Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
maka dining ɗin ko, saboda idan ka kammala ka samu hutu, kamar Shuraim ba zaiyi magana ba, sai kuma ya ce, "I prefer she takes me there" yanzu ma ya faɗi yana kallon ta, haɗe fiska kaɗan tayi tana yi masa kallon ka raina min hankali, kan tayi magana Dady ya ce, "'yata ɗan zo kaɗan". Gefe sukayi shi da Amna yana cewa, "don Allah kar ki ɓatawa wannan yaron rai kinji? He's my special guest, ki gabatar masa da abinci cikin girmawa, sannan ki nuna masa ɗakin nan na gefen hanyar can cikin kulawa, I’d love for Shuraim to feel happy and comfortable in this house, kin ji 'yata?" ya faɗi yana nuna mata ɗaki da yake ɗayan gefen, ba hanyar da ɗakin Ammu yake ba, a jiyar zuciya Amna ta sauke bayan ta gama jin maganar Dady, murmushin zanyi hakan tayi masa, sannan suka dawo. Murmushin da iyakar sa fatar baki tayi masa, sannan ta ce "can we go to the dining now?" Ta faɗi cikin dauriya saboda ba ƙaramin girma maganar yayi mata ba, don ta ga kamar so yake ya maida ta baiwar sa, ai kuwa gwara ta taka masa birki, idan ma don abinda ya faru ɗazu ne yake mata haka. Ta fiya ta farayi yana binta baya, taku yake kamar baya son taka ƙasn, kuma hankalin sa na kan wayar sa, sai ɗan ɗago kan sa da yake kaɗan, Amna kam sai tayi gaba sai ta juya ta ganshi a baya, yana tafiya kan tayis kamar wanda aka sa dole, "lallai, kuma wai Dady cewa yayi in basa kulawa, abin da ba zaiyu ba kenan" ta faɗi tana hararan inda yake, a haka har suka ƙarasa dining. Juyawa tayi ta ga babu alamar Dady a wurin, don yanzu bata hango shi kamar ɗazu, hakan yasa kafin ya kaiga zama a kan kujerar wurin ta furta, "kai malam" ba tare da ya kalle ta ba ya zauna a kan kujerar, hakan da yayi kuwa ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, matsowa kusa da shi tayi ta ƙara faɗin, "kai Malam da kai fa nake" ta faɗi da ƙarfi, ɗago idon sa yayi yana kallon ta ya furta, "are you talking to me?". Ya faɗi yana kafe ta da ido, cikin haushin tambayar renin wayon da yayi mata ta ce, "who else do you think I'm talking to? Of course you!" Murmushin gefen baki kawai yayi yana kallon ta yadda take masa magana kamar wata isassa. Fiska da murya cikin gargaɗi ta fara cewa, "ka ga Malam! Kada abun da ya faru ɗazu ka ɗauke shi a zuciyar ka, saboda naga sai wani take-take kakeyi, ni banyi kama maka da wanda zata yi soyayya da kai ba, idan ma don wannan ne kake nuna wani hali, to yafi maka tun wuri ka sani ni ba wacche za'a raina bace, don bazan ɗauki hakan ba" dariya ta bashi hakan yasa ya miƙe yana duban tsawon ta da murmushi ya ce, "Da gaske ba kyason raini jaruma?" Daga idon ta tayi tana kallon sa yadda fiskar ta yake ƙasan kan sa, don ya fita tsawo, "ni dai na faɗa maka" ta furta kawai tayi hanyar tafiya, "a ah Safna har Ya gama cin abincin ne?" Cewar Dady daya taho wurin, "a ah Dady dama zuwa zanyi in ɗan huta, saboda a gajiye na dawo" ta faɗi don baza ta iya tsayawa da wannan dogon ba. Alamar mantuwa Dady ya nuna sannan ya ce, "Oh i forgot, kinga na manta da yau kin fara zuwa company, kuma nasan kin sha aiki a can, to kije ki huta 'yata" "thank you Dady" ta faɗi tare da sakin murmushin jin daɗi ta wuce, amma wannan bawan Allahn yana da fahimta sosai. Zama Dady yayi kan ɗayan kujerar yana cigaba da sakewa Shuraim fiska ya zauna don ya taya shi hira. Amna kuwa tana zuwa ɗakin ta tarar da Ammu kan darduma, ɗaki kuma Jummala ta ƙara tsabtace shi kamar yadda tace mata, ijje jaka da mayafin ta tayi, ta shiga toilet dan watsa ruwa. Dady. "Eh ta fara zuwa company dan gudanar da aiki, a matsayin ta na C.E.O" cewar Dady, sai da Shuraim ya jin jina kai ka na ya ce, "But why would you give her such a position when she’s still so young? The job will be too hard for her." "Yes that's right, amma idan ba damuwa ko zan iya roƙan alfarma a wurin ka?" Cikin mamaki Shuraim da hankalin sa yake a waya ya dawo da hankalin sa gun Dady ya ce, "alfarma wani iri!?" Ya faɗi cikin ƙasaita. Sai da Dady ya ji nauyin maganar da ya ke son yi masa sannan ya fara faɗin, "tun da ka sanar da ni cewa, aikin da kazo yi ba yanzu zaka fara ba, shine nake neman alfarma akan kayi aiki a company na, a matsayin rage lokaci, amma kafin kace komai Shuraim, please don’t take my words as disrespect toward your position." Ya faɗi cikin sanyin murya don Shuraim ya amince, idan har ya samu wannan damar to kamar wata hanya ce ta samun muradin sa akan mahaifin Shuraim ɗin, shiru Shuraim yayi kamar mai nazari sannan ya ce, "ok i understood, so there's no need for me to think, if you want i can start from tomorrow" ya faɗi cikin nuna alfarma yayi wa Dadyn. Shi kuwa Dady wani irin farin ciki ya gauraye masa zuciya, duk da yanayin maganar da Shuraim yayi masa, amma ya san yana da sauƙin kai, da alama ya fara irga damar sa, "thank you so much my son, I'm so happy, n'a ji daɗi da ka karɓi alfarmata, kuma har zaka iya farawa daga gobe, amma na gode" Shuraim bai amsa ba. ƘARFE HUƊU. Ruki ce ta sauko ƙasa tana tafiya kamar wacche aka yiwa dukan tsiya, sabida har yanzu jikinta cikin tsami yake mata, kallon Dady tayi da ke ta hira à waya, da alama da wannan abokin na sa na London yake waya, zuwa tayi ta zauna kusa da shi, fiskarta alamar shogoɓa, dai dai lokacin Dady ya sauke wayar daga kunnen sa, duban ta yayi yana faɗin, "my Autah me yake damunki ne?" Sai da ta sauya fiska ta ce, "Dad kawai wani zazzaɓi ne ya kamani, but da sauƙi yanzu". Cikin kulawa ya kuma cewa, "Oh sorry dear, ko zamu je hospital ne?" "No Dady, na ji sauƙi yanzu" ta faɗi don tasan babu buƙatar zuwa asibiti, iyaka dai ta sha maganin tsamin jiki. Shuraim ne ya taho falon cikin wannan takun n'a sa na ƙasaita, tun da Ruki ta ga tahowar sa ta saki baki tana kallon wannan balaraben, duk da cewa ba baƙonta bane kallon mai launin fata haka, bisa tayi rayuwa a ƙasar wajen itama, amma wannan ya burgeta sosai, "ki rufe bakin ki mana Hajiya Ruki" cewar Amna bayan ta taho wurin bayan kiran da Dady yayi mata, sai kuma ta ga Ruki nawa Shuraim kallon ƙurilla, juyowa da sauri Ruki tayi gun Amnan tana haɗiye wani nyawun tunowa da abin da tayi mata. Zama Amna tayi dai dai da zamar Shuraim shima a gefe, da wannan halin na sa na rashin kula, sakewa Dady murmushi tayi haɗi da sake gaishesa, amsawa yayi da murmushi shima, sannan ya gabatar da Ruki gun Shuraim, barin wurin Ruki tayi, don ita harga Allah ba ta ƙaunar ta haɗu da Amna yanzu, juyowa Dady yayi gun Amna ya ce, "yata kasancewarki sabuwa a fannin company, kuma kike da babban matsayi, naga ya kamata ki samu wanda zai taya ki da kuma nuna miki yadda zaki gudanar da aikin ki cikin ƙwarewa". Jin jina kai Amna tayi don ya kamata ta samu hakan ƙwarai, saboda ta san yadda zata gudanar da komai cikin kulawa, "hakane Dady, zanyi farin ciki da haka" cewar Amna, sai dai fa tun da ta zauna ko kai idon ta batayi inda Shuraim yake ba, Dady ya cigaba da cewa, "na ji daɗi da kika fahimta, saboda haka na roƙi alfarmar ɗana Shuraim, kuma ya amince, harya bani tabbacin gobe zai fara". Amna da tun da Dady ya ambaci sunan Shuraim ta zaro ido, ta katse numfashin sa da faɗin, "Dady wani Shuraim kake magana?" Sai da Dady ya juya gurin Shuraim yayi murmushi sannan ya dawo da kansa gun Amna da murmushin ya ce, "Shuraim dai wannan 'yata, kuma na tabbata zai baki gudunmawa kafin ya bar aikin" kallon Shuraim tayi, ya sakar mata murmushin cikin baki, haɗe masa fiska tayi ta maida kallon ta ga Dady, kiran da ya shigo wayar Dady ne yasa ya furta, "excuse me" ya faɗi yana barin wurin da sauri. Juyawa Amna tayi zata wuce cikin ɓacin ran rashin daɗin abin da Dady ya faɗa, "da alama kina da girman kai 'yammata" taji muryar Shuraim bayan ta, juyowa tayi tana kallon sa da mamakin furucin na sa, miƙewa yayi yana kuma cewa, "don kin samu zan taimaka miki kike wani ɗagun kai? Amma nayi mamaki da kika kasance mai hali biyu" yayi maganar yana kallon inda take, ba tace da shi komai ba sai kallon sa da take kawai, shi kuma ya cigaba da cewa, "Then listen to me! Kar ki ɗauka zaki iya sake yin amfani da ni kamar yadda kika aikata, wai don ki tsira da mutuncin ki à gaban wani, I'm not a liar" Shima yayi mata maganar cikin gargaɗi, matsowa à hankali tayi wurinsa, cikin mamaki da kuma haushin kalaman sa ta fara magana itama cikin n'a ta salon, "dama a tunanin ka ni ɗin nayi arha har haka ne? To bari kaji, kar ka ɗauka don na gwada amfani da kai, zan zamo wata ballagazar mace a idon ka! Kamar yadda na faɗa maka da fari, nayi amfani da kai ne kawai a matsayin mafita gareni, idan ba haka ba me zaisa nayi mu'amala da mutum irinka? mai girman kai! Kuma don ance zaka taimaka min a company ba shi ke nuna zan buƙaci wata taimako daga gare kaba! Saboda bazan taɓa yin hakan ba". Tana ida maganar ta kuma juyawa zata wuce taji ya kuma cewa, "tabbas zaki buƙaci tai mako na Safnah!" Ya faɗi da yaƙini, "never!" Ta furta ba tare da ta juyo ba ta wuce abun ta. Tana isa ɗaki ta zauna kusa da Ammu tana cewa, "Ammu kina jin wani abun ɓacin rai? wai sai da Dady ya roƙe shi akan ya taimaka min! To akan me? Ni wallahi da ma ya barni nayi abu na a haka, wai Shuraim ne zai taimaka min akan aikin company, wani abun ɓacin ran ma wai alfarma Dady ya nema, wannan ai sai ya raina ni, dama gashi da wani girman kai!" Ta faɗi cikin masifa, Ammu kam jin ta take kawai, ba tare da ta fahimceta ba, saboda da sauri take yin maganar, haka ɗazu ma ta zauna tana yi mata magana kuma ta fahimta, harda ɓacin rai yake sa ta sauri a magana wani lokaci". Shuraim kuwa murmushi ya saki bayan tafiyar ta ya koma kan kujera. DARE. Dady ne zaune da Hajiya suna tattaunawa, "Hajiya kamar yadda nace miki, inason ki san yadda zakiyi ki shawo hankalin Auta na, ta faɗa soyayya da wannan yaron da kuma sa shima yaso ta" Cewar Dady cikin nunawa Hajiya manufar sa akan wannan haɗin da yake so, murmushi ta sakar masa ta ce, "indai wannan ne kar ka damu Alhaji, saboda ita da kanta ɗazu take sanar dani cewa ya burgeta, to kaga kuwa ai abun yazo da sauƙi, tun da ka sanar da ni tagomashin da zamu samu akan mahaifin yaron nan nake kwana da tunani, don haka kabar min komai a hannu na" "toh shikenan, inajiran jin sakamako mai kyau". WASHE GARI. Zaune suke suna breakfast, Amna ko kamar ɗure ake mata haka take cin abincin, saboda yadda Shuraim ke binta da murmushin gefen baki, hakan kuwa ba ƙaramin ɓata mata rai yake ba, hakan ne ma yasa take wani cin abin ci kamar dole, ai kuwa yayi sa'ar Dady na kusa da ya sani. Shi kuwa cin abincin sa yake kawai cikin natsuwa, Ruki kuma sai kallon sa take, su Saleem da Marwan kam suma haushin suke ji, ba don komai ba sai don maganar Dady akan su ba Shuraim respect. Ko dake bai kamata Marwan yayi fushi ba ma, tun da auren sa ya kusa, zai rabu dasu kaɗan, ko da bamu san à ina zai zauna ba. Dady ya ce, "my son idan ka kammala kuma ka shirya sai in haɗa ka da drivern da zai rinƙa kai ka, "ina ga ba wata matsala bace idan na tafi da Safnah" ya faɗi kansa ba gun Amna ba, don da ya ga wani irin kallon takaici da tayi masa, amma babu wanda ya lura da hakan, shi kuwa Dady farin ciki ne yayi masa yawa, sannan ya ce, "to shikenan yadda kake so". Miƙewa Amna tayi alamar ta ƙoshi, ta bar wurin. Shirin zuwa aiki taje tayi, da sauri ta fito saboda so take kar ta haɗu da kowa, bare Dady ya kuma cewa tare zasu je company da wannan Shuraim ɗin. Sai dai tayi rashin sa'a domin kuwa daidai fitowar Dady da Shuraim ɗin ta fito falon, fiskewa tayi wai don tayi kamar bata gan su, "'yata ya kike sauri haka?" Cewar Dady, tsayawa tayi ba tare da ta juya inda suke ba. "Oh shit!!" Ta faɗi cikin ranta. Ya kuke tunanin takun-saƙan da ya fara kasancewa tsakanin Amna da Shuraim? Kuna ganin Amna zata amince da tafiya tare da Shuraim zuwa company ? Ya zata kasance a company tsakanin Shuraim da Amna? Muradin Alhaji na Shuraim ya faɗa soyayya da Ruki zai yu? Hakan zai faru? 'Yan uwan arziƙi, Aisha G Umar taku {Mrs Umar} 👸🏽za ta bayyanar muku da komai, ___________________________________________________________________________________________________________ Part 9️⃣3️⃣▶️9️⃣4️⃣ "Oh shit!!" Ta faɗi cikin ranta, ƙara magana Dady yayi, "eh 'yata?" Juyowa tayi ta sakar masa murmushin ya ƙe tana cewa, "ai Dady wai so nake na isa gurin motar da wuri" "ok ai ga Shuraim ɗin ma ya shirya, sai ku tafi kunji?" Cewar Dady ya kuma juya da duban sa ga Shuraim ya ce, "na gode sosai Shuraim ɗana, Allah ya taimake ka ya biya maka buƙatun ka" "ba bu buƙatar kayi min godiya, saboda nima gurin rage lokaci na samu, ni ba mutum mai son zama a wuri ɗaya bane". Ta fiya Dady yayi ya bar su a tsaye a wurin. Wucewa tayi tana wani turo baki, shi kuwa bin bayan ta kawai yayi, sai dai yadda take tafiya da sauri yasa shi saurin shima, yana bin bayanta, driver ya buɗe mata ƙofar baya, amma ta nufi mazaunin gaba, da mamaki drivern ya bita da kallo, duk da ba mazaunin tuƙi ta nufa ba, Shuraim ya fiskanci ba ta son su jera ne yasa take son zama a gaba, hakan yasa kan ta ƙarisa ya ce da ita, "Your are more suited to being at the back like a Queen". Juyo tayi ta ɗan harare shi ta ce, "sai kuma aka yi rashin sa'a ni ba sarauniyar bace ba, ni C.E.O ce!" Murmushi mai ƙara ya saki ya kuma cewa, "C.E.O na ƙauye dai ko?" Ba ta amsa masa ba ta shige motar, juyawa yayi ya kalli driver ya fara yi masa magana cikin isa. "Zauna a baya ni zan ja motar, sai ka rinƙa yi min kwatancen hanyar" kafin driver yayi magana Shuraim ya buɗe mazaunin driver ya zauna, shi kuma drivern ya shige bayan motar, "me haka kuma?" Cewar Amna ganin Shuraim ya zauna mazaunin driver, "a matsayi na na assistance ɗin C.E.O bai kamata na zauna a baya ba, ko ki nada matsala da hakan ne?" Yayi mata maganar tare da yiwa motar key. Fiskar ta na kan hanya tana faɗin, "Kar ka ɗauki kan ka awani babban matsayi, domin nice shugaba a nan" ya bata amsa da, "wannan kam kar ya saki damuwa Madam C.E.O, ni dai kawai mai taimakon ki ne" Juyowa tayi ta dube shi ta furta, "Allah ya kiyaye! Kuma kar kasa na sauka a motar nan, don zan iya takawa da ƙafa ta" ta faɗi haɗi da haɗe hannayen ta don haushi, "amma da an buga jarida akan C.E.On da tayi tafiya a ƙafa har company" driver ko jin su kawai ya keyi da mamakin abin da yasa suke wannan cacar bakin, duk da dariya m'a suka bashi. Babu wanda ya ƙara magana har suka isa company, Shuraim yana yin parking Amna ta fito ko juyar da kan ta gurin batayi ba, mutane na ta bata girma cikin gaisuwa, amma ba wanda ta amsawa sai direct office ɗin ta da tayi, wasu na biye da ita amma ganin babu wanda ta kula yasa su barin ta ta sarara kafin suje inda take. Ijje jakar ta tayi tana sauke numfashi, da tunanin me zataiwa wannan mutum ta rabu da shi ne? Domin kuwa ta san aiki da shi bazai taɓa yuwwa ba. Ɗaya daga cikin réceptionist ne ta shigo cikin office ɗin, da neman izini da shigowar da tayi duk lokaci ɗaya, kallonta Amna tayi ta fara faɗin, "It seems you should first send me a request, and only after i grant permission can you come in, right? Amma me yasa ba kiyi hakan ba?". Cikin girmamawa da risinar da kai irin wanda ake yiwa shugaba, réceptionist ta ce, "I'm sorry ma'am, I already sent it to you, and i saw you didn't say anything, and the files i brought you are important, akan meeting ɗin da kike da shi gobe" shiru Amna tayi, don ta ji ƙarar shigowar massage à na'urar amma bata kai hankali ba, ce mata tayi ta ijje akan tebur kawai, sannan ta ɗora da cewa, "nan gaba bana buƙatar hakan ya sake faruwa, make sure I give you permission before you enter" amsa mata da zata kiyaye insha Allah tayi sannan ta wuce. Bayan Réceptionist ta fita, Amna ta fara duba files ɗin, lokacin Shuraim ya shigo da sallama, kallon sa tayi cikin haushin shigowa office ɗin da yayi, files ɗin tasa hannu zata ɗauka kawai ɗaya ya kauce zai faɗi, Shuraim da yake kusa yayi saurin du ƙawa ya ɗauko shi kan ya kaiga taɓa ƙasa, "Relax, take things easy and do everything with calmness, ko da yake ba damuwa you have a helper" ya faɗi da murmushin da Amna take ɗaukar sa rainin wayo yake mata. Ƙwace files ɗin tayi, ta yadda shi à ƙasa, sannan ta ɗauka ta juyo ta dube shi ta ce, "i don't really need any assistant!" Ta faɗi tare da zama, "tayu ke baki san waye ni ba, shiyasa kike sakaci dani, amma maganganunki sun fara sani nishaɗi mai makon haushi, can you tell me why?" Ɗago idon ta tayi tana kallonsa ta ce, "kai malam can you let me do what brought me here?" Sai da ya zauna a kan kujerar gefen ta ya ce, "absolutely, why not?" Bata kuma tanka masa ba sai duba files ɗin da take ckkin rashin sakewar kasancewar sa a wurin. Shi kuwa Shuraim shima ɗaukar wasu yayi yana dubawa, "Oh you have a meeting tomorrow!" Faɗin Shuraim ita ko binciken ta kawai take. Haka suka ɗauki awa ɗaya, suna nazarin files ɗin, kirar da ya shigo wayar sa ne yasa shi tashi daga inda take yana faɗin, "Madam C.E.O let me pick up the phone" yayi maganar yana wucewa, Dogon numfashi Amna ta sauke bayan ta bisa da ido har fitar sa, "Oh Allah wannan zai barni na sakata na wala kuwa?" Ta faɗi a fili haɗi da ƙara maida hankalin ta akan files ɗin da take dubawa. Massage ne ya shigo na'urar da ke gefen ta, taɓawa tayi taji tambaya, "Madam would you like some cofee,tea, or maybe something else to lift your mood while you work?" Murmushi tayi don taji daɗin haka, batayi tunani ba amma yakamata ta samu wani abun taɓawa yayin wannan duba files ɗin, saboda suna da yawa, ga na jiya bata gama dubawa ba, ga kuma na yau, sannan harda wani taro wai gobe, ba ma wannan ne damuwarta ba, matsalarta shine akan abin da za'a tattauna, ita kuma har yanzu bata ƙarasa kamo bakin zaren ba, bere ta san abu nagaba da zata yi, "sure i need some coffee" ta basu amsa, suka bata amsa da babu jimawa za'a kawo mata. Bai ɗau minti biyu ba aka shigo mata da coffee ɗin, nan da nan ta take sa, ai kuwa taji daɗin sa, nan ta basu order akan tana buƙatar wani. Bayan kusan rabin awa da yayi a waje, ya dawo cikin office ɗin, zaro ido yayi ganin kofunan coffee guda bakwai jere, zuwa yayi ya zauna yana bin su da kallo da alama ma ta gama da su, cikin zolaya da dariyar da ta bashi ya ce, "Da alama dai wannan C.E.O ce ta daban, kai kai amma ta iya shan coffee, but ya kamata tasan C.E.O bawai ga suna kaɗai ya ta'allaƙa ba". Kallon sa tayi da kuma bin kofunan da ido, ba makawa ita ta handame wa'yannan kofi bakwan reeras, dawo da idon ta gareshi tayi tana cewa, "da alama wannan ɗan ƙasar London ɗin ya iya hausa fiye da tinani, sannan kuma ya cika sa idon tsiya" dariya kaɗan yayi ya ce, "hakane zai iya sayar da C.E.O a maganar hausa" hmmm kawai tayi. Lokacin tashi. "Gwara ma ka cewa Dady ya neman maka driver, don bazan lamunci zuwa tare da kai ba komawa ma haka" cewar Amna bayan sun tsaya gun mota, amsa mata yayi da, "amma ban saba ganin mutum na gudun mai taimakon sa ba sai a wurin wannan shugabar", "oho dai ni dai na faɗa maka, wannan shine na farko na ƙarshe, akan zuwa da nayi tare da kai, da ma ka fasa wannan tayin da ka amsa" Shuraimya ce, "taya zan katse wannan nishaɗin da nake samu? Ke dai Madam shiga muje". "Bazan shiga ba, kai ka fara shiga" ta faɗi don idan ya zauna a baya ita kuma sai ta zauna a gaba, driver da ya tada motar tun ɗazu yake jiran su, zuwa gaban motar Shuraim yayi ya shiga, ganin hakan yasa ta sake murmushi ta shige bayan motar, sai dai tun kan ta zauna taji shigowarsa bayan, yana cewa driver ya tada motar, juyowa tayi tana kallon sa cike da takaici ta ce, "bazaka kiyaye ni ba ko? Me na sai ka zauna a kusa dani?" "Godewa Allah za kiyi da har mutum kamana, yana taimakon ki". "Wannan bai dameni ba ko kai wani irin mutum ne, nasan da kuɗi kake magana ko? Kuma karka sake cewa kana taimako na, nace maka bana buƙata! Ko baka ji bane?" Murmushin cikin rai yayi sannan ya fara dannan wayar sa, Amna kuma ta mayar da kan ta gefen glass, haka har suka isa gida. Nan ma bata jira driver ba ta fito harda manta fation bag ɗinta. Kallon jakar yayi ya saki murmushin da ke dawuyan fassara, ya fito bayan drivern ya buɗe masa shi. Da isan Amna ɗaki ta zube a kan gado, duk da aikin ba wai na yawo ko aikin ƙarfi bane amma ya bata wahala, domin ta basira da kuma hikima da fahimta take bin ko wani shafi, duk da Shuraim ɗin ya taimaka mata, ba tare da ta nuna taimakon na ta yayi ba, amma fa ya taimaka mata matuƙa, idan ya fara yi mata bayani akan abu nuna masa take

Chapter 25 of 56