Ta ya ka kasance Mai-daraja?" Takowa Mai-daraja ya fara yi a hankali har zuwa gaban Alƙali sanan ya buɗi baki ya ce, "ƙwarai zan warware komai ranka ya daɗe" yana faɗi ya juya kan Dady haɗi da zuwa kusa da shi, Dady da ya gama bushewa da kallon Mai-daraja ya yi saurin matsawa baya a matuƙar razani.
"Kana lafiya Jamilu? Shekaru da yawa? Ni ɗin ne ba wani ba, ba ka taɓa mafarkin hakan zai faru ba ko?" Cewar Mai-daraja tare da sakin murmushi ya ƙara cewa, "bayan na gudu daga wurinku Allah ya tsare ni ban mutu ba".
TUNANIN BAYA.
_bayan Mai-daraja ya samu damar shiga mota ya bar wurin su Dady, zuciyarsa sai bugawa ya ke yi, babu abin da ya ke yi sai zubar da hawaye masu zafi da ciwo daga zuciya, ba tare da ya san Jamilu ya sanya masa bom cikin motar ba. Ya ci mintuna bakwai da barin wurinsu Dady, yayin da ya rage saura minti uku nakiyar ta tashi. Wani kare ne ya fito da gudu daga cikin dajin ya yo kan hanya. Ganin dabba da ya yi kwatsam ne ya sanya shi saurin taka birki saura kaɗan ya bi ta kan karen. Kare kuwa dama shima ya rikice, yana kallon motar ta tsaya ya saki kukansa sannan ya ruga gaba. Sauke numfashi Mai-daraja ya yi ganin bai buge karen ba. Kafin ya kuma murɗa key ya ga mutane guda uku sun tsaya a jikin motar, hannunsu riƙe da wuƙaƙe. Su ne su ka sako wannan karen don su samu abin da su ke so, zamu iya kiransu da manyan 'yan fashi, ɗaya daga cikinsu ya yi saurin buɗe motar tare da cewa Mai-daraja ya fito ko su illata shi, cikin wani tsoron ya fito domin shi ya yi tsammanin ko Jamiln ne ya turo mutanen. Yana fita su ka ture shi gefe tare da yi masa barazana da idan har ya matso za su farka masa ciki, shigewa cikin motar su ka yi su ka ta da shi, da gudu ya biyo motar yana binsu. Lokacin bom ya cika, don haka ya tashi booom tare da tarwatsewa, iskar bom ɗin ya bugi Mai-daraja haɗi da ɗaga shi sama ya cillar da shi a can cikin dajin. Yana faɗi ya suma. Ragowar motar kuwa sai ci da wuta ya ke yi sosai, ko à haka aka barka ba za ka gane gawawwakin mutane nawa ba ne_
Gaba ɗaya mutanen kotu su ka sa surutu da labarin da Mai-daraja ya bada, yayin da wa'ayn da su ke bayan Dady su ka fara zuru-zuru da idanu, Dady kuwa babu abin da ya ke yi sai yarfar da gumi ya ke yi kamar ana tsoma shi a ruwa.
Mai-daraja ya kuma cewa, "haƙiƙa Jamilu ka cutar da ni, cutuwa mara misaltuwa, Jamilu na riƙe ka da amana tun bayan rayuwar iyayenmu, na sadaukar da karatuna saboda kai, na inganta karatunka don kawai na ga cewa ka zama mutum na ƙwarai, sannan wanda zaka iya dogara da kanka, ko da yaushe burina in yaye maka damuwarka, ba na son ko ta ya ya ka kasance cikin matsala, Jamilu ko matata ban taɓa fin sonta akanka ba, takan tambaye ni abu ban yi mata da wuri ba, amma kai da ka nemi abu a wurina na ke hanzarin in yi maka shi. Amma ka rasa abin da zaka saka min da shi sai abubuwan da ka min? Ka rabani da 'yata sannan ka yi yunƙurin kashe ni Allah ya tseratar da ni, sannan daga baya ka nakasa min matata ka maida min 'ya kamar baiwa. Mamakin da ka bani Jamilu har sai da ya girmi ƙwaƙwalwata, na daɗe ina jinyar abin da ka yi min à cikin zuciyata".
Mai-daraja ya ƙarashe faɗi tare da dafe zuciyarsa yana hawayen ciwo sosai, Amna da Safna idanuwansu sai aikin tsiyaya ya ke, su Shuraim da ragowar mutane masu kallo da 'yan Jarida ma ƙwallah ya cika musu ido. Mai-daraja ya cigaba da cewa, "na yi niyyar mallaka maka wasu ɓangarori na dukiyata, sai dai yanayinka da rashin kula aiki ya sanya na ƙi ba ka hakan da wuri, bayan haihuwar Amna da Safna. Wata rana na ɗauko wata daɗaɗɗiyar wayata tare da kunnawa don duba wani abu a ciki, ina kunnawa saƙon abokina Abdurrazak ya shigo, na shiga mamaki sosai domin kuwa na san ya daɗe da rasuwa, amma sai na yi tunanin to ko wani ne ya yi amfani da wayar ta sa? da gaggawa na shiga cikin saƙon don karantawa, amma gani na yi lokacin da aka tura saƙon tun kafin ya rasu ne, da gaggawa na fara karanta saƙon, "abokina Mai-daraja akwai abin da na ke son faɗa maka, wani na kusa da kai yana shirin ganin bayanka, so ya ke ya kashe ka sannan ya gama da ahalinka, yana son ya ƙwace kadaranka daga hannunka, ya kamata kasan dabarar da zaka yi ƙafin lokaci ya ƙure maka, saboda yana bin kowace hanya don ganin ya cinma burinsa akanka, nima da fari ya nemi haɗin kaina kasancewata na kusa da kai, amma na ƙi amincewa da shi, duk da cewa ya yi min barazana amma bai sa na amince ba. Na san cewa ko da ace na sanar da kai waye ne wannan mutumin ba za ka taɓa yarda da ni ba, amma na san duk daran daɗewa zaka san ko waye, idan kuma ka tabbatar da cewa zaka tsaya ka saurare ni don in faɗa maka waye wannan mutumin, sannan za ka yi bincike kafin kasan cewa ƙarya na ke yi ko gaskiya, to ka yi min magana zan sanar da kai" wannan shine saƙon da ya rubuta min. Cikin kullewar kai na ke ta nanata wannan saƙon, gashi yanzu Abdurrazak ya rasu bare in nemi ƙarin bayani a wurinsa. Sai à lokacin na tuna akwai wani lokaci da ya tambayeni na ga saƙonsa? Na ce da shi ban gani ba wani saƙo ya turo? Sai ya ce min ya tura min à layin airtel ɗina, na sanar da shi ai layin ya daɗe ba na amfani da shi, ya faɗa min wani saƙo ne wannan? Amma ya ƙi sanar da ni ya ce in sa layin à waya in duba saƙon. To daga baya kuma na manta kwata-kwata ma da batun, ko sati bai ƙara ba ya yi hatsari. Na yi ta yin nazarin saƙon nan na sa amma ban fahimci komai ba, hakan yasa na yi gaggawan zuwa bada wasiƙar mallakar da dukiyana ga 'yata Safna, wani tunanin da na yi ne ya sanya ni bada cewa idan har Safna ta mutu kafin cikar wannan shekarun, to à bada sadakan dukiyar gaba ɗaya wurin mabuƙata, Bayan haka ba jimawa na gano gaskiyar cewa bako wa bane wannan mai son hallaka ni face Jamilu ƙanina".
Duk mutanen wurin mamakin abun da ya faru su ka yi. A halin yanzu Dady saura kiris ƙafafuwansa su gaza ɗaukar jikinsa, saboda yadda ko wani gaɓa na jikinsa ke amsar tsananin tsoro, wai ace Mai-daraja bai mutu ba, duk shirin da ya aikata ya tabbatar yau ne zai ƙare. kafin Alƙali ya yi magana Mai-daraja ya dubesa ya ce, "ranka ya daɗe duk abun da aka sanar na zargin da ake yi masa gaskiya ne. Tura mutane ya yi su ka tsare ahalina, sannan su ka yiwa Amna barazana cewa zasu kashe su idan ba ta janye ƙarar ba, wannan shine dalilin da yasa Amna ta juya zancen." Mai-daraja ya ƙarashe maganar idonsa kan Amna, yayin da itama ta ke kallonsa idanuwanta bai tsaya daga fitar ruwan ba.
Sai à lokacin su Safna su ka gane abin da yasa Amnan ta canza zancen, "an kama mutanen yanzu haka, ba ma su kaɗai ba akwai mutanen da ya sa su ka tsare ma'aikatan Shuraim suma duk ankamasu, ranka ya daɗe ga wasu takardu da bayanan sauran mutanen da Jamilu ya ke aiki dasu, komai da komai yana ciki" faɗin Mai-daraja tare da miƙawa Alƙali wasu takardu.
Ba ƙaramin tashi hankalin su Hajiya ya yi ba da abun da ya faru, yanzu kenan gaskiya ta nuna Dady duk shine ya aikata abubuwan nan? Sannan ga Mai-daraja ya dawo shima bai mutu ba? Alƙali ne ya fara bayani bayan kammalan shaidu da kuma shaidar gani da ido, Alƙali ya umurci da nan da sati ɗaya à gurfanar da sauran masu laifi wato manyan da su ke aiki tare da Zabba-ba, bayan an gurfanar da su za a yanke hukunci à ranar, yana faɗi ya buga wannan gudumar katakon a kan table.
Ruki da ke tsaye ne ta fara jin jiri na ɗibanta, Hajiya da ta kai idonta kan Rukin ta zaro ido tare da sakin ihu tana riƙe Ruki ta furta, "Ruki 'yata me ya ke faruwa da ke?" Ta faɗi domin ganin yadda jini ke ta zubowa ta hancin Ruki har yana ɓata mata kaya.
Hankalin mutane gaba ɗaya ya koma kan su Hajiya kowa sai zaro ido ya ke. Ai kuwa kamar mai jira Saleem ma ya amshe jini na fito masa ta hanci ta baki, gaba ɗaya mutane sun ruɗe da abin da ke faruwa musamman Dady, cikin tashin hankali ya ke son isowa gun 'ya'yansa don ya ga me ke damunsu? ka da dai ace ƙwayar Pospa su ka sha, domin kuwa haka ya ke yi idan ya shiga cikin Jini kamar yadda su ka ƙirƙireshi, to a ina su Ruki su ka samu wannan ƙwayar?
Last part.
___________________________________________________
🤯ya ku ka ji wannan part ɗin? Mai-daraja bai mutu ba, lallai! Kun ji abin da yasa Mai-daraja ya mallakawa Safna dukiya tun kafin a ce ya mutu, ko à ina ya zauna tsawon lokacin nan?
Sannan ga su Ruki suna fitar da jini, shin kuma kuna ganin anya ba ƙwayar su ka sha ba kuwa? Hmm Dady dai shi tuntuninsa yana ganin ya yi dabara, da baya sayar da ƙwayoyinsa a garin Kaduna, saboda ka da yaransa su yi ta'amali da su, bai san cewa ba a wa Allah wayo ba.
Ko ya zata ƙarke? Mu kasance a next part don je amsoshin
*_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_*
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣7️⃣3️⃣▶️1️⃣7️⃣4️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar
_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_
Hankalin mutane gaba ɗaya ya koma kan su Hajiya kowa sai zaro ido ya ke. Ai kuwa kamar mai jira Saleem ma ya amshe jini na fito masa ta hanci ta baki, gaba ɗaya mutane sun ruɗe da abin da ke faruwa musamman Dady, cikin tashin hankali ya ke son isowa gun 'ya'yansa don ya ga me ke damunsu? ka da dai ace ƙwayar Pospa su ka sha, domin kuwa haka ya ke yi idan ya shiga cikin Jini kamar yadda su ka ƙirƙireshi, to a ina su Ruki su ka samu wannan ƙwayar?.
Amna da ta isa kan Ruki ce cikin tashin hankali ta ce, "wannan fa kamar cutar wannan ƙwayar ce, ƙwayar Pospa" gaba ɗaya sauran su ka zare ido cikin tsananin tsoro, musamman ma Hajiya, "nooo ba shi ba ne, babu abin da zai samu 'ya'yanna, ku matsamin, ku sake ni Autana, Saleem!" Cewar Dady da ƙarfi yana shirin zuwa inda su ke, amma police sai rirriƙe su su ke" Mai-daraja ne ya ce ayi gaggawan kai su asibiti tun kafin ya yi tsanani.
Yana faɗi Amna ta saɓi Ruki haka Saleem ma Shuraim ya ɗauke shi suna ficewa daga cikin kotun, Dady sai kuka ya ke yi da iya ƙarfinsa, kamar ma ya fi ita da kanta Hajiya shiga tashin hankali. Babu abin da ya ke tashi sai surutun mutane, 'yan Jarida sai naɗan komai su ke yi suna yaɗawa. A haka àka shigar da su Ruki mota aka ja zuwa asibiti.
HOSPITAL.
Bayan likitoci sun shige da su Saleem cikin ɗakin bada kulawa, kuka kawai Hajiya ke yi su Safna na tausanta, sauran kuwa duk suna tsaye cikin damuwa.
Juyowa Amna ta yi tana duban Mai-daraja ba tare da ta ce komai ba, idonsa ya kai kanta hakan yasa ya sakar mata murmushi tare da zuwa inda ta ke, ƙwallah ne ya cika mata ido ba tare da ta ɗauke idonta da ga gareshi ba.
''Yata" ya ambata da sanyin murya cikin tsananin soyayyar mahaifi, hakan yasa Amna sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idonta da sauri da sauri, juyowa sauran su ka yi hankalinsu kan Amna da mahaifinta Mai-daraja, Hajiya ma da ke kuka ta dakata tana kallonsu, Safna ma zuwa inda su ke ta yi tana kallon mahaifin na ta, "Abbyy!" Ta ambata tana hawaye, juyowa ya yi yana kallonta ya yin da shima idonsa ya cika da ƙwallah, Safna ta kama hannun Amna, Amna ta ɗago tana duban Safna.
Sannan su ka maida kallonsu duka zuwa ga Mai-daraja, "Amna Abbynmu bai mutu ba, shima ya dawo, ga shi muna ganinsa da idanuwanmu ba à hoto ba, maraicinmu ya fita yau duka" Safna na faɗi suka fashe da kuka ita da Amna, Mai-daraja ya rungume su yana hawaye. Ammu da su Baba da su ka iso ne su ka yi turus suna kallonsu, musamman ma Ammu domin jikinta har rawa ya shiga yi.
Amna ce ta fara ganin Ammu hakan yasa ta ambaci sunanta, ɗaga kai Mai-daraja ya yi tare da juyawa don ya ga Ammun da Amna ta ambata, kallonta ya ke sosai yana jin bugun zuciyarsa na cigaba da aiki, yayin da Ammu ma babu abin da ya ke fitowa daga idonta face hawaye ɗaya na bin ɗaya. Ta kasa motsi daga inda ta ke sai riƙe numfashinta ta ke yi.
Mai-daraja ne ya fara takowa zuwa inda ta ke, ba tare da ya ambaci komai ba, Ammu ta yi saurin rungume shi da fashewa da kuka, ba tare da ta san yaushe ta yi hakan ba, gaba ɗaya sauran cikin tausayawa da shauƙi su ke bin su da kallo, domin kuwa sun san abun da dukansu su ke ji daga ransu, Amna da Safna kuma su ka ƙaraso gabansu suna hawayen farin ciki, kama su Amna Mai-daraja ya yi ya ringume su su uku da matarsa da kuma 'ya'yan na sa.
Hajiya kuwa kauda kai gefe ta yi ta na cigaba da hawaye, Yazeed da Marwan ma ƙwallan su ke fitarwa saboda ba suma san me ya ke yi musu daɗi ba, ace ƙannensu biyu duka ba lafiya?. Saurin miƙewa Hajiya ta yi cike da tashin hankali ko da ta ga fitowan doctor, "dakta ya yaran nawa? Babu abin da ya same su? Sun warke?" Hajiya ta yi maganar wanda hakan ya dawo da hankalin sauran kansu, suma da sauri su ka taho don jin abin da doctor zai ce.
Sai da doctor ya ja numfashi sannan ya ce, "ina mai ba ku haƙuri" cikin ruɗewa Hajiya ta ce, "me ka ke nufi?!" Kallonta doctor ya yi ya ce, "ku yi haƙuri, mun rasa su, saboda ba ƙaramin illa abun da su ka sha ya yi musu ba, ku zo office zan fayyace muku komai" doctor ya faɗi sannan ya wuce, yana faɗi Hajiya ta sa ihu cikin fitar hayyaci, sauran su ka sa Salati matan ma su ka fashe da kuka, ta ke asibiti ya rikice sosai, aka rasa ma wa za a ba haƙuri.
Daga ƙarshe dai haka aka ba su gawan Ruki da kuma Saleem Su ka koma da shi gida don a gabatar da jana'iza.
BAYAN KWANA HUƊU.
Zaune Hajiya ta ke a kujerar falo kamar gunki, ƙasan tayiss kawai idonta ya ke gani, saboda gaba ɗaya garin tafashen zafi ya ke yi mata, 'ya'yanta sun rasu yau kwana huɗu da rasuwarsu, amma à ce ko da mutum ɗaya daga cikin danginta ba bu kusa sa ita, hatta jiya da ya ke ranar sadakan uku ma, amma sai mutanen su Mai-daraja kawai su ka zo, gashi yau shiru ka ke ji babu wanda ya leƙota ko da daga cikin maƙwafta, sabida tun da su ka ji labarin abin da mijinta Alhaji Jamilu ta aikata su ka yi baya da ita, sai dai a yi ta zuwa gurinsu Ammu amma ita ko gaisuwan ma da ƙyar ta ke samu a wurin wasu.
Dama ba ta kula su tun asali, idan ma sun zo bai wuci da kallon banza ta ke rakata su ba, saboda tana jin kanta Hajiya mai kuɗi, duk wanda ya zo mata da buƙatarsa akan ta taimaka, sai ta banzatar da mutum daga ƙarshe ma ta yi masa gargaɗin ka da ya ƙara zuwa gidanta da zancen roƙo, sai ga shi yau tana son ko yaya ta ga mutane cike da gidan su na taya ta alhini amma abun ya gagara.
Har ƙawarta Ladingo ma ba tun ranar da su Ruki su ka rasu rabonta da ta zo, duk da cewa dama Ladingon ta sanar da ita cewa ita ma fa yanzu ta ƙare mata, 'ya'yanta yanzu fushi su ke da ita, domin sun gane duk ita ce ke haɗasu faɗa da matansu, shi kuwa ɗanta ɗan shaye-shaye ƙaramin, wanda da ta ke son haɗa aurensa da Ruki, kwanaki ya yi sata aka zo aka kame shi kuma aka kulle, yayyinsa kuma su ka ce ba za su fiddo shi ba, tun da dama ai duk abin da ya ke da goyon bayan Ladingon mahaifiyarsu ya ke yi.
Safna ce ta taho da abinci kan plate haɗi da zama gefen Hajiya, "Hajiya na kawo miki abinci don Allah ki ci ko da kaɗan ne kin ji? Saboda kwanan nan ba kya samun cin abinci mai kyau" Cewar Safna cikin kulawa, a fisace Hajiya ta miƙe tare da sanya hannu ta ture abincin da ke hannun Safna da ƙarfi, plate ɗin ya fadi gefe haɗi da fashewa. Da sauri Safna ta miƙe tana duban inda abinci da plate ɗin ya watse.
"Ba shakka! Wato ga almajira kin kawo min abinci a pilet kawai, ko a kan tire ba za ki iya ɗaurawa ba yadda zai nuna kin darajta ni. To ni na ce miki ina da buƙatar taimakonki ne ma? idan ma munafurci ne yasa ki ke son yi min haka to ba ki isa ba" Hajiya ta faɗi sai kuma ta yi ƙasa da kai ta fara hawaye tana faɗin, "yau na rasa 'ya'yana, Autana da Saleem sun rasu, yanzu ba sa doron duniya, kuma ba ko wa ba ne ya yi sanadiyyar mutuwarsu fa ce ku!" Hajiya ta ƙarashe maganar tana kallon Safna da itama idonta ya cika da ƙwallah.
Yazeed da Marwan ne su ka shigo cikin falon à tare suna tattaunawa, sai kuma su ka ga abin da Hajiya ta yi, "no Hajiya, Safna ba su da wani alhaki akan mutuwar su Ruki kuma kin sani!" Cewar Yazeed suna ƙarasowa inda su Hajiyar su ke. Waigowa Hajiya da Safna su ka yi suna kallonsu, yayin da Hajiya ke bin Yazeed ɗin da kallon mamaki.
"Of course, kuma ba kowa ba ne ya yi sanadiyyar mutuwarsu yau face ke da Dady!" Marwan ya faɗi domin tun da abun nan ya faru shi ya riga da ya shiga taitayinsa, ko da matarsa Sumee ta taso masa da masifa ko maganar da zai ɓata masa rai, sai dai ya yi shiru kawai ba ya tanka mata.
Hajiya ba ta san lokacin da ta koma ta zauna kan kujerar zaman daɓas ba, saboda tsabar mamakin yau Marwan na kare Safna, Yazeed ya kuma cewa, "bayan duk abun da aka aikatawa Safna, amma bai hana ta kula da ke ba Hajiya, saboda kasancewarta mai halin ƙwarai" ahankali sauran mutane su ka fara hallara a wurin, saboda ƙarar da su ka ji tun farkon faɗin plate sannan kuma ga magan-ganun da su Yazeed ke yi"
Safna ta share hawayenta sannan ta ce, "yaya don Allah ku bar wannan zancen, duk abun da Hajiya ta yi a gareni daidai ne, saboda na san tana tattare da raɗaɗi a zuciyarta" sai da Amna ta ɗan ƙara buɗe idonta kaɗan tana kuma sake jinjina irin haƙurin Safna, sauran kuma sai yaba halin Safna su ke yi. Marwan ya dubi Hajiya ya ce, "kin gani ko Hajiya? Duk abin da ki ka yi mata amma ba ki da laifi a wurinta, Hajiya wai don Allah me yasa ki ka sanya mana tsanarsu tun muna yara ne?".
Ɗago ido Hajiya ta kuma yi tana kallon Marwan, Mai-daraja ya dubi Marwan ya ce, "Marwan ka daina wannan maganar ka ji?" "Uncle don Allah ka yi haƙuri ka barni in yi, saboda tun da na buɗe ido na ganku kai da anty Maryam da tsanarku na tashi, ko wace hanya Hajiya ta bi ta sanya na tsani ko da ace ganinku ne, lokacin da ka rasu ban yi baƙin ciki da rasuwarka ba, sai dai ma ince farin ciki mu ka yi ni da su Saleem duk da kasancewarsu sun fini yarinta, Yazeed da ka ke gani shi kaɗai ne ya koka da rasuwarka a cikinmu, hakan bai isa Hajiya ba, sai da ta kuma sanya mana tsanar Safna a ranmu tun tana ƙarama, ya zama ko giftawan Safna ba ma son gani, to duk me dalilin Hajiya na yi mana haka? Daga ƙarshe kuma ga shi ashe Dadynmu shine silar tarwatsa ku. Duk yadda ita da Dady su ka so kassaraku ga shi abun ya dawo kanmu, ƙwayar da ya yi don kashe mutane ya juyo ya kashe 'ya'yansa. Ba su ba mu tarbiyyar da ya dace ba, ako da yaushe ɗaukar mutane mu ke yi ba abakin komai ba gurin yi musu rashin kunya, komin girman mutum ba ma jin shakkar yi masa abin da mu ke so. Ga su Saleem sun rasu, shin Hajiya ta ba su tarbiyyar da zasu kare kansu daga azabar kabari? Ko lokacin Sallah ya yi ba ta tsawatar mana, ita da kanta ma sai lokacin da ta ke so sannan ta ke tashi ta yi, sai ya zama muma mun taso sai sanda ya game mu sannan mu bautawa ubangijinmu, babu abin da ya ke cikin zuciyarmu fa ce gurɓatacchen tunani. Yazeed shi ne ya fita daban à cikinmu, wanda abin da ya ke yi mu kuma gani muke takura kai ne kawai. To yanzu duk wa ta ƙare mawa? Komai da komai kanmu ya dawo, har ina jin na tsani rayuwar nan gaba ɗaya. Amma duk da haka bai isheta ba, ta kuma tasa Safna gaba tana faɗa mata muggan zantuka?".
Jinjina kai kowa ya yi da batun da Marwan ya yi, sosai su ka ji jikinsu ya mutu da magan-ganun Yazeed ji ya yi kamar Marwan ya taso masa da jin kunyar kansa, Hajiya kam fashewa da kuka ta yi tana cewa, "ba shakka maganar da ka faɗi gaskiya ne Marwan, ko shakka babu ba wata ƙarya cikin maganarka, na cuci kaina kuma na cuci 'ya'yana, ban ba ku tarbiyyan da ya dace ba, ako da yaushe ba ni da wani buri da ya wuce in samu kuɗi kawai a rayuwata, na azabtar da su Maryam musamman ma Safna, sai ga shi yanzu na rasa komai, komai ya lalace min fiye da yadda na aikatawa su Safna, don Allah ku yafe min, ku yafe min wallahi na tuba kuma na yi nadama" tana faɗi ta fashe da kuka sosai.
Bayan wasu mintuna.
Ankwashe plate da kuma abincin da ya zube, gaba ɗayansu zaune su ke kan kujera Mai-daraja ya ce. "Tun bayan shekarun nan ido na na kan komai, sai dai duk yadda zan yi don in dawo hakan ya gagara, saboda idan har na dawo to fa duk abin da zan ce game da Jamilu to ba zai yi aiki ba, saboda kasancewarsa yana amfani da sihiri da kuma wasu abubuwan, wannan shi ne dalilina na jinkirta har zuwa wannan lokacin, kuma ko da na gano Shuraim ɗana ma yana iya bakin ƙoƙarinshi hakan ya yi min daɗi sosai. Sannan na samu damar cigaba da sana'ata a inda na ke kuma Allah ya dafa min, a yanzu haka na mallaki abun da ya fi dukiyar da na bari".
Kowa da mamaki kawai ya ke bin Mai-daraja, daga ƙarshe dai Hajiya ta kuma sanya guiwoyinta a ƙasa tana neman gafara, a take su ka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 54 Chapter of 56