Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yasa bata gama gane waye wannan ba, Buɗe baki tayi tana kallon Shuraim da Safna da suke gefenta, Shuraim ma ya gama ɓaci da jini rigarsa duk ya zama ja, sannan ga Safna da dama ita ta riga da ta ji jiki, kafin Amna ta samu damar fitar da wani harafi, ta saki ƙara mai sauti, haɗi da mulmulawa gefe idonta ya fitar da ƙwallah gefen ido, sakamakon bugu da Dady ya dage ya kai mata a kanta, bayan ya ɗauke ƙafar da ya ɗaura mata cikin tsananin mugunta, sai da mayafinta da ya fara cirewa ya yi gefe, Bata kai ga yin wani ƙaƙƙarfan motsi ba Dady ya kula isa inda ta ke, ya cigaba da bata azaba daga wannan katakon, gimtse donta ta yi lokaci guda bata fahimtar komai yanzu, sau zafin da ke shiga jikinta cikin ko wani bugu na sa, tana ɗaga kai a duk lokacin da ya buga mata. Cikin tashin hankali Safna da Shuraim suka yi ihu suna ƙoƙarin miƙa hannunsu inda amnan ta ke, Safna na kuka Shuraim ma hawaye sai fito masa suke yi yana kukan zuci, "don Allah ka ƙyale Amna, kada ka cutar min da ita, ita ce rayuwata, ka ƙyaleta ita da Safna su tafi, ni ka min duk abin da kake buƙata don Allah" cewar Shuraim da ƙyar ya fara bayyanar da kuka cikin sassarfa, yana kallon Amna da jini ke ƙara gudu a Ƙasar kanta, idonta na neman ya rufe kamar ta daina gane komai. Safna ma cikin kukan ta ce, "a ah duk ba ku da laifi, ni ce da laifin komai, don Allah Dady ka rabu da su, Amna ba ta da laifi, bata san ya rayuwata ta ke ba, haka shima Shuraim babu abin da ya haɗa shi da ni, ina ni ce matsalarka ko? Ka kasheni ni, amma ka barsu n'a roƙeka" ta ƙare maganar da fashewa da matsanancin kuka, tana kallon inda Dady ya ke. Dady tsayawa ya yi da dukan da ya ke kaiwa Amna ya juyo yana kallonsu, tare da kuma haɗe razananniyar fiskarsa. Shuraim ya kuma cewa, "me kike faɗa ƙanwata? Ni yayanki ne, babu abin da zai same ki, Alhaji Jamilu, ka ƙyale su ina roƙonka, idan ma gunduwa-gunduwa kake son yi da ni duk ka yi, amma don Allah ka rabu da su, kada ka cutar da Amna da Safna". Tafi Dady ya fara yi yana juyawa kallon mutanensa ya ce, "ku tafa musu" nan suka ɗau tafi suma Dady ya kuma cewa, "da kyau! Wow wow wooow, gwanin burgewa, soyayyar 'yan-uwan taka, da kyaaauu!" sannan ya tako zuwa gaban Shuraim haɗi da tsugunnawa, "to da kuke ta shirin bada rayuwar ku, kuna ganin ni Zabba-ba zan iya barin masu bani matsala ne? Inaaa ba zan taɓa barinsu ba" ya ƙare faɗi yana kallonsu duka biyu, idanuwansu sai cigaba da fitar da hawaye ya ke suma suna kallonsa cikin tausayin kawunansu. Maida hanakalinsa ga Shuraim Dady ya yi sannan ya ce, "Shuraim ɗan Abu Shuraim na ƙasar London, kai da me ka ɗauki Shugaban ƙungiyar Pospa ne? Kai ɗauka ka yi yana da ƙwaƙwalwa kamar na ka ne?" Sakin murmushi ya yi sannan ya ɗaura da cewa, "ni Zabba-ba na wuce ƙarfin tunaninka ta ko wace fanni, na riga da san ko kai waye tun karon farko da ku ka tura masu yi muku leƙen asiri a ƙungiyar rukini na na farko, to amma me amfanin in bibiye ka don na yi maganinka? Ashe ban cika Zabba-ba shugaban ƙungiyar ba kenan". Ya faɗi haɗi da miƙewa yana cigaba da kallon Shuraim, "barinka na yi ka yi ta turo min mutane ni kuma ina gamawa da su, har sai ran da kai da kanka zaka kawo min kanka da kanka! Kamar dai yadda ka aikata yau, a can za'a gama min da mutanenka da nasa aka kama, anan kuma ni zan gama da kai!" Wani irin yunƙurawa Shuraim ya yi yana son ta shi cikin tsoro ya ce, "suna ina? No no kar ka kashe su" "Kwantar da hankali kwantar da hankali. ai ba za ka girgiza ba ma sai na faɗa maka wani abun kuma". Cewar Dady yana kuma sakin murmushi sannan ya juya gun mutanensa sannan ya ce, "ya har yanzu baku kawo min aiki na ba?" Da sauri wasu suka bar wurin don ɗauko masa abin da ya ce, mai da kallonsa kan Shuraim ya yi sannan ya ce, "tun zuwanka gidana ni na shirya komai, ni ne wanda ya sanya ka ji labarin ƙarya akan wani mai suna Abu Shuraim, wanda kuma hakan duk shirina ne". Ganin kallon da Shuraim ya yi masa mai ɗauke da wani mamakin yasa ya kuma cewa, "tukunnafa da sauran labari. Domin kuwa ba kai kaɗai ba hatta mahaifinka na sani" ya faɗi yana zama kan kujerar da aka ijje masa a bayansa, haɗi da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, ya sanya hannu ya gyara malafarsa, idon Shuraim na kansa, na Safna kuma na kan Amna tana ƙoƙarin zuwa gaban Amna da jan jiki da ƙyar, duk da cewa wani guri a jikinta n'a sake fitar da jini. "Sunan mahaifinka shine Abdurrazak, a shekarun baya da daɗewa shi ɗin ma'aikci ne a companynmu, wato MD company, ya kasance ɗaya daga cikin aminan Mai-daraja, hakan yasa na ne mi da ya bani haɗin kai gurin aiwatar da wani buri na, amma shi kuma ya ƙi, duk hanyar da zan bi don in nuna mishi hatsarin ƙin amincewa da umarni na ya ƙi, hakan yasa ni kuma raina ya ɓaci, kasan me na yi?".. Cewar Dady yana ɗauke kai, shi kuwa babu abin da Shuraim ya ke ji cikin zuciyarsa sai bugu mai matuƙar gaske, sakamakon abin da Dady ke faɗi game da mahaifinsa, ke nan dama ya riga da ya san komai game da shi? Dawo da kansa kan Shuraim ya yi haɗi da sake ɗaure fiska mai nuna mugun gaske sannan ya ce, "shine ni kuma na aikashi lahira daga shi har matarsa!!" sai da numfashin Shuraim ya yi saurin dakatawa, kansa na tsananta juyawa yana jin yadda zuciyarsa ke buga kamar zai fito. "Ka sake yin wani sabon mamakin ne? Tabbas ni ne na aika iyayenka lahira tun kana ƙarami! Da ba don baka tare da su a wannan lokacin ba, da har da kai zan haɗa, sai dai hakan bai ɓaci ba, ina ga yau ita ce rana mafi sa'a da zaka bar duniya, shiyasa ka rayu tsawin lokaci" Shuraim bai san lokacin da ya fashe da kuka mai gigita tunani ba, wanda yasa Safna ma amshewa tana sake jin jina baƙar zuciyar Dady, wanda rashin sani ya sata ɗaukar bayan mahaifiyarta a duniya babu wanda ke ƙaunarta kamar sa, ashe dai ta tafka babban kuskure a rayuwarta. "Dama kai ne wanda ya kashe min iyaye na? Wanda ya kassara min rayuwa, wani irin mutum ne kai, ka ɗauki ran mutane ba abakin komai ba, wannan wani irin masifa ne?" Shuraim da ke kuka ya faɗi hakan haɗi da kwantar da kansa yana kuma sharara kuka. "Kar ka damu yau duk zaku je ku haɗu da iyayenku" ya faɗi yana sakin dariya tare da juyawa daidai lokacin da aka shigo masa da tebura biyun nan, ɗaya Baba kwance ɗaya kuma sinadaran guba. Safna da ta samu damar isa inda Amna ke kwance ta ɗaura hannunta kan Amna tana matsar da gashin Amna da ya zubo kan fiskarta baya, sannan ta shafa kan goshin Amna dake kwance da jini, hawayen da ke tsiyaya akan fiskarta ya shiga zuba a kan fiskar Amna, "Amna ki tashi, ki yafe min duk ni ce, na ja ki cikin wannan hatsarin, kamannin da nake da shi irin na ki shi ya ja miki" ta faɗi cikin shaƙaƙƙiyar murya tana kuma fashewa da kuka, wannan maganar da kula kukan da ya biyo baya, haɗi da hawayen da ke zuba kan fiskar Amna ne yasa idont ya fara motsawa, tana jin magan-ganun Safna tamkar a saman iska ya ke tashi. Dady kuwa isa gaban Baba ya yi, yayin da idon Baban ya ke buɗe yanzu, bayan sun masa allurar farkawa, amma jikinsa ko kaɗan baya motsi sai ido kawai, yayin da idon na sa ke ta tsiyayar da hawaye sun yi jawur alamar ba yanzu suka fara fitar da hawayen ba, "barka dai Hassan, ko Hussaini ne?" Faɗin Dady ya sanya hannu ya ɗauki wannan ƙaton allurar yana murmushi ya kuma cewa, "ina ta ɓata lokaci, kuma ya kamata komai na ya kammala izuwa yanzu, amma kar ka damu tun da na yi maka adalci har zuwa lokacin nan". Idon Amna na ƙoƙarin buɗuwa bakinta da ya ɓaci da jini ta fara buɗewa, har jini yana zuba daga bakin nata kasancewar ba ƙaramin buguDadyya yi mata a fiska ba, duk ciwuka sun bayyana. Safna kuka ta ke yi idonta na kan Dady da ke son yi wa wannan mutumin da ta taɓa gani a baya,. __Lokacin da suke shirin zuwa gurin bikin wata ƙawarsu ita da Raheena, keke napen da suka hau ta samu matsala suka sauka, bayan wani mutum ya sanar da su inda zasu fi samun mashin ɗin wannan unguwa, suna cikin tafiya ya tsaya gabansu yana ta kallonsu ko kuma ta ce yana ta kallonta, sannan daga baya ya tambayeta ya sunanta__ Haka kawai ta kasa mantawa da wannan rana, ya tsaya mata a rai sosai, wanda hakan yasa lokacin da ta laɓe à ƙofar hall ɗin nan, ta ga Zabba-ba na neman soka masa allura bayan ganin fiskarsa da ta yi ta tuna haɗuwarta da shi, hakan yasa cikin tashin hankali ta bangaji ƙofa ta shigo. Amna da ta buɗe bakinta na fitar da jini tana kuma jin kukan Safna ne yasa ta ta ce da ƙyar, "me yasa, ki ke kuka? Ki dai na, kin ji 'yar-uwata?" Da sauri Safna ta dawo da kallonta kan Amna, "Amna kina ji na? To ki buɗe ido kin ji? Ki yafe min" kamar mai jiran umarni Amna ta buɗe idanuwanta kan Safna ta kuma cewa, "laifin me kika min?". Shuraim sai hawaye ya ke fitarwa yana jin kamar ba a duniyar nan ya ke bama. Dady kuwa sai da ya kuma jan ruwa baƙin nan sannan ya ɗaga hannu yana dariya wanda hakan ya karkato da hankalin dukansu, suka juyo à hankali kasancewar jikinsu amsawa ya ke yi kawai. Zaro idon Amna da jinin goshinta ya sauka a kai ta yi, zuciyar ta ya bada wani irin ƙara dammmmmmm, sakamakon ganin mutum tsaye gaban mahaifinta ya ɗaga rusheshiyar allura yana shirin saukewa, yayin da dariyarsa ke ƙara amsakuwwa cikin kunnenta. Zabba-ba kenan?" Tambayar da ya sauka a zuciyarta kenan, domin ita dama bata ga fiskar Dady ba. Last part. ___________________________________________________ 🥺🥺 Kuna ganin Zabba-ba zai ci nasara?. Ashe suma iyayen Shuraim kashe su aka yi, sannan kuma duk Dady ne. To ko me aikin da Dady ya sanya mahaifin Shuraim, wanda ƙin amincewarsa ne yasa ya kashesu? Mu kasance da ku a kashi na gaba don ganin abin da zai faru? ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣5️⃣3️⃣▶️1️⃣5️⃣4️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 Zuciyar ta ya bada wani irin ƙara dammmmmmm, sakamakon ganin mutum tsaye gaban mahaifinta ya ɗaga rusheshiyar allura yana shirin saukewa, yayin da dariyarsa ke ƙara amsakuwwa cikin kunnenta. "Zabba-ba kenan?" Tambayar da ya sauka a zuciyarta kenan, domin ita dama bata ga fiskar Dady ba. Da ƙyar ta waiwaya cikin tashin hankali ta kalli wani fashashshen tayis a ƙasa, samun damar ɗauka ta yi ta kuma juyawa tana kallon Dady da ke shirin sauke allurar, ƙarfinta ta tattaro baki ɗaya ta yi wurgi da wannan karyayyen tayis ɗin inda Dady ya ke, cikin sa'a wannan tayis ɗin ya bugi hannun Dady, wanda hakan yasa hannunsa ya ɗage allurar ya yi sama ya faɗi a can gaba. Ƙaƙalo murya ta samu ta yi da ƙarfi cikin tashin hankali, da raunanan da take ji azaba kota ina a jikinta, domin bata gama ankarewa da abin da ta wurga ya yi aikin da ya dace ba ta ce, "nooooooo, please-please, karka kashe min mahaifinaa, kada ka aikata masa komai ka rabu da shi, shi ɗin Babana ne kuma komai na, don Allah..." Dady a fisace ya juyo, cikin ƙufula da abin da ta yi masa, domin ta ji masa ciwo har jini ya fara fitowa, "me alaƙar ki da shi!?" Cewar Dady da ɗagun murya. Amna da kanta ya ke a ɗage wani jinin na tsiyaya kaɗan kan fiskarta tana shirin ɗaga hannu, idonta da ke shirin lumshewa ya tsaya kan Dady bata ko ƙyafta shi, shi kuwa ƙarasowa ya yi inda ta ke yana ta furzar da huci. Hankalin Safna da ke jingine ya dawo kansa, da kuma Shuraim da à yanzu har kukan ya ƙi fitowa sai zafi da ya ke ji daga cikin zuciyarsa. "Kin yi mamaki da kika ganni à matsayin Zabba-ba ko?" Cewar Dady domin ya riga da ya san bata ganshi da kyau ba ɗazun, bata iya amsa masa ba sai cigaba da kallonsa da raunannun idanuwanta da ta ke. Shi kuwa ƙara cewa ya yi, "me alaƙar ki da wannan ɗan jaridar?! Kina ɓata lokaci gurin son kare wanda babu wata alaƙa a tsakaninku!". Yunƙurawa da ƙarfi Amna ta yi cikin galabaita tana shirin tashi domin ranta ne ya fara ɓaci bisa ga maganar Dady, Safna ce ke ƙoƙarin tallafawa Amna don ta tashi, su biyun sai da suka kusa faɗi saboda rashin ƙwarin jikin na su, kallon Dady suke yi musamman Amna, numfashi mai zafi dukansu su ke saukewa kafin Amna ta yi juriyar cewa, "dama, duk abin da ake ɗin nan, kai ne Zabba-ba!? Kai ne, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar, abokina wali da wasu mutane? Amma kuma ka kasance mutum na ƙwarai, cikin al'umma? Kuma yanzu wani mugunta ka ke son sake yi min, bayan wanda ka yi? Akan me zaka faɗi wannan maganar rashin hanakali..?!". Dariyar da ya fitar ne yasa Amna shiru suna cigaba da kallonsa, shima Shuraim ya samu damar zama da ƙyar, "shin dama ke a tunaninki shi ɗin mahaifinki ne? Ohhh sorry bai taɓa sanar da ke ba ne?" Wani irin sauti Amna ta ji ya shige mata can cikin zuciya, sai da ta lumshe ido ta buɗe saboda tsaban haushi ko kuma tsoro ne m'a bata sani ba. Shi kuwa Dady ya juya zuwa ga Baba ba tare da ya ɗauki allurar da ke ƙasan ba, ya ce, "ka ga Hussain,i ka yi ma wannan 'yarinyar riƙon nan na ka bayani da kanka ko zata fahimta, ka yi mata bayanin cewa, cewa ba kai ka haifeta ba". Ba Amna kaɗai ba, hatta Safna da Shuraim sai da suka dakatar da numfashinsu, domin jin abin da Dady ke faɗi game da mahaifin Amna, ko da Safna sai yanzu ta san mutumin mahaifin Amna ne, shiyasa ya razana ranar da ya ganta. Baba kam hawaye ne ke ta zarya à idanuwansa. "Wani irin magana, ka ke faɗi ne Zabba-ba? Jamilu na yi dana sanin kiranka Dady da na yi a tsawon zamana cikin gidan nan! Kai ne Zabba-ba shugaban ƙungiyar Pospa, kai ne ka lalata tarbiyyar al'umma da dama, ka yi silar rabuwata da ahalina, ka yi silar rabuwar Safna da mahaifiyarta, komai da komai duk kai ne, sai dai ni na san wani abu ɗaya! Da alama kana tsoron abin da zamu iya yi maka ne, shiyasa ka turo aka shammace mu ta baya ɗazu! , Hakan ya kassara izzar da ka ke ji da shi, sannan kuma wani ƙarin kuskuren yanzu kana faɗa min maganar banza, kai ɗin babu abin da ka sani dangane da ni!". "Ohmm na fa manta ne, ke ce Amna wannan jarumar yarinyar, mara tsoro mai ƙarfin dukan kowa" Dady ya yi manar bayan ya juyo yana girgiza kai tare da yin ƙara a baki, ttath-ttath-ttath-ttath, irin wanda ya ke nuna tausayawa amma na mugunta, sannan ya kuma cewa, "amma kuma abun tausayi, duba halin da ki ke ciki, magana m'a da ƙyar ke fita daga bakinki, babu abin da zaki iya taɓukawa a yanzu, ba ma ke ba har shi ma ɗayan jarumin n'a ki". Ya faɗi tare da kallon Shuraim da shima ke sauke numfashi, sai kuma Dady ya saki murmushi. "Sannan kuma ni ne na sanki, wanda ke ma da kanki baki san kanki haka ba!". Dady na yin maganar ya juya ya yi wa mutanensa alama, babu ɓata lokaci suka kawo kujeran nan kusa da shi, Amna ta shiga cikin kullewar kai daga maganganun Dady, yayin da zuciyarta ya ke cikin wani yanayi mai kama da tsoro. "To bari na faɗa miki wani abu, tun bayan dawowana daga gurin gudanar da aiki na, wanda à tunanin mutane tafiya zuwa Instambul na yi" sai da ya zauna akan kujerar ka na ya kuma faɗin. "To bayan na dawo, na yi ta ɗarsa shakku a kan canjin da Safna ta yi, domin banbancin da ke wanzuwa a gareki saɓanin Safna, amma sai dai bayan ƙaryar da kika yi na cewa aljanu sun shiga jikinki sai na yarda, sai dai kuma, kin daɗa ɗarsa min wani abu bayan ranar da kika shiga ɗakina don bincike a ɓoye, a idona kika shiga cikin ɗakin, kuma ko ƙarar takalmin da kika ji, na yi sa ne don ki samu dabarar ɓoyewa ba tare da na kama ki ba, sannan bayan na shiga cikin ɗakin na san da cewa kin ɓoye a bayan labule, kuma shiga toilet da na yi, shima n'a yi sa ne don na baki damar fita, na yi mamaki sosai da tunanin me dalilin Safna na zuwa ɗaki na? Kuma alama ya nuna akwai abin da ta ke nema a cikin ɗakin, amma kuma na samu amsa ta ne washe garin ranar". Ya tsaya da maganar da ɗago hannunsa yana ganin ciwon da Amna ta ji masa, shafa gurin ya yi da ɗayan hannunsa ya shafi jinin da ke zaune a wurin, ya ce, "washe gari ɗaya daga cikin ma'aikatana ya zo, ya razana sosai ko da ya ganki, ya sanar da ni cewa tabbas sun kashe ki, har suka labarta min yadda komai ya faru cewa kin faɗa rami, na yi mamaki sosai da tunanin ya akayi hakan zai faru, daga nan na yi bincike a kanki na gano komai. Fitan da kika yi ta ƙofar bayan company duk na san da komai, domin kuwa na ganki cikin cameran da ke a cikin office ɗin, wanda ni ne na saka shi. Sannan ɓangaren bayan a kwai ma'aikata na masu aiki a ciki. Kun nufi kogo ba tare da sanin tuni na riga da na ɗauke Hussaini daga wannan wurin ba". Sai da Amna ta tuna abubuwan da suka faru, tabbas ta ga wasu alamu akan fiskar mutumin da ta gani tare da Dady, washe garin ranar da ta shiga ɗakinsa, wanda ta yi mamakin yadda mutumin ya amsa mata gaisuwa, sannan kuma a hanyarta ta fita bayan ƙofar company, nan ma taga abubuwan da zuciyarta ya sanya mata shakka da wurin. Dady ya ɗora da cewa, "kun je kun tarwatsa mana ragaman duka ayyukan mu da ke cikin kogo! Kun ɓata mana komai da ke cikin wannan wuri, kun kashe mana shahararren matsafinmu! Ba shi kaɗai ba, hatta duk wurin da muke amfani da shi na kogo duk kun salwantar da shi, a haka kuke ganin zan rabu da ku?!". Ya kai ƙarshe da ɗaga murya, sai kuma ya yi murmushiya ce, "noo i never do that!, da ba don aikin chemicals ɗina ya kammal ba, da kun min gagarumin àsara, amma ba komai, yau ne ranar da komai na zai cika!". Sauraron abin da ya ke faɗa kawai su Amna su ke yi, yayin da suke cigaba da jin mamakinsa da yawa, ya riga da yasan duk motsinsu ba tare da sun an kare ba. Shi kuwa Dady magana ya kuma yi da faɗin. "Amma kafun nan, ina son na kuma baku wani labari mai daɗi, kuma na tabbata zaku ji daɗinsa fiye da kima!" Yana yin maganar ya iso inda Amna da Safna suke, "Amna kin san wacece ke?" Ya faɗi haɗi da tsugunnawa Yana murmushin gefen baki, Amna ba ta ce masa ko ƙala ba, haka su Shuraim ma, "ok babu buƙatar amsawarki, ni zan baki amsa, kamar yadda na ce daga farko, babu wata alaƙa da ke tsakaninki da wancan ɗan jaridan, to amma kin san wacece mai kamannin kin nan wato Safna?". Nanma Amna bata ce komai ba, sai bugu da ƙirjinta ya ke yi babu hutu ko kaɗan, Safna bata bar kallon Dady ba, kamar yadda Shuraim ma bai yi hakan ba, so su ke kawai su ji abin da Dady zai faɗi, "ita ɗin 'yar uwarki ce, ma'ana, 'yar biyunki ce!" Wani irin duka maganar da Dady ya yi ya bugi kunnuwan Amna da Safna, sai Shuraim da ke gefe, da sauri Amna da Safna su ka haɗa ido suna kallon junansu cukin rikicewa. Safna ce ta dawo da kallonta kan Dady ka na ta ce, "imm, me ka ce?!!" Amna kuma ta ce, "kai wani irin mutum ne? Eh na yarda da cewa kana sane da ko ni wacece tun tuni, amma ina son ka sani! Ƙaryar da ka ke shirin zayyano min ba zan taɓa amincewa da shi ba!, eh Safna kamar 'yar uwa take a wuri na, domin haka n'a ɗauketa tun kafin na ganta, amma ina mai umurtanka da ka kiyaye harshenka!". "Kina burgeni da kasancewarki Jaruma Amna, domin da ba don tsanar da na yi miki ba, da zan iya ɗaukanki aiki ki zama ɗaya daga cikin ma'aikata na," sai kuma ya isa inda kujerarsa ya ke haɗi da dafa saman yana cewa, "baku kai wa'yan da da zan m'a ƙarya ba, domin so na ke kawai kusan ɗan wani abu kaɗan, domin kada ku mutu cikin duhun kai. sannan kun san me abun burgewan?" Ya yi musu maganar tare da juyowa yana kallon dukkansu, "ni ne wanda ya yi sanadiyyar rabaku tun ranar da aka haife ku!". Wani sabon mamakin da kuma tashin hankali, su Amna su ka sa ke kallon junansu sannan suka maida kallonsu kan Shuraim da shima cikin mamakin ya ke, babu ɓata lokaci suka ji Dady ya kuma tarar mamakin na su da wani masifaffen tashin hankalin da ya gigita tunaninsu. Cikin maganganun da ya fara zayyano musu, "To bari ku ɗan saurari wani labari mana, yadda kan ku zai fita daga cikin duhu" __SHEKARU DA YAWA A BAYA, ni da Abubakar mai daraja wa da ƙani ne, shine babba ni kuma ƙaninsa, tun tasowansa mutane ke sonsa, ko muna zaune ni da shi akan iya tsallake ni à miƙa masa abu, kyauta irir-iri ake masa, amma ni yadda kasan kashi haka mutane suke mai da ni, sai dai shi ya bani bayan an ba shi, abun nan ba ƙaramin ɓata min rai ya ke ba, haka har nake tunanin me yasa aka tsane ni shi kuma ake sonshi? Duk da cewa halayyarmu ya sha banban da na juna__ Tsayawa Dady ya yi yayin da fiskarsa ta bayyanar da ɓacin rai, sannan ya cigaba da cewa. __haka muka yi ta kasancewa har zuwa girmanmu, wani ƙarin baƙin cikin, sana'ar da ya fara yi wanda har na kan yi masa dariya akanta, ina ce masa wannan sana'ar audugan wahala ce kawai, ba zai taɓa iya riƙe mu ba, amma ya ƙi daina yinsa, har ya ke ce min mai nema yana tare da samu, kuma duk mai son ci gaba sai ya yi haƙuri ya dage, shiririta kawai na ɗauki zantukansa, sai gashi daga baya lamari ya fara sauyawa, wannan sana'ar audugan da ya ke na zuwa gonarta, sai aka dawo kawo masa yana siyarwa, kamar da wasa sai ga shi da kamfanin kansa cikin watannin da bai wuce shekara ba, na yi mamaki sosai da kasancewar hakan, sai dai amma ina ganin cewa koma yaya wata rana wannan kamfanin zai rushe.

Chapter 47 of 56