Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba ne sai da ta ga ta miƙe tsaye à kan ƙafafuwanta, kallon jikinta ta ke sosai tana ɗadɗaga hannayenta tana ganin ikon Allah, a hankali ta fara taka ƙafar ɗaya-ɗaya kamar mai koyon tafiya zuwa gaban madubi, kallon kanta ta ke yi sai shashshafa fiskanta take yi, bakinta ta yi ƙarfin buɗewa don furta Alhamdulillah, sai dai fa bata yi zaton bakin zai yi magana ba. Amma kamar à sama ta ji sautin muryarta ya daki majiyarta, ta furta "Alhamdulillah!" Bata san yaushe ta buɗe manyan idanuwanta ba, tana kuma ƙarewa kanta kallo cike da tsananin mamaki, hannu ta ɗaura kan bakinta tana taɓawa, "ni ce na yi magana? Ni ce?" Ta furta wasu hawayen ciwo da raɗaɗi n'a kwanciya akan fiskarta da ya manyanta ba kamar tsawon shekaru ba, juyawa ta yi jiki na rawa ta durfani gabas tare da zubewa à ƙasa haɗi da yin sujjada, tana godewa ubangijinta da ya nuna mata wannan rana da bata taɓa tsammanin zuwanta ba, ta ɗauka cewa à haka zata kasance har ƙarshen rayuwarta, sai gashi Allahu subhanahu wata'ala ya qaddamar da buwayarsa gareta. Hawaye take yi sosai a kan wannan sujjadan, tana ambato kalmomin godiya ga Allah, sai daga baya ta ɗaga kanta tana fashewa da kuka, kuka mai ratsa zuciya, kuka mai cike da farin ciki, kuka mai haifar da karaya cikin ranta. Kwatsam ta tuna magan-ganun da su Shuraim suka yi ɗazu, hakan yasa ta miƙe tana faɗin, "Amna! A ah bai kamata su je ba, akwai haɗari, kar suje gurin Zabba-ba, ya kamata na dakatar da su, bai kamata in bar su suje ba" ta faɗi cikin hanzari tana nufar ƙofar fita, sai dai kasancewar daɗewar da ta yi ba tayi tafiya ba, hakan yasa ta faɗi a ƙasa, amma duk da haka ta dage ta kuma miƙewa tana fita. "Hajiya Zainab wai nikam intambaya mana? Wai kin riga da kin saduda da wannan yarinyar ne? Naga ko maganarta yanzu ba kya yi min" cewar Ladingo tana kallon hajiya da jiran jin labari, Hajiya ta amsa mata da cewa, "ke dai bari Ladingo, kin san dama ina shirin yi mata gagarumin tuggu wannan auren ya dakatar, amma ba damuwa ina nan ina shirin wani, to ya naki matsalar ne? Kin fara shafa min ranar bikin yarannan". Numfashi Ladingo ta sauke sannan ta ce, "kin ga ni har kin tuna min ma, wai n'a ce kina jin labarin amaryar gidan naira Ruki kuwa?" "Inaa ai tun da aka kaita ba mu yi waya ba, jiya na kira layinta bai shiga ba" "amma Zainab kamata ya yi ki tura a je a duba ta, ya kamata kisan lafiya take?" Wani turo baki Hajiya ta yi sannan ta ce, "ke rabu da ita, yarinyar da yanzu take cikin daula, me abun da zai dame ni don banyi waya da ita ba, ke ai kin sanni, tun bayan da na auri Alhaji Jamilu, na jini tsamo-tsamo cikin arziƙi n'a yaye 'yan uwa na, duk da cewa lokacin ba mu samu komai yadda ya dace kasancewar komai na yayansa ne, amma bayan mun amshi ragama na kuma watsar da gaba ɗaya sauran 'yan uwa, saboda na ga su talakawa idan ka samu kuɗi sai su mayar da kai bankinsu, to don haka rabu da Autana ta sarara kaɗan, ni ina ma fatan kiran da zata min na farko sai dai inji abun alkhairi" hmm kawai abin da Ladingo ta yi, domin ita shaida ce akan abin da Hajiyar ta ce. Hajiya kuwa jin Ladingo ta dafata da ƙarfi kuma tana shirin janta ne yasa ta maida kallonta ga Ladingon, cikin mamakin yadda ta ga Ladingo ta zaro ido ya kuma sa ta tsayawa tana sake kafa mata ido, Ladingo dai sai ƙara baya-baya take ta ƙi tsayawa, "keh Ladi lafiya?" Ladingo bata yi magana ba sai ɗaga hannu da ta yi tana yiwa Hajiya nuni, cikin rashin fahimta Hajiya ta fara waigawa don ganin abun da Ladingo ke nuna mata, wanda yasa ta firgita haka. Fusss kake jin ƙarar faɗuwar wayar da ke hannun Hajiya, sakin baki ta yi kamar mahaukaciya, idonnan kai ka ce idon muzuru da ya faɗa hannun makashi, "imm...im...Maryam? Maryam" ta faɗi bakin ta na rawa sosai kamar an jona mata wutan lantarki, hannunta duka biyu ta sa ta fara murza idonta, domin ta san wannan ba ƙaramin mafarki ba ne, wai yau she ne m'a ta kwanta da har zata yi wannan gagarumin mugun mafarkin, sai dai ta yi rashin sa'a, domin kuwa ba mafarkin ta ke yi ba, bayan ta buɗe idonta da ta murje, ai kuwa idonta ya kuma gane mata Ammu. Ammu kuwa tahowa ta ke yi a hankali fiskarta na ta kwaranyar da hawaye, ta kusa isowa inda suke domin kuwa gurin step take nufowa. Kamar wata makauniya Hajiya ta fara laluben inda Ladingo ta ke, kama Ladingon ta yi tana faɗin, "ke ƙawata kinga abun da ido na ke gane mini kuwa, yau n'a shiga tara ba uku ba, idan ba haka ba wani irin masifa da jafa'i idanuna ke gane min yau? Wai fa wannan nakasashshiyar uwar Safna na ke gani a idanuwan nan na wa, wallahi banga ta zama ba, dole inje a ruƙe min kaina da addu'ar ruƙiyya". Kallon Hajiya Ladingo ta yi sannan ta ce, "ke Hajiya wallahi nima ina ganinta, ita ɗin ce dai wallahi" lokacin Ammu ta iso dap su, cikin ruɗewa Hajiya ta ce, "ki ka ce kema kina ganinta!?" Kafin Ladingo ta bata amsa Ammu kuwa ta fara kiran, Amnaa Shuraim!! Kar ku fita" Haba wa ai Hajiya daga jin wannan maganar ta zame ƙasa sumammiya.... Last part. ___________________________________________________ Hmmmmm!!! Amna da Shuraim zasu ƙara nufar wata matsalar, wacche idan ba'ayi wasa ba sai ya fi musu na baya haɗari, kuna ganin Zabba-ba zai ƙyale su? anya zasu yi nasara akan wannan alamari sabo na yanzu?. Su waye suka zo suka ta fi da ma'aikatan su Shuraim? Ko dai mutanen Zabba-ban ne?. Allah sarki Ammu ta tashi daga dogon jinyar da ta sha tsawon lokaci, to shin kuna ganin ya akayi Ammu ta tashi lokaci ɗaya hakan, me ne ne silar tashinta kan ƙafafuwanta? Akwai gagarumar ƙura! amma ku biyo ni don ji da hasaso komai. Taku Aisha G Umar✍🏼 {Mrs Umar} [Gimbiyar ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣4️⃣7️⃣▶️1️⃣4️⃣8️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 Kafin Ladingo ta bata amsa Ammu kuwa ta fara kiran, "Amnaa Shuraim! Kar ku fita" Haba wa ai Hajiya daga jin wannan maganar ta zame ƙasa sumammiya. Ammu kuwa hankalinta yana kan ta sauka a kan upstair kawai don ta tsaida su Amna, kada su tafi wannan wurin da suke son zuwa, duk da cewa bata san tuni suka bar gidan ba, don haka kawai taka matattakala ta fara yi. Ladingo kuwa kan Hajiya ta durƙusa tana girgizata amma Hajiya shiru kake ji bata amsawa. A yayin sauka saura kaɗan Ammu ta faɗi daga step, saboda tafiya ta ke yi kamar yaro mai koyon tafiya, haka dai har ta samu ta isa ƙasa, direct ƙofa ta nufa tana kuma kiran sunan Amna da Shuraim cikin tashin hanakli, dube-dube ta shiga yi a waje bayan ta fita, "kuna ina ne? Kar ku je, don Allah, 'ya'yana kar ku je" ta rinƙa faɗi da ƙyar cikin ruɗewa, wasu masu aiki suka tsaya suna kallonta cike da tsantsar mamaki, a iya saninsu tun da suka zo wannan gida basu taba ganin ta yi tafiya kamar yau ba, da ba don zuwan Amna ba ma, da wasu zama su iya cewa basu san da zaman Ammu a gidan ba. Jin cece-kucen masu aiki da suka fara yi ne yasa Jummala ta fito daga ɗakinta don ganin me yasa suke wannan surutun, babu wanda ya zo inda Ammu ta ke, ita kuwa sai kiran sunansu Amna ta ke yi, ganin alamar sun fita ne ya sata sake nufan gate, duk da cewa har ta fara jin gajiya sosai a jikin na ta, Baba Hambali da ya kara radio a kunnensa idonsa ya gane masa Ammu na tahowa inda ya ke da ƙyar, don yana iya ganin tana sauke numfashi, sai da ya saki radion da ke hannusa ƙasa, da sauri ya bar inda ya ke ya taho wurinta, kamar yadda Jummala ma cikin mamakin take nufo inda Ammun take da hanzari. "Ha...ha Hajiya da gaske ke ce!?" Ammu bata samu damar amsa masa ba sai ma cewa da ta yi, "Ham..bali.. ka taimaka ka tsayar, da su Amna, suna dosan mutuwarsu ne, ba zai barsu ba, ka tare su. Jummala, ku tare su Shuraim kar su tafi" ta ƙare maganar tana juyawa kan Jummala haɗi da sakin nishi, Baba Hambali da yaji abin da ta ce ne ya ce, "Hajiya ai sun daɗe da fita, sun ɗan jima" "what? No no no" Ammu ta faɗi tana shirin sakin jiki ta faɗi, domin yadda kanta ya fara juya mata, riƙe ta Jummala ta yi da sauri. Da ƙyar Ammu ta iya sake cewa, "ku kira su a waya, ku kira ku ce su juyo, kada su je" "to to shikenan Hajiya" cewar Hambali jummala ta kama Ammu suka nufi falo da ita, a kujera Jummala ta zaunar da ita, sannan ta nufi kitchen da wuri don ta ɗauko wa Ammun ruwa, ganin yadda yanayinta ya ke. Hajiya da ta samu damar farfaɗowa ne ita da Ladingo suka fara saukowa daga matattakala cikin fargaba, musamman ma ita Hajiyar sai sauke numfashi take yi, da kallo suke bin Ammu sannan suka samu wuri can gefe suna binta da kallo kamar masu kallon sabuwar halitta. Ammu kuwa ba abun da ta ke yi sai fitar da hawaye domin Hambali ya sanar da ita numban Shuraim baya shiga. AMNA DA SHURAIM kuwa suna cikin motar wayar Shuraim ya yi sautin shigowar saƙo, numbern uncle Musa ne ya bayyana a glass ɗin wayar, yayin da saƙon rubutun ya fito a a ƙasa, "kada ku je, ku tabbatar kun koma sai na kira ku, umarni ne!". Cire hannu ɗaya kan sitiyari Shuraim ya yi haɗi da ɗaukar wayarsa don ya ga saƙon da ya shigo wayar na sa, ya ga me aka turo? Amna ma juyowa ta yi tana kallonsa. MARWAN. Yana zaune a ƙasan carpet fiskarsa cike da haushi, can sai ga amaryar sa Sumee ta taho itama fiskarta ta bai bayyanar da farin ciki ba, kasancewar babu kujeru a cikin ɗakin ya sanya ita ma ta zauna a kan carpet ɗin tana kallon yadda ya yi da fiskarsa, taɓe baki ta yi sannan ta saki tsaki, hakan yasa ya juyo ya dubeta, sai kuma ya fara zagaya idanuwansa cikin falon yana ƙare masa kallo, falo ne babba kuma wanda ya haɗu sosai wurin gini, amma sai dai babu abun da ke cikin face madaidaicin carpet da bai kai ko rabin falon ba, in ban da wannan babu wani abu na musamman, cike da takaici kamar jiya da shekaran jiya ya kuma dawo da kallonsa ga Sumee, sai dai yadda ta ke wani yi da fiskanta ne ya ƙara sa shi tunzura yana cewa. "Ko kunya bakya ji ne ke? Dubi yadda kike wani shan ƙamshi kamar wata isassa, ni dai kin cuce ni, kuma wallahi zaki gani, lokaci kaɗan na ke jira in ƙara miki kishiya, don ba zan iya da wannan auren ba, haba, haka kawai!", ya yi maganar yana ji kamar ya dawo da hannun agogo baya, domin ya tarwatsa aurensa da ita, shi wallahi bai ga fa'idan wannan auren ba, tun da ya yi sa babu abin da ya ke ƙunsa sai baƙin ciki, shi ya zata ya auro 'yar attajira jikan ƙaruna, ashe dai 'yar bayan tukunya ce. Sumee ta yi ta yi masa shinfiɗar ƙare-rayi shi kuma ya yi ta zama a kai yana nashewa, ashe abin ba haka ya ke ba, sai da Dady ya ce zai sanya masa kayan ɗaki amma ya hana shi, saboda yana ganin amaryarsa Sumee zata taho da komai na musamman, sai gashi ashe ya riga da ya yiwa kitse kallon rogo, domin ko kayan arziƙi ba a kawo masa ba, domin suma su Sumeen zato suka yi zasu zo su tarar da kayan furniture da dai sauran su, shi Marwan babban abin da ya damesa ma, uwa uba abin da miji ya ke buri gurin amaryarsa shi bai samu yadda ya zata ba. To dama taya zai samu? Bayan à cikin 'yan shashancinsu ya gamu da ita, ni dai na ce 'ya'yan Hajiya sun yi gadon halin nan na ta na son kuɗi, ashe shima Marwan ɗin haka yake yana namiji ma. Ita Ruki ta auri mai kama da suffan Aljani, shi kuma Marwan ya auri tashi suffar, mai yin ciko a waje ciki kuma emty, amma fa Ruki tafi gamuwa da jafa'i🤭 Wani irin kallo Sumee ta kuma jefa masa sannan ta ce "dama me zaka iya furtawa in ba wannan ɗin ba? Kuma wallahi ka yi kaɗan! Baka isa ka kawo wata ba, zama da ni ni kaɗai ya zame maka dole, ko kana so ko baka so! Daman ka riga da ka san halina, wallahi sai in aikata abin da rai zai yi dana sani, kuma idan ma don akan kayan ɗaki ka ke wannan ban-bamin, kai ba abin kunya ba ne ma a kan ka a ce baka yiwa matarka kayan ɗaki ba? Kana ɗan mai kuɗin da mutane suka sani, ko da ya ke kai dai dama babu abin da ka mallaka na ka na kanka, tun da gidanma uban n'a ka ne ya siya ma mtseewww". Ta ƙarashe da sakin tsaki, kauda kai Marwan ya yi yana faman gun-guni sannan ya ce, "zaki gane idan kika ga an kawo miki kishiya cikin gidan nan, tun da sakinki ba zai yu ba kin zame mini ƙarfen ƙafa, amma aure kuwa ba zaki hana ni ba" Shima ya ƙare da sakin tsaki, wai shi yaushe ne m'a idonsa ya gane masa wannan ballagazar? Ya bi ƙyale-ƙyale yana ganin ya samu sarauniyar mata, ashe dai duk iskan balanbalan ne kawai, miƙewa Sumee ta yi tana shirin barin wurin, ya bita da kallo a zuciyarsa ya furta, "Allah ya isa!". saboda sanin halinta ne yasa ba zai iya sakinta ba, kuma ko kishiyar ma da yake cewa zai yi mata baki ne kawai, domin yanzu ma haka ita ta hana shi fita, kuma bai isa ya taka wajen gidan ba ba tare da ta amince ba, da baki kawai ta barshi ya faɗi abin da yake so. Ni kuwa na ce anya ƙalau kuwa? GIDAN GONA. Wani ƙatoton tsohon gidan gona ne da ya yi nisa da mutane kaɗan, kasancewar wurin ba ya ba da riba da albarkatu kamar yadda suke so yasa suka saida wurin, bayan sun sai da shi wanda ya siya ya fara gina wurin, daga baya kuma ƙungiyar Pospa ta amshe wurin da ƙarfi, haka wurin ya dawo kango-kango hanya-hanya lungu-lungu, ba kasafai Zabba-ba suke mu'amala a wannan gidan ba, sai idan abun na musamman ne, kamar yadda yau aikin da zai gabatar ya kasance ya zarce musamman ɗin. Amna ce na gano a hankali cikin hikima ta fara shigowa wurin bayan ta wuce ƙofar da ta gani na farko, sai dai a wannan ƙofar kuma ta ga mutane shidda munana da fiskarsu yake ɗaure tamau suna tsaye, laɓewa jikin bangon gefen ta yi haɗi dà tunanin abin da zata yi don ta samu damar shiga ciki, "me ya kamata inyi? Ya kamata inyi wani abu?" Ta yi maganar a ranta haɗi da sanya hannunta a kan goshi tana tunani, daga nan idonta ya sauka ƙasa kan wasu kyawawan duwatsu madaidaita, sai da ta ɗan leƙa su yadda ba za su ganta ko jinta ba, sannan ta durƙusa ta ɗauki dutsen ƙwara huɗu a hannunta. Leƙensu ta kuma yi sannan ta samu damar hurga dutse ɗaya ta can gefensu tare da saurin sake ɓoyewa, a tunaninta idan ta yi sa'a dutsen ya yi ƙara, ƙila su bar wurin ita kuma ta samu damar wucewa, sai dai bayan dutsen ya faɗi bai fitar da ƙara ba, numfashi ta sauke ganin gwajin farko bai yi aiki ba, hakan yasa ta kuma ƙara gwada jefa wani. Ya yi ƙara amma ba sosai ba, "kai baku ji ƙarar wani abu ba?" Cewar wani daga cikin su, "eh na ji amma ƙila tsuntsaye ne kawai" ɗaya daban ya kuma faɗin haka. Amna kuwa da take laɓe da gini tana jiran ta ga sun tashi daga inda suke, amma basu tashi ba, sai da ta sanya hannunta ɗaya daga kan fiskarta zuwa wuyarta sannan ta sauke numfashi da roƙon Allah yasa wannan karon haƙanta ya cimma ruwa. Ɗaga dutsen na uku ta yi sosai ta kuma wurga shi da ƙarfinta, ai kuwa ya sauka akan wani langa mai tsatsa à jiki, hakan yasa ƙarar ya fito sosai, sai da Amna ta razana kaɗan tare da saurin komar da kanta gefe gudun kada su ganta. Su kuwa mutanen nan da sauri suka tashi suna faɗin, ta can ne muje mu duba, suna faɗi gaba ɗayansu suka yi wurin da suka ji karar sautin ya tashi, Amna kuwa zuro kanta ta yi ganin sun tashi ne yasa ta sauke nannauyar numfashi tukunna da hanzari ta bi ta shige wannan ƙofar, tana shigewa kuwa ta ji hayaniyarsu suna dawowa inda suke haɗi da zama, nan ma samun wuri ta yi ta ɓoye kada ta kuma ganin wasu mutanen, haka dai ta rinƙa yin dabaru idan ta ga mutum ta ɓoye har Allah yasa ta samu isowa zuwa wani sashe. Wani babban sashe ne da ke wannan wuri a gine, sai dai ba wai ƙa wata wurin a ka yi ba, zan iya kiran wurin kamar hall, babu haske sosai a cikinsa sai dai zaka iya kallon wanda ya ke a ciki, laɓewa Amna ta kuma yi haɗi da sanya idonta tana leƙen ciki ta gefen ƙofar da yake a buɗe, mutane ne a can gefe sun yi layi kamar sojoji idonsu yana kan ogansu, yayin da wani table guda ɗaya ya ke cike da wasu irin kwalabe na magunguna iri kala-kala, ruwan maganun-nuwan, wasu green wasu kuma red, wasu black wasu blue, wasu purple wasu kuma white, haka dai suke nan iri daban-daban. Zaro ido Amna ta yi ganin wa'yan nan kwalaben, wanda da ka gansu kasan suna tattare da matsala, saboda yadda jikinsu ya ke ɗauke da wasu hotuna, wanda kasancewar Amna daga nesa ta ke hangensu sai bata tabbatar ba, mai da hankalin da idonta ta yi gefe, bayan jin wani irin sautin tashin takalmi da ta ji, ai kuwa idonta ya gane mata wani irin takalmi da ke sanye ƙafar wani ƙaton mutum, wato Zabba-ba, tafiya ya ke ita kuma idonta na biye da shi har ya iso gun wannan teburin kwalaben magun-gunan. A sannu Amna ta fara yin sama da idanuwanta kansa, idonta kan wani ƙaton allura da Zabba-ba ya sanya hannu ya ɗaga, sai da zuciyarta ya buga bisa arba da ta yi da wani irin ƙaton sirinji mafi girman alluran da ake yiwa manyan dabbobi, domin wannan ƙato ne sosai, ruwan cikin sirinjin wani irin kala da bata san wanne iri ba ne, domin bata san cewa anyi mixed ɗin ruwan wa'yannan kwalaben a ciki ba, shi yasa ya canza wannan kalan. Kafin idonta ya kai kan fiskarsa, ta kuma gani ya kafa bakin alluran zuwa kan wata kwalba da daga cikinta wani irin hayaƙi ya ke jujjuyawa a ciki, a hankali ta ga wannan hayaƙi ya kwanta, sai ya zamana wani irin baƙin ruwa ya bayyana a cikin kwalbar, ai kuwa ba jira ta ga ya fara zuƙo wannan bakin ruwan yana jirkita su da ruwan da ke cikin sirinjin, bayan ya gama ɗure ruwan, nan wani irin sauti ya fara fita tamkar ruwa na tafasa, bul bul bulu lu bul. Amna ba jin ƙarar ta ke ba, saboda ba ta kusa da shi, sai dai tsoro ne ke sake ratsata, maida idonta ta yi don ta ga waye wannan mutumin, sai dai bata samu damar ganin fiskarsa ba, saboda ya juya ya fara nufan wani wuri daban, bai tsaya ako ina ba sai a wani tablé ƙato da ke wurin, har lokacin bata ga fiskarsa ba, kasancewar ya bata baya, amma kuma sai ta sauke idon kan wani mutumi da ke kwance a kan table ɗin, kasancewar fiskarsa ya yi gefe ya sa ta gansa. Wani irin bugu zuciyarta yayi ta zaro idon cikin tashin hankali, rufe ido ta yi haɗi da sanya hannunta tana ɗaurawa a kanta tana yin wani tunani, tana buɗe ido zuciyarta ya bada rasssss ganin wannan mutumin da ta ke da tabbacin shine Zabba-ba ya ɗaga allurar nan, yana shirin saukewa a kan wanda ke kwance a kan table ɗin, da alama kuma soka masa ya ke shirin yi. Zabbaba ya ɗora wannan ƙatuwar allurar setin wuyar Baba da ke kwance kamar gawa, sakin murmushin mugunta ya ke ta yi yau burinsa zai cika, daga zarar ya sokawa Baba wannan allurar kuma saƙon ya kai inda ake so to fa shikenan, daidai zai soka ya ji ƙarar Amna "à aaaaaaaa!" Wanda hakan yasa shi saurin cire allurar kan ya kai ga ɗurawa, haɗi da saurin juyowa fiskarsa bayyane da mamaki!. Amna tana sakin wannan ƙara haɗi da bankaɗo ƙofar ta shigo ba tare da ta sani ba, tsayawa ta yi tana kallon inda Baba ya ke zuciyarta na sake bugu kamar ana haƙar duwatsu, sauran mutanen suka juyo suna kallonta tare da tahowa suna son su kamata, amma Zabba-ba ya ɗaga musu hannu, hakan yasa su dakatawa. Ita kuwa a hankali ta fara takawa zuwa kan Baba ba tare da ta kalli kowa da ke wurin ba, kallonsa ta cigaba da yi tare da fitar da hawaye cikin idonta, "me...me...à kan me?" Kafin ta yj wata maganar Zabba-ba ya saki dariya, saurin cire idonta kan Baba ta yi cikin ruɗewa, sannan ta dawo da dubanta gun Zabba-ba da ke dariya. Wani irin saurin ja baya ta yi kanta na fara juyawa, yanzu ma ɗaura hannayenta duka biyu a kanta ta yi tana lumshe ido cikin wani irin yanayi, buɗe ido ta yi bakinta na rawa tana son fitar da magana daga ciki amma ruɗewa ya hana ta. Hannayenta duka biyu ta ɗaga haɗi da nuna shi da yatsa, tana kuma ƙoƙarin yi magana jikinta ya fara rawa. Last part. ___________________________________________________ Hmmm nima fa na tambayi kaina yau😁 Me tunaninku game da maganganun Ammu da take yi? Sannan ga uncle Musa ya turo wa su Shuraim saƙo, shin sun gani? Ga dai shi Amna ta iso, ko a ina ta bar Shuraim? Ina Yazeed mai binsu?. Ga kuma Alhaji Marwan n'a amarya Sumee, anya ƙalau abin da ke faruwa tsakaninsu kuwa? Mu kasance a next part idan Allah ya kaimu. ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣4️⃣9️⃣▶️1️⃣5️⃣0️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 Hannayenta duka biyu ta ɗaga haɗi da nuna shi da yatsa, tana kuma ƙoƙarin yi magana jikinta ya fara rawa. Da ƙyar ta samu bakinta ta fara furta, "Zabba-ba? D..d..d..da" ta kasa haɗa kalmomin da take son faɗi, bakinta sai kyarma yake, dariya ya saki sannan ya ijje allurar da ke hannunsa, ya tako yana isowa gabanta, yayin da ita kuma ja da baya ta ke yi tana cike da tsoro, "da...da...Dady!!?" Ta samu damar faɗin kalmar hawaye na ƙara gudu kan kumatunta. "Eh Amna! Ni ne dai Dady, kuma Zabba-ba, shugaban ƙungiyar Pospa!" Cewar Zabba-ba wanda fiskarsa ya bayyanar da fiskan Dady, yana kallonta kallo wanda bata taɓa ganinsa a kan fiskarsa ba, wanda ya ke nuna tsantsar muguntar da ya ke tattare a cikin zuciyarsa. Sai da ta kusa faɗi jin amsar da ya bata, wani irin hajijiya n'a neman ɗaukarta, lumshe ido tayi na 'yan seconds sannan ta buɗe, ta kuma ɗora su akan wannan fiskar ta sa, wanda a yanzu ya canza mata sosai, "Dady this is a dream right?" Ta faɗi cikin sanyin murya sosai. Dariya ya sake yi sannan ya juya ya bata baya haɗi da yin taku biyar sannan ya juyo yana dubanta, ya kuma ta ku uku ya dakata yana sakin murmushi

Chapter 45 of 56