ya hana abun yin tsamari sosai, amma an daɗe kan maganar ya wuce, sai da Baba ya bada kuɗeɗen tritment.
Saurin fisge hannun ta tayi daga riƙe tan da yayi, ba tare da ta ɗago idon na ta ba, "baka da hankali ne? Da rai na wasu suyi maka wannan abun ba tare da sun karɓi fiye da abun da suka ma ba?" Ta faɗi cikin kakkausar murya, dariya su Jalo suka ƙara yi a karo na biyu, tsaida dariyar sa yayi haɗi da yin kan ta dan ya bata ma rin da zai sumar da ita, sai dai nushin da Amna takai masa a ciki ne yasa shi yin ƙasa warwas, har lokacin kuwa kanta ƙasa yake.
"Boss Jalo, Boss Jalo" shine su Zanga ke furtawa, juyowa sukayi inda take, dai dai lokacin da ta ɗago idon ta gare su, zaro ido gaba ɗaya 'yan wurin su kayi, ganin manyan idanun ta, ga ƙwayar idon kuma Ash colour, duk da idon ya fara rinewa izuwa ja, sai ta fito zak Baturiya, kallon ta kowa yake kamar yauce suka fara tozali da ita, daga Mazan har Matan, saɓanin Mubarak da abokan su, sabida sun riga da sanin ta haka, wow wow ko wannen su ke furtawa wasu a Zuciya wasu kuma a fili.
Yin kan sauran tayi ta fara basu nasu rabon, naushi take kai musu ta ko ina, ta hana su samun damar guduwa, yadda take jibgar su ko gajiya ba tayi ba, su kuwa ji suke kamar Rodi take buga musu, duk da haƙurin da Abokan ta suke bata amma kamar ƙara harzuƙa ta suke, haƙuri suka fara bata, ganin ba ta da niyyar barin su. Sai ihu suke, ƙattin banza.
Da ƙyar ta da kata dan riƙo ta da friends ɗin ta suka yi, jikin ta har jini ya taɓa saboda yadda itama ta far-fasa musu jiki, su kuwa su Jalo babu abin da suke sai sauke numfar-fashin wahala, "haaaa waiii wayyooo" suke faɗa sai juyi suke kowa na taɓo kota ina na jikin sa inda ke mai zugi, tare da dana sanin Shiga harkar Aljanar nan, dan batayi kama da mutum ba, siririn cikin su harda fitsari ya tsula a wandon sa.
mutanen wurin a tsorace suke, su iya ni Zubi kam tini ta koma baya dan ganin Amna take kamar ma ba mutum ba, sai wuƙi-wuƙi da ido take, "wai ace Mace ta yiwa shirga-shigan Mazan nan duka cab"
Jan Amna su kayi suna ƙara bata haƙuri, suka wuce, ita kuwa ji take kamar bai kamata ta barsu haka ba, sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri, idon ta ya rine zuwa ja, hakan yasa ya bada wani kala daban, sanya mata glass ɗin ta Mubarak yayi. Saurin ɗauko jakansu Zarah tayi sukayi hanyar fita, ko hakan zai ƙara lafa abun.
Kusan gaba ɗaya malaman makarantar ne suka yo wurin ganin cinci-rindon ɗaliban su a wurin sai surutai suke, kutsawa su kayi ciki suna tambayar dalilin dan-dazon na su, sai dai abin da suka gani ne yasa su dakatawa da tambayar, ganin samari Biyar a baje sai juyin a zaba suke, riga dik ya ɓa ci da jini.
"Kai wai Trela ce ta biyo ta Makarantar nan bamu sani ba ko me?" Cewar wata Malama tana ƙara ƙure su da kallo dan tabbatar da hasashen ta.
Sai da suka kai Mubarak chemist, sannan sukayi hanyar gida.
BABA.
Kamar yadda ya shirya yau ya fara ai watar da binciken sa, samun labarin wata sheɗaniya yayi daga bakin wasu 'yan shaye-shaye da ya jisu suna hira, ba tare da sun san yana sauraron su ba suke magana, su Uku, ɗayan yake cewa, "ai ita Zilla da kake gani, duk kan ƙwaya ta sani, babu irin ƙwayar da ba ta sha" dayan ya amshe da faɗin "ni fa har mamaki nake yadda kan ta yake ɗaukar kowani iri" na ukun ne yace, "kai to indai hakane kuwa, ai Zilla irin ta mu ce".
dariya Biyun suka kwashe da shi sannan wanda yafara maganar ɗazu ne yasake cewa, "lallai yau na ƙara tabbatar da kai baƙo ne a harkar Bariki, duk wani da ya san gurin Ƙoƙolwar ka Zan-Zan to yasan Zilla ba ta ƙananun marasa kunya bane, ko daga shigar ta, dirin surar ta batayi kama da ƙananun mata ba, ko rabin abun da take sha kana zaka iya sha ne?" Ɗayan ma yace "faɗa masa dai" Yana gama sauraron su ya yi gaba, yana tinanin inda Ƙoƙolwar ka Zan-Zan yake?.
bayan ya samu information akan wurin Zan-Zan babban wurin 'yan Shaye-Shaye ne, ka ya Black yasa haɗi da sa face mask, shigar ta masa kyau, sai ya dawo kamar ɗan saurayi, ya nufi wurin, Babu abin da yake ta shi sai warin Taba da giya, duk da cewa Babban wuri ne amma basu ƙaya ta wurin ba. Ko lafiyayyun kujeru babu sai Bencuna.
Guri ya samu ya zauna kan ɗaya daga cikin Bencin, tare da mamakin guri irin wannan, a zuciyar sa yana faɗin "fisabilillahi duba wurinnan babu abinda suke sai saɓon Allah, kamar ba su san me ake kira da mutuwa ba? Yadda kowa a cikin su yake Shaye-Shayen sa hankali kwance, maza da mata wa'iyazu billahi, wllh wani lokaci duk ƙoƙarin ka na ka gyara matsalolin tarbiyyar mutane ko, inka yi arba da wani abun sai kaga kamar babu abinda ma kayi, Allah ka kiyashe mu ta ɓewa" yana gama faɗin haka a zuciyar sa, ya fara wuwwula idanuwan sa da tinanin yadda zai ga ne wannan 'yar-duniyar cikin yawan mutanen nan.
"Zilla ɗan zo mana" yaji wani na faɗin hakan, juyawa yayi dan kallon wanda aka kira da wannan suna, aiko idon sa ya faɗa cikin nata, tsare shi tayi da ido.
Zubin ta Siririyar mace ce fara tass, amma farin Mai ne, sanye ta ke da ɗamammiyar Rigar kanti da bata kai mata ƙasa ba, bi ma'ana dai ta ɗan fi guiwa, sai gashin atach brown colour, sannan takalmi ma black, riƙe take da android a hannun ta.
----- amma fa banga wani irin waya bane, ni dai bata min kyau ba, amma a wurin mutanen wurin ba ƙaramin kyau tayi musu ba, dan ta fi duk matan wurin class, ni kuma nace a Bariki ba----
Ganin yadda take yi masa wani irin kallo yasa shi ɗauke idon sa a kanta, "wai wannan abar ce wasu suke ribibi akan ta, abu ko kyan gani babu" ya sake faɗi a zuciya, "kai ka kiyaye ni nayi maka kama da Rose irin ku ne?" Ta ba wanda ya kira ta amsa, har lokacin kuwa idon ta na kan Baba.
Ta kowa ta fara yi cikin salo irin na su, wanda wasu suke kallon na ta daban, zuwa tayi gaban sa tana ƙa re masa kallo, yayin da shi kuma kan sa yake ga wayar sa, "ya haɗu" ta furta a zuciyar ta, saboda da ganin sa ba irin Mazan da suke nan bane.
"Hii guy, what do you want" ta faɗa masa haka tare da zama gefen sa, ya furta "not now" "ok har zuwa yaushe kenan, da alama kai baƙo ne anan ko? faɗamin dik abin da kake so anan zan mallaka maka, saboda ka yi min".
Saida ya ɗago idon sa yakalle ta "yes I'm true, ka yimin" ta faɗi masa, duk da bajin daɗin kasan cewar sa anan yake ba, amma ya zame masa dole shima ya zama ɗan Bariki ko dan aikin da ya ɗauko".
Yace mata "ba wannan karon bane zuwa na nan na farko, ni na san ki amma sai dai wannan ne ganin ki da ni na farko, amma kice nayi miki? daga ganin Sarkin fawa" ta ƙarisa masa, "sai miya tayi zaƙi?, nasan karin maganar ai, ka ga, tun da har ka ce kasan ni, to kasan duk Mazan da suke a nan ko wannen su buri yake nayi masa magana, amma fa kai kaɗai ka burge ni a yau, duk da cewa bangama ganin fiskar ka ba saboda mask ɗin da kasa" ta faɗi tana ƙoƙarin shafo hannun sa.
Saurin miƙewa yayi yana faɗin "amma fa ni ba mai kuɗi bane kamar yadda kike so" dariya kaɗan tayi haɗi da miƙewa tace "ban cika neman kuɗi a wurin mutum ba, musamman irin ka, buƙata ta kawai naji daɗin kasan cewa da kai".
Murmushi yayi yana faɗin "zan wuce akoi abunda zanyi" ya faɗi yana fita waje, biyo sa tayi wajen tana cewa "babu abinda ka buƙata a nan kuma zaka tafi? Sannan baka gayamin sunan ka ba? Kuma baka nuna min kyakykyawar fiskar nan ta ka ba, ko kayi murmushi bana ganewa sabida ba ganin bakin ka nake ba"
'Yar dariya yai mata tare da tsayawa, "ina da tambaya ko? Nima bansan dalilin rashin Jan aji na lokacin da na gan ka ba, ka ga, ni suna na Zulahat amma ana kirana Zilla" kallon ta yayi jin sunan musulmai gare ta, duk da hausan ta raɗau yake amma yayi tinanin girma cikin hausawa ne yasa haka, shigar ta baza ka taɓa cewa shigar musulma bace, koda yake 'yar Duniya ce wace irin shiga ne baza tayi ba".
Faɗamin sunan ka mana haɗaɗɗe?" "Hamid ne suna na" "wow sunan ka me daɗi to mene ne laƙabin ka kaima?" Amsa mata yayi da babu, musayar number suka yi, ya wuce ba tare da taga fiskar sa ba mask ba.
Binsa tayi da kallon da ita kaɗai ta san manufar sa, yayin da shi kuma yaji daɗin samun da ma da wuri daga gare ta, da nufin gobe zai fara bugan cikin ta, ta yu ta san ƙwayar POSPA.
#Lalallai, bakuyi mamakin yadda Zilla ta shigo hannu da kan ta ba, wani irin manufa take da a zuciyar ta?
Shin Baba ya biyo hanyan bincike da kyau kuwa? Bugan cikin ta zaiyu kuwa?
A baya naji Baba shi kansa bason zuwa Kaduna yake ba, ko me dalili?
Ya su Ummee za suji yayin da aka mayar musu da Mubarak da rauni?
Su waye zasu min rakiya zuwa gaishe da su Jalo da jiki?😂
______________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣
Fannin baiwar Allah SAFNA. .
Ammu ce ta tashi da rashin lafiya duk magun-gunan da take sha Safna ta bata amma jikin sai ƙara zafi da yayi, tinanin yadda zatayi take amma ta rasa, Dady baya nan bere ya kai su Hospital, Hajiya kuwa tasan ko ji tayi Ammu suma take yi ba bu abinda zai sa ta ko kalle ta bere ayi maganar taimako.
Ganin jikin na ƙara zafi sosai yasa ta tashi tayi waje da sauri, turus tayi bayan bangazan Hajiya da tayi, 'ke!" Hajiya ta furta da tsawa da yasa jikin Safna rawa, "dan Allah, dan Allah Hajiya ki gafarce ni, wallahi ban lura bane, Ammu na ce ba lafiya jikin ta ya ɗau zafi sosai" ta ƙarashe faɗi cikin rawar murya.
Wani irin gigi taccen mari Hajiya ta sauke mata da yasa ta yin gefe goshin ta ya bugu da gini, durƙusawa tayi haɗi da saurin sa hannun ta kan goshin na ta, ta rintse ido jin yadda yake mata zugi, tana sauke hannun taga ya ɓaci da jini, ashe fashewa yayi.
Duk da ganin hakan bai sa Hajiya taji tausayin ta ba, sai ma jan tsaki da tayi tana wucewa, hawaye mai tsananin zafi ne ya koranyo daga cikin manyan idonuwan ta, dama fitan da tayi dan zuwa gurin Baba Hambali ne, ko zai bata wayar sa ta kira Dady ta sanar da shi halin da Ammu ke ciki.
Miƙewa tayi zuwa wurin sa, hannun ta da pe da goshin ta, zaune ta sami Baba Hambali kan kujerar zaman sa, ya ka ra Radio a kunnen sa yana sauraron shirin Inda Ran Ka, isa wurin sa tayi duk da tana jin zugi a goshin na ta, "Assalamu alaikum Baba ina wuni" ta gaishe sa, "Lafiya..... subhanallahi Meya same ki haka 'yata?" "Ba wani abu bane Baba, dan Allah ko zan samu waya in kira Dady?".
Tayi masa maganar tana sauke hannun ta a goshin na ta, sai dai jinin bai tsaya ba, sai ma ɓata mata kaya da yayi, "haba 'yata duba fa jinin yaƙi tsayawa ya kama...." Cewar Baba mai gadi cike da damuwa, sai dai katse sa tayi da faɗin "please Baba Hambali dont worry a bout this, kawai waya zaka bani ka ji dan Allah".
Ciro wayar sa burin ɗan garuwa yayi, irin ƙaton wayar nan mai bottle, ya miƙa mata, da sauri ta amsa tana tambayar sa wani suna yasa?" Dialing tayi bayan sanar da ita sunan da yayi saving numbern da shi, a kira na Uku ne ya ɗauka yana faɗin, "sorry I'm meeting now".
ganin cewa bai ma san numbern da aka kira sa da shi ba, yasa Safna cewa "Dady it's me Safna Ammu na ce ba lafiya Dady dan Allah ka taimake ni" ta ƙarashe faɗin tare da fitar da hawaye a idon ta, cikin tashin hankali yace "what happen with her?" Babu ɓata lokaci ta sanar dashi, "ok I'm coming right now".
Kashe wayar tayi da tinanin, da ma ta san indai Dady yaji to zai yi gaggawan zuwa, miƙa masa wayar tayi haɗi da yi masa godiya "Safna kan ki na zubar da jini sosai" kan ya ƙara yunƙurin wata maganar tace, "zanje in wanke yanzu" ta faɗi tana sharar ƙolla, ita fa da so samu ne, in mutum zaiyi mata magana yayi mata kalma ɗaya ko biyu ya wadatar.
Zuwa ɗaki tayi ta shiga toilet ta wanke jinin da ke zuba, ta ɗaura ƙyalle à wurin, bata tsaya canza kaya ba, ta nufi inda Ammu take "Hasbunallahu wa ni'imal wa kiil" ta faɗi lokacin da zafin jikin Ammu ya ratsa hannun ta bayan ta ɗaura à kan ta.
Saurin tashi tayi ta ɗibo ruwa a kwano ta ɗauko ya di mai laushi ta fara tsomawa tana matsewa sai ta ɗora kan Ammu tana mammatsa mata, da addu'an Allah yasa dabarar yayi kafin zuwan Dady.
Ta ɗau 30 minute ba ta tsaya ba, amma zafin jikin ya ragu, sai à lokacin Dady ya zo cikin manyar kaya, irin na hamshaƙan masu kuɗi, ɗaukar Ammu sukayi zuwa Hospital, Safna ma akayi mata bandejin goshin ta, Dady ya tambaye ta me yasame ta haka, sai ta bashi amsa da bugewa tayi, dan sanar da shi gaskiyar babu abinda zai amfane ta da shi.
Doctor ne yake sanar musu da, "ba wani babban abu bane yasa ta kasancewa a yadda take yanzu face rashin motsa jiki sosai da ba'a sa ta, kuma ya kamata a rinƙa kula da ita wurin fitar da ita waje ta rinƙa shan iska, saboda kasancewar ta kullum à ɗaki guri ɗaya zai kawowa da jinin ta rashin jin daɗi gurin kewayawa a jikin ta, kuma hakan zai haifar mata da wani abun daban, ku sai mata keken guragu zai tai maka muku wurin tura ta ba tare da ta sha wuya ba" Bayan sun gama jin abun da likita yace Dady yayi masa godiya, da kuma sanar da shi za'a kiyaye.
Bayan fitowar su suka nufi ɗakin da Ammu take, "shirya ta mu koma Gida Safna" Cewar Dady, to ta amsa masa dashi sannan tace "thank you so much Dady" "No my daughter akan me zaki yimin godiya? dama kula da ku a wuya na yake, so don't thank me" ƙasa kawai tayi da kan ta, da roƙon Allah ya bata abun da zata sa kawa Dady da shi, saboda shine mai kula da matsalar su à ko da yaushe.
AMNA.
Koda isan su gida Ummee suka shiga tashin hankali dan ganin Raunuka a jikin Ɗan su, duk da anyi masa tritment, tambaya suka shiga yi musu, sai dai har yanzu Amna batayi magana ba, sai ma wucewa ɗaki da tayi.
A hasale cikin ɗagun murya Ummee ta fara magana, "har yaushe zaki bar abubuwan nan da ki ke yi Amna? Tun da ki kayi shiru nasan bai wuci ke kika haddasawa Mubarak wannan raunin da yake jikin sa ba, ke wace irin Mutum ce wai, baki da aiki sai neman rigima?" Rintse idanun ta tayi yayin da taji magan-ganun Ummee a gare ta.
"a ah Ummee ba yadda ki ke...." katse sa Ummee tayi "rufamin baki dama duk san da zata kwaso rigima ai a bayan ta kake, kai ga ka mai 'yar-uwa" "Biba kada kice haka saboda baki san dalilin da yasa faruwar hakan ba, domin nasan Amna baza tayi abu ba tare da dalili ba" Cewar Mamma dake zaune gefe tana ƙara kallon Mubarak cikin tausayawa.
Ummee ce ta ƙara cewa, "haba Mamma dubi abin da ta jawa Ɗan-uwan ta, ita kam koda yaushe bata san haƙuri ba ne, ita kinga jikin ta da ko ƙorzane ne? Duk abun da ake faɗawa Amna a kan haƙuri ba ta ɗaukar sa, sai kace ita tafi kowa zafin zuciya" Ta ƙarashe maganar cike da masifa.
"Mubarak meya faru a makarantar?" Mamma ta tambaye sa, sanar da ita komai yayi, babu ƙari ba ragi, sallallami suka hauyi cikin tashin Hankali, "yanzu abun da ya faru kenan, Lahaula wa la ƙuwwata illa billah, Amna wani irin abu ki kayi haka? ba ku zuwa ku sanarwa da mahukuntan makarantar su ɗau mataki da kansu?" Cewar Mamma cikin tashin hankali da tinanin a binda zai biyo baya.
Ummee kam kasa magana ma tayi saboda tsaban tashin hankali, sai da ta sauke babban ajiyar zuciya sannan ta fara kiran Amna, fitowa tayi har lokacin bata cire kayan ta ba, kuma fiskar ta ko alamar fara'a babu, sai lokacin suka ga jinin da ke kayan ta, "wannan kenan duk jinin mutanen ne, na shiga Uku Amna zaki kashe ni da raina, wannan wani irin masifa ne? Yanzu waya san abun da zai faru, bayan abinda kika jawo mana"
Sai lokacin ta buɗe baki tace "Ummee ku duba raunukan da suka yi masa fa" ta faɗi tana nuna inda yake, kan ta ƙasa "munji sun yi masa rauni, to kuma babu wata hanya da za kiyi sai na ramawa?" Cewar Ummee, Mamma ma tace, "Amna nakan goyi bayan ki a ko da yaushe, duk da abin da yaran sukayi ba daidai bane, amma hanyar da ki ka bi bai dace ba, yanzu Allah kaɗai yasan abun da zai faru gaba, dan nasan iyayen su baza su bar maganar ba".
Miƙewa kawai Amna tayi ta wuce dan yin wanka tayi Sallah, bin ta da kallo su kayi Mamma tace, "babu ruwan ta fa" "ai kin san ta Mamma duk abinnan da tayi ganin dai-dai take masa" faɗin Ummee tana girgiza kai cike da takai ci, shima Mubarak miƙewa yayi da ƙyar, "sannu Mubaraka bari in tafasa ruwa in mammatse maka jiki, baka zauna haka ba", Mamma ta faɗi hakan tare da miƙewa.
DARE.
Su Ummee sun kasa sanar da Baba abun da ya faru, dan ko yanzu daya kira su hira kawai sukayi, ba tare da kawo maganar ba.
BABA.
Bayan ya gama magana da iyalan sa, ya ijje waya kenan kiran Zilla ya shigo wayar sa, dagawa yayi da mamaki, "ka yi mamaki ne? To ba abun mamaki bane beautiful, kawai naji ina son jin muryar ka ne, na ƙosa gobe yayi in haɗu da kai, saboda ina da abubuwa masu ban sha'awa da zan ba ka, amma kamar wani lokaci zamu haɗu?" Ta faɗa masa yana ɗaukar wayar.
"Da ma wai haka take da surutu ne ko me? Danni banga jan ajin n'a ta ba" Cewar Baba a zuciya, sannan ya amsa mata da, "kamar da yammaci" "kashsh gaskiya banji daɗi ba, yammaci yayi nisa, amma ba komai sai lokacin i love you beautiful" kashe wayar yayi ba tare da ƙarasa jin abunda take faɗa ba, wani takaici ya rufe sa, dan shi ƙyamar ta ma yake, "Allah ka bani sa'a akan wannan aikin da na ɗauko" kawai ya faɗi a fili.
WASHE GARI, ASABAR RANAR HUTU.
SAFNA.
Duk da abin da ya faru jiya bai sa ta hutawa ba, sanin cewa yau ranar Aikin ta ne, cike da juriya ta fara aikin har ta gama, ɗauko keken da Dady ya kawo wa Ammu tayi ta ɗora ta a kai, dan fitar da ita tsakar gida dan shan iska.
Tasa Ammu à gaba tayi tana kallon ta, bayan ta fito da ita waje, ta zauna akan kujera ita ma, "sannu Ammu, na san dai yanzu kin ɗan ji sauki ko?" Lumshe ido Ammu tayi sannan ta buɗe alamar eh taji sauki, "yauwa Ammu na haka nake so, insha Allahu nan bada daɗewa ba, zaki samu lafiya daga dukkanin Matsalar ki".
murmushi Ammu tayi mata dayin mata alama da "Allah yasa hakan, nima abinda na keso kenan" ta ɗago hannun ta da ƙyar alamar "matso kusa dani" murmushi ita ma Safna tayi, ta sauka kan kujerar da take, ta tsugunna haɗi da ɗaura kan ta a saman ƙafafuwan Ammu, tana mai jin farin ciki a ranta, rabon da Ammu ta fito ko ƙofar ɗaki ta manta bere waje.
#To fah, shin iyayen su Jalo zasu bar maganar kuwa?.
Ya Baba zaiyi idan yaji abunda autar sa tayi? Zai goyi bayan ta ko kuwa?.
Baba zai ci nasara ko daiii?. Nifa har na fara tinanin wani abu😁
Fitar da Ammu waje shan iska zai ɗore kuwa?.
______________________________________________________________________________________________
Part 2️⃣1️⃣▶️2️⃣2️⃣
Shafa kan ta Ammu take yi a hankali, yayin da zuciyar ta ke tinanin wani abu daban, katse mata tinani Safna tayi sanadiyyar ɗagowa da kan ta da tayi, tana faɗin, "Ammu na ina zuwa kinji, ba daɗewa zan yi ba" da ido lawai Ammu ta bita.
Ba ta ɗau lokaci ba ta dawo da ƙaton paranti à hannun ta, ɗauke da kula da kuma plate mai zurfi da cokali a ciki, ijje sa tayi haɗi da buɗe kulan, ashe ferfesun hanta ne a ciki yaji romo sai tashin daddaɗan ƙamshi yake wayyooo😋.
Diba tayi tasa a mazubin sannan ta rufe, ta mayar gefe, zama mai kyau tayi a inda ta zauna ɗazu tana facing ɗin Ammu, "musamman dan ke nayi wannan ferfesun Ammu nasan zaki so shi sosai, yana ɗaya daga cikin abincin da Doctor ya umurta da ki dinga ci" murmushin jin daɗi Ammu tayi da yadda 'yar ta ke kulawa da ita yadda ya kamata, da itane kawai take iya magana mai tsawo.
ɗibawa tayi à spoon ta fara ba ta tana ci, sosai ya yiwa Ammu daɗi, Safna kuwa tana ba Ummee tana yi mata hira.
Fitowa daga falon yayi yana waya, sai dai ganin su da yayi yasa shi tsayawa yana kallon su, musamman Safna da take bawa Ammu abinci tana ta bata labari, sakin baki yayi yana kallon yadda take magana tana ta murmushi wani gurin kam har dariya take, "Ashe dama tana magana haka? har dariya take yi" ya faɗi a zuciyar sa.
"Yazeed kana jina kuwa?, Yazeed" daga can ɓangaren ake cewa jin yayi shiru, "Aliyu zan kira ka" kawai ya furta tare da sauke wayar a kunnen sa, ci gaba da kallon ta yayi, ya fara takawa a hankali kamar wanda ake kira, har ya isa kusa dasu idon sa na kanta, yana jin yadda muryar ta ke ratsa kunnuwan sa.
Tana gama bata, ta ijje kwanon gefe, Ammu kuwa sai murmushi take yi, ganin yadda Mahaifiyar ta ke murmushi, yasa ta cikin farin cikin da ta daɗe bata tsinci kan ta ciki ba, ɗauke da murmushi a fiskar ta tace, "kin ji daɗin labarin da na baki Ammu?" Tayi mata tambayar kamar tana jiran Ammu ta bata amsa, "eh yayi daɗi sosai" taji maganar sa gefen su, ba tare da ko jin motsin zuwan sa ba.
Da sauri ta juya duk da tasan muryar waye amma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 56