Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tayi cikin ɓacin rai kuma idonsa a kan Shuraim, abincin ma ya daina ci. Zare ido kaɗan tayi, idan zuciyarta gaskiya take sanar mata to fa Yazeed kishinta ya ke, tabbas kuwa domin shi kallon Safna yake mata. Haɗa ido Saleem da Ruki suka yi, sabi da kishin da suka ga na giftawa tsakanin Shuraim da Yazeed, taɓe baki su kayi cikin jin haushi suna sake mayar da idon su kallon film. Shuraim kuwa sanyawa Amna ferfesun potato yayi wanda aka sarrafa shi tare da hanta, sanna ya ijje gabanta ya n'a cewa, "wannan yayi daɗi, and it's perfect for dinner, try it". "Ok thank you" Amna ta faɗi tare da sake kallon Yazeed ɗin, sake ganinsa tayi cikin wani ɓacin rai, hannunsa cikin cokali yana ɗan bubbuga cokalin kan plate ɗin abincinsa, har ƙara n'a ɗan fita, idonta na kansa ta fara cin abincin na ta, "ya kika ji shi?" Shuraim ya sake yi mata tambayar, ta basa amsa da cewa, "yes it's delicious" ta faɗi harda giɗa kai. Tashi kwai Yazeed yayi yana shirin barin wurin, Amna ta tsaida shi da faɗin, "ina zaka je? You haven't finished eating your food" "ya ishe ni!" kawai ya furta, "oh my god! Wannan fa kishi haƙƙun yake yi" cewar Amna a zuciya. WASHE GARI. Amna ce ta fito daga falo cikin shigar riga da skirt n'a Safna, duk da cewa ba wai iya ɗaurin ɗan-kwalo tayi ba, amma tayi ƙoƙari gurin ɗaura shi, Yazeed da ke ɗan nesa da ita ne ya hangeta, sai kuma ya ɗaure fiska ganin Shuraim da ya zo wucewa ya tsaya suna magana da ita, ba tare da ya ji me suke tattaunawar ba. "Sai ina madam C.E.O?" Faɗin Shuraim yana kallonta, "ina ruwanka ɗan sa ido?" "Call me by whatever name you want, amma dama haka atamfa take miki?" Ya ƙarashe faɗi yana ɗan sauya fiska, Amna tayi saurin faɗin, "me take yi min?" ta faɗi tana kallon jikinta domin ita a tunaninta bata yi kyau ba ne, sai da Shuraim ya yi kamar zai ce bai yi kyan ba ka na ya ce, "immm toh, kawai dai wani iri kika yi sabida kyan ki ya fito daya a ciki" ya ƙarashe cikin fara'a, murmushi ne ya bayyana a fiskarta, ta ji daɗin jin yadda ya ce tayi kyau ɗin. Raheena. Dama ta riga da ta sanar da Amna tana zuwa, hakan ne ma ya fito da Amna daga cikin ɗaki don ta tarbeta, shiga gidan tayi ta bar driver a waje, nufan hanyar da zai sada ta da falo tayi, nan ta hange Amna. Itama Amnan kallonta da tayi ne yasata barin wurin Shuraim ta ƙarisa inda take tana yi mata barka da zuwa, hangar Yazeed Raheena tayi cikin mamaki take kallon sa, Amna kuma ta kama hannunta suka shige ciki. Shuraim bai bar wurin ba, ya ɗaga hannu yana duba agogon hannunsa Yazeed ya zo wucewa, "barka dai Yazeed" ya faɗi hakan ya dakatar da Yazeed da shigewa falon da yake yi, takowa zuwa inda yake Shuraim yayi tare da cewa, "na lura tun da ka dawo ka ɗauke ni maƙiyinka, kuma à iya sani na ban taɓa sanin ka ba sai yanzu, to ko zaka iya sanar min menene silar ƙiyayyar da kake yi mini?". Cikin ɓacin rai Yazeed ya juya Haɗi da cakumar kalar rigar Shuraim, cike da haɗaka ya fara magana, "are you asking me? I say are you asking me!? Kana cusa kanka akan gurbin da ba naka ba, kana mu'amala da abin da ba naka ba, sannan kake tambayana me yasa?!". Ya ƙarashe faɗi cikin ɗagun murya. Shuraim da yake kallon sa ne ya saki murmushi, sannan ya ɗaga hannayensa tare da sanyawa akan na Yazeed yana ɓanɓaro hannayen Yazeed ɗin daga cafkar kolarsa da yayi masa. Kallon hannun Shuraim ɗin Yazeed yayi bayan ya sauke nasan, sannan ya maida maganansa ga Shuraim, "zai fi kyau ka adana kakkausan magan_ganun nan na ka a gareni, ni banyi maka kama da wa'yan da za ayi wa hakan ba! So be careful!" Cewar Shuraim yana wucewa ya bar Yazeed tsaye. Da wani kallo Yazeed ya bishi, zuciyarsa na sake tsanar guy ɗin karo na babu adadi, "wannan shi yana ɗaukar kan sa menene? Ko da yake duk Dady ne ya ja min wannan abun, akan me zai kawo mutum gidansa wai don wani abun da yake so?" Ya faɗi a fili cikin ɓacin rai, domin Dady ya sanar da shi komai. "Ke Amma yaushe Yazeed ya dawo ne?" Raheena ta faɗi cike da mamaki, "shekaran jiya ya ne" "amma ko ya miki wata maganar? Nasan dole zai ɗauka Safna ce" numfashi kaɗan Amna ta saki sannan ta sake cewa, "no he said nothing, amma da alama yana son faɗin hakan, kuma ni bazan bar hakan ta faru ba". Cewar Amna tana kallon inda mirror yake, amma tunani na wani wurin. Shuraim da isan sa ɗaki bai zauna ba, domin Yazeed ya ɓata masa rai sosai, "to duk akan me yake wannan abun ne? Akan Amnah? To akan ma me zaiyi hakan wa Amna? Duk da shi gani yake Safna ce, amma ai yaran Hajiya ba sa sonta, duk da cewa gwara shi baya yi mata mugunta kamar sauran, amma nuna kishi haka me yake nufi" ya faɗi tare da daidaita numfashin sa ya zauna kan gado. Sai kuma ya sake cewa, "no idan ma wata mummunar abun yake shirin yi to bazan taɓa barin hakan ba!" Ya faɗi domin shi bai san da maganar tsakanin Safna da Yazeed akan ko suna soyayya ba, don bai taɓa tambayar su Jummala akan hakan ba, a hankali kuma ya bar wannan tunanin ya koma kan Amna, "atamfa na yi mata kyau sosai" ya faɗi tare da sakin murmushi cikin annashuwa. Hajiya ce zaune ita da Ruki a cikin ɗakinta, "tun tuni nake son inji a ina kika tsaya da maganar aure na da Jaiz, sannan shima ya riga da ya ce min a shirye yake yanzu, kuma sun shirya komai shi da ahalinsa, yadda za'ayi komai ba tare da sun bayyana ga Dady ba, duk da cewa ya shi wahala kafin su amince da yin hakan, saboda haka Hajiya ki yi min ƙarin bayani, kin san ke ce duk dogaronmu a yanzu" cewar Ruki cikin nuna ta damu. Kamo hannayenta Hajiya tayi tare da murmushi tana faɗin, "to ke a tunaninki na rabu da maganar ne? Inaa ai bazan ma iya ba, duk kwanan nan babu abun da na sa a gaba kamar wannan zancen ni da ƙawata Ladingo, kuma albishirinki?" Da azarɓaɓi Ruki ta ce, "goro, goro Hajiya momyna" "to ki kwantar da hankalinki domin duk wani abun da ya kamata na kammala shi, don haka yanzu zan sanar da ke komai, da kuma yadda zaki faɗawa shi yaron kirkin". Cewar Hajiya tare da yin wa Ruki wani kallon da ke nuna kisha kuruminki. Last part. ___________________________________________________ To ko ya gasa zai cigaba da kasancewa tsakanin Yazeed da kuma Shuraim? Koya wannan auren zai kasance tsakani Ruki da Jaiz, gashi Hajiya da maƙon tsiya ta hana mu zuwa cin shinkafa da nama da kuma lemo na shagali kafin ranar aure😒 amma koma dai me qi dole muci na ranar biki🙃 Mu kasance da ku a next part don jin yadda zata kaya, alƙamin✍🏼 {Mrs Umar} [Gimbiyar Fasaha]👸🏽 ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣2️⃣1️⃣▶️1️⃣2️⃣2️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 YAU TALATA, SANNAN KUMA YAYI DAIDAI DA GOBE NE RANAR AUREN MARWAN. Tun shekaran jiya mutane suka fara taruwa a gidan, amma a ɗayan ɓangaren da basu kai wannan girma ba Hajiya ta fi hada-hadar, sai hidima akeyi Hajiya ta karɓar baƙinta, domin har da masu kwana. A ɓangaren sashin su kuwa, Amna ce ke fitowa daga falon, jiki a sanyaye, tafiya take yi amma hankalinta na wani wurin, ba komai bane ya sata wannan yanayi sai abun da ta gani. .......Bayan ta sauko daga upstair ta zauna kan kujera a falo tana jiran fitowar Shuraim su wice aiki, duk da cewa gobe ne auren Marwan Amma bai hana su zuwa aikin ba, kasancewar suna da ayyuka a office. Tana zaunen wayar Yazeed da yake gefenta saƙon sim ya shigo, idonta ne ta kai kan wayar tana faɗi a zuciyarta, "ina yayi kuma ya bar wayar anan?" Ta faɗi tana kau da kanta daga wurin, sai dai bayan ta kauda kan na ta sai taji tamkar akwai abun da idonta ya gane mata a fiskar wayar, ko da ta sake juyawa inda wayar yake hasken ya riga ya mutu, sa hannunta tayi don kunna wayar ko zata ga menene idon na ta ya gane mata da kyau, da tsananin mamaki ta bi hoton Safna da ya bayyana akan fiskar wayar sosai, kallon hoton take har hannunta na rawa ba tare da ta sani ba, hoton Safna a fiskar wayar Yazeed? Kenan hakan na nuna tabbacin yana son Safna? Saurin ijje wayar tayi ta miƙe zumbur tana maida numfashi, ta bar wurin don fita waje...... Wannan shine abun da yasa guiwarta ya saki, a take ta fara jin wani iri mai kama da tausayin Yazeed ɗin, ƙarasawa gurin motar Shuraim tayi ta tsaya, tana cigaba da saƙa da warwara cikin ranta. Mutane sun hallara sosai, duk da cewa mafi yawan su mata ne, kasancewar kowa na jiran wannan bikin, wasu da yawa suna tsakar gida, amma da yake gidan na da girma, hakan yasa ba sa ganin abun da ke wakana ta wani gefen. Yazeed ne ya taho daga wani gefen ba falo ba ya iso in da Amna ta ke, hanaklinta ba ya wurinsa hakan yasa ba ta ma san lokacin da yazo ba, "Safna" ya faɗi mata cikin murya tausassa, sai à lokacin ta ɗago ta kalle sa, sai tayi saurin saukar da kai kamar kunyarsa ta ke yi, ba tare da ya lura ba ya kuma cewa, "company zaki ko? To muje in kai ki". "No need!!" Cewar Shuraim da sigar dakatarwa, "hei wai kai me kake ɗaukar kan ka ne!?" Cewar Yazeed cikin ɓacin rai, "duk yadda ka ɗauka" Shuraim ya bashi amsa sannan ya buɗe wa Amna ƙofar mota don ta shiga, sai da Amna ta kalli Yazeed yadda jikinsa ke famar rawa fiskarsa cike da ɓacin rai, jiki a sanyaye ta shige motar, shi kuma ya kulle sannan ya zagaya ya shiga mazaunin tuƙi. Yazeed n'a sake da baki Shuraim ya ja motar suka wuce sa. Wani irin ƙollah ne suka tsatso masa cikin idanu bayan sun fice daga gidan, domin ko kaɗan bai yi tsammanin Safna zata shiga motar ba, sai gashi ta shiga har sun wuce. Shiga toilet yayi bayan ya shigo ɗakinsa harda rufe ƙofar da ƙarfi, duk da ƙarar da ƙofar yayi bai kai yadda zuciyarsa ta kenyi ba, yana shiga ya sakarwa da kansa shawa, tare da sanya hannayensa akan gani, ya ɗaga kan sa sama yana kallon ruwan da yake zuba yayin da yake jin zuciyarsa na yi masa suyar gashin nama. Daga zuciyarsa yake magana, "me yake faruwa da ni ne? Me yasa mafarkina ke shirin zama ƙarya? Wani irin zunubi ne na aikatawa Safna da har take yi min wannan horon haka? Bayan na tafi n'a daina samunta à waya, sanna n'a dawo na sameta da waya, amma bata taɓa nema na ba, ko da sau ɗaya ne, shin ta dai na sona ne, ko kuwa menene?" Sai kuma yayi ƙasa da kansa, zafafan hawaye ya fara zubar masa, bai san me ya kamata yayi ya dai na jin wannan yanayin ba, shawa n'a aikinsa suma idanu na aikinsu na hawaye. Sai da ya ɗau minti goma a cikin wannan hali ka na ya fito jikinsa jagof da ruwa, bai yi ƙoƙarin canza kaya ba, sai ma zama à kan kujera da yayi tare da lafewa à kai yana sauke ajiyar zuciya daga ta ciki. AMNA. Tun da suke tafiya cikin wannan motar babu wanda ya yi yunƙurin yin wata magana, bare ma Amna da jikinta har yanzu yake a sanyaye, ji tayi ta fara tausayin Yazeed kamar Ammu, "ya kamata mu daina yawan kasancewa taren" cewar Amna idonta na kan hanya, da mamaki shima Shuraim ɗin ya ce, "mu daina kasacewa tare? Kamar ya kenan kuma akan me?" "Mu daina yawan yin magana tare sannan kuma daga yau mu daina tafiya company tare zan rinƙa hawa wani motar kamar yadda muke a baya". Cikin ƙarin rashin fahimta Shuraim ya kuma tambayarta, "har yanzu baki faɗa min dalilin ba?" "Saboda Yazeed! Domin shi gani yake akwai wata alaƙa a tsakani na da kai" ta yi maganar da sauri, saboda ita gani ta ke kasancewar da suke ita da Shuraim ɗin n'a sanya Yazeed ɗin cikin halin kishi, ita kuma ba ta son ta ga yana hakan, domin sai ta ga kamar ba adalci tayi masa ba, tun da shi bai san ita asalin wace ba. birkin motar Shuraim ya ja a take gefen hanya ba, ba tare da ya shiryawa hakan ba, sai dai maganar da Amna tayi masa ne yasa shi ji kamar ta jefe shi da dutse a zuciya, dama bai gama fita daga kishin da yake wa Yazeed ɗin ba. Yayin jan birkin da yayi sai da gaba ɗayansu jikinsu ya girgiza haɗi da yo wa gaba, da babu igiyar maka-ra da tabbas hakan ya haddasa musu wata matsalar, Amna da taji taka birkin ba tare da shiri ba tayi saurin juyowa tana dubansa idonta alamar tsantsar mamaki da tambaya, saboda har sai da zuciyarta ya faɗa cikin ɗan tsoro, "me haka!? Ya zaka yi irin wannan taka birkin haka? Idan da wani abun ya faru fah?" Tayi masa tambayar da fiska da kuma baƙi. Ba tare da ya amsa mata ba ya fice daga motar, zuwa gefenta haɗi da buɗe ƙofar, ba ta fita daga mamakinsa da take ba taji ya furta, "fita daga motar!" Tana shirin magana ya katseta da sake furta, "na ce fitta!" Fitar tayi tana cigaba da binsa da kallo zuciyarta na bada wani zollo, tura ƙofar yayi da ƙarfi har sai da Amna ta rintse ido saboda yadda ƙarar ya Dakar mata dodon kunne. Ya juyo inda take fiskarsa na sake bayyanar da hasalar da yake a ciki, "what did you say?!" Ya faɗi cikin nuna ransa na ɓace, tare da fara taku zuwa inda ta ke, ita kuma ta fara jan ƙafafuwanta tana yin baya da su, domin sai yanayinsa ya fara sa ta tunanin ko akwai wani abu da ya faru da shi ne har ya ɓata masa rai haka? "Shu Shuraim lafiya kake kuw...?" "Tambayarki na ke me kika ce ɗazu?" Ya faɗi ba tare da ya daina taku ɗadɗaya zuwa gabanta ba, itama tana cigaba da matsawa. "Akan Yazeed ɗin can kike maganar mu dai na kasancewa a tare?" Ya kuma jefa mata tambayar, itama amsa ta bashi cikin kausasa ta ce, "eh akan sa! Saboda yana shiga damuwa a duk san da ya ganmu tare, kuma shi ɗaukar Safna ya ke min ka sani! gani yake kamar muna da alaƙar so a tsakanin mu, saboda na lura da yadda yake..." "to da ke me kike tunani!?" Ya katse ta da furta hakan yana dakatawa, itama tsayawar tayi tana binsa da kallon da bata gama fahimtar me yake son faɗi ba. "Dama ke wani tunanin ne kike yi? Ki na ganin babu wata alaƙa tsakani na da ke?" Sauya fiska ta sake yi ta furta, "to dama akwai wata alaƙa a tsakanin mu ne? Na san bab..." nan ma ya sake katseta da cewa cikin ɗagun murya, "tabbas akwai alaƙa a tsakaninmu! kuma wannan alaƙar ita ce SO" sakin baki Amna tayi, yayin da gaba ɗaya jijiyoyin sarrafa jini da ke jikinta ya fara gudana cikin hanzari sosai, sai da ta tsayar da numfashinta na wucen gadi ba tare da ta daina kallosa ba kamar yadda shima aikin da ya ke kenan. A hankali ya juya ya bata baya, sai da yaja wata numfashi zuwa cikin ƙirjinsa sannan ya fara cewa, "na daɗe da gane ina son ki, ba kuma yau ba, tun ranar da kika tsaida ni a mota, sai dai lokacin ɗauka nayi yanayi ne na shauƙi da mutane da dama ke fiskanta da zarar sun kalli budurwa wacche suke da burin samu" Juyowa inda take yayi yayin da ta ke tsaye tana kallonsa kamar itache. "Amna a yanzu na riga da na amincewa kaina ina son ki, shiyasa nake jin masifa kishinki a duk lokacin da na ga kina murmushi da Yazeed, ba ma shi kaɗai ba koda ma ace wani ne daban, wanda haƙƙin aure ke iya hawa kansa da ke, wannan shine gaskiyar, kuma ina sanar da ke wannan maganar ne daga ko wace gaɓa ta zuciyata, don haka bana jin shakkar ko waye ya san da hakan". Haɗiye wani nyawun da ta rasa a wani fanni zata sa shi tayi, tana mai cigaba da kallonsa, yayin da zuciyarta ke yi mata wani bugu na musamman, cikin wani yanayi ta juya zuwa inda marfin motar ya ke, "ba wai na faɗa miki wannan maganar ba ne don ranki ya ɓaci, ba lallai ne ki na so na ba, kamar yadda ya ke ba lallai ne ba kya so na ba, sannan ba zan tirsasa ki ba, duk abin da zuciyarki ta ke so shi zata yi Amna, amma ki sani ina ƙaunarki" Ya faɗi tare da sauke ƙaƙƙarfan numfashi, domin yadda tayi masa maganar cewa akan Yazeed take da buƙatar suyi nisa da juna, sai ya sa shi jin zuciyarsa ta tunzura, domin yin nisa da ita a halin da ake ciki yanzu tamkar wata matsala ce a gare shi, domin yadda yake jinta a zuciyarsa har ya wuce tunani, shiyasa wani lokaci yake kiranta da nufin tsokana amma so yake kawai ya ga yana magana tare da ita. Bata yi masa magana ba, sai ma buɗe motar da tayi ta shiga ta zauna, zuciyarta na ke cigaba da bugawa da sauri da sauri. Shima Shuraim zuwa yayi ya shige motar, sai da ya juya ya dube ta yadda idonta yake akan hanya kawai, ganin ba bu shirin yi masa magana da tayi ne yasa shi yi wa motar key kawai. Yazeed. Duk tantamar da yake akan ko Safna ta dai na son sa ne, amma zuciyarsa ta kasa gasgata masa hakan, domin ya san Safna bata yi kama da mayaudara ba, duk da cewa ba wai ya fito fili ya sanar da ita hakan bane, wani tunani ne yazo ransa hakan yasa ya je ya sauya kaya sannan ya fita ɗauke da key da kuma waya a hannu. Bai tsaya a ko ina ba sai a shopping shop, bayan mintuna da yayi a ciki ya fito riƙe da leda a hannu, sanna ya shige motar ya kuma ja zuwa wani wurin daban. Amna tun da suka je bata yi wa Shuraim magana ba, har hakan yasa shi da ya sani bai sanar mata gaskiyar ba. Amna ce zaune da Raheena cikin office ɗin Amna ta fara yiwa Raheena magana, "wani abu nake son sanar da ke Raheena" "ina jin ko ƙawata" sai da Amna ta numfasa sannan ta ce, "wata magana ce, yau a hanyar mu ta zuwa...." nan ta sanar da ita komai, sannan ta ɗora da faɗin, "to me ma zaisa yayi wannan maganar da ni? Taya zaice min yana ƙaunata? Na san ni da shi ba ma shiri a baya, yanzu kuma mun shirya, to me zaisa ya bijiro min da irin wannan...". "Ke kina ganin bakya son shi?" Raheena ta jefe mata tambayar tana ƙure ta da ido, kallonta itama Amna tayi, domin dama ɗazu ba kallon Raheenar ta ke ba, domin yin magana take yi har da alamu da hannu, "me kike son faɗa, akan me zaki yi tunanin ina son shi?" "Ke fa ranar kika sanar da ni cewa kinji wani kamar kishi a ranki da kika ga yana wasu kalamai a waya da hakan ya nuna da budurwa yake wayar" Amna ta cigaba da magana cikin sauri, "eh na san na ji amma yanayi kawai, yanayi kawai, kuma ba hakan yana nufi da komai ba". Taran numfashinta Raheena ta sake yi da cewa, "ke nan ki na ganin ba kishinsa ki ke yi ba? Ke nan ko da ace zai kasance da wata da gaske yana yi mata maganganu da suka fi na wancan babu abin da zai dame ki?" Shiru Amna tayi tare da saukar da kai ƙasa, tana yawo da idanunta saman kayan dake kan teburi, "Amna! Maganar gaskiya ke ma kina son yallaɓai Shuraim, kawai dai baki fiskanci hakan ba ne, kiyi tunani mai kyau" ɗago ido Amna ta sake yi zuwa kan Raheena, ita kuwa Raheena ta yi mata alama da tabbas. LOKACIN TASHI COMPANY. Ba tare da Amna ta ce masa ko uffan ba ta shige mazaunin gaba, hakan yasa ya tada motar yanzu ma zuwa gida. Bayan sun isa gida, kafinAmna ta fita ya kira sunanta, "Amna..." sai daii kafin ya ƙarashe abun da ya ke son faɗa mata ta buɗe motar ta fice, ran sa ba da daɗi ba ya jinginar da kansa kan kujerar mota yana lulawa tunaninta. Ijje jaka da kuma wayar da ke hannunta a kan gado Amna tayi tare da zama a kai, hannayenta ta sa kan katakon gadon tana murzawa zuciyarta na faɗawa nazari, maganar Raheena da tayi mata na sake zuwar mata, "kenan maganar Raheena haka ne? To taya ma hakan zai faru da ni ni Amna?" Ta yi maganar cikin zuciyarta tana sake zurfafa cikin tunani. magan-ganun Shuraim da yayi mata kamar yanzu yake faɗa mata su haka take ji, ta ɗau mintuna biyu tana jin maganar cikin kunnuwanta sannan ta miƙe zuwa gefen Ammu da take a kwance, hannunta ta sa ta fara shafar suman kan Ammu da ke ɗauke da gashi mai tsawo kwance, yayin da Ammun kuma take bacci, ta lura da yanzu Ammu ba ta ɗaukar dogon lokaci ba tare da tayi barci ba. Jummala ce ta shigo cikin ɗakin tare da sallama, bayan sun gaisa Amna ta fara tambayarta, "yauwa Jummala, na ce wai idan kuna kula da Ammu ba kwa ko ganin hannu ko ƙafarta na motsi?". "Gaskiya babu, domin ko ɗaga ta muke yi ma jikin ta da ƙyar yake lanƙwasawa", cike da tausayawa ta juya zuwa kan Ammu tana kallon fiskarta, "ok to amma lokacin da Safna take nan hakan ya taɓa faruwa kuwa?" Amsa mata Jummala ta sake yi domin ta riga da tasan Amna tasan komai, "gaskiya a iya sani na hakan bai taɓa faruwa ba, duk da jikin na ta ya sha tashi lokuta da dama amma bai taɓa kasancewa haka ba" da jin amsar Jummala ta jinjina kai tana cigaba da kallon Ammu cikin tausayawa da neman mafita. DARE. Yazeed ne ya doso ɗakin su Amna ɗauke da wani ƙaton ledar gift a hannunsa yana murmushi, sallama yayi amma ba'a amsa ba, hakan yasa yayi tunanin ba ta ciki, to dama surprise ne yake son yi mata, don haka ya kamata ya ijje ba tare da saninta ba, shiga cikin ɗakin yayi ya ijje gift ɗin akan kujera, sannan yasa hannu a aljuhu ya ciro papern da ya rubuta mata wasiƙa a ciki ya ɗaura saman gift ɗin, har zai wuce sai kuma ya nufi in da Ammu ta ke kwance kan gado, domin yanzu Ammu kwance take kawai, ta zama tamkar sai an kwantar sai an tayar. Gaisheta yayi amma ganin bata ba ta mishi alamar da take yi a baya idan ya zo gaisheta ne yasa shi cewa, "anty Maryam yanzu ba kya min murmushi, ko kinyi fushi da ni ne?" Ya faɗi domin shi bai lura da bata motsa jikinta yanzu ba, Ammu kallo kawai take

Chapter 35 of 56