miki da kyau bane?.
Sai da Ladingo ta taɓe baki a can gefen sannan race, "to ai baki tsaya na ƙara sa ba, abinda nake nufi shine karki manta fa wannan dukiyar da kuke fa ca ka dashi na ta ne, saboda na mahaifin ta ne, kuma ke da kanki kika sanar dani shekarun da zata fara aiki a kan kamfanonin ya kusa, kuma dai kinsan mijin ki ba hana ta zaiyi ba, dan yana bata kulawa, to mezai hana baza ki bar ɗan ki ya aure ta ba? kinga daga nan sai ku ƙwace ragamar dukiyar gaba ɗaya a hannun ta".
Sai da Hajiya ta ni sa sannan tace "hmmm ba shakka ƙawata maganarki m'a na da amfani, to amma kinsan Yazeed fa, tunda yace yana ƙaunar ta to bazai taɓa cutar da ita ba, kwanan nan ma baki ga yadda yake bata kulawa ba, rannan auta na zuwamin tayi tana kuka wai Yazeed ya duke ta akan yarinyar".
"Komai zai zame mana mai sauƙi idan har ya aure tan, kibari bayan ya dawo daga ƙasar da yake son zuwa sai mu shirya komai, zuwa yaushe zai tafi ne?" Amsa Hajiya ta bata "ina jin cikin watannan zai tafi, kuma zai ɗan jima kan yadawo, dan ina ga zai yi shekara ko fin haka ma" Ladingo ta ƙara cewa, "yauwa to ki bari sai ya dawo mu tsara komai, abinda nake so dake yanzu ki nuna masa kina tare da shi".
Hajiya tace "kina ganin hakan zaiyi?" "Haba ƙawata shekaru nawa muke tare dake, komai fa tare muka ƙulla shi, wannan ma zamu yi nasara kamar baya, ke dai mujira lokaci".
-a haka dai suka cigaba da wasu hirar su wanda ni ban tsaya jin su ba-
Hajiya ta nuna wa Yazeed goyon bayan ta akai, kuma tace zata bashi duk wata gudunmawa, amma tace masa yayi haƙuri da maganar hai izuwa lokacin da zai dawo daga turai, kuma kada ya sanar wa Alhaji har sai lokacin, ganin yadda ta nuna masa amincewar ta akan lamarin yasa shi amincewa da abinda tace.
Haka suka cigaba da hira da Safna duk da bai sanar da ita yana son ta ba, haka itama, domin fa itama fa ta shaida da cewa soyayyar sa ta shige ta, musamman yadda yake bata kulawa, har ta fara jin daɗin zama a gidan domin yanzu ko Hajiya ta rage wasu abubuwan da take mata, Ruki da Saleem kuwa sai harara ne ke rabasu indai zasu haɗa ido da ita, kai ko himar ɗin ta suka hango sai sunja tsaki, domin yanzu basu isa suyi mata wani abunba don Yazeed na nan.
Marwan ne ke mata wani cin kashin, da zarar hakan ya faru gaban Yazeed kuma to fa kusan faɗa suke yi, halin Yazeed ya ɗan fara sauyawa, domin yanzu duk fa inda zai shiga to sai yayi sallama.
#Too 'Ƴan-uwan arziƙi kun dai ji yadda soyayyar Yazeed da kuma Safna ta fara kasan cewa, shin kuna ganin zai kai labari kuwa?
Me Hajiya da ƙawar ta Ladingo suka shirya a baya? Me kuma zasu ƙara shiryawa a gaba?
Me zai faru bayan Yazeed yayi tafiya?
______________________________________________________________________________________________
Part 4️⃣3️⃣▶️4️⃣4️⃣
Marwan ne ke mata wani cin kashin, da zarar hakan ya faru gaban Yazeed kuma to fa kusan faɗa suke yi, halin Yazeed ya ɗan fara sauyawa, domin yanzu duk fa inda zai shiga to sai yayi sallama, hakan ya fara kasan cewa ne wani lokaci bayan ya shiga ɗakin su Safna kamar yadda ya sa ba.
A natse tayi masa bayanin badai dai bane abinda yake yi, sallama abu ne me kyau, idan da so samune ma bayan sallama kane mi izini kafin kashiga, wannan shine abinda manzon Allah (S.A.W) ya koyar, sai da tayi masa gamsashshen bayani sosai, duk da tana jin tsoron abinda zaice mata.
Amma a mamakin ta sai ya karɓi gyaran kuma yayi da nasanin rashin yin hakan abaya ma, yadda ya karɓi laifin sa hakan ya ƙara sanya mata sonsa a zuciya, a yanzu babu wata maganar tsoro tsakanin Safna da Yazeed, duk da har yanzu babu wanda yayi wa ɗan uwan sa bayanin yadda yake ji a ransa, amma alamu duk sun nu na.
Safna sosai take jin daɗin yadda rayuwa ta fara sauya mata, wanda ba kowa bane sila fa ce Yazeed, Yazeed ɗin nan dai wanda a baya take ɗaukar sa kamar dodon ta, wanda ko muryar sa taji sai jikin ta ya amsa, amma sai gashi Allah ya haɗa zuciyoyin su guri guda yanzu, fatan da take shine wannan farin cikin ya dauwama a gare su baki ɗaya, sai dai ta kanji fargaba in ta tuna zancen tafiyar da zaiyi, duk da shekara ne, amma sai take ganin kamar wata hanya ce ta ƙara fa ɗa wa cikin wata matsalar fiye da na baya.
Haka haka har lokacin tafiyar Yazeed yayi, da sassafe yazo dan yi musu sallama, Safna ta sha kuka sosai, kuka ne me cike da kewar masoyin ta, da kuma tinanin halin da zata shiga bayan tafiyar sa, shima da kansa ji yake kamar yafa sa tafiyar, to amma babu da ma, domin tafiyar na da matuƙar mahimmanci à gare sa, lallaɓar ta yayi tayi akan zasu rinƙa chat ko bayan ya tafi, addu'a daga ita har Ammu sukayi masa.
Haka dai ya wuce rai babu daɗi, duk da yayiwa su Saleem warning akan kada ya ji sun yiwa Safna wani abun da bai da ce ba amma baiji daɗi ba, ƙarfe 07:00 daidai jirgin su ta ɗaga sai ƙasar UK 🇬🇧
Sai dai tun bayar tafiyar Yazeed ta cigaba da ansan mugunta daga wurin Hajiya da 'ya'yan ta wanda yafi na da ma, domin sabon fanni suka ƙara buɗe mata ta fannin musguna wa.
BAYAN WATA TAKWAS DA TAFIYAR YAZEED
Safna na zana exam na ƙarshe a jami'an su.
Wayan da ya siya mata tuni Ruki ta ƙwace shi, kuma ba tada bakin magana,Yazeed kuwa hankalin sa ya tashi lokacin da ya dena samun Safna a waya, idan ya tambayi su Hajiya kuma cewa suke basu san me dalilin ba, ƙila ma blocking ɗin sa tayi, a haka dai har yade na tambayar su ita. Ya ƙara zama ko yaushe ba tada aiki sai hawaye ko kuka, shi kuma Alhaji ba sa idon sa yake akan al'amuran ba
Musamman Hajiya tayi takanas zuwa gidan Ladingo. Gidan Ladingo ba wani na azo a gani bane, domin gidan gadon 'ya'yan ta ne, shi kuma mijin dama ba wani kuɗin kirki yake da ba, dan duk abinda zataci ma 'ya'yan ta maza ne masu kawo mata, ita yanzu bata da aiki sai musguna wa matan yaran ta, duk da ba gida ɗaya suke ba, amma tana matuƙar ta kura musu,
Ladingo da Hajiya ƙawaye ne tun suna 'yan mata, kuma masu mugun hali, wanda hakan ya bisu har izuwa girman su, Ladingo tana zuwa gurin boka don yanzu ma yiwa 'ya'yan ta take akan kada su kula da matan su sai ita kawai, abunda Hajiya bata sani ba Ladingo kishi take da ita, yadda take zaune gidan dukiya tana fachaka ga shi kuma ba ta bata komai, dan dama Zainab maƙon tsiya gare ta, ƙila da badon ta su tazo ɗaya ɓangaren mugunta ba da ba sa tare.
Suna zaune a falon ta bayan Hajiya ta ɗan taɓa kayan marmarin da aka kawo mata sai ta fara cewa, "kinga Ladingo nifa ba na tinanin shawara akan Yazeed ya auri Safna hanya ce mai ɓillewa, dan haka ni dai na samo wata shawarar, in tura ta can wani wuri da niyyar zataje gurin dangin su, kinga daga can sai musan abinda za muyi mu kora ta karta dawo, inyaso lokacin da ya dawo dole ya haƙura in bai ganta ba, kuma maganar dukiya kuma ai ta zama na wa, koya kike ganin shawarar?"
Sai da Ladingo ta sauke ƙafar ta da ta ɗora kan ɗaya ƙafar sannan tace "shawarar yayi to amma kinsan dai zata dawo, tunda ba haukacewa tayi ba, ko kuma ta mutu" "kinga Ladingo nifa bana son maganar mutuwa kuma kin sani" sai da ta murmusa ka na tace, "hmm Hajiya Zainab kenan, ke dai kiyi muguntar ki amma banda kisa?" Hajiya tace "to kinga laifi na? A dai illata mutum banda kisa kada zunubin yayi yawa ah toh".
"To ma duk ba wannan ba, yadda za'a kora tan da baza ta dawo ba yakama ta muyi tinani a kai yanzu, kuma dai ke baki cika son harka da bokaye ba yanzu ya za'ayi kenan?" Hajiya ta amshe "ai dole yanzu na amince amma fa inaso sai bayan Alhaji ya yi tafiya kafin nan, dan ya sanar da ni shima za shi ƙasar waje ko ista ko me?" "Istanbul kenan ai ƙasar Turkish ne" Ladingo tayi maganar.
Hajiya tace "yauwa nan, shima zai ɗan jima, dan haka nake son mu aiwatar da komai bayan shima ya tafi, wannan karon ko gurin bokan ne aje nidai insamu biyan buƙata, saboda wallahi ina ga indai Yazeed ya auri Safna bansan yadda zanyi ba, ke wallahi gwara na ƙare rayuwa ta a nakashe akan hakan ta fa ru".
Giɗa kai Ladingo tayi tana mai ƙara jinjina tsanar da Hajiya take wa wannan Yarinyar sannan tace "kar ki damu kedai ki bani isashshen kuɗi ta yadda za'a miki aiki ba wasa shine kawai" "kar ki damu indai kuɗi ne baki da matsala, zanbaje su kamar yadda nakeson amin aikin" murmushi Ladingo tayi tana jin daɗi a ranta koba komai hanyar samun kuɗin ta yayi, domin kuwa sai tasan yadda zatayi ta tatse Hajiya ko kaɗan ne itama ta lasa rabon ta.
Sai da suka ƙara tattauna wasu abubuwan yau ma sannan Hajiya ta koma gida.
WASHE GARI.
Bayan sun fito daga exam kafin su ƙara komawa Raheena ce ke tambayar Safna dalilin sauryawar da tayi sosai, wanda ke son ya taɓa karatun ta. Duk da ba yau bane tambayar da tayi mata na farko, ganin yauma bata niyyar bata amsa ne yasa ta yin fushi tana cewa "shi kenan besty na daina tambayar ki damuwar ki daga yau, tunda ban cancanci in sani ba, kuma nima bazan ƙara sanar dake komai game da ni ba, tunda a yamzu bani da wanni mahimmanci à gare ki, thank you".
Ta faɗi tana ƙoƙarin tashi daga kan ɗaya daga cikin kujerun hutawar makarantar, saurin riƙo hannun ta Safna tayi tana marai-raice mata fiska, "please sit my Rahee" ba tare da tayi magana ba ta zauna fiska a haɗe, cikin sigar rarrashi Safna ta fara magana "Raheena kar kiyi fushi please, dalilin da yasa naƙi sanar dake damuwa ta bakomai bane sai sanin halinki da nayi, nasan zaki ɗaurawa kanki damuwa ne sosai, shiyasa badon banason ki sani ba".
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "amma kinsan rashin sanar dani ya fi saka ni cikin damuwa, kwanan nan Momy take tambayana wai meyasa na sauya? Ni kuma nace mata 'yarki Safna ce ke sani cikin damuwa" ƙaramar dariya Safna tayi wanda har kyawawan haƙoran ta suka bayyana tace "wato dai na sawa Momy ɗiya cikin damuwa?".
Dariya Raheena tayi tana cewa "kinji yadda hausar ki ta fito kuwa? Kamar bahaushiya" "to dama ni mecece yanzu ai hausawa kun ƙwace ni" Raheena ta ƙara yin dariya tace "Allah? Kenan yanzu ba kyajin fulatan ci?" Tayi murmushi ta bata amsa "inaji amma yaushe rabon da inyi, tun fa kafin Ammu ta fara rashin lafiya".
"Allah sarki to yanzu dai tell me abinda kesa besty na cikin damuwa?" Sanar da ita duk abinda ya faru tayi, banda soyayyar Yazeed tun da dama Raheena tasan dashi, tana gama sanar da ita tace "hmm wallahi Safna ni na ƙosa bawan Allahn nan ya dawo, koda yake koya dawo babu abin da zai gane tunda nasan ba sanar da shi zaki yi ba".
"Raheena kenan taya ya zan haɗa tsakanin ɗa da uwa, ko kuma tsakanin sa da 'yan uwansa ba abu mai kyau bane" "eh ai dama na sani ke adila ce, amma ni kam zanso inga auren ki da Yazeed wallahi inga wai Hajiya suma zatayi ko mutuwa?" Sai da Safna ta juyo ta kalle ta tace, "nifa bana tunanin hakan zai faru, kuma bai sanar dani yana sona ba".
"haba Basty wani sanarwa zaiyi bayan kin fiskanci duk abinda zuciyar sa ke son isar wa? Kamar yadda kema kika isar da na ki, Allah na tare dake insha Allahu komai zai wuce, inaji a jiki na zaki zamewa su Hajiya abinda basu taɓa tinani ba, kuma duk abinda suke miki sai ya koma kansu by the grace of God" da amin Safna ta amsa suka tashi suka wuce class.
Bayan Alhaji shima yayi tafiya Istanbul, Hajiya ta samu dama dan aiwatar da abunda take buƙata, Safna ta shiga tashin hankali lokacin da Hajiya ta sanar da ita cewa wai dama Alhaji nason sanar da ita ya manta akan zata je gurin dangin mahaifin ta da suke Nijer, dan kai musu ziyara, dan haka ta shirya jibi za ta tafi.
Ta roƙi Hajiya da tayiwa Dady magana akan in ta tafi bamai kula da Ammun ta, amma Hajiya sai rufe ta da masifa tayi, wai so take taƙi bin umarnin sa saboda bashi ya haife ta ba? Bayan duk kulawan da yake bata fiye da 'ya'yan da ya haifa? Ko gidan kango ne babu mutanen da suke a ciki bere su kula mata da mahaifiyar ta ta?.
Haka ta sun kuyar da kai ganin Hajiyar nason kai mata bugu, washe gari haka ta zana jarabawar ta na ƙarshe badon tasan abinda ta za na ba, don gaba ɗaya hankalin ta baya kan komi sai tinanin da yayi mata zaune a zuciya, koda ta sanar wa Raheena itama ta shiga kotankwacin yadda Safnan ta shiga, amma ya zatayi tunda ba tada hanyar ceton ta, don wani lokaci ta kan ji haushi idan ta tuna yadda Safna take azabtuwa a gidan su, ita kuma ba tada hanyar tai maka mata.
RANAR TAFIYA.
Doguwan riga atamfa da kuma gele mai faɗi Safna ta sa, tayi kuka sosai kamar ranta zai fita, ita ma Ammu hawaye masu raɗaɗi ne ke ta zarya a kumatum ta, ba tada bakin magana da ta sanar da 'yarta cewa mahaifin ta baida wasu 'yan'uwa a Nijar, amma ina, riƙe hannun Safna tayi sosai kamar yadda itama ta riƙe na Ammun.
"Ba shakka! Naga alama dan kin ga ina shige miki gaba akan tafiyar nan shiyasa kike min iskan ci ko Safna? Tun yaushe aka ce miki lokacin tashin motar na ku ya kusa? Shikenan baza ki dawo bane in kin tafi? Dazaki tisa uwar ki a gaba kina kuka?" Hajiya Tayi maganar tana shigowa ɗakin, wanda ta daɗe bata taka ko ƙofar shi ba.
#Hmm ana wata ga wata, kai amma muguntar Hajiya sai dai addu'a, koya zuwa Nijar zai kasance?
______________________________________________________________________________________________
Part 4️⃣5️⃣▶️4️⃣6️⃣
Sai da ta rungume Ammun ta sannan ta fara ja baya a hankali tana jan akwatin ta tana ci gaba da kuka har suka bar ɗakin, sai da Hajiya ta gallawa Ammu harara tana ayyana abinda yakamata tayi mata itama a ranta sannan ta fice, direba ne ya amshi akwatin yasa shi a bayan mota Hajiya na jadda da masa kada yabar wurin har sai yaga tafiyar su Safna.
Haka kuwa akayi don tunda ya ijje ta kuma ya sauke mata jaka bai matsa a wurin ba. Wai Safna 'yar gidan Mai daraja ce zata yi tafiya a mota, motar ma irin lalatattun nan, wanda yaran Hajiya ko a mafarki baza su yarda da hakan ba, koda yake dama ba tafiyar Allah da Annabi bane.
Ana cikin loda kayan mutane a motar tafiyar wayan direban yayi ƙara, Ruki ce ta kira sa take ce masa ya zo tana da buƙatar shi, akoi inda take son zuwa, koda ya fara sanar da ita abin da Hajiya tace, sai cewa tayi wallahi inbai zoba sai ta sa ankore shi, kuma sauran ya faɗawa Hajiya ta kira shi, Dan dole yabar wurin, yabar Safna ta rafka uban ta gumi.
Motar baza ta je Nijer kai tsaye ba, a ƙalla sai ta canza mota ko sau ɗaya ne kafin ta hau na zuwa cikin Nijar ɗin, amma Hajiya tasan yadda tayi aka nuna wa Safna direct zuwa Nijar ne, ita kuma ba sani tayi ba bare tayi tinanin da wata a ƙasa, ita da daga gida sai makaranta? Ko cikin Kadunan bata taɓa zuwa wuri mai nisa ba bere barin gari.
Babu abinda take juyawa a hannun ta sai dubu biyar ɗin da Hajiya ta ba ta akan na abincin hanya, da kuma 'yar takarda wai adreshin da zata sauka ne, ta rasa meyasa Hajiya ta nuna tana son tafiyar?. Buɗe zip ɗin akwatin tayi ta sanya papern da kuma kuɗin a ciki tunda ba jakar hannu ta riƙo ba, tana zaune gefen har aka gama lodi, saiji tayi ana maganar azo ashiga mota zata ta shi, da sauri ta shige ba tare da ta lura da ba'a saka akwatin ta aciki ba, saboda tsabar tinanin da take ciki.
Bayan mota ta fara tafiya kusan minti talatin dan har anfara shiga dajin fitar gari, lokacin ta tuna ba a saka mata akwatin ta ciki ba, to kuma adreshin fa? Ai nan ta fara yi wa mai motan magiya da ya tsaya ta manta jakar ta, da ƙyar ta samu ya tsaida motar, mutanen ciki kuma suka fara mi ta, su baza su tsaya jiranta ba, ba tada hankaline da baza ta tsaya ta kula da ansa mata kaya a mota ba har mota ya tashi? Kowa dai da abunda yake faɗa.
Ƙarshe dai haka aka sauke ta su kuma su kayi gaba, sai lokacin ta ga ashe a daji aka sauke ta, rasa abinyi tayi domin babu abinda yake hannun ta, tana cikin tinanin abinyi kunnen ta ya fara jiye mata kamar sautin maganganu can ciki ciki.
Maida hankalin ta guri ɗaya tayi dan ta tabbatar da abinda take ji, "kamar, kamar ta cikin dajin nan ne nakeji fah" tayi wa kan ta maganar tana duban inda take kyautata zaton nan ne ake haya niyar, kuma da dukkanin a lama masu wannan surutu suna can cikin dajin.
"Bari inje induba" Ta ƙara yiwa kanta magana, ba tare da ta jira zuciyarta ta bata yaƙinin shiga ba, ta fara sanya ƙafa ciki, tana kan tafiya a ɗar-ɗar ta ga wata baƙar mota duk ta dagargaji, da alama accident mai muni motar tayi, sai da ta jinjina kan ta yanzu wannan hatsarin bil'adama ne su kayi, ko sun fita da rai? Ta yi maganar a zuciyar ta cike da far-gaba, -wannan motar ta su Zilla ce lokacin da sukayi hatsari ta wun tsula wurin, gawar su kam ba abun magana bane, don ko alamar sa babu-
Barin wurin tayi tana ci gaba da tafiya sai dube-dube cikin dajin ta keyi, duk da har yanzu daga nesa take jin sautin, zuciyar ta na yi mata gargaɗi a kan ta fice daga wannan dajin, amma sai take jin tana da buƙatar zuwa dan ganin me mutane suke yi cikin daji haka? Sannan me yasa suke magana da ƙarfi? Koda itama tasan da ba don kunnen ta da jiye-jiyen magana koda daga ne sa ba ne, da ba abunda zai sa taji hakan.
Tun tana hango kan hanya inda aka ijje ta har ta dena hangowa, Tafiya mai nisa tayi dan harta gaji sosai amma har yanzu bata ƙa rasa inda take jin sautin ba, bata sa re ba dan tafiyar ta cigaba da yi haɗi da waige waige, domin ko kukan wani tsuntsu taji sai zuciyar ta ya tsinke, amma fa sai kace wacche aka sa.
Ta samu nasarar isa gurin mutanen, amma duk ta bi ta galabai ta, dan da ƙyar take fitar da numfashi, laɓewa tayi a bayan wani bango wanda yake kewaye da ciya yi, dan da ba don sun shagala da wasu maganganu ba da babu abinda zai hanasu jin alamar zuwanta, koda ace baka tawar da mutane a wurin ba, zaka iya tabbatar da wannan gurin bana ƙalau bane.
Saboda yadda aka daddasa duwatsu da kuma banguna suka kewaye wurin, duwatsun jajaye ne sai bangwayen kuma kewaye suke da ciyawu kore shar, mutanen suna da yawa, dan zasu kusa talatin, kuma gaba ɗayan su sanye suke da fararen tufafi, kamar sababbin gawawwaki, sai ƙyalle baƙi da suka rufe fiskar su banda ido, tsaye suke gaban wata shirgegiyar Bishiya baƙa ƙirin kamar ansha fa mata baƙin penti.
A tsorace Safna take binsu da kallo, saboda gaba ɗaya ba suyi kama da mutanen ƙorai ba, ɗaya daga cikin su ne yayi gefe, wanda ɗazu bata hangesa ba, ƙatoton mutum ga jiki ga kuma tsawo ya haye kan wata doguwar dutse wacche akayi mata rubutu wanda ita kanta Safnar bata fiskan ci wani iri bane, tsayawa akai yayi yana duban sauran mutanen da ƙananun idanun sa, sai dai shi na sa baƙin ƙyallen mixed da ja ne ruwan kafirai, wanda haka ke iya nuna maka shine babba a cikin su.
Magana ya fara yi musu cikin wata ƙatuwar murya, -da innace zan kotan ta muku tofah hannuna ce zai tsaya- "wannan mutumin maci amana ne, kamar yadda hukuncin maci amanar Ƙungiyar mu ta POSPA shine mu ra taye mutum jikin baƙar Bishiya har sai mun raba kansa da gangar jikin sa, to hakan shima zamuyi masa, ƙarƙashin jagorancina ni Vapi shugaban tsakiyar rukunin ƙungiyar POSPA, dan ya ƙara zama izina akan masu wannan niyyar a gaba, kun riga da kunsan cewa mai gida ZABBA BA ba ya tsoron maci amana, sai dai shi ba ya yafe duk wanda yayi masa laifi, kamar yadda a dokar sa take babu ɓata lokaci zamu aiwatar da hakan".
Yana ƙa re maganar sai gashi an gurfa nar da maci amanar a gaban su, mutumne da bazai gaza shekaru hamsin ba, domin gashin kansa har ya fara fari-fari a lamar tsufa ya fara bayyana, shi kuma sanye yake da baƙin kaya, gumi ne yake tsatstsafo masa daga tsakiyar ka har zuwa ƙafafuwan sa, saboda tsabar tsoro, duk da yasan yau babu abinda zai hana shi ba ƙuntar lahira, babu ɓata lokaci aka rataye wuyar sa cikin jar igiya, igiyar da ka gan ta ka san ita kanta sheɗaniya ce.
Take jikin Safna ya hau kyarma saboda ganin yadda marasa imanin nan suke yiwa mutumin, domin bayan sun saƙala masa igiyar a wuya sai suka fara jan wata igiyar kuma, yana fara yin sama igiyar ta fara yanke masa wuta, yadda kasan reza, shima mutumin sai ihu yake yana neman ya fiya, haka har ya dena motsi.
Yana dena motsin suka ja igiyar da ƙarfi, hakan yasa maganar da suka ce farko ya bayyana, Safna bata san lokacin da tasa ihu ba ganin munin a binda ya faru a idanuwan ta, wanda ko a labarin mafarki ko tatsuniya bata taɓa jin hakan ba, saurin mannewa jikin ginin tayi, tana toshe baki, dukkan su suka dawo da kallon su inda su kaji wannan sautin, ganin bakinta ya riga yayi suɓul da baka ne yasa ta zaro ido, sannan ga shirun da mutanen su kayi alamar hankalin su ya dawo kan ta.
ba tare da gajiyan zuwa wurin ya fita a jikin ta ba, amma ta fara ƙoƙarin barin gurin, gusawa daga jikin bangon tayi ta fara gudu cikin ta shin hankali, umarni shugaban na su yaba mutane biyar a ciki akan su kama wanda yayi wannan ƙarar su kashe shi kan su kawo masa gawar, amsa umarnin sa sukayi suka fara gudu neman ta.
HAJIYA.
"Nace miki ta tafi, direban dana sa ya kaita ya tabbatar min sun tashi, nidai burina ya cika shine kawai" cewar Hajiya dake waya da Ladingo, itama Ladingon cewa tayi "ai baki da matsala tun da dai kin tabbatar da ta tafi, dan bokan cewa yayi yadda zata bar garin nan to baza ta taɓa sha'awar dawowa ba, ko sunan shi sai dai taji a bakin wani ba dai ita ta furta ba bere sunan ku, indai Safna ce to ki cire babin ta a rayuwar ku".
Murmushi cike da jin daɗi Hajiya tayi tana ƙara cewa, "shakka babu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 56