ta kallesa ba ta ci gaba da lallatsa computern tare da ɗan haɗe fiska.
Murmushi mai sauti sosai Shuraim yayi, wanda hakan ya ƙara harzuƙa zuciyar Amna, "oohh! Amma kin iya kalamai masu daɗi, har ji nake kamar zuciyata zata shiɗe, ok to me kike so?" Ya faɗi cikin sanyin murya. Ahalin yanzu Amna ta rasa me ta keyi a cikin computern, domin sai kaiwa take tana kamowa da hannunta akai, domin zuciyarta sai wani tafarfasa yake yi, wani zafi da baƙin ciki ne ke ta zarya a zuciyarta, sai danna madannan computer take da ƙarfi, hannunta na rawa alamar rashin nutsuwa.
"Aiih my love! Abun da kike so kenan? To kamar kin samu, duk abun da kike so zan mallaka miki, kai tsaye ki ƙara sanar min abun da kike so, ni kuwa zan baki ba tare da ɓata lokaci ba, imm da gaske nake" Shuraim ya kuma faɗi tare da sakin murmushi mai sauti wanda ya fi na ɗazu ƙara. Amna bata san lokacin da ta ture computern ba, domin sai da ya kusa faɗi daga teburin, sannan ta miƙe tana kallonsa cike da ɓacin rai, da sauri ta taka izuwa gabansa haɗi da fisge wayar, da kallon mamaki ya bi ta, yadda ta fizge masa waya sannan ga yadda take fitar da numfashinta da sauri da sauri.
Ita kuma magana ta fara yi cikin ɓacin rai da zafin zuciya, akan lamarin da bata san me dalili ba. "Wannan wani irin abu ne eh!? Akan me zaka shigo kana waya da budurwarka? Idan wayar kake son yi me yasa tun daga waje ba kayi ta ba? sai da kazo inda nake? Wannan wani irin cin fiska ne haka? Ko dan kaga nayi shirun ban kula ka ba? Da nayi shiru me yasa baka fiskanta ba? To ai sai kaje waje kayi duk hirar da kake son yi da...." dariyar da Shuraim ya farayi ne ya dakatar da ita daga tambayoyin masifar da take yi masa ko numfashi ba ta saukewa.
Kallonsa take da mamakin dariyar da yake yi mata, "akan me kake yi mini dariya!? Ko kana ganin abun da kayi daidai ne!" Barin dariyar yayi da kallonta yana kuma yi ciki-ciki ya ce, "me yasa ranki ya ɓaci haka? Ko dai kishina kike yi ne?" "Ni dai! Kuma kishinka? To akan me?" Ta faɗi har da wani taɓe baki, "kawai dai haka kika ce, amma ni na ga alama, amma kuma ya kamata ki sani bai kamata kiyi kishina ba, domin budurwata ta fiki kyau da tsari, because she's special!".
Cikin ƙarin baƙin ciki ta ce, "zancen ƙarya kake faɗi, duk budurwar da zata so ka bata isa ta kai ni ba! domin baza ka samu iri na ba" "oh oh oooh, 'yanmata kar ki zaƙe da yawa haka, domin zaki kunyata ne if you see her, idan kuma kin ce ba haka ba, to ga tanan ki kalleta ko a video call ne kafin zahiriyyarta" ya faɗi tare da nuni da wayar da ke hannunta dama kirar bai katse ba, "shikenan zamu gani!" Ta faɗi tare da yaƙini akan tasan ko wacece m'a bazata kaita kyau ba, sannan ta fara ɗaga wayar dake hannun na ta idonta na kanshi, sannan ta maida idon kan wayar.
Zaro ido tayi sosai zuciyarta na bada bugun dakan turmin ƙarfe, sosai take kallon glashin wayar kamar tana gasar zare ido, kallonsa tayi cike da mamaki. Shi kuma ya ɗaga mata gira yana faɗin "Kin ga abin da na gaya miki ko? Ta fi ki kyau da komai" maida kanta ga wayar tayi zuciyarta na ci gaba da bugun sittin saba'in, durƙushewa tayi à kan tayis ɗin ofishin mai ɗaukar ido, idonta na cika da hawaye, take suka fara kwaranyowa ba tare da ta shirya musu ba, sosai take hawaye harda shashsheƙa.
Da ƙyar ta iya buɗe bakinta da yayi mata nauyi ta furta, "Mammah! Ummeeh! HMubarak!" ta faɗi tare da fitar da iska daga bakinta, su Mamma da su ne akan wayar suma suka fashe da kuka, kowannensu kuka yake mai ratsa zuciya, kuka ne mai cike da kewa da kuma soyayya, sun ɗau kusan mintuna biyar a haka, Amna hawaye take yi, su mamma kuma harda sauti, shima da kan sa Shuraim ɗin sai da idon sa ya kawo ƙwallah, har wani yanayi yaji a jikinsa da ya kasance sune silar raba Amna da ahalinta.
Ummee ce tayi juriyar fara magana da cewa, "ƴata kina lafiya ko? Babu abin da ke damunki? Yi min magana inji miryarki" Mamma ma ta amshe, "Aminatuna mun yi kewarki sosai da sosai, fatan kina lafiya?" Mubarak ma ya ce, "Amna 'yar uwata kiyi magana don Allah" sai da ta matse ƙwallan da ya sake cika à idonta, wani irin yanayi ta ke ji yau ta ga wa'yan da ko da yaushe take burin gani, tayi kewansu har ta gaji, buɗe idon tayi tana ci gaba da kallonsu, cikin farinciki maƙura ta buɗe bakinta ta fara faɗin, "ina lafiya sosai, idan ma akwai abun da ke damuna bai wuce ku ba, kuma kuna lafiya? Na yi ta tunaninku sosai, da fargaba iri daban-daban" ta faɗi hawaye na sake fita daga idanunta, wanda hakan ya ƙara sa suma su Mamma na su ya cigaba da fitowa da hawaye.
"Kuyi haƙuri, ku daina kuka, ko da yaushe so kuke kuga juna, to amma me yasa yau kuma kuke kuka? Ko dai yau sai hawayen ya shanye maganganun da zaku yiwa junanku ne?" Shuraim da ke tsaye sun cika shi da tausayi ya faɗi hakan da zolaya. Murmushi dukkansu sukayi tare da share hawayensu Mamma ta ce, "ja'irin yaro! Idan maganar tamu ta tafi kai ka ne mota ai" dariya sukayi gaba ɗaya, Shuraim ya kuma cewa, "eh mana zan nemo muku maganar, amma sai na samu kwale-kwale saboda iyo da shi zanyi cikin hawayen da zaku tara, daga nan sai in kawo muku zantuttuka har gabanku".
Dariya suka sake yi, "wannan yaro baka da dama" Ummee ta faɗi tana share hawayenta, miƙewa Amna tayi ta koma kan kujerarta, tare da maida hankalinta gaba ɗaya kan su Mamma da ke waya, kasancewar à computer aka yi kiran hakan yasa gaba ɗayan su suka fito mata da kyau cikin wayar, juya wayar tayi zuwa ta kwance don ta ƙara ganinsu da kyau.
Nan suka fara tattaunawa cikin shauƙi da kewan juna, "ni na fi su Mamma kewanki sosai" cewar Mubarak Mamma na kai masa dunguri a ƙeya tana faɗin, "ka ji min ɗan shishshigi, wani kewan na ta kayi banda faɗar da kuke yi kamar kaji?" Dariya Amna tayi cikin nishaɗi, Murmusawa Shuraim ma yayi domin ba ƙaramin burge sa su kayi ba, har gani yake kamar shine a matsayin Amna. Ummee ce ta ce, "ai kuwa dai, domin kewar da yayi kenan, sai ya zauna shi ɗaya wai ina ma Amna tana nan, da ya tsokaneta" tura baki Mubarak yayi kamar yadda Amna takeyi cikin ba'a yake kwai-kwayan maganar Amna cikin shogoɓa ya ce, "Mamma Mubarakan ki ne faah".
dariya suka kwashe da shi Amna ta ce, "ai kai dama na san da ƙyar kayi kewata, sai dai kewan haɗa ni da Mammata da kake yi, da kuma yin min rinto a wasa" washe baki suka sake yi, Shuraim ya ce, "wannan kam ai dai dai kenan, kai Mubarak dama haka ka iya wasa?" "To kaga wanda ya maye gurbinka a nan, ba shi da aiki sai tsokanata, don haka kar kaji damuwa ka samu wakili" cewar Amna tana kallon Shuraim.
Haka su kayi ta hira gwanin sha'awa gwanin burgewa, hirar uwa da 'ya, kaka da jika, ɗan uwa da 'yar uwa, tashi Shuraim yayi ya basu wuri, yadda zasu samu damar yin hira da kyau.
Bayan sun ɗau lokaci a haka, Mamma ta ce, "muna nan muna yi miki addu'a Aminatuna, Allah ya baki sa'a har a kammala wannan shiri da Shuraim suka shirya, daga nan kuma komai zai wuce" "insha Allah Mamma, zan cigaba da kewanku har sai sanda muka kasance tare" "ku ji min 'yar jafar uba, to yo ke fa mace ce, zakiyi aure kiyi rayuwa a wani wurin ba damu ba, don haka kima daina wannan tunanin" tura baki Amna tayi tana faɗin, "kai dai Mamma Aminatun ki ce faah" suka ƙare maganar tare da Mubarak, dariya suka kwashe kafin daga bi sa ni Ummee ta ce, "to bari mu barki yanzu, ki cigaba da maida hankali akan aikinki, kuma mun sanki da jajircewa to ki ƙara kinji?".
Bayan sun kashe wayar ta ijje wayar akan tebur tana sauke numfashin farunciki sosai, ta samu sauƙi sosai game da tunaninsu da take. Lokacin Shuraim ya dawo office ɗin ya sameta tana ta yin murmushi, naɗe hannuwa yayi haɗi da jingina a wurin ƙofar, yana kallonta cikin burgewa, bai san lokacin da shima ya saki murmushin ba, ɗago kanta tayi idonta ya dira kan Shuraim da bata ji ƙarar shigowarsa ba, hakan yasa ya bar jikin ƙofar tare da nufa ciki yana ci gaba da murmushi mara sautin.
"Ya kika ga budurwan ta wa?" Ya faɗi tare da ɗaga mata gira, sauke kai tayi ta saki murmushin jin kunya, "dama na ce miki daga baya kunya zaki ji, kuma gashi hakan ta faru" "ba wani kunya, to amma wancan ranar fa? Ranar da na ganka kana waya sannan kana magan-ganu makamantan wa'yannan?" Sai da ya zauna akan kujera ka na ya ce, "ranar ma da Mamma nake magana". "Da Mamma?" "Eh amma dai naga da alama akwai dalilin wannan kishin da kike yi min ko dai...?"
Saurin magana tayi, "a ah ba wani abu, kuma kada ma ka ɗauki hakan da wata manufa, wancan ranar ma ba don kai raina ya ɓaci ba, yau kuma ai damu na kayi shiyasa, amma ba wani abu, gwara ma ka sani" dariya kaɗan yayi sannan ya ce, "ohhhh haka ne? To amma ina da wata tan-tama" miƙewa tayi da sauri ta na sake faɗin, "na faɗa maka ba wani abu bane, gwarama ka cire ko wace tan-tama" ta faɗi tare da ɗaukar wayarta tayi hanyar ƙofa. Sai kuma ta tsaya bayan ta bashi baya, ta ɗan kar-kata kanta kaɗan ta gefe kar zata juya inda yake, sai kuma ta saita kan tare da sakin murmushi mai daɗi har zuciyarta.
Kasancewar ba da wata budurwa yake waya ba yasa taji annashuwa cikin ranta, duk da cewa bata gama sanin manufar hakan ba, barin tsayuwar tayi da wucewa murmushin na maƙale a fiskarta. Shima Shuraim murmushin yayi mai ƙayatarwa, domin yaji daɗin ganin kishinta akansa, shima dai bai tabbatar da meyasa ba.
YAZEED.
Wani irin daɗi ne ya ƙara tsananta a zuciyarsa ganin sun doshi shiga gidan bayan an buɗe babban gate ɗin gidan, numfashi yake ta saukewa a jere a jere. Ana parking ɗin motar ya fito, haɗi da shaƙar iskar da ya kaɗa shi, kallon kewayen da motar yake yayi, gani yayi gurin ya ƙara haɗuwa domin da alama ana ba grass da kuma flowers ɗin kulawa sosai, "my son ya dai, ko kana tunanin canzawar wurin ne?" "Yes Dad, gurin ya min kyau sosai, yana samun kulawa" murmushi Dady yayi ya basa amsa da faɗin, "duk wannan aikin 'yata Safna ce, ita ce take gudanar da abubuwa sosai a gidan nan, ko wani fanni tana bashi kulawa".
"Dad! Kana nufin wannan duk aikin Safnata ne?" Yazeed ya faɗi cikin farin ciki da abun da Dady ya ce, tare da maida idanuwansa yana sake kallon komai na wurin. Cikin rashin fahimta da yadda Yazeed ya kira sunan Safna Dady ya ce, "your Safna?" Sai a lokacin Yazeed ya lura da abun da ya ce, domin shi Dady bai san da wata maganar da ya shafi tsakaninsa da Safna ba, domin Hajiya ta hana shi faɗa masa, "Oh Dady Safna na ke son faɗi baki na ya ƙara harafi biyu" ya faɗi duk da yasan dole zai sanar da Dady komai, amma ai sai sun nutsu tukun, murmushi Dady yayi yana kuma cewa, "ok to mu ƙarasa ciki mana".
"Oyo yo ɗan albarka! Barka barka da dawowa, sannuh, ya hanya?" Cewar Hajiya cije da murna bayan sun kaiga shiga cikin falo, shima Yazeed cike da kewa ya bata amsa da cewa, "fine Hajiya, I'm happy to see you! Hope na same ku lafiya?" Zama Hajiya tayi a kujera ta amsa masa, bayan sun gama gaisuwan ta ce, "to ya kamata muje ka ci abinci, na sa an girka maka abinci kala daban-daban sai wanda ka zaɓa" "to ni dai bari in shiga ciki" Dady ya faɗi yana miƙewa, lokacin Ruki da Saleem su kazo, zama suma su kayi suna yi masa sannu da hanya cikin kewa kaɗan, domin sunyi murna da dawowarsa.
"To muje ka ci abincin ko?" Cewar Hajiya tare da miƙewa, "Hajiya na ce ina Safnah ne? Ban gan ta ba, ko tana ɗaki ne?" Jin kamar saukar aradu Hajiya ta ji cikin zuciyarta, abun da take tsoro kenan, sai gashi tun yanzu ya tambayeta, bata basa amsaba, sai ma kallonsa da take cike da takaici, Saleem ne ya ce, "ka ce Hajiya dai, don yanzu ta fi ƙarfin Safna" kallon rashin fahimta yayiwa Saleem ka na ya ce, "kai me ka ce?" "To ni kuwa me na ce? Ai ba zaginta nayi ba, naga kana min kallo kamar zaka dake ni".
Ran Yazeed ne ya soma ɓaci ya ce, "Saleem kake ko? Ko ka canza sunan? To kar ka ga na dawo yau! Domin ban canza daga Yazeed ɗin da nake ba, don haka respect your self" ya faɗi domin baya son ya katse murnan dawowarsa, idan ba haka ba da ya fara maganin ƙanin na sa, in ma raini ya ƙaro sai ya ji. Juyawa kan Hajiya yayi da take kallonsa kamar gunki, "bari inje ɗakinsu ina ga tana can" ya faɗi tare da tashi don zuwa sashen su Safnan, "ai ba ta can, sun canza ɗaki!" Cewar Ruki da ƙarfi don dakatar da shi da nufa tsohon ɗakin su.
Dawowa inda suke yayi da mamaki ya ce, "sun tashi a ɗakin! To ina suka koma?" Sai da Ruki ta miƙe domin shararo masa rahoto ta ce, "ai ina faɗa maka Yazeed! Yanzu Safna ta zama abun da ta zama, domin..." katseta yayi da faɗin, "naji kamar da sunanta kika kirata?" Yayi mata tambayar yana ƙureta da ido, sai dai ganin yadda take ƙoƙarin koro masa zance yasa shi dakatar da ita, domin shi yanzu Safnarsa ce kawai abin da yake son gani, "Ruki ki dakata da zantuka masu tsawon da kike ƙoƙarin faɗa min yanzu, banda time, just tell me wani ɗaki suka koma?".
"Ɗakin Hajiya! Shine ɗakin da suka koma, kuma sai kaga yadda ɗakin ya dawo, sun gyara shi, harda sanya masa kaya masu tsada, Hajiya kuma ta zaɓi wani ɗakin, kuma fa ita ce ta ce Hajiyar ta tashi, wato Safnar" faɗin Saleem, "wai Safnan?!" Yazeed ya faɗi tare da dakatawa yana tunani sosai, har Hajiya na sakin fiska, don a tunaninta ai yanzu zai fara tsanar Safna, tun da ta ɗaga ta a ɗakin da take. Sannan kuma gashi ya faɗi hakan da mamaki.
Sai dai abun da ya fito daga bakin Yazeed ɗin ne yasa zuciyarta sake komawa sashen da take n'a haushi, "wow! Kenan yanzu sun bar wancan ruɓaɓɓan ɗakin? Yanzu na san rayuwarsu ta ƙara inganci sosai" gaba ɗaya suka tsaya suna kallonsa da tsabar mamaki, Hajiya harda komawa kujera ta zauna, don inba haka ba Yazeed zai hana ƙafafuwanta motsi mai kyau. Nufan upstair yayi don zuwa ɗakin Hajiya, Ruki ta kuma katse shi da cewa, "bata dawo ba ai" ta faɗi itama cikin haushi.
Sai da ya ni sa da tunani ka na ya ce, "oh i forgot! Bata dawo daga company ba ko? Bara naje can ɗin" ganin yadda ya ƙagu har wani gargar yakeyi ne cikin ɓacin rai Hajiya ta samu damar buɗe baki ta ce, "ba shakka! To sai ka jira dawowarta ai tun da ba kwana zata yi a can ba, yadda kake ɗaukin ganinta ko ni ba kayi hakan ba" cikin rashin maida hankali da maganarta yayi hanyar falo yana fita.
AMNA DA SHURAIM ne a cikin mota suna tafiya, "wai Madam C.E.O kin lura da cewa yanzu kin fara neman taimako na kuwa?" Shuraim ya faɗi mata bayan ya danna hon daidai ƙofar gidan, ko kallonsa bata yi ba ya kuma cewa, "kin san me? Da ace zaki kasance a garin kurame ko? Da babu wata tantama za a baki sarauniyar kurame, saboda shirunki" ya ƙarashe maganar bayan sun shigo cikin gidan yana ƙoƙarin parking.
Duk yadda ta kai da son ƙin buɗe bakinta akansa amma hakan baiyi nasara ba, dariya ta fara yi wanda bata taɓa yinsa a gabansa ba, shima kallonta yake yana dariyar bayan yayi parking, kyau tayi masa yayin dariyar ma, don haka ita tana dariya shi kuma yana kallonta da murmushi, don ko ƙoƙarin fita bata yi ba.
Yazeed ya fito daga falo kenan yaga shigowar mota, zuciyarsa ce ta tsananta bugu domin ta gama sanar masa Safna ce a ciki.
"Dariya na yi miki kyau sosai 'yanmata" kallonsa kawai tayi ta juya tana cire belt ɗin kujera tare da buɗe ƙofar motar tana cigaba da dariya amma mara sauti ba kamar na ɗazu ba, shima Shuraim ɗin buɗe ƙofar yayi yana fita.
Idon Yazeed ko gezau baya yi yayin da yake kusantar inda motar yake, sai dai ya dakata zuciyarsa tayi mugun bugawa, bayan yaga fitowarta, sannan ga ta tare da wani saurayi, kuma fiskarsu alamar nishaɗi.
Kamar da wasa idon Amna ya kai inda mutum yake tsaye ƙam idonsa cikin na ta.......
Last part...
___________________________________________________
Da alama zamu iya cewa, Amna da Shuraim sun fara jamewa🥰
Cikin farinciki Amna ta ga iyayenta🥲
Sannan ga dai Yazeed ya ga Amna kuma itama ta ganshi. To ko ya abun zai kasance?
Mu kasance tare da ku a next part idan Allah ya kaimu.
Alƙamin ✍🏼 {Mrs Umar} [Gimbiyar Fasaha]👸🏽
______________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣1️⃣7️⃣▶️1️⃣1️⃣8️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Kamar da wasa idon Amna ya kai inda mutum yake tsaye ƙam idonsa cikin na ta. "Wannan! Idan ban manta ba shine Yazeed ko?" Tayi tambayar wa zuciyarta tana cigaba da kallon inda yake.
Shuraim ma kallon Yazeed yayi yadda yake kallon Amna sosai. Amna kuma tafiya ta fara yi don zuwa inda Yazeed ɗin yake, yayin da shima yake tahowa gurinta, bayan sun haɗu suka dakata da tsayuwa, Amna tana cewa fiskarta da mamaki, "amm! Yazeed ka dawo kenan? Sannu da dawowa" duk da cewa kiransa tayi da sunansa, amma baisa ya damu ba, sai ma daɗi da yaji a ransa.
Murmushi mai haɗe da kewan da yayiwa Safna tsawon lokaci ya sakar, yana mai ƙara jin annashuwa a ransa, sai abun da yaji a zuciyarsa da ganinta da wani ya disashe, a hankali ya ambaci sunanta tare da fitar da iska sosai a ƙarshen sunan, "Safnahh!" Murmushin itama ta sakar masa duk da jin ya kirata da sunan Safna, "na'am Yazeed, welcome back" "na gode sosai da barkan da kika yi min, to mu ƙarasa ciki ko?" Ya faɗi tare da yi mata a lama da hannu, nan suka jera suna tafiya.
Kauda kai gefe Shuraim yayi, saboda wani yanayi da ya ziyarci zuciyarsa, da ganin yadda Amna ta jera da Yazeed. "Are you missing me?" Jin maganar da yayi ne ya sata cewa à ranta, "da alama shi wannan yana da banbanci akan sauran, shi baya ta kurawa Safnah kenan?" A fili kuma ta ce da shi, "kana ganin bazan yi kewarka bane?" Maida kansa gurin hanyar falo yayi sannan ya ce, "da kuwa nayi mamakin hakan" ya ƙarashe da cigaba da murmushi.
Dai dai zuwan su gurin falo, "to ka gani? Na yi kewarka idan har kai ma kayi nawa" ta faɗi daidai shigar su, kan yayi magana ta wuce shi, don nufar ɗakin Ammu, hakan yasa ya ɗan yi dariya mai kamar murmushi tare da rakata da kallo. Dafe ƙirji Hajiya tayi, lokacin da ta hange sa shi da Safna, ji tayi kamar juwa na neman ɗibanta, don haka ta wuce don zuwa ɗaki kawai, taso ta aiwatar da abun da take son yi akan Safna, sai dai bijirowar maganar Ruki da Jaiz ne ya dakatar da ita, so take ta gama aiwatar da komai ba tare da an samu matsala ba.
Shuraim ma idonsa ne kan kallon murmushin da Yazeed ke faman yi wa Amna, sannan kuma ga kallon da ya ke binta da shi, da haushi ya wuce zuwa ɗakinsa ba tare da ko sannu ya wa Yazeed ba. Sai da Yazeed ya daina hango ta sannan ya fara nufar upstair shima don zuwa ɗakinsa, zuwa yayi don yin wanka ya canza kaya, wani farin ciki ya sake kanannaɗe masa zuciya, wanda ya daɗe bai ji hakan ba, fitowa yayi bayan ya ya.shirya cikin wasu kayan masu kyau, yana nufan ɗakin su Amna kai tsaye, ba tare da ya ko ci abinci ba, don so yake kawai ya ga sun zauna sunyi magana da ita.
Amna ma wasu kayan ta sauya mara nauyi, tache gashinta tayi ya kuma kwanciya, sai ƙyalli yake a kwance baƙi tass, sannan ta zauna gefen gado tana latsa waya ba tare da ta sanya komai ta rufe kan ba, Ammu ma gefe take kwance idonta biyu.
shiga direct yayi cikin ɗakin ba tare da sallama ba, kallon haɗuwar ɗakin ya fara yi sosai, tabbas an ƙawata ɗakin iya ƙawatuwa, don ko a turen sai haka, yana cikin ci gaba da kallon ɗakin ne hankalinsa ya kai kan Amna dake daddanna wayarta, kalonta ya fara yi sosai yadda ta ƙara yi masa kyau, ga gashinta da idonsa yake gane masa tamkar kaɗawa suke yi, ya san tun tana ƙarama yarinya ce mai gashi, amma bayan ta girma bai ƙara ganin wannan gashin na ta waje ba, amma yau gashi ya ganta saɓanin baya, kuma har tsawon gashin na ta.
Kallonta yake cigaba da yi harda wani karkatar da kai, murmushi na cigaba da kasancewa a kyakykyawar fiskarshi. Amna da jikinta ya bata kamar ido na kanta yasa ta fara kallon ɗakin, haɗi da sanya hannunta tana yin gefe da silin gashinta huɗu da ya hau mata kan fiska, tana dubawa don ganin ta ina ake yi mata kallon, idonta ya fa ɗa kan Yazeed, wani haushi ne taji cikin ranta, ko sallama ba zai iya yi ba, wai su meyasa yaran Hajiya suke da wannan mummunar ɗabi'ar ta rashin sallama? Kawai su wani faɗo ɗaki kamar ɗakinsu.
Fiska à haɗe ta ɗauki ƙaramin mayafin da yake a gefenta ta sanya, lura da ƙila har da ganin gashin m'a yasa yake yi mata wannan kallon ƙurillan. Sai à sannan ya farga da abun da yake yi, murmushi mai bayyanar da haƙora yayi yana ƙarasa shigowa ciki, "sorry na dakatar da ke daga latsa wayar da kike ko?" Ya faɗi cikin kame-kame, ba tare da ta sake masa fiska ba ta ce, "no problem!".
Lura da yadda ta ƙi sakar masa fiska yayi, hakan yasa shi sake wayan cewa da faɗin, "ai nazo ne dama don in gaishe da anty Maryam" ya faɗi tare da nufar in da Ammun take kwance, "Antyna kina lafiya? Ya jikin na ki? Kwana da yawa sai yau n'a dawo" yana faɗiwa Ammu maganar tare da juyar da kansa kaɗan yana kallon inda Amna take, tana ci gaba da yin amfani da wayarta, Ammu kam kallonsa take domin ta san ya ɗauka Safna ce Amna. Ci gaba da magana yayi cikin tattausar murya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 56