yafe mata sannan su ka ɗaura da Allah ya ji ƙan Saleem da Ruki, domin suma karankansu sun ji mutuwar kuma har yanzu kan alhininta su ke.
Mai-daraja sai da ya sa ke godewa Baba bayan godiyan da ya sha yi masa a baya, domin Baba ya yi masa komai a rayuwa, sannan ya kuma ɗorawa da godewa su Ummee. Baba ne ya numfasa sannan ya ce, "Babu abin da zamu ƙara yi sai sa ke godewa Rabbil alamin, domin dama duk abin da ya faru shi ya tsara mana, kuma ya ba mu nasara. Bayan haka, dama tun-tuni ya kamata mu koma inda mu ka fito, amma sai kuka hana mu ku ka ce mu bari sai an kammala komai, to ni ina ganin yanzu dai komai ya bayyana, don haka idan Allah ya yi mun kasance cikin aminci zuwa gobe lafiya, ina mai shaida muku cewa zamu kama hanyar komawa insha Allah".
Zuciyar Amna ne ya bada sautin rashin jin daɗi ta samu ta ce, "tafiya kuma Baba?" ta faɗi tare da tashi ta koma tsakiyar Ammu da Mamma, tana kallonsu kallon shagwaɓa, murmushi su ka yi mata Baba ya ce, "ƙwarai zakanyar Babanta tafiya fa, insha Allah gobe zamu koma" sannan ya juya yana kallon su Ammu da Mai-daraja da kuma su Shuraim gaba ɗaya ya kuma cewa, "mun gode sosai da kulawanku à garemu, kuma muna yi muku fatan alkhairi gaba ɗaya, idan Allah ya bada iko zamu rinƙa ziyartar juna, saboda à yanzu mun zama 'yan uwa".
Mai-daraja ya saki murmushi ka na ya ce, "ina za ku je? Ai muna tare da ku insha Allah, kamar yadda ka ce mun zama 'yan uwa, to kuwa babu wani buƙatar komawarku garin Gombe, nan da lokaci kaɗan za'a fara gudanar da aiki a gida na kusa damu ɗin nan guda biyu, za'a rushe du ai gini mai ƙayatarwa, ana kammalawa ya zama na ku, don haka muna nan da ku da yardar Allah" cikin farinciki su ke godewaMai-daraja, inda ya ce ai duk abun da zai musu ba zai biyasu abun da s ka yi masa ba, daga ƙarshe su ka yi godiya cike da farin ciki.
RANAR KAMMALA SHARI'A.
Kafin lokacin Shari'a.
Dady ne zaune a ƙasa, ƙafarshi ɗaya à miƙe ɗaya kuma à tankwashe, ya canza gaba ɗaya daga suffanshi, saboda yadda ya ke kamar ba ya cikin hankalinsa, tun da aka sanar da shi da rasuwar yaransa ya zama kamar wani zautacche. Amna da Safna ne tsaye à gabansa, "duk tuggun da kasha aikata mana, sai ga shi komai ya juye a kanka, shin ko hakan bai isheka izina ba?" Cewar Amna taré da juyawa ta ba shi baya haɗi da ɗaurawa da cewa.
"Har yanzu, har yanzu kana da wata damar Jamilu, damar neman yafiya ga wa'yan da ka yi wa laifi, ka ne mi yafiya ko da ace zaka samu sassauci ga ubangijinka". A hankali Dady ya miƙe kamar zai faɗi, "ina cike da raɗaɗi sosai cikin raina, bayan gaba ɗaya taka tsantsan ɗin da na ke, da kuma tsare 'ya'yana da gudun faɗuwa wata matsala, sai ga shi yau sun mutu, Saleem da autana sun bar duniya, duk faɗi tashin da na sha yi ya tafi a banza! Komai ya lalace" faɗin Dady haɗi da ɗaura kansa jikin gini ya sunkuyar.
Kallonsa Amna da Safna su ke yi, sai kuma wani police ya iso ya sanar da su su fito maganar ya isa haka, yanzu za a zo a fita da Dadyn zuwa kotu., hakan yasa su ka juya don barin wurin. Dady ne ya sanya hannunsa cikin aljihun wandonsa ya fito da wani abu mai tsini da za mu iya kiranshi da kibiya, ɗaga shi ya yi yana kallo yayin da hawaye ke gangara a fiskarshi. Tun jiya wani ɗan aikinsa ya kawo masa kibiyan, akan shine kaɗai abin da ya rage masa daga cikin kayan tsafin kogo.
Ɗaga kai ya yi tare da juyawa yana kallon Amna da Safna da ke ƙoƙarin fita, "ba zan taɓa neman yafiya akanku ba, kuma na yarda da duk hukuncin da za a aikata min yanzu, amma dole sai na kashe ku dukanku biyu, don in biya diyyan 'ya'yana da su ka mutu!" Cewar Dady a zuciyarsa ɓacin rai mai tsanani na bayyana a fiskarsa, da gudu ya yi kan su da kibiyan nan gefen Amna, domin ya fi tsananta fiye da ma Safnan. Kamar ance da Safna ta juyo da kanta ta zaro ido, saboda ganin Dady na yo wa kan Amna da wani baƙin kibiya da ke hannunsa, hakan ya tabbatar mata da cewa cutar da Amna zai yi, don haka isowansa dap Amna kafin ya kai kibiyar jikin Amna.
Safna ta yi saurin shan gabansa ta hanyar zuwa bayan Amna, sakin gigitacchen ƙara ta yi tare da jan numfashi. Amna da ba ta fahimci abin da ya ke faruwa ba, jin ihun Safna ya sanya ta ta yi saurin juyowa tare da zare idanu. "Yar uwataaaa!!" Ta ambata cikin tsananin tashin hankali.
Last part.
___________________________________________________
Hmm to ko ya zata ƙarke? Mu kasance da ku a kashi na gaba.
*_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_*
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣7️⃣5️⃣▶️1️⃣7️⃣6️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar
_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_
Safna ta yi saurin shan gabansa ta hanyar zuwa bayan Amna, sakin gigitacchen ƙara ta yi tare da jan numfashi. Amna da ba ta fahimci abin da ya ke faruwa ba, jin ihun Safna ya sanya ta ta yi saurin juyowa tare da zare idanu. "Yar uwataaaa!!" Ta ambata cikin tsananin tashin hankali.
A hankali ta fara sauko da idonta ƙasa gurin cikin Safna, gani ta yi Safna ta riƙe hannun Dady fiskarta ya nuna alamar gaba ɗaya ƙarfinta ta ke sawa, don dakatar da shigar kibiyar nan cikinta kamar yadda burin Dady kenan, saboda shima gaba ɗaya ƙarfinsa ya ke sawa yana tura kibiyar don ya soka mata.
Cikin tashin hankali Amna ta sanya hannunta don matsar da hannun Dady, nan su ka fara kokuwa su ukun, Dady ya buɗe baki cikin fitar numfashi yana cewa, "dole yau za ku bi su Saleem, saboda ku ne ku ka sanya hakan ya faru da su, da ba ku sa an kamani ba, da na ba su kulawa ta yadda hakan ba zai faru ba, ku ne sila!" Safna ta samu damar yin magana, "kana cigaba da aikata kuskure, da na ɗauka zaka ga ne kurenka, ashe zuciyarka ta riga da ta bushe, zunubinka ne ya koma kan 'ya'yanka Dady".
Amna ta katse Safna, "ki daina ce masa Dady, domin ko kusa bai cancanci hakan ba. Jamilu ka ji ɗaci saboda ka rasa 'ya'yanka, amma su wa'yan da ka yi sanadiyyar tarwatsewar rayuwansu cikin farin ciki ka ke son su shiga?!" Amna ta ƙarashe faɗi bayan ya dawo daga ita sai Dady su ke kokuwa, "Amna ki bi, ki bi à hankali, Dady don Allah ka daina, ƙoƙarin sokawa 'yar uwata, ka daina" Safna ta faɗi domin bakinta ya kasa daina kiran sunan Dady, abun ka da sabo.
Amna kuwa da ba don tana gudun kada wannan kibiyar ta zamo da hatsari ba, da tuni ta fizge shi, amma ta na gudun kada garin fizgewa ta yi garaje wani abun ya faru, sabida yadda Dady ya dage don ya soka mata ya tabbatar mata da abun mai matuƙar hatsari ne. Samu damar buge hannun Amna Dady ya yi da ƙarfi hakan yasa ta yi baya, ƙafin ta ɗago ya tura hannunsa da ƙarfi. Itama Amna à yanzu ƙara ta saki, cikin gigicewa, Safna ta ambaci sunan Amna da ƙarfi tare da yin baya ƙirjinta na bugawa.
Saura kaɗan kibiyar Dady ya taɓa jikin Amna Yazeed da ya shigo lokacin da Dady ya ture Amna ya yi tsallen zaki tare da riƙe hannun mahaifinsa, Dady da ya yi zaton Safna ce ta riƙe masa hannu ya sa ya juyo da ƙarfi, Yazeed kuma ya yi saurin turashi gefe. turesan da Yazeed ya yi ne ya sanya shi tafiya da ƙarfi gun gini tare da buguwa, ya saki wani gigitacchen ƙara, wanda wannan ƙarar ne ya sanya Amna da Safna da su ka rintse ido jikinsu na faman rawa su ka buɗe.
Yazeed zaro ido sosai ya yi yana kallon mahaifin na sa cikin tashin hankali. Amna jikinta ta fara kallo, Safna ma tana dubanta saboda ta ga babu abin da ya samu Amnan, ka na su ka yi saurin kai dubansu kan Yazeed da ba su san yaushe ya zo ba, a tare su ka kai dubansu kan Dadyn daidai juyowarsa kibiyar nan soke a setin ƙirjinsa, ashe bayan Yazeed ya hankaɗa shi hannunsa da ke riƙe da kibiyar ya lanƙwashe, hakan yasa kibiyar ya soku a ƙirjinsa, ya soke kansa da kansa kenan. "Dadyyy!!" Cewar Yazeed cikin tashin hankali yana miƙa hannu gun Dadyn.
"Dadyy!" Safna ta faɗi tare da dafe ƙirji, "Jamiluu!" Amna kuma ta faɗi idonta à zare. Yayin da shi kuma Dady ba abun da ya ke, sai zare idonsa da jijiyoyinsu su ka fito raɗo-raɗo yana jin wani irin yanayin azaba na shigarsa. Da gudu Yazeed ya yi kan Dadynsa tun kafin ya faɗi ya yi ƙasa da shi, su Amna da Safna ma da gudu su ka ƙaraso haɗi da tsugunnawa, numfashi Dady ya ke fitarwa da ƙyar tare da rintse ido saboda tsabar masifaffen raɗaɗin da ya ke ji na ratsa jininsa. Lokacin folisawan da ke wurin su ka ƙaraso suna ganin abin da ya ke faruwa.
"Dady dady, buɗe idonka, ka buɗe ido Dady" faɗin Yazeed yana girgiza Dady idonsa na hawaye, duk da abun da Dadyn ya aikata, amma yanzu sai ya ke jin wani irin yanayi a jikinsa da abun da ya samu Dadyn. Dama uba ai ba wasa ba. Dady da ƙyar ya samu ya buɗe idonsa da ya fara canzawa sannan buɗe baki ya ce, "ɗana Yazeed, my favourite son, ni ni mutuwa zan yi, domin ta wa ta riga da ta ƙare, tun da har wannan baƙar kibiyar ya shiga jikina, tabbas komai ya dawo kaina, duk sanda zan aikata musu abu sai ya dawo kaina, na, na gane babu wanda ya isa, ya aikatawa ɗan adam abin da ubangiji bai amince ba, duk abun da na aikata, sai ga shi ƙarshena zai zama mai matuƙar muni, ku ku yafe min, don Allah ku yafe min, saboda ni ma yanzu zan tafi, inda su Saleem su ka tafi" faɗin Dady murya ciki-ciki yana fitar da numfashinsa kamar zai ɗauke
Sai yanzu ya ke jin da ya sani, duk da yana ganin lokaci ya riga da ya ƙure masa, shi ya kasance mai baƙar zuciya, bai damu da ya kowa ya ke ba, shi dai kawai ya aikata abun da ya ke so don cikar muradinsa. Tsawon shekaru da ya shafe yana tara munanan zunubai, sai ga shi Allah ya kawo ƙarshensa a ɗan lokaci ƙalilan.
Yazeed ya share hawaye sannan ya ce, "no Dad babu abin da zai faru da kai, yanzu zan kai ka asibiti" ya faɗi yana ƙoƙarin ɗaga Dady, Amna da Safna sai binsu da kallon tausayawa su ke yi, suma suna jin yanayin rashin daɗin abin da ya faru yanzu, Safna kam tuni hawaye ya wanke mata ido itama, kafin Yazeed ya ɗaga Dady, ya ji Dadyn ya kuma sakin numfashin wahala yana cewa, "à ah kar ka wahalar da kanka, ka manta maganar da ka yi ranar? cewa ka yi, Dady dole ka amshi abun da ka.. ka shuka da hannu bibbiyu" girgiza masa Yazeed ya kuma yi yana ta ruwan hawaye.
Dady kuwa ta ke ya fara tari jini na fitowa daga bakinsa kamar fanfo, a haka ya yi ƙarfin yin murmushi ya sake yunƙurin cewa, "ka..ka yi gaskiya my son, maganarka ya tabbata, yan..zu lokaci ne da zan amshi sakamakona, ko...ina so ko...Ba na so" sa kuka Yazeed ya kuma yi hankalinsa na ƙara tashi, ganin yadda jini ke ta amayowa daga bakin Dady, sannan kuma jikinsa ya fara yin wani iri kamai mai saɓan maciji.
Miƙewa Safna su ka yi zuciyarsu cike da tsoro kan abin da ya ke sake faruwa, cikin 'yan sandan da ke wurin su ka fara ɗaga Yazeed daga jikin Dady, tashi ya yi yana ta kiran sunan Dady hawaye na cigaba da wanzuwar masa.
Dady kuwa sai da ya yi wani irin ƙara mai ban tsoro, sannan ya fara juyi da ƙarfi yana girgiza daga baya numfashinsa ya tsaya cak, launin baƙi ya kewaye gaba ɗaya jikinsa, sai kuma yana tsotsewa, bayan mintuna da bai gaza uku ba, Dady ya dawo ƙwarangwal baƙi ƙirin. Gaba ɗaya naman jikinsa ya zagwanye ya dawo kamar baƙin gari. Sai da su Amna su ka yi baya tare da rintse idon mummunan abun da su ka gani, Yazeed kuwa sakin jiki ya yi ya yi ƙasa tare da ijje guiwoyin na sa a ƙasa, yana kallon yadda mahaifinsa ya dawo. Sauran 'yan sanda kuwa babu abun da su ke sai mamaki.
Da hanzari Safna ta zo gurin Yazeed itama ta durƙusa idonta da ƙwallah, kafin ta yi magana Yazeed ya dubeta ya ce, "Safna na kashe Dady, ni na kashe shi da hannuna, ya aka yi na kashe shi? Du dubi yadda ya koma" Ya faɗi tare da fashewa da kuka, girgiza kai Safna ta shiga yi masa tana sanar da shi ya daina faɗin haka, ba shi ya kashe Dady ba.....
KOTU.
Da fari lauyan Dady ya fara ta da magana akan kashe Dady da aka yi, amma sai ya gimtse bakinsa ko da aka gabatar da videon abun da ya faru, domin da ma an sanya cameran sa ido akan Dadyn. Anji kuma anga duk abin da ya faru tsakanin Dady da kuma su Amna, anji cewa su Amna zuwa su ka yi don su faɗakar da shi ya yi da ya sani akan abin da ya aikata sannan kuma ya nemi yafiya, amma daga ƙarshe ya so kashe su Allah ya kare.
Haka dai aka gabatar da sauran manyan mutanen da bakinsu ya ke haɗe da Dady, inda al'umma su ka yi ta mamaki kasancewar su manyan mutane, nan aka yankewa ko wannensu hukuncin da ya yi dadidai da abin da su ka aikata, daga ƙarshe zaman kotu ya ƙare.
Kowani mutumin da ya halarci kotun sai da ya tsorata kuma ya ɗau izina game da wannan shari'a, saboda sun ga cewa mutum ya ji tsoroon Allah, sannan ya gane cewa a duk lokacin da Allahu subhanahu wata'ala ya mallakawa bawansa wani abu to ya yi masa fatan alkhairi kawai, da kuma yi wa kansa addu'a akan Allah ya azurtashi shima, ya kuma ba shi ta hanyar halal, ba wai ya kasance mai hassada ga ɗan uwansa ba, domin shi hassada a hankali ya ke yin girma sannan ya haddasa tsana fiye da ƙima, misali akan Jamilu, da kaɗan kaɗan ya fara sanya hassada azuciyarsa kan Mai-daraja, daga baya kuma sai ya girmama ya dawo babu abin da ya ke so face ganin bayan Mai-daraja wansa, da kuma tarwatsa iyalinsa, ya mayar da zuciyarsa ta zama mummuna, ya aikata abubuwa bila adadin, kisan kai lalata rayuwar matasa, da dai sauran kurakuran, ga shi yanzu Allah ya kawo ƙarshensa lokacin da bai zata ba kuma bai tsammata ba, to ya zai ƙare da haƙƙin mutane?.
_to abu na ƙarshe sai dai mu ce. Ya Allah ka kiyashemu taɓewa, ya Allah ka tsare zuciyarmu da yin hassada, ya Allahu ka tsarkake mana zuciyarmu ka nufe mu da aikata alkhairi, ya Allah ka rabamu da aikata sharri, ya Allah ka tsare mu da yin ta'amali da miyagun ƙwayoyin, da kuma sauran kayan maye, masu aikatawa ya Allah ka ganar da su, ka kuma ba su damar gyarawa, Ameen_
_mutuwa ba ta zuwar mana a lokacin da mu ka tsammata, yau sai ka ga mutum yana hidimarsa zuwa anjima ka ji ya rasu, yau sai ka ga mutum ya kama hanya kawai kuma ka ji an sanar da kai ya yi hatsari, yau mu ji can an mutu gobe can, watarana kuma utuwarkmu za a sanar, 'yan uwana mu dage da aikata alkhairi domin kuwa duniya babu tabbas, Allah ya datar da mu Ameen_
Yazeed ne zaune a garden kansa na sama kamar ya faɗa duniyar tunani. Safna ce ta tsaya daga nesa tana kallonsa, sosai yadda ya ke yi ya ke damunta, barin tsayuwar ta yi tare da zama gefensa da nisa tana nazarinsa ka na daga baya ta buɗe ba ki cikin sanyin muryarta ta ce, "yaya Yazeed" da sauri ya farga daga duniyar da ya ke ya juyo yana dubanta, murmushi ta sakar masa tana shirin yin magana sai ya miƙe da cewa, "excuse me" ya faɗi yana shirin barin wurin.
Da hanzari ta miƙe, "please Yaya Yazeed kar ka tafi" ta faɗi cike da damuwa, yadda ta yi maganar sigar magiya ne ya sanya shi tsayawa, Safna kuma ta taka zuwa gabansa tana dubansa ta ce, "yaya Yazeed, me yasa ka ke min haka? Na lura tun da abin nan ya faru, ko na zo wuri sai ka tashi ka rabu da ni, ba ma ni kaɗai ba, gani na ke kamar yanzu, ba ka son shiga cikin family, ko mun aikata maka wani laifi ne? Don Allah tell me yayana, saboda abun da ka ke yi yana sani cikin damuwa sosai".
"Babu abin da ki ka min, kawai dai kunyar haɗa ido da ku na ke yi, saboda Dady ya aikata muku abubuwa da dama, sannan kuma mahaifiyata ma, ki yi haƙur..." kafin ya ƙarasa Safna ta yi saurin girgiza kai da cewa, "don Allah" hakan yasa Yazeed ya tsaya yana kallonta idonsa cikin marairaicewa, Safna ta ce, "ta ya zaka sa wannan tunanin a ranka yayana? Kar ka manta, kai ne wanda ya bani kulawa, à duk lokacin da na shiga wata matsala, ba ka jurar ganin an muzanta ni, to kuwa idan akwai wanda, ya kamata ya bada haƙuri akan abubuwan nan, to ni ce, ka yi haƙuri, amma don Allah ka da ka ƙara yin burus da ni, inba haka ba..."
"Inba haka ba me?" Yazeed ya yi mata tambayar ganin bata ƙarasa maganar ba kuma ta yi ƙasa da kai, "zuciyata za ta buga" Safna na faɗi ta juya da sauri ta bar shi tsaye, murmushi ya yi don ya lura kunya ta ji.
Amna da Shuraim ne cikin mota suna dawowa gida, Amna ta ce, "gobe Abby ya ce zai je company da kuma shirya wasu ayyukan, ka san me?" Shuraim ya ce, "ta ya zan sani? Bayan tun ɗazu kin hana ni yin magana, bayan kuma ina da abu mai mahimmacin da na ke son sanar miki, amma kin saki baki sai zuba ki ke min, numfashi ma da ƙyar na ke samun damar fitarwa, ni na rasa ina ki ka samo wannan surutun, ko siya ki ka yi?".
Ya faɗi yana juyowa kallon Amna, ita kuwa da ta riga da ta buɗe baki saboda abubuwan da ya ce mata, cikin ɓacin rai ta ce, "hhhhmm lallai malamin nan to wallahi ka ki ya ye ni ba fa canzawa na yi ba, akan me zaka faɗa min maganganu haka? To da kai da ka ke cewa na hana ka yin magana wace magana na hanaka yi? kame bakinka na yi na ɗaure ne ko kuwa me kake son cewa? Ni ban hana ka yin magana ba duk lokacin da ka ke so kawai ka yi maganarka, ni ba zan ma sa ke yin magana da kai ba da ga yau, kai daga yanzu ma, akan me ka dakatar da motar?" Amna ta ƙarashe maganar tana kallon Shuraim da ya tsaida mota.
Shi kuwa Shuraim da ba komai ba ne ya sanya shi yin hakan, sai yadda Amna ta ke ta zuba zance cikin ɓacin rai ko numfasawa ba ta yi da ta ke maganar, kallonta ya yi ya ce, "magana magana magana, to ba za ki iya tambayata insqanar da ke abun da na ke son faɗa miki ba?" "Ba na so ka riƙe abin da zaka ce, ni ai dama na ce maka ba zan sake magana da kai ba!" Amna na faɗi ta juya tare da naɗe hannunta tana kallon gaban mota ita nan ta yi fushi.
"Ko ma dai me sai na faɗa" cewar Shuraim, "ka riƙe kayanka na ce ba na son ji" "dole ki ji kuma ki saurare ni" "a ah ba na son ji" "ƙwarai dole ki ji abin da zan ce i love you" "na ce maka ba na son..." sai kuma Amna ta ƙasa ƙarasawa domin ji kalmar i love you da ya ambata, Shuraim yana kallonta da murmushi ya kuma cewa, "yes dama na daɗe da faɗin haka, kuma yanzu ina mai ƙara nanatawa, your my life".
Amna ta kasa magana sai kallonsa da ta ke yi, "ina son gabatar miki da wani tambaya, can i?" Ɗaga masa kai kawai Amna ta yi shi kuma ya ce, "ina son tambayarki, shin Amna 'yar Abubakar Mai-daraja, da kuma Hussaini Baba, shin zaki yarda ki kuma amince da ni? Zaki auri MR Shuraim Abdurrazak?" Saurin kawar da kai Amna ta yi tana jin yanayin ƙauna a zuciyarta, zuciyarta na motsawa, lumshe ido ta yi sannan ta ce, "zamu iya tafiya? ya kamata ace mun isan gida" "to me zai sa ba za a bani amsa ta ba? Ina ce yanzu babu wani maganar Yazeed?" Cewar Shuraim yana murmushi tare ta da motar su ka tafi.
Bayan sun isa gida, Amna ta buɗe ƙofar motar ta fice, Shuraim ya sauke numfashi haɗi da sunkuyar da kansa ƙasa, ya rufe ido cikin damuwa, me yasa Amna zata ƙi ba sa amsa, gashi har ta wuce ba ta ce da shi komai ba. Ƙwan-ƙwasa gilas ɗin motar da aka yi ne ya sanya shi buɗe ido ya juyo ba tare da ya ɗaga kansa sosai ba, sai kuma ya yi saurin ɗaga kan saboda ganin Amna da ya yi ita ce mai ƙwan-ƙwasawan, murmushi ta yi masa wanda ya ji shigarsa cikin ransa.
"Ka da ka yi tunanin wani abu ne na dawo sanar maka yallaɓai MR" kallonta kawai Shuraim ya ke bai ambaci komai ba, "to ka saurare ni, so na ke na sanar maka cewa, ina ƙaunarka da gaba ɗaya zuciyata nima, a yanzu ina shirye da in zama matarka" Amna na faɗi ta kuma sakin murmushi cikin shauƙi ta bar wurin, Shuraim kuwa ɗaga kansa ya yi sama tare da ɗaga hannu biyu yana godewa Allah.
BAYAN WANI LOKACI.
Amna ce ta taho gun Yazeed da ke zaune a falo, zuwa ta yi ta zauna kusa da shi, "my Amna ya dai? Ya na ga kamar kina cikin damuwa? Amma fa kwalliyar nan ya yi miki kyau" sake fiska daga damuwar ta yi sannan ta saki murmushi ta ce, "thank you yaya Yazeed, dama ni wata magana ce ta kawo ni wurinka" "ina jinki faɗi duk abin da ki ke so" faɗin Yazeed, "lokacin da ka dawo daga Australia, ka yi ta nuna min alamomin ƙauna wanda daga ƙarshe na amince da zan aureka".
"Eh haka ne, amma me ya ke faruwa yanzu?" Amna ta ce, "a gaskiya tun bayan nan ni dai ina sonka kuma zan aure ka" zunbur Yazeed ya miƙe yana kallonta ya ce, "my Amna what are you saying? Hhh wasa ki ke yi ko? Na sanki da son raha" "No yaya Yazeed I'm telling the truth" "hhh ba na son wannan wasan Amna, ke fa Shuraim ki ke so haka shima yana sonki" "Ni na taɓa faɗa maka ina son Shuraim? Ni kai na ke so, kuma na ke son aura". "Whattt!!"
Shuraim. Yana shirin shiga falo Safna ta tsaida shi, ƙarasowa ta yi ta ce, "yaya Shuraim barka dai, ashe ka dawo tun ɗazu na ke nemanka" murmushi ya yi mata ya ce,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 56