Share this page
? ba yace yana jaan hannun Yakaka su fice daga falon , babu yadda ta iya ta bi shi sai dai suna fitowa suka hango Amnee na tahowa daga sashin Baa , " Yaa Doctor Allah ya kiyaye hanya ya kai ka lafiya , ya kare ka , ta harhaɗo kalmomin cikin sauri tana ƙoƙarin kwace hannun ta daga cikin nasa , kafin ƙarasowar Amnee ya sake ta da sauri ta taka tana komawa ciki , da murmushi ya bi bayan ta da kallo wani irin nishaɗi ne mai daɗi yake huɗa shi . Ƙarfe uku ya ɗau hanyar Abuja tare da sofiya wacce ya biya gidan su ya ɗauke ta dole bayan ya mata jaan ido tare da barazanar barin ta ta cigaba da zama a gidan su na wasu kwanaki da take son yi dai-dai yake da rabuwar su baki ɗaya , jin haka ba shiri ta tattaro ƴan kayan ta ta bi shi, ba tare da ta kula Momy kori sun yi wata sallamar kirki ba saboda haushin ta da momy kori take ji . ASSALAM ALAIKUM MASU KARATU DA FATAN KUNA LAFIYA ? INA GODIYA DA YADDA DAI HAR KULLUM KUKE HAƘURI DA NI . INSHA ALLAH SHAFI NA GABA SHINE ƘARSHEN LITTAFIN MHR DA ZAI BIYO BAYA NAN BA DA JIMAWA BA. NAGODE [2/5, 10:29 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI ( Hargitsin Rayuwa) Umm'muaz 49 MARADI-NIGER Kwanakin da suka biyo bayan bayyanuwar mummunan aikin da Gimbiya maimounatou ta aikatawa Biyamuradi Youssouf , tare da sa hannun Mammadou da Hajiya Mama , Masarautar maraɗi ta kasance cikin alhini mai tarin yawa , kusan kullum aka yi zaman fada da Waziri ne ke jagoranta ba'a da wani batu da ya wuce na sake tattaunawa kan wannan mummunan lamari haɗi da yiwa Biyamuradi Addu'ar samun lafiya tare da fatan dawowar Maimartaba . Da har yau da suke cika kwanaki ishirin da ɗaya basu baro india ba , Amma ana saka ran dawowar tasu a yau ko gobe saboda saƙon yiwuwar dawowar tasu ya iso musu . Akwai labari daga majiya mai tushe cewar gimbiya Siyama tare da ƙanin Biyamuradi Youssouf , 'Bilal wanda shine mai binsa a haihuwa sun fara shirin tafiya India domin cigaba da jinyar sa da har kawo yau babu wanda yasan takamaimai a halin da lafiyar Youssouf ɗin ke ciki . Ta ɓangaren Hajiya Mama kuwa duk yadda ta kai ga sanyawa idanun ta toka ta mustsiƙe ta cigaba da yin harkokin ta yadda ta saba , amma ta gagara domin yadda labarin sa hannunta da na ɗan ta wajen yunƙurin kisan da Matar Biyamuradi tayi masa , ya bazu ba a bakin bayu da hadiman cikin masarautar Maradi kaɗai ba har jama'ar gari da na wasu jahohin labari ya kai musu . Ake kuma kucin-cina labarin tare da sake liƙa masa baƙaƙen sassa ana sake munana sa ba ƙaramin tasiri hakan yayi wajen kassara mata duk wani karsashi haɗi da ɗagawar da take tinƙaho da shi na kasancewar ta matar Sarki . Dan haka gaba ɗaya sai take neman zama mujiya , tsarguwa take da irin kallon da bayun gidan suke mata , gefe guda ga dumuwowi birjik da suka mata ƙawanya , wanda bata saba shiga makamantan su ba , mafi girman su halin da ɗan ta tilo namiji yake ciki wanda yake tamkar ga ƙoshi ga kwana yunwa a wajen ta , domin kuwa tasan muddin Youssouf ya rasa ransa, cikin hakan akwai yiwuwar shima Mammadou ayi masa huƙunci mai tsauri da ka iya kawo ƙarshen shima tasa rayuwar . Ga Maimartaba da bata san matsayin ta takamaimai a wajen sa ba , bayan tonon sililin da Maimounatou tayi mata a gaban sa , gefe guda kuma ga Mairamar sarki da take autar ta sannan mafi soyuwa a wajenta cikin 'ya'ya da tun bayan faruwar wannan lamarin da ta samu labarin kome bayan kuka bata wani taɓuka abun kirki , Rufe kanta take a ɗakin ta da yake sashin uwar-riƙon ta , ( Hajiya Umma ) ta ci kuka ,domin lamarin ya mata tsauri wajen ɗauka duka biyu a lokaci guda , dan kuwa bayan kasantuwar Youssouf yayan ta mafi kusanci da yawan ƙauna a tsakanin su fiye da duk sauran 'yan uwan ta , ta shaƙu da shi tunda ta buɗi ido ta ga kanta riƙe a hannuwan sa , shiga hatsarin rasa shi ba abune mai sauƙi a wajen ta ba . Damuwar ta tana sake hauhawa da hango rugujewar zancen auren ta , tare da ma guntilewar alaƙar su ita da masoyinta da suka ɗibi tsawon shekaru uku suna soyayya wanda yake yaya ne ga gimbiya Maimounatou , uwa ɗaya uba ɗaya gaf ma ake da yanke ranar auren su cikin watannin gaba kaɗan a sha biki , sai ga shi wannan mummunan lamarin ya shata layi a tsakanin su , domin kuwa ko ba'a sanar da ita ba ta san makomar soyayyar su ita da Khaalifa , sannan tun kafin a hana ta ita ya kamata ta fara zare soyayyar sa daga ran ta , bayan abunda ƙanwar sa ta aikata ga Biyamuradi ai babu wani sauran alaƙa mai girma da zai sake shiga tsakanin masarautun nasu biyu . Ba tun yau ba ta riga ta san wasu daga cikin munanan halayen Mahaifiyar su da ita koyaushe huɗubar ta tare da yunƙurin ta bai wuce na ganin ta raba kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ta da uwar-goyon ta tare da sauran ƴan uwan ta da suka haɗa uba ɗaya ba , da ita kuma ko kusa bata ganin aibun su , sannan duk wasu laifuka nasu da hajiya Mama ke faɗin sun aikata ko suna kan aikatawa , ita bata kai ga kama su da ko guda ba dan haka koyaushe take biris da huɗubar ta , tare da toshe kunnuwan ta , ƙaunar ƴan uwanta a jinin ta yake tana ƙaunar su kwatankwacin ƙauna tare da zallar kulawa da su ma suke nuna mata a matsayin ta na ƙaramar ƙanwar su , ga hajiya Umma kuwa ba zata ce kome ba da ya wuce fatan alheri tare da godiya ,riƙo ta mata na haƙiƙa ba irin riƙon ƴar kishiya ba , dan haka take jinta basu da wata maraba da Hajiya Mama , sau dayawa ma tafi kusanci da Hajiya Umma akan ita Hajiya Mama ,( goyo guba ) Amma ace sanadin son zuciya irin na Hajiya Mama duk ta rusa mata farin-cikin ta a lokaci guda ? Gani take kamar Hajiya Umma da sauran ƴan uwan ta duk zasu tsane ta akan laifin Mahaifiyar ta da ɗan uwanta , a tsakanin hakan take yawaita tambayar kanta anya kuwa tayi sa'ar uwa ??? An cigaba da tsare Gimbiya Maimounatou tare da Mammadou a Niamey , saboda rashin sanin halin da Youssoufa ke ciki ya hana a tura su ga kotu , kawo yanzu kuwa Mammadou iyakar nadama ya yita , ko abincin da ake ɗan kawo masa , baya iya ci duk ya lalace yayi duhu , bai taɓa zaton akwai wani lokaci da zai zo yayi danasanin zazzafar ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan sa ba irin wannan lokacin da ya sarƙe cikin sharrin Gimbiya Maimounatou da ta tsaya kai da fata kan shi ya kawo mata gubar da ta ciyar da Youssouf da a zahiri ba gaskiya bane ba shi ya kawo mata ba ,ba shi kuma da wata masaniya akan haƙiƙanin me ya faru ga Youssouf a wannan daren , iyakar abunda ya sani shine yaje gidan Youssouf mintoci kaɗan bayan ƙiran sa da tayi saboda kusancin da yake tsakanin gidajen nasu biyu da wuri ya isa , ƙarƙashin jagorancin gnala da ta tare shi tun a babbar ƙofar gidan ya cimma har falon da Youssouf ke yashe a ƙasa cikin halin fitar hayyaci , a lokacin shi da kansa ya shiga ruɗani ganin halin da ɗan uwansa ke ciki , a ɗimauce ya shiga tambayar gimbiya Maimounatou " Ya mutu ne ? Da gaske Youssoufa ya cimma kushewa tai ? Bai gama tantance da abunda ke faruwa ba lokacin da suka tsinkayo jiniyar 'yan sanda , Kallon-kallo aka yi tsakanin su ukun , da ruɗani ya bayyana a fuskokin su sannan da wani irin sauti Gimbiya Maimounatou tace , " Mammadou ka shigo da ha'inci cikin lamarin mu amma kayi kuskure ka kuma yi shuka a idanun maƙwarwa , muddin kuwa baka yi wani yunƙuri ba tarkon da kayi na iy afkawa har da kai da makusantan ka , Cikin ruɗewa yace , "ki bar surutan banza ki faɗi wanne tanadi kika yi kafin ki aikata wannan aikin domin nayi gaugawar shafe girman laifin ki kafin lokaci ya ƙure miki , ko kin manta Yarima ɗiyan sarki kin ka kashe ? Kafin yin wani yunƙuri mai girma jami'an tsaron da bai kai ga tantance kakin soji ne a jikin su ko kuwa na 'yan sanda ba , suka dunga tururuwar shigowa falon kafin ya farga sun cika falon , bai shaida fuskar ko ɗayan su ba , sai fa Tafeeda da shi kuma tun shigowar sa ya rufu ga Youssoufa bakin sa ɗauke da sallalami gami da addu'o'i . Hanjin cikin sa ya kaɗa lokacin da ya lura jami'an tsaron wajen riƙe suke da bindigogin su da suke ɗane a saitin su shi da gimbiya Maimounatou , tsoro mai girma ya ziyarce shi lokacin da ya farga da tsaka mai wuyar da yake ciki , da dukkanin alamun da suka bayyana ya taka sawun ɓarawo . masaniyar sa ɗaya shine yasan gimbiya maimounatou tana da mummunar manufar kashe Youssouf tun shekarun baya da ta taɓa furta musu hakan shi da Hajiya Mama lokacin da suka yi wata ganawa ta sirri da su da ita wanda a lokacin suka haɗa hannu wajen ganin sun kai Youssouf ɗin ƙasa da shi da Hajiya Mama ba burin su kashe shi ba , ( kashe shi abune wanda ba sa hangowa kansu hanya mai ɓillewa ta nan ) kwaɗayin su tozarta shi suke irin tozartuwar da zata kai shi ga rasa damar sa ta hawa ƙaragar mulki burin su ya bar nahiyar su yayi nesa da sarauta , yayi rayuwa mai cike da baƙin-ciki tare da rashin nasara to ko'ina Mulkin Maradi ya zama na Mammadou . Ga rashin sa'ar su sai ta ritsa da su munafunci shi ai daman dodo ne ubangidansa yake cinyewa , Mammadou ba shi da wata kafar kufcewa daga zargin da yake ciki , Maimonatou kaɗai ita ce ke iya fidda shi ita kuwa bata shirya hakan ba , kafin a raba musu ɗakin da ake tsaron su cikin a cikin sa , babu irin roƙo da magiyar da bai mata ba kan ta tausaya ta faɗi gaskiya , amma tayi funfurus sai yaɓa masa baƙaƙen kalmomi masu cike da raini take yi wanda a lokacin shi basu ishe shi sauraro ba bare yayi hanƙoro akai , nadamar son zuciyar da ya aikata cikin kowanne sa'a guda na sake yi masa dabaibayi . Gimbiya Maimounatou kuwa ? Zuwa yanzu lamura sun fara zuwa saɓanin tunanin ta , dan kuwa har kawo yau da take cika satika uku , sau ɗaya bata ji daga wani nata ba wanda kuma tana da masaniyar tuntuni labari ya je musu , to yaya haka ta kasance mata ? Tana sane ko kowa ya iya kauda idanunsa daga gareta sakamakon laifin da ta riga ta aikata , Abban ta ba zai iya ba , saboda sanin da tayi tauraruwar ta ta ɗara ta kowa haskawa a zuciyar Mahaifin su sumfurin ƙaunar ta kuma mai banbanci ce da ta sauran ƴaƴa , duk kuwa da kasancewar ta ɗiya mace , Tun tana sanya ran za'a buɗo kofa ace ta zo ga Maimartaba mahaifinta yazo ganinta da kansa ,tare da Mahaifiyar ta , daga nan ta san zasu nemi belin ta tana da tabbacin za'a basu idan yaso daga baya sun haɗu a kotu su da mutanen Youssoufa da take jin ba wani nisa shari'ar zata yi ba za'a kawo ƙarshen ta sanin da tayi tasu masarautar ai tafi ta su Youssoufa ƙarfi har ma da dukiya . shiru ya tsawaita babu wani motsi daga iyayen ta . ta sassauko burin ace ko da wani daga cikin tarun yayyunta maza da mafi yawa basu wani cika shiri da ita ba musamman waɗanda suke yan uba , amma duk da haka tana harin ko uku daga cikin ne su zo ko da kuwa ace zasu ƙare mata zagi, ita dai ta yadda su zo su ƙarbi belin ta . Har ta kai cikin ƴan kwanakin nan ta fara burin ina ma da ace ko da wani babba daga cikin masarautar su ne ya zo ganin ta ? ko da ace bai nemi belin ta ba ya jishe ta labari na daga abunda ke faruwa ga iyayen ta da ma masarautar su baki ɗaya da yasa suka yi watsi da ita a cikin wannan maƙasƙancin wajen da yafi dacewa da wajen hora maƙasƙanta daga cikin bayun ta . Jita-jita ya kasance gaskiya domin kuwa a daren ranar Maimartaba sarkin Maradi tare da Hajiya Umma suka dawo cikin masarauta . Da dawowar su bai fi da awa guda ba labarin samun lafiyar Biyamuradi ya kewaye masarautar , inda ake da tabbacin farfaɗowar sa daga magagin ciwo sai dai an yi masa aikin da yasa zai ɗan sake yin wasu kwanaki a can ƙasar India kafin ya warke baki ɗaya ya dawo . Tamkar rana haka masarautar ta ɗauki murna har da ƴan bushe-bushen algaitu na bayyana jin daɗin samuwar lafiya ga Biyamuradin Maraɗawa wanda tamkar hatsarin rasa shi da aka shiga ne ya wanke duk wasu laifukan sa na baya da ake ganin sa da shi tare da haɓɓako da ƙaunar sa a zuciyoyin Al'umma . ruwan ƙiyayyar kuma da ganin aibun sai yayi tsallen alkafira ya wanke Hajiya Mama tare da Mammadou , ta ukun su Maimounatou babu wasu abun aibatawa da ya wuce su lungu da saƙo na birnin na maradi murnar dawowar Maimartaba ake tare da farin-cikin jin cewa Yarima yana samun sauƙi . Siyama wacce tunda Hajiya Umma ta shigo sashin nata da daman ita ma tun bayan faruwar lamarin ta baro ɓangaren gidan su ta dawo ɗakin ta da yake sashin uwar riƙon ta , Ita ta bi bayan Hajiya Umma har zuwa ƙuryar ɗakin ta ta kuma shiga Hidimar abincin Hajiya Umma , tana sauraron duk wasu amsa waya da Hajiya Umma ke yi da 'ya'yan ta da sauran jama'ar ta , da duk dai batu ne kan samuwar lafiyar Youssoufa , cikin wayar ne ta ji Hajiya Umma na lissafa sunayen waɗanda zasu tafi India domin cigaba da zama da Youssoufa na ƴan wasu satika kaɗan nan gaba , ƙannen sa maza biyu kawai ta lissafa bata ji sunan ta a cikin masu tafiyar ba. amma duk da haka zuciyar ta cike take da farin-cikin jin lafiya ta fara inganta ga Mijinta , bayan irin tashin hankali tare da fargabar rasa shi da ta shiga da har ta kai ta ga kwanciya rashin lafiyar sati guda sai da ta fara samun labarin samun sauƙi a gare shi sannan ita ma ta fara gyagijewa . Bayan ta kammala haɗawa Hajiya Umma abincin a can ɗakin ta na ƙurya inda ba wani mai shigar sa cikin bayu sai fa su 'ya'yan ta da kuma makusanta na sosai , fitowa tayi daga ɗakin ta dawo ɗan madaidaicin falon da yake tsakanin ɗakin da sauran manyan faluka ta zauna . Hajiya Umma bayan ta idar da sallah ta ɗan taba abincin sama-sama , sai ta ɗaga waya ta ƙira Siyama , nan take kuwa ta shigo tana rike da hannun Yumna , wacce da shigar su ɗakin ta saki hannun mahaifiyar ta tayi wajen kakar ta da gudu ta faɗa mata akan ƙafafu , Da ƴar dariya Hajiya umma ta ɗago ta tana cewa , " ke zainaba ki ɗagga ni kadda ki ƙarasa min ƙafafu ki sa ni ɗingishi dagga dawowa ta daman yaya lafiyar ƙafar ? Birgima yumna ta sake yi akan ƙafar Hajiya Umma kafin cikin 'yar muryarta mai cike da wayo tace ' Umma na faɗi miki ni suna na ba Zainaba ba suna na Yumna ko Mamaa ? Da murmushi Siyama ta ɗan yi gurfano daga gefe tana ƙoƙarin janye Yumna daga kan Hajiya Umma tace , " Yumna bakya jin magana ko idan baki ɗagga Umma ba gobe ban tahiya dake unguwa . Da sauri ta ɗaga Hajiya Umma ta faɗawa uwar a jiki tana cewa ," kin ka ce wajen Baba na zamu tai ba unguwa ba ? Shiru Siyama tayi bata amsa ba , illa ƙafafun Hajiya Umma da ta fara dannawa a hankali tana mata tausa . Da tausayi a ƙwayar idanun Hajiya Umma take kallon Siyama , sarai ta fahimci yadda Siyamar take a ƙagauce da ta ji halin da Mijinta yake ciki ta kuma ji wani batu kan tafiyar su da aka tsara har da ita a waɗanda zasu ganin lafiyar Youssouf ɗin , sai dai zuwa lokacin tahowar su da Youssouf ya nanata kan cewa kada a taho da Siyama cikin masu tahowa wajen sa , tayi zamanta kawai har zuwa lokacin da Allah zai sa ya dawo yasa aka fasa tafiyar Siyama . Hajiya Umma ta so ƙin amincewa saboda ita tafi ganin dacewar zuwan Siyaman da take matar sa fiye da sauran ƴan uwansa , sannan kuma ita ma Siyamar hankalinta zai kwanta muddin ta gan shi da idanun ta saboda tun a india su na da labarin irin mawuyacin halin da ta shiga na fargabar rasa Mijinta . Sai dai duk yadda ta so Youssouf ya amince da zuwan Siyama ƙi yayi a ƙarshe da ta dame shi ana gobe dawowar su , yana kwance kan gadon sa na asibiti Hajiya Umma da Maimartaba kuma suna daga kan doguwar kujerar da take falon , Hajiya Umma ta sake tada batun zuwan Siyaman , da jin haka yasa Youssouf miƙewa a hankali ya zauna yana ɗan cije baki saboda wajen da aka yanka aka masa aiki a uwar hanjin sa har yanzu bai kai ga warkewa ba cikin kwana biyun nan ne ma yake iya miƙewa zaune da kansa Fuskar sa da tayi fayau ta ƙara yin haske babu walwala , bai yadda ya dubi Hajiya Umma sosai ba yace ," Umma , Dan Allah Siyama kadda ta zou , babu wani alfanu a zouwan na ta . Da ƙaruwar mamakin ta take kallon sa ,muryar ta da ɗan fushi wannan karon tace , " to wai mene ne dalilin ka ? Ina sane fa tunda ka farfaɗo baka yadda kun yi kou da waya ta kirki da yarinyar nan ba dagga ta gaishe ka sai ka ajiye waya , me zai sa ka dunga yi mata haka , ita ai wankakkiya ce bata da wani laifi cikin abunda ya afku . Kan shi ya mayar gefe , muryar sa can ciki yace ," kiyi haƙuri Umma , amma Siyama ma ai macce ce , kaidin macce kouwa abun a gudu ne , hatsarin ta mai girma ne baka sanin abounda ke binne cikin ruhin ta , zahirinta cike yake da ƙarairayi da hilata , Allah kaɗai ya san abunda macce take iya ɓoyewa . A lokacin Maimartaba ya ɗago kan shi daga karatun jaridar Hindustan Times da yake , ya kai duban shi ga Yousouf da yake komawa ya kwanta bayan gama zancen sa , Yunƙurowa Hajiya Umma tayi zata sake yin magana , Maimartaba ya dakatar da ita , fuskar ta a marairaice take kallon sa tana son ya ce wani abu ga Youssouf a lokacin , amma sai bai ce kome ba ya komawa karatun jaridar sa . Ko da suka keɓe shi da ita , ƙorafi ta shiga yi masa kan hukuncin da take tunanin Youssoufa ya yanke wanda bai kamata ba ko kusa laifin da Maimounatou ta aikata ya shafi Siyama . Murmushi kawai Maimartaba yayi ,kafin yace " Ki kwantar da hankali , a ba shi lokaci zuwa lokacin da zai gama dawowa ga nutsuwar sa daga ruɗanin da ya shiga , Macce ai mahaɗin rayuwa ce ga Ɗa Namiji , shi da kansa zai safko . Muryar Siyama ta katsewa Hajiya Umma tunanin da ta faɗa , " Umma babu abunda zan sake yi miki ? Girgiza kai tayi , " babu kome ɗiya ta , sai magana da nake so mu yi da ke , Da sauri Siyama ta gyara zama zuciyar ta cike da ɗokin ko zancen tafiyar ta wajen Youssoufa za'a mata ? tace " To Umma , Da tausasawa a muryar Hajiya Umma ta cigaba da cewa , " Nasan kina son zuwa ki ga jikin mijinki to amma saboda halin da zuciyar sa ke ciki yasa aka dakatar da zuwan naki har zuwa lokacin da zai dawo dai-dai, kiyi haƙuri kin san dai yadda wannan mamagunciyar ɗiyar ta zuba masa dafi a zuci da gangar jiki, to sai a hankali zai koma dai-dai dan ma Allah yayi kwanan sa na gaba da zouwa yanzou sai tashin zance , Allah ya ƙara ɗaura mu akan maƙiyan mu na fili da na ɓoye , kiyi haƙuri kin ji ko ? Da murmushin da ta ƙalato Siyama ta gyaɗa kan ta , tana shafar kan Yumna da har ta fara bacci a jikinta idanunta na kallon ƙasa tace ," Umma Allah ya ƙara girma oumarnin kou abun bi ne a gareni shi kouma Allah shi daɗe shi da lafiya . "Amin ,Amin Siyama Allah shi miki Albarka ya dauwamar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin ku , Umma ta amsa tana mata duba mai cike da so da tausayi , A zuci ta amsa lokacin da take miƙewa saɓe da Yumna a kafaɗun ta tana barin ɗakin , Lokacin da ta shiga ɗakin ta dake falon tsakiya , kwantar da Yumna tayi a kan gado , a hankali ta zame ta zauna a ƙasa ,hawayen da take riƙewa tuntuni ya samu damar shimfiɗowa da gudu , tunanin abu biyu zuwa uku suka fara mata ƙaraƙaina a zuci . "anya ba jikin Biyamuradin bane babu daɗi shiyasa aka hana ta zuwa ta gan shi amma Umma ke ɓoye mata ? Amma kuma ai ta ji sun yi waya da duk wasu makusanta ta kuma tabbatar musu da samun lafiyar sa . " ko kuma ba ita yake son gani ba matar sa Fatima yace a kai masa ? " kadda dai ace abunda Maimounatou ta yiwa Mijinta ya ɗarsa masa tsanar mata da yasa shi gudun su ? idan kuwa hakane babu shakka ba zata taɓa yafewa ɗiyar Agades ba ,da bayan tsawon shekarun da ta kak-kange ta hana ta damar samun gamsasshiyar soyayyar mijinta , ta himmatu wajen hilatar sa da salon soyayyar ta na ƙarya, tsakanin karya da gaskiya har ya aukawa son wata daban ba ita ba , Bayan kuma ga ta ita da ta ɗauki shekaru wajen ƙoƙarin ginawa kan ta matsugunni kome ƙanƙantar sa a zuciyar sa , ta haɗiye duk wani ɓacin rai ta kawar da kai ta danne tasirin kishin ta , amma sai da lokaci ya gabato mata da zata girbi ladan haƙurin ta , sai mummunan nufin Maimounato ya nemi mayar mata da hannun agogo baya ? Runtse ido tayi tana jin ƙauna tare da tausayin Mijinta gefe guda tsoron sake rasa kulawar da ya fara nuna mata take yi . , tunowa da lokacin rabuwar su taki kaɗan kafin tafiyar sa sashin Maimounatou , yadda ya riƙe ta ajikin sa , irin kalmomin da ya furta mata da suka zama tamkar magani ga wani daɗaɗɗan raunin da take fama da shi a rai , da hakan yasa ta jin kwaɗayin son cigaba da samun makamancin daɗaɗan kalmomin sa ya haka , cikin rashin sanin ta mummunan lamari na gaf da afkuwa musu . Buɗe ido tayi tana karanto addu'o'in samun nutsuwar zuci . Washegari da sanyin safiya saƙo ya isowa Hajiya Umma cewa " Hajiya Mama na mata barka da zouwa sannan kouma tana nan tafe zuwa sashin Hajiya Umman , fuskar Hajiya Umma bata nuna wani yanayi ba na farin-ciki ko saɓanin sa tace "a je a ce tana yiwa Gimbiya Saratu Maraba . Zuwa hantsi misalin ƙarfe tara da rabi hajiya Mama ta iso , ƙarƙashin rakiya bayun ta su huɗu ,waɗanda tun

Chapter 83 of 103