Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hankali ya juyo yana duban Safna murmushi ya sakar mata mai haɗe da dauriya, saboda bayan kalaman Dadynsa ya gane cewa, wannan wacche ya dawo gida ya tarar ba Safnarsa ba ce, sannan ita ba ta kiranshi da yaya, gashi wannan kuma ta kirasa da yaya Yazeed, hakan ya nuna mishi cewa wannan wacche ya ke gani ita ce Safnarsa, giɗa mata kai ya yi alamar kece Safna haɗi da kiran sunanta. Giɗa masa kai Safna ta yi amsar eh ni ce, idonta ya fito da wasu hawayen masu raɗaɗi, shima Yazeed ƙwallan da ya cika masa ido ya fitar. Alama Dady ya yi wa mutanen da su ka kama Yazeed, hakan yasa su ka sake sa suna yin gefe, "Ah my son kai ne? Ya aka yi kazo nan? Zo in yi maka bayani" Dady ya faɗa haɗi da kama hannun Yazeed don ya ja shi gefe su yi magana, sabida bai gama tabbatar da Yazeed ya ji batunsa ba. Ɗauke ido Yazeed ya yi daga kan Safna ya dawo da kallon kan Dady da ya riƙe masa hannu, da ƙarfi ya fincike daga riƙon da Dady ya yi masa. Dady ya kuma saurin juyowa yana kallon Yazeed, ya ji Yazeed ɗin ya ɗora da cewa, "babu bayanin da ya rage ban ji ba Dady! Idan ma akwai wanda ya rage, to shine ka faɗa min gaskiyar cewa ni ɗan ka ne?" Cewar Yazeed yana kallon Dady cikin ido, Dady ya kasa ba shi amsa, sai kallonshi kawai da ya ke shima, "na kasa gasgata abin da kunnuwana su ka jiye mini Dady, sai dai dolena in yarda domin ba wani ba ne ya sanar da ni, daga baikinka na ji Dady, kai wani irin mutum ne, duk laifukan da ka aikata amma ko a jikinka, har yanzu ma kana son aikata wani gagarumin laifin, anya mu da kanmu 'ya'yanka baka yi mna wani abun ba kuwa? Ka faɗamin Dady me mu kuma ka yi mana?" Yana faɗi ya fashe da kuka tare da durƙushewa. Hawaye ne sabo ya ke cigaba da bin fiskar Safna tana kallon Yazeed da ke kuka, wanda bata taɓa kallon ko da hawayensa ba. Matsowa kusa da shi Dady ya yi sannan ya ce, "a ah my son don't cry, kukan da ka ke yi ba daɗinsa na ke ji ba, duk duniya babu abin da na fi so kamar 'ya'yana, duk abin da na ke aikatawa a duniya ina son na ganku cikin farin cikie, bana son duk abin da zai zama matsala a gareku, tun kuna ƙana na na ke kula da ku, na ke sawa a bibiye duk inda zaku je don kawai à kula da lafiyarku, duk abin da zai zam muku matsala nake matsar muku da shi". Dady ya ƙare maganar da juyawa ya ba Yazeed baya, Yazeed kuwa kallonsa kawai ya ke yana ƙara jin zafi a ransa, "saboda ku yarana na hana safarar duk wasu muggan ayyukana a nan garin Kaduna! Duk saboda gudun kada kuyi ta'amali da kayan mayen da na ke siyarwa, don haka ɗana Yazeed ka sani! Na yi sadaukarwa da yawa duk saboda ku, ko auren Ruki da aka yi da wanda ban sani ba, wannan aiki nawa da na ke son isarwa yanzu, shi ne ya hana ni maida hankali akan ta. Sannan abu na ƙarshe! Ko dukiyar da na samu cin nasarar karɓa yanzu na Mai-daraja ku za ku fi morarsa" Dady na gama maganar ya juyo ya dubi Yazeed sannan ya daɗa cewa, "don haka ka koma gefe kawai, domin zan kammala aiki na, babu wanda zai hana ni aikata hakan?". Cike da takaici Yazeed ya ce, "tir Dady! Wallahi na tsane ka Dady! Na tsani kasancewarka uba a gareni, ina ma ba kai ka haifeni ba, na ji kunyar amsa sunan ɗanka da na yi tun ina ƙarami" yana faɗi ya kuma sa kuka mai ban tausayi. Murmushi kawai Dady ya yi sannan ya ɗaga ido ya kalli mutanensa ya ce, "ku kama shi kuyi min gefe da shi, idan na gama abun da nake son yi, zan san abin da ya kamata in yi masa. Kama sa mutanen su ka yi suka kai sa gefe can. Juyawa Dady ya yi ya nufi inda Baba ya ke, ya ɗauki wannan allurar da yaƙinin yanzu dai komai zai kammala, sauran mutanen kuma suna nufan inda su Amna su ke riƙe da makamai a hannu, kamar yadda Dadyn ya ba su umarni da fari. Kici-kicin ƙwacewa Yazeed ya ke yi yana kuka da roƙon Dady ya rabu da su Amna, amma ina Dady ko sauraronsa ma ba ya yi. Amna har yanzu kanta na sunkuye, wannan tabon gefen ba shi, haka eye colour ɗin ma duk sun yi ƙasa, jikinta ne ya fara murɗewa a hankali, yayin da Safna kuma ta fara tsintar kanta cikin wani yanayi. Lokaci ɗaya Amna ta buɗe idonta, ƙwayar Idon ya dawo tamkar garwashin wuta da ya yi jawurr, Safna kuwa Amna na buɗe ido ita kuma na ta idon ya rufe haɗi da kwantawa kamar an tunkuɗa ta. Mutanen nan sun zo kan su Amna, haɗi ɗaga makaman hannunsu don su sauke akansu. Sai dai kafin su kaiga cinma burinsu. Amna ta tashi kamar iska haɗi da ɗaukar katakon da ke ƙasa ta bugawa mutumin da ke dadai ita da kuma sauran da suke kan Safna da Shuraim, tana buga musu ta nufan inda Dady ya ke da wani irin gudu kamar ba na mutum ba. Soka Allurar Dady ya yi gefen wuyan Baba, hakan yasa Baba rintse ido hawaye na biyowa baya, murmushi Dady ya sake tare da matsa wannan ruwan Alluran. Sai dai ƙarar da ya ji na mutanensa da kuma riƙe masa hannun da aka yi lokaci guda sai yama rasa wanne ya riga wani, juyawa ya yi da sauri ya kalli mutanensa a ƙasa sai juyi suke yi suna sakin ƙara, sauran kuma idonsu a kansa fiskarsu da mamaki. Dawo da kansa kan hannunsa da aka riƙe ya yi, sai da ya zaro ido ganin jijiyoyi raɗo-raɗo a saman hannun da ya riƙe shi, a hankali ya fara ɗagowa don kallon mai wannan hannu. Sai da ya ƙara zare idonsa ganin Amna da ya yi, gasinta ya barbazu saman fiskarta, sai dai yana iya kallon ƙwayar idonta da ya yi jawur kamar wuta na ci a ciki, kafin ya yi ƙwaƙwƙwaran motsi Amna ta cire Allurar da ke wuyan Baba, sannan ta hankaɗa Dady da ƙarfi, wanda ya sanya shi sai da ya bugi bango da ƙarfi, sannan ya yi ƙasa a galabaice, sauran mutanen Dady ne ganin abun da ya ke faruwa ya sanya su kuɗunzuma zuwa ga Amna. Shuraim da ya riga ya daina yunƙurin tashi ne ya bi Amna da kallo, haka Yazeed ma da yake kiciniyar ƙwacewa daga riƙon da aka yi masa, suka zubawa Amna ido, ba tare da sun ankare da cewa Safna ta suma ba, duka Amna ta ke kai musu kota ina, zn iya cewa kamar dai Amna ba'a hayyacinta ta ke ba, domin wannan faɗar da ta ke yi, yafi duk faɗan da ta taɓa yi a rayuwarta, kamar ba ita kaɗai ta ke yinsa ba, jan idonta har yi ya ke kamar tartsatsin wuta na fita daga ciki. Sai da Shuraim da Yazeed su ka razana da abin da ya ke faruwa, musamman Shuraim da ya yi mamakin yadda ta ke wannan faɗar, saboda yadda jikinta ya yi liƙis bai yi tunanin zata iya wani abu ba, don shi da kansa yanzu tashin ma ya gagare shi, sai fidda numfashi da ya ke yi kawai. Dady kam bai ma gama dawowa daga azabar bugu da buguwan da ya yi ba, kallon Amna ya ke idon nan kamar zasu lumshe. Tsoro ya fara shigansa musamman yadda ya ke ganin Amna na jibgan mutanensa kamar ba mutum ba, dole ya san dabarar da zai yi in ba haka ba zata yi masa asara mafj girma a rayuwarsa. Tsawon mintuna babu abin da ya ke tashi sai ihun mutane da ƙarar dukan da Amna ta ke wa ko wannensu, gaba ɗaya ta bazad da mutanen Dady da suka haura Arba'in, ba tare da jikinta ya nuna galabaita ba. Da gudu Yazeed ya yi inda Safna ta ke, sai da ya kalli Shuraim sannan ya maida kallonsa kan Safna da bata motsi, a matuƙar tsorace yake girgizata amma ji ya ke jikinta na sake, "my Safna open your eyes, ki tashi, wai me ya same ta ne?, Dady ka cuce ni" Abin da Yazeed ke faɗi kenan cikin ruɗewa da hawaye. Jin haka ya sanya Shuraim jan jiki ya matso kusa da su, "me me me ya sameta? Ƙanwata ki tashi, ki tashi Kin ji Safna, na yi miki alƙawariin kulawa da ke a wannan karon, ba zan taɓa barin kowa ya cutar da ke ba, kinji? Ki tashi Safna" faɗin Shuraim yana fidda hawaye shima. ƙurawa Shuraim ido Yazeed ya yi, sai kuma suka maida hankalinsu gaba ɗaya kan Safna, amma fa Safna da alama ma ba jinsu ta ke ba. Amna kuwa bayan ta gama da duk mutanen Dady ta jijjin musu rauni sosai ba tare da ta kashe su ba, sai kawai ta juya zuwa inda ta tura Dady amma bata gansa ba, haɗe fiska ta yi sosai har ya zama kamar ba ita ba, juyawa ta fara yi sai ta kalli Dady na sake neman yinwa Baba alluran, gudu tasa ta tsaya a gabansa tana fitar da huci kamar zakanya. A tsorace Dady ya sakar da allurar ƙasa yana kallonta cikin firgita da lamarinta, bai taɓa tunanin zata iya tashi daga raunin da ya yi mata ba, sai gashi yadda ya ga ta ke jibgar mutanensa da salon yadda ta ke yi kamar ba ita ba, anya wannan ba aljana ba ce? Ya kuma tambayar kansa a karo na biyu. Hannu Amna ta ɗaga tare da ɗaurawa a wuyar Dady, shaƙe shi ta yi sosai tana raba ƙafarsa da ƙasa. a take Dady ya sanya hannu yana neman cire hannun na ta amma ina ya kasa, fiddo ido ya shiga yi yana buɗe baki sai wutsul-wutsul da ƙafa ya ke yi, jin sa ya ke kamar lahira na nemansa. Sai da ta ɗaga shi sama sosai sannan ta yi wulli da shi zuwa kusa da su Shuraim, da sauri suka juyo suna kallon Dady. Shi kuwa Dady cikin azaba ya samu damar tashi daga kwancen da ya yi silar hurgoshi da Amna ta yi, hannunsa ɗaya ya ɗaura a wuya, ɗaya kuma a dafe da ƙasa yana neman matsawa baya, sai hangame baki ya ke yana jin kamar Amna bata sakan masa wuyan ba. Amna kuwa doso shi ta fara yi gashin nan baje a kan fiskarta, babu abin da ta ke yi sai fitar da numfashi mai uban ƙara, tana isowa gabansa ta tokare shi haɗi da ɗaura ƙafanta ɗaya saman cikinsa tana dannawa, ƙara ya kuma saki karo na babu adadi, wanda hakan sai da ya sanya Yazeed kawar da kai gefe hawaye na zubar masa kan kuncinsa. Baba tun yana kallon abubuwan da ke faruwa har idonsa ya rufe, saboda wannan ruwan allurar ya riga da ya shiga jikinsa, duk da cewa ba sosai ba, jijiyoyin jikinsa ya fara motsawa kamar ana jijjiga masa su. Dady da ya ke ihu yana roƙon Amna ta ƙyale shi, saboda ji ya ke kamar wani nannauyar ƙarfe ne aka ɗaura masa a kan cikinsa, da ƙyar ya juya yana kallon Yazeed da ya kawar da kai ya ce, "ɗa na, my son, ba zaka iya taimakon mahaifinka ba? Ni ne na haife ka, kuma babu wanda ya kai ni sonka a duniya, duk abin da na yi saboda ku na yi sa". "Bai kamata na ce ka yi ƙarya ba, amma ya kamata na ce haka Dady! Ƙarya ka ke yi, duk abun da ka yi don kanka ne ba don mu ba" Yazeed ya faɗi tare da sake mayar da kansa gefe, duk da cewa yana jin wani irin yanayi da tausayin mahaifin na sa a cikin ransa, sai dai mahaifin na sa ya cancanci duk wani hukunci, saboda zunubin da ya yi sun yi yawa. Amna kuwa ɗauke ƙafarta daga kan cikin Dady ta yi, sannan ta juya ta je ta ɗauki wani icche ta dawo wurin Dady, kafin Dady ya yi ihun ganin abin da Amna ke shirin yi masa, ta ɗaga itachen ta buga masa lafiyayyu guda uku. Sai da Yazeed ya rintse idanuwansa, domin yadda ya ke jin dukan na shiga ransa. Shuraim kuwa ji ya ke dama shima yana da ƙarfin tashi, da ya ƙarawa Dady da na sa. Dady sai sauke nishin azaba da ƙarar raɗaɗin da ya ke kyautata zaton ya fi wanda ya ganawa su Amna ya ke yi, hannu Amna ta sanya ta kuma ɗaga shi sama, amma wannan karon kwalarsa ta cakuma ba wuya ba, nan ta fara fitar da magana da muyar da ke amsa kuwwan muryoyi guda biyu, wanda za'a kira shi da muryar Amna da kuma na Safna. Last part. ___________________________________________________ Hmm ga dai Amna ta tashi, anya kuna ganin Amnan ce kuwa? Ko dai ya haɗe da wani abun wanda ba mu sani ba? Ashe dai Dady saboda 'ya'yansa ne baya safarar miyagun kayan mayensa a Kaduna. Kun ji daɗin abin da Amna ke aikatawa Dady? Shin kuna ganin zata bar Dadyn haka ko kuwa kashe shi zata yi? Yazeed zai cigaba da zuba ido ana yiwa mahaifinsa haka ko zai yi wani abu?. Mu kasance a next part don jin yadda zai kasance ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣5️⃣9️⃣▶️1️⃣6️⃣0️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 Hannu Amna ta sanya ta kuma ɗaga shi sama, amma wannan karon kwalarsa ta cakuma ba wuya ba, nan ta fara fitar da magana da muyar da ke amsa kuwwan muryoyi guda biyu, wanda za'a kira shi da muryar Amna da kuma na Safna. "Yau ne ranar da zaka amshi sakamakonka! Yau ne ranar da zaka tuge shukar da ka shuka! Yau ne ranar da zaka je gurin wa'yan da ka kashe! Da kai ka ɗauka zaka ƙare rayuwarka da zunubai ba tare da ka ɗan-ɗani kuɗanka ba?! Ba zamu taɓa rabuwa da kai ba! Yau zamu kashe ka!". Ta faɗi tare haɗi da bugashi da jikin bango ba tare da ta sauke shi ba. Dady sai amsan gashi ya ke, idanuwansa kamar zasu rabu da gidansu, Amna kuwa kallonsa ta ke yayin da ta ke ƙara azaman shaƙe masa wuya, lokaci ɗaya ƙwayarIdon Dady ya canza izuwa baƙi, yayin da baƙin hayaƙi ke fita daga ciki, hakan na faruwa ya samu ɗaga hannunsa da ƙarfi ya ture Amna. sakin wuyan Dadyn ta yi haɗi da ja baya da ƙarfi tare da sakin ƙarar ta ita da Safna, wato dai murya biyu yanzuma ya yi amsa kuwwa, ta sunkuyar da kanta idonta a rufe. Yazeed da ke ƙoƙarin taimakawa Shuraim miƙewa su ka yi saurin maida hankalinsu kan Amna, a tare su ka kira sunan Amna da ƙoƙarin isa inda ta ke, sai kuma su ka fidda ido, sakamakon abin da suka ga ni. UNCLE MUSA Sallama ya yi a ƙofar amma ba a amsa masa ba, hakan yasa ya shiga yana kiran, "yata Safna?" Amma shiru ba amsa, dama wayarsa da ya bari ne ya taho ɗauka, nufan inda ya bar wayar ya yi, ya ɗauka haɗi da dubawa, dama akwai abin da ya ke son turawa ne, da ba zai ma dawo ba, garin tura massage sai ya ga kamar da sunan Shuraim a wurin, hakan yasa ya yi saurin shiga, domin kuwa ya san dai babu message ɗin da Shuraim ya turo masa, amma gashi wannan ya nuna har an buɗe, zare ido ya yi bayan ganin saƙon da ya ƙunsa a ciki. "Kenan Safna ta gani?" Ya tambaye kansa haɗi da ɗaga kai yana kiran Safna, zuciyarsa ne ya tsinke kada dai ta nufi wurin? Da hanzari ya duba numbern Shuraim ɗin haɗi da kira, amma ba ya shiga, cikin rashin nutsuwa ya fita yana faɗin, "ohh 'yata Safna ya zaki je wurin nan?". GIDAN GONA. Jijiyoyin jikin Baba ne ya dawo baƙin ƙirin, baƙin hayaƙi na tashi jikinsa, wanda hakan ne ya sanya ƙwayar Idon Dady ya koma baƙi mai tattare da hayaƙin. Ɗagowa Amna ta yi tana kallon Dady, shi kuwa ya fara sakin dariya babu ƙaƙƙautawa, bai yi zaton aikin na sa zai yu ba, saboda da yana ganin kaɗan ruwan sinadarin ya shiga jikin Baba, sai ga shi ashe hakan ma zai yi. Amna ce ta yunƙura zuwa inda Dady ya ke, amma tana isa Dady ya kuma kai mata wani bugun, yin baya da ƙarfi ta yi haɗi da faɗi tare da dafa setin ƙirjinta da ke yi mata zafi. Shuraim da Yazeed ba ƙaramin razana da abin da ya faru da Amna su ka yi ba, sai dai Shuraim jin kansa na juyawa ya yi, ha kan yasa ya fara rage ido yana ƙoƙarin faɗi, Yazeed ya kama shi yana yin ƙasa da shi, tare da ambatan sunansa. Tsaida Dariyar Dady ya yi da cewa, "kin yi kaɗan yarinya! Baki isa ki ga bayana ba, yanzu na riga da na mallaki duk abin da nake so, na mallaki komai yanzu, na samu tsafin da na daɗe ina son samu!" Ya yi maganar da sake yin dariya. Kan Amna na ƙasa ta kasa ɗagowa, sabida yadda take jin wani irin abu na juya mata a cikin ƙirji, hayaƙin da ke jikin Baba ne ke dawowa kan Dady, aikuwa sai Dady ya fara juya hannunsa kamar mai yin siddabaru, baƙin hayaƙin nan na komawa cycle a hannunsa kamar ƙwallo, Dady ya san in har ya jefawa Amna wannan tsafin to fa shikenan Amna sai dai wata. Zaro ido Yazeed ya yi koda hankalinsa ya kai inda Dady ya ke, hakan yasa ya miƙe tare da kalloninda Amna ta ke, saboda lura da ya yi kanta Dady ke ƙoƙarin jefa wannan abun, da gudu ya nufi inda Amnan ta ke cikin tashin hankali, domin kuwa ya ga taƙi ɗago kai, sannan kuma Dady na son cutar da ita, gwara ya yi hanzari zuwa ya matsar da ita kafin Dady ya wullo tsafin da ya ke fitarwan nan. Sai dai yana isa gaban Amna wannan abu da Dady ya riga da ya wullo ya sauka a bayansa, ƙara ya saki tare da yunƙurin faɗi. "Noo Yazeeed!!" Dady ya ambata cikin ruɗewa sosai ganin abin nan a kan ɗansa Yazeed ya sauka. Saura kaɗan Yazeed ya faɗi Amna ta yi saurin taroshi a hankali ta yi ƙasa da shi shima, hawaye ne ya fara kwaranyowa a idon Yazeed kamar ba gobe, hwayensa ya zuba a kan hannun Amna, ɗago hannun ta yi tana kallon hawayen sai kuma ta miƙe tana kallon Dady da ya durƙusa yana hawayen abin da ya ma ɗan na sa, jan wutar kalar ƙwayar Idon Amna na sake ruruwa tana dosan inda Dady ya ke. Dady kuwa ganin Amna na doso shi ya sa ya miƙe don ya kuma kai mata wani harin yanzu. Da mamaki ya bi hannunsa da ya ke shirin sake yin abin da ya yi ɗazu da kallo, ganin hayaƙin ya fara barin hannunsa, idonsa ma ya fara washewa daga wannan kalar, da sauri ya juya yana kallon inda Baba ya ke, ai kuwa ya ga jijiyan Baba ya fara washewa daga baƙin, hayaƙin da ke tashin ma ya kwanta, "no no bai kamata ya zama haka ba, komai ya ya tafi", ya faɗi cikin tashin hankali. A tsorace ya juyo inda Amna ta ke, sai da ya yi baya ya kusa faɗi ganin ta riga da ta iso gabansa, ya kuma cewa "à ah, Am Amna kar ki min komai, kada ki taɓa ni" ya faɗi cike da tsoro yana girgiza kai, "ba Amna zaka ce ba!! Amna da Safna nee!!" Sai da Dady ya sake razana da muryar da ya ji Amna ta fitar yanzu. Naushi Amna ta fara bashi kota ina, jina jina ta yi da jikinsa da kuma fiskarsa, ihun da ya ke fitarwa ma yanzu ya kasa fitar da su, zuwa ta yi ta ɗauki wannan allurar ta nufo sa da shi. Duk da a galabaice ya ke amma bai hana shi sakin wani ƙarar da ƙyar ba, saboda ganin ta nufo shi da allura, wanda kuma idan har ta yi masa to ta sake ƙare masa, sai ya ɗan-ɗani azabobi bila adadin kafin ya bar duniya, "kar kiyi min allura, ki yafe min" maganar da Dady ya samu damar fitarwa da ƙyar kenan. Amma ina Amna ko sauraronsa bata yi ba, sai ma ɗaga shi da ta yi. "Kar ki kashe shi!" uncle Musa da ya shigo da folisawa ya faɗi hakan. Sai dai shima kamar Amna bata ji maganar shi ba, domin kuwa har ta riga da ta sokawa Dady allurar, abin da ya rage kawai shine ta matsa ruwan. Da gudu uncle Musa da police su ka iso inda Amna ta ke, "Amna no kar ki kashe shi, ki bari hukuma ta hukunta shi, tabbas ya aikata laifuka da yawa, amma bai kamata ya mutu a hannunki ba, kiyi haƙuri ki rabu da shi" Amna da ta ɗaga ido tana kallon uncle Musa sanda ya ke magana, da wa'yan nan garwashin idanuwan nan na ta, amma kamar bata fahimci maganarsa ba. Ta juya kan Dady da ke fitar da nishin tsananin azaba, domin saboda yadda ta yi masa lilis da jiki, hakan yasa ko motsin ƙwace allura ma baya yi, sai jiran ɓullowar wani azabar kawai ya ke yi, domin matsafi ya gama tabbatar masa, idan har aka yiwa wani wannan allurar ba Baba ba, to fa ba za a samu abin da ake so ba, sannan shi wanda aka yi wa allurar, sinadarin zai yi masa masifaffen illoli a jiki, bayan azaban da yasha daga baya kuma zai mutu. Hannu Amna ta sa a sama gurin matsawa, duk magiyan da uncle Musa da kuma sauran 'yan sandan suke yi amma bai sa ta fasa abin da ta yi niyya ba, "Amna!" Wata murya ta kira, da sauri Amna ta juya tana kallon Baba tsoho da shine ya kira ta, sai da Baba tsoho ya iso inda Amna ta ke ka na ya ce, "ki rabu da shi 'yata, hukuma ta yi aiki a kansa" ba musu Amna ta zare allurar da ke hannun Dady, wanda hakan ya sanya Dady ya samu damar sakin numfashi. Tana cirewa ta miƙe daga tsugunnen da ta ke, tana kallon Baba tsoho, a hankali tartsatsin wutan ya fara tafiya, daga bisani wutan kalar garwashin ma ya tafi àsalin kalar ƙwayar idonta ya bayyana, yana bayyana kuma ta zube ta faɗi yaraf sumammiya. Da uncle Musa ya tsorata da abin da ya faru da su Amna, ganin dukkansu babu mai motsi à cikin su, amma sai Baba tsoho ya ce da shi kada ya damu, ba wani abu ba ne, ita Amna da Safna wani abun ne ya sanya su yin hakan kuma zai sanar da su daga baya, Shuraim kuma azabar da yasha n'a duka, shi kuma Yazeed wannan abin da mahaifinsa ya sanya masa ne, sannan Baba kuma kasancewar allurar sinadarin da àka yi masa ne, duk da kaɗan ne ya shiga jikinsa, ka na ya haɗa da alluran da aka sha yi masa a baya, don haka ya yi gaggawar kaisu asibiti dukkansu, matsalar Baba da kuma Yazeed zai san abin da zai yi daga baya. Babu ɓata lokaci kamar yadda Baba tsoho ya faɗi, uncle Musa suka kwashi su Amna zuwa hospital. Wasu police suka tsaya sannan aka kuma kawo wasu motacin aka kwashi Dady da muƙarrabansa suma zuwa asibiti. AMMU. Zaune ta ke ta yi tagumi idanuwanta duk sun kumbura da kukan da tasha, har jin zazzaɓi take a jikinta, kasancewar tashin hankalin da ta shiga ya haɗe mata da yanayin jiknta. Ana haka Baba Hambali ya shigo da sauri bayan ya yi sallama tare da isowa ciki, itama Ammu da hanzari ta miƙe tana kallonsa, "ka... ka same Shuraim ɗin à waya ne?" Ta yi masa

Chapter 49 of 56