har ya fara yankar fatar saboda kaifin wuƙar, rintse ido sosai Shuraim ya yi, yana son yin addu'a amma harshensa ji ya ke kamar babu addu'ar da ya iya a rayuwarsa.
Amna kuwa bayan ta faɗi a kan zoben da Baba tsoho ya bata, kawai jikinta ya fara dawowa kalarta a hankali, sai kuma hankalinta ya fara dawowa, har hannunta ya yi matsi kaɗan, amma da yake wannan matsafan hankalinsu na kan Shuraim sai basu lura da ita ba, ƙafarta ne ya yi motsi shima sannan sai numfashinta ya fara dawowa kaɗan, idanuwanta kamar an ɗaura mata dutse ta fara buɗe su da ƙyar.
Wani irin bugu itama zuciyarta ya yi bayan idanuwanta sun sauka akan Shuraim da taga an sanya masa wuƙa a gefen wuyarsa, ƙwallah ne ya cika mata ido, cikin tashin hankali ta buɗe bakinta cikin nauyi ta fara fitar da addu'a kaɗan kaɗan mara sauti, yayin da take ƙoƙarin tashi, "Allahumma... inni a’uzu bika...min zawali ni’matika, wa tahawwuli ‘afiyatika, wa fuja’ati niqmatika,
wa jami’i...sakhatika" ta yi addu'ar kalmomin suna fita cikin rawar murya, amma kowacce kalma tana haifar da haske a cikin zuciyarta da kuma zoben da ke ƙasanta.
Matsafi kuma cire wuƙar ya yi daga wuyar Shuraim da jini ya fara fita kasancewar wuƙar ya yanke sa kaɗan, idonsa Shuraim rintse bai buɗe ba sai haɗiyen yawun tsoro da fargaba yake yi, ya gama sani cewa yau zai mutu a hannun matsafa. Shi kuma matsafin nan kuma ɗaga hannunsa da ke riƙe da wuƙar sama ya yi, yana ɗaga wuƙar hasken wutar da ke wurin ya bugi gefen wuƙar, ƙahon nan da ke saman dutse ya haskar da wuta kamar ƙahon shaiɗan, sai kuma matsafin nan ya kuma sakin wata dariya da ta tunzura baƙar zuciyarsa, dawo da wuƙar wuyar Shuraim ya fara yi, da niyyar cire masa wuya.
Babu abin da yake so face ya ga kan Shuraim a ƙasa, amma kan ya ƙarisa kaiwa jikin wuyar wani irin iska ya kaɗa shi da ƙarfin gaske, cikin hanzari da mamakin abin da ya faru ya juyo bayansa, ai kuwa ya ga Amna a miƙe kuma ga launin da yasanya mata na ɓacewa, sannan muryarta na tashi cikin addu'a mara ƙara sosai. Jin muryar da yake da tabbacin Amna ne yasa Shuraim buɗe idonsa da ya kulle, sannan ya kai dubansa inda Amna take, ta ke shima ya ji bakinsa ya buɗe, suka fara kirawo sunayen Allah da addu'oi à tare, firgita sosai duka mutanen nan suka fara yi, ganin abin da su Shuraim suka fara aikata musu.
Amna na ƙarasa miƙewa wannan zoben ya bayyana, tun da dama tare shi ta yi sanadiyyar faɗin da tayi a kansa, farin samansa da yake kamar diamond ne yafara bayyanar da haske. Zare ido sosai shugaban matsafa ya yi yana yin gefe daga inda Shuraim ya ke, wuƙar da ke hannunsa ya faɗi, jikinsa ya fara bayyanar da razani sosai, suma sauran muƙarraban na sa sun shiga cikin rikicewa.
Cikin tsananin mamaki da tsoro Amna ta fara duban wannan zoben, yayin da haskensa ya karaɗe ila hirin wajen, hannunta ta fara gani babu wannan jan launin da ta ga fatarta ta yi ɗazu, shima Shuraim kallon jikinsa ya yi ya fara dawowa daidai, cike da farin ciki da jin daɗi ya ke ganin Amna, domin ganin da yayi ta tashi cikin dauriya, ga kuma tsoron da ya fara gani na bayyana a fiskokin matsafan nan, jiki na rawa Amna ta fara durƙusawa tana sanya hannunta kan wannan zoben, duk da cewa zuciyarta na harbawa sosai, sannan kuma jikin na ta na cikin rashin ƙarfi sosai, sai dai tana jin kamar wannan hasken zoben da kuma addu'ar da take na bata ƙwarin guiwa.
Hannun na ta na rawa ta ɗauki zoben, sannan ta fara ɗaga shi a hankali, wannan jan da idanuwanta ya yi ya fara tafiya shima. Lokaci ɗaya mutanen nan suka saki ƙara mai ƙarfin gaske, wanda Amna da Shuraim suka ji kamar ba iya ƙarar su ba ne, wannan ƙahon da ke gilas ɗin nan ne ya fara girgiza da ƙarfi, hasken wutar da ya yi ya fara zama baƙi, wanda ya ke fita da wani sauti na ban tsoro, zuciyar Amna da Shuraim sai lilo ya ke cikin tsoro da tashin hankali, amma addu'a bai daina fita daga bakinsu ba.
"Zo...zo...ben haske...aa ah... ba zai yu ba...inaaa hakan ba zai taɓa yuwa ba!!!!" Cewar shugaban matsafan yana cigaba da yin baya, cike da wahala da kuma tsoron abin da ya ke gani, kyarma jikinsa ya farayi sosai idanuwansa na wani irin zubar da baƙin hawaye, ya kuma cewa, "zoben haskee!!? Ya aka yi haka!? Addu'a.. addu'a suke yi! Ku daina à aaah!!" Ya faɗi da ƙara yana kuma ja baya cikin tsananin rikicewar ƙwaƙwalwa, sauran ma sai ihu suke ta yi sannan suka zube ƙasa cikin azabar da ke son fin wanda su Amna suka ji ɗazu, ihun nan na su kuma ya ke kuma ba Amna da Shuraim tsoro.
Last part.
___________________________________________________
Too to, da alama wannan zoben da Baba ya ba su shi zai yi silar cetonsu, tun da ga dai shi nan ya fara kore musu duhun ƙwaƙwalwar da aka sanya musu na mance yin addu'a.
Shin zasu yi nasarar fitan ne? Ko dai matsafan zasu kuma con nasara a kansu?.
Mu haɗu à kashi na gaba idan Allah ya nufa...
Alƙamin✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar} [Gimbiyar Fasaha]👸🏽
Don jin yadda zata kaya✌🏼
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣4️⃣1️⃣▶️1️⃣4️⃣2️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Durƙushewa matsafin ya yi yana wani irin kururuwa mai fitar da gurnani, idonsa na cigaba da fitar da hawaye baƙi, wannan ƙahon kuma sai tsalle ya ke yi sosai, yana furzar da wani ruwa a jikinsa, jikinsa ya fara zagayewa da wazu rubutu masu haske kamar wuta, "ku dainaa, kar ku kawo ƙarshe na, bai kamata ba, bai kamata na ƙare tun yanzu ba, a a a ah, ku bari zan rabu da ku ku tafi, ba zan cutar da ku ba, zan bar ku ku tafi" cewar matsafin yana kuma sanya ihu yayin da jikinsa ya ke sa ke galabaita, domin addu'ar da suke yi da wannan hasken zoben sai cutar da shi ya ke.
Ijjiyar numfashi Amna ta yi ganin kamar komai na shirin warwarewa, hakan ya sa cikin jarumta ta fara tahowa gabansa, tana cigaba da jero addu'oi, "a ah, ki dainaa, na ce zan barku, babu abun da zan yi muku, ku bari, ki ɓoye wannan zoben, ki daina kusanto ni da addu'a, zan barku" ya faɗi ganin tana sake yowa gurinsa, saboda hakan da take yi yana kuma samar mishi da wani masifar sosai, wannan kalar jikin na sa ya soma rikiɗewa zuwa baƙi kamar dodo.
Sauran muƙarraban nan na sa kuwa, tuni wasu suka fara fitar da baƙin kumfa daga bakinsu, idanuwansu ya fara canzawa, dakawata Amna ta yi da zuwa wurinsa da kuma yin addu'a, jin maganarsa da kuma ganin yadda ya fara dawowa, sai dai bata ɓoye zoben ba kamar yadda ya nema, baki na rawa ta futa, "ka kwance shi" da ƙyar matsafi ya miƙe zuwa inda Shuraim ya ke don ya kwance sa, amma jin addu'ar da Shuraim ke yi ya kuma dakansa ne yasa shi saurin yin baya ya faɗi, "zan kunce, zan kunce ɗin, ki ce ya daina yi" ya faɗi yana sanya hannayensa a ƙafaɗunsa, yayin da ya ke sake ɗandanar wata azabar.
Amna ta maida kallonta kan Shuraim, hakan yasa ya dakata da addu'ar, sai wannan matsafin ya samu ya ja jikinsa sannan ya ɗauki wannan wuƙar da ke ƙasa, don ya yanke ɗaurin da ke ƙafar Shuraim, tsoro ne ya ɗarsu a zuciyar Amna, kada wannan matsafin ya yaudareta ya cutar mata da Shuraim, hakan yasa ta saurin kusantowa inda yake, "idan har ka cutar da shi, sai na ga bayanka yau wallahi!" Ta faɗi da ƙarfi, shikuwa matsafi ƙara yasa da yi mata alƙwarin babu abin da zaima Shuraim ta daina matsowa da wannan zoben,, domin ya riga da ya san hatsarin zoben nan a garesa.
Da sauri ya yanke igiyoyin da ke jikin Shuraim ba tare da ya yi masa komai ba, barin wurin Shuraim ya yi ya koma inda Amna ta ke, cikin kulawa da tausaya Amna ta ce, "babu abin da yasa me ka?" "Babu komai my Amna, tun da kema kina lafiya" Shuraim ya bata amsa da sakar mata murmushi, idanuwansa sun gama ramewa, kamar yadda ita ma Amnan haka na ta ya yi.
Matsafin nan kuwa ganin Amna da Shuraim sun juya suna magana da junansu, yasa shi fara tashi a hankali, yana jan raunannun ƙafafuwansa zuwa inda wannan baƙin ƙahon ya ke, ganin ƙahon ya yi ya daina tashi, ya sanya hannu ya ɗauki ƙahon da kuma ankarewa kada su Amna su ganshi, duk da ya ga kamar sun shagala da magana da junansu, sai fitar da wahalallen nishi ya ke yi, yana kallon su ya saki wani murmushin muguwar mugunta, saboda ya san idan har ba wani abu ya yi ba, to fa ba shakka su Amna zasu kawo ƙarshen tarihinsa yau ɗin nan, tun da har suka riƙe zoben haske a hannunsu, zoben da suke tsoronsa sosai, wanda shine silar kashe babban shugansu, domin shi hawa karaga yayi bayan babban na su ya mutu, sai ya zama kuma shine makusancin Shugaban dama, shine mafi baƙin zuciya a cikin sauran, hakan yasa aka bashi wannan matsayi, tsawon shekaru yana ƙoƙarin neman inda wannan zoben ya ke don ya lalata shi, amma sai gashi ba tare da ya yi tsammani zoben ya zo inda suke, to a ina ma wa'yan nan yaran suka sami wannan zoben ne?.
Murmushi ta yiwa Shuraim sannan ta ce, "kayi haƙuri akan taurin kan da na nuna maka, naƙi sauraronka, sai gashi abubuwa da dama suna ta faruwa" kan Shuraim ya kaiga bata amsa idonsa ya gane masa wannan matsafin ya hurgo ƙahon nan setin da suke da ƙarfi kuma da alama kashe su yake yi, saura kaɗan ƙahon ya iso su ya yi saurin janye Amna, sai ƙahon su wuce su haɗi da faɗawa cikin wutar da ke ci a can gefe.
Juyowa su kayi cikin firgici suna kallon matsafin nan, wato saboda sun barshi har ya samu damar son hallaka su? Cikin ɓacin rai Amna ta yo inda ya ke Shuraim na rufa mata baya, addu'a suka cigaba da yi suna kusanto inda yake da ɓacin rai, matsafin yayi baya yana zazzaro idanu, sannan yana cigaba da ihu haɗi da roƙonsu su rabu da shi haka, "saboda mun barka shine kai kake son kashe mu? Ina mahaifina ya ke!? Ina kuka ijje shi? Ka faɗamin ko na kasheka da wannan zoben.
Numfashinsa na fita a hankali, hatta jinin jikinsa ji ya ke yana azabtar da shi, suffansa na cigaba da lauyewa har ya canza duka jikinsa, ya dawo kamar dodo sak, su Amna da Shuraim sun tsorata sosai da ganin wannan suffar ta sa, sannan ga suma sauran mutanen jikinsu ya fara dawowa makamancin na wannan matsafin, sai dai shi na sa ya fi muni sosai. Ƙahon tsafi da ya jefa musu ya faɗi cikin wuta, yana faɗi wutar ta fara ruruwa, tare da amayar da ƙananun tartsatsi, ta fara tashi kaɗan kaɗan, sai dai daga su Amna da wannan matsafin babu wanda ya lura da komai. "Na ce ina mahaifina ya ke!?" Amna ta yi maganar da ƙarfi, Shuraim ma ya ce, "ina yake!? Zaka faɗa ko kuwa!?" Ya faɗi tare da ɗaura addu'a duk wanda ya sani.
Matsafi kuwa yana zaune a ƙasa yana ta juyi, da ƙyar ya fara magana cikin wata iriyar murya, sai dai ba da ƙara sosai ba, kasancewar ya galabaita matuƙa, muryar fita ya ke kamar maganar mutane biyu ya ce, "baya.. nan, baya nan" cikin fargaba Amna ta ce, "kamar ya baya nan? Kana son ka yi mana ƙarya kuma? Ka sanar mana yana ina?".
"Yana wurin Zabba-ba, ya... ya ijje sa ne, domin ya gudanar da, ai kinsa na ƙarshe.." Shuraim ya ce, "wani aiki Zabba-ba zai gudanar da shi? Me yasa ya ɗauke sa, me yasa aka saka cewa ya mutu alhalin yana nan, kayi mana baya ni!!" Kallon Shuraim Amna ta yi cikin tashin hankali, yayin da zufa ke ta tsatstsafo mata kamar tana cikin ruwa, domin jin abin da wannan matsafi ya fara faɗi game da Babanta, sai kuma ta maida kanta kan matsafin don jin amsar da Shuraim ya tambaye sa.
Nan ma da ƙyar yana juyi yana magana, "bai mutu ba, na..na gano, a aikin Zabba-ba, domin na gano, na gano shine cikamakon aikin da Zabba-ba ya ke, son mallakar iko a hannun sa, a kanshi ne kaɗai ruwan iko zai fara, daga nan shikenan, komai zai zama yadda, Zabba-ba ke so, ya tafi da shi wani, wuri, à can ne, zai kammala komai, gobe ne zai kammala komai, eh haka ne, can...can.." cikin wani sabon bala"in Amna da Shuraim suka haɗa baki gurin cewa, "a ina ne ya kaisa?! Me sunan wurin? A ina zamu same sa?!".
Mai makon ya amsa musu tambayar sai ya ce, "tun baya, ni ne, na hana à kashe ki ke Amna, ni ni na hana, eh hakane" cike da ɓacin rai na rashin ba su amsar da ya dace Amna tayi kansa, riƙe da wannan zoben à hannu, ta matsar da hannun inda ya ke sosai, hasken zoben na sake ƙaruwa, shikuwa bai ƙara cewa komai ba, sai ƙara mai wuce tunani ya ke sakewa sosai, a firgice Amna suka miƙe a tare, jin wani sautin da ke tashi kuma ta bayansu, shi kuma matsafi can ciki ya fara cewa, "bai kamata ba, ƙarshena ya yi? A a, bai yi ba, ni ne fa shugan matsafa, babu abin da...zai same ni, ni ke da ikon kashewa, ba..ba dai a kashe ni ba, ni ba zan mutu ba, yanzu zan mutu? A a ba zan mutu ba, ƙaho ka ceceni mana, mun daɗe muna yi maka biyayya, ka cece ni mana".
Ya faɗi jikin nan nasa na yin wata girgiza, "dole yau komai zai ƙare!!! Ka tura ni jikin wuta!!! Sannan ka kasa samo zoben haske!!! Yanzu ga shi ya zo da kanshi!!! Ka kawo ƙarshenmu da kanka!!!" Wannan matsafi ya ji muryar nan mai ƙarfi da ƙaraji, idanuwan nan na sa masu kama da 'yan china suka fara juyawa kamar ana gara taya, ƙirjinsa na bugu kamar zai faɗo hannunsa, jin muryar aljanin ƙaho da ya yi. Amna da Shuraim da ke tsaye suna kallon wuta na tashi kamar halittar shanu mai ban tsoro da firgitarwa, sai kuma suka sake jin wannan maganar, sai da suka faɗi haɗi da toshe kunnuwansu, amma duk à banza, addu'a suka cigaba da yi sannan suka buɗe idanuwansu da suka runtse.
Gani suka yi wannan wutar ya fara cinye wuri, sai tashi yake yi da sassautuka n'a tsoratarwa, tashi suka yi suna juyawa kallon junan su, matsafi da muƙarrabansa kuma suna cigaba da sakin sauti shima mara daɗi kwata-kwata, da sauri Amna ta juya gurin matsafi tana cewa, "ka faɗa min inda mahaifina yake ya yana ina?" Tana faɗi ta fashe da kuka, wutar nan sai faɗaɗawa take a wurin, shi kuma wannan matsafin a yanzu babu abin da ya ke sai ihu, domin gaba ɗaya ya haukace, fatar jikinsa sai kumbura ya ke yi yana fitar da kumfa, haka sauran ma, sai dai na shi yafi tunzura, dama shi shugaba ai ya kamata ya samu fiye da mabiyansa.
Shuraim jan Amna ya ke ta zo su bar wurin nan, idan ba haka ba hatta su ƙonewa zasu yi cikin wannan wutar, amma ita Amna ta ƙi, sai sake tambayar matsafi take ina mahaifinta, ya faɗa mata ko ta illata shi, baƙin hayaƙi ya fara zagaye wurin, hakan ya haddasa musu sarƙewar numfashi suka hau tari, ƙarfin gaske Shuraim ya samu ya fara jan Amna, amma sai ce mishi take ya bari wannan matsafin ya sanar da ita inda zata samu mahaifinta, tana faɗi tana tari sai tirjewa take yi.
Janta ya ke da ƙarfi yana cewa ta bari in Allah yasa sun koma gida zasu nemi in da mahaifin na ta ya ke. Wutar nan sai mamaye wurin take, Shuraim kuma na jan Amna suna fita daga ɓangaren, kuka Amna ta ke tana kiran Babanta shi kuma Shuraim yana cigaba da janta, wata wutar ne ta mulmulo kansu, fitar da idanu su kayi tare da tsalle suka sauka a gaban ƙofar wannan ɓangaren suna cigaba da tari sosai, wutar nan kuma ta fara lamushe komai da ke ciki. Saurin ansan zoben da ke hannun Amna ya yi don yaga tana shirin faɗarwa, so ya ke su fita daga kogon ma gaba ɗaya, to amma ta yaya?.
Miƙewa suka yi suna kallon abin da idonsu bai taɓa gani ba, yadda wannan wutar ta ke cinye wuri gata ko kyan gani babu, sai baƙin hayaƙi da ke sake mamaye har inda su ke, Shuraim tunanin hanyar da za su bi don fita ya ke, ita kuma Amna idon ta na kan wannan masifar da ba ta tunanin zata kuma arba da shi a rayuwarta, suna a haka katsam suka ga wannan zobe ta haska wata siririyar hanya, da mamaki suke kallon wannan hanya, juyowa su kayi suna kuma kallon juna, haɗi da cigaba da sauke tarin da suke yi, numfashin su na kuma hawa, girgiza kai à tare su kayi akan su bi wannan hanyar.
Kafin su fara tafiya suka yi saurin juyawa, ganin wutarnan suka n'a shirin fitowa, idan da ba wutar ƙunar tsafi ba ma, ai da tuni wata maganar à ke ba wannan ba, domin wutar juyawa ya ke kamar ruwa, rugawa suka fara yi suna gudu da iya ƙarfinsu, hasken zobe da addu'oinsu n'a haske musu hanya, yayin da shi kuwa wanna wutar sai mamaye wurin ya ke gaba ɗaya, ciki ikon Allah suka fara hangen ƙofa da ya bayyanar da hasken waje, cike da firgici suka ƙarawa gudunsu sauri, domin yadda suke ji tamkar wannan wutar na biye da su abaya, duk da basu iya ko juyawa bayan, kamar kuwa sun sani, saboda wutar nan ko ina take karaɗewa, idan kuwa suka tsaya, to fa sai buzunsu.
Daidai ƙofar suka iso amma suka fara ganin ƙofar kama yana shirin haɗewa, bugun zuciyarsu ya ƙara bankaɗa, Amna ce ta fara fita, saura kaɗan ƙofar ya haɗe da Shuraim ya samu ya tsallake, aikuwa sai ƙofar nan ta haɗe ƙam kamar ba a taɓa yin wata hanyar shiga kogo ba, matsawa suka yi tsakaninsu da wurin kaɗan, suna kallon wurin tsoratar da ke jikinsu bai gushe ba, balbal gurinnan ya ke ci sosai, hatta bishiyoyi da duwatsu da duk wani abu da ke da alaƙa da kogon nan ya ƙone ƙurmus, suka fara ganin kogon nan na zagonyewa yana dawowa tamkar ƙasa.
Tarin su Amna ya lafa, amma ganin abun mamakin da ke ƙara tashi ne ya su saka duk maganansu suna kallon ikon Allah, wurin nan ya dawo yashi gaba ɗaya, kamar wani abu mai suna kogo bai taɓa wanzuwa a wurin ba. kuka ne ya tahowa Amna, yin ƙasa ta yi tana kuka, saboda ita ta gama ɗauka cewa ƙila wannan matsafin ƙarya ya ke yi, mahaifinta na cikin wannan kogon, gashi kuma komai ya tafi, kenan shikenan ta rasa mahaifinta? Barin kallon wurin Shuraim ya yi, sannan ya durƙushe yana rarrashinta, sai kuma ya ɗan saki ƙara tare da ɗaura hannunsa gefen wuyansa, da sauri ta ɗago tana dubanshi, zaro ido ta yi bayan ganin ya cire hannunsa wani ƙaton ciwo na yanka ya bayyana a wurin, wato wurin da matsafi ya ɗaura masa wuƙar nan.
Cikin ruɗewa ta ce, "sannu, yana maka zafi ko? Sannu" ta faɗi hawaye ta sake fito mata, tana yunƙurin tashi don ganin ciwon da kyau, idonta da ya kuma sauka akan jikinsa babu riga, hakan ya sa ta saurin kawar da kai gefe, don ita sai yanzu ma hankalinta ya gane mata ashe babu riga a jikinsa, taɓa kanta ta fara yi don ciro gelenta da tayi rolling, don ta yaga masa ya sanya a wurin ciwon na sa, amma sai gashi hannunta ya taɓa gashin kanta, gashinma a zube ko rimbom babu, bata san cewa tun farkon abu gele da rimbom suka fice ba, don duk bata lura ba sai yanzu, to dama ana ta kai wake ta kaya?.
Last part.
___________________________________________________
Alhamdulillah! Amna da Shuraim sun samu tsira daga cikin kogo mai hatsari, wanda ba komai ba ne yasa suka yi wannan nasarar sai ƙarfin addu'oin da suka sa a gaba, da kuma tallafin zoben haske da baba tsoho ya basu, duk wanda yasa Allah gaba tabbas zai yi nasara.
To shin waye ne wannan tsohon? Ya aka yi ya mallaki wannan zaben? Kuma ya aka yi ya san da zoben zai basu gudunmawa a kan masifar da zai tunkare su? Wanda su a lokacin ba su sani ba.
Sannan kuma ga matsafi ya sanar da su cewa Zabba-ba ya tafi da Baba, to da gaske ne? Idan da gaske ne kuma ya ce gobe ne Zabba-ba zai aikata komai, to shin kuna ganin zasu yi nasarar taimakon mahaifinsu ba tare da Zabba-ba ya cimma manufarsa na sanya masa ruwan iko ba?.
Mu kasance da ku a kashi na gaba, don jin yadda zata kaya.
Alƙalamin AISHA G UMAR {Mrs Umar} [Gimbiyar Fasaha]👸🏽
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣4️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣4️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Miƙewa Amna ta yi tana share hawaye haɗi da zagaye idanuwanta tana neman mayafin na ta, shima Shuraim ya tashi yana sanya hannunsa kan wurin ciwon, domin zafi yake yi masa, ƙila ma don ana cikin tashin hankali ne ya sa ɗazu bai ji ciwon ba, wai sahun giwa ya ta ke na raƙumi, "me ki ke nema ne? ya ki ke wani dube-dube kamar kaɗangariya n'a neman ɗiyarta?" Bata juyo ba ta cigaba da neman gelenta, shi kuma dariya ya fara fitarwa a hankali, sannan ya kuma cewa, "yammata magana na ke fa".
Bata kuma tanka masa ba sai ma tsayawa da ta yi tana nazari, domin dai bata ga mayafin na ta ba, idonta ne ya sauka kan ruɓin rigarta da ya fara yagewa ta ƙasa saboda karan battan da aka sha, da sauri ta sunkuya tare da sanya hannunta ta yage shi siriri, sai ta ɗago tare da miƙa masa ƙyallen tana cewa, "ka ɗaure wurin ciwon!" ta faɗi ba tare da ta juyar da fiskanta kansa ba, saboda ba tason kallonsa kasancewar babu riga a jikinsa. Shi kuwa Shuraim da ya tsaya yana kallonta da mamakin ganin yadda ta yage rigarta saboda shi, amma fa ya yi farin ciki mara misaltuwa.
Hannu yasa ya amsa sannan ya fara ƙoƙarin ɗaure wurin ciwon, sai dai bayan ya ɗan yi ƙasa da kansa don ya saƙala ƙyallen ya ɗaure sai ya ji ya yi masa zafi, hakan yasa ya ɗan fitar da sauti a bakinsa, da sauri Amna ta juyo tana dubansa, amshe ƙyallen ta yi haɗi da rufe idonta wai don kar ta ga jikinsa, a haka ta ɗaure masa à hankali, yayin da shi kuma idonsa ya ke a kan fiskarta cike da murmushi, Amna na kammalawa ta tashi ta fara tafiya, sai da Shuraim ya taɓa inda ta ɗaura masa sannan ya fara rufa mata baya.
Sauri suke yi don zuwa inda motarsu ya ke, tafiya suke yi a wahale sabida dama hanyar shiga wannan dajin da nisa, shiru suke ji a hanyar ba sa jin ko da kukan tsuntsu ɗaya, ba kamar yadda ɗazu suka ji ba, haka dai har suka samu isowa inda motar su yake, jingina jikin motar suka yi suna sauke numfarfashi, "ya kamata mu huta kafin mu kama hanya ko? Don na ga da alama jarumtar C.E.O ya tafi, na yi gaskiya?".
Juyowa Amna ta yi da niyyar yi masa masifa, amma kuma sai ta yi saurin juyawa, cikin takaice ta tame fiska tana cewa, "wai kai malam kam baka jin kunyar yawo ba riga ne? Ya kamata ka samu ko da, ko da wani ganye ne ka rufe wannan jikin na ka" dariya ya fashe da shi sosai, sake juyowa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 43 Chapter of 56