Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Amma sai gashi daga baya ya kuma bunƙasa, kamfanin Abubakar Mai-daraja ya dawo kamfanin da ake alfahari da shi, kamfanin auduga mai kyau, wanda yake fitar da kaya masu ƙarko da inganci, sunan shi ya gama karaɗe mutane kasancewarsa mai kyauta da taimako, kamar à cikin mafarki Abubakar ya zama mai kuɗi na gaske. Ni kuma hakan ba ƙaramin sanya ɗarsuwan baƙin cikin a zuciyata ya yi ba. taya ni da nayi karatun zamani, na ke ɗan ƙwalisa amma ace wai ni na kasa mallakar koda rijiya tawa ta kaina? Na sha kama business masu ƙarfi wanda nake ganin zan fisa kuɗi ko ta ina, sai dai da na fara komai zai lalace, na gwada yin business masu kawo kuɗi kusan biyar amma duk babu nasara. Wata rana na je na same sa yana zaune kan kujerarsa mai matuƙar kyau, hannunsa riƙeda wani littafi yana buga lissafin kuɗaɗensa, na zauna a gefensa ina ce, "yaya Mai-daraja ina son yin wata magana da kai" barin abin sa ya ke ya yi tare da maido hankalinsa kaina ya ce, "ina sauraronka ƙanina" sai da na numfasa na ce, "yaya kana sane da rashin nasarorin da nake akan business ɗin da duk na kama ko?" "Eh haka ne, kuma ai na riga da na ce da kai ka bar wa'yan nan shirmen abubuwan, ka zo mu cigaba da gudanar da komai tare" ne ce, "a ah yaya, ni fa wannan aikin n'a ka bai karɓe ni ba, ni na riga da na gano bakin zaren, rashin isassun kuɗi ne ya ke sa ni rashin nasara, shine yanzu n'a ke son ka mallaka min kamfaninka babba, in sayar da shi inyi amfani da kuɗin don business ɗin da nake son yi, na san cewa ba ƙaramin riba zan samu ba, zan zama mai kuɗi na bugawa a jarida, sannan sai in biya ka kamfaninka har da ma ƙarin rib..." kan na ƙarisa magana na ji muryarsa ya katseni cikin masifa har sai da ya tashi daga zaunen da ya ke yana cewa, "yau n'a tabbatar da baka da hanakali Jamilu! Wato duk kuɗaɗen da na ke ba ka da sunan aiki basu ishe ka ba? Sau nawa nake kwasan kuɗi inba ka da suna zaka yi business, amma daga ƙarshe sai ka dawo min da cewa sun salwanta, duk da haka ba zan ƙi ɗaukar wani inbaka idan ka nema ba.....__ Last part. ___________________________________________________ Kun numfasa 'yan uwan arziƙi?. Hmm ni dai na ce mu kasance a kashi na gaba idan Allah ya kaimu. Last part. ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣5️⃣5️⃣▶️1️⃣5️⃣6️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 __"Yau n'a tabbatar da baka da hanakali Jamilu! Wato duk kuɗaɗen da na ke ba ka da sunan aiki basu ishe ka ba? Sau nawa nake kwasan kuɗi inba ka da sunan zaka yi business, amma daga ƙarshe sai ka dawo min da cewa sun salwanta, duk da haka ba zan ƙi ɗaukar wani inbaka idan ka ne ba. Amma yanzu zaka zo min da wata magana? To ka kiyaye ni! Idan zaka zo muyi komai tare a company ka zo, idan kuma baka buƙata to ka cigaba da yin abin da ka ke so" yana yin maganar ya barni zaune ya wuce ɗakin sa. Ya ɓata min rai sosai, taya ni zan kasance a ƙasansa ban da gashin kaina? Sai dai tunanin da na yi kada ya janye bani 'yan kuɗaɗensa sanadiyyar maganar da na yi masa, hakan yasa na je na same sa cikin ɗakin sa, na bashi haƙuri n'a kuma tabbatar mishi da na amince da aiki tare da shi, ya yi farin ciki sosai da jin kalamaina. Toh haka dai na cigaba da aiki tare da shi, muna komai tare, duk abubuwan da ya ke min na kyautatawa, ni gani na ke kawai ni bawa ne a ƙarƙashinsa, saboda ko matsayin shugaba na ƙaramin company bai ba ni ba. Lokuta da dama ina tunanin abubuwan da zan yi don nima na mallaki dukiya fiye da na shi. Kawai wata rana na haɗu da ɗaya daga cikin masu aiki da matsafin kogo, babu ɓata lokaci na amince da zama ɗaya daga cikin membernsu, nan nima na fara kafa tawa mulkin a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba, daga nan suna Zabba-ba ya fara amfani a kaina. Matsafi ya tabbatar min da idan har Mai-daraja yana rayé buri na ba zai taɓa cika ba, duk rashin nasarar da ke samu na shine sila. Ni kuwa dama abubuwa sun girmama a zuciyata a garesa, daga nan na fara neman hanyar da zan kawar da shi, domin kuwa matsafin ya tabbatar min da cewa ba da tsafi ya kamata ya mutu ba. Ban samu cinma buri na ba har bayan aurenmu wanda aka yi rana ɗaya, sannan muka zauna a ƙayatacchen gidan da shi ya gina mana. To daga nan ne na samu Abdurrazak mahaifin Shuraim domin kasancewarsa na kusa da Mai-daraja, amma ya ƙi ba ni haɗin kai, ni kuwa na haddasa masa hatsari yayin da suke kan hanyar zuwa shopping shi da matarsa. Sai kuma duk lokacin da matar Mai-daraja Maryam ta samu ciki, sai na zubar da shi ta hanyar ba ƙahon tsafi jininsa, haka na sa suka yi asarar yaransu da dama. Domin ni ba zan iya barinsa ya samu ɗansa à duniya ba, tun da shima kashen shi na ke son kawo wa. Sai dai tun da ta sami cikin ku, duk yadda za'ayi a zubar ya ƙi yiwuwa, tasha wahala sosai! Saboda yadda ake tura mata abubuwa daban-daban don cire cikin, amma haka har cikin ya girma, har aka zo haihuwa. Ban san 'yan biyu ba ne a cikinta, hakan yasa na tilasta doctor Salis karɓar haihuwan shi kaɗai, yadda zai raba 'yar da Maryam wato Amna, tun kafin Maryam ɗin ta farka, duk da cewa da fari ya ƙi, amma kasancewar barazanar da na yi masa akan zan kashe matarsa da ke ɗauke da juna biyu yasa ya amince ya yi min, sannan kuma shi da kansa na ba umarnin ya je ya kashe yarinyar. Sai dai doctor Salis bai san na riga da na kashe masa matarsa ba, saboda ni ba a min gardama sau ɗaya ba tare da na yi abun da ya dace ba!. Duk da cewa matsafina ya ce kada a kashe yarinyar wato Amna kenan, cewa ya kawai awurgar da ita, ƙahon tsafi baya son jininta, amma ni na umurcesa da ya kashe ta, domin hankalina zai fi kwanciya idan hakan ya faru, koda na so ni in aiwatar da komai da kaina. Amma abun mamaki daga fita harabar asibiti na dawo na tarar da yarinya à hannun mai-daraja, ashe 'yan biyu ne a cikin maryam daga baya nurses su ka ciro ɗayar, babu yadda zanyi haka na rabu da su__ Dady katse tsayuwar da ya ke ya yi tare da zama, yana murmushin nan na gefen baki, ya sanya guiwoyin hannayensa a kan cinyarsa, tare da sunkuyowa kamar zai tashi, yana kallon Amna da Safna rungumae da juna su na ta kuka sosai kamar ransu zai fita, Shuraim a can gefe yana yin na sa hawayen baƙin cikin, babu mai rarrashin kowa, zuciyarsu babu abin da ta ke yi sai bugu kamar ganguna, baƙin ciki, takaici, tausayin kawunansu, duk suke ta yi babu sassauci. Jin maganar da Dady ya ɗora ne ya sanya su sake kallonsa da idanuwansu mai kamar yaji. __Bayan ya samu yarinya su ka yi ta murna mara misaltuwa, domin shi mutum ne mai son yara sosai, ni kuwa wannan murna ta sa kamar ruwan zafi nake jinta cikin raina. Daga baya na samu wata idea, ranar sunan 'yarsa na sanya aka kira shi da sunan anyi kidnap ɗina, cikin tashin hankali ya hawo motarsa ya baro hidimar sunan 'yarsa ba tare da ya sanarwa kowa ba, domin umarnin da na sa su basa kenan, haka dai ya shararo da motarsa ya yi parking à wannan gidan gonar, ya samu damar shigowa cikin wannan hall ɗin, ko da shigowansa à ɗaure ya ganni fiskanta duk jan kala wanda shi ya ɗauka cewa jini ne a jiki na, ya durƙusa yana kallona da hawaye tare da taɓa ni cikin tausayawa, daga bayansa aka buga mai katako à kai kamar dai yadda na yi muku, haka ya matsa baya yana ƙoƙarin faɗi, ganin mutanen sun tsaya a baya na riƙe da makamai ne yasa shi cewa cikin raunannar muryarsa, "kada ku aikata wa ƙanina komai, don Allah kada ku cutar da shi, me kuke nema a garemu?" Sai dai bai ƙara wata magana ba, fiskarsa ya bayyanar da mamaki, irin mamakin da zai iya busar da mutum, ya girgiza sosai, duk saboda jin dariyar da na fara yi ina miƙewa daga zaunen da nake, haɗi da warware igiyoyin da dama ba ɗaure suke a jikina ba, cikin jin haushin da na daɗe ina yi na fara ce masa, "yaya n'a yayana, barka da zuwa masarrafata, n'a daɗe ina dakon zuwanka ban yi nasara ba sai yau, kai ne ka zame mini cikas cikin rayuwata, kai ne silar daƙushewar nasarorina da dama, kasancewarka à duniya babban barazana ce ga gobena, nine na hana ka samun ɗa a duniya, na yi ta salwantar maka da 'ya'ya tun kafin su girma a cikin matarka, amma duk da haka cikin 'yan biyun da ta samu ya zauna" na faɗi ina kallonsa yayin da shi kuma idonsa ke ta fitar da hawaye, "ka yi mamaki ko? To cikin da Maryam ta haifa 'yan biyu ne, ni na sanya a ɗauke 'yar da ta fara haifa aje a kasheta, amma fa da na san 'yan biyu ne, da bazan barka ka kalli koda hannun 'yarka ba, bare har ka zauna da ita, wani ƙarin abu, nine na kashe aminin aikinka Abdurrazak da matarsa, don haka yau kai ma zan kasheka! In huta da duk takura da ka ke wa rayuwata, kaima kuma ka huta da muguntana, Ƙasa ya durƙusa yana kuka sosai, daga baya ya ɗago idonsa kaina ya ce, "yanzu Jamilu dama zaka iya aikata min haka? Na yi mamaki wanda ba zan iya kwatanta shi ba, ban taɓa koda tunanin mafarki akan zaka zama haka ba, kai ne silar rasa 'ya'yana da na yi a baya, ka sanya Maryam tasha wahala sosai à duk sanda cikinta ya zube, sannan ka bata wahala a wannan cikin da ta samu, sannan kuma ka rabamu da 'yarmu ɗaya tun kafin mu ganta, anya kai mutum ne ma kuwa? Ka kashe min aboki na akan muradinka kawai, wani irin baƙar zuciya ka mallaka kai kuwa?" ban sake yi masa magana ba, sai ma kallon ma'aikatana da na yi, hakan ya sa muka fara nufan inda ya ke don mu gama dashi a tare, Amma muna isa ya samu damar shanmatanmu da yin amfani da garin pentin dake cikin buhu a kusa da shi, ya watsa mana cikin ido, muka rintse idanuwanmu muna ƙarar zafin da muke ji cikin ido, shi kuma ya samu damar fita daga cikin wurin, binsa muka yi muna goggoge idanuwanmu, muna fita muka gansa riƙe da hannu a kai yana shirin shiga mota, kafin mu tadda shi har ya tada motar ya ja ya bar wurin, mutane na suna shirin binsa na hana su, "oga Zabba-ba tafiya fa ya ke, ya kamata mu cin masa" cewar ɗaya daga cikin mutanen, murmushin mugunta na yi na juya ina kallonsu, na ce, "kamar dama na san da hakan zai iya faruwa. Bar shi ya tafi, bar shi. Bai mutu a nan ba, amma zai mutu cikin motarshi" da mamaki wani ya kuma cewa, "oga ta yaya?" Juyawa na yi na kalli inda motar ya ke, sannan na ce, "booom! Bom na cikin motar, nan da mintuna goma ya yi yawa zai tarwatse!" na faɗi cike da farin ciki. A wannan ranar aka shafe tarihin Mai-daraja. Amma kuma bayan ina murnar cewa zan mallake gaba ɗaya dukiyarsa, na tadda à she ya riga da ya sa hannu, cewa 'yarsa Safna ita ce zata mallaki companynsa bayan ta cika shekara ashirin da uku a duniya, idan kuwa mutuwa ta yi, to gaba ɗaya dukiyarsa ya mallakawa ƙasarsa, wato dai za ayi sadaka a baiwa mabuƙata. Na yi mamaki da hakan ya kasance, domin kuwa ya bada wannan wasiyyarne tun kwana biyu da haihuwar Safna, na bi duk wata hanya don in ruguza wannan rubutacchen wasiƙar ta sa, amma ba dama, domin yadda ya yi amfani da ijje wasiƙar, ƙasa gaba ki ɗaya ya ba wannan ijjiya. Nan farin ciki na ya koma baƙin ciki, babu damar na kawar da Safna, idan na yi haka zan rasa komai, shiyasa na nemi da Maryam ta zauna gidan ta girmar da 'yarta, domin in samu damar cinma abin da na ke so, bayan ta zama 'yar shekara ashirin da uku, sai dai innar Maryam taƙi yarda, hakan yasa na bijiro da maganar aurenta, kuma na sihirceta yadda zata amince da kanta, hakan yasa ta amince da buƙata ta da kanta ba tare da anyi mata dole ba, Zainab ta fara tada hankali akan auren, amma da na sanar mata kawai na yi ne don tarbiyyar Safna ne, kuma babu abin da zai haɗa ni da ita wanda ya danganci mata da miji, hakan yasa Zainab ta amince. Aka yi aure wanda ba wai auren aka yi ba, kawai na shirya yadda komai zai faru ne, yadda mutane zasu ɗauka n'a aure Maryam à zahiri, amma a baɗini ba aurenta na yi ba. Nan kowa ya san cewa, Maryam ta tashi daga matar Mai-daraja ta dawo matar Jamilu,. Kasancewar dama ba son auren ta ke ba, hakan yasa ba ta damuwa da rashin kula tan da na ke yi, domin ko ɗakinta ba shiga na ke ba, dama matsafi ya sanar da ni kada n'a yarda wani abu ya shiga tsakanina da ita. Bayan Safna ta cika shekara biyar, Maryam ta gano gaskiyar ko ni waye, duk da cewa ba zata iya faɗawa kowa ba, amma sai matsafi ya sanar da ni akwai buƙatar ayi wa Maryam ɗin wani abu, saboda ya gano ita zata iya zame min matsala a gaba, hakan yasa aka gudanar da sihiri a jikinta, hakan yasa na ɗauketa da sunan kaita asibiti ba lafiya, amma kaita wani wuri na yi, a gaban idonta aka gurɓata mata jinin jiki, tana kuka tana hawaye, tun daga nan ta kasance ba ta iya magana, motsima jikinta baya yi mai kyau, duk zuwa asibiti da nake yi, da kuma neman maganin gargajiyar da nake yi à sufa ina nema mata lafiya ne, duk ni na ke shirya komai. Haka n'a cigaba da nunawa Safna kula kamar ina matuƙar sonta, amma cikin zuciyata na tsani ganin koda fiskarta! ina jin daɗin yadda Zainab ta ke nuna mata tsana ita da yarana, sai na kan nuna mata cewa ba na so, amma a bayan raina cewa na ke, ki daɗa mata fiye da na kullum. Haka har shekaru suka wuce, ban mallaki dukiyar Mai-daraja ya zama nawa ba, sai dai ya kasance a ƙarƙashin kulawata, sannan ina gudanar da ayyukana na Zabba-ba a can gefe guda. Bayan na zo na gane wannan Amna ce ta maye gurbin Safna, na barta ta cigaba da yin wasan kwai-kwayonta, domin ni buri na kawai a yi ƙaddamarwan bada ragamar dukiyar mai daraja a kanta, domin na shirya wani abu yadda komai zai dawo tafin hannuna, ranar kuwa manyan lauyoyin ƙasa sun bayyana, aka gudanar da abin da ya kamata, duk da cewa na tsorata sosai koda akazo gurin signing, sai gashi abin mamaki signing ɗin 'yan biyun da basu san juna ba ya zama kala ɗaya, daga baya ba tare da Amna ta ankare ba, ta sanya min hannu cikin takardun dukiyar mahaifinta kamar yadda na tsara. Too haka dai, kawai ranar cikin bazata, wai jikin Maryam ya tashi an kai ta asibiti, ba tare da na sani ba aka sauya mata jini, wanda kuma dama sharaɗin wannan sihiri kada a yadda à ƙara mata jini, za'a barta daga ita har Safna sai lokacin da na kammala sinadarin iko na, wanda zai zama kariya a gareni da zuwan dukkannin wata matsalata, daga nan sai na san inda zan jefa su, amma sai ga shi an ƙara mata jinin, sannan kuma doctor Salis shine wanda ya yi hakan. Ban taɓa tunanin zan sake sanya shi a ido ba sai wannan ranar, domin tun bayan aikin da na sa shi na bashi gawar matarsa, sannan na bashi kwanaki biyu, ya gama duk abin da zai yi ya bar ƙasar, idan ba haka ba shima zan kashesa. Amma sai gashi ya dawo da kansa, ranar na kuma bashi umarnin awa ashirin da huɗu ya bar garin Kaduna, kafin ya bar gari na kuma ƙwamushe shi, na ba shi azaba akan me yasa ya ƙi kashe wannan jaririyar da na bashi? A nan ne ya sanar da ni ya kasa kasheta ne, hakan ne ya sake tabbatar min da cewa, Amna itache wannan 'yar biyun Safnar. Taƙurun-ƙusss, labari ya ƙare__ Dady ya ƙarashe maganar tare da jingina jikinsa bayan kujera yana dariyar farin ciki. Ƙara fashewa da kuka Amna da Safna su ka yi, kuka mai jefe mutum duniyar tunani, kuka mai cike da raɗaɗi sosai, kuka mai cike da tausayin rashin rayukan da aka musu. Tashi daga kujerar Dady ya yi ya kuma yin wannan sautin, ttath ttath ttath ttath ttath, "ayyaaahh! Abin tausayi, har kun sa na tuna da ɗan uwana Mai-daraja da na kashe, amma ku yi haƙuri, ni na muku alƙwari, wallahi zan tura ku inda ya ke, cikin salama, na yi alƙawari" ya faɗi da yin musu alama da fiska akan tabbatarwa. Ya kuma cewa, "na riga da na samu dukiyar Mai-daraja a yanzu, bugu da ƙari kuma aikin chemicals ɗina zai cika, to me ya rage min?" Safna ta daina kuka amma hawaye sai fita daga idanuwanta ya ke, Amna kuwa tun ɗazu ta yi ɗip da kukanta, kanta a ƙasa, tana jin wani yana yi ya fara shiganta, wanda bata gama gane menene ba, eye colour ɗin da ta ke sanyawa na Safna, sai ga shi ya fara zamewa daga cikin ƙwayar idonta, asalin kalan idonta na ash yana bayyana, wannan tabon gefen bakinma yana ɓanɓarewa. Shuraim kuma ƙoƙarin tashi ya ke yi yana runtse idon zafin jiki. Dady ya mai da kallonsa kan mutanen nan na sa, ya ce, "bai kamata tarihi ya maimaita kansa ba, na kashe iyayen su, bai kamata a ce suma ni zan kashe su a hannuna ba, don haka n'a baku dama, ku yi mu su murjin tumatir, yadda karnuka zasu ci namansu cikin jin daɗ..." "Dady!!" Da sauri Dady ya juya don ganin wanda ya ji ya kira sunansa cikin ɗagun murya mai cike da al'ajabi. Ai ko idonsa ya sauka kan Yazeed da mutanensa suka rirriƙe, yayin da Yazeed ɗin ke jefa masa wani irin kallo daga jajayen idanuwansa masu tsiyayar da ƙwallah. Sai da Dady ya zaro ido da ganin gudan jininsa a wannan wuri. Safna da Shuraim ma su ka juya da hanzari suna kallonsa, Safna cikin shaƙaƙƙiyar muryarta ta ambaci, "yaya Yazeed". Last part. ___________________________________________________ 'Yan uwan arziƙi, kun ji gaskiyar komai daga bakin Dady, lallai Dady ya amsa sunan mugu gaba da baya, ya kashe mutane da yawa a rayuwarsa, a ciki harda ɗan uwansa mai ƙaunarsa Mai-daraja. Hmm ga Yazeed kuma mutanen Dadyn sun kama, kuna ganin ya ji duk magan-ganun Dady? Mu kasance a kashi na gaba don jin yadda zata kaya, ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣5️⃣7️⃣▶️1️⃣5️⃣8️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 YAZEED. Sai da su Shuraim suka isa gidan gona da wasu mintuna kafin shima ya isa, kasancewar Shuraim gudu ya ke yi da motar, domin da ya ɗauka ma sun riga da sun ɓacewa ganinsa, kafin daga baya ya hangi motarsu, kasancewar wannan gidan gonar shine kaɗai gida da ya ke a wurin, hakan yasa ya tabbata nan su Shuraim suka dosa. Mamaki ne ya ke ta ratsa Yazeed yayin da ya ke kutsawa ciki, tunani ya ke ta yi na me zai kawo Shuraim da Amna wurin? A kan wani dalili zasu zo tsohon gidan gonar nan? Tafiya ya ke amma bai ga wani ko wata ba, sannan ko hayaniya ba ya ji, à haka ya yi ta zagaye wannan wuri ya rasa ina zai gansu, bayan lokutan da ya yi har ya fara gajiya, gashi ko hanyar da ya biyo ma ba ganewa zai yi ba. Ana haka ya iso ta wani kango, ta setin windown wannan kangon idonsa ya hangan masa kamar mutum ta can windown hall ɗin, har ya kauda kai amma ya yi saurin juyowa, zuciyarsa ce ta fara bugawa ya yin da ya kalli kamar mace ce "Safna!" Ya ambata daga zuciyarsa cikin tsoro, kada dai Safnarsa ce, domin kasancewar yana da tazara à tsakaninsa da gurin yasa bai gama gane wace ba. Kallon windown kangon ya yi ya dafa haɗi da tsallakesa da hanzari, sannan ya cigaba da nufar windown hall ɗin. Gabansa ne ya faɗi ganin Shuraim à kwance jiki duk jini, da sauri ya maida kallonsa gun macen da ya gani tun daga nesa ɗazu, amma me zai gani, ganin Safna ya yi da kaya ba irin wanda ta taho wurin ba, gefe ɗaya kuma ga mai kaya irin na Safnan amma ita bai ga fiskarta ba, sannan kuma duka jikinsu jini ne sosai, yadda suke fitar da numfashi zai tabbatar maka da ba ƙaramin wahala suka sha ba kuma suke ƙara sha yanzu, sannan ga wani sautin dariya da ya ke ji yana tashi, kafin ya gama tantance abinda ke cikin kwanyarsa, sai ga shi kwatsam ya ga ɗagowar ɗayar budurwar. Sai da ya ja da baya daga jikin windown hall ɗin da sauri haɗi da zare ido sosai, zuciyarsa ya bada wani irin sauti mai cike da yanayin kullewar kai sosai, gefe ya kalla sannan ya sake dawowa da odonsa kansu, sai kuma ya sake fiddo ido, tabbas ba makawa Safna ce guda biyu ya kalla da gaske, matsawa gun window ya kuma yi da sauri saboda ya samu damar buɗe baki ya ƙwala kiran sunan Safna, ƙila daga nan zata dawo ɗaya ba biyu ba, wato zata haɗe. Amma kuma me? Babu zato babu tsammani ya ji dariyar nan ya tsaya, magana ya biyo baya, maganar da ya ji ya yi kama da na Dadynsa, duk da bai gama tabbatar da da muryar ba, kasancewar yadda mutumin ya ke magana cikin mugunta kamar muryar mugu, jkinsa ne ya hau kyarma babu ƙaƙƙautawa, jin labarin da Dadynsa ya ke bayarwa, domin ya samu damar hangen Dadyn sannan ya ga fiskar, rawa jikinsa ya ke yi sosai. Zuciyarsa na bada sauti, ya rasa gane me ya ke yi masa daɗi a duniya, wai duk wannan labarin Dadynsa ne ke bayarwa? Sannan kuma shi ya aikata duk abubuwan da ya faɗa? Yazeed ya tambayi kansa lokacin da Dady ya ƙare maganar da dariya, ya kai idonsa kan Amna da Safna da ke kuka mai ratsa zuciya, ƙwallah ne ya tarun masa à idanu kansa ya fara juyawa. "Kai waye wannan? Ku kama shi" cewar wani mutumin Dady. Babu ɓata lokaci suka kama Yazeed suna zagayawa da shi cikin hall inda Dadyn su ke, bai yi yunƙurin ƙwacewa ba, sai ma binsu da ya cigaba da yi ba musu. Rikicewa ya sake yi da jin maganar da Dadyn ya yi dai dai shigansu cikin hall, bai san lokacin da ya ambaci sunan Dadyn da wani irin sautin al'ajabi ba. "Dady!!" Da sauri Dady ya juya don ganin wanda ya ji ya kira sunansa cikin ɗagun murya mai cike da al'ajabi. Ai ko idonsa ya sauka kan Yazeed da mutanensa suka rirriƙe, yayin da Yazeed ɗin ke jefa masa wani irin kallo daga jajayen idanuwansa masu tsiyayar da ƙwallah. Sai da Dady ya zaro ido da ganin gudan jininsa a wannan wuri. Safna da Shuraim ma su ka juya da hanzari suna kallonsa, Safna cikin shaƙaƙƙiyar muryarta ta ambaci, "yaya Yazeed". A

Chapter 48 of 56