wanda har da shi aka ture tsohon ya fara magana, "kai tsoho! Duk abin da ya faru kai ka ja wa kanka, baka da ido ne? Baka ga yadda kowa ke sauya hanya ba? Amma kai ka yi taurin kai ka biyo inda muke, to akan me ture ka da mu kayi zai zama laifi?".
Hankalin ɗaiɗai cikin mutane ya dawo kan abin da ke faruwa, duk da cewa sun san halin wa'yan nan samarin, ba sa kallon giran kowa da gashi, "kai to baka gansa tsoho tukuf ba ne? Idon ma da ƙyar in yana da shi" cewar wani daban, yana faɗi kuwa suka sake sa dariya, "ya'yana abun da ku ke yi ba abu ba ne mai kyau, kuma tsufa in dai da rai ba ku mutu ba, to dole kuma ku zama kamar ni" tsohon ya faɗi cikin haushi da takaicin abin da suka yi masa, sannan ya juya yana dogara sandarsa zai bar wurin.
Ba tare da duba tsofuntarsa ba, wani cikin su ya janyo sa baya, saura kaɗan tsohon ya faɗi amma ya samu ƙafafuwansa suka dai-daita, amma har karkarwa suke yi, "kai tsoho, wato har yi mana fatan dawowa kamar ka ke yi? Wato baka da masaniya a kanmu? Da alama kai baƙo ne ko?" Cewar wanda ya janyo sa, "ina kuwa zai sani, idan shi baƙo ne to ya kamata mu sanar da shi mu waye? Don gobe ya kiyaye" wani ya kuma faɗin haka, gaba ɗaya sauran suka zo gaban tsohon, shi kuwa tsohon kallonsu da mamaki ya ke, yadda ba su duba girmanshi à matsayinsa na tsoho.
Amna suna cikin mota, har yanzu babu abun da suka furta a tsakanin su, kamar ance ta juya idonta ya gane mata wa'yan nan mutane, su na yiwa tsoho rashin ɗa'a, domin harda amshe bakkonsa su kayi haɗi da yaddawa à ƙasa, sannan suka kwashe da dariya. Wani haushi ne ya ziyarceta, "ka tsaida mota, ka tsaida na ce!" Ta faɗi da ƙarfi ganin yana ƙoƙarin shan kona, tsaida motar Shuraim yayi cikin mamaki da yadda tayi maganar, don shi har tunani ma yayi ko so ta ke ta sauka, juyowa yayi yana shirin yi mata magana ya ga ta fice daga motar, domin yana jan birki ta yi saurin buɗe ƙofa ta fice.
Ɗaya daga cikin samarin yasa hannu don kamo ƙafaɗar wannan tsohon, da niyyar ya tura shi a cikin ruwan lambatu, idan yaso ko ƙarasa karerayewa ma zaiyi sai yayi, domin daman jikin na sa ya tsufa sosai. Kafin ya kai hannun Amna ta buge hannun na sa da ƙarfi, saurin matsawa yayi haɗi da riƙe hannunsa jin zafin da yayi masa ya saki ƙara, gaba ɗaya sauran samarin suka ƙura mata ido a mamakance, ba tare da ta bi ta kansu ba, ta komar da hankalinta kan Tsohon, cikin nuna kulawa ta ce, "Baba babu abun da dai suka yi maka ko?".
Ta ƙarashe maganar tare da duƙawa tana ɗauko masa abubuwansa da suka faɗar masa, "lafiyana ƙalau 'yata" tsohon ya amsa mata yana murmushi, wanda ta bugewa hannu ne cikin haushi da ganin har yarinyar nan ta isa da zata yi masa wannan abu, cikin ɓacin rai ya taho haɗi da hankaɗata da ƙarfi, domin da so yayi ya kai mata mari da fari, amma kuma bari ya fara da wannan. Itama saura kaɗan ta faɗi, domin bata lura da tahowar sa ba, "keh kin isa!? Wa ce ke da zaki buge min hannu?".
Tsohon ya kai dubansa gare su ya ce, "haba yara, abun da ku keyi fa ba abu ne mai kyau ba" ya faɗi yana matsawa kusa da Amna a hankali ya ƙara cewa, "babu abun da ya same ki ko?" Shima yayi mata tambayar, Ita kuwa Amna ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba, a kan taɓa ta da yayi yayin ture ta, ɗago idonta tayi cike da ɓacin rai ta ɗaura su akan wannan wanda ta bugewa hannun, gaba ɗaya dariya samarin nan su ka kwashe da shi, ganin kallon da take musu kamar wata jaruma wacche ta ke ganin zata iya taɓuka komai akan su.
Shuraim kuwa da ganin Amna ta fita da mamaki ya ce, "ohhh, wannan madam C.E.On tana caza min kai sosai, yanzu akan me zata fita haka a wani fisace? To ni laifin me nayi ne wai?" Yayi maganar tare da fitowa daga cikin motar, yana dubawa ya ga ina ma ta je domin bai hangeta ba, daidai lokacin da ta ɗauki bakkon tsohon ya ganta, girgiza kai yayi yana murmushi, sai dai ganin turata da wani ɗan iska yayi ne take zuciyarsa ya harzuƙa, fiskar nan ya haɗe ta mau, domin idan har mutumin da ya ture masa Amnarsa ya shiga hannunsa, to sai ya gane kuransa, nufan wurin ya fara yi yana huci kamar wani zaki.
Last part.
___________________________________________________
Hmmm, ko ya zata ƙarke? Shuraim ne zai yi maganin wa'yan nan 'yan iskan ko kuwa Amna? To ko dai zasu fi ƙarfin su Amnan ne?
Sannan su Ruki an shiga daga ciki, to ko zasu samu abin da suke so daga wannan auren ko yaya?.
Mu haɗu da ku a part na gaba.
Alƙalamin✍🏼 Aisha G Umar
______________________________________________________________________________________________
*🖤AMNA DA SAFNA🖤*
Part1️⃣3️⃣3️⃣▶️1️⃣3️⃣4️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Matsowa samarin su ka yi inda Amna ta ke, suna murmushin mugunta, ɗaya daga cikin su ya ce, "yammata kina da kyau, don haka ki share wannan tsohon ki zo mu dame kawai" ya ƙarashe faɗi daidai isowansa gab da ita, yana sauke kalmar ƙarshe Amna ta kifa masa wani mari lafiyya mai armashi, "aiiiii wayyo Allah!" Ya faɗi da ƙarfi yana yin gefe hawaye na fitowa daga idanuwansa, domin zafi da zugin da ya ziyarce sa.
Cikin rashin fahimta sauran suka juya suna kallonsa, ganin mace ta mare sa amma ya ke wannan ihun, "yata je ki kin ji? Ki rabu da wa'yannan yaran kawai, kar su illata ki" cewar Tsohon cikin tsoron abin da zai iya faruwa gaba, duk da cewa bai gama gane dalilin da yasa wancan saurayin yayi ihu ba, Amna bata bashi amsa ba, sai ma fara matsawa kusa da sauran da ta yi.
Ko da Shuraim ya ga abun da ya faru amma bai hana shi ƙarasawa ba, samarin nan suna kallon Amna tana isowa inda su ke, amma mamaki ta ke ba su, ko da yake tsautsayi ne yasa ta zuwa wurin, don haka za su gyara mata zama, saurin shan gaban Amna Shuraim yayi, ganin alamar ranta à ɓace, sannan kuma tana son tayi faɗa da samari ƙattai haka, domin wa'yan nan daga ganin su a dabancin ma sun yi digree, shi kuwa ba zai so wani abu ya sameta ba, duk da cewa ya san tana da ƙarfi, amma wa'yan nan suna da yawa.
Dakatawa Amna tayi tana bin Shuraim da ya tsaya a gabanta da kallo, ganin ya ɓoye ta ba m'a ta ganin gabanta, saboda tsawon da yake da shi, kasancewar idan ranta na ɓace bata iya magana, amma yau sai da ta yi ƙoƙarin ɗaga bakinta da yayi mata nauyi ta ce, "kai malam, ɗan ƙasar London! Me haka?" Karkatar da kansa yayi kaɗan inda ta ke yayi mata magana kamar raɗa yana cewa, "na'am malama mai ji da ƙarfi, to ki saurare ni ki ji, gwara ki sanpe à hankali ki koma mota ki jirani, domin hakan zai fi miki sauƙi, kin dai ga wa'yan nan ƙattin 'yan daba ne, ba irin mazan da kika saba faɗa da su ba" wani irin murmushin takaici Amna ta yi, ganin yana son ya mayar da ita raguwa.
Su kuwa samarin nan kallon Shuraim suke yi, wato shi ma zuwa yayi ya tare mata faɗa kenan? Mutanen da ke tafiya suka tsaya, wa'yanda ba tafiyar su ke ba dama idonsu na kan abin da ke wakana, wasu kuma tsoro da gudun kada abun ya ritsa da su su ka sanpe. Shuraim yana cikin yi wa Amna magana cikin raɗa, bai ankara ba wani ya dunƙule hannunsa ya kawo masa naushi a ciki, da saurin gaske Amna da ta lura da hakan, tayi saurin yin gefe haɗi da tura hannunta ta riƙo hannun saurayin.
Dawowa gaban Shuraim ta yi haɗi da murɗa hannun da ta riƙen, Shuraim kuwa baki da ido kallon Amna kawai ya ke yi, ba tare da Amna ta saki hannun mutumin ba, ta ɗago idanuwanta ta sauke su a kan Shuraim da ya saki baki yana kallonta, kamar yau ne ya fara ganin wannan jarumtar ta ta, "ni bana buƙatar tsoro! Ni ce fa Amna! Ko ka ɗauka Safna tayi rinjaye à tattare da ni!?" Ta faɗi cikin dakewa idonta babu alamar tsoro a ciki, sai ma nuna masa da tayi akan yayi kuskure da ya bari zuciyarsa tayi wannan tunanin, kauda idonta daga garesa ta yi, haɗi da dawowa kan samarin, wani irin kallo suke yi mata yanzu, wanda yake nuna bayyanar tsoro kaɗan.
Shi kuwa wanda ake juyawa hannun sai ihu ya ke sakarwa cike da azaba, yana roƙonta da ta sakar masa hannu, domin ji yake kamar zata raba masa hannun da ƙashinsa, sake masa hannun tayi haɗi da tunkuɗa shi da ƙarfi yayi baya, tare da faɗi ya saki ƙarar zafi da kuma wahala, wani ne ya kuma kawo mata hannu shima ta kame na sa, tare da juya masa da hannun baya, sai ya zamana ya juya mata baya, ƙara ya ke saki na azaba, hannunta ɗayan ta sa ta ɗan ɗaga riganta ta ƙasa, domin ta samu damar yin abin da take so ba tare da dogon rigar ya bata matsala ba, duk da cewa dogon riga take sakawa, amma bai hana ta sanya dogon wando daga ta ciki ba, domin ko ba komai hakan na da kyau, sai gashi ranar amfaninsa ya zo.
Ɗaga ƙafanta tayi ta saki hannunsa haɗi da tokare shi da ƙarfi yayi gefe, nan ta fara bi ta sauran kowa na amsan daminsa, tun da dama shi suka nema, mutuminku Shuraim mai zuwa kare Amna, sai gashi ya shiga sahun 'yan kallon da ke wurin, wannan tsohon na gefe yana ganin ikon Allah, duka Amna take musu sosai kamar ba gobe, Shuraim ganin Amna ta ƙi tasayawa, kuma tabbas dukan da takewa samarin nan suna jin jikinsu, domin babu abin da suke sai ihu da ƙara, hakan yasa Shuraim zuwa kusa da ita yana cewa, "shikenan Amna calm down know, ya kamata ki barsu haka".
Kamar ba ayi mata magana ba, ba ta bar abun da take ba, samari sai ihu suke suna ne man yafiya, "ku kuke ganin mu, mu bamu isa mu ganku ba, don Allah kuyi haƙuri mun tuba! Wallahi mun tuba,wayyooo Allah, tai makoo, tai makoooo" cewar ɗaya daga cikinsu, sauran ma suka amshe baki na rawa, sannan kuma suka ƙare da ihu, wani ma a cikin su na shirin sake magana, sai kuma ya saki ihu a maimakon abin da zai faɗa, saboda take ƙafarsa da Amna ta yi, abun ya ba mutanen da ke wurin tsoro sosai haɗi da mamaki, ganin abun da Amna ta ke yi yayi tsanani sosai, hakan yasa wasu da ke cikin 'yan kallo suke cewa, "shikenan yau sun taɓo abun da ya fi ƙarfinsu, sun taɓo aljanu gangarai ba tare da sun sani ba".
Hatta Shuraim lamarin Amna yanzu ya fara ba shi tsoro, ganin kamar ba ta da shirin barin gayun nan, to kuma kar abun yayi yawa kuma, domin ya kamata yanzu ta rabu da su, don da dukkanin alama bayan wuya harda dana sani sun yi, ashe duk yadda ya ke tunaninta ta ma wuce haka, ya rasa me zai yi ya tsaidata, domin yayi mata magana amma kamar kunnuwanta a toshe su ke, "Amna ya isa haka mana!" Ya faɗi da ƙarfi tare da sanya hannunsa ya kama hannunta da take sake shirin kaima wani bugu, janyo ta da ƙarfi baya yayi, a fisace ta ƙwace hannunta, haɗi da dunƙule shi, ta ke ta ɗaga haɗi da juyawa zata kaiwa wanda ya kuma riƙe mata hannu naushi, "a kan me zaka taɓa ni!!" Ta faɗi cikin ɓacin rai tana kai masa dunƙulin hannunta kan fiska a hasale.
Rufe ido kawai Shuraim yayi yana jiran saukan wannan naushin da ta nufo da shi zuwa fiskarsa, bayan zuciyarsa ya dakata na wucen gadi, tsayawa cak da hannunta tayi saura kaɗan ta takai jikin fatar fiskar ta sa, ba komai ne yasa ta wannan dakatawar ba, sai fiskar Shuraim da ta gani, don à tunaninta wani ne can daban, a hankali Shuraim ya fara buɗe idanuwansa jin abun da ya ke jira bai faru ba, yana buɗe idanuwan suka sauka a kan jajayen idanuwan Amna, kallon-kallo su ke yi à tsakaninsu, Amna kallon Shuraim ta ke kamar mai shirin tuna wani abu, sai daga baya kuma ta zare idanuwanta daga cikin na sa, tare da juyawa tana ganin gayun da babu abin da suke yi sai ƙara.
Ihu suke sosai kowa sai alhinin jikinsa ya ke yi, maganar dana sani ma ba a yi ba, domin tun kan komai yayi nisa su ka riga yin haka, roƙon Amna suke yi sosai, akan ta taimaka ta ya fe musu, baza su ƙara aikata abun da suka yi ba, saboda gani su ke kamar yadda ta ke kallonsun nan to sake dawowa kansu da duka zata yi, mutanen da suka taru suna kallon abin da ke faruwa, ta ke su ka fara zabga tafi, na jin daɗi da kuma jinjinawa na mijin ƙoƙarin da Amna ta yi, saboda karanbattan da ta sha a kan 'yan iskan da suka addabi rayuwarsu, a yanzu sun fahimta ba wai aljanu ba ne, kawai dai baiwa ce daga Allah, juyawa kawai Amna ta yi tana kallon masu tafin kamar bata san abin da tayi ba.
ƙarfin hali da kuma tsoron kar Amna ta sake dawowa garesu, suka fara jan jiki suna barin wurin da ƙyar da kuma ɗingishi cike da tsoro, , magana Shuraim yayi wa Amna a kansu su tafi yanzu to, nan ma bata ba shi amsa ba, sai ma wurin tsohon nan ta juya don ta je inda ya ke, ahankali mutane suka fara barin wurin ganin komai ya ƙare, kowa da abun da ya ke cewa, wasu mamakin ƙarfin Amna, wasu kuma farin ciki da abun da tayi wa samarin nan, domin sun addabesu sosai, dama babu yadda suka iya da su ne.
Ɗaga sandar Tsohon da ke ƙasa Amna ta yi ta miƙa masa cikin girmamawa, sannan ta riƙe buhunsa a hannu, sai dai bata ce da shi komai ba, hatta fiskarta ma bata sake ba, saboda har yanzu zuciyarta na cikin ɓacin rai, cikin farin ciki da abun da Amna tai masa na girmamashi da kuma yin faɗa saboda kare masa mutuncinsa, hakan ba ƙaramin farin ciki ya sa shi ba, cikin muryarsu na tsofaffi ya dubeta tare da murmusawa sannan ya ce, "na gode miki sosai 'yata, kin taimake ni kuma kin kare min ƙima ta, kin nuna wa masu so su wulaƙanta ni, cewa ni ba abin wulaƙantawa ba ne".
Girgiza masa kai kawai Amna tayi ba tare da yi ce komai ba, "mu je Baba, sai mu rage maka hanya ka ƙarisa gida" cewar Shuraim bayan ya matso kusa da su, tsohon ya amsa da cewa, "a ah kar ku damu 'ya'yana, ai ni na kusa isa gida, nan nan ne ba nisa, ba sai kun sake wani shan wahala da ɗawainiya à kaina ba, kar ku damu ku yi tafiyarku, na gode Allah yayi muku albarka" da Ameen Shuraim ya amsa sannan Amna ta miƙa masa ƙullalliyar buhunsa, ya amsa yana kara godiya, sannan suka juya zasu wuce.
Tsaida su tsohon yayi da cewa, "ku ɗan dakata kaɗan yarana" Juyowa su kayi suna kallonsa, yayin da shi kuma ya sauke baƙar buhun nan na sa ƙasa, sanna ya zura hannunsa ciki bayan ya kunce, sai da yayi lalube kaɗan, tukunna ya fito da wani zobe daga cikin buhun, miƙawa Amna yayi, cikin rashin fahimta ta amsa zoben, da mamakinta ta ji nauyi tattare da zoben, saɓanin irin zoben da ta sani, kallon zoben ta ke ta yi, kolliyar saman zoben kamar diamond ya ke, fari ne t'as babu alamar wani launu a jiki, da alama ma sabo ne fil, domin sai shining ya ke yana ɗaukar ido.
Juya zoben Amna ta fara yi tana sake kare masa kallo, shima Shuraim ɗin abin da ya ke yi kenan idon sa na kan zoben, mayar da kallonsu kan Tsohon su kayi alamar suna neman ƙarin bayani, "wannan zoben yana da amfani sosai, kuma na tabbata zai amfane ku, ko yanzu ko wani lokaci, shine ka ɗai abin da nake da shi, wanda zan iya saka muku da abun da kuka yi min" yana yin maganar ya rataya buhunsa a baya sannan ya wuce, Shuraim ne ya buɗe baki yayi masa godiya, Amna kam da kallo kawai ta bisa, domin zata iya cewa bata gane me ya ce ba,
Shuraim ne ya tsaida kallon da ta kewa Baba tsoho da faɗin, "Muje koh?" Ɗauke idonta ta yi daga kan Baba da ya fara nisa da su, sannan ta juya ba ta ce da Shuraim komai ba.
Har suka isa company Amna taƙi buɗe baki ta yi magana, wucewa office ɗinta tayi kai tsaye, ana gaisheta amma ta ƙi amsawa, tana isa ta zauna a akan kujera, yadda take ji a zuciyarta ita ma da kanta bata sani ba, shin saboda faɗan da ta yi ne? Ko kuma saboda me? Ita ma bata sani ba, zoben da ke riƙe a hannunta ta ɗago tana sake ƙare masa kallo kamar mai neman abu a jiki, sai kuma ta miƙe haɗi da ɗage doguwar rigarta ta sanya zoben à cikin aljuhun wandonta.
Bayan ta sauke rigar ta juyo da kanta ƙofa jin sallama haɗi da buɗewa, bakinta ko amsa sallamar bata yi ba, sai dai ta amsa cikin zuciyarta, Shuraim na shigowa ta kauda kanta a kansa, sannan ta zauna cikin rashin nuna kula, "me yake damunki Amna? Da na ɗauka saboda baki so in ɗauko ki ba ne shiyasa kike fushi, amma yanzu na kasa gane miki, to ko don abin da ya faru akan hanyar zuwan mu ne?" Cewar Shuraim bayan ya iso gaban table ɗinta, domin rashin kula san da ta ke yi ya fara damunsa sosai.
Bakinta da take jin sa da nauyi sosai ta buɗe tana cewa, "wai kai me damuwarka? Me cece damuwarka da sai na tanka ka!?" Ta faɗi da ƙarfi tare da ƙure sa da ido, kamar yau ne ranar gamuwanta da shi na farko, da mamaki ya zagayo in da ta ke zaune, ya ce, "ni masoyinki ne! Dole na damu da duk abin da ke damunk..." Kafin ya ƙarisa Amna ta miƙe suna facing ɗin juna ta fara magana cikin ɓacin rai, "wannan sunan zai fi kyau ka daina ambatarsa, saboda a yanzu babu wannan alaƙar a tsakani na da kai, a yanzu! Yazeed shine wanda na ke so, kuma shi zan aura, idan ba mantawa kayi ba ka riga da kaji wannan kalaman, saboda kai ka zaɓarmin hakan da kanka!".
Wani irin suka ya ji da wannan maganar, shima cikin fisata ya fara cewa, "Yazeed ba zai taɓa zama..." sai kuma ya dakata da maganar, sakamakon kira da ya shigo wayarsa da ke aljuhu, zarosa ya yi don ganin wa ye mai kiransa, domin dama yana dakon kiran a ko wani lokaci, ganin numbern da dama shi yake dako ne yasa ya fiddo Ido kaɗan, sannan ya maida kallonsa kan Amna, ganin tana ƙoƙarin sa idonta kan wayar ne yasa shi saurin katse kiran, domin baya son ta gano wani abu, sannan ya dawo da kallonsa gareta, kawai kuma sai yayi saurin juyawa ba tare da ya ƙara wata kalmar ba.
Binsa tayi da magananta har ya fice, yana fita ta sauke kanta kan table, sannan ta koma ta zauna, cikin rashin nutsuwa, amma yadda ta ga ya katse wayar, da kuma kallota da yayi, sannan kuma yadda ya wuce da sauri, haka kawai sai ta ji zuciyarta ya ɗarsa mata ayar tambaya a kansa, don haka ta miƙe tana tunanin ko dai ta bisa ne?.
Shuraim yana fita bai tsaya a ko ina ba, sai a can wani gefe a companyn, yadda zaiyi waya ba tare da kowa ya gansa ba, da sauri ya ɗago wayar yana shirin kiran wanda ya kira shi, sai kira ya kuma shigowa cikin wayar, da sauri yayi piking ya n'a karawa à kunnensa da cewa, "ina jinka Ali, ya maganar binciken?" Daga can gefen wanda aka kira da Ali ya fara cewa, "MR mun gama gano komai yanzu, duk da munsha wahala, amma abun ba ƙaramin mamaki ya bamu ba, saboda...".
"look Ali! Kawai abin da na ke so da kai yanzu, ka tafi kai tsaye kan maganar, ba na son wani surutu, ka bari inyaso daga baya ka min sauran sharhin" Shuraim ya faɗi domin ba wannan ne abin da yake so ba, kuma ya san Ali, idan ya barshi haka zasu ɗau dogon lokaci yana yi masa bayani, ba tare da yaji abin da ya ke so ba, "shikenan MR, bayan dogon binciken da muka yi, mun gano wannan mutumin yana rayé, bai mutu ba" ka fin Ali ya kamo wata maganar Shuraim cikin ƙaguwa da mamaki don tabbatar da abun da Ali ya sanar da shi, yayi saurin cewa, "kana nufin mahaifin Amna yana rayé!? Mahaifin Amna bai mutu...!" Ƙarar faɗuwar abu da yaji daga bayansa ne, yasa shi saurin juyawa a firgice.
Yana juyowa idonsa ya gane masa Amna, da ta saki wayar da ke hannunta ƙasa, har sai da wayar ta fashe saboda buguwan da tayi, manyan idanuwan nan na ta suka sake girma kamar ka zura hannu ka fiddo su, duk da cewa har yanzu ba su dawo fari t'as ba, gaba ɗaya jikinta ya kama rawa, hatta bakinta kyarma ya ke, da ƙyar ta iya haɗa haruffa, cikin tashin hankali da maganar da ya shige cikin dodon kunnenta, ta ce, "ii... mm... me... na ji... kana magana... a kai Shuraim?" ......
Last part.
___________________________________________________
To fah, wata sabuwa😳 wai Baba bai mutu ba! Tooo, me kuka yi tunani? Baba bai mutu ba? Tayaya? Ya a kayi? Shin da gaske ne ko kuwa?
Sannan ga Tsoho ya ba Amna zobe, to ko amfanin me zoben zai yi musu? Gayu dai anji jiki.
To ko wace suya za'ayi?
Mu kasance a next part in Allah ya kaimu.
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣3️⃣5️⃣▶️1️⃣3️⃣6️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Kallonta ya ke yana ji ina ma a kwai hanyar da zai bi don kada ta fahimci komai, amma ina ta riga da ta ji, zuwa gabansa Amna ta yi tana kallonsa, yayin da jikinta yake ɓari sosai, ƙafafuwanta suka kasance marasa nauyi a gareta, cikin sassarfa kamar mara gaskiya Shuraim ya ce, "Amna, ya à ka yi, ki ka fito?" Ba ta amsa masa tambayar shirmen da yayi ba, sai ma tambaya da ta ɗora masa, muryarta cikin rashin ƙwari ta fara magana da inda-inda tana cewa, , "Ka sanar da, ni, da gaske mahaifina, Baba n'a, kuma komai na, yana rayé? Da gaske ne abin da kunnuwana suka jiye min daga bakinka?" Tana ƙarashe maganar ƙwalla ya cika mata ido, yayin da suke rawar fitowa.
Shiru yayi ya n'a tunanin abin da zai ce mata, amma to me amfanin ƙarya? Kawai gwara ya fito fili ya tabbatar mata, cikin dauriya ya giɗa mata kansa, alamar eh da gaske ne abun da kika ji,
Harbawa zuciyarta ya yi, tare da yunƙurawa zata faɗi, yayi saurin zuwa gareta don ya tarbota, ba tare da ya riƙe tan ba ta samu ƙafafuwanta suka tsaya, sannan ta samu damar jingina da ganin da ke gefenta, wani irin yanayin farin ciki da mamaki ne ya fara ratsata, wa'yannan hawayen suka zubo yaraf kan kumatunta, cikin muryar da ke
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 56