Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar wanda ke ƙirƙiran mugunta a ransa. "Ba mafarki ki ke yi ba, ni ɗin ne idon ki yake gani, kuma kallo na ƙarshe da zaki yi a rayuwarki!!" Kukan da ta ke riƙewa ya fara fitowa mai sauti, yayin da shi kuma babu abin da ya ke yi sai murmushi, cikin muryar kukan ta ce, "Dady, dama kai ne wannan shahararren maci amanar ƙasan? Dady dama kaina wannan wanda ya yi silar jefa ni cikin haɗari? Dady dama ka..." "Dakata!! " Ya tsaida ta da ƙarisawa sannan ya kusanto inda ta ke ka na ya tsaya yana kallon fiskarta, babu alamar sakewa kan fiskarsa ko kaɗan. Zamu iya cewa fiskar Zabba-ba ba Dady ba. Shiru ta yi jikinta n'a ta faman kyarma cike da tsoro, sai a sannan ya yi magana da cewa, "baki da buƙatar tambaya ta, duk labarin da kike ji akai na, to duk ni ɗin ne ba wani ba!" Girgiza kai ta fara yi tana cewa, "no no this is not true, wannan ba gaskiya ba ne" ta faɗi cikin ruɗewa tana kallon sauran mutanen da ke gefen, wanda suke tsaye babu abin da suke sai kallonta. Dawo da dubanta garesa ta yi, cikin muryar da ke nuna tana shirinyin kuka ta ce, "Me yasa zaka yi haka? Dady kai ne wanda na ɗauka tamkar uba a wuri na, kai ne wanda na ke gani, kana share mini hawaye à lokacin da nake cikin damuwa, kai fa mahaifina ne Dady" tana sauke maganar Dady ya sauke mata mari mai mugun ƙara, wanda ya sanya ta har sai da ta faɗi a ƙasa, ko samun damar ɗaura hannu kan kuncinta bata yi ba, saboda yadda mamaki ya ke ta sake shigarta ba bu ƙaƙƙautawa, jin muryarsa ta ji yana magana bayan ya ranƙwafa kanta. "Kar ki sake kira mahaifinki, domin ni ban taɓa zama uba a gareki ba! Kuma ba zan taɓa zama ba har abada! Kuma kar kiyi tunanin basajar da ki ke yi zai yi aiki a nan, domin ni na riga da na san duk abin da kike yi, hasalima duk wani motsinki na sani, ban taɓa tsanar wasu a duniya kamar yadda na tsane ku ba, domin ke ce wacche kika hana ni rawar gaban hantsi a rayuwata, ku ne kuka hana shiri na kammala tun kina cikin ciki! Don haka, yau zan aika ki inda mahaifinki ya ke, wala'alallah ya ƙare yi miki bayanin komai game da ni à can" Wani girgiza ta ji kanta ya yi mata, sai da ta tsaida numfashinta na ɗan mintuna kafin ta sauke da ƙarfi, idanuwanta suka cika da ƙwallah ta rufe ido ta fiddo su, duban Dady da ya miƙe daga ronƙwafar da ya yi take yi, kamar wacche bata fahimci me ya ce ba, domin wani irin yawo kalamansa suke yi cikin ƙwaƙwalwarta. Cikin ƙara ji ta sake jin Dady ya ce, "dama na san da zuwanki wannan wuri Amna, hakan yasa na shirya dole yau zaki bar duniya Amna!!!". Yana yin maganar ya juya yana shirin ba wa'yannan mutanen umurnin abin da zasu aikatawa Amna. Cikin rashin fahimta ta buɗe baki tana cewa, "Amna!? Me...yasa ka ke kira na da Amna?" Wannan maganar na ta ne ya dakatar da Dady daga umurnin da ya ke shirin bayarwa, juyowa ya yi yana kallonta sannan ya saki murmushin nan dai yana cewa, "yarinya ke nan, baki ji abin da na ce a baya ba Amna?, Basajar da kike yi ya ƙare a nan, domin a sane na ke da ko wacece ke". Samun damar tashi ta yi ta share hawayen da ke idonta ta kuma cewa, "Dady me kake cewa ne? Ban gane me kake magana ba" takowa ya yi zuwa gabanta haɗi da ɗaukar wani katakon da ya ke a ƙasa, ba ta gama fahimtar abin da zai yi da katakon mai ɗauke da ƙusoshi à jiki ba, sai da ta ji saukarsa a kan ƙafaɗarta, ƙara ta saki tare da yin baya tana kai hannunta gurin da ya yi mata wannan bugun, saboda ji da ta yi ƙashin ƙafaɗarta sai da ya yi ƙara, wasu hawaye suka sake fitowa, ciro hannunta da ke kan ƙafaɗar ta yi tana kallo, idonta ya sauka kan jini. Rintse ido ta yi tana jin yadda gurin ya ke mata zugi, hawaye bai tsagaita fitowa daga idonta ba. Matsowa wurinta Dady ya yi tare da tsugunnawa Yana kallonta, "na riga da na san ko ke wace ce, sunan ki Amna, sannan fiye da haka ma na sani a kanki" buɗe ido ta yi tana kallonsa, sai kuma ta fara ƙoƙarin tashi tana dariyar ƙarfin hali, fiskar Dady ne ya dawo na mamaki saboda dariyar da take yi,. "Wacece Amna? Ni ba Amna ba ce, kuma ban ma taɓa ganinta ba" Ta faɗi tare da cigaba da dariyarta. Hannu ya ɗaga yana nuna ta da yatsa da mamaki ya furta, "kar ki raina min wayo! Wa cece ke idan ba Amna ba?!". BARI MU ƊAN WAI WAYA BAYA, LOKACI KAƊAN NA YAU. Wannan baƙar yarinyar ce kwance a kan gado, fiskarta na fitar da hawaye lokaci bayan lokaci, yayin da uncle Musa yake gefenta zaune yana kallonta cikin tausayawa, sai da ya numfasa ya ce, "ƴata ki natsu mana, sau nawa nake sanar da ke ki ringa kwantar da hankalinki? Bana son ki rinƙa sanya damuwa à ranki, duk daran daɗewa zaki koma kiga abin da idonki ya ke son gani, kuma na sanar da ke lokaci kaɗai zaki jira, zan cika miki wannan burin na ki, mun dawo garin nan ne don na tabbatar miki da hakan". Ajiyar zuciya ta ijje sannan ta juyi da idanuwanta garesa, sannan ta sakar masa da murmushin don nuna masa cewa zata yi hakan, miƙewa uncle Musa ya yi ya kuma cewa, "aikin maganin nan ya ƙare, zaki iya cirewa yanzu. To bari na je waje akwai abin da zanyi" yana faɗi ya wuce, itama da toh kaɗai ta amsa masa haɗi da miƙewa daga kwancen da take. Toilet ɗin da ke cikin ɗakin ta nufa haɗi da shiga a hankali, ta haɗa ruwan da zata yi wanka sannan ta fara gabatarwa. Babu abin da ke tafiya gurin makwararan bayin face wani baƙin ruwa sosai, tana a cikin bayan gidan ta ji wayar uncle Musa da ya bari a cikin ɗakin yana ƙara, dai dai lokacin da ta fito wayar ya tsinke, kallon inda wayar ta ke ta yi, sannan ta nufi walldrop don ta sanya kaya, sai dai kuma ta ƙara jin kira ya shigo cikin wayar, juyawa ta kuma yi tana kallonsa, kamar baza ta ɗauka ba, sai kuma ta yi saurin isa gun wayar. Sunan Shuraim ta gani ya bayyana a jiki, tana ɗauka ta kara a kan kunnenta. Zare ido ta yi jin mutumin da ya kira yana wani magana, wanda ta ji fitar wani mai suna Zabba-ba daga cikin zancen na sa. Bata yi magana ba har Shuraim ya gama zayyana komai, har ya kashe wayar, minti kaɗan ta ga ya turo da adreshin inda ya ke maganar zasu je, hannunta ta shiga kallo tana mai tunanin magan-ganun mutumin nan. __Yayin da ni kuma Aisha G Umar n'a kalli fatar ta da ya dawo fari t'as, saɓanin da da yake kamar baƙin ƙuna, a hankali na maida kallona kan gaba ɗaya jikinta, don tabbatar da abin da ido na ya gani, shin ko dai hannun nata ne kaɗai ya ke farin?. Kasan cewar tawel ne ta ɗaura hakan ya sa na kuma shiga wani mamakin daban, domin kuwa ganin launin fatarta na yi fari t'as shima, da hanzari n'a maida kallona kan fiskarta, haba wa ai sai da idanuna suka faɗi ƙasa na maida su da sauri ina kuma ƙare mata kallo, fiskar da Amna ta ke amfani da shi na gani wato fiskar Safna! Har sai da zuciyata ta bani tunanin to ko dai surgery a kayi wa wannan baiwar Allahn ne?__ CIGABA. Bata tsaya da dariyar da ta ke ba, kamar yadda bata amsa masa tabmbayar da ya yi mata ba, haushin hakan ya sanya Dady ya kuma buga mata wannan katakon da ke hannunsa, wanda hakan ya dakatar da dariyar da ta ke yi, ta saki ƙara tare da faɗi ƙasa, yanzuma hannu ta sanya a wurin tana jin yadda take ji, amma ta yi ƙarfin halin danne kukan raɗaɗin da ke shirin zuwar mata, ta saki murmushi, "Wacece ke na ce! Akan me zaki yi wasa da hankali na? Waye ya ɗaura miki wannan fiskar? Domin ba abin mamaki ba ne don kin kasance da wannan fiskar, ta yi kin sanya ta ne, tun da yanzu zamani ya sauya, sai dai tabbas akwai wanda ya mara miki baya, amma ki sani kin kawo kanki gurin da kabarinki ya ke". "Me ka ke cewa wai Dady? A ah na yi kuskure, Zabba-ba ya kamata na ce" cikin dauriya ta ke maganar duk da cewa hawayen raɗaɗi n'a zuba daga idonta, cigaba da magana ta yi da cewa, "ni sunana Safna! Kuma wannan suffa ta ce, ka ɗauka tura ni da rukuninka na tsakiya suka yi na mutu ne? To ban mutu ba, ina rayé kamar yadda ka ke gani" sakin katakon da ke hannunsa ya yi ƙasa, sautin faɗuwar ya yi ƙara, Dady ya yi baya kaɗan yana kallonta cikin mamaki sosai!, nan ita kuma ta samu damar sake yin magana. "Tabbas haka al'amarin ya ke, ni Safna ban mutu ba Dady! Allah ya tseratar da ni daga sharrinku, amma na yi mamaki matuƙa da ya kasance kai ne wannan mugun Dady" sai da ta matso ƙwallah mai ɗauke da zafi ta kuma cewa, "kuma idan na fahimci maganarka, kayi zaton ni Amna ce ko? Amna wacche ta zauna amatsayina, wacche aka ce min muna kama, to idan ita kake magana ba zata zo nan ba! Domin na tura musu saƙon kada su zo" ta faɗi tana haɗe fiskanta na raɗaɗin da take ji, sannan ta giɗa kai tana sake cewa, "duk abin da ka ke so za ka iya yi min, idan ma kashe ni za ka yi kamar yadda ka ce, to Dady ina jira! Ka kashe ni, saboda ba zan bari ka cutar da wacche ta kasance da Ammu na tsawon lokaci ba, ita ce ta sai wa mahaifiyata 'yanci wanda ni na kasa yin hakan, Amna kam baza ka taɓa cinma manufarka a kanta b...". Bata ƙarisa ba sakamakon marin da Dady ya sakar mata gigitacche, wanda ya sanya ta riƙe kumatu haɗi da rintse ido tana jin kanta na juyawa, kafinta buɗe ido ta ji duka ya fara sauka a kan jikinta da wannan katakon, jikinta ya kasa jurar zafin, don haka ta kwanta tana jin saukar dukan tana kuka. "Wato Safna baki mutu ba? Duk ɗaukar da na yi na rabu da ke a she kina nan, kin ma kanki àdalci, da alama kin fi sha'awar mutuwa a hannuna" bata fahimci me ya ce ba, saboda yadda ya ke zabga mata katakon da ke ɗauke da ƙusoshi. AMNA DA SHURAIM. Ya ɗaga wayar yana shirin duba saƙon da aka turo masa, Amna ma idonta na kansa, sai dai kan ya kaiga ganin saƙon wayar ya faɗi daga hannunsa, wanda gargadar da suka shiga ne ya sanya hakan, bai bi ta kan wayar ba domin abin da ke gabansu yana buƙatar tsanaki, kuma maida hankalinsu ga hanya suka yi a ƙagauce. Bayan lokaci sai gashi sun iso, daga nesa suka tsaida motar sannan suka sauko suna tahowa gidan gona. A hankali suke sanya kai ciki, sai dai ba bu wanda suka gani a waje kamar yadda suka zata, hakan yasa suka cigaba da shiga duk da suna kuma ankarewa don kada a shammace su, babu wani makami da suka riƙe don ceton kansu, su suna jin ko wanne yana da ƙarfi, don sun dai san gurin nan ba zai kai kogo hatsari ba, sai dai shi Shuraim ya san tun da ya riga da ya yi wa uncle Musa magana to zai yi wani abu a kai. Zagayawa suke ta yi cikin wannan gidan gonar, sune shiga kango suna ta dubawa, amma ba sa ganin kowa a ciki, sai shiru da wurin ya ɗauka. Haka dai har suka isa wannan hall ɗin. Kallon wurin suke da mamaki, domin dai babu wani fanni mai kama da hall ɗin da suka gani duk zagayen da suka yi, juyawa Amna da Shuraim suka yi suna kallon junansu. Sai kuma suka maida kallonsu gun wannan ƙofar hall ɗin, da ankarewa à hankai suka fara shiga ciki, sautin motsinsu kaɗai ke tashi, emty suka ga cikinsa, babu wani abu bai kama da benci da suka gani, wato teburin Baba da kuma na sinadaran maganin nan. Ganin babu kowa a ciki ya sa su sakin jiki suna dubawa, ganin babu abin da suka gani ne yasa su juyawa zasu bar wurin, kunnen Amna ne ya jiye mata wani sauti da ke tashi kamar na mutum, saurin dakatawa ta yi tana dakatar da Shuraim ma da kwantacciyar murya, gudun kada sautu ya ratsa hall ɗin. "Kana jin abin da na ke ji kuwa?" Shuraim da ya juyo yana kallonta ya kasa kunne don ya saurari abin da ta ce ɗin, da sauri suka juya can gaba a tare jin wannan sautin ta can ya ke fitowa, da sauri Amna ta nufi wurin don dama tun shigowasu basu isa wurin ba, shima Shuraim rufa mata baya ya yi, kwana suka gani bayan sun isa wannan wuri. Zuciyarsu n'a bada ƙarar tsoro suka farayin wannan kwanar, idanuwansu ne ya fara gane musu ƙafar mutum zaune, sannan wannan saukar numfashin wahalar na ƙara tashi. Jan birki suka yi cike da razani, bugun zuciyarsu ya daɗa sauti, cikin ankarewa da shirin kota kwana suka cigaba da sanya ƙafafuwansu da idanuwansu don ganin waye?. Wani birkin suka sake ja a tare daga Amna har Shuraim, yayin da suka ji kaɗawar iska mai wani irin yanayi cikin ƙwaƙwalwarsu, zaro ido sosai Amna ta yi tana kallon Safna da ke zaune jingine da gini, sai fitar da numfashin azaba take yi idanuwanta a rufe, gashinta baze a ƙafaɗunta wasu kuma kan fiskarta, rigar da ke jikinta ya ɓaci da jini. Amna da Shuraim babu wanda ya fiskanci wacece kasancewar yadda ta ke, da gudu suka ƙaraso inda take suna durƙusawa kanta, cike da tausayawan yadda suka ganta suke kallonta, magan-ganu suka fara yi wa Safna amma bata amsa ba, sannan idonta bata buɗe ba, Amna ce ta buɗe baki ta ce, "me ya kawo ki nan? Wacece ke? Shuraim mu kaita asibiti, ta raunana sosai". Zuciyarta ne ya bada sauti mai amo cikin ƙirjinta, jin muryar da yake kusan irin na ta, idanuwanta da yayi mata nauyi tare da yin jawur a kumbura ta fara ƙoƙarin buɗe sa, a kan Amna dake gefenta idon ya sauka, hawayen da babu shiri ya sauka daga kan fiskarta, 'ƙwarai tana kama da ke sosai 'yata Safna, sai ma kin ganta zaki fi sanin komai, don haka ki cigaba da haƙuri, na tabbata zata kula miki da mahaifiyarki fiye da yadda ke kika kula da ita' maganar uncle Musa da ya faɗa mata kenan wani lokaci da ta damu kan Ammu. Sai dai ganin Amna yasa ta ga cewa kamar uncle Musa ya rage faɗar wani abu dangane da kamannin da yake suffanta mata Amnan ma, domin yanzu gani take tamkar ita ce ta ke ganin kanta jikin madubi, dama bata ga Amnan a hoto ba. Da ƙyar ta iya buɗe bakinta da ya fashe ta furta, "Am...Amna, kada ku tsaya a wurin nan, kuyi gaggawar, barin nan". Amna bata fahimci abin da Safna ta faɗa ba, sai dai bugun da zuciyarta ya yi jin maganar wannan budurwar da bata gama gane wace ba, dama ƙoƙarin tashi ta ke yi don ta ɗauketa su kaita asibiti, amma jin bugun zuciyarta ya yi yawa ne yasa ta kuma durƙusawa kan Safna, a hankai ta fara ɗaga hannunta da ke rawa, don ta ɗauke wannan gashin da ke kan budurwar don ta ga fiskarta da kyau. Shima Shuraim ɗin kallon Safna ya ke yi jin maganar da ta faɗa, sannan saitin muryarta ya fito kamar na Amna, duk da cewa bai yi ƙara ba da ƙyar ta yi maganar. Sai da Amna ta wuntsula baya zuciyarta na sake fitar da tsantsar sauti, Shuraimkuwa zare ido ya yi ba tare da ya gusa ba, bakinsa ya buɗe yana faɗin, "Safna?!! Me ya kawo ki nan!? Me aka yi miki haka?" Wani irin duhu Amna ta ji Shuraim ya kuma jefa ta wato shima ya kalli abin da ta gani kenan? Safna fa ya kira, "m...me ka ke nufi Shuraim? Safna fa ka ce" ta ƙarashe tare da maida kallonta kan Safna, Shuraim ya juyo ya dube Amna fiskarsa cike da damuwar halin da ya ga ƙanwarsa ciki. "Eh Amna, Safna ce, dama bata mutu ba". Sai da Amna ta girgiza da abin da Shuraim ya ce, Safna bata mutu ba, kenan ƙarya ya yi mata wancan lokacin? Safna kuwa sake buɗe baki ta yi ta kuma faɗin, "ku bar wurin nan, kada ku zauna". Last part. ___________________________________________________ 😱wai wai wa wai!! Dady Zabba-ba!? Cab ɗin jam. Sannan ga Safna bata mutu ba!! kenan daman tana rayé ƙarya kawai su Shuraim suka yi wa Amna, to ko me dalilinsu na yin hakan? Ga su Amna da Shuraim suma sun shigo. Shi tunanin Shuraim da uncle Musa ya yi magana. Ashe daiii Shin zasu ɗauki Safna zuwa asibiti ko me zai faru?. Mu kasance a kashi na gaba da yardar Allah. ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣5️⃣1️⃣▶️1️⃣5️⃣2️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 "Eh Amna, Safna ce, dama bata mutu ba". Sai da Amna ta girgiza da abin da Shuraim ya ce, Safna bata mutu ba, kenan ƙarya ya yi mata wancan lokacin? Safna kuwa sake buɗe baki ta yi ta kuma faɗin, "ku bar wurin nan, kada ku zauna". Tana yin maganar ta sauke numfashi, Amna kuwa tashi ta yi tana kallon Safna yayin da ta rasa a wani matsayi shock ɗin zuciyarta ya ke, sai da ta kalli Shuraim ta jefa masa kallon tambaya sannan ta yi ƙasa tana kallon Safna, baki na rawa ta ce, "Safna baki mutu ba? Dama ba ki mutu ba?" Da ƙyar Safna ta ɗaga mata kai hawaye na sake fitowa à idonta, ya yin da itama Amnar ƙwallah ya cika mata ido., Hannu ta kuma ɗagawa a hankali tana ɗaurawa kan fiskar Safna ta fara shafawa, hawaye ya zubo mata tana cigaba da kallon Safna, itama Safnan hannunta da ƙyar ta ɗaga ta ɗaura kan fiskar Amna, Shuraim ma hawaye ya fito masa yana kallonsu. "Safna bata mutu ba, tun tuni kina ina Safna? Kika bar Ammu cikin kewarki, ta zubar da hawaye lokuta da dama duk saboda rashinki, nagode Allah! Da ina ta tunanin yadda zata san cewa kin rasu, amma alhamdulillahi tun da hakan bai kasance ba" cewar Amna cikin murya raunanna tana hawaye, rufe ido Safna ta yi ta fito da wasu hawaye jin sunan Ammu da Amna ta ambata. Shafa fiskan juna suke cike da tausayi da kuma ƙaunar da ke shiga cikin jikinsu, hannunta ne ya isa wurin wani karcen ƙusa da ke haɓar bakin Safna, ga jini a wurin, shafo jinin Amna ta yi tana kallo cikin ruɗewa, zuciyarta ya amsa cikin wani yanayi, "Safna faɗa min waye ya miki haka? Ki faɗa min ni zanyi maganinshi!" Ta faɗi tare da share hawaye cikin nuna jarumta. Safna da ke jin jikinta n'a cigaba da ɗaukar raɗaɗi ne ta sauke hannunta daga kan fiskar Amna, sannan ta lumshe idonta daga bisani ta buɗe a hankali ta maida kallon na ta kan Shuraim, cikin tausaya ya ke kallonta idonsa da ƙwallah ya ce, "eh ƙanwata ki sanar da mu suwa suka aikata miki wannan raunin? Saboda ba zan taɓa yafe musu ba!". Murmushi da ƙyar ta yi masa sannan ta kuma juyawa inda Amna ta ke. Idonta kamar zata kuma lumshewa, tana jin kamar bakinta ba zai buɗe ba ta ce, "na ce ku yi gaggawan barin..." Amna ta yi saurin katseta da cewa, "Shuraim mu kaita asibiti da wuri, kada jinkirinmu ya haddasa wani abun" ta faɗi tana miƙewa haɗi da ƙoƙarin ɗaukar Safna. Ita kuwa Safna ta kasa sanin yadda zata fahimtar da su su yi gaggawan tafiya, ta rasa me yasa suka zo ma, ita da take farin cikin ba za su zo ba saboda ta tura musu saƙo. Shuraim ya miƙe da kuma Amna dake sanya hannu son ɗaukar Safna, suka ji saukar wani abu mai kama da gun-gun icche à kansu, miƙewa su ka yi cikin gigice tare da sanya hannyensu a saman kan, matse ido Amna ta yi tana ƙyaƙyƙyaftawa, domin yadda ta ke jin kanta na yi mata sai layi ta ke yi kamar zata faɗi. Shima Shuraim layin ya ke ɗaukarsa idonsa a buɗe. Mutanen Dady Zabba-ba ne suka fara bayanna à wurin wanda dama cikinsu ne suka buga wa Amna da Shuraim manyan katakwaye masu nauyi, suna da yawa zasu kusa kai mutane arba'in, fiskarsu babu alamar rahama ko kaɗan. Cikin muryarta da ya shige cikin tashin hankali Safna ta fitar da ƙara hawaye na sake buɗe ƙofar fita daga idonta. Kafin su Amna su gama gane wan'yanda suka aikata musu hakan, wani daga cikin mutanen nan ya kuma ɗaga nannauyar katakon ya saukewa Amna a gefen kai da ya sauka har fiskarta. Wanda hakan yasa ta rintse ido ta yi gefe da ƙarfi haɗi da bugan bangon kusa da ita, sai da jini ya fita daga bakinta ya watsu à jikin bangon wani kuma na sake fita kan fiskarta, buɗe idon ta yi tana kallon gaba ɗaya wurin n'a kasuwar mata kashi-kashi. Shuraim da ya miƙa hannu cikin tashin hankali yana son tare ta duk da kansa na juyawa, sai dai shima sakar masa da icchen suka sake yi a gadon bayansa, sau biyu a jere, a tare suka faɗi ƙasa shi da Amna. Cikin tashin hankali Safna ta ke ihu tare da son isa Inda Amna ta ke, haɗi da juyawa tana kallon Shuraim, amma ƙafanta da aka buge mata ɗazu ya gaza ɗaukar tsayawarta, hakan yasa ta sulale ta zube à ƙasa haɗi da sake buguwa sosai. Kan Shuraim mutum ɗaya ya je yana jibgar Shuraim sosai haɗi da sanya ƙafa ya ture Safna da ke roƙonsa ya rabu da Shuraim. Dayan kuma daban ya nufi inda Amna ta ke, tare da ɗaga icchen da ke ɗauke a hannunsa yana shirin saukewa akanta. "Stop!!" Cewar Dady yana ƙarasowa yayin da ake matsawa ana bashi hanya, hakan yasa mutanen nan suka dakata da abin da su ke yi, su ka tsaya suna jiran isowan Dady. Har gaban wanda ke wurin Amna Dady ya tsaya yana bin Amna da Safna da kuma Shuraim da kallon tsananin mugunta, sannan ya karɓi icchen da ke hannanun mutumin ya yi musu alama da su matsa. Kamar yadda Dady ya ba su umarni su ka matsa can cikin 'yan uwansu, Dady kuwa ya ɗaga ƙafarsa mai ɗauke da ƙaton takalma mai nauyi ya ɗaurawa a kan gadon bayan Amna da ke kwance idonta rufe sai fitar da numfashin azaba ta ke yi. Dariya ya saki wanda ya sanya Shuraim da shima ya rufe ido yana sauraron raɗaɗin jikinsa, da kuma Safna da itama jikinta ke kuma amsan hakan, suka fara ƙoƙarin daga kai don su ga mai dariyar, koda Safna kam ta riga da ta san ko waye, wani irin zaro ido Shuraim ya yi ko da idonsa ya sauka kan fisakar Dady da ke sanye da hula mai malafa. Sai da ya kwantar da kansa da ya ɗago ƙasa fiskarsa cikin zafi da kuma mamaki, "Barkanku da zuwa masarrafar Zabba-ba dukan ku! Hahhhha hahhhha" dukansu suka ji saukar ƙatuwar muryarsa a cikin kunnuwansu. Amna buɗe lumshashshun idanuwanta ta fara yi da ɗayar idon ma gefensa jini ke fitarwa, sai dai ta kasa ƙaƙƙarfan motsi sannan kuma ga ƙafar da aka ɗaura mata a baya ana taka ta da karfi, hakan

Chapter 46 of 56