mai daɗin amo da shiga zuciya ya ce, "na daɗe ban ganki ba, amma daga yanzu bazan sake bari inyi nisa da ke ba, saboda kina à matsayin rayuwata ce, kuma farinciki da tunani na"
Kalamansa da ya shiga cikin kunnen Amna ne yasa taji kamar da ita yake, a hankali ta ɗago don juyawa inda yake, kan ta ƙarisa juyawar yayi saurin mai da kansa gun Ammun yana cewa, "eh Anty wannan maganar da gaske nake yi miki" maida idonta tayi kan wayar tare ijje numfashi, Yazeed da ya miƙe yana ci gaba da kallon Amna ya ƙara cewa, "babu ranar da zata zo ta wuce ba tare da kalleki a idanu na ba, sannan a zuciyata" ya faɗi yana fara taku da ƙafafuwansa zuwa inda take a hankali.
Da mamaki Amna take kallonsa ganin yanzu kamar tabbas da ita yake, kuma gashi yana niyyar zuwa inda take, sai dai har yanzu fiskarta ba a sake ba. Ta buɗe baki zata yi masa magana massege ya shigo wayarta, "ko zamu iya haɗuwa? Akwai abun da nake son mu tattauna" saƙon da Shuraim ya rubuto mata kenan, hakan yasa ta miƙe haɗi da gyara gelen da yake a kanta ta ce, "excuse me Yazeed" sannan ta fice ta barshi.
Baiji daɗin tafiyar da tayi ba, duk da ya lura da taƙi sake masa fiska, to amma me yasa? Bayan yasan Safnarsa sun saba sosai kafin yayi tafiya, bata taɓa haɗe masa fiska kamar yau n'a, ya faɗi tare da zuwa ya zauna kan kujerar ɗakin, sai a lokacin ya tuno abun da yasa ta hakan, tabbas rashin sallamar da baiyi ba ne, "oh my god! Ya akayi n'a manta banyi ba? Ooo Tabbas shine yasa" ya faɗi yana jin haushin kansa, sai kuma ya miƙe tare da fita daga ɗakin don zuwa ya bata haƙuri ya manta ne.
Ya kusa zuwa upstair kenan Dady da ya hangesa ya kira shi, amsawa yayi tare da zuwa inda Dadyn yake, "ɗana baka ci abinci ba fa, muje ka ci" "No Dad bana jin yunwa sosai, so sai dare kawai zanci" ya faɗi yana juyawa har zai wuce sannan ya ce, "am Dad waye wancan guy ɗin ne?" "Shuraim kake magana ko? Yaron abokina Abu Shuraim ne, daga ƙasar London yazo gabatar da wani aikinsa a nan, so amma yana hutu tukunna" "oh!" Yazeed ya furta tare da wucewa.
Yana fita ya hangi Amna na nufar ƙofar gida, hakan yasa shi dosar inda take. Amna kuwa buɗe ƙofar tayi ta fice waje, Shuraim ne tsaye a wajen yana kallonta tun da yaji buɗewar ƙofar ya maida idonsa ta wurin, tana isowa gabansa ta fara faɗin, "gani nan, wace magana kake maganar zamuyi?" Murmushi mai sauti Shuraim yayi sannan ya ce, "kawai ina son in ganki ne, inga fiskar nan ta ki ya take? Kalar kabewa tayi ko tumatir, ko kuwa baƙa?"
Yazeed ya kusa zuwa gurin ƙofar ya fasa da faɗin, "a ah in bari sai ta dawo sannan" yana faɗi ya juya.
Amna kuwa cikin haushin kan fiska kawai ta juya gefe da fiskarta, "kaii your so beautiful da irin wannan fushin" cewar Shuraim yana sake faɗin, "but amma fa baza ki taɓa kai budurwata ba" Juyawa tayi ta kalle sa, shi kuma ya sake faɗin, "eh da gaske nake, amma fa ba budurwata ta jiya da kika gani ba, wata ce daban yanzu" "da ace akwai gwam a nan da ka ga yadda zanyi maka" "me zakiyi min?" "Manne maka baki zanyi, kuma inyi wucewata in barka, ka dawo magana da kurmanci" ta faɗi tare da juyawa.
"Da na fi kowa farin ciki, domin abun zai burge sosai" Shuraim ya tsaidata da faɗin hakan, juyowa ta yi tana dubansa, shi kuma ya ɗaga mata gira da murmushi, buɗe ƙofar gidan tayi ta shige tare da tsayawa a ƙofar tana yin dariyar jin daɗi da kalamansa ƙasa-ƙasa. Shima a ɓangaren Shuraim sai da ya jingina da bango saboda nishaɗi.
DARE.
Bayan gaba ɗayansu sun hallara a wurin cin abinci, Dady ya juya wurin Shuraim don gabatar masa da Yazeed, "my son wannan shine Yazeed ɗana" ɗaga ido Shuraim yayi yana kallon Yazeed kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya miƙawa Yazeed ɗin hannu tare da cewa, "I'm happy to see you Yazeed" kallon hannun Shuraim da ya miƙo masa Yazeed yayi, abun da ya faru ɗazu ne ya dawo ransa, wato ganin Safna da yayi da wanda aka kira Shuraim yanzu, kamar bai ga miƙa hannun da Shuraim yayi masa ba ya furta, "your welcome" ba tare da ya haɗa hannun n'a sa da na Shuraim ɗin ba, Murmushin gefen baki kawai Shuraim yayi haɗi da sauke hannun na sa.
WASHE GARI. ASABAR RANAR HUTU.
Jiya da tunanin Safna ya kwana, gaba ɗaya ya rasa ta ina zai fara yi mata maganar dake cikin zuciyarsa, da cewa yayi yana zuwa zai tarbeta da maganar, amma ya rasa me yasa ya kasa? Amma ya kamata ya ƙwarara kansa akan haka.
A falo ya taddata zaune tana kallon TV, sai da ya tsaya daga nesa yana kallonta na mintuna kamar uku sannan ya ƙarisa zuwa falon, ya zauna a kan kujerar kusa da ita, "are you watching a movie?" Ya faɗi tare da kallon inda TV yake, murmushi kawai tayi masa ba tare da ta ce masa komai ba, "ina baki haƙuri akan jiya" Juyowa tayi tana kallonsa da cewa, "me ya faru jiyan?", "na shiga ɗaki na same ki ba tare da sallama ba" juyawa tayi tana cigaba da kallonta ta furta, "oh, indai wannan ne don't worry about it, kawai dai ka gyara gaba, shi sallama abu ne mai kyau ga mutum ko ba musulmi ba, bare musulmi".
"Insha Allah that's is last time, an thenn! Imm ina son yin wata magana da ke mai mahimmanci" "ok go ahead!" Sai da ya ni sa kamar ya bar maganar Sai kuma ya ce, "dama ina son yin magana da ke akan tsakanin mu" da mamaki Amna ta ce, "tsakaninmu kuma?" Gyara zama yayi don yayi mata maganar don tabbatar da amsarta, "yes tsakaninmu, ina son in faɗa miki abun da ke cikin zuciyata, sanna kema inji daga gare ki".
Itama mai da hankalinta tayi kansa don ya sanar da ita abun da yake son faɗin, amma kafin ya sake yin maganar Shuraim ya iso wurin, hakan yasa Yazeed fasa abun da yake son faɗin yayi shiru, "sauraronka nake ya kayi shiru?" "Ba komai sai wani lokacin kawai" ya faɗi tare da tashi ya bar wurin, don shi baya son ganin Shuraim ma bare, don ya lura da cewa kishi da Shuraim ɗin ya ke, "amma bai kamata na tafi n'a barshi da ita ba" cewar Yazeed cikin zuciya, tare da juyawa don komawa falon.
Sai dai da zuwan shi ya tarar da su suna hira, wani irin abu ne ya kuma bugan zuciyarsa à karo na biyu, bai san lokacin da ya juya ya wuce ba. Amna ta juya inda yake kenan ta ga kamar ya juya ranshi ɓace, da mamaki ta bisa da ido, domin ta ga kamar ganinta da Shuraim ne yasa ya tashi ɗazu, sannan kuma yanzu yaƙi ƙarasowa juya fiskar sa alamar damuwa.
Bayan Amna ta koma cikin ɗaki, tsaye take tana tunanin me yasa Yazeed yake nuna wannan halin haka ne? Ɗaga kai tayi alamar yauuuwa na tuno, "Ashe fa mantawa nayi, dama fa shi ne wan da suka fara soyayyya da Safna koh?" Ta fadi tare da zama kan kujerar, "kamar yadda Raheena ta sanar da ni, kawai dai basu furtawa junan su bane, idan kuwa hakane, to ƙila maganar da yake son faɗa min ɗazu kenan ya tsaya da ganin Shuraim ya zo, cabb! Lallai wannan shine ƙarin wata matsalar, aikuwa duk hanyar da zanbi sai na bi don kaucewa zancen da yake son sanar da ni ɗin" ta faɗi tare da sauke numfashi.
HAJIYA. Tana zaune gefen gado Ladingo kuma saman kujera, kallon kallon suke Ladingo na yin ƙasa da kai sanna ta ce, "haba ƙawata, shekaru aru-aru muka shafe muna tare amma sai yanzu ɗan ƙaramin abu ya rabamu? Aminci bai ce haka ba" "Ke kike ganin ƙaramin abu sabili da baki san zafin su bane shiyasa, domin in da kin taɓa yin asararar abu kamar yadda nayi ai ba kya ce ba" cewar Hajiya, "haba Hajiya wace magana kike faɗawa aminyar cin mushenki haka? Kuma da kike cewa ban san zafin su ba, ke zafin sun kika sani ne? Ina ce kema a ɓagas kika samu duk abun da kika samun?".
"Ba shakka, wato zuwa kika yi dama ki sake ƙunsa min baƙin cikin ashe, to tashi kiyi tafiyarki, dama ai ke kika kawo ƙafarki" a hankali Ladingo ta soma cewa, "a a kinga ƙawata, kuma Hajiyata, ni fa zuwa nayi muyi sulhu ba wai sake kamo wata mtsalar ba, in dai don shawarar da na baki ne to kiyi haƙuri, haka Allah yaso za ki rasa kadararki sanadiyyar shawarar" cewarta harda wani nunawa Hajiya kamar itama bata so hakan ba, ajiyar numfashi Hajiya ta sauke tana cewa, "toh shikenan, ai ke ɗin ce da mummunar baki kike, kokin bani shawara gurguwa take zama, yanzu da ace lafiyayyar shawara kika ban ai da komai ya riga da ya sauya yanzu".
"To ni dai kamar yadda na ce ayi haƙuri, Allah ya tsare na gaba, kuma duk magan-ganun da na faɗa miki ki yi min haƙuri akan su, dokin zuciya na hau shiyassa, amma cewa da nayi kina da maƙo duk zance ne, ai ke in dai fannin kyauta ne to sai dai kizo na ɗaya, kawai baki na ne yayi ta zuba cikin hasala" "toh shikenan na yarda yanzu komai ya wuce" "yauwa Hajiya mai halin arziƙi, jininki na arziƙi, 'yan'yanki na arziƙi, ke hatta jikoki da tattaɓa kunnuwanki baza suyi talauci ba" washe baki Hajiya tayi sannan ta miƙe tana faɗin,
"Tun da nake da ke baki taɓa faranta min rai kamar yau ba, don haka zan baki dubu goma sha biyar goma wanda na ara biyar kuma kyauta" duk da Ladingo bata ji daɗin jin hakan ba amma ta ce, "nagode sosai ƙawata". Bayan Hajiya ta bata kuɗin sannan suka zauna ta fara sanar da ita abubuwan da take shiryawa yanzu, shiru Ladingo tayi don kada ta bada shawar da zai dawo matsala.
YAMMACI.
Amna ce zaune da Shuraim a garden yana bata labarin wani lokaci da yake a London, "kawai na tsaya ina ta faman yi wa mutumi faɗa ina cewa, "wani irin rashin mutunci ne na ga kana yiwa matar nan, taya zaka watsa mata ruwa sannan kana yi mata maganar soyayya, bayan gata da yaro a hannunta, daga ganin hakan ka san ita ɗin matar aure ce" haka dai nayi ta yi wa wannan mutumin masifa, matar na ƙoƙarin yi mini bayani amma na ƙi bata dama, ni nan ina kare mata mutuncin, akan mai neman yi mata abun da bai dace ba, harda cakumar rigarsa"
Yazeed ya fito neman Safna, nan aka sanar da shi tana garden, ai bai tsaya ba ya nufi wurin don ya ƙare komai yanzu, wato ya amayar da abubuwan da yake son sanar mata, yasan ita ɗaya ce a wurin don haka yanayin ma zai fi yin daɗi sosai, nufan wurin yake tare da jin farin ciki a ransa, sai washe baka yake, yana shirya yadda zai fara yi mata maganar.
Shuraim ne ya cigaba da cewa, "bayan na cakume shi kawai matar ta fara cewa "ya issa! A kan me zaka rinƙa yiwa mijina irin wa'yannan maganar?" Ta faɗi cikin ɓacin rai, ba sai na hangame baki ina kallon ikon Allah ba" dariya Amna ta fara yi sosai cikin jin farin ciki da wannan labari da yake bata, "lallai kace ka shiga tsakanin ma'aurata? Kai nan mai kare haƙƙin mata" Sannan ta cigaba dariyar, shima dariyar yayi sannan ya ce, "ina faɗa miki ba sai na fara rage hannuna daga cafkar da nayi masa ba" "hahhhhha to amma ya kayi daga baya?" "Kallonsu na fara yi ina ta washe baki kamar gonar auduga, ina faɗin suyi haƙuri matsalar gani aka samu, sannan a hankali na fara zamewa ina son fecewa, mijin matar ya fara cewa, hei he wait, ai sai na sa gudu na bar wurin. Tun daga nan nake an karewa, don su 'yan ƙasar wajennan akwai su da soyayya da yawa, ko ina suke ba sa jin ba daidai ba"
Dariya sosai su keyi a tsakanin su harda ƙyale-ƙyalewa, Shuraim ya dakata da dariyar da yake yana kallonta ya ce, "amma kuma nima inason inyi koyi da irin wannan soyayyar, yadda ko a gaban waye zan yiwa wacche nake burin aure soyayya gwanin burgewa," shiru itama Amna tayi tana kallonsa cikin ido da jin maganar tasa, nan suka fara kallon ɓoyayyiyar soyayya.
Yazeed kuwa da ya nufo wurin cikin farin ciki, amma sai ya tsaya cak, zuciyarsa ta fice daga cikin farin cikin da take ta dawo baƙin ciki, sanadiyyar cin karo da kalaman Shuraim ga Safnarsa, sannan sun fara wani kallo wa junansu daga shi har Safanar.
Last part.
___________________________________________________
Soyayya tsakanin Shuraim da Amna ya fara bayyana, kuna ganin zasu gane hakan kuwa.
Sanna gefe ɗaya kuma ga kishin Yazeed da Amna.
Shin kuna ganin Yazeed zai ƙarasa a haka yake ya sanarwa da Amna kalaman da ke ɓoye à zuciyarsa ku yaya?
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣1️⃣9️⃣▶️1️⃣2️⃣0️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Yazeed ji yayi ƙafafuwansa babu ƙarfi tamkar an ɗora musu kaya mai nauyi, ba zai iya ƙarisawa wurin ba, domin yadda yake jin zuciyarsa na yi masa, a hankali ya samu damar jan ƙafafuwansa ya bar wurin, tafiya yake amma idanuwansa tamkar suna gane masa duhu, don da ace akwai tudu da kwari a cikin gidan da ba makawa ya afka ko faɗuwa.
Ruki da ta ganshi ya taho kamar ya baro ɓangaren garden, sannan kuma yanayinsa na ɓacin rai ne yasa ta fara tafiya don zuwa ganin abun da yasa shi hakan, Tana isa ta tarar da Shuraim da Amna suna cigaba da yiwa junansu wannan kallon, yadda kasan wa'yan da suka tafi wata duniyar, "iimmm abun da ya sauya masa yanayi kenan?" Ta faɗi a cikin zuciyarta tare da yin musu gyaran murya, da sauri suka dawo daga hankalinsu suna kallonta, ita kuwa yi tayi kamar bata san da su a wurin ba, ta zauna kan wata kujerar tana kallon wayarta.
"Am ni bari naje n'a koma ɗaki" cewar Amna tana wucewa ta bar wurin, a zuciyarta tana cewa, "amma me yasa na ji yanayin farin ciki game da maganar da ya faɗa ne? Oh Amna kina shirin dawowa wata Amnar fa" ta faɗi tare da sakin wata murmushin ta wuce.
Yazeed. A falo ya zauna yana mai cigaba da jin zafi a ransa, idanuwansa babu abun da suke nuna masa fa ce Safnarsa da Shuraim suna kallon da ya ɗauka n'a soyayya. Nufowa in da yake Amna tayi bayan ta shiga falon, "Yazeed kana nan kenan? Huta..." kan Amna ta ƙarisa maganar ya miƙe rai ɓace ya wuce ya ƙyaleta tsaye, da kallon mamaki ta raka shi har ya nufi upstair, sai wani sauri yake faman yi har yana ƙoƙarin faɗuwa.
Ruki da shigowarta kenan bayan ta baro garden ganin shima Shuraim tashi yayi daga sanda Amna ta bar wurin, sake kallon Yazeed tayi yana hayewa step da sauri da sauri, juyar da kanta tayi tana kallon Amna da ke kallon Yazeed mamaki faɗaɗe a fiskarta. Amna kuwa zama kan kujera tayi tana kunna wayarta.
Yazeed kam bayan ya shiga ɗakin sa ya zauna gefen gado tare da sa hannayensa duka biyu a goshinsa zuwa gashinsa, yana kai kawo da su da ka gani kasan yaƙi da azabar baƙin cikin da ke zuciyarsa yake yi. A hankali Ruki ta shigo ɗakin na sa tare da kiran sunan sa, bai amsa mata ba sai ma cigaba da shafar kan na sa da yake yi, zuwa tayi ta zauna a gefen sa kan gadon sannan ta fara magana cikin munafurci, "dama na san zaka tsinci kan ka cikin wannan halin da zaran ka dawo, kuma gashi hakan ya kasance".
Barin abun da yake yayi tare da juyawa inda take, kallonsa itama tayi ta cigaba da cewa, "eh Yazeed dama na san dole zaka tsinci kan ka a halin da kake ciki yanzun, domin Safnar da ka sani a baya ba ita ba ce yanzu" "Ke bana son maganar banza kuma kin sani!" Yayi maganar muryarsa ba wasa, ta san halin sa hakan yasa ta sake cewa, "wallahi Yazeed ni ba maganar banza nazo yi maka ba, gaskiya ce kuma ni kaɗai ce wacche zan faɗa maka".
"Wace gaskiyar?" Nan Ruki ta fara zayyano masa magan-ganu ƙarya da gaskiya, ta bashi labari har shaƙar da tayiwa Hajiya, sai dai bata ce masa aljanu ne ba, kamar yadda Amnar ta sanar da su lokacin. sai da Ruki ta gama ba shi labarin rankata-kaff sannan ya juyo ya dube ta cikin mamaki ya ce, "haka née?" Ruki ta furta, "Yes of course!" "Ooh are you finish?" Da mamaki ta ce, "me kake nufi? Ni fa ba ƙarya na ke ba" miƙewa daga zaune yayi yana sake juyowa ya dubeta ya ce, "kina gani ƙaryar da kika zauna kika shirya min zan yarda? Na riga da na san ki, sannan kuma ita kanta Safnar, Koda ma ace giya na sha nayi tatul, ba zan taɓa yarda da wannan zancen ba, kuma idan kika ƙara ƙoƙarin ko da ace faɗawa wani wannan zancen, to zaki gane kuranki ne a hannuna da kyau, sannan yanzu fitar min daga ɗaki!".
Cikin haushi Ruki ta miƙe tana kallonsa ta kuma cewa, "yanzu ƙarya ka ɗauk..." "idan kika ƙarisa saina maida dogon bakin nan na ki ganda yanzun nan! Wawuya kawai, ke ga ki kin yi shiri don ki sa min tsanar Safnata a raina ko?" A sanyin guiwa Ruki ta baro ɗakin tana bin ƙofar ɗakin da kallo, "wallahi dana sani da ban je ba" ta faɗi tana shaƙan wani ƙarin baƙin cikin.
Yazeed kuwa kwanciya yayi a kan gadon yana sauke numfashi kaɗan-kaɗan, "na yarda da ta sauya, amma bai kamata ta rinƙa yin magana da wani ba, ni ne kaɗai wanda ya kamata tayiwa murmushin nan na ta mai haske" ya faɗi tare da juyawa ɓangare dama yana tuna wani lokaci.
___Zaune yake shi da Safna a falo, yana riƙe da littafinta a hannun, wanda shine ya buƙaci da ta kawo masa, "to ai kamar ma kin fini ƙwaƙwalwa, kalli yadda kika ba da amsa cikin hikima, wow Safna your so special" murmushi ta sakar masa a hankali ta ce, "haba dai, yaya Yazeed, taya zan iya zama kamar kai?" "Ba gashi ba" ya faɗi yana binta da ido, ƙasa da kai tayi ba tare da ta sake magana ba, "zan yi kewarki idan nayi nisa da ke, sai dai ni gani na ke kamar ke baza ki damu da hakan ba ko?" A hankali ta miƙe tana shirin barin wurin yayi saurin miƙewa da tsaidata da faɗin, "me yasa zaki tafi? Ko gaskiya ne ba za kiyi kewan na wa ba?" Juyowa tayi tana kallonsa kaɗan, sai kuma tayi ƙasa da kai, yayinda hawaye ya zubo kan fiskarta, cikin tashin hankali ya matso dap ita yana faɗin, "me yasa? Hawaye? A a karki yi kinji?" Ya faɗi cike da damuwa har da ɗan ruɗewa, domin idan akwai abun da yafi tsana to zubar hawayenta ne. "Meyasa kake tunanin, bazan yi kewarka ba yaya Yazeed? Tun da ka sanar da ni batun tafiyarka ban sake nutsuwa ba" ta ƙarisa faɗi hawaye na kuma zubowa ɗaya bayan ɗaya. "Please sit down my sister" cewar Yazeed cikin damuwa, a hankali ta zauna, shi kuma yayi saurin cire hankicif ɗinsa yana ƙoƙarin share mata hawaye, amma bata bar shi yayi hakan ba ta amsa ita ta share da kanta, cikin sanyin murya ya fara ce mata, "Safnah kin san kuwa wannan zubar da hawayen da kike yi ba ƙaramin cutar da ni suke ba?" Ba tare da tayi masa magana ba ta ɗaga ido tana kallonsa..........
Tashi Yazeed yayi yana sauke numfashi bayan ya gama tunowa, "to amma me yasa take sauya min haka yanzu?" Ya wulla wa kansa tambayar fiskarsa da damuwa, sai kuma ya miƙe tsaye, "no! No ni no! bazata sauya min ba, nine kawai nake yi mata mummunar fahimta, amma na san baza ta yi min hakan ba, kuma na tabbata she's love me" ya faɗi tare da komawa ya zauna yana sake murmushi.
DARE.
Hajiya da Marwan suna ɗaki suna tattaunawa akan maganar bikinsa, hakan yasa basu samu damar halartar gurin cin abinci ba, Dady kuma ya fita. Hakan yasa dining ya kasance, Ruki da Saleem, da kuma Yazeed da Shuraim. Babu abin da Yazeed yake aikatawa Shuraim fa ce kallon tsana, gaba ɗaya ya tsani guy ɗin wallahi. Shuraim ya lura da hakan tuntuni sai dai ya nunawa Yazeed kamar bai san da hakan ba.
Suna cikin cin abinci Amna ta iso wurin, "hi guys, are you eating but have you forgotten about me?" Tayi musu maganar tana sakin murmushi, Shuraim da Yazeed murmushi suma suka yi mata ban da Ruki da Saleem, ƙarasowa ta yi zuwa kusa da su, Yazeed ya buɗe baki zaiyi mata magana akan ta zauna akan kujerar da yake kusa da shi sai Shuraim ya riga sa, kallon Shuraim yayi yana ɗan ɓata rai ita kuma Amna ta zauna inda Shuraim yayi mata nunin kusa da shi.
Miƙewa Yazeed yayi yana ɗaukar plate tare da tambayarta, "which one do you want?" Ya faɗi tare da yi mata qlama da hannu akan sauran kulolin, Shima yanzu Shuraim da haushi ya kalli Yazeed ɗin, Amna kuwa ba tare da tunanin komai ba ta furta, "whatever you want" Yazeed daɗin furucinna ta yayi har cikin ransa, sai dai fa shi Shuraim saɓanin hakan ne.
Saleem da Ruki kuwa duk suna lura da su, musamman ma Ruki ta fi sanya musu ido sosai, sai wani jijjirkita fiska su keyi.
Bayan Yazeed ya kammala sanya mata shinkafa da wake da kuma soyayyar kifi da nama, wanda aka sarrafa su dafa duka, ya ijje mata a gabanta tare da faɗin, "wannan ne zaɓi na yayi miki?" "Eh yayi aini ina son jolof rice and beans" Amna ta bashi amsa tana ƙoƙarin sanya cokalin da ta ciko da abincin dan kaiwa inji markaɗenta, domin har ƙaguwa tayi da cin sa, domin colourn jolof ɗin ya burgeta, uwa uba ga ƙamshin da ya kanannaɗe manumfasanta.
"Dakata!" Cewar Shuraim cikin dakewa, tsayar da shigar da cokalin baki cak Amna tayi, Yazeed kallonsa yayi su Ruki masu gulma ma tsayawa su kayi suna kallon Shuraim ɗin. Shuraim kuwa ansan cokalin yayi ya maida kan plate ɗin sannan ya ture palate ɗin gefe, cike da mamaki Amna ke kallonsa tare da neman ƙarin bayani, amma ta kasa magana, sai da ya kalli inda Yazeed yake ka na ya ce, "the food was not delicious! Sun sanya gishiri da yawa, you can't eat, don haka bari in sanya miki wani".
Ya faɗi tare da miƙewa, "to shikenan" cewar Amna tana murmushi tare da ɗan girgiza kai kaɗan, idonta ne ya fa ɗa kan hannun Yazeed da ya dunƙule a jikin teble, kallon hannun tayi sosai sannan ta dawo da kallonta zuwa kan fiskarsa da mamaki, sai dai yadda ta ga fiskar ta sa ne yasa ta saki fiskarta daga mamakin da yake ciki, bayan kallon fiskar ta shi da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 56