Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bara barazanar rufewa, "Madam ki tashi dan Allah ki ga farceni" ta faɗi har muryar ta na rawa, har zata fita nemo ɗauki sai kuma ta fa sa, saboda tunawa da tayi da ta cire eye color. Da sauri ta nufi kofin jug ɗin da ke ƙasa, wanda take sanya ruwa ta ijje, ta dau ƙaramin kofin sa tana tsiya ya ruwa a ciki, tallabo kan Ammu tayi tana kai kofin bakin ta, sai da ya ɗau minti huɗu kafin Ammu ta fahimci abinda yarinyar ke ƙoƙarin sa ta tasha, hakan yasa ta ɗan sha ruwan kaɗan, tana sha Amna ta sauke kofin haɗi da bubbuga bayan Ammu a hankali, cikin ikon Allah hankalin Ammu ya fara dawowa jikin ta. Jinginar da ita Amna tayi jikin kan gadon, sauke numfashi mai zafi kawai Ammu take, hawaye sai zarya yake akan kuncinta, innalillahi wa inna ilaihi raju'un take ta na na ta wa cikin ranta, zama kusa da ita Amna tayi tana faɗin, "I'm so sorry! Da nasan zaki shiga wannan halin da bazan sanar da ke ba" da ƙyar Ammu ta kamo hannun Amna, saida ta kai idonta kan riƙon da matar tayi mata a hannu sannan ta maida kanta ga Ammu tana cewa, "nima bansan inda 'yarki take ba" ta faɗi ba tareda ta san abunda Ammun ta tambaye ta ba kenan. "Haɗe idanun ta tayi wasu ƙollan na ƙara fitowa, zuciyar ta na yi mata ƙuna, da tayi tinanin 'yarta ce ta dawo, tayi zaton ko wasu ɗabi'u ne ta koyo a inda taje ashe ba haka bane. "Ina 'yata take? Ina aka kaimin ke Safna ta? Wacece wannan da aka kawomin a matsayin ki? Ya akayi kuka kasance masu kama da juna haka? Ya Allah kai ne kaɗai kasan duk abinda ke faruwa a kaina da kuma 'yata, ya Allah ka kawo mana mafita, ka kare min Safna ta a duk inda take" maganar da take tayi acikin zuciyar ta, haɗi da buɗe idanuwanta wasu hawayen na koranyowa. Amna kuwa hankalin ta yaƙi kwantawa sam, musamman da taga Ammu na kuka, sai tayi da nasanin maganar da tayi, suna a haka sai ga Ruki ta faɗo cikin ɗakin, da sauri Amna ta rufe idonta da hannu ɗaya, tayi zumbur ta miƙe, ƙa re musu kallo ta fara yi ganin a yanayin da suke, ga mahaifiyar ta kamar tana kuka ita kuma ta wani miƙewa zunbur kamar mai laifi sannan ga rufe ido ɗaya da tayi. Matsowa kusa dasu Rukin tayi tana cigaba da binsu da kallon baku kaiba sannan ta ce, "me ke faruwa a nan? Ke kuma wani irin iskanci ne yasa ki rufe ido?" Danne haushin dake niyyar zo mata tayi ta ba ta amsa, "am ƙwaro! Ƙwaro ne ya fa ɗa min cikin idon" tana faɗi idonta ya faɗa kan eye color ɗin da ta cire kan gado, sai da ta zaro idon da bata rufe ba sannan ta faki idon Rukin tayi wuff ta ɗauke shi, jan tsaki Ruki tayi ta ƙara cewa, "aikin banza! Ba cewa nayi kizo kimin wanki ba? Ko har yanzu abunda kika koyo a yawan gantalin na ki bai bar kan ki ba?". Shigewa bayan gida kawai Amna tayi, domin tasan idan har ta tsaya sauraron Ruki babu abinda zai hana ta nakaɗa mata duka, "Iyyehh! Wato ma shigewa toilet kikayi kika ƙyaleni, lallaii! To wallahi zakiga abinda zanyi miki tsinanna kawai" tana faɗi ta bar ɗakin, saida Amna taji alamar barin ɗakin da tayi ka na ta fito, da sauri ta rufe ƙofar ɗakin, tana sauke ajiyar zuciya ta furta, "sai na yi maganin yarinyar nan zata shiga tai-tayin ta" ta faɗi tana jan ƙofa, zuwa drawer tayi ta buɗe ta ɗauki jakan da abubuwan suke a ciki dan ta maida alamar a fiskar ta. Tana gamawa ta fice ba tareda ta ko kalli inda Ammu take ba, bare taga ta daina kukan ne ko kuwa, Ammu kuwa babu abinda take fa ce sauke ajiyar zuciyoyi a jere, Amna ko tana fita ta samu wani wuri a harabar gidan ta tsaya bayan ta naɗe hannayen ta biyu, ranta har yanzu a ɓace tana tinanin ta yadda zatayi maganin su Hajiya, amma agefe guda kuma tana tuna maganar mutumin nan ɗan kidnapping. RAHEENA. Yauma shiryawa tayi dan tazo gidan su Safna ta ga ko ta dawo, sai dai yau driver ne ya kawo ta har ƙofar gidan, bayan an buɗe mata ƙo fa ta gaida Baba Hambali, tun kan ta tambaye shi dawowar Safna ya sanar da ita, farin ciki sosai ta shiga jin aminiyar ta ta dawo, "tana ciki yanzu haka?" Tayi masa tambayar cike da ƙaguwa, yana tabbatar mata tawuce tana dosar ƙofar falo, har jikin ta na rawa saboda farin ciki. Kamar ance mata ta juya ta hango ƙawarta, a hankali ta nufa wurin, Amna na tsaye kawai taji an rungumeta ta baya, ture Raheena haɗi da ɗaga hannu zata wankawa wanda yayi mata haka, domin da ma a hasale take, zaro ido Raheena tayi ganin abinda ke shirin faruwa, dakatar da marin tayi ganin wacche bata sani ba, da kallon mamaki Raheena ta bita ganin abinda tayi kamar ba Safna ba?. "Safna! Lafiyar ki kuwa?" Cewar Raheena yayinda ita kuwa Amna ke tinanin, "wacece wannan kuma? Ba'a nunamin ita ba gashi kuma ta kira sunan Safna?" Kallon-kallo suke a tsakanin su, Amna na yiwa Raheena kallon rashin sani, ita kuma Raheena na wa Safna kallon mamaki kamar bata gane ta ba. "Safna nice fa Raheena wai ko baki gane niba ne?" Cewar Raheena, "wataƙil fa wannan ƙawar Safna ce, idan kuwa hakane dole ki mayar da ita ƙawarki Amna" Amna ta faɗi a zuciyar ta, ta ke ta hau ya ƙen dariya tana faɗin, "aahhh Raheena yakike ya kwana da yawa?" Raheena tace "lafiya lau amma me ke damunki ne? Yi fa kikayi kamar baki sanni ba, har mari n'a fa kikayi niyya" "haba haba ke kuwa ƙawata, kawai so nayi naga react ɗinki fa, kuma na gani" ta faɗi tana cigaba da murmushi. Murmushi itama Raheena tayi tana faɗin, "yau kuma ke ce da zolaya haka?" Gefe Amna tayi da idon ta zuciyar ta kuma cewa, "oh ita Safna ba ta zolaya kenan?" a fili kuwa tace, "zolayar n'a da kyau ai, koba komai zamuyi nishaɗi" "hakane amma fa kin tsorata ni, yaushe ma kika dawo ne? Kin dawo ko ki neme ni, Baba Hambali bai sanar dake sintirin da na rinƙa yi a gidan nan ba? Amma shine kika manta dani bayan kin dawo ko? nayi fushi". Jan hannun ta Amna tayi zuwa wani dogon kujerar da ke can gefe suka zauna ta ce, "haba ke kuwa kar kiyi fushi kina raina, kawai dai Allah bai nufa zuwana bane, amma ba gashi kinzo ba?" Sai da Raheena ta murmusa sannan ta ce, "wai kece kike zuba zance haka?" "Wayyo ni Amna wai ita Safna ko magana ba tayi ne?". Raheena ce ta katse mata maganar zuciyar da take da cewa, "ya jikin Ammu?" Kallon Raheena tayi ta ce, "wace Ammu?" Cikin mamaki Raheena ta ce, "Wace Ammu kuma? Ammu mahaifiyar mu mana" a zuci ta kuma cewa, "ohoo ashe sunan da Safna ke kiran Madam shine Ammu" a fili ta saki dariya kamar ɗazu ta kuma cewa, "yau dai so nake nayita ganin react ɗinki, amma kinga yadda fiskar ki ta koma kuwa?" Dariya itama Raheena tayi ta ce, "besty na kin sani farin ciki wallahi, naji daɗi da naga kina magana haka, abinda tintini nake so, nayi farinciki da dawowarki, yau dai Momy zata gane kan 'yarta". "Nima naji daɗin ganin ki ƙawata" "ƙawar ki kuma? Malama ki kirani da besty kamar da, nafi jin daɗin haka" faɗin Raheena, Amna ta ce, "indai wannan ne baki da matsala" Raheena tace, "to muje inga Ammu, tun kwanaki na zo amma Ruki ta hanani shiga, harda min maganganu marasa daɗi, ni kuwa naji haushin haka muka kaure da faɗa, saida na fasawa shegiya baki". "Kin min daidai!" Cewar Amna harda murmushi jin Raheena ta fasawa Ruki baki, har tana jin in ama itace Raheenar ai da ta faffasa mata fiska ba baki kaɗai ba. #Shin ko Amna zata ɗauki Ammu matsayin mahaifiyar ta? Zata zama ƙawar Raheena à madadin Safna? ______________________________________________________________________________________________ Part 6️⃣3️⃣▶️6️⃣4️⃣ "Kin min daidai!" Cewar Amna har da murmushi jin Raheena ta fasawa Ruki baki, hartana jin ina ma itace Raheenar ai da ta faffasa mata fiska ba baki kaɗai ba. Ruki. Tunda ta bar ɗakin Ammu ta nufi kitchen tana ƙofa, "zaki san ni kika ƙyale wato gani banza ko? Meyakamata in mata ne?" Ta faɗi tana cizan yatsa, sai kuma ta cire yatsar daga bakinta ta furta, "yauwaa!" Tana faɗi ta ɗibi ruwa cikin ƙaramin bucket ta sanya cikin freezer. Zama tayi a wurin saida ta tabbatar da ruwan yayi sanyi sosai sannan ta ciro shi ta nufi ɗakin su, sai dai bata samu Amna a ciki ba hakan yasa ta fita waje nan ta hango ta ita da Raheena, "dai dai kenan! hatta ƙawar ta ta sai ta samu rabon ta yau, shegiya dama itama haushin ta nake ji, aida nasan zata zo da na sanya ruwan da yawa" ta faɗi tana doso inda suke. Saida ta kusa zuwa dap su ƙafar daman ta ya zame, hannun ta yayi sama da bucket ɗin tayi ƙasa lapp, tun kan ta saki ihun azaban fa ɗin da tayi ruwan ya juye kanta shaa, wani irin sanga-memen nishi ta ja saboda tsaban sanyin da ruwan yake dashi, bata san lokacin da ta sake shaƙaƙƙiyar ƙa ra ba. Jin hakan yasa su Amna waigawa dan ganin abinda ya faru, ganin ta sukayi ƙasa ga jikin ta a jiƙe shakof da ruwa sai sauke wani irin numfashi take tana ƙame jikin ta, sai da suka miƙe sannan suka fara dariya a tare, dariya suke sosai wanda ya ƙara harzuƙa Ruki, ta gina ramin mugunta amma ita ta afka, da ƙyar ta iya miƙewa tana ɗingishi ta bar wurin ko bucket ɗin bata ɗauka ba, ga faɗuwa da kuma ruwan sanyin da ya jiƙa ta, sannan ga dariyar da Amna da Raheena suke mata duk ya haɗe mata haushi ya cika ta. Barin dariyar da take tayi tana kallon Amna ganin yadda rake dariya tsakanin ta da Allah, wanda ita a wurinta Safna bata taɓa makamancin hakan ba, kallon Amna take sosai. Ba ƙaramin daɗin abunda ya faru da Ruki Amna tayi ba, jin Raheena ta taɓa tane yasa ta tsagaita dariyar tana kallon ta, "kee besty! Nifa wallahi na rasa gane miki yau ɗin nan" tsaida dariyar duka Amna tayi jin abinda Raheena tace, kar dai fa tana yin abubuwa da yawa wanda Safna ba tayi, "me yasa kika haka?" Cewar Amna tana kallon Raheena, Raheena ta ce, "dariyar da naga kinyi ya ban mamaki sosai ban taɓa gani kinyi hakan ba". Kan Amna ta bata amsa wayar Raheena yayi ƙara, saida Amna ta ɗan zaro ido kaɗan ganin waya mai tsadar da Raheena ke riƙe da shi, ji tayi Raheena ta ce, "eh Momy Safna ta dawo ganinan tare da ita ma, dama ina son kiran ki ince miki sai anjima zan dawo kamar bayan azahar, yauwa Momy thank you, to shikenan zan faɗa mata" ta juyo ta kalli Amna dake kallonta ta ce, "Momy na miki barka da dawowa kuma tana gaishe ki". Murmushi kawai tayi tana faɗi a ranta, "da dukkan alama wannan ƙawar Safna ce ƙud da ƙud, ƙila zata san abubuwa da dama dangane da Safna, kuma abinda nakeson sani kenan, to amma taya zata ban labarin bayan ita a tinanin ta Safnan ce ni?". "Besty muje wurin Ammu in gaishe ta" Cewar Raheena bayan ta katse wayar ta miƙe. Bayan sun isa ɗakin Raheena ta nufi inda Ammu take kan gado, domin yadda Amna ta barta bata gusa a wurin ba, da sauri ta je kusa da Ammu ɗauke da murmushi a kan fiskar ta, durƙusawa ƙasa tayi tana yiwa Ammu gaisuwan girmamawa, amma taga yau sam Ammu ba tayi mata wani alama dake nuna ta amsa gaisuwan ba, kuma ga idon ta da ya sauya kala, "besty What's wrong with Ammu?" Ta faɗi tana juyawa kallon Amna. Matsowa kusa Amna tayi tana kallon Ammu dan ga no sanadin tambayar da Raheena tayi, "ƙila tun maganar ɗazu ne hankalin ta bai gama kontawa ba" ta faɗi a zuciyar ta, a fili ta ce, "Lafiyan ta ƙalau fa, kawai dai jikin na ta ne sai a hankali" kauda kallon da takewa Amna tayi ta maida su kan Ammu ta furta, "Ammu Allah ya baki lafiya" da ameen Amna ta amsa tana ƙara faɗin, "Raheena ina son muyi wani game dake" ta faɗi domin so take tabi hanyar da zataji labarin Safna koda kaɗan ne kuwa. Sai da Raheena ta miƙe daga tsugunnen da take tana murmushi ta ce, "faɗamin wani irin game ne?" Amna ta ce, "Let's go outside before" garden ɗin da Safna ke zama suka je wanda baida flowers dan a tinanin Amna nan zaifi yi musu daɗin labarin, samun wuri sukayi suka zauna. Kallon dogon ƙarfen dake wurin Raheena tayi tana cewa, "wannan shine ƙarfen da ya taɓa jan ki?". "Kedai muje kai tsaye akan game ɗin da zamuyi" Amna ta faɗa dan kawar da zance kar Raheena ta ƙure ta tun yanzu, "to muje ina jinki" cewar Raheena, sai da ta gyara zama ka na ta fara magana, "yauwa wasan da zamuyi shine a tsakanin mu kowa zai bada labarin kowa, yanzu misali, ni ba Safna bace idan nace ki bani labarin ƙawar ki Safna zaki iya bani?". Murmushi Raheena tayi sannan ta ce, "sosai ma! Bayan Ammu nice wacche zan bada cikakken labarin ki Safna" "to bismillah ina jinki" cewar Amna tana ƙara gyara zama da kyau, Raheena ta fara magana kamar haka, "sunan ƙawata Safiyya amma ana kiran ta (Safna) tana da ɗabi'u masu kyau da ya kamata ayi koyi dasu, bata da girman kai bata da fitina, ba ta da yawan surutu wanda wasu zasu iya kiran hakan da girman kai, saboda bata cika shiga abinda ba'a gayyace ta ba, koda kuwa an gayyace ta to bata da shishshigi, ba ta kula samari bare tayi wasu dogon magana da su" Sai da ta sauke numfashi ta cigaba da cewa, "tun tana da shekaru biyar a duniya mahaifiyarta ta kamu da wata cuta wanda ba ada tabbacin wani iri ne shi, duk da kasan cewar ta mai ƙananun shekaru amma a haka take kula da mahaifiyar ta, domin idan ba ita ba babu mai kula mata da ita, mahaifin ta ya rasu ba tare da ta san shi ba illa a hoto kawai, ya kasance mai kuɗi sosai amma ita da mahaifiyar ta suka zama marasa ga lihu a cikin gidan da suke da haƙƙi a ciki, domin kuwa na mahaifin ta ne, musgunawa iri daban-daban take fiskan ta acikin gidan su tsawon shekaru". Amna ko ƙyafta ido ba tayi a kan kallon Raheena, "kinyi mamaki da na ƙara sanin wasu abubuwan ko?" Amna da ta maida hankalin ta gaba ɗaya wajan Raheena tana jin labari, taji Raheena ta faɗi haka, amsa ta bawa Raheena da faɗin, "eh nayi mamaki amma yanzu dai ki cigaba da min bayani" tayi maganar domin ita so take ta ƙare mata labarin Safna. "Toh! Sai dai wani lokaci tana bani haushi" kan ta kuma wani maganar Amna ta katseta da faɗin, "me yasa take baki haushi?" Ci gaba da magana Raheena tayi, "duk da cewa haƙuri abune mai kyau amma na ta yayi yawa" nan dai Raheena ta sanar da ita duk abinda ta sani game da Safna. Ita da kanta Amna taji takaicin abubuwa da dama musamman yadda su Hajiya suka rinƙa musgunawa Safna amma babu abinda tayi, "amma ita wannan Safnan wace iriyar mutum ce? Sai kace babu zuciya a jikin ta" cikin zuciyarta ta faɗa, "kuma duk Hajiya da 'ya'yan ta sukayiwa Safna hakan?" Kallon mamakin da Raheena ta bita dashi ne yasa ta dabur cewa kar dai ta fiskanci wani abun ta ce "kar kimin wata fahimtar, ba ce miki nayi à misali ni wata ce ba? To shiyasa". Sai da Raheena ta ɗan share ƙwallan da yaɗan zubo mata na labarin da ta ba Amna ta kwashe da dariya tace, "nima ramawa nayi naga react ɗinki" murmushi Amna tayi ta ƙara cewa, "amma ya akayi kika san duk wannan?" "Ita ƙawar tawa ce ta sanar da ni, domin ta kura mata nayi ta bani tarihin ta bayan na bata nawa". "Da kyau gaskiya ku ɗin aminai ne na haƙiƙa" cewar Amna tana murmushi, ƙawancen n'a su ya burge ta sosai, duk da ita dasu Zarah ƙawaye ne amma bata faɗa musu sirrin ta kamar haka, "wato shiyasa nima suke min irin cin kashin da suke mata kenan? Saboda sun zata ita ɗin ce, sannan kuma cikin yaran Hajiya akwai mai matuƙar son Safna? Lallai! Amma yadda Hajiya ta tsani baiwar Allahn nan zata iya bari ta auri ɗan ta kuwa? Cab ashe akoi aiki a gabanki Amna". Katse mata tunani Raheena tayi da faɗin, "keh malama baza fa kimin wayo ba, naga kinyi shiru to nima sai kin bani labarin Raheen, ni na gama nawa saura naki" "sai da Amna ta haɗiya nyawun ta ƙa re min sannan ta ce, "shirun da nayi kai na ne yaɗan harba min shiyasa, ciwo yake min" ta faɗi domin kaucewa Raheena, domin ita ko hanyar gidan su bata sani ba bare tasan labarin ta. Da sauri Raheena ta miƙe cikin damuwa ta ɗaura hannun ta kan goshin Amna tana cewa, "sorry besty na, kuma babu alamar zafi, to ko ta ciki ne yake miki ciwo?" "Eh kamar kin sani ta ciki ne" cewar Amna harda rufe ido ita ga mai ciwon kai, "sannu! muje ɗaki ki sha magani". Zaunar da Amna tayi à kan kujera vayan sun isa ɗakin, ta nufi inda tasan Safna na ijje magun-guna ta ɗauko, "wato har ɗakin ta san shi sosai" cewar Amna a zuciya da taga Raheena ta ɗauko maganin, "ba wani matsala besty idan na ɗan rintsa kaɗan zai bari" ta faɗi bayan Raheena ta miƙo mata maganin, Raheena ta ce, "toh shikenan ki konta ɗin". Kwantawa Amna tayi gefen Ammu da ta samu damar rintsawa. "Ni zan koma, Allah ya ƙara sauƙi" "komawa kuma? Ina cewa kikayi sai azahar?" Raheena ta kuma cewa, "so nake in barku ku huta sosai, ko kina da buƙatar wani abun?" Da à ah Amna ta amsa mata, "toh shikenan besty ni zan tafi Allah ya ƙara sauƙi ki gaida min da Ammu in ta tashi" cewar Raheena tana wucewa cike da damuwa domin ba tason abinda zai taɓa lafiyar bestyn ta. Raheena tana fita Amna ta tashi ta zauna, ƙurawa fiskar Ammu ido tayi tana jin wani irin haushin su Hajiya a cikin ranta, su wasu irin marasa imani ne? Mutane da gidan su amma su maida su bayi, duk laifin Jamilu ƙanin mahaifin safna ne, duk da baya musguna musu yana ɗan basu kulawa amma ya kamata ya sai musu daraja a idon sauran" a binda ta faɗi a fili kenan cike da ɓacin rai. Bankaɗo ƙofan Hajiya tayi, take kan Amna tayi, ji kake taas taas ta sakewa Amna tagwayen maruka biyu a kumatu, a fisace Amna ta miƙe tana kallon Hajiya da tayi mata wannan marin. #Amna ta san wasu daga cikin labarin Safna yanzu, Ga Hajiya kuma ta mare ta ba ɗaya ba har biyu, kuna ganin zata haƙura? Toohh muje dai zuwa. ______________________________________________________________________________________________ Part 6️⃣5️⃣▶️6️⃣6️⃣ Guri ne mai kama da kogo, domin kuwa gaba ɗaya wurin duwatsu ne da aka sarrafa su da ƙasa, sai wasu abubuwa mai kama da na tsafi a mammane jikin bangon, da kuma rubuce-rubuce da baza kasan wani yare bane, hanyar shigan sa siriri ne sosai, kuma yana da matuƙar nisa kafin zuwa ciki bayan kona-kona masu tarin yawa, da ace wanda baisan wurin ba ya shiga tabbas zai ɓace ɓat aciki, bayan haka da ƙyar yayi awa ɗaya mai kyau ba tareda ya gommace da acikin ramin kunamu aka sa shi ba, domin yadda wannan kogon yake da matuƙar hatsari, amma idan da sanin mai kogon ka shigo to babu abinda zai sameka. Mutane huɗu ne gurfane a ƙasa cikin wannan kogon, kowannen su guiwar sa a ƙasa hannayen sa kuma a haɗe ɗaure guri guda kuma ta baya, kan su kuma a ƙol-ƙole ba gashi, yayin da jikin su keta kyarma saboda tsananin tsoro da tashin hankalin da yake ziyartan kowannen su, tunda aka nufo su wannan kogon suka kasance cikin tashin hankali, bare bayan shigan su, abinda basu taɓa gani ba, ai ko ziyara akace suyi cikin wannan kogon abin tsoro ne, bare laifi sukayi aka kawo su ciki. gurin na da sanyi sosai amma yanayin da suke n'a tashin hankali yasa gaba ɗayan su zufa sukeyi mai matuƙar yawa kai kace tsomasu a ruwa akeyi. Gefe guda kuma shugaban nasu ne tsaye, sai hular da yake kasan cewa a kansa kamar kullum wato hula mai malafa baƙi, kayan sa kuma ash colour bayan sa kuma PA ɗin sa ne Salman shima tsaye. Ɗayan gefen kuwa wani gajeren mutum ne zaune kan kujerar sa mai kamar ƙashi da kuma wasu sur ƙulle à jikin kujerar, ƙugun sa ne kaɗai da yadi jawur dogo kamar wanda ya ɗaura zani, sai wasu abubuwa masu kama da layoyi a wuyar sa da damatsan hannun sa, sai wasu irin abubuwa kuma masu kama da jigida suma a ƙugun na sa, launin fatarsa kuwa kamar ansha fa mata launin blue, sai jajayen ƙananun idanun sa mai kama da idon 'yan China, fiskar sa a tamƙe babu alamar annuri ko ɗigo kamar bai taɓa dariya a duniya ba, yanayin sa dakuma shigen gaba ɗaya yafi kama da boka ko kuwa ince matsafi. Shine matsafin dake jagorantar ƙungiyar POSPA, domin kuwa babu abinda maigida ZABBA BA yakeyi ba tareda sun bashi izini ba, sanadiyyar wannan matsafin ne ya ƙidaye wa muƙarraban sa sanya tifafin tsafi, dik abinda zasu aiwatar to shima na tsafi ne, domin ko kisa zasuyi sai sunbi dokar da Zabba ba ya ijiye musu ta hanyar bin wata hanya ta tsafi. Misali. Idan zasu aiwatar da kisa to sai suyi amfani da bishiyar da aka sihirce ta. A cewar matsafin ƙahon tsafi ne ke shan jinin ta wannan hanyar, Rukunuwan muƙarraban Zabba ba guda uku ne, kuma babu sunan da suke kiran wannan rukenin face. RUKUNIN FARKO. RUKUNIN TSAKIYA. RUKUNIN ƘARSHE. A haka kawai suke kiran su, kuma kowani Rukini an ƙawata shi ne da surƙullen tsafi, ko wanne kogo ne masarrafan su, amma fa ko kusa sunfi wannan kogon kyan gani, domin ko gurin shigar sa kaɗai ma abin tsoro ne. Mutane ti ƙa-ti ƙa ne kewaye da su, suma ƙugun su ne kaɗai da marufi, amma su na su farare ne, suma suna sanye da nasu kalar layun. Zabba ba ne ya miƙe yana kallon wannan bokan ya ce, "maganar ka ne kaɗai muke jira a halin yanzu, dan a aiwatar da abun da ya kamata" ya faɗi yana zuwa inda mutanen suke sai da ya ƙare musu kallo dukkan su sannan ya ce, "dama na riga da na sanar da ku, in har kuka kuskure min to fa bazan bari ba" ɗaya daga cikin wa'yanda ke gurfanen ya fara magana a ɗar-ɗar yana cewa, "shugaba dan Allah kayi mana rai, wallahi bamu san abin zai yi haka ba, a gafarce mu baza mu sake ba" ya kai ƙarshe yana

Chapter 16 of 56