Share this page
ya dafa kafaɗun ta , cikin kwantatciyar muryarsa marar amo yace , " khaalas Amnee , Dan Allah kar kiyi hayaniya ki bawa kan ki stress kiyi haƙuri kin ji ? Ganin ta ta sauƙe akan sa idanun ta cike da ƙwallar ɓacin rai , jin irin mummunan ƙazafin da Hajja kori ta yi mata a gaban jama'a , zata yi magana ya katse ta " Kiyi haƙuri Ummii mu je ki huta . Hajja kori wacce ta ƙulu da yadda ya juya mata ƙeya yana rarrashin uwar sa alhalin ita tudu biyu take ci a wajen sa na babar sa kuma surukar sa , a fusace tace " Kai Hamza ƙaramin marar kunya munafikin maza , tare da kai watau aka haɗa baki aka munafunce mu kana sane , watau kai gaka mai uwa ko ? To ka tabbatar da cewa sai ka zaɓa tsakanin 'yata da wannan koɗaɗɗiyar shegiyar yarinyar da ake shirin aura maka , ƴar da ba'a san asalinta ba . Bai juyo ba , yace " Momy kori kema kiyi haƙuri Dan Allah . "Amnee mu tafi ɗaki ki huta , yace yana juya kafaɗun ta suka fara taku , " Doctor , Chak ya tsaya lokacin da sautin muryar Sofiya ya doki kunnuwan sa ,da sassarfa kamar ana tunkuɗa ta ta ƙaraso ta zagayo ta gaban su , idon ta da suka firfito da ke bayyana tsantsar firgicin da zuciyar ta take ciki ta tsattsare sa da su , cikin wata irin murya tace " Da gaske za ka ƙara aure ? Kai ne za ka auri yarinyar nan Yakaka ? kuma wai gobe ne auren naku ? Ganin sa ya kai kan Amnee da take raba ganin ta a tsakanin su , fuskar ta na bayyana ciwon da ran ta ke ciki, muryar sa can ƙasa yace " Gaskiya ne Amma ki bar maganar nan daga baya zamu yi . Kewaye ta yayi suka wuce cikin ɗaki , Ukhtee Rahima da take tsaye daga bakin ƙofar ɗakin idanun ta cike da ƙwallar tuno da wata rana mai kama da wannan a cikin wannan falon lamari mai muni ya haka ya faru ta silar dangin Prof da sanadin haka ne rayuwar su ita da 'ya'yan da ta haifa suka faɗa a garari , sai ga shi a yau tarihi yana sake maimaita kan sa sun kuma gwada hakan akan 'yar ta, daga ƙasan ranta take tambayar kanta wai laifin me ta musu ne da suka tsane ta , tsana mai muni ya haka ? Juyawa tayi ta rufa musu baya suka rufo ƙofar . Wani irin zaman 'yan dabaro Sofiya tayi a ƙasa dirshan kafin ta ƙwala wani irin ihun da yasa Rahima da Yakaka hanzarin ƙarasa shigowa falon da suke daf da ƙarasowa daman . " Ƙarya ne , inaa no no wallahi ƙarya ne , Doctor baka isa ka min haka ba , Momy kice mafarki nake dan Allah ? Ta ƙarasa sambatun da take tana miƙawa Momy kori hannu daga inda take kamar 'yar yayen da take son uwar ta ta ɗauke ta, A fusace Momy kori ta ƙaraso wajen , ta fara jaan hannun ta tana ƙoƙarin ɗaga ta , bakin ta har kumfa yake lokacin da take cewa , " sai ki tashi mu tafi ai shugabar 'yan taurin kai marar zuciya , tun farko ai na faɗa miki akwai ranar ƙin dillaci muddin kika yadda kika auri ɗan wannan Annamimiyar matar , amma da yake kafiya ce da ke kika nace kika liƙe masa kika ƙi kowa kika zauna zaman jiransa shekara da shekaru . "to ai ga shi nan kin fara gani kishiyar rana tsaka ,baki da ko darajar da za'a sanar dake bare a miki abunda ake yiwa mata a al'adance idan aka tashi musu kishiya , idan baki bar gindin auren ɗan Amina ba kaɗan ma kika fara gani daga cikin irin ƙiyayyar da zata zuba miki , A haukace Sofiya ta warce hannun ta daga cikin na Momy kori , da ƙaraji a muryar ta tace , " ki bar ni Momy , nace ki bar ni wayyo Allah na na shiga uku Doctor meyasa za ka min haka duk irin kula da son da nake nuna maka irin sakayyar da za ka min kenan ? Wani mummunan tsaki Momy kori ta jaa a fusaace tace , " to kar ki tashi dan uban ubanki ki zauna kina kuka anan , kina sambatun wofi akan wani lusarin yaron da bashi da zaɓin kan sa , shegiya mahaukaciya zauna anan nace , Daga haka ta fice a fusace , wasu daga cikin dangi da suke 'yan kanzagin ta suka rufa mata baya , wasu kuma duuu suka yi kan sofiya wacce take ta rafsa ihu kamar wacce uwar ta da ubanta suka mutu a haɗarin mota . Yakaka wacce duk haukar da Sofiya take yi tana kallon ta , a hankali ta fara jaan ƙafafun ta tana yin baya-baya zuciyar ta kuwa cike da tsoron kar Sofiya ta gan ta , Ai kuwa bata yi nasara ba domin kamar ancewa Sofiya ɗago kan ki karaf ta sauke idanunta akan Yakaka , Wata irin zabura tayi ta miƙe har tana ture matan da suka taru suna rarrashin ta dayawa daga cikin su rayukan su a ɓace yake da irin cin zarafin da suke ganin an yiwa 'yar uwar su , yi mata kishiya ba tare da an sanar da ita ba , sai a wajen bikin ta samu labari babu shakka a wajen mata wannan shine iyakar cin zarafin da ɗa Namiji zai iya yi musu . Kukan kura tayi ta kaiwa Yakaka cafka , da gudu Yakaka ta kewaya ta bayan kujeru tayi ɗakin Amnee dai-dai da murɗo ƙofar da Doctor Hamza yayi ya fito daga ɗakin , Tana zuwa ta shige jikin sa ta ƙanƙame shi , a bazata ya ji shigar sa jikin sa , dan haka ya ɗago kai a firgice dai-dai tahowar Sofiya , a cikin ƙanƙanin lokaci ƙwaƙwalwar sa ta fahimci abunda ke faruwa dan haka ya juya baya da sauri , dukan da Sofiya ta kawo gami da chafkar da taso yiwa maƙogoron Yakaka ya sauƙa a bayan sa , Tun ƙarfinta ta shiga dukan bayan sa da ya yiwa Yakaka rumfa da shi , tana ɗura ashar tare da shan alwashin a kan sai ta kashe Yakaka , Da kyar ya ɓanɓare Yakaka daga jikin sa wacce ta shige masa jiki ta runtse ido gam zuciyar ta bayan bugu ba abinda take yi , addu'o'i iri-iri bata gama wata take kama wata . Ƙofar ɗakin Amnee ta murɗo ta leƙo , lokacin da yake zare Yakaka daga jikin sa , " Menene kuma hakan ? Amnee ta tambaya a tsawace , Yakaka tana jin muryar ta ta juya da gudu ta kutsa ta bayan ta ta tsaya tana kallon Sofiya , tsintar kan ta tayi da kwashewa da irin dariyar nan ta na tsira , da kuma ƙarin ganin yadda Makeup ɗin da Sofi tayi duk ya mata muzu-muzu a fuska ya kwaɓe mata , kamar wata dodo . Ganin Amnee bai sa Sofiya ta bar zage-zagen da take yi ba , sai ma daɗa zabura da take yi tana son kamo Yakaka , wacce har lokacin dariya take yi da gajerun fararen haƙoran ta , Dariyar ta ta shagaltar da Doctor Hamza wanda yake ta faman rirriƙe Sofiya kamar wata tunkiyar da take rawar turke , fuskar sa da ɓoyayyen murmushin da ya barranta da yanayin da yake ciki a zahiri a sace yake kallon Yakaka , yaƙi matsawa daga wajen kamar wanda aka dasa shi banda kokawa babu abunda yake da sofiya . Muryar Amnee ce ta dawo da shi cikin hankalin sa , inda take cewa , " ka jaa ta ku bar nan wajen nace bana son hauka da rashin kunya kana jina ko ? Da ƙarfi ya murɗa hannun sofiya , muryarsa cike da gargaɗi yace " ki nutsu Sofiya meye kike ne haka ? Ki zo mu tafi . Ta tsakanin Mata da yaran da suke tsaye carko-carko suka wuce yana riƙe da tsintsiyar hannun ta Sun zo kusa da sashin sa ta warce hannun ta da ƙarfi , muryar ta tana rawar kuka tace " Ka daina jana Hamza , ina wai za ka kaini ? so nake kawai ka faɗa min gaskiya , dan ni har yanzu ban yadda da abunda yake shirin faruwa ba . Matsowa yayi daf da ita yana satar kallon tsirarun mutanen da suke sabgogin su a harabar gidan yace " Sofiya kiyi haƙuri dan Allah muje ki nutsu na miki bayani.. Da ƙarin ƙarfin kukan da ta take yi tace " Bayani ? Bayanin me za ka min ? Doctor meye bana yi maka a zaman mu na aure da za ka min kishiya da wannan ƙazamar kuchakar Yarinyar ? Kuma ma wai har ka ɓoye min Doctor ka ƙi sanar da ni tun wuri da na yiwa tufka hanci . Kwantar da murya yayi yace " Sofiya wallahi ba ni nace zan aure ta ba Baa da Amnee ne suka haɗa lamarin nan , ki bari zan miki bayani sosai idan mun zauna, yanzu ki bar kukan da kike muje cikin ɗakina ki wanke fuskar ki , kin ga magariba ta gabato bana so na rasa jam'i , Juyawa tayi maimakon ta ɗau hanyar cikin gidan sai ta kama hanyar sashin Prof , a tsorace ya sha gaban ta wannan karon fuskar sa babu alamun wasa yace " Ina za ki ? Ita ma da wata irin faffaɗar murya tace " wajen sa zan je naji dalilin da zai sa ya mun haka , sannan kuma na roƙe shi dan Allah ya warware wannan mummunan ƙullin da yake son yiwa rayuwata , Muryar sa a dake da bayyanuwar ɓacin rai yace " Sofiya ki nutsu ki shiga hankalin ki , iyayena fa ba abun wasan ki bane , naga duk irin haukar da kika yi a gaban Amnee dan na miki uzuri dalilin cewa ke ma an miki kuskure ba hakan ne zai sa ki dunga yin duk abunda kika ga dama ba akan su , ki nutsu nan gaba zan iya ɗaukar mummunan mataki akan ki muddin kika nemi cin zarafin iyayena , Daga haka ya wuce ya bar ta a wajen , wajen famfon dake zubar ruwa ya nufa yana daura alwala , Da saurin da ya wuce ƙima Sofiya ta tasamma ƙofar gidan ta fita tamkar zata kifa , Zuciyar sa babu daɗi ya bita da kallo , wannan tashin hankalin yake gudu daga gareta yasa tun farko ya kasa sanar da ita , sam shi ba mutum bane mai ƙaunar hayaniya . Yana kammala Alwala ya shiga motar sa ya tayar aka buɗe masa ƙofa , yana fita kafin ya dai-daita kan motar a bisa titi ya hango motocin su Doctor Suleiman tare da na wasu abokan sa su huɗu , motoci biyar kenan , a sarari yayi tsaki kafin yace " wannan kuma Uban 'yan didimar sai da ya min gayyar da na ce bana so . Hannu kawai ya ɗaga musu tare da matsa ham , ya bi bayan sofiya wacce ya hango har ta kusa titi . Da kyar ta yadda ta shiga motar ya miƙa ta gidan su , sai dai ko ficewa a layin gidan nasu bai yi ba ita ma ta sake fitowa a cikin motar Momy kori da gudun gaske ta ɗau hanyar gidan gogaggen Malamin ta da ta yadda da shi ɗari cikin ɗari aikin sa na ci , aifa zama bai gan ta ba . Matar mutum bata zama ta wanin sa , washegari da misalin ƙarfe goma na safe taron jama'ar da suka cika suka tumbatsa suka shaida ɗaurin auren Hamza Mustapha Dilmari tare da Amina Muhammad Kalama . Bayan ɗaurin Aure walima ta biyo baya , abokan Doctor Hamza da suka tasamma su ishirin sun sanya shi a tsakiya gami da sauran dangi , bayan fara'a babu abunda yake kamar ba shi bane ya sha ɓacin-rai da jin labarin auren , Shi da kansa bai san takamaimai me yake bashi nishaɗi ba illa yasan wani ɗan tsiron farin-ciki ne daga can saƙon zuciyar sa da ya zata ya mutu tun-tuni yake sabunta kan sa a yau . Ɗan gefe guda Suleiman ya jaa shi bayan ya gama tsokanar sa yadda ransa ke so a ƙarshe yace masa ya kamata Amarya ta fito su gaisa saboda su anjima kaɗan zasu juya . Baya so ko kaɗan Suleiman ya fahimci akwai wani abu marar daɗi a tsakanin sa da ita saboda ko babu kome ita a yanzu wata ɓangare ce ta rayuwar sa ba zai so ya zubda mata da ƙima a wajen wasu nasa ba dan haka yace ," Abokina mu je daga sashi na a ƙira ta ta gaishe ka kai kaɗai amma sauran sa haɗu watarana kawai . " Ayi haka kuwa abokina ? Doctor Suleiman yace da ɗan shakku , hannun sa Doctor Hamza ya jaa tare da cewa "ai anyi ma , suka fara tafiya zuwa sashin sa yana ƙiran Amnee a waya , bayan ta ɗaga yake sanar da ita buƙatar sa na son a turo Yakaka sashin sa zasu gaisa ita da Suleiman . Cike da murnar da tunda aka ɗaura auren lafiya yake mamaye ta , Amnee ta miƙe daga bakin gadon ta da take suke zaune ita da wasu ƴan'uwanta suna tattaunawa ta nufi ɗakin da ta bari a ɗazu Hajje Nadiya tana shirya Amaren a ciki , Tana tura ƙofar idanun ta suka yi farin gani da kyakkyawar farar fuskar ta da yau hasken ta ya ninku har wani sheƙi take , tana ɗaukar idanu iyakar kyau Yakaka tayi sa cikin farar Lafayar da aka naɗa mata mai adon ƙananun flowers baby pink da ash color akan sissilkan yadin da aka mata siririyar doguwar riga da shima launin baby pink , kan ta an naɗa mata ɗaurin ɗankwali simple an soke mata shi a gashin ta . Rungume ta Amnee tayi ta sumbaci goshin ta kafin ta kamo hannuwanta da suka sha ƙunshi irin zanen ƙunshin mutan chadi jazur da su sun yi gwanin sha'awa , da manyan awarwarayen zinaren da Amnee ce ta bata su , suka daɗa fiddo martaba da kyaun hannunwan nata . " da hannu ta yafito Falmata wacce take tsaye daga bakin window da alama akwai abunda yake taɓa ran ta a dai-dai lokacin , taƙi yadda a mata makeup sai yar hoda da man baki masu kyau aka shafa mata a cewar ta idanun ta basu cika lafiya ba bata son makeup , ita ma shirye take cikin wani pink ɗin leshi da aka mata ɗinkin Buba da zane tayi kyau fes da ita an mata ɗaurin ɗankwalin da ya fiddo zagayayyar cikakkiyar fuskar ta da ta sake yin tuɓus-tuɓus tana sheƙi sakamakon gyaran Hajje Nadiya da fatar ta ta karɓa . Haɗa hannuwan su waje ɗaya tayi , tana cewa Falmata ," ki je ki raka Yayar ki sashin Yayan ku Babba zata gaisa da baƙi , idan sun gaisa ki tabbatar kin dawo min da ita hannu na yadda na ɗanka miki ita kin san yau ita tafi lu'ulu'a daraja . Ƴar kyakkyawar dariya Falmata tayi kafin tace " an gama Amnee watau yau ni ce ƴar jagora ba ni za'a jagoran ta ba kai Alhamdulillahi Allah mun gode maka da ka nuna mana wannan ranar, Amnee tana dariya ta roko su har ƙofar sashin ta ko'ina suka gifta ana ga Amarya ga Amarya ana bin ta da kallon sha'awa har da masu yi mata hoto , Falmata ita ta fara yin sallama a ƙofar falon , da aka musu iznin shiga ma sai da ta kai kusan minti guda a ciki kafin Yakaka ta saɓile takalman ta ta sanya ƙafafun ta ciki kan ta a ƙasa ta samu gefe zata zauna daga ƙasa , da sauri Falmata ta riƙo ta dai-dai lokacin da Doctor Suleiman ma yake cewa " Kai kai Amarya ya za ki zauna a ƙasa ? Tashi-tashi ƙanwata yau ai ranar ku ce kamata yayi ma a dunga miki yawo da kujera ta musamman dan zaman ki kin san yau ke da sarauniyar England matsayin ku kai-da-kai yake . A hankali ta ɗago kanta bayan ta zauna akan kujerar da Falmata take kai suna gaisawa da Doctor Hamza jin muryar sa raɗau tayi mata kama da na wanda ta sani , shima Doctor Suleiman yana ƴar dariyar tsokanar ta da yake sauran Kalaman bakin sa suka maƙale masa a maƙogoro ganin fuskar ta ɗauke da kwalliya da sheƙin Amarci bai hana shi ya gane ta ba duk kuwa da cewa ganin sa da fuskar tata sau biyu ne rak , amma ta riga ta zanu a zuciyar sa mafarkin ta a yanayi ya irin haka a gaban sa abune da ya jima yana yi , Sai dai a wannan karon zahiri ita ce a bayyane a gaban sa amma ba a matsayin ta sa ba da kullum yake hari , a matsayin matar aminsa na ƙud da ƙuɗ take , cike da ruɗanin da ya gagara ɓoyewa bayan ta ɗauke ido daga kan sa da sauri , yace " Abokina daman wannan ce Amaryar ta ka ? Daga Yakaka , Youssouf har falmata sai da zuciyoyin su suka sauya bugu da mabanbanta tunaninnika da ya musu dirar mikiya , Ɓangaren Doctor Hamza a take ɓakin-cikin sa ya nemi dawowa sabo abunda yake gudu kenan tun farin farko da kuma ya sashi tsanar ta , cuɗanya da tayi ta yi da mazaje . Da sautin da shima bai ɓoye ɓacin-ran sa ba a daƙile yace " eh ita ce , ki gaishe shi mana ku koma ciki . Muryar Yakaka na maƙyar-ƙyartar da ta ƙarawa Doctor Hamza tabbacin rashin gaskiyar ta ta gaishe da Doctor Suleiman da gumi yake tsattsafowa a goshi , yana share gumin ya amsa da " lafiya lau Aminatu , nayi muku murna kin ji Allah ya sanya Alheri . A ɗan kaikaice Doctor Hamza yake kallon sa lokacin da Yakaka da Falmata wacce jikinta yayi sanyi laƙwas da yanayin da ta gani a tare da su biyun suka fice daga falon . Kafin Doctor Hamza yayi wani yunƙuri Doctor Suleiman da ya miƙe tsaye cikin wani irin yanayin da yake bayyana alhinin da zuciyar sa ke ciki yace " Hamza ka min shigar sauri , why ? Amina da nake baka labari ita ce wannan Abokina ita ka Aura . Da sauri Doctor Hamza shima ya miƙe , kafin yace kome Doctor Suleiman ya sake katse shi cikin yanayin da yafi na ɗazu rauni , ya cigaba da cewa , " Na taya ka murna Abokina babu shakka Allah ya arzuta ka da kamilar Mace mai nagartattun halaye , ina taya ka murna sosai ina kuma yi muku addu'ar samun ɗorewar zaman lafiya babu shakka matar mutum daga gare shi take ... Katse shi Doctor Hamza yayi a mamakance yake cewa ," kana nufin wannan Aminar ita ce Amina , Amina da kake bani labarin ta ? " ƙwarai da gaske ita ce . Shiru su biyun suka yi baƙon yanayin da ya ziyarce su yana samun damar mamayar tunanin su , muryar Doctor hamza ta sake ratso wajen da yake cewa " Abokina Dan Allah ka bani labarin haɗuwar ku da duk wani abunda ka sani game da Amina . Bayan komawar su Yakaka cikin gida gaba ɗaya sai ta rasa sukuni sarai ta gane ko wanene abokin Yaya dakta , shine mutumin da ya dunga bibiyar ta da sunan soyayya tsawon shekaru wanda har Malama Maryam da Lubna sun san shi , sai yau ta tuno rana ta farko da ta fara ganin shi a duniya ranar da suka fara haɗuwa da shi da kan sa Doctor Hamza tare ta fara ganin su , shine wannan abokin nasa da ya ji tausayin su a lokacin da Doctor Hamza yake hora su kan fitsarin da Falmata ta yi masa a office har ma ya basu kuɗi yace su sayi hijabi su suturta jikin su . Sai yau ta gane shi gaba ɗaya , amma yanayin da ta hango a fuskar Doctor hamza kafin barin su falon bayan Suleiman ya nuna ya san ta ya bata tsoro , sanin da tayi daman ita a wajen sa abar tuhuma da zargi ce , tsoronta ya ninku lokacin da tayi hasashen kar Suleiman ya sake dasa zarginta a zuciyar Doctor Hamza . An cigaba da shagalin biki zuwa Yamma aka fara shirye-shiryen tafiya Dinner da dangin Mijin Rahima ne suka shirya saboda su nan Baa baya son ire-iren bidi'o'in baya yarda a kama waje a tafi biki kome za'a yi a harabar faffaɗan gidan ake yi , sai dai fa idan dangin miji ne suka shirya abunsu ko kuwa bayan an miƙa amarya gidan ta ayi ta can . Shiri ake ta yi sosai saboda har Amnee da Khaalty Rahima ma zasu su a karon farko saboda ta roƙi Baa yau ɗaya tal ya bari su tafi tare har da Yakaka da Falmata tunda shi yaƙi yadda a shirya ayi daga Aljihun sa . Albarkacin farin-cikin da yake ji na wannan ranar bai jaa gardama sosai ba yace su je amma a kula a kuma dawo da wuri . Ana gaf da tafiyar bayan isha'i Doctor Hamza ya shigo gidan da tunda ya fita raka abokansa bai dawo ba ya zarce gidan su sofiya wacce tunda aka ɗaura auren take ƙiran sa a waya daga ya ɗaga sai ta fashe da kuka tana ihu tare da cewa sai ta kashe Yakaka , Tun abun na ba shi dariya har ya fara damuwa sosai tausayin ta ya tsirga masa , shi shaida ne akan irin son da take yi masa yana tsoron kar wani abu ya samu ƴar mutane ta dalilin haka dan haka da yayiwa su Suleiman rakiya suka rabu cikin raha da barkwanci sai ya kama hanyar gidan su Sofi Kacha-kacha ya tarar da ita tayi manƙas cikin ƙwayoyin da ta dunga afawa , tun lokacin da labarin ɗaurin auren ya zo ma bayan a jiya sai da ta bi malamai kusan biyar akan lamarin duk kuma suka tabbatar mata kan cewa za'a yi aikin da zai sa a fasa auren a daren kafin gari ya waye , sai dai ga shi babu wanda aikin sa ya ci sai asarar kuɗi da ta tafka . Tun kuma a jiyan ta dunga ƙiran layin Samy baby amma bata samun ta , damuwar ta ta ninku ba adadi . abunda ya mummunan kaɗa masa ƴan hanji bai taɓa sanin Sofin sa na shan kayan maye ba , ashe duk ihun da take masa a waya bata cikin hayyacin ta ? Kwayoyi ta fara sha a sanadin ƙarin auren da yayi ? Ƙwalla ne suka tarar masa a ido yana jin takaicin uwa irin Hajja Kori da baza ta iya tanƙwara ƴar ta ba , tayi ko ta bari , da ya shigo gidan ma bai ganta ba ko tana ina ? oho Haka da kyar ya sha kokuwa da ita tana doddoke shi tana zagin Yakaka wasu lokutan har da Amnee da Baa , haka dai ya daure ya sa tayi wanka ya taya ta shirya yana yi yana rarrashin ta , ya rubuta Allurar da yake son yayi mata ya bawa maigadi ya sayo ya kawo ya danna mata , bayan ya haɗa mata tea ta sha kaɗan tayi bacci . A gajiye liƙis ya baro gidan , zuciyar sa cike da tunanin maganganun da Suleiman ya faɗa masa game da Yakaka

Chapter 81 of 103