin tafiya nima ko Allah zai sa na haɗu da ita a tasha , na tarye ta Hajja ina ƙaunar Falmata ita ce kaɗai jinina a duniya ina tsoron rasa ta Hajja , zan tafi bazan iya zama ba nima .
Guntuwar ƙwallar da ta tarawa Hajja a ido ta sa hannu biyu ta shafe fuskarta ta muttsuƙe ,
" To Shikenan Yakaka tunda kin ce haka bari nima na haɗa ƴan kananun kayan buƙatu na mu tafi tare , ai nima zama bai ganni ba , to na zauna nayi me ƴar nan ? Ai tunda ganga ta fashe sai ƴan rawa su watse ,
Da hanzari Hajja ta shiga harhaɗa kayanta, tana cewa ,
"bari na tafi da waɗanda dole zan iya buƙatar su , sauran kuma idan Allah ya min dawowa na cigaba da Amfani da abuna idan kuwa ma tafiyar kenan , to a biyo ni da tsunmokara na , wannan lamari dai da ɗaure kai yake babu shakka da walakin wai goro a miya .
Yakaka da har lokacin a tsaye take akan ƙafafunta bata ce da ita ƙala ba ,
Cikin ƴan mintoci kaɗan ta haɗe kayanta a cikin wata babbar jakar matafiya da Youssouf ya taɓa saya mata , tana shirin yafa mayafinta suka tsinkayo sallamar Youssouf daga ƙofar falon , Hajja ta amsa tana nufar falon
A tsaye ta tarar da shi shirye tsaf cikin riga da wondo na kaftani da ya sha aiki irin na saraki , ba tare da ya yadda Hajja ta ga ƙwarar idanunsa ba fuskarsa babu walwala ko kaɗan sai tarin damuwa da tashin hankali da suka bayyana kansu ɓaro-ɓaro , cikin Amonsa da a yau ya sake kaurara da buɗuwa yace
"Hajja ni zan tai Maraɗi yanzou Hajiya Umma tai ƙirana , don Allah ku zauna a gida har na kai ga dawowa nan da kwanaki biyu , lamarin Fatima kouwa zan yi dukkanin ƙoƙarina da Yardar Allah babu abunda zai samu Matata da abinda ke cikin ta .
Ɗan karkata kai Hajja tayi da sigar tausayawa tace ,
" Babban soja Allah ya tsare hanya , sai dai kuma yanzu na gama fama da ita yayar Falmata kan cewa da tayi a yanzu itama za ɗau hanyar Nigeria saboda ko Allah zai sa su gamu da ƴar uwarta a tasha idan sun isa Maidugurin dan ita Maiɗakin naka ai kasan bata san ko'ina ba a can ko gidan shi mariƙin nasu bata sani ba , ana gudun kar ta ɓata ko ta shiga wani mawuyacin hali kuma a can , da naji haka sai nace to fa nima zama bai kamani ba tare zamu tafi , to kaga shirin nan da nayi ma na tafiyar ne ga kayana ma can na haɗa su gu ɗaya .
Bayan ya gama sauraron Hajja da tayi shiru tana tsumayen iznin sa , sai yace ,
" hakka ma shawarace mai kyaou Hajja , to idan hakka ne ku taho na sauƙe ku ga tasha na sanya kou a mota , nima sai na tai gida ,
"Amma Hajja doumin Allah dagga kun cimma gida kun tadda Fatima ki sanar min ta téléphone , sabadda na san halin da kuke ciki a can , duk da nima ba da jimmawa ba zan tai can Nigeria ɗin , kuma a nan sojin mu zasu yi bakin ƙoƙari wajen duba hanyar da ita Fatima zasu bi , sai dai kouma idan har ta ɓarauniyar hanya ta daban zasu ɓulla yanzou fatan mu dai yana ga Fatima ta cimma gida lahia .
" to babu laifi Babban soja ai sai mu tafi ɗin , Allah dai ya sassauta wannan lamari , bari na ƙira ita Yakaka ,
Mota ɗaya suka tarar wacce zata tafi Kano kai tsaye daga Niamey dan haka Youssouf ya biya musu gidan baya na motar su biyu rak da daman mutum ɗaya suka tarar a gaban motar dan haka nan take aka shiga neman direba ya zo kuɗin kujerun mota sun kammala ,
Laluba aljihunsa yayi ya fiddo kuɗaɗen ciki da baki ɗaya CFA ne , mayar da su aljihunsa yayi saboda sanin da yayi daga sun bar shiyar ƙasar su ba zasu musu wani amfani na sosai ba , ya zaro wallet ɗin sa da dalolin Amurka ke ciki a miƙe , ya matsa kusa da gilashin motar da yake sauƙe ta sashin da Yakaka take ,
Ba tare da ya dubi fuskar ta ba yake miƙa mata kuɗin da bai riga ya ƙirga ya san adadinsu ba ,
Yakaka wacce tunda ta shiga motar ta ɗauke kai daga barin kallon sashin da yake tsaye , amma tana ankare da shi ta kuma ga tsayuwar sa akanta yana miƙa mata ƙudi , bata son sake kallon fuskarsa ne dan haka taƙi ɗago kanta ,
Hajja wacce take raba ganinta a tsakanin su biyun , ta ɗan zunguri Yakaka ,
"Babba uwar Mama , Babban soja yana baki saƙo ,
Da wani irin yanayi na gargaɗi a fuskarta ta kafe Hajja da idanunta da suke da kaifin kallo masu kamar gilashi ,
Galala Hajja tayi tana mayar mata da martanin kallonta , sai kuma ta muskuɗa ,tana cewa
"Ajabba inji kanurai, o ni hauwa'u ,
sai kawai ta maida ganinta can gefe tana kyeɓe baki .
A hankali Youssouf ya zura hannunsa kaɗan ta cikin motar ya sauƙe mata kuɗaɗen akan cinyarta yana cewa "Hajja Allah shi kiyaye muku hanya don Allah Hajja duk yadda lamari ya kassance muku ki jisheni ,
" Amin Amin Babban soja , da yardar Allah zan sanar da kai duk yadda ake ciki , kaima kuma Allah ya tsare maka hanya , mungode , mungode
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 73 Chapter of 103