Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"ƙanwata kenan, to lafiya ake nema na haka?" "Dama yaya Shuraim i want say, i love you" murmushi ya yi ya ce, "of cause i know you love me, and i love you too, be cause your my best little sister" Safna ta sunkuyar da kai ta kuma cewa, "ba fa irin soyayyar da ka ke nufi ba, ni ina sonka kuma zan aureka yaya Shuraim" murmushi mai sauti ya yi ya ce, "yau tsokana ake son yi ne?". "No yaya Shuraim gaskiya na ke faɗi" "whattt!!" Shuraim da Yazeed su ka ambata da ƙarfi a tare. Jin sautinsu ya fita a tare ne ya sanya Yazeed nufowa ƙofa don ya ji me yasa Shuraim ya ambaci hakan, kamar yadda shima Shuraim shigowa falon ya yi don ya ga me yasa Yazeed faɗin haka, Safna ta biyosa shi kuma Yazeed Amna ta biyo shi Tsayawa su ka yi lokaci ɗaya, Yazeed na kallon Safna da ke bayan Shuraim, shi kuma Shuraim na kallon Amna da ke bayan Yazeed. Last part. ___________________________________________________ Kun dai ji komai da ya faru yau 'yan uwan arziƙi, Dady yaso kashe su Amna amma ya koma kansa ya mutu. Hmm sannan ga Safna ta ce da Shuraim tana son shi, sannan kuma Amna ta ce da Yazeed tana son shi, to ko abun zai juya ne? Mu kasance a kashi na gaba idan Allah ya kaimu. *_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_* ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣7️⃣7️⃣▶️1️⃣7️⃣8️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar _🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_ *_END_* Tsayawa su ka yi lokaci ɗaya, Yazeed na kallon Safna da ke bayan Shuraim, shi kuma Shuraim na kallon Amna da ke bayan Yazeed. Da sauri Shuraim da Yazeed su ka haɗe zuciyarsu na bayyanar da yanayin fargaba, "me ta ce maka?" Nan ma su ka yiwa kansu tambayar a tare, su ka kuma amsawa a tare, "kai me ta ce maka?" Amna da Safna ne su ka fara dariya ganin yadda hankalinsu Shuraim ya tashi, su Yazeed su ka juya suna kallonsu cikin rashin fahimta. Ta bayan Shuraim ne ta ɗaga hannunta ta sanya a wurin tabo da ke gefen bakinta ta cire shi, sannan ta mayar da hannun zuwa ƙwayar ido ta cire eye colour, nan fiskarta ya bayyanar da Amna, fidda ido da mamaki Shuraim da Yazeed su ka yi, à hankali su ka juya gurin Amna da ke bayan Yazeed, tun da ga Safna ta koma Amna, to wannan Amnar fa?. Ganin dukkansu sun sanya mata ido ya sanya ta ɗaga ƙyallen hankicif ɗin da ke hannunta ta fara goge kwalliyar da ke fiskarta, tana gama sharewa su ka ga tabon gefen bakin ya bayyana, domin dama hodar da aka shafa sosai ne ya ɓoyesa., sannan ta ɗaga hannu ta cire eye colour ɗin da ke jikin idonta, nan fiskarta ya koma asalinta wato Safnan, dariya su ka kuma sanyawa suna kallon su Shuraim, Safna ta ce, "kai masoyiyata, dama haka ki ka sha wahalar sanya eye colour?" Amna ta yi dariya ta ce, "ke dai bari, kuma duk MR ɗin nan ne ya yi ta ba ni wahala". 'Wato dai dama shiri aka yi gagarumi kenan? Amna ta zo min à Safna sannan tana faɗin tana sona" cewar Shuraim, Yazeed ma ya ce, "nima Safna ta zo a matsayin Amna sannan ta ce tana so na, 'yammatan nan wai duk a ina ku ka koyo wannan tsokanan ne? Kun rikita mana ƙwaƙwalwa kawai" Murmushi Amna su ka yi sannan Amna ta ce, "ehhh toh, mu dai kawai ji mu kayi muna da buƙatar nishaɗi, shi ne fa muka shirya wannan wasan, ko habibty Safna?" Safna ta giɗa kai, "oh oh ohhhh, wato nishaɗi ko? To ai kuwa sai na rama" cewar Shuraim, Yazeed ma ya kalli Safna ya ce, "nima sai na rama". Amna ta ce "to tsaya, amma taya zaku rama? Bayan ku dai ba ku da masu kamanninku kamar mu, don haka kuwa, sai dai ku haƙura brothers" Safna ta giɗa kai alamar ai kuwa. Tafin da su ka ji a bayansu ne ya sanya su ka juyo dukkansu, Mubarak su ka gani da Raheena sun shigo falon, "kai kai, ni dai idan zaku sake irin wannan wasan ku faɗa min saboda in yi shirin ɗaukarsa, domin kuwa na san zai zama film ɗin da ba a taɓa yinsa ba a duniya". Dariya su ka sa sannan Safna ta je ta kama hannun Raheena tana faɗin, "yaushe ki ka zo besty?". Raheena ta ce, "yanzu zuwana, amma ban zo da wuri ba ga shi ɗaukar ya ƙare" "ɗaukar me?" Faɗin Safna, Raheena ta juya ta kalli Mubarak su ka yi dariya ta ce, "ɗaukar wasan da kuka haɗawa yaya Shuraim da kuma Yaya Yazeed" murmushi su ka yi dukkansu Su Shuraim su ka ce, "rabu da su zamu rama ai, ta yu muma muna da na mu 'yan biyun ba mu sani ba, don haka zamu nemosu". Cikin nishaɗi su ke hira su shidda, "ni fa akwai wani tunanin da na yi, Muba na ga kamar akwai wata iska da ya kaɗa a tsakaninka da Raheena, don haka me zai hana ka bayyana mata a yau?" Saurin kama hannunta Raheena ta yi a hankali tana cewa, "ke ƙawata me haka?" "gaskiya na faɗi, ko brothers?" Cewar Amna tana kallon Safna, su Safna suka giɗa mata kai alamar ƙwarai kuwa, "to ɗan uwana Mubarak ka faɗa mata anan? Ko ba komai zamu zame muku shaida, na yi gaskiya?" Cewar Shuraim shima Yazeed ya ce, "sosai ma, Mubarak kai muke saurara". Gaba ɗayansu hankalinsu kan Mubarak da ya ke yi musu kallo kawai, Raheena kuwa duk kunya ya isheta, har ji ta ke ma da bata zo ba, akan ne Amna za ta ce haka?. Tasa Mubarak su ka yi suna ta yi masa surutu akan sai ya shaidawa Raheena cewa yana sonta, ya amince ya so ta. Gajiya ya yi da yadda su ke yi masa hakan yasa ya miƙe a fisace ya ce, "ya ishe ni!" Yadda ya yi maganar ya sanya su miƙewa daga zaunen da su ka yi, suna kallonsa da mamaki. Raheena kuwa kallonsa ta ke yi zuciyarta na bugawa gabanta na faɗuwa, yadda ya miƙe a fisacen nan ya nuna mata cewa ba ya sonta, duk da cewa ba ta gama gane abin da ta ke ji akansa ba, amma ta san idan har ya ce baya sonta zata ji babu daɗi sosai cikin ranta. Mubarak ya kuma cewa, "kun isheni sai ƙoƙarin tursasani ku ke yi! To akan me za ku tirsasamin akan abin da na riga da na so shi!" Gaba ɗayansu su ka sake fiska suna kallonsa jin maganar da ya faɗa, Raheena ba ta gama gane abin da ya ce ba ta ga ya kalleta yana cewa, "tabbas na daɗe da sonta, kuma ina son in aureta" ya faɗi yana murmushi, ita kuwa Raheena saurin ƙasa ta yi da kanta zuciyarta na bugawa. "Me ya ke faruwa a wurin nan?" Faɗin Ummee da su ka sauko daga upstair su da Ammu, sauran kallonsu Ammu su ke suna murmushi. Raheena ce ta rikice saboda kunya, ta yi saurin cewa, "am ina wuni Ummee ina wuni Ammu, am dama ni yanzu zan tafi, sai anjimanku" tana faɗi ta yunƙura zata tafi Ammu ta ce, "ina zaki? Ai mun riga da mun ji komai" rintse ido Raheena ta yi don kunya ba tare da ta juyo ba, kuma ta kasa tafiya. Sauran ne su ka saki murmushi mai sauti, Ummee zuwa gurin Raheenar ta yi haɗi da kama hannunta, hakan yasa Raheena juyowa amma ta kasa haɗa ido da Ummee, "na yi farin ciki da wannan al'amari, kuma na amince da ki zama surkata 'yata" a hankali Raheena ta ɗaga idonta tana kallon Mubarak da ke ta faman washe baki, suna haɗa ido ya kashe mata ido ɗaya, hakan yasa ta yi saurin sunkuyar da kai tana cewa, "nagode Ummee, am dama Momyna ta ce kada in daɗe, na tafi" tana faɗi ta juya da sauri ta bar falon. Murmushi dukkansu du ka yi, Ammu ta dubesu bayan ta ƙaraso, "wato ku ga ku masu yin haɗi ko? To ko ku kun samo wa'yan da ku ke so?" Ammu ta faɗi tana kallonsu, nan dukkansu su ka rikice, da ɗaiɗaya su ka bar wurinsu Ummee, juyowa Ummee ta yi ta kalli Ammu sai su ka sa Dariya, "Ja'iran yara" faɗin Ummee. Amna ce zaune kan gado tana waya da Zarah, ɗazu Shuraim ya bata wayarta wanda ya sa aka amsa tun ranar da aka shirya barinta garin Kaduna, cike da kewa su ke wayar ita da Zahra, "ashe Nabila ta yi aure? Ayyaah, amma na ji haushi da ba na nan, ki ka ce ke ma aurenki saura sati ɗaya yau? Ah dole na zo, don haka kar ki damu Zarah, insha Allah aurenki da ni za'a yi, kawai ke dai ki jarayi zuwa na, zanzo miki da labari irir-iri" a haka su ka yi sallama da Zarah cikin farin ciki. An kammala ginin gidan da Mai-daraja ya sa a rushe, hakan yasa ya mallakawa su Baba takardun gidan da kuma mukulli, bayan haka ya haɗa da mallakawa Baba wasu dukiyansa, su Baba sun yi farin ciki matuƙa, sanna su ka godewa Allah da ni'imar da ya ba su, sanadiyyar Amna ga shi rayuwarsu ya canza. BAYAN WATANNI UKU. Ƙarfe goma sha ɗaya na safiyar ranar Juma'a. Gaba ɗaya mutane sun cika a babban masallacin don ɗaura aure guda uku. Har da uncle Tukur ya zo bikin shi da matansa, domin kuwa tun bayan da komai ya lafa Baba ya je ya same shi. Babu ɓata lokaci aka ɗaura auren, (Mubarak Hussaini & Raheena Mus'ab) sai kuma aka ɗaura auren (Shuraim Abdurrazak & Amna Abubakar Mai-daraja) sai kuma auren (Yazeed Jamilu & Safna Abubakar Mai-daraja) Alhamdulillah kowa ya fara faɗi cikin farin ciki, yayin da angwaye sai washe baki su ke yi babu hutawa, farin cikin da ke cikin zuciyoyinsu babu misaltuwa, sanye su ke da manyan kaya gare masu shegen kyau da kuma tsada, wanda anko su ka yi dukansu.yayin da acan gefe kuma iyayen na su maza ne suma cike da farin ciki. Can gida kuwa. Mutane ne cike a gidan sai hidima ake ba kama hannun yaro. Hajiya da Ladingo tsaye gefe, itama kayan da ta sanya wanda su ka yi anko da su Ammu ne ya yi mata kyau sosai, Ladingo ta ce, "Hajiya dai komai ya zama ba yadda aka so ba, yanzu shikenan kin saduda?" Sai da Hajiya ta wurgawa Ladingo harara sannan ta ce, "ko shakka babu ƙarya cikin maganarki, ke idan ma akwai abin da ya fi kalmar saduda ki faɗa, domin kuwa ni tuni na riga da na tuba, saboda na ga izina iri daban-daban bayan abubuwan da su ka faru, yanzu haka maganar da na ke yi miki ɗin nan, babu abin da ya ke wanzuwa araina face farin ciki, ɗana Yazeed zai auri yarinyar da ya ke so, kuma yarinyar kirki, yaran nan duka yanzu na ɗaukesu tamkar 'ya'yana, don haka babu wata mummunar shawara da zaki bani wanda zai yi aiki a kaina, kuma ya kamata kema ki gane kuma ki daina abin da ki ke yi, saboda abun da ki ke yiwa yaranki shi ya hanasu cigaba a rayuwa". Numfashi Ladingo ta yi ka na ta ce, "hmm ai faɗa ma ɓatawa, tuni na riga da na nemi yafiyar 'ya'yana kuma sun yafe min, sai dai na riga da na yi asara, saboda ni ne na ja aka kori yarana daga aiki, gashi yanzu abun da zamu ci ma gagaranmu ya ke yi, ina faɗa miki wata rana haka na ke kwana babu abin da na ci, ga jikokina duk sun dawo gurina, saboda na sa an saki iyayensu, da ace su nan da zasu rinƙa ƙuƙutawa su nemo abin da zasu taimaka mana, saboda dukka matan yarana sun iya sana'ar hannu, amma yanzu komai ya lalace, kuma wani abun baƙin cikin ma, ashe ɗan autana ya saida gidan nan ba mu sani ba, ya sace takardun gida ya sayar har ya kashe kuɗin, yanzu haka nan da sati aka bamu mubar gidan, shine fa na ke cewa idan na zo gurinki in nemi afuwa, ko zan samu kuɗin da zan kama haya? Ki taimaka min ƙawata Zainab". Itama Hajiya sai da ta ja numfashi sannan ta ce, "wato dama ke kin tuba, amma ni ki ka zo ki sake harzuƙa ni. To shikenan ba damuwa, ki ne mi gida mai kyau insha Allah zan siya miki" zare ido Ladingo ta yi cike da mamaki ta ce, "Zainab wai da gaske ke ce? Ke ce zaki siya min gida?" "Ba shakka, to da wa ce? Ba na son iskanci fa" cewar Hajiya, cikin farin ciki Ladingo ta ce, "kai amma nagode nagode nagode ƙawata, wayyo farin ciki zai kashe ni". Hajiya ta dubeta ta ce, "da ba don mutanen nan mutanen arziƙi ba ne, da ƙila sai dai ni innemi taimakonki, amma zama su ke da ni kamar babu abin da ya faru, sun mallaka min wani ƙayataccen gida, da kuma kuɗaɗe masu tarin yawa, ni ce na nemi da su barni in cigaba da zama tare da su, hakan yasa su ka amince, babu abin da zance sai in godewa Allah da ya nufe ni da shiriya tun kafin na mutu da haƙƙin wasu akaina, shiyasa na ke son aikata ayyukan alkhairi, yanzu da na ji mutum na neman taimako da gudu na ke taimaka mishi, hatta 'yan uwana na koma na nemi gafaransu" Ladingo ta ce "Ƙwarai kin yi sa'a kam, nagode da wannan taimako" Hajiya ta kuma cewa, "amma fa ba wai ki je ki samu gida mai tsada ba, ki samo ɗan daidai kar ki nemo mai kuɗi dayawa, ah to" kallonta Ladingo ta yi domin ta ga har yanzu halin fa bai tafi duka ba. Kira ne ya shigo wayar Hajiyar ta ɗaga, Marwan cikin farin ciki ya sanar da ita an ɗaura aure. Saboda tsabar farin ciki ta bar Ladingo tsaye, tana shirin komawa ciki ta sanar da su Ammu labarin mai daɗi, tana hawa upstair da sauri kawai ƙafanta ya lanƙwashe, hakan yasa ta faɗi akai tare da gangarawa tana ƙara. Mutane su ka yo kanta da sauri suna salati. Amare Amna da Safna ne zaune a ɗaki, suma cikin ankon na su na less mai tsananin kyau, sai ƙawayensu da su ka zo, har da su Zarah da Nabila ma sun zo, sai hira su ke gwanin sha'awa da barkwanci, sun kira Raheena vidéo call sai hira su ke kamar suna tare, domin da ba don ba zai yu ba ma, da tare zasu kasance. Suna à haka aka shigo aka sanar da su abin da ya samu Hajiya, cikin tashin hankali su ka tashi su ka fito, kamar yadda uwayen Amare ma su ka fito, kan Hajiya su ka yi babu ɓata lokaci aka yi asibiti. BAYAN WASU AWANNI. Hajiya ce kwance a gadon asibiti, anyi mata triment ɗin inda ta ji ciwuka, so ta ke ta tashi amma Nurse ta hanata, ko da ta tambayi me yasa Nurse ɗin ta hana ta? Kafin ta bata amsa aka kirata a waya, hakan yasa ta juya haɗi da ɗaga wayar, "eh ta riga da zama gurguwa, don ina ganin yanke ƙafar za ayi ma" abun da Hajiya ta ji Nurse ta faɗi daga wayar. A take Hajiyar ta ɗaga kanta sama, zantukan da ta sha yi ne ta fara tunawa, "wallahi akan Yazeed ya auri Safna, gwara in ƙare rayuwata a gurguwa!" "Na gwammace gurguwa ce ni akan Yazeed ya auri Safna" "Ke sai dai idan na dawo gurguwa ba zan iya zuwa inganta ba, to shine zata auri ɗana" wa'yan nan su ne magan-ganun da ta sha yi lokaci da dama a baya, idan tana magana da Ladingo. Sauke kanta da ga tunanin maganganunta ta yi, Nurse da ta gama wayar ta juyo tana kallonta, kawai sai ta ga Hajiya ta fashe da matsanancin kuka, hakan yasa Nurse da ta gaji da cewa ta yi shiru ta fice, sai ta dawo da su Ammu dukkansu, kama da ga su Baba da dai sauran, dama zuciyarsu na tsinke suna jiran ganin awani hali Hajiyar ta ke?. Tana cikin kukan ta kira Safna, domin duk haƙurin da mutane ke ba Hajiya ta ƙi sauraransu, zuwa kusa da ita Safna ta yi damuwa na fiskarta, kama hannun Safna ta yi ta zaunar da ita a kujerar, ba tare da ta saki hannun Safnan ba ta ce, "yata ina mai ƙara ba ki haƙuri, kin ga yadda na dawo yanzu ko? Don Allah ki sake ya fe min kin ji?" Safna ba ta fahimci inda Hajiya ta dosa ba, amma sai ta ce da Hajiya, ai ita ta riga da ta yafe mata. Hajiya dai ta inda ta ke magana ba tanan ta ke fita ba, babu wanda ya fahimci me yasa Hajiyar damuwa, "Hajiya wasu irin magana ki ke yi ne? Ba fa wanda ya fahimci maganarki" cewar Yazeed yana kallon Hajiya, Hajiya ta tsaida kukan da ta ke ta ce, "au su likitocin ba su sanar da ku cewa na zama gurguwa har sai an yanke min ƙafa ba? Kuma duk ni na jawa kaina, da ace lokacin da na ke furucin cewa akan Safna ta auri Yazeed gwara na ƙare a gurguwa, da ace wani maganar na yi mai kyau da yanzu hakan bai faru da ni ba, amma yanzu ga shi ana ɗaura auren maganar da na sha yi ya tabbata, ashe dai 'yan ameen sun amsa". Hajiya ta faɗi tana kuma marairaice fiska tana kuma yin dana sani. Sa dariya kowa da ke wurin ya yi saboda yadda ta ƙare maganar, sakin baki Hajiya ta yi tana kallonsu, sai ta kuma sanya kuka tana cewa, "eh na sani, dama na zama abin dariya, ga shi yanzu a gurguwa zan ƙare rayuwata, oh ni Zainabu" "Hajiya wai wa ya ce miki kin zama gurguwa?" Cewar Yazeed, ɗaga kai Hajiya ta yi tana nuna Nurse ta ce, "ita ce ta ke waya da cewa na zama gurguwa". Nurse ta ce, "madam ni fa ba da ke na ke ba, magana na ke akan mageta da ta samu matsalar ƙafa, kuma aka ce sai an yanke, ba da ke ba fa" "da gaske ka ke? To amma me yasa ki ka hanani tashi? Sannan ga ƙafata a kewaye da farin yadi?" Cewar Hajiya tana ƙoƙarin tashi tare da washe baki, Nurse ta ce, "na hana ki tashi ne saboda za azo akunce miki yadin". Bayan an kwance yadin da aka ɗaura akan ƙafar Hajiya, wanda dama ba wai na wata matsala ba ne, sai aka sallami Hajiya su ka koma gida. WASHE GARI. An kammala duk hidimar biki, yanzu saura akai ko wace amarya ɗakin mijinta abun ƙaunarta, ɓangaren Raheena iyayenta da 'yan uwanta sun tasa ta a gaba, sai nasiha su ke yi mata. Haka ɓangaren Amna da Safna, su Ammu, Hajiya, Ummee, Mamma, da wasu manya su na ta yi musu nasiha, kamar yadda filinsu Shuraim, Yazeed, Mubarak ma suna a gabansu Mai-daraja, Baba, uncle Musa, uncle Tukur da dai wasu. Ko wani ɓangare nasiha ake zubawa mai ratsa zuciya, daga ƙarshe dai aka tashi daga wannan zaman, amare sai kuka su ke yi suna rungume iyayensu, yayin da iyayen ma idonsu ke ta fitar da hawaye. Sun yi ta godiya ga Allah da ya kawo wannan rana. Haka rayuwa ta cigaba da kasance musu cikin farin ciki, Marwan ma da amaryarsa Sumee, a yanzu sun shirya babu abun da su ke zubawa ga junansu sai ƙauna da jin daɗi................................. Final part. ___________________________________________________ *ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!* *DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAHU SUBHANAHU WATA'ALA, MAMALLAKIN KOWA DA KOMAI, TSIRA DA AMINCI SUN TABBATA GA ANNABINMU ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) DA AHALINSA DA SAHABBANSA.* *INA ƘARA GODEWA MAHALICCINA DA YA NUFE NI DA KAMMALA LITTAFIN AMNA DA SAFNA CIKIN AMINCI, BA TARE DA WANI TARGATSO BA, SANNAN INA GODIYA A GAREKU MARA MISALTUWA, MABIYA WANNAN LABARIN, NAGODE NAGODE NAGODE MUKU, INA YI MUKU FATAN ALKHAIRI KAMAR KO DA YAUSHE* *SAI MUN HAƊU DA KU ACIKIN LITTAFIN SANADIN ƘADDARATA, AFTER EDITING INA FATAN ZA KU KASANCE TARE DA NI A CIKINSA IDAN ALLAH YA BA MU IKO* *_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_* *BISSALAM🙏🏻* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 56 of 56