Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shigo, ƙarasowa kusa da su yayi, sai da ya ijje ledar daya shigo da ita sannan ya zauna gefen gadon, sai kuma ya tashi ganin idon Ammu na zubar da hawaye. Tissue ya fitar daga aljuhun sa ya hau share mata yana cewa "Anty Maryam na fa ce miki babu abin da zai same ta zata farka, likita ya tabbatar min da haka, kinga ma takeaway nayi muku, bari inbaki na ki, inyaso ita in ta tashi sai taci nata" ya faɗi yana ɗago ledar. Murmushi Ammu tayi masa lokacin da ya ciri takeaway ɗaya, ya buɗe yafara miƙa mata a baki tana ci, shima yana bata yana yi mata labarin da zai sanyaya mata zuciya daga damuwar da take, ana haka Safna ta farka à hankali ta fara buɗe idon ta, juyawa gefen ta tayi jin maganar Yazeed ta wannan gefen. Ba ƙaramin burge ta yayi ba yau ɗin nan dan tsintar kanta tayi cikin farinciki sosai, ganin yadda yake kula mata da farin cikin ta, murmushi take yi sosai tana kallon su, har yagama ba Ammu abin ci, "Anty Maryam ruwa ko tea kike so yanzu? Sai in dafa miki tea yanzu, ko kuma ina ga in haɗa miki duka zai fi ko?" Yazeed yayi maganar kamar Ammu zata basa amsa. "Aa ruwan ma ya yi" Safna tayi maganar ba tare da murmushin fiskar ta ya ɓace ba, da sauri ya juyo yana kallon inda take, ganin yadda take murmushi yasa shima maida mata da martanin murmushin, yayin da gefe guda kuma Ammu itama ɗauke da na ta murmushin tana bin fiskokin kowannen su da kallo. Ta shi tayi ta zauna tana shirin sauka a gadon, miƙewa yayi yana faɗin "ya kike ƙoƙarin tashi kuma bayan kina buƙatar hutu?" "Zanyi sallah ne" ta bashi amsa a taƙaice, "ok let me help you" yayi maganar yana zuwa kusa da ita, tayi saurin faɗin "a'a zan iya" tana takawa, aikuwa rashin ƙarfin jikin ta ya sata yin baya zata faɗi. Da zafin nama ya taro ta kan ta ƙarasa, "kin gani ko? Nasan baza ki iya ba ai" tashi daga hannun sa tayi duk da bai sake ta ba ta ce, "ni dai ka barni in tafi da ƙafa ta" "ƙafar ta ki daba ƙwari?" Yayi mata maganar yana dariya, kallon Ammu tayi taga ta yi ƙasa da kanta, sai kunya ya kamata ganin da alama Ammu taga abinda ya faru ɗazu. Wucewa tayi duk da ƙafar ta ba ƙwari sosai amma ta daure dan kada ya ƙara taɓa ta, sai da dariya ya kusa kuɓuce masa ganin yadda tayi tafiyar tangal-tangal kamar me koyon ta ta ta, sannan yace "Anty Maryam bari in kawo miki ruwan" ya faɗi yana fita daga ɗakin ya nufa kitchen, ruwan gora mara sanyi ya ɗauko sannan ya koma ɗakin. Bawa Ammu yayi saida tayi alamar ya ishe ta, sannan ta rufe ya ijje kan table ɗin dake gefe, lokacin Safna ta fito daga toilet, ta tarar har ya shimfiɗa mata garduma da kuma himar a kai, har da carbi, ɗauka tayi ta sanya himar ɗin ta tada Sallah. Yadda take aiwatar da Sallahr cikin natsuwa ne yasa shi tsayawa kallon ta, ba ƙaramin birge shi tayi ba. Toh fah Hajiya dai sai dai ince miki sorry, domin kuwa ina ga abun ya fara fa😀 ______________________________________________________________________________________________ Part 3️⃣9️⃣▶️4️⃣0️⃣ Har ta idar da Sallar yana kallon ta, tana idar wa ta zauna zaman lazumi, "to malama Safna ai ya ci ace dai an yi sallama ko? Ya kamata kici abincin nan before yayi sanyi" Yazeed yayi maganar ganin bata da niyyar tashi, sosai taji saukar furta sunan ta cikin zuciyar ta, domin kuwa sautin ya fito daban da yadda kowa ke kiran ta. Sai da ta lumshe ido ka na ta buɗe, ji take gaba ɗaya tsoron da take masa ya disashe, kamar an tsige mata daga cikin zuciya, sai da ta gama tasbihi kafin ta miƙe tana naɗe garduman duk da Isha'i ma ya kusa, "zauna nan" ya faɗa yana nuna mata mazauni kan kujera, zama tayi ba musu tana binsa da ido inda yake ƙoƙarin buɗe takeaway. "Yi haƙuri ka ƙyaleni inci da kaina please Yaya Yazeed" ta faɗa masa hakan ganin yadda yake neman miƙa mata cokali zuwa baki, shima ce mata yayi "dube ki fah, har yanzu jikin ki ba ƙwari yayi ba, dan haka banason musu" saida ta juya inda Ammu take taga idon ta ba'awannan gefen yake ba, badon taso ba ta amince. Yana kammala bata abincin ya ɗaura mata da magungunan da Doctor ya bata sannan yayi musu sallama da cewa gobe da Safe zai zo duba su, da kallo Safna ta bisa har ya fice a falon suna idar da sallahr Isha'i Safna ta shiga wanka saboda tsaftace jikin ta ko zata ji daɗi. Bayan ya dawo daga sallah kai tsaye ya nufi haɗaɗɗen bed room ɗin sa, sai da ya watsa ruwa yasa kayan bacci sannan ya zauna gefen gado ya janyo laptop ɗin sa, sai dai hankalin sa ya ƙi tsayawa guri guda, yayin da idanun zuciyar sa fiskar Safna kawai yake gani. Mayar da laptop ɗin yayi inda ya ɗauko shi, ya kwanta yana mai tinanin Safna, "ita ɗin yarinyar kirki ce, duk abubuwan da ake mata bai hana ta taimako na ba, tana da halaye masu kyau, tsawon shekarun nan ban taɓa fiskantar hakan ba sai yau, kash! I forgot ban bata haƙuri ba" shine maganar da yake a zuciyar sa. Sai kuma ya tashi ya zauna yana murmushi a fili yace "gobe zanje inyi mata godiya, zance mata Safna ki yafe min, zan roƙe ta yafiyar abunda na jima ina yi mata na rashin kyautata wa, bazan damu da duk abinda Hajiya za tace ba, sannan daga yau bazan ƙara bari wani yaci zarafin ta ba, wannan alƙawari ne nayi wa kaina, zan zame mata ɗan uwa, zan zame mata majinginan ƙuncin ta da yardar Allah" shine abinda ya faɗi yana komawa ya kwanta, yana mai cigaba da tunanin ta sai murmushi yake kamar tana ganin sa. Ɓangaren Safna itama kusan hakan yake, domin kuwa yadda Yazeed ya bata kulawa yau ba ƙaramin burge ta yayi ba, "dama yana da irin wannan zuciyar? Duk da cewa yana raga min kuma yana taimako na lokuta da dama, amma ban taɓa tunanin zai iya kulawa dani haka ba, ban taɓa tunanin yana da wannan fiskar ba" shine abinda take faɗawa kanta daga zuciya. Juyawa tayi ɗayan gefen da take kwance tana kallon fiskar Ammu, hakan yasa ta sakin murmushi tana tuna kulawan da Yazeed yayiwa Ammun ɗazu, da kuma murmushin daya yi mata lokacin da tace ruwan ma ya isa, "da ma murmushi kada ya taɓa yanke wa daga fiskar sa, sabida ba ƙaramin kyau yake masa ba" sai kuma ta giɗa kanta tana kara cewa "Safna karkiyi saurin tinanin haka, ta yu yayi hakanne kawai dan kin taimake sa shine kawai" duk wannan maganar a zuciyar ta tayi ta. WASHE GARI DA SAFE. Kamar yadda ya ce gurin ƙarfe bakwai ya nufi sashin su, kamar yadda ɗabi'arsu take ko sallama baiba yafaɗa cikin ɗakin, bacci ya samu Ammu na yi, waige-waige ya hauyi yana tinanin inda Safna take, ko toilet take ne? Nan kuwa ya tina yau tana nan tana aikin gida saboda yau Asabar, zuciyar sa ce ta buga bayan ya tina hakan, duk da ba tada lafiya amma Hajiya ta sa ta aiki bayan ko doctor sai da yace abar ta sai sati ɗaya kafin tayi wani abu. Yana gama wannan surutun ya fice yana dudduba ta, haɗuwa da Ruki yayi bayan ta fito daga kitchen da kofin tea a hannun ta, bakinta duk yawun bacci, ido kuwa duk kwantsa, sai sosa ƙeyar ta take yi, saboda barcin ba isan ta yayi ba, dama fitowa break fast tayi tana gamawa ta koma, "keh! Where is Safna?" Yayi mata tambayar ba tare da dogon zance ba. Duk da cewa tayi mamakin sa na neman Safna da yake, da kuma yawan ambatan sunanta daya fara daga jiya zuwa yau amma tayi saurin cewa, "kamar naga fitar ta waje" domin kuwa tasan ƙara tambayar da zai yi mata inba ta yi saurin amsa wa ba mari ne, dan Yazeed ya tsani yayi maka tambaya ko magana ka tsaya ɓata lokaci gurin amsawa, ɗaukar hakan yake da raini. Ba tare da ya kalleta ba ya doshi hanyar wajen, chan harabar ƙofar falo ya isketa tana shara, "me kike yi haka?" Safna da take shara a galabaice saboda rashin ƙarfin jiki ta tsinkayi muryar Yazeed, kuma babu alamar farin ciki a muryar, saurin ɗagowa tayi tana kallon sa a razane, "what are you doing here?" Ya ƙara yi mata tambaya. Duk da cewa tayi mamakin maganar saboda yasan da duk weekend tana hakan amma sai tace "aiki nakeyi" haba ai sai ya fara zuba masifa, "kinsan baki da lafiya amma kike wannan aikin, baza ki iya haƙuri bane? Maza yanzun nan ki ijje tsintsiyan nan ki wuce ciki, kije kiyi break fast ki kwanta". Mamaki ne ya ƙara fa ɗaɗa a fiskar ta, "yaya Yazeed bazan iya ba saboda....!" Ya katse ta "bana son musu ki ijje tsintsiyar nan kiwuce ciki nace, inba haka ba zan iya marin ki" ya faɗi cikin ɓacin rai, "kamar ya ta shiga ciki? Gama aikin tayi ne?" Marwan da ya fito yanzu ya faɗi hakan, shima da mamakin abunda yaga Yazeed ya yi, juyowa Yazeed yayi yana cewa "bata gama ba kuma baza ta gama ba". Yayi masa maganar yana juyawa inda Safna take ya ƙara cewa "tsaye kike har yanzu?" Da sauri ta bar wurin jiki na rawa, ganin yadda fiskar sa yake a haɗe ne yasa ta jin tsoron ya dawo "lallai Yazeed wato so kake kawai kace ka fara son ta" "eh na fara son ta, I love her then what?" Yazeed ya faɗi hakan yana wucewa ciki, cike da zafin rai. Shima Marwan ransa ne ya ɓaci "lallai Yazeed abun na ka ya fara yawa, dole Hajiya taji wannan labarin tun kafin yafi ƙarfin ta" yayi maganar yana komawa ciki shima dan zuwa ɓangaren Hajiya. Yazeed kuwa zuwa kitchen yayi yaga Safna na ƙoƙarin haɗa breakfast ɗin kamar yadda yace da ita, tsayawa yayi yana kallon ta yadda jikin ta yake rawa da kagan ta kasan ba ƙalau take ba, hakan yasa shi cewa "kije ɗaki za'a kawo muku break fast ɗin" tun kafin tayi magana ya bar kitchen ɗin, hakan yasa ta yin ɗakin su dan bata son wani abun ɓacin rai ya faru kuma. Yazeed kuma fitan da yayi yasa masu girki su haɗa mata break fast, Marwan ne ya fito yana kallon inda Yazeed yake zaune a falo, sai da yaji haushi a ransa domin yadda Hajiya take yawan nuna fifita wa tsakanin su, "Hajiya na kiran ka, kuma inaso ka sani, in ka manta intuna maka I'm your brother, dan haka baka da damar yimin kowani maganar da yazo bakin ka" Marwan ya ƙarashe maganar yana kallon Yazeed cikin isa. Sai da Yazeed ya miƙe sannan ya murmusa, irin lallai ɗin nan, yana kallon Marwan yace "a baɗini haka ne amma a zahiri ba haka bane, kasan meyasa? Saboda ba ka kama girman ka, ba ka da tausayi kai ko da yaushe baƙin hali ne a ranka, da 'ace baka da duk wannan ƙila da ka zama yayan na gaske". Cike da ɓacin rai shima Marwan yace "naji duk abinda kace indai hakane kuwa ita kanta wacce ta haif...." ai sai yayi saurin da katawa jin maganar Hajiya tana cewa "wai me Yazeed ɗin ke jira bayan na kira shi?" Tayi maganar tana ƙarasowa, kallon ta dukan su biyu sukayi sannan Marwan ya fita. Allah ya taimaka da fa cewa zai yi, "ita kanta wacce ta haife ka hakan take don a wurin ta na koya" hmm ashe da yau yasha ƙanin tsinuwa wurin Hajiya, cab zuciya za ta sashi ɓaran-ɓarama duk da gaskiya ne, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya shige motar sa. Fannin Hajiya kuwa tana saukowa ta fara aikawa Yazeed wani irin kallo da saida ya kauda idon sa, "kiran nawan ne baza kazoba ko kuwa?" Ta jefa masa tambayar tana cigaba da kallon sa, "Hajiya maganar banza yake faɗamin shi ya hana ni zuwa kiran da kika min" "to na ji! Amma me yasa ka hana shegiyar nan aikin da take yi a duk ranar Asabar da Lahadi? A wani dalili zaka ce ta bari eh?" Ta ƙara yi masa tambayar ba tare da ta zauna ba, "haba Hajiya kamar baki san abinda ya faru da jiya ba? Har yanzu jikin Safna fa bai warware ba, kuma kina ji doctor yace a ƙalla a barta tayi one week tana hutawa, ko makaranta ma so nake ta barshi har ta warware, amma sai tayi aikin gida haka". Kallon mamakin sauyawar sa take matuƙa, sai da ta ɗan ni sa tace "shakka babu Yazeed ka sauya, kuma na ji duk abinda kace, yayi mai tausayi, ah dole na yiwa tifkar hanci, iyyeh!" tayi faɗi tana samun wuri ta zauna, ba tare da ya fahimci inda maganar ta ya dosa ba ya wuce kitchen, ya samu sun gama haɗa komai. Ɗaukar tray ɗin abincin yayi ba tare da yayi musu wata magana ba, ya fice, Hajiya na zaune Yazeed ya wuce da abinci a hannun sa ya nufi side ɗin su Safna, ai batasan lokacin da ta miƙe ba, ta fara muzurai, ba tama sanin abinda bakin ta ke cewa, saboda yadda take zuba masifa, duk da shi Yazeed ba ya ma jin maganar don bata ɗaga murya sosai ba. "Wai yaron nan me yake buƙata ne? Yanzu abinci fa zai kai musu, lallai sai na ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan tsinanniyar yarinyar nan, inba haka ba to ni zan kwana a ciki. Barin surutan tayi ta nufi ɗakin ta, da sauri ta ɗauki wayar ta dake kan miro ta fara duba numbern aminiyar ta Ladingo, bugu ɗaya ta ɗaga kamar me jira, ko sallama Hajiya bata yi ba ta fara magana. "Ƙawata Ladingo akwai matsala fah" "matsalar me kenan Hajiya?" Ladingo tayi tambayar, sai da Hajiya ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya haɗi da zama gefen gado ta ce, "ina faɗa miki Yazeed ya fara ƙaunar shegiyar yarinyar nan, alamu sun fara bayyana, yanzu ni ya zanyi?". "Haba Hajiya me yasa kike saurin zato ne, kece kika sanar dani abinda ya faru jiya, tayiwu ko don hakan ne kawai yake bata kulawa, kema fa kinsan ɗan na ki ba wawa bane duk da kyawun da yarinyar take da amma shi ba class ɗin ta bane, don't worry about criticism". "Kin ga Ladingo yi min hausa na fi gane wa, na rasa gane miki duk da sunan ki na ƙauyawa ne amma kin iya turan ci" murmushi kawai tayiwa Hajiya daga wayar, don ta san ƙawar ta da je fawa mutum baƙar magana kuma ita baigame ta ba, haka dai har suka ka mo wata maganar daban. #Ya kuke tunanin zata kasance a wannan gida cikin 'yan kwanaki masu zuwa? ______________________________________________________________________________________________ Part 4️⃣1️⃣▶️4️⃣2️⃣ Yana isa ɗakin ya tadda Safna na wa Ammu tausa a ƙafa, wato tana ɗan mammatse mata ƙafar ta, suna zaune kan lallausan kafet ɗin ɗakin "ita da ko ƙarfin jiki ba tada amma matse ma Anty Maryam ƙafa take wai" yayi maganar daga zuciyar sa yana ƙa rasowa ciki. Juyawa tayi tana kallon sa har lokacin da ya ijje tray ɗin kusa dasu, -hmm Safna kam akoi kallo fa wani zubin- saurin kauda kanta tayi lokacin da ya dawo da hankalin sa gare su, duk da mamaki ne ke ƙara cika ta a karo na babu adadi dan gane da shi. Sai da ya gaishe da Ammu sannan ya ce "nima yunwa nake ji ban karya ba, zamu iya ci tare?" Yayi maganar kamar da Ammu yake, duk da Safna ba taso hakan ba amma suka ci tare, inda shine ma ya ciyar da Ammu, bayan sun gama ya mayar da tray kitchen da kan sa, tinawa yayi da bai gode mata akan abunda yafaru jiya ba, hakan yasa shi ƙara komawa ɗakin. Lokacin ya tarar da Ammu kan Kujera ita kuma tana shimfiɗa Gado, sai da ya tsaya kamar bazai yi magana ba sai kuma ya kira sunan ta, ƙara maida hankalin ta tayi kansa bayan ta amsa, "am, kin sha maganin ki kuwa?" "Eh nasha tun ɗazu" "ok tom, to jikin na ki fa?" Shima ta bashi amsa da "yayi sauki sosai yanzu" ta bashi amsa tana tinanin meyasa yake tambayar ta haka? Kuma kamar ba abinda yake son faɗa ba?. Saida ya maida kallon sa inda Ammu take ka na yace, "nagode da taimako na da kikayi min jiya" yana faɗi ya juya zai fita, nan yaji tace "nima na gode da kulawan da ka bani" saurin juyowa yayi yana kallon ta, yayinda tayi ƙasa da kanta, murmushi mai ƙara ya saki sannan ya wuce, Ita da bata san sanda tayi masa wannan godiyar ba itama tayi murmushi. Kamar yadda doctor yace Yazeed ya kasa ya tsare Safna ko tsinke baya barin ta ta ɗaga da niyyar aikin gida saidai na ɗakin su, hatta makarantar ya hana ta zuwa duk da ta sanar dashi cewa babu abin da ke damun ta, amma yace ina maganar doctor zai bi, cikin wannan kwanakin koda yaushe yana zuwa ɗakin su Safna, domin ko fita bai cika yi ba, saboda dabara ce ta ya hana mahaifiyar sa da 'yan uwan sa ƙuntata mata har ta gama warwarewa. Ita ko tun tana ɗar-ɗar da shi har ta fara sabawa, saboda ba ƙaramin sauyawa Yazeed yayi ba, zama yake yana musu hira sosai ita da Ammu, wani lokaci har takan taɓa hirar itama, shi da kansa yake mata jagora gurin fitar da Ammu waje, cikin sati ɗaya alaƙa mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Yazeed da Safna, duk da rashin maganar ta. A yanzu Yazeed ya tabbatar wa da kansa haƙiƙa tsawon lokacin nan da kon soyayyar Safna yake, saboda yadda da ya yi nisa da ita yake tinanin ta, hakan yasa shi siyan mata waya domin ko ya koma ɗaki sai ya rinƙa jin muryar ta, duk da kuwa ba wani maganar azo a gani take ba. Hajiya gani tayi abun Yazeed yayi yawa, koda yaushe yana manne da Safna da nakashashshiyar uwar ta, sannan Ruki ko Saleem basu isa suyiwa Safna wata banzar magana ba sai yayi maganin su, da tayiwa Alhaji magana kuma cewa yayi wai to me abun damuwa, rashin kwanciyar hankali ne cikin 'yan kwanakin nan yayi mata yawa hakan yasa ta yi wa Yazeed kira na musamman zuwa ɗakin ta. Bayan ya shigo gaishe da ita ya fara yi cike da girma-mawa haɗi da zama kan kujerar da ke cikin ɗakin, fari t'as sai ɗaukar ido yake, yayin da ita kuma take tsaye kansa, yadda ya same ta lokacin da ya shigo, ɗakin Hajiya zan iya cewa shine ɗakin da yafi ko wani ɗaki a gidan kyau domin yadda aka zuba kayan a latu à ciki. Amsa masa gaisuwan tayi kamar dole, ganin yadda tayi masa ba yadda yasa ba gani bane yasa shi cewa "Hajiya hope are you ok? Ya n'a ganki tsaye ko akoi abinda kike buƙata ne?" Sai da ta jefa masa hararar jin haushi sannan ta fara yi masa magana cikin ƙa ra ji. "Koma dai Me kake tinani can maka, ka sani cewa duk cikin 'ya'yana kai nafi so, amma meyasa ko da yaushe cikin bani kunya kake?" Cikin rashin fahimtar inda zancen na ta ya dosa yace "Hajiya I'm not understand, me kike son faɗa ne?" "Kai ba nason iskanci yimin magana da yare na kana ji ko? Ba cewa nayi kaimin zancen turawa ba" nan ma ta faɗi a hasale. Tana ƙara cewa "abinda nake so da kai yanzu shine, ka raba kanka da yarinyar nan, kada na ƙara ganin ka inda suke, ina ce likita sati ɗaya ya ba ta? to satin yayi, dan haka bana buƙatar ƙara ji ko ganin abu maka mancin wanda kayi cikin satin..." "Hajiya i can't bazan iya ba" ya katseta da faɗin hakan yana miƙewa yayin da ita kuma babu abinda tayi sai kallon sa da take. Cigaba da cewa yayi "cikin 'yan kwanakin nan ne na tabbatar da cewa akoi abinda nakeji a game da Safna, wanda ban fahimci hakan ba sai yanzu, ko baki kira ni yau ba ina da niyyar zuwa in sanar dake...." "Yazeed!" Ta dakatar dashi cikin tsawa hatta idon ta sai da ta rufe. Ba ƙaramin shock yaji ba yadda ta furta sunan na sa, hakan yasa shi saurin ɗago idon sa gare ta, duk da bai kamata yayi mamaki ba, sai lokacin ta buɗe idon ta tana cewa, "kar kaga ina lallaɓa ka fiye da 'yan uwan ka kayi tinanin zan zuba ido akan duk abinda kake so, yanzu menene cikakken abinda kake son sanar dani? Ina jinka faɗa min?". "Hajiya me nene yasa kika ɗauki wannan maganar babba haka? i love her ina matuƙar ƙaunar ta, ba tada mugun hali, sai dai ma..." ta ƙara saurin katse shi tana ƙara yi masa magana cikin tsawa "ya isa! Ai ka riga da ka faɗa min abinda ke ranka, to kasani gwara tun wuri ka janye, saboda ni dai Hajiya Zainab kuma mahaifiyar ka bazan taɓa bari ka auri Safna ba, koda kuwa ita ce matar da ta rage maka kaɗai a duniyar nan". Shima cikin haushin furucin na ta yace "Hajiya kamar yadda nace ina son ta, to inason ta nake nufi, kuma bazan iya rabuwa da ita akan wani dalilin ki wanda ni bansan shi ba" yana ƙarasa faɗa ya fice cike da ɓacin rai, bai taɓa tinanin zai wa Safna irin wannan soyayyar ba, amma a halin yanzu ji yake bazai taɓa rabuwa da ita ba, duk da bai sanar mata ba, bai kuma san cikakken abin da ita take ji game dashi ba. Zama tayi a kan kujera inda Yazeed ya tashi, sai furzar da iskar takaici take daga bakin ta, saida ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya sannan ta fara magana da kanta "ba shakka! hakan na nufin mai afkuwa ta afku kenan? Abinda Yazeed zai min kenan? Duk taka tsantsan ɗin da nake yi duk ya tafi a banza? yanzu wai Yazeed da bakin sa yake cewa yana matuƙar son Safna? So wanda bazai iya rabuwa da ita ba? Acikin sati ɗaya kawai? Kuma duk laifi nane, da ban hana Alhaji sawa ayi gyara a kan ƙarfen nan ba da duk hakan bai faru ba. A ah ba laifi na bane, laifin sheɗaniyar yarinyar nan ne, to wallahi baza ta saɓuba, ba zaiyu uwarta ta aure min miji itama ta auren ɗa ba, dole insan abinyi, ƙorai kuwa". Tana ƙarashe maganar da takewa kanta ta miƙe har zata fita sai kuma ta dawo, ɗaukar wayar ta tayi tana neman numbern Ladingo, tayi kira na biyu amma bata ɗaga ba, ba ƙaramin ƙara tinzira tayi ba, cikin kira na Uku ta amsa, "Haba Ladingo wai ina kika ijje wayar ne? Sai ayi ta kiran ki amma bakya amsa waya?" Hajiya ta hau zuba wa ƙawarta masifa. "Hajiya Zainab ki kwantar da hankalin ki dan Allah, kiran da kikayi min fa ina toilet ne, amma me nene ya sa ki hasala haka?" Ƙara sauke ajiyar zuciya a karo na biyu tayi sannan ta fara ba ƙawar ta labarin abinda ya faru, bayan Ladingo ta gama jin komai tace "kinga Hajiya Zainab nifa yanzu akoi tinanin da yazo raina, to indai har da gaske Yazeed na son ta me zai dame ki..." "bangane me zai dame ni ba? Ko wai bakiji abinda nace

Chapter 10 of 56