Share this page
ta ta mata tsiya . Wayar Mamar su ta faɗo mata a rai tasan babu tantama akwai number sa a kai , to ko zata ɗauka ta ƙira shi kawai ma ta wayar ta ta ƙila yafi ɗagawa da wuri fiye da idan ta layin ta ta ƙira da bai san layin ba . Da sauri ta miƙe ta shiga ciki , ta hau sama ɗakin Khaalty Rahima da sa'ar ta babu kowa a ɗakin , daga gefen gado ta hango wayar , da sauri ta ɗauka ta shiga neman sunan sa cikin jerin sunayen dake kan wayar bata sha wahala ba ta samu sunan tare da number sa . Shiru tayi ta gagara danna ƙiran , tana son tattaro kalmomin da zata yi amfani da su wajen yi masa magana , Idon ta ta kai kan agogon wayar ta ga sha biyu saura tasan dai duk tsiya yanzu ya tashi a bacci duk kuwa da cewa yau lahadi ce ba aiki . Fargaba bai rabu da ita ba ta danna ƙiran layin bayan ta kai wayar kunne ta runtse ido gam tana jin wani yanayi mai ƙarfi na shigar ta , daga can ƙasan ran ta addu'ar samun nutsuwa ta fara yi . Wural ta buɗe idanun ta lokacin da ta ji sautin muryar computer na bata tabbacin babu kuɗin da zai isa ƙira a wayar . Dariya tayi da ƙaramin sauti , kafin tace " kai Maman mu sai a bar ta ko meyasa take barin waya ba kuɗi ? Ita kamar ma bata wani damu da wayar ba . Numbers ɗin ta kwafa a wayar ta , sai da ta zauna a bakin gado sannan ta danna ƙiran . ABUJA Daga can Sofiya ce a ɗakin Doctor Hamza tana gyara gadon da basu wani jima da tashi a kai ba Doctor Hamza ya shiga wanka . Tana gyara bargon su lokacin da wayar sa dake gefen gado ta ɗau kiɗa alamun shigowar ƙira . Ba tare da ta dau wayar ba ta leƙa fuskar ta ga lambobi ne reras ba suna , ɗan yamutsa fuska tayi ta gatsina guntun hancin ta kafin tace "yau Sunday ma ba za ku bar mutum ya huta ba shi kenan cikin jigila tsakanin asibiti da gida yau kam rana ta ce sai na more lokutana da aka cinye na sauran kwanaki tsawon sati . Har wayar ta gama ƙara bata ɗaga ba . Daga can Yakaka tayi jim da waya a hannun ta , cike da tsoron kar ta dame shi ta daure ta sake danna ƙiran a karo na biyu , Wannan karon har Sofiya zata fice a ɗakin sai ta dawo baya , ta ɗau wayar kai tsaye ta ɗaga ƙiran tana kara wayar a kunne tace " Hello who's on the line ? " Mukut Yakaka ta haɗiye yawun firgici , jim tayi kafin tace " amm ni ce Yakaka ina kwana ? bata tsaya ba ta zarce da cigaba da cewa "ki kaiwa Yaya doctor wayar . Ba domin Sofiya tana shakkar kar Doctor Hamza da tasan kunnen sa yana iya jiyo ta ba da ba abunda zai hana ta ɗuɗɗurawa Yakaka zagi . Baki ɗaya fuskarta tayi jaa a take tana huci tayi ƙasa da murya kafin tace " To akuya sarkin naci ana ƙorar ki kina daɗa naniƙewa , shugabar 'yan rashin zuciya Miji bai damu da ke ba sai ke ce ke neman sa jarababba , to ƙwalelen ki ke da Doctor sai gani sai hange daga nesa-nesa dan kuwa zaman ki kenan a inda kike 'yar ..... Ƙit ! Ta ji Yakaka ta katse ƙiran , Daɓas ta zauna a bakin gadon baki ɗaya ranta ya cunkushe har wani raɗaɗi take ji a hancin ta kamar ta shaƙi barkono ," wannan jarababbiyar yarinyar watau har ƙiran Mijinta take yi ? " Sofi waye ya ƙira ni naji kamar kin ɗaga wayar ? Da sauri ta waiga kafin ta miƙe tsaye ta ƙarasa zuwa gaban shi inda yake tsaye yana goge kansa da towel , Tana zuwa ta karɓi towel ɗin ta shiga goge masa jiki , bata yarda sun haɗa ido ba fuskar ta babu walwala tace , " Akuya ce ta ƙira ka ? 🙄 "Akuya fa ? Ya tambaye ta yana duban ta da mamaki , Cike da bagararwa ta kai hannun ta ƙirjin sa tana ɗan tsikarin sa tace " eh dan kukan akuya nake ta ji tunda na ɗaga wayar ina Hello , Hello , Hello . Ba'a cewa kome sai Kukan Akuya . Jawota yayi ya haɗe tsakanin su , yana kallon cikin tsakar idon ta yace " Sofi baki fa da kirki a wasu lokutan nasan daga Office ne aka ƙirani , Ni yanzu muje ki bani abinci na ci yunwa nake Ji ina son na fita akwai wani waje muhimmi da nake son zuwa yau . Kicin-kicin tayi da fuska jin cewar zai fita yasa ta sake jin tasowar ɓacin rai da ya ɗan fara lafa mata sanadin haɗuwar fatar jikin su . Bai kula ɓacin ran ta ba yayi shirin sa cikin wani yadi mai ɗan nawi ruwan zuma ya fesa turare tare da ɗaura agogon sa sai lokacin ya juyo ya dube ta da take zaune a bakin gado ta kumbura suntum . Fushinta bai wani taɓa masa rai ba yace " mu je ki bani abincin ba daɗewa zan yi ba zan dawo nima so nake na huta yau ɗaya . Bayan ya ɗan cac-cakali Omelet da kidney Sauce ya ɗan kurɓi ruwan tea ya miƙe a gurguje ya mata sallama yana barin gidan . Da fitar sa ta yi jaɓar ' akan kujera tunanin ƙiran wayar sa da Yakaka tayi ya bata tsoro , ita da ta saki baki ta zauna malumman ta sun ce mata an yiwa Yakaka da Hamza farraƙu to tayaya Yakaka ta iya samun damar ƙiran sa ? Kada dai ace asirin nan bai ci ta ba ? Wani irin huci take yi lokaci guda ta tashi da gudu ta hau sama ɗakin ta ta shige laluben wayar ta , ya zama dole ta sabunta aikin ta .😂 *** Doctor Hamza kuwa yana fitowa hankali kwance ya dai-daita motar sa akan titi unguwar su Malama Maryam ya tasamma da bata kasance ɓaƙuwar unguwa a wajen sa ba , ya sha kai sofiya gidan ƙawar ta Samira . Tsawon sati biyu da yayi yana bin duk wasu Matakai daki-daki domin tabbatar da zancen da Suleiman ya sanar da shi game da Yakaka gaskiya ne ko ba gaskiya ba ? Duk da cewa yana da tabbacin Suleiman ɗin ba zai masa ƙarya ba amma yana da buƙatar samun ƙwararan hujjoji ko dan ya wanke zargin ta daga ransa da hakan shine kaɗai zai ba shi damar samun nutsuwa tare da ita da zai iya rungumar ta hannu bibbiyu , tun usul ƙaunar ta bata tunbuƙe ba daga ransa girgiɗi kawai tayi da a yanzu kuma ta dawo ta tsaya chak da ƙafafun ta ta kuma shiga kaiwa duk wasu gaɓɓan jikin sa mamaya . ASSALAMU ALAIƘUM MASU KARATU . Da fatan duku kuna lafiya ? Sakamakon saƙonnin da nayi ta amsa daga masoya masu karatu kan taƙaice ƙarshen MHR da wasu ke ƙorafi wasu kuma suka nemi Alfarmar na ɗan sake jaan zaren labarin nayi dalla-dalla ko da kuwa ban yi filla-filla ba , hakan yasa na karɓi ƙorafi na kuma ɗan jaa kaɗan ba mai yawa ba da nan gaba kaɗan mu kan iya rufe bangon littafin mu adana shi Insha Allah A ƙarshe ina godiya sosai da sosai ga dukkanin makaranta MHR na fili da na ɓoye daɗa nasan na ɓoyen sun ninka na filin yawa "ghosts readers barkar mu dai ina gaisuwa fa 😜❤nasan kuna tare da ni domin ina ganin inuwar ku , ko da kuwa baku bani tukuici ba . Nagode.Mafari ( Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 50 Lokacin da Doctor Hamza ya isa unguwar su Malama Maryam dai-dai layi da gidan da Doctor Suleiman ya kwatanta masa sai ya ga ashe ma ya taɓa sanin gidan duk kuwa da cewa da dare ya taɓa zuwa amma bai manta da yarinyar da ya taɓa taimakawa ba a wani dare ana ruwan sama babu shakka a ƙofar wannan gidan ya sauƙe ta . Kasancewar ana haramar sallar Azahar a lokacin dan haka a masallacin da yake kusa da gidan nan yayi Sallah . Bayan ya idar sai ya matsa ya miƙawa Liman hannu suka yi musabaha , nuni ya yi masa kafin ya ɗora masa bayanin gidan da ya zo , to amma kasancewar an sanar da shi matar tana da aure ya zama dole sai da iznin Mijinta zai gana da ita , tunda ba sanin juna suka taɓa yi ba dan haka yake son sanin Mijin ta da farko , a zahiri wata buƙata ce ta son samun wasu bayanai daga bakin Matar da ake ƙira Malama Maryam yasa shi tasowa musamman domin ganawa da ita . Dan jim liman yayi yana sake nazarin Doctor Hamza , kafin yace " bawan Allah lafiya dai ko ? Ba dai wani al'amari bane marar daɗi ya auku da har yasa kake neman Malama Maryam ? Da sauri Doctor Hamza ya girgiza kai kafin yace ' ah ah ba wani abu bane marar kyau , kawai tambayoyi nake so nayi mata akan wata ɗalibar ta da ta koyar wacce aka ce daga baya ta zama kamar 'yar ta saboda kusanci da ta samu da ita , sunan yarinyar Amina . Shiru Liman ya sake yi kafin yace 'Kana nufin Amina Mustapha Dilmari yarinya 'yar Maiduguri ? " ita fa Malam . "Allah sarki yarinyar kirki ce ai Amina , ta koma can garin su a halin yanzu har an aurar da ita sati biyu da suka wuce , Malama Maryam da kake nema ai Mata ta ce , kuma ita ce Malamar Amina tsawon shekaru Shida da suka yi tare , bari na shiga gida sai nayi mata bayani na haɗa ku , amma kafin nan zan so jin ko kai wane ne ? Kuma daga ina kake ? Cike da jin daɗin ganin sauƙaƙuwar lamura Doctor Hamza yace " Malam ai ni ne Mijin Amina bayan haka kuma ni wan ta ne da muke 'ya'yan mata biyu . " Masha Allah ka ce babban baƙo ne da mu , to Bismillah mana mu shiga daga cikin Falona kafin na yi mata magana . Ganawar Doctor Hamza tare da Malama Maryam ya zo masa da wani irin sauyi mai girma da yake sauraren bayanan da take yi  masa game da baki ɗayan rayuwar da Yakaka tayi tare da ita har ma da wanda tayi gidan uwarɗakin ta samy baby da a farko su kayi zaton yayar ta ce , kafin daga baya lokacin da ta faɗa musu haƙiƙanin gaskiyar kome game da ita ,su gane cewa basu da wata alaƙa ta 'yan uwantaka . " alaƙar ta da Samy Baby da duk irin Yaudarar da tayi mata . har yadda daga baya Samy baby take son tilasta ta shiga harkar banza amma ta ƙi yarda da hakan shine ya kawo sanadin komawar ta Maiduguri . Nisawa Malama Maryam tayi tana murmushi ta cigaba da cewa " Abu mafi daɗi da yasa nake yin Alfahari da Amina shine jajircewar ta wajen neman ilmin addini fiye da na boko , Amina ta fara karatun addini bata kai ga sanin ayoyi bakwai na Suratul-Fatiha ba amma sai ga shi cikin shekaru shidda da Yarjewar Allah ta samu cikakkiyar kyakkyawar Haddar izif talatin . " bata san yadda ake yin cikakkiyar Alwala ba a shekaru shidda baya a yanzu Amina daga kan farillai , sunnoni da mustahabbai har makruhi na alwala ta sani , haka kuma sharuɗɗan Sallar ta sun inganta ta kuma san yadda zata yi gyara ga Sallar ta idan ta ɓaci. " Amina ta san baƙi , ta iya karatu da rubutun Arabic ta kuma samu tarin ilmi daga littatafan addini da hadisai masu inganci dan haka ta san dukkanin haƙoƙin Ubangiji dake kan ta . " Alhamdulillah shine kawai abunda zance da Allah ya rataya min nawin tallafa mata ta hanyar samu ilmin addini , ya kuma bani ikon koyarda ita tare da ni da sauran Malaman da ta ɗau ilmi a wajen su , nagodewa Allah da kafin barin ta wajena ta fita daga duhun jahilci . "Halaye da ɗabi'un Amina mafi rinjayen su masu kyau ne ababen koyi , tundaga lokacin da tasan irin tarin zunubin da yake cikin kuskuren da tayi na baya bata sake kwatanta aikata makamancin sa ba , tayi kyakkyawan tuba da irin sa ake son duk wani mumuni ya yi . " babu shakka kayi sa'ar Mata , Allah ya ɗorar da zaman lafiya a tsakanin ku, a ƙarshe shawarata shine kayi ƙoƙarin ganin ta samu cigaban karatun ta na addini kamar yadda ta ke fata a koyaushe watarana ta haddace Alkur'ani Mai girma Dan Allah ka bata dama ka taya ta wajen samun cikar burin ta irin Amina sune Al'umma suke amfana da su . " Ya Rabb lakal-Hamdu ,  Alhamdulillah , Masha Allah . Doctor Hamza yake furta haka fuskar sa ɗauke da wani irin annuri na farin-ciki , har wani irin zillo yake ji zuciyar sa na yi masa . fuskar sa ɗauke da faffaɗan murmushi ya miƙawa Malam Idris ( Mijin Malama Maryam ) Hannu suka yi musabaha , lokacin da yake miƙewa da shirin tafiya , bakin sa ɗauke da duk wasu kalmomin da ake iya amfani da su wajen godiya ga mutumin da ya kai maƙura wajen yi maka Alkhairi . Da farin-ciki su ma suke amsa masa suna masa rakiya , fitowar su tsakar gida ya zira hannuwansa duk biyu a Aljihu , kuɗaɗen ciki da bai ƙirga su ba su ya tattaro baki ɗaya ya danƙawa Sadiq da yake tsaye a gefe cike da ladabi ya sanya hannu biyu ya amsa yana godiya . Sun rabu cikin mutunta juna ya jaa motar sa yana barin unguwar , daga cikin zuciyar sa yake jin ɗaguwar wani abu mai kama da nannauyan dutse da ya danne masa zuciya ya taƙaita masa walwalar sa shekara da shekaru , ji yake kamar an tsamo sa daga cikin wani zuzzurfan ramin da ya faɗa a ciki , yanayin da yake ji bai taɓa tsintar kansa a ciki ba soyayya mahaɗi ce ta rayuwar kowanne ɗan Adam wanda da zarar an samu tangarɗa ta bangaren ta sai rayuwa ta zama kamar lami babu armashi a cikin ta . Tuƙin da yake yi yaji yana neman gagarar sa zuciyar sa na neman abokin taya ta murnar da 'yancin da ta samu , dan haka ya gangara gefen titi ya tsaya , jingina kansa yayi da jikin kujerar motar bai ankara ba ya tsinci kansa da yin murmushi lokacin da ya ji wani ruwa-ruwa na taruwa a gurbin idanun sa ( ƙwallar farin-ciki ) shi kaɗai kawai yake ta murmusawa wanda bai san shi ba wanan lokacin zai zaci mutsa-mutsai ne suka hau kan sa . " Alhamdulillah ,yace yana kai hannu kan wayar da take ajiye a gefen sa ya ɗauka laluben wanda zai ƙira a dai-dai lokacin yake yi , Doctor Suleiman shine wanda ya fara faɗo masa arai domin ya raba farin-cikin sa da shi, saboda sanadin sa ya samu kubta daga ramin da zargi ya haƙa masa a zuci ya faɗa . sai dai tunowa da ya yi da alaƙar da ta taɓa giftawa a tsakanin sa da Yakaka ya sa shi fasa ƙiran sa , daga ƙasan ran sa yake jin tasowar kishin son da Suleiman ya taɓa yiwa Yakaka . Ajiyar zuciya yayi yana jin yadda zuciyar sa ke bijiro masa da wacce tafi dacewa da ya ƙira a lokacin . Tunowa yayi da ba shi da number ta , ba ma shi da tabbacin ko tana da waya,ko babu , shiru yayi jim ! Yana tunanin ina zai samu layin ta ? Yana jin nawin Amnee da Khaalty Rahima ba zai iya tambayar su ba . Rahima ƙarama ita ce ta faɗo masa , yasan muddin dai tana da waya zai samu layin ta wajen Rahima ' Yana ƙiran ta kuwa ta ɗaga , bayan sun gaisa ya ɗan yi gyaran murya kafin yace " Rahima kina da number Mata ta kuwa ? Ɗan shiru Rahima tayi kafin tace " eh Big bro ina da number Auntie Sofiya... " Ba sofiya nake nufi ba Number My Pure Woman nake nema ai tana da waya ko ? Murmushi Rahima tayi lokacin da ta fahimci wacce yake nufi amma dan ta sake tabbatarwa sai tace " number Yakaka ko Big Bro ? "Yakaka ba suna bane ku daina ƙiran ta da wanan sunan ku dai samar mata da wani sunan da ya dace da ita mai daɗin saurare idan ba za'a ƙira ta da Aminah ba. Ya zarce da cewa "ki turo min da Number ta yanzu . bai saurari dariyar da take yi ƙasa-ƙasa ba ya sauƙe wayar sa . Ba'a cika mintuna biyu ba Rahima ta turo number , cikin zumuɗi ya danna ƙiran yana fatan Allah yasa ta ɗaga da sauri . Yakaka wacce tunda ta ji irin zagin da Sofiya ta biyo ta da shi , ta tsorata jikin ta kuma yayi sanyi lakwas daga haka tana iya hango kusancin da suke da shi da Matar sa tunda har tana iya ɗaga wayar sa idan an ƙira , wani sashi na zuciyar ta ma raɗa mata yake cewa duk a gaban sa sofiya ta ƙira ta da Akuya . Hawaye ta ji yana neman zubo mata , ita kam wannan auren nata bata hango jin daɗin sa ba . Jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin,  ta sauƙa ƙasa inda ta tarar Amnee na yiwa Falmata ƙunshi a ƙafafun ta da ƴan yatsu zama tayi tana taya Amnee gyarawa Falmata tsaruwar layin ƙunshin , fuskar ta babu walwala sosai tace " Falmata naso raka ki har ɗakin ki , na mayar da ke saboda ni nayi sanadin tahowar ki , amma ban samu dama ba Yaa Dakta bai barni ba , amma insha Allah idan kin haihu zan je kin ji ko ? Gyaɗa kai Falmata tayi da ɗan murmushi tace " Yakaka ai daman nasan Yaa Dakta ba zai yarda ba  Amaryar sa ta kama hanyar ƙasar Niger rairayin ƙasa ya turbuɗe masa ke .. " ki min shiru , Yakaka ta katse ta tana 'yar hararar ta tare da satar kallon Amnee wacce tayi kamar bata jin me suke cewa , Dafe baki Falmata tayi kafin tace "to nayi shiruna Allah ya kai mu. Daga haka tayi shiru daga ƙasan ran ta tana ji rashin daɗi da bata samu rakiyar Yakaka ba saboda duk guri idan har da Yakaka tana jin wata irin kariya ta musamman daga jiki har ruhin ta . Bayan Yakaka ta idar da Sallar azahar tana zaune akan sallayar wayar ta ta fara ƙidan shigowar ƙira . Da sauri ta miƙa hannu ta ɗauki wayar zuciyar ta na ƙirgo mata waɗanda zasu iya ƙiran ta a dai-dai lokacin , number da ta gani ta sa bugun zuciyar ta sauyawa, take zuciyar ta ta bijiro mata da tambayar "me kuma Sofiya ta ƙira ta sake cewa ? Ko cin mutuncin da tayi mata ne bai ishe ta ba ? Har wayar ta tsinke bata ɗaga ba , a take kuma aka sake ƙira , tsoron ta ya sake ninkuwa da ta tuno ko dai shine yake ƙiran nata ? Kar kuma tayi laifi idan taƙi ɗagawa Dan haka kafin wayar ta kai ga katsewa sai ta ɗaga ƙiran a ɗan tsorace ta kara wayar a kunnen ta tayi shiru . Doctor Hamza da ya ƙagauta da ya ji muryar ta ya saita sautin sa ƙasa kaɗan kafin yace " Hello Wafaa , ya kike ? Shiru Yakaka tayi tana son daidaita nutsuwar ta dan ita gaba ɗaya ma a gigice take da jin muryar sa dan haka sai tace " Salamu Alaikum Yaya Dakta , ba Wafaa bace ba ni ce . Shiru ta ji yayi kamar baya kan wayar ɗan dubawa tayi ta ga yana nan akan layin tsoron kar ya kashe wayar ba tare da ta faɗa masa abunda take son cewa ba yasa ta cigaba da cewa " Daman ina so ne Dan Allah..... " Shiiit ki tsaya mu gaisa Wafaa , ko haka ake gaishe da Masoyi? Saƙato Yakaka tayi da wayar tana jin mamakin sa a take tayi tunanin ko dai bacci yake yana mafarki da wata can wai wafaa ? Dan haka cikin sanyin murya ta sake cewa "Yaa Dakta ni ce fa ? Dariyar da take taso masa ya danne yana sake ƙasa da murya yace "  ke ce wa? Kamar zata fashe da kuka tace " Ni ce fa Yakaka yayar Falmata . Murmushi yayi yana rufe idanun sa cikin ran sa cewa yake " tana son sunan nan tana kuma son ƙanwar ta . " sunan ki ba Yakaka ba , sunan ki Amina kin ji ko wafaa ? Shiru tayi , tana son haɗa kalmar da za ta faɗa a lokacin fahimta da tayi zuwa yanzu ya gane ta kawai walaƙanci ne ya sa shi ƙiran ta da wata wai wafaa , ɓata rai tayi kamar yana ganin ta tace . "Ni dai daman iznin raka Falmata Niger nake nema a wajen ka ? 'Yan uwan mijin ta sun zo zasu koma da ita shine zan raka ta . Wani irin bugu zuciyar sa ta shiga yi kamar tana gaban sa ya tattare girar idanunsa cikin muryar sa da bata cika ƙarfi ba yace " Wafaa me kike son cewa ?  Da auren nawa akan ki za ki tafi har Niger ? Ki je ki ga wannan ɗan.... Shiru yayi yana son dawo da nutsuwar sa da kishi yake neman raba shi da shi nan take , da wani irin sauti yace " baza ki tafi ba kina jina ko ? A tsorace tace " ina ji . . "Good . yace kafin ya kashe wayar sa . Wani irin zafi yake ji a zuciyar sa kan cewa da tayi zata je Niger garin su wannan ɗan iskan sojan har cikin gidan sa kuma ? Alhalin da yau yana da iko bayan duk labarin da Malama Maryam ta sanar masa har auren sa da Falmata a halin yanzu ko Fatima ba zata sake kwana da igiyar auren sa ba , tunani ma ya dunga yi kan me yasa Baa ya ba shi auren Fatima ? Alhalin shi ɗin bai can-canta ba . Ko ma meye shi dai zai killace matar sa daga yin duk wata mu'amala da shi ko dangin sa duk kuwa da cewa yana auren ƙanwar ta ba zai jura ba ya ga ko da kalmar gaisuwa ta sake shiga tsakanin su.( anya kuwa likita ayi haka ?? ) Bai bari maganar da ta faɗa ta ɓata masa farin-cikin sa ba saboda zuwa yanzu yasan wacece haƙiƙanin ta , mace ce mai kyautayi da son kyautatawa mai saurin yarda da yawan sadauƙarwa halinta kenan halittar ta ce shiyasa ya raɗa mata suna ( Wafaa ). Abun da ya ɗan so tayar masa da hankali bai wuce rashin sanin matsayin sa ba a wajen ta ? sai dai ya yarda da kan sa shi ai Namiji ne zai iya sauya ta zuwa yadda yake so ya koyar da zuciyar ta ƙaunar sa da hakan shi zai samar da nishaɗi a zaman su tare da taimakon sassanyar zuciyar ta mai cike da tausayi da jin ƙai . Tayar da motar sa yayi yana nufar gida cikin ran sa cike da ƙudirin zuwa Maiduguri a ƙarshen sati mai zuwa ya fara kafa gwamnatin sa tun yanzu kafin nan da ƙanƙanin lokaci da zai dauƙe ta ta dawo kusan sa . Har zuwa lokacin da ya koma gidan ya tarar da Sofiya yadda ya bar ta , sai daɗuwar damuwa da tashin hankalin da yake iya gani akan koɗaɗɗiyar fuskar ta Kamar wacce take jiran sa yana zama ta zo ta zauna a ƙafafun sa tana kaɗa ido tace " Doctor na har ka dawo ? . "Har na dawo Sofi ta daman ai na faɗa miki ba zan daɗe ba . Murmushi tayi tana raɓa kan ta a kafadar sa ta cigaba da cewa " Doctor na bayan fitar ka na yi mana wani tunani , akan yarinyar nan ƙanwar mu Yakaka take

Chapter 86 of 103