Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
riga da na san waye yasa aka yi min duka wancan ranar, ba kowa ba ne mahaifinki ne, to don haka ina son ki sani, ni da ke har abada ba za ki taɓa rabuwa da ni ba, dole ki zauna da ni mijinki, ina tabbatar miki da ce wa idan har aka ci galaba akan mahifinki to kisa a ranki maganar da na faɗa an gama!" abin da ta fahimta daga magan-ganunsa kanan. Yana faɗi ya juya ya shige motarsa ya barta tsaye, dafe ƙirji ta yi ta furta, "ni dai na shiga uku!" Rai ɓace ta shige gida sai numfarfashi ta ke fitarwa, Kafin ta shige cikin ɗakinta ta ga kamar Saleem na shiga ɗakinsa da sauri, ji ta yi tana son ta je ta ga abin da ya sanya ya yi saurin shiga ɗaki haka, don dai ba ta saba ganin ya yi hakan ba.. Saleem yana shiga ɗakinsa ya fito da wata leda baƙa daga cikin aljuhunsa, haɗi da zaunawa kan gado ya kwance ledar sannan ya ijje a katifa. Turo ƙofar da aka yi ba tare da zato ba ne ya sanya ya yi saurin ɗauke ledar ya ɓoye hannunsa a bayan sa, tsaki ya saki ko da ya ga ashe Ruki ce ta shigo. "Ke me haka zaki wani bankaɗo ƙofa kamar ɗakinki? Ba za ki iya yin nuking ba ne?" Da mamaki Ruki ta ce, "yau kuma wani sabon salo ne haka? Akan me sai na nemi izininka tukunna zan shigo, kai haka ka ke yi in zaka shiga ɗaki na?" Tsaki ya kuma ja sannan ya dawo da ƙwayoyin da ya ɓoye gabansa yana buɗewa ya ce, "saboda faruwar abun nan ne ya sanya na ke taka tsantsan, dama ga abun da aka ce Dady ya aikata, kin ga in aka ganni da ƙwaya sai a kuma samun matsala, saboda gudun faruwar hakan yasa na ke ɓoye kayana, insha cikin ɗakina hankali kwance". "Oho to me ne ne wannan ɗin? Ni dai ban taɓa ganin ƙwaya irinsa ba" sauke numfashi Saleem ya yi ya ce, "nima da kaina ban taɓa ganin irinsa ba, wani abokina ne ya dawo daga tafiya, shi ne ya dawo mana da su, ya faɗa min irin ƙwayoyin duniya ne, idan ka chake su to jin ka zaka yi ka samu cikakken 'yanci. ni fa wallahi duk abubuwan nan sun dameni, shiyasa na amsa don na samu na sarara abina, samun wuri Ruki ta yi ta zauna gefensa itama ta ce. "Kai dai bari, komai ma ya fi kacime min wallahi, ga abubuwan da ke faruwa da Dady, sannan ga wa'yan nan mutane da su ke son yi mana fin ƙarfi yanzu cikin gida, tun yanzu sun gama mmamaye komai, komai ya rikice mana, gefe ɗaya kuma ga wannan aljanin Jaizu, yanzu haka daga waje na ke, wai ya ce min sai na koma gidansa indai har Dady bai yi nasara a kotu ba, duniyar duk ta min zafi, kawai ni ma ba ni in afa ko na samu sauƙin problèmes ɗin nan". Ba ta ya yi sannan ya ce, "kada ki sha min à ɗaki, koma ɗakinki ki je kisha, saboda ance min rikita ƙwaƙwalwa ta ke yi sosai, don ni ma idan na sha babu inda zan fita sai ya sauka". Kamar yadda ya ce da ita ta miƙe ta bar ɗakin, har Allah-Allah ta ke ta isa ɗaki tasha abinta. RANAR SHARI'A. Sun riga da sun kammala komai na shirin kotu, har za su fito sai Shuraim ya ce, "ni yanzu zan je in ɗauko doctor Salis kamar yaddana sanarda ku hiya, kawai mu haɗu a kotun kamar yadda aka tsara" ya faɗi domin ya riga da ya gano inda doctor Salis ya ke tuntuni, ɓoyesa ya yi don kada a samu matsala, domin doctor Salis babban shaida ne a gare su. Yazeed ya ce da Shuraim su tafi tare, don haka su ka fice daga gidan zuwa ɗauko doctor Salis. Su Hajiya da sauran 'ya'yan na ta kuwa, dama tuni Dady ya sanar da ita ranar zaman kotu su zo wurin da wuri, kada su ce zasu jira su Ammu, sabida haka su ka fice tun da Sassafe. Wayar Amna ne ya yi ƙara, ta ɗaga tare da sanyawa a kunnenta, "hello Amna ni ne lauyanku, ina son ki gaggauta zuwa kotu don akwai abin da na ke son nuna miki kafin a shiga shari'a" "ok to gani nan zuwa" cewar Amna tana juyawa ta dubi su Ammu ta ce. "Ammu akwai wani abu na gaggawa da ya taso, ya kamata in tafi kotu nima yanzu, kafin su Mamma su gama shiryawa zai ɓata min lokaci, saboda haka ni zan tafi in sun gama sai kuzo daga baya kun ji?" Ammu ta dubi Amna ta ce, "my daughter ya kamata mu tafi tare, ban yarda da tafiyarki ke kaɗai ba, ki yi haƙuri kaɗan na san yanzu za su fito" "ki yi haƙuri Ammu, akan maganar shari'ar nan ne fa, kuma tun da har lauyan ya kira ni to na tabbata abin na da mahimmanci, kada ki damu don na tafi ni kaɗai, babu abin da zai sameni kin ji ko?" Cewar Amna tana ƙoƙarin fita. "To a jirani mana" Safna ta tsaida Amna da faɗin hakan, sannan ta juya gun Ammu ta ce, "Ammuna karki samu damuwa, ni zan kula miki da ita" murmushi Amna ta yi ta ce, "ko dai a kula da ke ba? To mu hanzarta dai, Ammu sai kun zo, zan yi wa dribobin nan magana su tuƙa ku cikin salama har zuwa kotun" Amna ta ƙarashe faɗi tana kallon Ammu ka nasu ka fice ita da Safna" da kallo Ammu ta bi su tana jin kamar ta tsaidasu, ba ta san me yasa tun da ta tashi da safe ta ke jin wani fargaba a ranta ba. KOTU. Ko da isan su Amna su ka tarar da lauyan na su, sai dai da mamakin Amna babu abin da lauya ya nuna mata mai mahimmancin, kamar yadda ya sanar da ita a waya, "ni banga abin da yasa ka ce mu yi gaggawan zuwa kotu ba, babu abin da ka nuna mana, haba don Allah wannan bai da ce ba, tun da ka san ba wani abin kirki zaka nuna mana ba akan me zaka taso mu? Ga shi su familyn har yanzu ba su ƙaraso" babu abin da lauya ya ke yi sai kame-kame, ya kasa sanar da ita takamemen abu ɗaya, wanda hakan ya ɗarsa mata wani abu a cikin ranta. Safna ce ta dafa ta tana cewa, "kwantar da hankali kin ji" ajiyar numfashi Amna ta yi sannan ta ce, "abun ne da haushi, sai da Ammu ta ce injira mu taho tare amma na ƙi. Wai kin kira su kin ji sun kusa isowa kuwa?" "Har yanzu na kasa samun kowa a cikinsu, duk layin da na kira ba ya shiga" cewar Safna damuwa na bayyana a ranta. Da mamaki Amna ta ce, "baya shiga kuma? Kin gwada layin ko wanne a cikinsu?" "Eh na gwada amma shiru, to ko network ne?" Faɗin Safna, barin inda su ke lauyan ya yi, Amna ta bisa da wani kallo ta ce da Safna, "Safna ban yarda da wannan lawyern ba" kafinSafnata bata amsa Raheena da mahaifiyarta su ka ƙaraso, bayan sun gaisa Amna ta kuma cewa Safna, "je ki da su Momy cikin kotun tun da anfara shiga, ni kuma bari na ƙara trying numbers ɗin". Gefe ta koma ta yi ta kira nombobin har da na su Hambali ba ya shiga, damuwa ta shiga sosai da abin da ya ke faruwa, ya kamata ace tuntuni sun iso amma ace har yanzu shiru?. Amna ta gaji da kiran nombobin ba ya shiga, hakan yasa ta yi tunanin zuwa gidan, ta ga ya su Ammun su ke me ya han su zuwa har wannan lokacin haka? Sai dai maganar Shuraim ya dakatar da ita, juyawa ta yi tana kallonsu, Shuraim ne sai Yazeed da uncle Musa, sannan doctor Salis a tare da su, duk da cewa fiskar doctorn na ɗauke da rauni" tambayarta su ka yi ya ba su ga su Ammu ba, ta ba su amsa da abin da ya ke faruwa, "lokacin shari'a ya riga da ya yi, ƙila ko wani abun ne ya hana su zuwa" faɗin uncle Musa, cikin damuwa Amna ta ce, "uncle amma fa duka layukan su baya shiga" kafin ya bata amsa su ka ji an fara gudanarwa don haka su ka shige ɗakin shari'ar kawai" Ko da shigansu Safna ma ta tambayi Amna akan ina su Ammun? "Har yanzu ban same su ba" Amna ta bata amsa tare da zama kusa da ita cikin tunani, dukkansu kowa da tunanin da ya ke saƙawa a ransa na fargaba. A yau kotun ya cika sosai, domin kuwa harda 'yan jarida da kuma manyan masu kuɗi, wanda zamu iya cewa ƙila suna da alaƙa da Dady. Duk 'yan jaridar sun zo ne bisa tsarin Dady, shiyasa a kirasu su zo domin bayan an fitar da shi daga zargi ya wanku a idon gaba ɗaya mutane. SHARI'A YA YI SHARI'A, sai dai yadda shari'ar ya ke gudana ba ƙaramin ta da hankalin su Amna aka yi ba, domin kuwa kota ina lauyan Dady ya kanan-naɗe su, sannan basu gane kan lauyansu ba, babu abin da ya ke taɓukawa kamar ma kare Dadyn ya ke yi. Duka zuciyansu ya tsinke gaba ɗayansu, Amna, Safna, Shuraim, Yazeed, uncle Musa. Su Hajiya da Marwan, Saleem, Ruki kuwa farin ciki ne fal ransu. Juyawa Amna ta yi ta kalli Safna ta ce, "Safna, na tabbata akwai abin da mutumin nan ya ke ƙullawa ko kuma ince ya riga da ya ƙulla, kuma idan ban yi kuskuren fahimta ba lauyanmu ma yanzu haka yana ƙarƙashinsa ne". Zaro ido Safna ta yi ka na tace, "idan kuwa haka ne, zai tsira kenan? Ya za mu yi yanzu?" "Zan san abin yi, domin wannan mutumin ba zai taɓa sha a banza ba!" Cewar Amna tana miƙewa, da miƙewarta da vabreshin ɗin wayarta lokaci ɗaya, number ta gani a kan wayar hakan yasa ta koma ta zauna haɗi da ɗaga wayar. "Ya kamata ki fita waje zaki fi fahimta na" cewar mutumin da ya kira ta, Safna ta dubi Amnan ta ce, "Su Ammun ne?" Amna ta girgiza mata kai alamar a ah, sannan ta ce, "ina zuwa kaɗan" da mamaki su Shuraim su ka bi Amna da kallo da tunanin me ya fitar da ita waje?. "Kai waye ne wai? Me yasa zaka ce in fita? See, yanzu zan kashe waya saboda akwai abin da na ke mai mahimmaci à wannan lokacin" cewar Amna kafin ta katse ta ji ance, "idan ki ka kashe kin yi asarar danginki baki ɗaya!" Wani irin faɗuwa gaban Amna ya yi da jin wannan mummunan furucin, cikin ruɗu ta ce, "wha what do you mean? Who are you? Menene tsakaninkada Familyna?" Dariya ya yi ba tare da ya bata amsa ba. Sai da ta ƙara maimaita tambayar sannan ya dakata da dariyar ya katse kiran, Amna ta rasa abin da ke yi mata daɗi, kafin ta dannan numbern don sa ke kiran layin, ƙarar kira ya kuma shigowa,, dubawa ta yi cikin ruɗewa har hannunta na rawa, vidéo call aka kirata, kasancewar dama Datan ta a buɗe ya ke, ɗagawa ta yi me idon ta zai gane mata?. Su Ammu, Mamma, Baba, Ummee, Mubarak, Hambali, Jummala da sauran masu aikin gidan duka an ɗaura musu manyan bindigu a saman kawunansu, sannan ga shi da alama à galabaice su ke. Jikin Amna gaba ɗaya ya fara rawa, zufa ya fara tsere a gaba ɗaya jikinta, "kkkkk kada ku cutar da su, don Allah kada ku aikata musu komai, me kuke so?" Ta faɗi cikin masifaffen tashin hankali sosai, mutumin ya ce, "tambaya mai kyau! Abin da na ke so shi ne, ba tare da ɓata lokaci ba, ki je ki warware tuhumar da ku ke yiwa Jamilu yanzu! Ke da bakinki ki je ki sanarwa kotu cewa, duk abubuwan da ku ka shigar akan Jamilu ya aikata ƙarya ce, ku ne kawai ku ka haɗa don ku ɓata masa suna" "a a akan me zan faɗi hakan? Kun san abin da mutumin nan ya aikata mana kuwa?" Kafin ta kuma yin magana Mutumin ya ce, "duk abin da ya aikata muku bai kai asarar da za ku yi mana idan aka hukunta shi ba" cikin ɓacin rai Amna ta ce, "to ba zan aikata abin da ku ke so ba!" Tana ƙarashe maganar ta ji ƙarar bindiga daga cikin wayar da kuma ihu kamar ihun Mubarak ne, kawai kuma ta daina ganin komai" ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba tana faɗin, "zan yi, zan yi wallahi duk abin da ku ke so, ka da ku kashe kowa, ka da ku taɓa su, yanzu yanzun nan zan je in yi abun da ku ka ce" "yarinyar kirki" mutumin ya kuma ambata sannan ya kashe wayar. Saurin tsaida kukanta ta yi tana share hawaye don komawa cikin kotu, ko da shiganta ta haɗa ido da Dady da ke tsaye gurin tuhuma, shu'umin murmushin mugunta ya sakar mata, hakan yasa ta sauke kai tana jin azaba cikin ranta, zama ta yi Safna ta tambayeta lafiya yanayinta ya canza? Ko wani abun ne ya samu su Ammun? Ta yi mata tambayar cikin tsananin damuwa, ƙirƙiro murmushi Amna ta yi ta sakar mata sannan ta ce babu komai, duk da Safna ba ta gamsu ba amma ta yi shiru. Doctor Salis aka kira don bada shaida kamar yadda aka ce. Doctor Salis ya fara magana kenan Amna ta dakatar da shi da kuma neman izinin yin magana, "baiwar Allah ya sunanki?" Cewar Alƙali, Amna ta gabatar da sunanta da kuma dangantakan da ke tsakaninta da Dady, sannan ta kara da cewa tana so a bata dama, zata faɗi gaskiyar komai da komai, tana da hujjojin da za ta sanarwa kotu game da shari'ar. Abun ya ba su Shuraim mamaki sosai, Safna kuwa murmushi ta yi, domin ta yi zaton wani babban hujja Amna ta samu, kamar yadda ta ce ɗazu zata yi wani abu game da Dadyn. Babu ɓata lokaci aka nemi da doctor Salis ya koma ya je ya zauna, ita kuma Amna ta hau wurin zuciyarta cike da raɗaɗi, sai da ta kai dubanta gun Dady sannan ta ja numfashi ta fara magana kamar haka. Last part. ___________________________________________________ 'Yan uwan arziƙi kuma ku ja numfashi da kuma dakon next part, me tunaninku ya ba ku akan abin da zai faru gaba? Shin Amna zata faɗi abin da aka ba ta umurni don gudun kada wani abu abu ya samu su ahalinta? *_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_* ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣7️⃣1️⃣▶️1️⃣7️⃣2️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar _🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_ Babu ɓata lokaci aka nemi da doctor Salis ya koma ya je ya zauna, ita kuma Amna ta hau wurin zuciyarta cike da raɗaɗi, sai da ta kai dubanta gun Dady sannan ta ja numfashi ta fara magana kamar haka. "Ya mai girma mai shari'a, duk abubuwan da ake tuhumar Alhaji Jamilu da su, ko kaɗan bai aikata ba, duk shiri ne". Wani irin bugu ƙirjin Safna ya yi da jin abun da 'yar uwarta ta faɗi, ba ta san lokacin da ta miƙe bisa ƙafafuwanta ba. Su Shuraim ma da sauri su ka miƙe da tsantsar mamakin abun da Amna ke cewa. Amna ta kuma cewa, "tabbas hakan batun ya ke ranka ya daɗe, Jamilu bai aikata komai ba, shi mutumin kirki ne, ba zai taɓa aikata abin da aka ce ya aikata ba". "A 'yar uwata lafiyarki kuwa!? Kin san abun da ke fitowa daga bakinki?" Faɗin Safna cikin tashin hankali, suma su Shuraim su ka fara yiwa Amna magana, sauran mutanen kotu hankalinsu ya dawo kan su Shuraim, Hajiya ma ta miƙe tana faɗin, "dama ni na sani ai, kuma..." tsawatar musu da Alƙali ya yi ne ya sanya su yin shiru, sannan su ka zauna kamar yadda Alƙali ya ce, "Amna me ki ke yi haka? Akan me yasa?" Safna ta faɗi a zuciya hawaye na zubo mata, Raheena da mahaifiyarta su ka dafa Safna suma cike da damuwa. Yazeed ya juya ya dubi su Shuraim cikin tsananin mamaki ya ce, "wai me yasa za ta sauya haka ne? Ta ya Amna zata ce Dady bai da laifi bayan yana da laifin?" Shuraim kam kasa magana ma ya yi sauran kuwa sai mamaki su ke cigaba da yi. Amna kuwa saurin kai idonta gefe ta yi saboda ganin Safna da ta yi tana hawaye, hannunta ta sanya ta share idonta kafin ƙwallan da ke shirin fitowa ya zubo, "ku yi haƙuri Safna, na san abin da na ke yi bai kamata ba, amma ba ni da wani zaɓi ne, dole-dole in aikata hakan, saboda ba zan iya jurar rasa ko da ɗaya daga cikin ahalina ba. Na yi alƙawarin zan kare ku har iya ƙarshen rayuwata, ba zan taɓa bari wani abu ya same ku ba, wannan shine asalin ni wacece" ta faɗi daga zuciyarta tare da sake share idonta. Dady kuwa babu abin da ya ke sai murmushi, "muna sauraronki yarinya" faɗin Alƙali wa Amna, sai da Amna ta lumshe ido ka na ta buɗe ta cigaba da zanyana komai akan duk shiri ne, Dady bai aikata komai ba, ta ƙarashe maganar da faɗin, "Sannan ya mai girma mai shari'a, duk abubuwan da aka aikata, ba kowa ba ne ya aikata face ni, ni ce na aikata komai sannan na shirya, ni za ku hukunta ba wani ba". Sake tashi su ka yi à tare cikin wani tashin hankalin, taya Amna zata faɗi wa'yan nan magan-ganun? Ya aka yi ta juya abun ya koma haka? Sannan kuma harda ƙara cewa ita ta aikata komai, me ya shiga tunaninta ne wai? Ta ma san nufin abin da ta ke cewa kuwa? Saboda idan har kotu ta amince da zantukanta, to fa zata iya maye gurbin hukuncin da za a yiwa Dady. Safna ji take kamar ta fashe da kuka, saboda yadda ta ke ji cikin ranta, "ya mai shari'a Amna ba gaskiya ta ke faɗa ba, ta yu ko a rikice ta ke, amma wannan mutumin ya aikata duk tuhumar da à ke yi masa!" cewar Yazeed yana kallon Dady cike da tsana, shima Shuraim ya ce, "tabbas haka ne ranka ya daɗe" Dady kuwa haushi ya ji a ransa kan abin da Yazeed ke aikata masa. "Ku yi haƙuri don Allah, yau rana ce ta faɗar gaskiya, don haka saboda kaina kawai ba zai sa na bari a cutar da wasu ba, ku bari a aikata min hukunci daidai da abin da na aikata" faɗin Amna tana bin su Safna da kallo. Girgiza kai su Safnan su ka hau yi alamar ka da ki aikata haka. Kotu ta rikice kowa da abun da ya ke cewa, sai da Alƙali ya kuma tsawatarwa tukunna aka yi shiru, su Safna kuma su ka zauna duniyar tana yi musu ɗaci. Bayan Alƙali ya ɗan yi wasu rubuce-rubucensa ya kuma duban Amna ya ce, "ta ya ya zama ke kika aikata komai a iya shekarun da ki ke da shi? Bayan kuma labarin da aka bayar tun baya na kashe Mai-daraja?" Haɗiye nyawu Amna ta yi kana ta fara inda-indan abun da zata ce. Kafin ta yi magana lauyan Dady ya miƙe yana mai cewa, "ranka ya daɗe idan aka yi duba da maganganun da Amna ta yi, za'a gane cewa duk da kasancewarta ƙarama ba zai hana ta aikata manyan munanan ayyuka ba, saboda ita yarinya ce mai tauri da kuma zafin zuciya, zata iya aikata komai ga duk abin da zai kawo mata matsala, ina da cikakken shaida à kan haka, sannan maganar mutuwar Mai-daraja kuma, ba kashe shi aka yi kamar yadda su ka ce da fari ba, mutuwa ya yi ta Allah da annabi". Bayan shirun da Alƙali ya yi yana ta rubutu da kuma duba wasu takardu, daga ƙarshe ya ɗago kai don kawo ƙarshen komai, gaba ɗaya camera an maida shi kan Alƙali don aji me zai ce. Kan Amna na ƙasa ta rufe ido zuciyarta na bugun taɓaryar ƙarfe, sai ambatan suna Allah ta ke yi babu ƙaƙƙautawa, babu abin da ta ke jira sai jin hukuncin da za'a yanke mata, ko wani irin hukunci aka yanke mata kuwa, zata yi maraba da shi da kuma godewa Allah. Jikin Safna kuma babu abin da ya ke yi sai rawa zuciyarta na bugawa itama, hawaye na ta zarya cikin idonuwanta, Raheena ma idonta ya ciko da hawaye, fiskar momy kuwa tsoro. Ɓangaren su Shuraim kuwa, Shuraim hannayensa duka biyu ya damƙe su, ko da ace zai samu damar rage zafin da ke cikin zuciyarsa, Yazeed ma zuciyarsa sai bugawa ya ke yi tare da tsoro. Haka uncle Musa ma da doctor Salis, idon su ko gezau ba yayi akan Alƙali yayin da su ke cike da fargaba. A ɓangaren su Hajiya da 'ya'yanta kuwa saɓanin haka ne, zuciyarsu cike da murna za a wanke mahaifinsu daga laifi, musamman ma Hajiya, don à halin yanzu in har aka ce babu Alhaji to ya zata yi, Ammu ta riga da ta farka, to me yarage mata kuma? Dama tun asali Ammu ba sa'arta ba ce, saboda ko da wasa ba ta sake mata fiska tun da ta gane nufinta. Alƙali ne ya fara cewa, "bayan duba da duka jawabin da Amna ta gabatar wa kotu, da kuma sauran hujjoji da aka gabartar, kotu ta tabbatar da cew..." kafin Alƙali ya kai ƙarshen maganar, wani police da ya shigo ya tsaida shi, "ya mai girma mai shari'a, wani bawan Allah ne ya ke son a ba shi dama kafin a gama yanke hukunci" Alƙali ya ce ba damuwa à shigo da shi. Fiskar Dady ne ya bayyanar da mamaki sosai, waye wannan mutumin kuwa? Me ya haɗa shi da shari'ar da har zai ce a dakatar da yanke hukunci? Safna kanta na ƙasa ko ɗagashi ta kasa yi, ji ta ke ma kamar zazzaɓi na neman kama ta, shigowa sauran 'yan sanda su ka yi mutumin da ya nemi izini na bayansu, matsawa gefe su ka yi mutumin ya bayyana a tsakiya. Dady saurin cire hannunsa ya yi kan katakon kotu, tare da yin baya yana neman faɗi, gabansa ya yi mugun faɗi da abin da idonsa ya gani, hannuwansa biyu ya sanya yana murza idon na sa da kyau sannan ya buɗe. Su uncle Musa su ka yi saurin miƙewa suna ganin mutumin da ya shigo, jin yadda su ka tashi ne ya sanya Shuraim waigawa inda su ke kallo, shima ya yi saurin tashi tare da zaro ido sosai. Haka su Hajiya ma duka tashi su ka yi cike da tsoro, sauran mutanen kotu ma idonsu na kan mutumin da ya shigo ɗin. "Bawan Allah kai kuma waye ne? Me alaƙarka da wannan shari'ar?" Cewar Alƙali yana kallon mutumin, buɗe baki mutumin ya yi sannan ya furta, "ni suna na Abubakar Mai-daraja!" Wani irin yawo maganarsa ya yi bayan ya shiga cikin kunnen Amna da Safna, dama dukkansu kansu na ƙasa, don haka ba shiri su ka ɗago da sauri suna duban wanda ya yi wannan maganar. daidai ɗagowarsu mutumin ya ƙara cewa, "ni ne Abubakar Mai-daraja wanda aka ambata cikin wannan shari'ar". Faɗin yadda Amna da Safna su ka girgiza ma ɓata baki ne, domin kuwa har sai da su ka tsaida numfashinsu na wasu seconds da ganin Mai-daraja da su ka yi. Hatta mutanen cikin wannan kotun sai da su ka haure da muhawara kan sabon abin da ya ke shirin faruwa. Tsaida su Alƙali ya kuma yi sannan ya kai dubansa kan Mai-daraja cike da mamaki ya ce, "kamar ya kenan?

Chapter 53 of 56