Share this page
, Ƙure mata kallo take yi , cike da son ganin ta fiye da yadda take iya hango ta dusu-dusu a yanzu , Runtse ido tayi ta buɗe a hankali 'Mama    Ta ƙira sunan ta,  Dariya Mama tayi tana ɗora 'yan hannuwanta akan hannun Falmata da take tallafe da kumatun ta , Ta ga hasken haƙoran Mama da fuskar ta , a yanzu ta yadda da cewa ta samu waraka , irin ganin da take yi dusu-dusu shine ganin da ta haƙiƙance kowanne ɗan adam yana yi , Irin haske marar ƙarfin da take gani shi ta aminta da cewa shine hasken duniya , ita kuwa mai zata yi da ya wuce godiya ga Allah da ya nufe ta da samun waraka ? rungume Mama tayi tana faɗin kalmar Alhamdulillah , Alhamdulillah babu ƙaƙƙautawa , Raf-Raf-Raf likitocin da suke wajen suka ɗau tafi , cike da bayyana farin cikin su na samun nasara kan aiki , Youssouf wanda farin cikin sa bazai misaltu ba ya tako zuwa gaban gadon Falmata , " Fatima Ya ƙira sunan ta , da amon muryar da take cike da shauƙi da zumuɗi , cike da ƙwaɗayin son ganin Fuskar wannan ma'abocin Alheri a gare ta ta ɗago kan ta daga fuskar Mama da take ta son sake gani tamkar mai son haddace kamannin ta a ɗan tsakanin lokacin , Dariyar haƙoran sa ta fara cin karo da su , kafin hasken farar fuskar sa irin na Mama da ta fahimci basu kai sauran mutanen wajen haske ba , ta bayyana mata ,  Kafe shi tayi da ido tana burin ganin kamannin sa ko da kuwa ace shine abu na ƙarshe da zata iya samun nasarar gani kafin hasken da ta samu ya koma duhu da har yanzu ta gaza yadda a zahiri ne ba mafarki ba cewa idanun ta suna ganin duniyar da ta rayu tsawon lokaci a cikin ta , Irin riƙon da ta yiwa fuskar Mama shi ta masa , ta kai hannun ta kan sajen fuskar sa ta tallafo fuskar tana kallon sa da irin ganin da ya sawwaƙa a gare ta  , Dariya Youssouf ɗin ya cigaba da yi da haƙoran sa ganin yadda ta riƙe masa fuska ƙam-ƙam , kamar wanda zai ƙwace ya gudu , ko kuwa ya ɓace mata , Da ƴar dariyar mai tafe da amon da  ke bayyana tsantsar farin-cikin ta , ta kai goshin ta ta haɗa da nashi , tsinin hancin su na gugar na juna , "Baban Mama nagode , nagode nago...   "Fatima ki godewa Allah da ya baki lafiya , ni ma shi nake godewa , da ya nufa aka cimma nasarar aiki , Zama yayi daga gefen ta a bakin gadon , Mama tana tsakiyar su ya sanya hannu sa ya kewaye su da shi ya rungumo su jikin sa , yana jin matsanancin farin-ciki na zagaya ruhin sa , Tamkar a ire-iren shuɗaɗɗun lokutan da suka wuce cikin rayuwar ta da Yakaka , sautin ta ya bijiro cikin tunanin ta tamkar a lokacin take furta mata , " Falmata na ina ji a jikina watarana za ki warke , za ki ganni kamar yadda nake ganin ki . Hawaye masu ɗumi suka silmiyo ta ƙarƙashin gilashin idanun ta , kewa tare da ƙaunar ahalin ta suka bijiro mata , a sarari ta furta " Allah ya jiƙan ku Baba , Mama , Yakaka,  Bakura da Baana , 'Amin  Youssouf ya amsa mata . ***** Cike da tarin sabbin dokoki da sharaɗin ziyartar likita a duk bayan mako guda na tsawon watanni biyu , Suka samu sallama daga asibitin , tafiyar ƙafa suka yi zuwa gidan su , inda Falmata ta dunga bin titi da ganin ta marar ƙarfi , Murna fal cike da zuciyoyin su ita da Youssouf , kome ta hango shatin sa sai ta tambaye shi wannan abun menene shi ? Meye sunan sa ? Shi kuma babu gajiyawa cikin jin daɗin tambayoyin da take masa yake bata amsa tare da faɗa mata sunayen abubuwan . Ƙofar gidan Musa suka tsaya , farin cikin da zukatan su ke ciki ya tunbatsa so suke su yi ɗaukanin sa da wani , alhalin babu wani nasu makusanci tare da su , dan haka gidan Musa suka yada zango , Musa da Ramlat sun taya su murna sosai inda a ƙarshe har 'yar walima suka shirya musu nan cikin falon su, Yana riƙe da hannunta suka shigo gida , Suna shiga tun kafin su zauna ta ce  shi , "Baban Mama ka ƙira Hajja a waya na faɗa mata na warke nima yanzu ina gani , Yana murmushi ya zaro wayar sa daga Aljihun sa ya shiga lalubar layin Hajja , Ya san dole tana neman wani makusanci nata wanda zata raba farin-cikin ta da shi , Nigeria Tsawon satikan da suka biyo bayan Rayuwar Yakaka tayi su ne wajen ganin ta cigaba da ƙokarin wanke laifin ta daga idanun jama'ar gidan Prof , Babu inda take zuwa kullum tana gida ita ke yin mafiya yawan aiyukan gidan , A hankali Hajja ta fara fahimtar kyawawan ɗabi'un Yakaka , na kawaici da gudun tashin hankali , sannan kuma me sakakkiyar fuska ce ma'abociyar murmushi ,uwa uba yawan ibadar da ya zauna mata . Hakan ya sa ta fara sakar mata fuska har takan ɗan ja ta da hira a wasu lokutan , A yau ma zaune suke , suna 'yar hira Yakaka tana taya Hajja tsinke ganyen zogalen da zata yiwa Prof girki da shi Wayar Hajja da take ajiye a gefe ta ɗau ƙara , Da sauri Yakaka ta ɗau wayar ta miƙa mata , "Ni hauwa'u waye ke ƙirana da wannan sanyin la'asar ɗin ? Allah jishe mu Alheri , ɗaga ƙiran tayi dai-dai da ƙwanƙwasa ƙofar falon da aka yi , Yakaka ta miƙe da saurin ta tana cewa " Oyoyo Rahima . Ta nufi ƙofar , "Assalamu Alaikum Hajja ni ce Falmata , Muryar Falmata ta karaɗe kunnen Hajja ta cikin wayar ta mai maɗaukakin sauti , Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye ɗingis-ɗingis ta nufi ɗakin ta da yake gefe , "Lale Lale Marhabin da uwarɗakina Fatima mutan turai , Ta furta hakan lokacin da take ƙarasa shigewa ɗaki cike da son kar Yakaka ta san da wacce take waya , " Uwarɗakina ince dai duk kuna lafiya ? Ya Babban soja tare da 'yar rigima Mama , dafatan an samu nasara wajen neman magani ? "Hajja Alhamdulillahi ki taya ni murna , na warke Hajja na samu lafiyar idona , "Da gaske Fatima kai Alhamdulillah nayi murna , nayi murna Allah Abun godiya kin warke Fatima ,? Buwayi gagara misali , Murnar Yakaka ta rikiɗe zuwa Fargaba lokacin da idanun ta suka sarƙe cikin na Sofi matar Yaya Dakta , Kallon-kallo na daƙiƙoƙi suka yiwa juna kafin ta tsinkayo muryar Doctor Hamza wanda yake tsaye daga bayan sofi ,   "Malama kauce ki bada guri mutane su wuce kin yi wani sanƙanƙam a tsaye kina zarewa mutane ido , Da sauri Yakaka tayi baya tana komawa falon ƙarƙashin rakiyar mummunan tsakin da sofi ta bita da shi . Ɗan diri-diri tayi a falon rashin ganin Hajja yasa sum-sum ta nemi mafakar ta a can ƙarƙashin kafar benen da yake falon ta samu guri ta zauna ran ta duk a dagule . "Me ya sake dawo da shi yau kuma ? har ma da matar sa ? Daga inda take tana iya jiyo tashin Muryar su , Da Sallamar da Docto Hamza ya yi , Basu ko zauna ba Sofi ta fara faɗin "Wannan kuma wacce jemammiyar 'yar aiki aka samu haka a gidan nan ? Sai tashin ƙarnin man masu bleaching take ,  Doctor ba dai ita take yin wanke-wanke ba , ? Dan bana jin zan iya riƙe ko chokalin da ta wanke , A kaikaice Doctor hamza ya dube ta yana samarwa kan sa mazauni akan kujerar falon mai cin mutum guda , Motsa laɓɓan sa yayi kamar zai ce wani abu sai kuma yayi biris da ita yana zaro wayar sa daga Aljihu , Hannun kujerar da ya zauna ,Sofi tayi matsuguni a ɗosane tana cigaba da cewa , "Ni kamar ma nasan Fuskar ta a wani waje ? A hankali ya ɗago kai yana duban ta da ita ma ta karkato gare shi , fuskar ta ɗauke da wani irin yanayi na tsantsar ɓacin rai da bai kai ga sanin dalilin samuwar sa ba , " akan wa kike magana ne ? " wannan yarinyar mai kama da farar kura , " Ta furta hakan lokacin da tunanin ta ya gama tuno mata da inda ta taɓa ganin Yakaka a gidan Samy baby , Dariya ce ta so kama Doctor Hamza jin an kwatanta Yakaka da farar kura ,      " ko ina sofin sa ta san wannan gantalalliyar yarinyar ?        Ya tambayi kansa a zuci . " okay , Yace a taƙaice yana mayar da hankalin sa ga fuskar wayar sa , "irin karuwan nan ce masu tsayawa a bakin hanya suna ne... Fitowar Hajja cikin Murna ya katse mata zance da ta ɗauko yi , " a a' ah Babban likita kaine tafe iwar haka ? Sannu da zuwa sannu da zuwa ka sha hanya tun daga birnin tarayya, Da 'yar fara'a Doctor Hamza yake amsawa Hajja gaisuwar da take masa , Hajja ta ɗora ganin ta kan Sofi wacce ta jirkita sosai kan kafaɗun Doctor Hamza kirjin ta daf da fuskar sa , fiye da rabin cinyar ta na kan jikinsa ,  kan ta a ɗage sai shan ƙamshi take , ko ƙala bata cewa Hajja ba , "ah to wacece ita 'yar aikin zata gaisar ? Ƙanƙan da ido Hajja tayi , " Yau ina ganin taɓara maigida da kukan tsarki , mene haka wata shaɓatartar da ke kin wani ɗaɗɗane ɗan mutane ƙin kalmashe shi ? O ni hauwa'u inda ranka ka sha kallo , ikon Allah 'ya'yan zamani , mu lokacin mu ina muke iya ɗaga ido mu dubi miji a gaban mutane ? Cike da 'yar kunya doctor Hamza ya miƙe bayan ya ture Sofi daga jikin sa ,  yace , " Rahima bata nan ko Hajja ? A ɗan sama mana abinda zamu ci please ina tare da yunwa , " Rahima bata nan likita , bata ƙaraso ba daga Makaranta , to babu laifi yanzu kuwa za'a samar da abinci ,sannun ku da hanya , Wani banzan Kallo Sofi ta jefawa Hajja tana bin bayan mijinta , cikin ranta cike da haushin kalaman Hajja , cikin ran ta tana cewa , "ji min tsohuwar nan da kinibibi ? Ko ina ruwanta da ni ," ? Idan har ta ce zata shiga harka ta kafin na bar gidan nan sai na ratsa mata tarbiyya ,' " Mts   Hajja ta saki tsaki bayan barin su falon , "abun haushi Nama na jan kare ,  me ake da mace marar kunya da kamun kai ? Kunya ai ado ce . Murnar labarin da Falmata ta bata na samun warakar ta ya taso yayi awon gaba da takaicin da sofi ta bata , ***** Washegari bayan Doctor Hamza ya shirya kai tsaye ya nufi yin abunda ya kawo shi garin . Bayan ya je sun gaisa da Prof shi da Sofi , daga bakin mashigar sashin Prof ya dakatar da ita daga binsa , " Sofi ki koma ciki , ni fita zan yi sai na   dawo , Zunɓur-ɓur ta turo baki ,    Cikin salon da koyaushe take amfani dashi idan tana gaban shi na ƙoƙarin ta nuna masa ƙuruciyar ta da a zahiri ta riga ta yi mata adabo ,         A shagwaɓe tace "Haba mana Doctor please zan bika mu tafi tare naga gari , ka ga fa irin yanayin gidan shiru ba... "please Sofi kar ki ɓata min lokaci a banza ai kin san yanayin gidan babu abokin hira kika dage sai kin biyo ni , kuma ni wajen aiki zan tafi ba yawo a gari ba ,   Juyawa yayi ya ƙarasa ga motar sa ya shige ciki bai ko sake waigowa ta kan ta ba ya tada motar yayi tafiyar sa , " jagale ! Tayi a tsaye ranta cike da ƙuna ,     "so take ta san meye Doctor yake ƙullawa a garin da yake ta zirga-zirga a tsakanin Maiduguri da Abuja , Cikin wata guda wannan ne zuwan sa na uku , ita fa duk wani abu da zai sha gaban ta , ya mata katanga kome ƙanƙantar sa da Doctor Hamza yaƙi take yi da koma menene , Ko aikin sa dan bata da ikon hana shi ne amma da tuni ta shata layi tsakanin su , so take koyaushe ya zama bashi da uzuri sai nata , A fusace ta juya ciki , **** Kai tsaye gidan Amne ya nufa , ya taddata tana karin kumallo da Fankaso da miyar gandar ƙafar sa , Ya gaishe ta cike da ladabi , ta amsa tana mai farin-cikin ganin sa , Tambayar sa tayi ya safiyya ? Ya shaida mata ai tare suka zo garin . "Shine kuma baka kawo min ita mun gaisa ba ? Ta furta haka lokacin da take zuba masa miya akan fankason da ta zuba masa , "Amnee fita zamu yi tare zuwa wani waje , Ya furta haka lokacin da yake kai lomar farko bakin sa. " ina kuma zamu ? Allah yasa dai Lafiya . "lafiya lau Amne sai Alheri , cikin nutsuwa ya gama cin abincin sa , Bayan ya wanke hannu , yace "Amne zamu iya tafiya yanzu ko kina da wani uzurin da zaki yi ? "ba abunda zan yi , amma tukun wai ina zaka kai ni ? Kaƙi sanar da ni . "kiyi haƙuri Amnee mu je ki gani , "to bari na yafa mayafi na , Tare suka fito shi da ita ya buɗe mata gidan baya na mota ta shiga ya rufe , gami da zagayawa ya shiga ya tada motar yana barin unguwar , Ya riga ya gama tsara hanyoyin da zai bi domin ganin ya dai-daita lamarin iyayensa , wanda daman burin sa ne tun ma kafin bayyanuwar Khaalty Rahima a gare shi , Bayyanar ta ya sauƙaƙa masa lamarin , ya kuma ji daɗi domin yasan dawowar ta a dai-dai lokacin matakin nasarar gyaruwar kome ne wanda hargitsewar kome yake da nasaba da ita , Bayan duk lallamin da yayi mata akan  ya mayar da ita gida , amma taƙi amincewa , Cikin dogon nazarin da yayi ya yanke shawarar haɗa su kitsumun , ba tare da sanin kowaccen su ba . Dan haka a yanzu da ya ɗau Amnee kai tsaye ya nufi gidan da Khalty Rahima take ba tare da ya sanar da kowaccen su game da 'yar uwarta ba . Suna 'yar hira shi da Amnee har suka iso ƙofar gidan , ya fita a motar ya nemi iznin shiga gidan daga maigadi inda ya amince nan take har ma yake sake jaddada masa , ai kuwa Mamar Bulama tana , Tare da Amnee suka shiga wacce take cike da mamakin ina Hamza ya kawo ta ? Gurin wa suka zo ? Allah dai ya sa lafiya , Shi ya fara shiga sashin da Khaalty Rahima take , daga bakin ƙofa ya dogare ,  yana fuskantar Cikin gidan daga inda yake yana hango Khaalty Rahima wacce ta duƙufa yin wanki daga gefe , Babu Alamun ta san da tsayuwar sa a wajen , "Bissmillah Amnee shigo , " Assalamu Alaikum , Amne ta ce lokacin da ta shigo filin gidan , Dai-dai da ɗagowar Khaalty Rahima wacce sautin Hamza ya ankarar da ita tsayuwar shi a wajen , Zuciyoyin su suka buga da wani irin yanayi mai girma , daga ƙasa har sama Amnee take kallon ta , Kowanne irin jirkituwar halitta ce ta samu Rahima ƙanwar ta , ba zai sa ta gaza gane ta ba , "Rahma,  Rahmatullah , Ta ƙira ta da wani ɗan guntun sauti , "Rahmatullah hal hdha haqiqiun lak 'Yaa ukhtee ? ( shin dagaske ke ce 'Yar uwata ? ) A hankali ta saki rigar hannun ta da take wankewa  , Da hannu biyu Amnee ta rufe fuskar ta lokacin da hawayen farin-ciki ya fara zarya akan fuskar ta , Bata jira ƙarasowar Rahima ba wacce take tahowa da sassarfa , ta taka da sauri ta tadda ta , Rungume juna suka yi hawayen murnar ganin junan su na sauƙa , Khaalty Rahima bata san haka take cikin maricin tare da kewar 'yar uwar ta , yayar ta , madadin uwa agare ta ba sai yanzu da ta gan ta tsaye a gaban ta bayan tsawon shekaru fiye da ashirin da suka kwashe basa tare . Hannu biyu Amnee ta sa ta riƙe fuskar Rahima , "ke ce wannan Rahimatullah ? Meyasa kika tafi kika barni ? Kina garin nan Rahimatullah duk tsawon shekarun nan bakya nema na ? Meye na miki mai girma haka Rahimatullah  ? "Rahimatullah wacce irin Rayuwa kike yi tunda kika barni ? Nan ne gidan ki ? Kin yi aure ne ? Ina maigidanki ? ki min magana mana ƙanwata Muryar Doctor Hamza ta ratsa tsakani , shi da kansa ƙwalla ta taru masa a ido , irin ƙaunar da yake hangowa a fuskar kowaccen su ga 'yar uwar ta , ta masa yanayi da na yaran nan biyu 'yan gudun hijira . "Amnee ki kwantar da hankalin ki , Khaalty Rahima ta gamu da larura tana jin magana amma bata iya mayarwa , Sabon Kuka Amnee ta fashe da shi , "Rahimatullah ce ta kurunce ? Meye haka ya faru da ke Rahimatullah ? Cikin ruɗani ta waiga ga Hamza " mu tafi asibiti a duba min ita yanzu Rahimatullah Amana ce a wajena , Da sigar rarrashi khaalty Rahima ta jijjiga hannun Amnee da yake cikin nata , Waigowa tayi tana kallon ta , Murmushi tayi mata , ta kai hannu ta goge mata hawaye tana girgiza mata kai , ƙoƙarin taro ta Amnee take lokacin da ta ga tana ƙoƙarin tsugunnawa , tare suka durƙusa , Khaalty Rahima ta rubuta mata a ƙasa cikin yaren su , "ki daina kuka , murna yakamata muyi da sake ganin junan mu Yaa Amina . Bayan Awanni biyu Doctor Hamza , tare da Amnee da Khaalty Rahima da Bulama suka kama hanyar komawa gidan Amnee. Ga mamakin Hamza Khaalty Rahima bata yiwa 'yar uwarta irin tirjiyar da tayi masa kan komawa gida ba , Ko daman dan bata ga 'yar uwar tata bane a gaban ta ? abunda ya ɗan riƙe su a gidan shine batun tafiya da Rahima da ɗan ta da suka yi wanda da farko matar da khaalty Rahimar take yiwa aiki bata Amince ba . sai da suka bata gamsassun bayanai tare da ƙwararan hujjoji ta kuma ga shaida tare da Amincewar ita kanta Khaalty Rahimar tukun ta yarda ta sallami Rahima tare da yi mata fatan Alheri . Da shigar su gida Amnee ta shiga hidimar Khaalty Rahima , kama daga shirya mata wajen zama na musamman har zuwa gyara mata shimfiɗar da zasu kwana ita da ɗan ta. Abunda ya sake bawa Hamza tausayi shine duk inda Amnee ta gusa , Khaalty Rahima zata matsa kusa da ita tana yunƙurin karɓe aikin da take yi , Amnee taƙi sakar mata , banda murmushi mai cike da tarin ƙauna da tausayi babu abunda suke yiwa junan su . Sai da Amnee ta gama gyara musu waje tsaf sannan ta dawo ta zauna kusa da Rahima , ta riƙo hannun ta tace , "Rahimatullah ina son jin labarin yadda kika yi rayuwa bayan barin ki gida , amma babu dama a yanzu , inshaAllah daga gobe zaki fara ganin likita , Gyaran murya Doctor Hamza yayi , "Amne Ya ƙira sunan ta , a hankali ta waigo gare shi , "Amnee ina son dan Allah yau ki bani labarin abunda ya faru da rayuwar ku ke da Baba da Khaalty Rahima ? Dan Allah kar ki ƙi , ki ban labarin a matsayin tukuicin dawo miki da Khaalty Rahima da nayi . Shiru tayi na wani ɗan lokaci , kafin ta sauƙe ajiyar zuciya , *** "Labarin ba wani mai daɗi bane da kake naciyar sanin sa , "Kamar yadda ka sani ne mu 'Yan asalin ƙasar Chad ne daga Babban birnin N'Djamena , inda aka haife mu , iyaye da dangin mu baki ɗaya.  "Mahaifin mu sajjan ne ( mai gadin gidan yari )  a babban alsijn na ƙasar mu , albashin sa bai cika yawa ba dan haka mai ƙaramin ƙarfi ne sosai , dangin sa duk talakawa ne ,  haka ma mahaifiyar mu ta fito daga gidan talakawa sosai , sana'ar iyayenta sarrafa gishiri daga bakin teku su kawo cikin gari su sayar , ni ce Babbar  'yar su sai ƙanne na maza huɗu "Salihu , Mohammed , Usman da Jamil  sai ƙaramar mu Rahimatullah . "Rahimatullah tana shekaru biyar ni ina da goma sha shida Mahaifiyar mu ta rasu , inda ba'a ɗau lokaci ba bayan mutuwar ta Maifinmu ya sake yin aure , ya auri wata mata mai 'ya'ya huɗu daga ƙabilar N'gambaye mabiyar Adinnin Christian ƴar ainahin ɗarikar Roman Catholic . "zuwan "Aichawa rayuwar mu shi yayi sanadiyyar faɗawar mu ƙunci domin Aicha irin mugayen matan nan ce marar imani , babu irin aikin wahalarwa da bata sanya mu , Su salihu sun zame mata masu nemo mata kuɗi , inda ni kuma na zama baiwar ta mai yin duk wasu aikin cikin gida, hatta Rahimtullah da take ƙanƙanuwa bata tsallakewa izaya daga hannun Aicha ba . "shi da kansa Mahaifin mu bai tsira ba daga bala'in ta dan a wasu lokutan har duka take yi masa , idan ta nemi kuɗi bai bata ba, hakan ya sa yake masifar tsoron ta ba shi da kataɓus , ya auro jaraba . "mugun neman kuɗi irin na Aicha ya sa nima ta sama min aikin goge-goge a babban ofishin jakadancin ƙasar mu tun a wancen lokacin da ba'a cika barin 'ya'ya mata fita neman kuɗi ba , "karatu ma alokacin iyakata primary ban ci gaba ba .  "da murna na fara zuwa aikin saboda ganin zan huta daga masifar Aicha da wahalar aikin gida , sai dai kuma tunanin Rahimatullah da zan dunga bari a gida ya rage min karsashi , " ganin cewa aikin nawa shara ne da goge-goge sai na nemi iznin na dunga zuwa da Rahimatullah tana zama a gefe ni nayi aikina , saboda nasan idsn na bar ta a gida azaba za'a dunga gana mata , cikin sa'a aka amince min . "Tafiya ce miƙaƙƙiya a ƙafa daga unguwar mu zuwa wajen aikina , amma haka nake goyon Rahimatullah daga alfijir ya keto mu ɗau hanya , kafin lokacin da muke isa gari ya waye sosai , "Haka zan yi aikina Rahimatullah tana ƙiriniyar ta , "Rahimatullah irin yaran nan ce masu son wasa , hakan ya sa sai ina aiki ina kaffa-kaffa da ita kar ta yi musu ɓarna dan wani lokacin ma sai na neme ta na rasa ta shige ƙarƙashin tebura ko tayi wani wajen , "Amne ta tsagaita tana duban fuskar Khaalty Rahima wacce take murmushi , "Ashe Bulama ba a ƙasa ya tsinta ba gado yayi ,   Doctor Hamza ya kitsima hakan a ransa , Amnee ta cigaba da cewa , "Na ɗau tsawon watanni shida ina aikin goge-goge a ofisoshin guda biyar kafin a rage min yawan su zuwa kula da ofishi biyu rak , na wata mata Basudaniya ( Sudanese )"Mademe Laura , da kuma na wani jakadan ƙasar Nigeria "Al-Mustafa Dilmari . "tsakanina da su Gaisuwa msi cike da girmamawa ne idan sun iso ofis sun tarad dani a bakin aikina , "wata alaƙa bata taɓa gifta tsakanin mu ba sai Ranar da Rahima tayi wata mummunar ɓarna a ofishin Ambassador Mustapha , inda ta yayyaga wasu takardu masu muhimmanci da ya mance ya tafi ya bar su a ofishin sa ba tare da ya adana su ba , "Ranar na shiga tashin hankali domin kuwa faɗa sosai ya dunga yi min , bai tsagaita ba sai da Rahimatulla wacce take goye a bayana , saboda zamu tafi ƙiran sa ya cimmin ,

Chapter 63 of 103