tambayar cikin ƙaguwa, baba Hambali ya amsa mata da faɗin, "eh suna asibiti Hajiya" Zuciyar Ammu ne ya ƙara tashi jin abin da baba Hambali ya ce, cikin rawar murya ta ce, "me kake cewa ne? Me ya same su? Muje ina son inje asibitin".
Hajiya da ke zaune gefe tana kallonsu kawai, Ladingo kuwa tuni ta ƙarawa rigarta iska ta bar gidan, sai Saleem da shima ya shigo ya tarar da abin da ya ke faruwa hakan yasa ya zauna kusa da Hajiya yana bin Ammu da kallon tsantsar mamaki da ganinta zaune, don da da farko ya ɗauka wata ne ma.
Jummala ce taje ta nemn wa Ammu hijab ta sanya mata, ka na suka fice don zuwa asibiti, shiga mazaunin baya Ammu da Jummala su ka yi, shi kuma baba Hambali ya zauna a gaba, sai driver da zai tuƙa su à mazauninsa.
RUKI.
Da gudu ta doso gidan kamar wacche ba ta cikin hayuacinta, fiskarta ya yi baƙi irin baƙin rashin kwanciyar hankali, wannan doguwan rigar da Yazeed ya siya shine har yanzu a jikinta, kanta ko ɗankwali babu, haka ƙafarta babu takalmi, kafin ta kaiga shiga cikin gidan motar da su Ammu ke ciki ta fito, sai dai ba ta da natsuwar tsayawa ganin waye, saboda burinta bai wuce ta shiga gidan ba.
Shigewa ta yi tun kafin a kulle gate, da gudun dai ta nufa ƙofar falo haɗi da shgewa, Hajiya da ta ke ƙofa ta yi tsaye tun bayan fitansu Ammu, ta rasa ma me ya ke yi mata daɗi a duniya, babu wani tunani da yazo ranta sai jugum ɗin da ta ke yi, kafin ta juya daga tsayuwar da ta yi ta ga shigowan Ruki, sai da ta razana sosai, Ruki kuwa tun da ta gane Hajiya ce a tsayen nan ta faɗa jikinta haɗi da sakin kuka sosai.
Saleem ne ya ƙaraso gun Hajiya da sauri yana ƙarewa Ruki kallo, ita kuwa Hajiya sanya hannunta ta yi ta ɗaga Ruki da ke jikinta, fiskarta cike da mamaki da fargaba ta ke kallonta, samu damar buɗe baki ta yi da faɗin, "ke...ke Autana, me ya faru haka? Ya aka yi ki ka zo nan? Ina shi mijin na ki? Ya za ki baro gidan mijinki haka?" Ta jerowa Ruki tambayoyin da ya kuma sanya ta fashewa da wani kukan.
Janta Hajiya ta yi cikin tashin hankali suka nufi kujera suka zauna, shima Saleem daga gefe ya zauna fiskarshi alamar damuwa da ganin ƙanwarsa kuma abokiyar shawararsa tana kuka, "wai ke Ruki me haka ne? Ki yi mana bayani amma sai faman kuka ki ke" cewar Saleem ɗin, ɗago idanuwanta da suka yi shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce, "Saleem ba ka san tashin hankalin da na shiga ba, Saleem baka san iftila'in da ya riske ni ba" tana faɗi ta kuma sanya kuka.
Hakan ya sanya Hajiyar cewa, "na shiga uku na, wani irin iftila'i kika shiga Autana? Ina shi angon na ki Jaiz? Waii to ko matsala kuka samu ne?" "Hajiya ba fa wannan mutumin da kika sani da suna Jaiz na aura ba" cewar Ruki tana ƙoƙarin share hawaye, rass gaban Hajiya ya faɗi, Saleem ma sai da ya zaro ido da jin abin da ƙanwarsa ta ce.
Last part.
___________________________________________________
Hmm ga dai uncle Musa ya kai su Amna asibiti.
Shin me zai faru gaba? Me nene Baba tsoho zai sanar da su daga baya? Sannan waye ma Baba tsoho ne?.
Ruku ta dawo gida, ya akayi ta dawo?.
Mu kasance a next part idan Allah ya kaimu.
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣6️⃣1️⃣▶️1️⃣6️⃣2️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar
_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_
*BARKANKU DA WANNAN LOKACI 'YAN UWAN ARZIƘI, INA MAI SHEDA MUKU CEWA NA CANZA SUR NAME ƊINA🤭 DAGA YANZU INSHA ALLAH ZAN CIGABA DA AMFANI DA. AISHA G UMAR ZAHRA-TUL-QALAM. INSHA ALLAH HAKA ZAKU CIGABA DA SANI NA DA SHI DAGA YAU, INAI MUKU GODIYA DA NUNA ƘAUNA, FATAN ALKHAIRI GAREKU🙏🏻*
Hakan ya sanya Hajiyar cewa, "na shiga uku na, wani irin iftila'i ki ka shiga Autana? Ina shi angon na ki Jaiz? Wai to ko matsala ku ka samu ne?" "Hajiya ba fa wannan mutumin da kika sani da suna Jaiz na aura ba" cewar Ruki tana ƙoƙarin share hawaye, rass gaban Hajiya ya faɗi, Saleem ma sai da ya zaro ido da jin abin da ƙanwarsa ta ce.
Nan Ruki ta zayyane musu duk abin da ya faru, da kuma yadda aka yi ta dawo gida.
_ranar da abun nan ya faru Sam Ruki ta kasa sukuni, kuka ta ke ta yi kamar hawayenta zasu ƙare, ace a matsayinta wai irin wannan miji ta aura, ita tsoronsa ma ta ke yi, hakan yasa a ƙarshe zuwa ta yi ta kulle kanta cikin toilet ta ƙi fitowa, a ciki ta kwana, duk magiyan da Jaizu ya yi mata akan ta fito shifa yau angonta ne, amma sai cewa ta yi don Allah ya daina yi mata magana, wallahi tsoro ya ke bata, kuma duk inda asalin mijinta Jaiz ya ke to ya nemo mata shi, don ƙarya ya ke yi shi ba mijin da ta aura ba ne, haka ta kwana ga yunwar da ya dameta, amma ta ƙi fitowa har ta kwana a ciki, washe gari, da yunwa ya addabeta ta miƙe tana tunanin me zata yi, sai da ta kara kunnenta jikin ƙofa, jin shiru ya sanya ta buɗewa ta fita, ai kuwa tun ledar da ya shigo da ita jiya ne, don haka ta wawuri ledar ta kuma komawa toilet, haka ta kuma sake kwana cikin bayi, Jaizu na zaune a gefen gado, fiskar nan ta shi ya kuma haɗeta tamau, taya amaryarsa Ruki zata yi masa haka? kawai ya ji dirar mutane cikin ɗakin, ko da ya ɗaga idonsa ɗayan nan ya ga samari tiƙa-tiƙa guda uku, kafin yayi magana ɗaya daga cikinsu ya ce, "kai ƙaramin ɗan iska ina ita Rukun ta ke?!" A razane ya furta, "cu waye u?" Ya faɗi da wannan muryar ta sa, ai kuwa aka ɗaura masa bindiga a kai, a razane ya nuna musu toilet, ai kuwa suka isa wurin su ka fara bubbugawa, Ruki da ta shiga tashin hankali bayan ɗan hayaniyar da ta ji, ta yi saurin ja da baya wasu hawayen na jero mata a fiska, nan ta tsinkayi muryarsu suna faɗin "ki fito" ganin ta ƙi fitowa ya sa suka kuma cewa, "idan baki fito ba zamu fasa ƙofar sannan mu fasa kanki da bindiga!" Tun kan su ida maganar Ruki ta tashi daga daɓashen da ta ke jiki na rawa ta buɗe ƙofar ta fito, kota ina na jikinta ɓari ya ke hatta bakinta, kallonsu ta ke da masifaffen tsoro, domin ta zata shi Jaizun ne ya aiko a kasheta kawai ta huta, tun da ita dai kwaɗayayyiya ce, amma bata san cewa Dadynta ne ya aiko su su fitar da ita daga gidan ba, domin ya saka ayi masa bincike a kan wanda ta auran, idan sun gano to su fitar da ita daga gidan kafin daga baya ya san abin yi, bayan ya gama mallakar komai. Ɗaga kai Ruki ta yi zuwa inda Jaizu ya ke, amma kuma ta ga shi kansa Jaizun jikinsa ɓari ya ke yi, su kuwa wa'yan nan mutanen rufe Jaizu da duka suka yi, sai ihu ya ke yi da lauyayyen muryarsa, suna gamawa suka juyo inda Ruki ta ke, da sauri ta durƙusa tana kukan da dama bata bar yinsa ba ta ce, "don Allah ku yi haƙuri, wallahi ni ban san shi ba, cutata ya yi ya kawo ni gidan nan, shi zai ba ku duk kuɗin da kuke buƙata, amma wallahi ni banda ko asi" ta faɗi domin yanzu ɗauka ta yi ɓarayi ne su ka shigo gidan, "wuce muje!" Ɗaya ya faɗa mata da ƙarfi, ba musu ta yi gaba tana haɗiye kukanta. A mota suka sanya ta, sannan su ka ja motar, zuciyar Ruki ya ƙi tsagaitawa, yanzu kuma ta gama sadaukarwa 'yan kidnapping ne su, suna zuwa daidai gate ɗin shiga unguwar su ka ce da ita ta sauka, su kuma suka ƙarawa motar giya, juyowa ta yi tana kallon a ina suka ijjeta, domin bata yi tsammanin gida suka kawota ba, aikuwa da mamaki ta ga ashe a unguwarsu a ka ijjeta ma, ai kuwa sai ta sa gudu zuwa gidan_
Salati da sallallami Hajiya ta saka bayan Ruki ta gama shafa musu abin da ya faru, "wai kuwa yau wace iriyar rana ce haka? A ce abubuwan bala'i sai faruwa da mu suke? An ma wallahi na tsine wa wannan yaron ɗan iska! Ya cuce ni ya cuci 'yata, yanzu ashe dama ba shi ba ne ki ka aura, amma an yi ɗan iska wallahi! Ni Zainabu ina zansa kaina?" Cewar Hajiya ta sa kukan takaici, itama Ruki rungumarta ta kuma yi tana kuka, shi kuwa Saleem kallonsu kawai ya ke ya ma rasa ta cewa.
"Yaron nan ya riga da ya sa ni a bakin diniya, ya yaudare mu, yanzu duk maganar alƙawarin da ya yi mana ya zama shara kenan?" cewar Hajiya tana matse ƙwallan baƙin ciki, Saleem ya numfasa ka na ya ce, "lallai an ɗura ku a buhu Hajiya, ke Ruki amma dai babu abin da ya shiga tsakaninki da shi ko? Gwara ki faɗa mu ji tun wuri Hajiya ta neman miki magani, don kar kin shigo mana da cuta cikin gida, saboda yadda ki ka suffanta mana shi zai yi wuya baya tattare da wasu cututt..."
"Ba shakka! Rufa min baki ko in faffashe maka shi a wurin nan, ku ji min rashin daɗin magana, wallahi Saleem ka kiyayeni, muna cikin alhini idan baka taushe mu ba ai ba ka ƙara mana ba, shashasha kawai, matsalar ƙanwarka bata dameka ba kenan?" Cewar Hajiya cikin ɓacin rai, shiru Saleem ya yi bai kuma yin magana ba, sai ma miƙewa da ya yi yana latsa wayarsa.
HOSPITAL.
Ko da su Ammu su ka isa Asibiti, kai tsaye gurin uncle Musa Ammu ta nufa, domin ta gane shi abokin Mai-daraja ne, "Mum... Musa me ya sami Shuraim da Amna? Kada ka ce mun wani mummunan abu ya faru da su, suna ina?" Ta yi maganar tana hawaye, domin bata san cewa ba Shuraim da Amna kaɗai ba ne a asibitin, shi kuwa uncle Musa da dama bushewa ya yi kawai yana kallonta, ganin da tafiya ta iso gabansa, kuma ya san dai bata iya ko tashi Shuraim ya sanar masa, juyawa uncle Musa ya yi yana kallon Hambali da kuma Jummala, hakan yasa Hambali ya iso kusa da shi.
Ya ce, "yallaɓai muma mun shiga kwatan-kwacin yadda ka shiga yanzu a mamaki, mu ma kanmu ba mu san ya hakan ya kasance ba, shiyasa ko da ka kirani ban sanar da kai komai ba, sai mun zo ka ga ni da kanka" uncle Musa ya maida kallonsa ga Ammu da ke fitar da hawaye ya ce, "ikon Allah kenan, Maryam yau ke ce a kan ƙafafunki?" Sai da Ammu ta share hawaye sannan ta ce, "ƙwarai kuwa ni ce, kamar yadda ka ce ikon Allah, to tabbas ikon Allah ne, ya nufeni da warkewa ya bani lafiya, kuma na gode masa sosai da wannan waraka da ya bani, abin da na ke son ji daga gareka Musa, don Allah ka yi min bayanin me ya sami yaran nan? Hankalina ya gaza kwanciya tun da suka bar gidan, an yi ta kiran numbernsu baya shiga".
ta faɗi tare da sunkuyar da kai ta ɗaura da faɗin, "ni dama na riga da na san zuwansu wannan wurin hatsari ne, ba za su iya da Jamilu ba, mutum ne mara imani, amma sai ga shi na makara, har suka fita ban dakatar da su ba" wasu hawayen ne suka gangaro à idon Ammu, "ka faɗa min me ya same su yanzu?" A hankali uncle Musa ya ce, "ki kwantar da hankalinki Maryam, likitoci suna iya bakin ƙoƙarinsu yanzu haka a kansu, kuma insha Allah muna sa ran za su warware" "Allah ya sa" cewar Ammu tare da zama a kujera ta yi tagumi.
BAYAN WANI LOKACI.
Likitoci sun ba Ammu damar shiga ɗakin da aka kwantar da Amna da Safna, saboda yadda suka ga ta damu sosai, à hankali ta buɗe ƙofar ta shiga, nufa inda Amna ta ke ta yi tana zubar da hawaye, duk da cewa ta san ba 'yarta ba ne amma tana jinta har cikin jininta, zama ta yi a kan gadon da Amna ta ke kwance.
Hannunta ta ɗaura a kan hannun Amna tana shafawa a hankali, tana kallon yadda aka kewaye kan Amna da bandeji, ga gefen fiskarta ma da wasu ɓangarorin jikinta duk sun sha auduga, cike da tausayawa ta ce, "yata? 'Yata ki buɗe idonki mana, ki ga Ammu na yi miki magana, ba ko da yaushe kina ce min kina da burin jin murya ta ba? Kina ce min Ammu ina son jin ya muryarki ta ke, to yau gani ina yi miki magana Amna ki buɗe idonki ki ganni, kin ji Amna?" Ta faɗi hawayen da ke cikin idonta bai tsaya ba.
Gefe ta yi da idonta tana matsar wasu hawayen masu raɗaɗi, kwatsam idonta ya gane mata wata mace a kan gado da ke can gefe, wanda ba ta yi la'akari da shi ba tun shigowanta, zunbur ta miƙe tana kallon wacche ta ke kwance da fiskar "yarta, da sauri ta juyo da fiskanta kan Amna, sai yanzu ta lura babu tabon gefen bakin da Amnan ke sanyawa, zare ido ta yi haɗi da dafe ƙirji.
A hankali ta ke takawa zuwa gaban Safna, bakinta na karkarwa ta ce, "Ss..ss..Safna ta" ta faɗi wasu sabbin hawaye na koranyowa daga cikin idonuwanta babu ƙaƙƙautawa, a hankalin ta zauna a gefen Safna haɗi da ɗaura hannunta a gefen fiskar Safnan, itama ga shi an yiyyin mata triment sosai a jiki, sai dai ita ba a kewaye mata kai da bandeji ba.
Cikin marairaice fiskar da ke neman fashewa da kuka Ammu ta ce, "Saf safna, Safnata ki buɗe ido kin ji? Yau ranar da zan fita daga ciki tsohon jinyar kewarki ne my daughter, ki buɗe ido ki ga Ammunki, ki buɗe ido mana Saf Safna, na daɗe da kewarki har ya zame min jinya, 'yata" Ammu na faɗi ta fashe da kuka haɗi da kwantar da kanta a jikin Safna.
Sai kuma ta tsaida kukan tare da miƙewa tana share hawaye, "kin ga a tsaye na ke my daughter, na warke, ina motsa ko wace gaɓa ta jikina" ta faɗi tana jujjuya hannayeta don ta tabbatarwa Safna, ta kuma cewa, "kin ji magana ma ina yi, na dawo kamar da, na riga da na warke yanzu, ki buɗe ido ki yi min magana don Allah 'yata" tana ƙarashewa ta kuma sakin kuka ta koma jinkin Safna.
"Ammuna" kamar daga sama ta ji muryar Safna da ke tattare da jinya cikin kunnenta, saurin buɗe idonta ta yi haɗi da ɗaga kanta don ganin da gaske maganar Safnata yi? Cikin ƙarfin hali na majinyaci, da kuma farin cikin da ya cikata na ganin Ammu a kusa da ita, domin dama ba ta da wani burin da ya wuce wannan, hakan yasa ta sakarwa Ammu murmushi tare da fitar da hawayen jin daɗin da babu misali, "my daughter!" Ammu ta furta cikin muryar kuka, Safna ta ƙara samun damar cewa, "my Ammu ta warke? Ammuna ta samu lafiya? Ammuna na ke gani? Haka ne ko Ammu? Ba mafarkin da na saba ba ne ko? Ke ɗin ce ko?" "Ni ce 'yata, ni ce ba mafarki ki ke ba, ni ɗin ce a gabanki" Ammu na faɗi Safna ta fashe da kukan tausayi, Ammu ma ta rugume Safna daga kwancen da ta ke suna kukan tare, sun ɗau mintuna a haka ka na Ammu ta samu damar tashi tare da sharewa Safna hawaye.
"My daughter ina ki ka shiga tsawon lokaci haka? Ko da ya ke na san tura ki Nijar da muguwar nan Zainab ta yi ne ko?" "No Ammu" cewar Safna itama tana ƙoƙarin gogewa Ammu hawaye duk da jikinta babu ƙwari, riƙe hannunta Ammu ta yi fiskarta alamar tambaya ta ce, "me ki ke nufi da no daughter?" Nan Safna ta ba Ammu labarin abin da ya faru har lokacin da ta faɗa rami kana ta ƙara da cewa, "bayan na faɗi ne su uncle Musa su ka samu damar samuna yashe a gaɓar teku, nan su ka ɗaukeni su ka yi ta yi min magani, domin na share lokaci ba tare da na san ina hankali na ya ke ba, cikin ikon Allah na samu lafiya Ammu".
Alhamdulillahi Ammu ta ambata da kuma matso wasu ƙwallan, "Allah sarki, lokacin da Amna ta zo da na ɗauka cewa ke ce, duk da wasu alamomi da su ka bayyana a gareta, ta sanar da ni labarin ahalinta, kuma tana ƙaunarsu sosai, da daɗewa na ke mata burin komawa garesu, duk da cewa na saba da ita, amma zan so ta kasance tare da su saboda zata fi yin farin ciki, amma kin ga ita bata buɗe ido ba, bata farka ba, bamu yi wa Amna adalci ba, itama tana tare da kewan familynta, saboda na fiskanci hakan a gareta lokuta da dama.
Ammu ta ƙarashe maganar tana kallon inda Amna ta ke, "Ammuna Amna baza ta koma ko ina ba, saboda mu ne asalin danginta" cewar Safna tana ƙoƙarin zama da ƙyar, murmushi Ammu ta yi tare da juyowa inda Safna ta ke, sai da ta share hawaye sannan ta yiwa Safna alama da ta daina ƙoƙarin tashi, ka na ta ce, "na sani my dear, Amna ta cancanci zama tare da mu, saboda yarinyace mai kirki, yarinya ce da take cire duk mutumin da ta gani yana cikin damuwa, amma dole mu yi haƙuri ta koma gurin danginta, zata fi samun farin ciki".
"Ammuna Amna 'yarki ce, ke ki ka haifeta ba wata ba," cikin tsananin mamaki Ammu ta ke cigaba da kallon Safna jin wani ruɗaɗɗen maganar da ta faɗa, taya Safna zata ce ita ta haifi Amna? Don kawai kasancewar Amna kamanninta? Duk da cewa tana jin son yarinyar har cikin ranta, amma ta ya hakan zai yu?, "yes Ammu Amna 'yar uwa ta ce, 'yar biyu na ce ita".
Last part.
___________________________________________________
😌 abin da zance yau, idan ana son in ƙara yawan typing à yi mini like fisabilillah🙏🏻 sannan à yi min sharing, tun da dai ana yi min rowan Comment, muƙus fa nake jinki 'yan uwan arziƙi kamar anyi ruwa an ɗauke😁 ko ba ason in kammala AMNA DA SAFNA da wuri ne?
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣6️⃣3️⃣▶️1️⃣6️⃣4️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar
_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_
"Ammuna Amna 'yarki ce, ke ki ka haifeta ba wata ba," cikin tsananin mamaki Ammu ta ke cigaba da kallon Safna jin wani ruɗaɗɗen maganar da ta faɗa, taya Safna zata ce ita ta haifi Amna? Don kawai kasancewar Amna kamanninta? Duk da cewa tana jin son yarinyar har cikin ranta, amma ta ya hakan zai yu?, "yes Ammu Amna 'yar uwa ta ce, 'yar biyu na ce ita" Safna ta kuma faɗin hakan don tabbatarwa Ammun.
"My dear kin san abin da ki ke cewa kuwa? Ya aka yi ki ka yi irin tunanin nan?" "Tabbas Ammu gaskiya na ke faɗa miki, a yau Dad.." sai kuma Safna ta dakata da kiran Dady ta ce, "Zabba-ba ya tabbatar mana da hakan, Ammu ashe duk shi ya kashe min mahaifina? Ammu yau na ji abubuwan tashin hankalin da ban taɓa ji ba a rayuwata, na ji abubuwan da su ka kerewa hasashena, haƙiƙa Dady ya cuce mu Ammuna, ba zan taɓa yafe masa ba!" Safna ta ƙarashe da sake yin wani kukan, rungumarta Ammu ta yi ita ma tana hawaye tare da bubbuga bayanta kaɗan.
"Tabbas haka ne, Jamilu ya cuce mu cutuwa na haƙiƙa, amma ban fahimci maganarki ba 'yata, me tsakaninmu da Amna har Jmilun ya faɗa?" Kaɗan daga cikin labarin abin da ya faru Safna ta ba Ammu, tun kan ta ƙarisa Ammu ta kuma fashewa da matsanancin kuka, dai dai shigowar uncle Musa, ƙarasowa inda su ke uncle Musa ya yi da ganin sai kuka su ke daga Ammun har Safna.
"Maryam don Allah ki bar kukan nan, ke ya kamata ki rarrashi Safna amma kema ki na yin hakan, kuma kinsan dukkanku ba isashshen lafiya ba ne da ku" cewar uncle Musa yana kallonsu cikin tausayawa. Ɗago kai Ammu ta yi tana cewa, "ya zan yi to Musa? Ni fa macece mai rauni, dole na yi kuka saboda Jamilu ya cuce ni ta ko ina. Da fari ya yi sanadiyyar salwantar min da 'ya'yana tun kan su daɗe a cikin cikina, sannan ya kashe min mijina kuma farin ciki na, ashe dai ya tafka min wani babban baƙin cikin ba tare da na sani ba, dole inyi kuka Musa".
Tana faɗi ta kuma tuntsurewa da wani kukan, jin jina kai kawai ya yi tare da maida kallonsa gefe, saboda tausayi suke ƙara ba sa sosai, Miƙewa Ammu ta samu damar yi tana kallon inda Amna ta ke kwance, sai kuma ta juya wurin Safna, Safna ta ɗaga mata kai alamar, jeki gurin 'yarki Ammu, tare da sharar hawaye.
Ammu ta ƙara mayar da idonta gun Amna haɗi da isa inda ta ke, hannayenta gaba ɗaya rawa suke yi sun kasa daidaita zuwa taɓa jikin Amna. Kafin Ammu ta samu damar ɗaura hannun, wani irin numfashi mai ƙarfi Amna ta ja da ya rikita Ammu, domin kuwa bayan wannan jan numfashin ƙirjin Amna ya fara ɗagawa, kamar dai numfashin na ta baya fita yadda ya dace, "Ammu me ya sami Amnan?" Safna ta yi tambayar cikin rashin nutsuwa.
"Nima nima ban sani ba 'yata, amma kamar numfashinta..." Kafin Ammu ta kai ƙarshen maganar Amna ta kuma jan wani numfashi da ƙarfi wanda ya fi na ɗazu ƙara, "me ya ke faruwa ne, Am Amna me ya same ki?" Cewar Ammu cikin ruɗewa. Ƙoƙarin sauka Safna ta ke tare da rintse idon ciwo, amma dole ta tashi ganin abin da ya tada mata hankali.
Uncle Musa ne ya shigo da likitoci cikin ɗakin, domin kuwa tun farkon jan numfashin Amna ya fice kiran doctors. Kan Amna doctors su ka yi suna ƙoƙarin gano abin da ya ke sanya ta haka, "ya kamata muyi gaggawan kaita ɗakin emergency ina ganin hakan zaifi" cewar babban doctorn.
Hankalin su Ammu ba ƙaramin tashi ya yi ba da jin abin da doctor ya sanar, hakan ya nuna musu cewa al'amarin babba ne, Safna da ta samu damar isowa kusa da Ammu tana hawaye, ta dafa Ammu da ke faman kuka, shigowa da gado mai taya aka yi don ɗaukar Amna, su ka ɗaurata akai a kai ka na suka doshi hanyar ƙofa suna tura gadon, bin baya Ammu ta yi tare da son taɓa Amna tana kuka, durƙushewa a ƙofa ta yi bayan an fice da Amna daga cikin ɗakin.
"wai me ya samu 'yata ne? A ah babu abin da ya sameta, tun tana cikina ban san da zamanta ba, ban san na haifeta ba, ban zauna da ita ba, ban ɗauketa à hannuna ba, ban ji ɗuminta à jikina ba, sai yau na san da cewa ita ɗin 'yata ce, ya Allah ina roƙonka ka da ka bar wani abu ya same ta" faɗin Ammu cikin muryar kuka, Safna ma faɗi a jikinta ta yi suna ta rusan kuka. Uncle Musa cikin tausayawa ya buɗe baki zai yi magana, amma shigowar Shuraim ya dakatar da shi.
Shigowa Shuraim ya yi yayin da jikinsa shima ya sha ɗaure-ɗauren asibiti, yanayin shigowarsa cike da tashin hanakali, domin tun da ya samu damar farkawa ya ƙi zama, duk yadda nurses su ka yi da shi amma ya ƙi, hakan yasa ya taho ɗakin da su Amna su ke don ya ga ya lafiyarsu.
Tsayawa ya yi yana kallon
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 56