Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cigaba da kallon inda take hangensa cikin ruɗu. Sai kuma ta bar kallon na sa ta wuce falo da Ammu sannan ta sake fitowa tare da gyara mayafin da ke sanye kanta tana kallon inda yake ɗin, nan ta fara takawa zuwa inda yake, domin ji tayi kamar bazata barshi ba tare da ta ji me yasa shi yin hakan ba, bata san me yasa ba amma tausayinsa take ji sosai, duk da cewa bata san sabida ita ya shiga wannan halin ba. Yazeed kuwa tun bayan da ya zauna jikinsa gaba ɗaya ya hau mazari babu ƙaƙƙautawa, wani masifaffen zazzaɓi na rufe shi, idanuwansa sunyi masa nauyi, suma da kansu zafi suke yi masa, hawaye suka fara fitowa daga ciki, idan ya tuna abin da ya gani tsakanin Shuraim da Safnarsa sai yaji tamkar ana tsiyaya masa tafasashshen man gyaɗa a cikin zuciyarsa, ya kasa dauriya, ya kasa amincewa da abun da idanuwansa suka gane masa. Koda wani abokinsa yayi masa maganar me ke damunsa, da ƙyar ya iya buɗe baki ya sanar da shi yaje ɗaurin auren kawai shi bazai je ba. Bayan Amna ta iso wurin har yanzu kansa a ƙasa yake ba tare da ya ɗago ba, sannan hawayen ma bai daina zuba ba, da ka gansa ka san akwai abin da ke damunsa, sai da Amna ta zauna a kujerar gefensa ba tare da ya sani ba, domin yadda ƙwaƙwalwarsa ta yi balaguro izuwa zantukan da ke sake rikita tinaninsa, Binsa da kallo tayi sosai tana mai nazartarsa na ɗan wani lokaci, jikin na sa ya ƙi daina rawa, cike da bayyanar da damuwa a kan fiskarta, cikin sanyin murya ta ce da shi, "Yazeed lafiya kuwa?". Kamar wanda aka tsikara ya ɗago da mugun sauri yana ɗaura jajayen idanuwansa da suka fara ƙanƙancewa zuwa fiskarta, sannan ga wasu sabanbin hawaye na sake sauka akan fiskarsa. Zaro ido Amna tayi tare da miƙewa da sauri tana dubansa cike da mamaki da kuma fargaba, domin a yadda tayi tozali da wannan fiskarsa ya sake tabbatar mata da akwai wani gagarumin abun da yake damunsa, idan ba haka ba harda hawaye sai ka ce va namiji ba?. Sake jefa masa tambayar tayi cikin nuna kulawa a karo na biyu, "Yazeed me ya same ka haka!? Me yasa na ga, idanuwanka na hawaye? Idanuwanka sun canza, sannan kuma jikinka, duka dai kana a wani yanayi na tsananin damuwa, duk me ha..." Kafin ta ƙare maganar da ta ke yi masa cikin sanyi murya mai ɗauke da raɗaɗi ko kuma a ce wanda ya tashi daga jinya Yazeed ya furta, "baki sani ba?" Shiru tayi ta tana sake ƙare masa kallo cikin mamaki da ɗan furucin nan da yayi ka na ta ce. "Eh ban sani ba, to akan me zan sani, yanzu faɗa min me yake damun ka? me yasa ka cikin wannan damuwa?" Ta sake faɗi cike da damuwa a kan halin da ta tsince shi ciki, kamar ba zai yi magana ba ya kau da kai kamar mai danne wani abun da yake taso masa, sannan ya juyo ya dube haɗi da miƙewa yana sa hannunsa ya share hawayen tare da kallonta cikin ido ya ce, "baki san abin da yasa ni cikin wannan halin ba? Kina son ki sani?" Cikin kokwanto da maganar sa ta furta eeh a hankali. Ba tare da ta ankara ba Yazeed ya riƙo hannunta ɗaya sai da ta ji zafin a hannunsa sosai sanadiyyar zazzaɓin da yake ɗauke a cikin jikinsa, ya fara janta yana tafiya da ita ba, "kai, kai Yazeed me haka? Sake min hannu!" Sai dai bai saurare ta ba ya nufi hanyar gate da ita, ba tare da ya juya ya dubi inda fiskarta yake ba. Cike da mamaki ragozar mutane matan da ke wurin suka raka su da ido, domin ganin abin na 'yan gida ne. Fita da ita Yazeed yayi waje yana cigaba da janta riƙe da hannu, ita kuma tana ta yi masa magana akan ya rabu da ita, me haka yake yi? Ina zai kaita? Sai dai sam yaƙi tsayawa ya saurareta, Amna kuwa ganin cewa Yazeed ko kaɗan kamar bai san tana magana ba hakan yasa zuciyarta itama ya hasala, ta ji baza ta cigaba da barinsa yana janta haka ba, to akan me ma zai riƙe mata hannu? Bashi da hankali ne? Dakewa tayi a tsaya ba tare da ta ce masa komai ba, shi kuma Yazeed da yaja hannunta amma yanzu ya ga ya kasa janta sosai ne cikin mamaki yayi ƙoƙarin juyowa inda take. A fisace Amna ta fisge hannunta kan ya ƙarisa juyowa, tana sakin wani hucin ɓacin rai yayi mata abin da wani namiji bai taɓa yi mata ba, wai ya riƙe mata hannu, don haka bazata juri wannan iskancin na, girar sama da ta ƙasa haɗe ƙam, fiska cikin nuna ɓacin rai tsantsa wanda shi kuma Yazeed bai taɓa kallo ko jin hakan daga gareta ba. Sosai yake kallonta bakinsa ya sake cewa ko uffan, domin mamaki da yadda ta fisge hannunta daga cikin na sa kuma ga fiskarta ya haɗe, Amna kuwa cikin tsanin masifa ta fara magana cikin ɗagun murya, tare da ɗadɗaga hannu tama ciccilawa tana magana itanan tana yi masa bayani da kuma ɓacin rai, "me hakka!? Akan zaka riƙe min hannu? Taya zan rinƙa ce maka ka rabu da ni amma kamar ba ka jin yaren da nake maka magana da shi?". Matsawa kusa da ita ya yi ya fara magana shima cikin zafin da zuciyarsa yake a ciki ya ce, "oh ke damuwarki na riƙe miki hannu? Kin ma san me kike cewa kuwa? Kuma wai tambayana me yake damuna kike yi, kina son ce min baki san me yasa na shiga halin da nake ciki ba? Ko da yake dama bazaki damu ba! Saboda kanki kaɗai kika sani, baki yi tunanin halin da zan shiga ba ko ka aikatamin abin da kike so!" Cikin wani mamaki Amna take kallonsa ba tare da ta fahimci inda maganarsa ke dosa ba, cikin ɗagun murya ta sake cewa, "wai kai me kake cewa ne? Ni babu abin da na fahimta cikin kalamanka, wani son rai na aikata maka?" Sai da ya girgiza kai tare da ciza bakinsa kaɗan, yana sake jin zafin furucinta sannan ya ce, "har yanzu tambaya fa kike ƙara yi, na baki kyauta cikin farinciki da murnar daɗin da zaki ji idan kika gansa, amma ke me kika yi? Ki ka watsa min ƙasa a ido, sannan kika bani amsa yadda zai ƙona min rai, ki ka je...." "Wai dan Allah akan me kake magana ne? Wani kyauta? Wani ɓacin rai? Ni fa har yanzu ban san à kan abin da ka ke magana a kai ba, ban kuma san me kake nufi da wa'yan nan maganganun na ka ba, kawai ni ganinka nayi cikin damuwa, kuma na tambayeka, to me hakan zai sa ɓacin rai eh? Wai duk akan wani dalili ka ke yi min magan-ganu marasa ma'ana? Ba zan tsaya ba, ba zan kuma sake sauraron ka ba! Wucewa zan yi" Tana ida maganar ta juya don barin wurin cikin ɓacin rai, sai dai kan ta ƙarisa Yazeed ya dakatar da ita da yin wata magana da ta dakatar da bugun numfashinta ba tare da ta shirya ba, ƙafafuwanta suka ƙame ba tare da sun bar wurin da dama shirinsu kenan ba, "be cause i love you Safna!!!" Abin da ya fito daga bakin Yazeed kenan jijiyoyin wuyarsa na fitowa ɓaro-ɓaro, yayin da zuciyarsa ta fara wani irin bugu hatta ƙarar yana bayyana kaɗan. Minti biyu ba tare da Yazeed ya sake wata magana ba, sannan Amna ta kasa sake yin wani taku zuwa gaba, sai a sannan Yazeed ya tako zuwa gabanta yana kallonta yayin da itama ɗago manyan idonta tayi zuwa kansa, "i love you! Yes Safna i love yoouu!" Ya sake faɗi cikin ƙara ba tare bugun zuciyarsa ta tsaya ba, sai da Amna ta rintse idanuwarta domin itama ta ji saukar wannan kalma cikin ranta, a bisa yadda furucin ya fito daga bakinsa. Sai da ta haɗiye wani irin nyawu sannan ta buɗe ido tare da sake haɗiye abin da ke zuciyarta haɗi da ƙyafta ido sau biyu ka na ta dubesa ta fara magana kamar mai koyon eiina ta ce, "ka ga, ka ga Yazeed, wannan, wannan maganar da kake faɗa, kawai, tunaninka ne, ka samu ka huta, daga nan, komai zai zamar maka daidai, eh dai dai, don haka ni zan koma gida" ta faɗi tana yin gaba cikin ƙwarin guiwa kada maganarsa ya karyar mata zuciya. Da sauri Yazeed ya sake shan gabanta, hakan yasa ta dakata tana yi masa kallon wani sabon mamakin, cikin raunananniyar murya ya fara cewa, "dama ko da yaushe tunanin nake yi Safna, kuma ba ko wani tunani ba ne illa na ki! Ba ki san yadda na ke ji a zuciyata ba, baki san yadda na kasance tsawon watanni bayan na bar ki ba, ko kin san ko wace ranar da nayi ba tare da ke ba sai kin min gizo a zuciya da kuma idani na? Ko wace rana sai na sanya hotonki gaba na ina ta kallon tsawon awanni" Ya faɗi haɗi da ba ta baya yana taku uku zuwa huɗu sannan ya juyo yana cigaba da magana, sai dai a yanzu muryar ta koma kamar mai jiran takk yayi kuka, saboda zafin da yake ɓoye à cikin zuciyarsa tsawon lokuta. Wanda duk wanda yaji wannan murya sai jikinsa yayi laƙass. "Na kasance cikin tsananin tunani, ƙaguwa, mararin son haɗuwa da ke bayan tasowana don dawowa gida, na shirya kalaman da zan miki a karo na fari idan na haɗu da ke, na ɗauka kema haka yake a wurinki ashe ba haka ba ne, na lura da cewa ba ni kike so ba Shuraim, shine wanda zuciyarki ta amince da shi, amma sai dai zuciyata tana yawan sanar da ni a duk lokacin da nake kawo wannan tunanin cewa ban fahimceki ba ne". Tsaida maganar yayi tare da sanya hannunsa à saman ƙirjinsa yana mai jin yadda yake masa, sannan ya matse idanuwansa da yake cike da hawaye masu zafi ya cigaba da cewa, "amma yau n'a ƙaryata zuciyata, na ƙaryata maganar da take sanar da ni, saboda yadda n'a ganki ke da Shuraim yau ya tabbatar min da kina son shi kuma shma yana sonki". Sake tsaida maganar yayi haɗi da durƙusawa ƙasa yana fashewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya, bai san cewa shi cikakken rago ba ne sai yau, sabi da yadda yake jin zuciyarsa ba tada ƙwari ko kaɗan. Amna har ta yunƙura da niyyar zuwa ta tarosa sai kuma ta rabu da shi, rintse idanuwanta tayi wani irin hawayen da bata san da fitowarsa ya koranyo zuwa kan kumatunta, da sauri ta share hawayen domin wannan ba halinta ba ne, duk da cewa kalaman n'a sa ba ƙaramin ratsata suke ba, Yazeed kuwa ba tare da ya share hawayen na sa ba ya ɗago idonsa yana kallonta, sannan ya ciga da magana, yana mai ƙara jin ƙirjinsa na sake ruruwa ya ce. "Wallahi wallahi ina son ki, soyayya ta gaskiya, soyayyar da ba nayiwa kai na, Safna na roƙe ki kar ki rabu da ni, kada ki ƙyale ni, ki tausayamin don Allah! Domin na san ba lallai ne naji daɗin rayuwa idan na rasa ki ba, ke ce wacche zuciyata ta yarda da ke zamo matata, wallahi ina son ki! Tun da nake ban taɓa jin wata a zuciyata ba kamar ke Safna, shin ko ina da wata matsala ce da ya hanaki jin so na a ranki? Ko akwai wani aibu da nake da shi wanda ke kuma ba kya son shi? Ki faɗamin ni kuma zan gyara, amma don Allah kar ki rabu da ni, don Allah ki soni, don Allah ki kasance kusa da ni, Safna ki aure ni, nayi alƙawarin baki duk wata kulawa da kike so, duk abin da kike so zanyi miki, amma kada ki barni, please pleaaasee!" Ya ƙarashe maganar tare da sakin wani irin kuka mai ratsa zuciya, da sauri Amna ta kauda kanta gefe yayin da ta ji itama kukan na shirin kufce mata, duk yadda tayi da dauriya amma ta kasa, kalamansa ko ɗaya bai ƙi tsaya mata a rai ba, hawaye idonta ya fara yi ba tare da ta ankara ba, bakinta yaƙi buɗuwa bare ta bashi wata amsa, to wani ma amsa zata bashi? Bayan ba ita ba ce wacche ya da ce ya faɗawa kalamansa, to amma ina wacche zai faɗama wan?. Ya bata tausayi mara misaltuwa sai dai bai kamata ta cigaba da sauraron wa'yannan kalaman nan na sa ba, idan ba haka ba itama kukan zata hauyi, don ta lura da yanzu ta canza sosai, sai da ta aro jarumta sannan ta share hawayen da suka fita ɗin, kamar abun bai dameta ta sake yunƙurawa zata bar wurin, "ki yafemin da riƙo hannunki da nayi, idonuwana ne suka rufe, na ji ba zan iya bari ba sai na amayar miki da zantukan da yake rai na, amma ki yafe min, ki ya fe min Safna, kar ki guje ni, kar ki ƙi amincewa da ni, ki aure ni, zan iya fiskantar barazana sanadiyyar ƙin da zaki min, ni ne wanda ya dace da ke ba Shuraim ba, don Allah, pleeaase Safana ke ce rayuwata!". Ya na faɗi ya kuma rintse idanu yana matse hawaye, sai dai duk kalaman nan na sa bai sanya Amna tsayawa ba, sai ma wucewa da tayi zuciyarta na harbawa babu ƙaƙƙautawa, kuka na ta ƙoƙarin kufce mata, idan har ta tsaya to komai zai iya kufcewa. Wani irin kuka mai sauti ya fashe da shi, tare da sake yin ƙasa da kan na sa, yana cigaba da kuka zazzaɓin jikinsa na sake dawowa sabo. Ɗadɗaikun mutanen da ke wurin suna ba idon su abinci, suna kallon ikon Allah soyayyar indiyawa, "ta tafi, ta tafi? Ta tafi, hakan na nuna cewa har cikin zuciyarta ba ta sona? Kenan bazan auri Safna ba? Kenan yaudarar kaina nake yi? Me yasa Safna ta kasance yadda ban zata ba?" Ya faɗi tare da cigaba da kuka kamar ƙaramin yaro, tabbas so shi ke karya zuciyar mutum duk girman sa, duk matsayinsa, duk ƙan-ƙantarsa, sannan duk tsufansa, yadda Yazeed ya kasance ba zaiyiwa duk wanda yake da zuciyar tausayi daɗi ba. Amna barin wurin da tayi hanyar gida ta nufa da sauri, domin dama ba wai nisa sosai sukayi ba, tana kallon mutanen da suke cikin gidan amma hankalinta baya ta kansu sam, kusan bangazan juna sukayi ita da Hajiya, sai dai Amna ko juyowa inda Hajiya ta ke bata yi ba ta wuce, da kallo Hajiya ta bita tana mai sake jin haushin yarinyar, sai dai itama yanzu tana cikin ta ta matsalar, domin jiran matsalar da zai dawo bayan an ɗaura auren Ruki da Jaiz, domin ta san ran Alhaji in yayi dubu ya ɓaci yanzu haka, don haka ta wuce don tattaunawa da Ruki duk da daman sunyi shirin ƙaryar da zasu yi idan su Alhajin sun dawo daga wurin ɗaurin aure. Amna ko inda Ammu take zaune bata kai idonta ba, sabida yadda zuciyarta take mata a yanzu, ta na shiga ɗaki ta rufe ƙofa kamar akwai wanda ke biye da ita, nufan gado tayi tare da faɗawa akai, ta haɗe idanuwanta guri guda tana jin sautin dake fita daga zuciyarsa, magan-ganun Yazeed ya ratsa kunnuwanta, tausayinsa ya cika ta, idanuwanta sai gano mata shi yake lokacin da yake wa'yan nan zantukan da kuma kuka, kasancewar shi suffar jarumi na miji bai kamata ace zuciyarsa ta yi masa irin wannan karayar ba, amma sai gashi ya rinƙa rusa kuka kamar jariri, ita da kanta yau ta shaida tsantsar ƙaunar da yake yiwa Safna, to amma ai duk tausayinsa da take ji a banza ne, saboda babu wata hanyar da zata iya yi masa maganin matsalarsa. Buɗe idanuwanta tayi wasu hawaye na biyowa bayansu, tashi tayi ta zauna ta fara magana cikin muryar kuka, "wai me haka? Me haka neee? Na ce me hakkaaaa!!!" Ta faɗi tana sakin kuka mai sauti kaɗan, wanda ke nuna kukan rashin mafita da ƙarin damuwa take yi, cikin kukan ta cigaba da cewa, "me yasa zuwana gidan nan ya canza ni? Me yasa na kamu da cutar tausayi da kuma tsoro? Wai dama akwai ranar da zan rinƙa yin kuka akan abin da bai kai ya kawo ba? Sai yaushe zan fita daga cikin wannan rayuwar ƙaryar da nake? Sai yaushe zan zama mai 'yanci inyi amfani da ko ni wacece a idon kowa?". Ta faɗi tare da sake lumshe ido tana buɗewa, hawayen suna sake samun wurin fita cikin idanuwanta. A hankali ta fara sauka daga gado sakamakon wani ƙara kaɗan da take ji cikin kunnuwanta, share idon na ta tayi sosai tare da ƙwarara kanta, akan cewa kuka bai kamaceta ba, ita ce fa Amna, ako wani hali bai kamata ta kasance mai rarraunar zuciyaba, fiskarta alamar tambaya ta fara baro ɗakin, don ganin wannan surutun na menene?. Yazeed sai da ya sha kukansa mai cin rai ka na ya miƙe da ƙyar, ba tare da ya lura da dattin da wandonsa yayi ba ya fara barin wurin, yana tafiya ƙafarsa kamar ba na sa ba, tafiya hake tangal-tangal tamkar zai faɗi, domin yadda jiri ya kuma dawo masa yanzu, idanuwansa sun kumbura suntum sannan sunyi jazir, zazzaɓin da dama ba barin jikinsa yayi ba ya ƙara tsananta. Saura kaɗan wata mota ta bugeshi kasancewar kamar ba a hayyacinsa yake ba, kamar ba zai iya isa gida ba Allah ya nufe sa da shiga, tura ƙofa yayi da ƙarfi kamar wani ɗan shaye-shaye, hankalin mutane ya dawo kansa bisa ga yadda ƙofar tayi sauti, tafiya ya cigaba da yayi ba tare da ya lura da ina yake nufa a gidan ba, sai kuma yatsaya ya sanya hannunsa à kai yayin da ya ke jin kansa na juya masa ko wani ɓangare, babu ɓata lokace jikinsa ya saki ya faɗi yaraf a ƙasa, har sai da kansa ya bugu da ƙarfi kan wani ƙarfe dake dashe a wurin. Nan mutane suka fara kururuwa ganin abin da ya faru, daidai shigowar Dady gidan a fisace da ka ga fiskarsa sai gabanka ya faɗi, sai dai ganin ɗan sa da yayi ne yasa shi nufo inda yake da gudu, Shuraim da wasu mutane na biyo sa. Lokacin Amna ma ta fito cikin tashin hankali ta nufo wurin duk da ba wai gane asalin abin da ya faru ta yi ba, don ko ganin fiskar wanda ake cewa faɗi fa yayi bata yi ba, matsar da mutane take yi don ta ga me yafaru, kawai idonta ya faɗa kan Yazeed da Shuraim da Dady da suke ƙoƙarin ɗagawa, ga jini ta kansa wanda ruɗewar da take ciki bai barta ta san ta ina ya ke fitowa ba. Last part. ___________________________________________________ Hmmmmmm, gaskiya na tausayawa Yazeed matuƙa. To 'yan uwa, ga dai Yazeed ya faɗi sannan har da buguwa akai yayi, ya kuke ganin Amna zata yi daga baya? Shin zata amince da shi ne bayan ganin halin da ya shiga ta haƙura da soyayyar da take yiwa Shuraim ko yaya? Sannan ga Dady dama ya dawo a fisace, ƙila kuma auren da Hajiya suka haɗa ne a kayi, to ko ya zai kasance daga baya bayan angama da matsalarYazeed? Wani ƙarya su Hajiya zasu rangaɗa masa? Ku kasance tare da Alƙalamin Aisha G Umar {Mrs Umar} [Gimbiyar Fasaha]👸🏽 Don jin yadda zata kaya. ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣2️⃣7️⃣▶️1️⃣2️⃣8️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 Cikin gaggawa suka sanya shi a cikin mota cikin tsananin tashin hankali, Hajiya ce ta fito da gudu bayan labarin abin da ya faru da ƙaunataccen ɗan na ta ya isa gareta, "wayyo Allah na me ya same shi?" Ta faɗi cikin ruɗewa sosai. Amna kuwa ta kasa yin ko motsi bare wani yunƙuri, domin tsoro da fargaba ya cika ta maƙil, da kallo kawai ta bi su har suka sanya shi cikin mota, gashi ba bu wani alamar motsi a tattare shi. Hajiya ma shigewa cikin mota tayi kamar wata mahaukaciya, Allah ma ya nufa tana sanye da gele da haka zata ɗunguma zuwa asibitin. Ganin masu gida ma sun bazama ne hakan yasa mutane ma fara sanɗewa a hankali ya zamana saura 'yan ƙwaranni a cikin gidan. Amna bata san lokacin da ta durƙushe a ƙasa ba, idon ta na fitowa da ƙwallah, domin tana da kyakykyawar zaton cewa abin da ya faru tsakaninta da shi ne yasanya shi faɗuwa gashi kuma har ya fashe kai, hawayen ta cigaba da yi masu raɗaɗi, da dana sanin barinsa da tayi ba tare da ta sanar da shi wata magana mai kwantar da zuciya ba, ƙila da tayi hakan da komai bai kwaɓe ba. Ji tayi ba zata iya zama ba tare da ta ji halin da yake a ciki ba, don haka ta nufi wurin mota driver ya kaita, sai dai ta bar wayarta à ɗaki tun lokacin da ta shiga, kafin tayi tunanin zuwa ɗauko sa don sanin asibitin da aka kai Yazeed ta ga Ruki ta shiga cikin wata mota tana shirin tadawa, ba tare da ta tsaya tunanin komai ba ta shige, mazaunin kusa da driver, da ido Ruki ta bi ta kamar zata yi wani magana sai kuma ta yi shiru, domin ganin yadda idon Amna ya canza kala kuma sun ɗan kumbura kaɗan, hakan yasa ta gimtse baki ta maida idonta gun key tana murɗawa, ta tada motar suka fice daga gidan zuwa hospital. Koda suka isa an riga da an shiga da Yazeed ɗakin bada kulawa, ga Hajiya zaune Alhaji kuma da abokinsa tsaye cikin rashin nutsuwa, sannan gefe ɗaya ga Shuraim, Marwan da kuma Saleem, suma haka, da sauri Amna ta nufa wurinsu cike da damuwa sosai har bakinta na ɗan kyarma kaɗan ta ce, "me ya ke damun Yazeed ɗin, doctor ya ce wani abu? Yana lafiya?" Tayi tambayar cikin ƙaguwa da jin lafiya ya ke. "Har yanzu dai ba mu ji wata magana daga garesu ba, suna kan aikinsu akansa" cewar Dady murya cikin sanyi, da kaji maganar ta sa kasan yana cikin damuwa shima sosai, kallonta Shuraim yayi ganin yadda ta tada hankalinta sosai a kan Yazeed, sai da ya ji wani abu mai kama da kishi ya ɗarsu a ransa, amma bai bar hakan yayi tasiri a kansa ba, cewa yayi, "ki zauna a kan kujera, zaki gaji a tsaye" babu musu ta je ta zauna inda Hajiya take da kuma Ruki da yanzu ta zauna kusa Hajiyar, sai zazzare ido Hajiya take yi, saboda tunanin halin da ɗanta ya shiga. Bayan wasu mintuna, doctor ne tsaye yana sanar da su halin da Yazeed yake a ciki, "mun gama duk abin da ya kamata a kansa, sai dai ya bugu a kai sosai, sannan jikinsa na ɗauke da masifaffen zazzaɓi, kuma ba ma wannan ba ne abun dubawa à halin yanzu" Dady ne yayi saurin taran nufashin doctor da cewa, "to doctor me ne abin dubawa sosai?" Ya faɗi har muryarsa n'a rawa. "Kafin ya faɗi zuciyarsa tayi zafi sosai, kuma ya zo ya haɗe da faɗuwar da yayi lokaci guda, a gaskiya yanzu yana cikin mawuyacin hali, domin duk da cewa a cikin suma ya ke, amma zuciyarsa ta ƙi samun sauƙi, har yanzu gudu take yi, babu abin da zance sai mu jira sanda allurar da muka yi masa zata sake shi, muga ya zuciyar ta shi zata dawo? Kuyi fatan zuciyar ta dawo dai dai idan ba haka ba gaskiya ban da ta cewa" doctor na gama faɗin hakan cikin nuna damuwa ya juya ya bar su tsaye. Ba ƙaramin tsinkewa zuciyar Amna yayi ba, musamman yadda ta san don ita zuciyar ta sa ta ɗau zafi". Hajiya kuwa sakin jiki tayi itama tana niyyar faɗi Amna ta taro ta, sai da ta juya ta dubi Amna fiskarta kamar mai shirin yin kuka, duk da ta ga fiskar Amnar ma yana à makamancin hakan, Dady kuwa doctor na barin wurin ya juya

Chapter 37 of 56