Share this page
ta na kai-kawo wajen tantance shi ɗin ne ko ba shi bane ? Juyowar da yayi ya hutatshe da zuciyar ta daga tunanin tantance shi , saɓanin haka zallar farin ciki ta ji yana tunbuƙowa daga ƙasan ranta , tamkar tayi tsalle ta rungume shi take ji a lokacin    Hannunta biyu ta kai tana rufe bakin ta da haƙoranta ke buɗe tana dariya , sai kuma tayi ɗan tsalle tana matsawa daf da shi ta haɗo haruffan sunan sa cikin wani irin sauti mai nuni da ɗoki da farin-ciki da take ciki tace.       " Gha°ddafi ? Kai ne ? je ne peux pas croire mes yeux mon amour ,    Dariya yake lokacin da ya zare baƙin tabarau ɗin dake idanun sa , cike da murnar ganin ta ya kai hannu ya riƙo hannuwanta ya jaa ta yana ƙarasa rufe tazarar dake tsakanin su ya haɗa ta da jikin sa , cike da salon son ya burge ta ya harhaɗo kalmomin da ya shafe tsawon wata guda yana koyon su yace ,      " tu m'as tellement manqué chérie , Bayan sun gama ɗokin ganin juna , Maimounatou ta kasa ɗauke idanun ta daga kan sa duk wani motsin sa ƙara burge ta yake yana sake nutsar da ita cikin ƙaunar sa , Yadda yayi shar da shi yayi gayu ya sake fiddo tsantsar kyaun sa , da cikar zatin sa na matashin Namiji , kasa jurewa tayi ta tambaye shi ,     " Ghaddafi ina ne ka samou dukiya hakka mai yawa har ka sai moto ta hawa , ka gan ka kouwa yadda kayi gayu tamkar ɗiyan saraki wallahi ka burge ainun ,   Ƴar dariya yayi ,kafin yace da ita    " cikin dukiyar amren mu da na fara taru na ɗauki kaɗan na sayi suturu doumin nayi kwalliya na burge ki , kadda samarin jami'a ƴan gayu su kwace min ke , Ba tare da ta damu da ta tambaye shi wacce sana'a ya fara yi ba ta washe ƙaramin bakin ta tana cewa    " Duk faɗin babban birnin Niamey babu namijin da zai iya kwace maka ni Ghaddafi ,   Da murmushi a fuskar sa ya buɗe kujerar motar sa na baya ya shiga fiddo manyan kwalayen da yayi mata birthday gift yana jera mata a gaban ta , Zuciyar ta tana sake bunƙasa da ƙaunar sa take bin sa da kallo bata ƙi ba ace cikin wata mai kamawa a ɗaura auren su . ***** Cikin shekaru huɗu na karatun ta Ghaddafi ya bunƙasa ya zama hamshaƙin attajiri , ya ma ɗauke iyayen sa da ƙannen sa daga Niger ya mayar da su can ƙasar su Mali ya gina musu sabuwar rayuwa ya ƙere musu gida na zamani . Zuwa lokacin ita da kan ta Maimounatou tasan Ghaddafin ta ya sha kwana , ana kuma damawa da shi a harkokin masu dukiya , sai dai ita da kan ta ba zata ce ga takamaimai sana'ar sa ko aikin sa ba , baza ta ce ga inda yake samun kuɗaɗen da yake mata wasa da su cikin kyautuka na bajinta ba da har wasu lokutan takan yi masa faɗan kuɗaɗen sun yi yawa , amsar da kullum yake bata shine        " wannan kaɗan ne dagga cikin dukiyar Amren ki da nake biɗa ina tarawa Maimounatou, Soyayyar su kuwa sai abunda yayi gaba kusan kowa da yasan Maimounatou yasan da soyayyar ta ga Ghaddafin ta , idan aka cire iyayen ta amma hatta ƴan uwanta makusanta kowa ya san sunan sa , sun kuma shaida wasu daga cikin manyan kyautukan da yake yi mata , Haka shi ma ta ɓangaren Ghaddafi tun daga kan iyayen sa da ƴan uwa zuwa abokanan sa tun na farko da suka riga daman suka san da Gimbiya Maimounatou har zuwa kan sabbin abokan sa babu wanda bai san labarin Gimbiya Maimounatou ba , A cikin shekarar ne kuma gwamnatin ƙasar Niger tayi hoɓɓasa kan gagararrun ƴan fashi da makamin da suka addabi baki ɗayan kusurwowin ƙasar ta Niger ta kan kowacce boda guda bakwai da kasar ke da su ta Nigeria, Chad, Algeria, Mali, Burkina Faso, Libya, da Benin. sun hana duk wani ɗan kasuwa shan ruwa ya tsirga masa cikin ƙasa da shekaru biyar , da har suna ne da su na musamman da ake ƙiran su da shi escouade de lions . escouade de lions sun gagari kananun sojoji su waye kuma ƴan sanda ? bare kuma ma'aikatan hana safara da miyagun kaya ,  ƙananan ƙwari a wajen su kenan , Kisa suke tare da ɓarna yadda suka so suka ga dama , gwamnati ta rasa yadda zata yi da su , dayawa daga cikin su ɓoyayyun fuska ne da su babu takamaimai wanda ya san fuskokin su , sannan an gaza gano takamaimai madakatar su da za'a iya taƙile su ta nan . Youssouf Abdoul-Azizou Baskore ,shine sojan da babban hafsin soja na ƙasar Niger ya wakilta a matsayin wanda zai ja tawagar aikin da zai kawo ƙarshen waɗannan gungun ƴan fashi da makamin , lokaci kaɗan bayan dawowar sa daga ƴakin da aka tura su Libya. Cike da zuciyar jarumta da son kare hakkin ƴan ƙasar sa Youssouf ya karbi aikin da aka ba shi , inda ya nemi taimakon haɗin guiwar ƴan sandan ciki da dole sai da taimakon su za'a kai ma nasarar cafke ƴan fashi da makamin . A dai-dai lokacin rayuwa ta yiwa Ghaddafi da Maimounatou daɗi domin watanni uku kaɗai ya rage mata ta kammala karatu baki ɗaya ta bar makaranta , abu na gaba shine ta gabatar da Ghaddafi ga iyayen ta , a ɗaura musu aure daga nan su shilla zuwa ƙasar France da suka zaɓe ta a matsayin kasar da zasu barji amarcin su a can. Kafin cikar watannin wani irin liƙewa Ghaddafi ya yiwa Maimounatou koyaushe yana sintiri tsakanin garin da yake da Niamey , Duk da cewa Maimounatou tana jin daɗin yadda yake yawan ziyartar ta a ganin ta ƙaunar da yake yi mata ne take sake hauhawa a zuciyar sa da daman take tantamar kamar ƙaunar da ita take yi masa yafi wanda yake yi mata yawa , Sai dai yadda yake yawan taɓa ta tare da bayyana mata cewa shi fa a sarari a matse yake da ita yana da muradin ta , lamarin yana damun ta , domin ita ta san bata cika ƙarfi ba muddin akan ƙaunar Ghaddafi ne , sannan.ta ɓangaren gangar jikin ta ma rarrauna ce . Cikin haka abunda take ƙoƙarin gujewa ya auku , shaiɗan tare da tsantsar son da take yi masa ya sa ta bashi kan ta a wani dare , Daga lokacin kuma sai gurɓacewa ta shigo cikin soyayyar tasu domin tamkar busa ake musu ko umarni , koyaushe suka haɗu sai sun yi ta'asa kafin su rabu , a hakan daga zuciyoyin kowannen su niyyar auren juna bata sauya ba , a ganin su zinar da suke ba kome bace tunda aure zasu yi illa ƙarawa juna so tare da ƙoƙarin kiyaye juna daga zuwa ga waɗansu mutanen daban  ( abunda matasa dayawa suke ta'alaƙa ƙazamtatciyar rayuwar su akai , ba kome bane illa tsagoron son zuciya da rashin shan tsabga da ace ana zane matasan mazinatan da duk aka kama da laifin zina a nahiyar mu kamar yadda addini ya tanadar da abun ya ɗan ragu ) . Daren yau bayan sun gama fasiƙancin su a ɗakin otel ɗin da musamman Ghaddafi yake da ɗakin sa ,    Yake sanar da Maimounatou kan cewa tafiya ta kama shi zouwa Benin da zai iya kaiwa tsawon kwanaki goma kafin dawowar sa da zuwa lokacin kwanaki biyu kachal ya rage tayi jarabawar ta,  ta ƙarshe  .    Ba domin ran ta ya so ba suka yi bankwana washegari da safe da alƙawarin zasu dunga yin waya koyaushe ,  ya kama hanya bayan ya ajiye ta a bayan makarantar su . Sun cigaba da yin waya har kwanaki uku bayan tafiyar sa kafin daga baya kuma ta daina samun wayar sa , shima kuma bai ƙira ta ba , ta damu ainun saboda hakan ɓakon lamari ne a gare ta su shafe tsawon wasu kwanaki ba tare da sun yi magana a waya ba ko da kuwa baya ƙasar . Wasa-wasa sai da suka shafe tsawon kwanaki shida babu waya a tsakanin su zuwa lokacin hankalin maimounatou ya kai ƙurya wajen tashi , jarabawar ta ma sai tayi da gaske take iya rubutawa , Bata da aiki sai gwada ƙiran layukan sa da duk take da su , cike da fatan ko Allah zai sa ta same shi , Bayan ta fito daga jatabawar ta ta yau waje ta samu daga can gefe ta zauna tana cigaba da lalubar layin Ghaddafi , amma kamar koyaushe cikin kwanakin duk layukan sa basa tafiya  , Tsumu tayi a zaune idanun ta cike da ƙwalla , hirar da ta ji wasu matasa na yi daga gefen ta ta ɗan ɗauki hankalin ta , inda ta ji suna labari akan jajirtatcen sojan ƙasa Youssouf ɗa a wajen sarkin Maraɗi wanda cikin watanni da basu cika uku ba , a kwanaki biyar da suka wuce tawagar sa da yake jagoran ta ta tarwatsa gungun ƴan fashi da makamin da suka yi mafaka akan tekun rairayin saharar tenere da yake boda tsakanin Niger da Chad ta yankin Bilma dake ƙarƙashin jahar Agades. An kashe mafi yawa daga cikin ɓarayin manya daga cikin su kuma sun gudu , ciki har da shugaban su da ba'a kai ga sanin cikakken sunan sa ba amma bayanai sun tabbatar da cewa ɗan asalin ƙasar Mali ne . Kalmomin yabo iri-iri suka dunga yiwa Biyamuradin maraɗawa , bayan sun gama tsinewa ƴan fashi da makamin suna kuma fatan Allah yasa a kai ga samun nasarar kashe sauran da suka rage ko Al'umma sa yi kai-kawo a tsakanin ƙasashe cikin kwanciyar hankali , Ita bata wani ji abun burgewa ba , idan ba lalacewa ba me yakai ɗan sarki Yarima a yadda ta ji sun faɗa , yin aikin soja bauta ?wannan ai shine a aiki kare ya aiki wutsiya . Miƙewa tayi tana nufar wajen da ɗakin kwanan ta yake sai dai kafin ta ƙarasa ta ji wayar ta na kiɗan shigowar ƙiran Ghaddafi , cike da ɗoki ta daga wayar tana ajiyar zuciya tamkar wacce tayi gudu . Cikin abunda ke ƙasa da mintoci goma sha biyar tayi shiri cikin doguwar ɓakar rigar ta ta rufa hula baƙa a kan ta tare da rufa ɗankwalin rigar da ta kare rabin fuskar da shi tundaga kan ta , ta nufi babban wajen hutawar da Ghaddafi ya sanar mata yana jiran ta a wajen ta je ta same shi . Yadda ta gan shi duk a firgice da ƙananun raunika a fuska da hannuwan sa da suke sarari ya duƙushe tasirin farin-cikin ganin sa da tayi , sai ta shiga tambayar sa kan ko hatsarin mota yayi ? Ko kuwa ƴan fashi ne suka tare sa akan hanya ,? Bai bata takamai-mai ɗin amsa ba a madadin haka wata sabuwar sallama ya shiga yi mata cikin sanar da ita sabuwar tafiyar da yake da nufin yi a yau zuwa France , da yace yana iya kaiwa watanni biyu zuwa uku , Da wani irin yanayi na tsoro take kallon sa , yaya zai tarki yin tafiya haka mai nisa bayan yasan suna mataki na ƙarshe ne na gaf da cikar burin su me hakan ke nufi ? Duk yadda ta so ta masa rigima yaƙi bata dama , dole ta yadda suka yi sallama ,cikin kwantatciyar muryar sa ya cigaba da rarrashin ta kafin wayar sa take danƙe a hannun sa tayi ƙarar alamun shigowar saƙo , yana karanta saƙon ya miƙe a ɗimauce yana raba ganin sa a da'irar wajen hankalin sa baki ɗaya ba'a kwance yake ba , da ido ta bi shi ƙwalla na taruwa mata , yadda ya juya bai ko saurare ta ba , ya taɓa mata rai babu shakka akwai abunda yake faruwa da shi da bata kai ga sani ba , taku biyu yayi ta ƙira sunan sa , a hankali ya juyo yana ɗora ganin sa akan ta tsayayyun idanun sa na bayyana wani irin yanayi na tsoro . " Ghaddafi , kada ka manta da ni zan jira ka koume tsawon lokaci , ta furta hakan tare silalowar hawaye daga kwarmin idanun ta , Daga inda take ta hango yadda laɓɓan sa suka motsa ko da kunnuwan ta basu iya jiyo mata amon sautin kalmomin sa ba ta fahimci cewa cewa yayi ,     " Maimounatou ina son ki . Ƙarar harbin bindiga da ya gifta ta kunnen ta shi yasa ta kusa hantsilawa daga kan kujerar da take zaune ,  kafin ta farga harbe-harbe sun yawaita a sararin wajen da nan take mutane suka kaure da guje-guje , akan idanun ta Ghaddafi ya ɗaga kafafunsa ya taka da gudun gaske yana barin wajen kamar fitar kibiya . Ta miƙe tsaye amma ruɗani ya sa ta koma da ƙarfi ta sake zama tana toshe kunnuwan ta biyu , ta gaban idanun ta takun ƙafafun sa da suke sanye da manyan takalman sa na soji ya wuce da gudun gaske ya dafa baya akan hanyar da Ghaddafi ya bi . Ba zata iya sanin iyakar adadin mintocin da tayi durƙushe a gurin ba, zuwa lokacin da harbin bindugogin ya tsagaita , lokacin ta samu damar miƙewa daga durƙuson da tayi a ƙasan teburin gaban kujerun wajen . Ba tare da ta tantance yanayin da take ciki ba ta fara taku da sauri da niyyar ficewa a wajen , can gefen zuciyar ta na son sanin halin da Ghaddafi ke ciki , sai dai bata saurara ba domin tana buƙatar nutsuwa mai tarin yawa a dai-dai lokacin . Kamar ance ta ɗago kan ta lokacin da ta ɗaga ƙafa tana barin wajen , idanun ta suka sauƙa kan dogon sojan da yake sanye da kakin sa da jini ya ɓata gaban rigar , har yana ɗiga ta wajen hannun sa ,  yana tafe da takun sa na jarumta a hankali ta sauƙe ganin ta ƙasa inda ya riƙo ƙafar mutumin da ya harbe yana jaan sa tamkar kayan wanki , idanun ta suka sauƙa kan fuskar Ghaddafi da jinin da ya ɓata fuskar sa zuwa ƙirjin sa bai hana ta gane shi ba , Duk wasu jijiyoyin jikin ta ne suka tsayawa yin aiki , jinin ta ya daskare , kamar yadda kunnuwanta suka toshe , numfashi kuma ya fara kokawar kufce mata , ƙafafun ta taji suna mata girgiɗi.     " Ya kashe min Ghaddafi , Ya kashe min Ghaddafi . Sune kalmomin da suka ƙwanƙwashi ran ta suka farkar da ita daga suman zaune da tayi , wani irin ihu ta sa mai sauti da ya jawo hankulan tsirarun mutanen da suka rage a wajen da zuwa lokacin daman ma'aikatan wajen ma korar jama'a suke . Babu wanda ya saurari kukan da take yi da ake zaton na firgici ne aka tisa ƙeyar ta zuwa wajen park ɗin . Mutuwar Ghaddafi bata zowa Maimounatou da sauƙi ba domin tamkar hauka tayi , surutai kawai take yi tana sambatun da ba'a wani fahimtar me take cewa , bata rubuta jarabawar ta ta ƙarshe ba hukumar makarantar ta turawa da Maimartaba mummunan saƙon rashin lafiyar ƴar sa , Nan take aka tado da mutane ciki har da manyan yayun ta suka zo Niamey suka  ɗauke ta zuwa gida Agades . Kowa ya ga yadda take yi a lokacin cewa ake gamo tayi , aljannu ne suka taɓa ta, dan haka aka shiga magungunan iska ba ji ba gani , Ganin ana ta banka mata hayaƙi babu gaira ba dalili , ya sa ta rusuna ta bar surutai da ƙiran sunan Ghaddafi , sai ta koma ba un ba un'un , bata iya ci bata iya shan ruwan kirki wanka ma bata yi , Ba'a tsahirta da magunguna ba , aka cigaba da kawo magani iri-iri , na wanka da na sha da na turare , kai har da na shafawa da shaƙawa , Mafi yawa zubda su take yi , ta kuma kasa sanar da kowa dalilin tashin hankalin ta , to cikin iyayen ta biyu wanene ya san Ghaddafi ?? Ya san Alaƙar su ? Babu . Tsawon wata guda ta fara dangana sai kuma rashin lafiya Mai tsanani ya taso ta a gaba , ciwon ciki mai tsanani duk ɗan abunda ta samu ta ci sai tayi aman sa , ga zazzaɓi mai zafi tare da ciwon kai , Kasancewar ta wayayyiyar ƴar jami'a ita da kan ta ta fara bincikar kanta game da sauyin yanayin da take ji a jikinta  , a sirance ta aiki Gnala ta sayo mata abun awun tabbatar da samuwar ciki . Da zaton motsuwar kwakwalwar ta Gnala ta karɓi kuɗin ta sayo mata , Kamar yadda tayi zato gwajin farko ya nuna mata samuwar ciki a jikin ta , Ranar damuwa ta dawo mata sabuwa dal , tayi kuka irin wanda tun mutuwar Ghaddafi bata samu damar yin irin sa ba sai ranar , " ina zata da cikin jikinta tana ɗiyar Martaba ɗiyar Asali ɗiyar sarki ?? Ya zama dole ta rabu da cikin , ina ma da ace aure suka yi ita da Ghaddafi ta samu cikin nan ? Da zata fi kowa murna da samuwar sa , Ita da kanta ta saci hanya ta fita , wani babban ɗakin sayar da magani ta je , bayan ta wadata mai sayar da maganin da maƙudan kuɗaɗe ya ɗau maganin zubar da ciki mai ƙarfi  ya bata , Tun da ta saya maganin sau uku tana yunƙurin shan maganin tana kasawa , cikin satin gaba ɗaya ta sake lalacewa ta rame tamkar wacce take tsananin ciwo , A karo na huɗu ta runtse ido ta haɗiye maganin , ta yi kamar yadda pharmacist din ya faɗa mata , Cikin ƙasa da mintoci arba'in kachal jini ya fara sauƙa mata kafin ciwon ciki mai tsanani ya biyo baya , jini kuma ya ɓalle mata , Kasancewar ta kulle ƙofar falon ta bayan ta kori bayun da suke kula da ita sai Gnala kaɗai ya sa babu wanda ya san irin wahalar da ta sha da irin zubar jinin da tayi daga ita sai Gnala , Da kyar jinin ya dai-daita ciwon cikin kuma ya lafa ta samu bacci , Sai zuwa la'asar ta farka ta ji ƙarfin jikinta duk wasu kasala da rashin ƙarfi irin na masu ƙaramin ciki ta rabu da jin su ,  dan haka tayi wanka ta shirya tana jin raguwar damuwar da take ciki da kaso goma cikin ɗari , Kai tsaye sashin Mahaifiyar ta ta yiwa tsinke , inda ta tarar da ita a babban falon ta tana kishingiɗe bayu na mata hidima , ganin ta ya sa ta miƙe zaune cike da jin daɗi ta rungume ta tana murnar ganin alamun samun lafiyar ta , Duk da cewa ta hango wasu yanayi da bata gane da su ba a tare da ita amma ta danganta kome da larura irin ta jinnu da babu abunda basa sawa . Suna zaune aka hasko fuskar Colonel Youssouf Abdoul-azizou baskore a babban tv da yake kafe a gaban su , ana bayani akan ƙarin girman da ya samu sakamakon samun nasarar kawo ƙarshen gungun 'yan fashi da makamin nan da ake yiwa take da escouade de lions , inda bayan rundunar su ta tarwatsu su daga terene , ya samu nasarar kashe manyan huɗu daga cikin su , ciki har da shugaban su Ghaddafi Yacouba Dango .   Raba hoton aka yi biyu , gefe hoton gawar Ghaddafi ne , gefe kuma hoton Youssoufa ne yana dariya lokacin da ake masa ƙarin girma . ****    Gimbiya Maimounatou ta sanya hannuwanta biyu ta share hawayen ta , kafin tayi ƴar dariya da take nuni da tasowar miƙin ƙasan ranta ta cigaba da cewa " Tun daga wannan ranar na kuɗurci aniyar ɗaukar fansa akan sojan da ya kashe Ghaddafi da hannun sa , nima so nake na kashe shi, so nake na ɗanɗana masa baƙin-ciki irin wanda ya samar a gareni .      " Ban damu da laifin da ake tuhumar Ghaddafi da shi da yasa aka kashe shi ba , a ganina Ghaddafi bai cancanci mutuwa a yanzu ba kome kuwa girman laifin sa , akwai sasauci hukuncin kisa yayi tsanani ga Ghaddafi , mafi girman sashi na raina ma ban yadda da laifin da aka danganta Ghaddafi da yi ba , saboda ni ban taɓa ganin sa yayi kisa a gabana ko satar kayan wani ba .   " daga lokacin na shiga bin hanyoyin da duk nasan zasu taimaka min wajen cimma nasara kan ƙudiri na , a ƙarshe kuma nayi nasarar sanyawa Youssouf so na da har ta kai ga ya amre ni sanin da nayi wannan ce hanya mafi sauƙi da zata kaini ga kashe shi , " ga jin daɗina lokacin da nake bibiyar rayuwar sa ina kafa masa tarko bayan auren mu , sai na fahimci ba ni kaɗai bace ba ke farautar rayuwar sa , ciki har da kai da Mahaifiyar ka Mammadou , babu ɓata lokaci muka haɗa hannu wajen ganin ƙarshen maƙiyin mu , kuma ga shi a ƙarshen ƙarshe mun yi nasara ,   Wata ƴar dariya ta sake yi tana tsare ɗan sanda da ido , tace " wai ya ƙarasa mutuwa ne ko kuwa har yanzu yana shan wuya ?     Wani ƙaƙƙarfan marin da aka ɗauke ta da shi da ya sanya ta yin tangal-tangal tare da giftawar walƙiya a idanun ta ya sanya ta rufe bakin ta ruf , Da wani irin yanayi a muryar Tafeeda yace ,   " Babu shakka kin kasance mayaudariya , azzaluma ban yarda ke kina da ɗigon imani ba a ran ki , kamar yadda kika ce hukunci wanda yayi kisa ko ta yaya ne a kashe shi a irin naki ƙwaƙwalwar mai cike da duhun jahilci , da ke da duk wasu masu hannu cikin wannan mummunan aikin da kuka yiwa Youssouf muddin ya kai ga rasa ransa kamar yadda kuka so , wallahi baki ɗayan ku sai na kashe ku da bakin bindiga ta koda kuwa hukunci ya so muku sassauci , ni sai na kashe ku , sai na ....   Muryar sa ce ta sarƙe jikinsa har tsuma yake idanun sa sun koma ciki tsabar tashin hankali , ya juya da sassarfa ya fita zuciyar sa cike da ruɗani ashe masoyin ka da ka yadda da shi kan iya zama mai farautar ranka ? Da ya tuno irin tsananin son da Youssoufa ke yiwa Maimounatou sai hawaye ya sauƙa a idanun sa , wacce irin zuciya ce haka a ƙirjin Mammadou da Hajiya Mama da zai sa a haɗa baki da su wajen kashe mutum irin Youssoufa shin me ya taɓa yi musu da zafi da ya cancanci ƙiyaya irin haka ? Babu shakka mutum ya tsoraci maƙiyin sa da yake ƙin sa babu wani dalili bayan ta hassada , irin wannan ƙiyayyar mai zafi ce , tsawon zamani baya tasiri wajen goge ta . Yana kai ga ficewa daga harabar ofishin motar su Maimartaba da kansa ta sawo kai dan haka yayi baya da tasa motar tare da sake kashe ta ya fito , Sama-sama suka gaisa da Maimartaba a tare da shi da mahaifin shi kansa Tafeeda , sai kuma Hajiya Mama su uku ne kawai tare da direba , Hajiya Mama tayi firi-firi da tashin hankali ta bi bayan su Maimartaba , Tafeeda ya dafa musu baya yana jin kamar ya shaƙe Hajiya Mama , A ciki kai tsaye suka nemi da a haɗa su da Maimounatou da Mammadou , Bayan shigar su inda suke da har lokacin kowannen su bai rusuna ba , Mammadou yana ganin iyayen sa ya fashe da kuka yana ƙaryata duk wasu kalmomin da Maimounatou ta yi , akan yana da hannu wajen kisan Youssouf ,   " Ranka shi daɗe wallahi ƙarya take min ban san kome ba , bani da hannu wajen mutuwar ɗan ouwana wallahi Abba ƙarya take min , Cike da nutsuwa Maimartaba

Chapter 77 of 103