masu ƙara ya sanya Alƙali ɗaga shari'ar zuwa wata mai kamawa. Haka dai aka tashi daga shari'ar zuciyar masu ƙara ba daɗi, yayin da ɓangaren Hajiya da sauran 'ya'yanta kuwa farin ciki ne ke wanzuwa cikin zuƙatansu. Haka aka kuma tasa Dady gaba don à sake tsare shi har sai ranar da Alƙali ya yanka na sake sauraron ƙarar.
Amna da Safna kallon Dady su ke yi cikin ido, suna aika masa da kallon ba za ka taɓa tsira ba, shi kuwa yana binsu da kallon za ku gani.
Bayan an fita wajen kotu.
Wani babban mutum ne ya tsaya a gaban Dady kafin ya kai ga shiga motar hukuma, kallonsa Dady ya yi tare da sakin murmushin da su biyu za su gane me su ke nufi, "kar ka damu! Zamu aikata duk mai yiwuwa don ganin komai ya tafi yadda mu ke so, kawai ka ƙara haƙuri" cewar mutumin, Dady ya ce, "ba na son akasin abin da na so!" Yana faɗin haka ya shige motar hukuma su ka bar wannan mutumi da abokin aikin Dady ne tsaye.
Har su ka yi nisa da shi kafin ya sauke kai ƙasa, ka na ya ɗago wayar da ke hannunsa ya dannan wata numbern da babu suna a kai, ringing ɗaya aka ɗaga wayar, "an gama na yau, sai a shiryawa na gaba, nan da kwana ashirin da ɗaya masu zuwa" daga can gefe aka ce, "za'a shirya!"
Su Amna na tsaye da lauyansu da kuma wasu 'yan sanda suna maganar ta ya hakan ya faru? "Gaskiya nima na yi mamaki, ban san ya aka yi aka shirya wannan batutuwan ba, amma abin da zai faru shine, mu tabbatar da mun samu cikakkun shaida, domin tinkarar kotu karo na gaba" cewar lauyan na su. Yazeed ya ce, "tabbas dole mu tashi sosai, don samun gamsashshiyar shaida, saboda bai kamata a barshi ya sha ba, dole à hukunta shi kamar yadda ya aikatawa mutane".
Kallonsa su Amna su ke musamman Safna, domin kuwa tana iya fiskantar raɗaɗin da ya ke a ciki, kafin Yazeed ya gama rufe baki daga maganar da ya ke, Hajiya da ta iso ta ji yana maganar ta wanke shi da mari mai ƙara, rufe baki sauran su ka yi da mamaki, Safna kuwa rintse ido ta yi domin marin ya shigeta har zuciya, kamar ita Hajiya ta mara. Riƙe kumatu Yazeed ya yi tare da kallon mahaifiyarsa, cikin ɓacin rai Hajiya ta fara cewa.
"Ba shakka Yazeed! Amma ka ba ni mamaki wallahi! Yanzu à ce da kai aka haɗa baki ake son ganin bayan mahaifinka ba tare da aikata wani laifi ba? Ban yi zaton za ka yi hakan ba, wato ko da ace ni ce abin da zaka aikata min kenan ko?".
Last part.
___________________________________________________
Hhhhmmm, kuna ganin su Dady za su yi nasara a karo na gaba? Ya zata ƙarke?
Mu haɗu da ku a kashi na gaba don jin yadda zata kaya.
_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣6️⃣7️⃣▶️1️⃣6️⃣8️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar
_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_
"Ba shakka Yazeed! Amma ka ba ni mamaki wallahi! Yanzu à ce da kai aka haɗa baki ake son ganin bayan mahaifinka ba tare da aikata wani laifi ba? Ban yi zaton za ka yi hakan ba, wato ko da ace ni ce abin da zaka aikata min kenan ko?".
Yazeed ya ce, "Hajiya ba ki san abubuwan da na ji daga bakinsa ba ne, Hajiya Dady ba yadda ki ke tunaninsa haka ya ke ba..." "Rufa min baki! Ba na son sake jin wani abu daga bakinka, kai har ka isa ka sanar da ni waye mahaifinka?" Cewar Hajiya tana juyawa kallonsu Shuraim da ke wurin, su kuwa su Marwan suma sai aikawa sauran kallon banza su ke.
Sai da Hajiya ta gama zagaye idanuwanta gun su Amna sannan ta dubi Yazeed ta ce, "tun farkon maganar na gane sharrin aka yi masa, sai ga shi yau na tabbatar, wallahi idan har ka bari wasu su ka yi galaba akanka, na su sauya maka tunanin tsanar mahaifinka, to ko shakka babu za ka haɗu da matsanancin fushina!" Tana faɗi ta juya su Saleem su ka mara mata baya. Dafa ƙafaɗan Yazeed Shuraim ya yi alamar rarrashi, shi kuwa Yazeed ƙasa kawai ya yi da kansa, juyawa Amna ta yi tana kallon Safna da ta kauda kai gefe saboda haushin abin da Hajiya ta yi wa masoyinta.
Su Ammu da su ka ga abin da ya ke faruwa kuma har sun ji wasu daga cikin kalaman Hajiya, bayan sun ƙaraso inda su Yazeed ɗin su ke Ammu ta ce, "Yazeed, abin da mahaifiyarka ta faɗa tana da gaskiyarta, don haka ina son ka yi yadda ta ce, ka koma bayanta ka da ka kasance a bayanmu, ko ba komai ita uwa ce a gareka" "haba anty Maryam, taya zan kasance a bayanta bayan na san gaskiyar komai?" Faɗin Yazeed idonsa na ƙoƙarin yin launi.
Uncle Musa ya ce, "maganar Maryam gaskiya ne, ko da ace ba za ka koma bayanta akan kare mai laifi ba, amma ka nisanci shiga cikin al'amuran da ake don bayyana gaskiya, ita mahaifiyarka ce, ba zamu so ta yi maka furucin da bai dace ba". Haka dai sauran manyan su ka rarrashesa, daga baya su ka kama hanyar komawa gida.....
Amna da Safna ne su ka kama hanya zuwa gidansu Raheena, ko da su ka isa Safna ta tsaya a waje ita kuma Amna ta shiga, daidai fitowar Raheena harabar gidan fiskarta ɗauke da murmushi, ko da ta iso gaban Amna sai ta bita da kallo, "ni fa da na ɗauka ba za ki gane kwatancen ba, don ba ki taɓa zuwa ba... kai ƙawata me ya same ki? Na ga fiskarki da raunuka sannan babu alamun da ki ke canzawa, kuma dubi har hannunki ma da ciwo, har gefen wuyanki ma" cewar Raheena tana ɗaga hannun Amna da kuma duba fiskarta har da ma wuyan na ta, ta yi maganar ne cikin damuwa da abin da ta gani.
Kama hannunta Amna ta yi sannan ta ce, "kwantar da hankalinki ƙawata, ina lafiya da ki ke gani na haka" "to amma ya aka yi ki ka samu raunukan nan?" Faɗin Raheena tana ƙure Amna da ido, "duk share wannan tambayar, dama ba na ce miki akwai wani abun da zan nuna miki ba?" Cewar Amna tare da ɗagawa Raheena gira, Raheena ta ce, "eh amma mu ƙarasa ciki sai ki nuna min" "no a nan zan nuna miki, kawai abin da na ke so da ke, just close your" cikin mamaki Raheena ta rufe idanuwanta kamar yadda Amna ta ce.
"Yauwa, amma kada ki buɗe fa, idan ba haka ba kin rusa suprice ɗin" cewar Amna tare da yiwa Safna da ke ƙoƙarin shigowa alama da ta taho. Amna na ƙoƙarin komawa bayan Raheena ta ce, "Yauwaa! To yanzu" Safna ta ƙarashe da cewa, "open your eyes" a hankali Raheena ta buɗe idanuwanta ta sauke su kan Safna, zaro ido ta yi sosai tana kallon Safna, ita dai ta san kafin ta rufe idonta Amna ba ta sanye da kayan basajar Safna, to ya aka yi kamar ƙiftawa da bismillah ta sanya?.
Kafin ta yi wani furuci Amna da ke bayanta ta fara dariya, a razane Raheena ta juya tana kallon Amna, sai kuma ta fara jin murmushin Safna, nan ma ta kuma juyawa tana bin Safna da kallo. Ko ƙwaƙwaran motsi ta kasa yi saboda tsabar mamakin da ke cikin idanuwanta, hannu ta ɗaga kamar babu jini a jikinta, kamar bakinta ba zai iya furta wani abu ba ta ce, "Bastyy?" Safna ta giɗa mata kai a hankali tare da rufe ido ta buɗe, daidai zagayawar Amna ta tsaya kusa da Safna suna kallon Raheena.
Jan numfashi Raheena ta yi sannan ta saki ihun farin ciki da bata san yaushe ta yi sa ba, sai da su Amna su ka rintse ido yadda ƙarar ya daki kunnuwansu, tana ƙarashe ƙarar ta rugume Safna cike da murna tana faɗin, "besty yaushe ki ka dawo, wayyo daɗi bestyna ta dawo Allah na gode maka!" Kallon su Amna ta ke yi cikin farin ciki tana sauke murmushi.
Momyn Raheena ce ke fitowa cikin ruɗewa da jin ihun ɗiyarta da ta yi, "Raheena lafiyank..." kafin ta ƙarshe maganar ta yi turus tana bin su da kallo, Raheena ta ɗaga jikinta daga Safna su ka juyo duka suna kallon Momyn, da gudu Raheena ta isa gaban Momynta tana cewa, "Mo momy bestyna ta dawo!" Tana faɗi ta kuma komawa gurinsu Safna ta riƙo hannunsu dukkansu biyu ta janyosu zuwa gaban Momy. Ita kam Momy tuni iskan mamaki ya buge ta, babu abin da ta ke yi sai kallon fiskokin su Amna, su kuwa su na yi mata murmushi.
A tare su ka furta, "ina wuni Momy" "la lafiya" Momy ta furta tare da juyawa gurin Raheena ta ce, "ke Raheena wai su biyun ne na ke gani!?" "Tabbas kuwa Momy" cewar Raheena, Momy cikin mamaki ta kuma faɗin, "to to ku shigo, ku ƙaraso ciki yarana". Shigewa su ka yi tare da zama cikin kyakykyawan falon, saboda murna Raheena ba ta ma yi tunanin kawo wa su Amna ruwa ba. Bayan sun sha hira na ɗan lokaci su Safna sun ɗan fayyace musu wasu abubuwan, duk da cewa Amna ce ta fi yin maganar.
Su Raheena sun ƙara mamakin abin da ya faru, wato ashe dai wannan kama da ke tsakanin Amna da Safna yana da dalili, daga ƙarshe su ka bi su da addu'a, "my daughter ko ruwa ba ki kawo wa yarana ba" cewar Momy, Raheena ta ce, "Momy murna ya hanani, ko tunanin ma ban yi ba, amma yanzu kuwa zan ba wa yaranki ruwa harda abinci, don dai yau na san za su ƙwace min ke" murmushi mai sauti su ka yi dukkansu, domin yadda Raheena ta yi maganar, Momy ta ce, "ƙwarai kuwa yau dai ga 'ya'yana nan sun zo" Safna ta ce, "aikuwa Momy, Raheena sai ki nemi inda, za ki fake "Ni ko na ke da wuri, tun da Momy ta juyan baya sai in je gurin Ammu, ita zata riƙe ni hannu bibbiyu" faɗin Raheena, suka sa dariya dukkansu, Raheena kuwa ta tafi kawo abinci.
Bayan awanni su ka tashi don komawa gida, da Raheena ta ce zata bi su gida ta je ta duba su Ammu, amma Momy ta ce ta bari gobe sai su je tare.
Kamar yadda Momy ta ce washe gari su ka shirya ita da Raheena zuwa gidansu Safna, bayan sun isa cikin gidan su ka haɗu da Jummala, su na cikin gaisawa da ita Raheena ta ce, "ooh Momy n'a manta da takardun da na ce miki na taho da su cikin mota" momy ta ce, "wai takardun menene kam?" "Na company ne zan ba su Amna, akwai abin da ya kamata ta duba à ciki, tun tuni na ke son kawo mata ta hana ni zuwa, to jiya da su ka je kuma farin ciki ya mantar da ni" faɗin Raheena, Jummala ta ce, "ba damuwa je ki ɗauko ni bari na ƙarasar da ita ciki" "toh nagode" cewar Raheena tare da juyawa waje, ita kuma Momy Jummala ta shige mata gaba zuwa ciki.
Bayan Raheena ta ɗauko takardun ta na cikin shigowa gida, Mubarak da ya fito riƙe da waya a kunne yana magana, ya bangaji Raheena cikin rashin sani, pepers ɗin da ke hannunta su ka fice daga cikin file, saurin riƙo hannunta ya yi kafin ta yi baya, hakan ya hanata faɗin da ta yi shirin yi, kallon junansu su ke a hankali musamman ma Mubarak, yadda ya ke kallonta ba tare da ya cire wayar daga kunnensa ba, kuma bai saki hannunta ba.
Cire idonta ta yi daga cikin na sa tare da daidaita ƙafanta daga tsayuwa cikin kunya ta ce, "za ka iya saki na yanzu" tana faɗi ya saki hannunta cikin wayan-cewa da daɗewan da ya yi yana kallonta ba tare da sani ba, ya sauke wayar da ke kunnensa ya ce, "Oh sorry, ga shi na yi miki ɓarna" ya faɗi yana kallon pepars ɗin da su ka zube ƙasa tare da tsugunnawa don ya tsinte su, "à ah karka damu, zan kwashe su da kaina, zaka iya tafiya" ta faɗi tare da tsugunnawa itama tana tsincewa,.
Bai yi mata magana ba har ya kwashesu, sannan ya miƙe yana faɗin, "kawo file ɗin in sa miki à ciki" ba musu ta miƙa masa file ɗin da ke hannunta ya amsa sannan ya saka papers ɗin ya kuma miƙo mata, ansa ta yi tare da yi masa godiya, shi kuwa murmushi kawai ya yi mata ita kuma ta shige cikin gidan. Binta da kallon ya yi sannan ya jinjina kai haɗi da duba wayansa.
Ammu ta ji daɗin zuwan Momyn Raheena sosai, ta gabatar da ita ga sauran mutane, haka su ka zauna su na ta hira abinsu.
Su uku su ka fito harabar gidan suna hira, Raheena ta ce, "bestyna ki yi koyi da Amna, mu rinƙa yin hira sosai da ke, saboda na fi son in mun zauna mu yi ta hira" Safna ta ce, "a ah, cewa za ki yi, in mun zauna mu yi ta zuba kamar gidan radio" kallon Amna Raheena ta yi ta ce, "kin gani ko ƙawata? ai dama na faɗa miki ita fa bestyn nan ta wa da ki ke gani miskila ta ke burin maida ni ako da yaushe, to in ba haka ba akan me zata ce min ina zuba kamar gidan radio?" dariya su ka kwashe da shi, duk da Safna ba sosai ba.
Amna ta ce, "Kar ki damu in dai don wannan ne, ki ba ni nan da ɗan lokaci, in dai surutu ne to Safna ta ma riga da ta koya, ke yanzun ma baki ga ta ɗan sauya ba? Yanzu fa Amna na cikin jikinta in ba ki sani ba" Safna ta ce, "za ku gama dukkanku, babu wani surutun da zan yi, ku dai ku fama, ba za ku sanya min ciwon baki ba" Amna ta ce, "yanzu ma ai kin yi, ƙawata Raheena tun da ki ke da ita ta na irin magana sosai haka ne?" "A a fa, ko labari ta ke ba ni in ta faɗi kaɗan, to fa sai bayan wani lokaci zata ƙarashe mini, shi ɗin ma sai na nuna mata na ɓata rai" dariya su ka sake yi a tare.
Suna à haka Mubarak ya zo wucewa, Amna ce ta yi saurin zuwa inda ya ke tare da janyosa gurin su Safna, kallon Raheena ya ke da murmushi sannan ya juya gurin Safna ya ce, "yar uwata kina lafiya dai ko? Na san wannan yarinyar ta addabeki da surutu, haka muke fama da ita" buga ƙafaɗan shi Amna ta yi shi kuwa ya ɗan saki ƙarar ban dariya ya ce, "osh, kin ga halin na ta ko? Ko da wasa kada ki bari ta taɓa ki da hannun guduman nan na ta" dariya su ka yi Amna na hararansa, Safna ta ce, "kar ka damu ɗan uwana, zan miƙa maka komai a hannu, idan ta dame ni sai ka yi min maganinta".
"Ooo wato kun haɗe min kenan? To na ji ni kuma da ƙawata Raheena zamu haɗu mu cika muku ciki da surutu, har sai kun tuba, ko ƙawata?" Amna ta faɗi tana kallon Raheena, Raheena ta amsa da ƙwarai kuwa, Mubarak kuwa sai kallon Raheenar ya ke yi, "Ƙawata wannan shine ɗan uwana Mubarak da na baki labari, Muba wannan ita ce Raheena ƙawa kuma aminyar Amna da Safna" cewar Amna tana gabatarwa Raheena.
"Ayyah ina wuni" faɗin Raheena tana rausayar da kai, amsa mata Mubarak ya yi "lafiya alhamdulillah fatan ke ma haka? Y gida?" "Lafiya ƙalau Alhamdulillah" itama Raheena ta mayar masa, ya yi musu sallama ya juya ya tafi.
BAYAN LA'ASAR.
Hajiya ce ke riƙe da kofin tea mai zafi a hannunta, ganin Safna na tahowa ne ya sanyata bin inda Safna ta ke, ganin Safnan kamar hankalinta baya wurin, niyya ta yi ta ture Safnan don ta juye mata ruwan tea mai zafi a jiki, amma tana isa inda Safnan ta ke ta yi yunƙurin tureta kenan saboda yadda ta ɗaga jiki ya sanya kofin juyowa inda ta ke, ruwan tea ɗin ya zuban mata a hannu kaɗan, zafin da ta ji ya sanya ta yin baya tare da sakin kofin duka a ƙasa, hakan kuwa ya sa ragowar ya zube mata à ƙafarta.
Sakin ƙara ta yi zata faɗi Safna ta yi saurin kama ta, cikin ɓacin rai ta fizge daga hannun Safna, ta yi ƙasa haɗi da sanya hannunta kan ƙafanta da ruwan shayi mai zafi ya zuba, sai zugi ya ke mata, Safna ba ta kula don yadda Hajiya ta ƙwace jikinta ba, cikin kulawa da nuna damuwa ta yi ƙasa tana cewa, "sannu Hajiya, sannu, wallahi ban lura ba ne, bari na ga gurin" ta yi tunnin ita ce silar abin da ya faru da Hajiya, kafin ta kai hannunta kan ƙafan Hajiyar, Hajiya ta ture ta gefe haɗi da daurewa daga zafin da ta ke ji ta miƙe, cikin masifa da baƙin ciki ta ce.
"Ba shakka! To ka da ki sake ki kai hannunki kan ƙafata, wato kina ƙoƙarin salwantar da rayuwata gurin yi wa mijina sharri, shine nima ki ke so ki kassara ni? To ta Allah ba ta ki ba! Shiyasa ki ka tafi a ka kawo mai kammaninki don ta ga bayan mu ko?" Miƙewa daga ƙasan da Hajiya ta turata ta yi ta ce, "Hajiya ban...".
"Yi min shiru! Ba na son jin ko mai daga bakinki, yanzu ke don Allah ba ki ji kunya ba? Duk abin da bawan Allahn nan ya yi miki a rayuwa amma ki rasa da me zaki saka mishi sai da yi masa sharri? Sharrin da zai sa a kashe shi mu kuma rayuwarmu ta lalace, Mutumin da ya ke fifita ki akan 'ya'yan da ya haifa? Ashe ba ƙaramin kuskure Alhaji ya tafka ba a rayuwarsa ba, amma kin yi asara a ray...".
"Hajiya!!" Cewar Amna cikin ɓacin rai bayan ta iso kuma ta ji kausasan magan-ganun da Hajiya ke yiwa biyunta, dakatawa Hajiya ta yi a tsorace tana kallon Amna. Amna na isowa ta tsaya gaban Hajiya fiska a haɗe ta ce, "akan me zaki rinƙa yi wa 'yar uwata magana haka?" Saurin kama hannunta Safna ta yi alamar ta yi shiru, saboda gudun kada zafin zuciya ya kaita aikata wani abun.
Amna kuwa kallon Safnan ta yi ta ce, "ke rabu da ni, don ni ba zan tsaya inga ana yi miki abu inyi shiru ba" ta faɗi tare da juyawa gurin Hajiya ta kuma cewa, "Hajiya ke duk abin da ki ka yi mata na wahala tun tana ƙarama ita da mahaifiyarmu, sannan yanzu bayan angano abin da mijin na ki ya aikata mana, amma kina da bakin faɗa mata haka?"
Janta Safna ta fara yi don su bar wurin Hajiyan ma baki ɗaya, Safna na janta amma sai da ta kuma buɗe baki ta ce, "wallahi kin yi sa'a na rabu da ke ne don Safna, idan ba haka ba ko" ta ƙarashe da ƙwafa.
"Haba 'yan matana, bai kamata ki tankawa Hajiya ba, ko ba komai ai ta girmemu" cewar Safna bayan sun tsaya a wani gefen, hararanta Amna ta yi ta ce, "to ita ta kama girman na ta ne? Ohh na fa manta, cewa zaki yi ko ba komai ita ce mahaifiyar yaya Yazeed masoyina fa" Amna ta faɗi cikin raha tare da kai ƙafaɗanta jikin Safna tana dariya.
Kallonta Safna ta yi tana murmushi ta ce, "ke dai babu yadda aka iya da ke, amma don Allah ya kamata ki zama kamar Safna kema, yadda nima na ke ƙoƙarin zama kamarki, sarrafa fushi abu ne mai kyau, kada ki fiye biyewa zuciya, domin akwai lokacin da sai kin aikata za ki yi da kin sanin ɗaukar fushin. idan ki ka tsinci kanki cikin fushi ki yawaita ambatan sunan Allah a zuciyarki, kin ji 'yanmata na?".
Sauke numfashi Amna ta yi tare da saukar da kai ƙasa, "shikenan ai dole na na yi abin da 'yanmata na ta ce min, insha Allah zan kwatanta har na saba, amma zai min wuya don tun asali haka na tashi".
A ɓangaren Hajiya sai da su ka yi nisa kafin ta sake tsaki, sai kuma ta yi saurin yin ƙasa tana dafe ƙafan na ta da ke cigaba da zugi, domin ta san ko ya sai wurin ya tashi.
SAURA KWANA HUƊU ZUWA KOTU.
Hajiya da Marwan ne su ka nufi inda aka kulle Dady, bayan an ba su damar ganinsa Hajiya ta fara kuka tana cewa, "Alhaji ban san ya aka yi su ka laƙaba maka wannan sharrin ba, amma ta Allah ba ta su ba, insha Allah sai ka fita daga wirin nan, yau fa daura kwana huɗu sauraron ƙaran nan, amma zuciyata sai tsinkewa ta ke yi, idan har wani abu ya sameka to mu ina muka kama? Kai ne ƙarfinmu Alhaji, kai amma mutanen nan sun cuce mu wallahi"
Hajiya ta faɗi tana kuka, Marwan ya ce, "Hajiya ki daina kuka" "Ka da ku damu, babu abin da su ka isa su aikata min, sai dai ma ya koma a kansu, saboda haka ku kwantar hankaliku!" Faɗin Dady cikin dakewa.
"Haka ka yi tunani, amma dole ka amshi abin da ka yi da hannu bibbiyu kuwa, i hate you Dady!" Faɗin Yazeed da ya iso wurin yanzu idanuwansa babu farin ciki a cikinsu. Juyowa su Hajiya su ka yi suna kallonsa.
Last part.
___________________________________________________
Hhhmmm Dadyfa yana da ƙwarin guiwa.
To ni dai na ce muje zuwa.
_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣6️⃣9️⃣▶️1️⃣7️⃣0️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar
_🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_
"Haka ka yi tunani, amma dole ka amshi abin da ka yi da hannu bibbiyu kuwa, i hate you Dady!" Faɗin Yazeed da ya iso wurin yanzu idanuwansa babu farin ciki a cikinsu. Juyowa su Hajiya su ka yi suna kallonsa.
Dady bai yiwa Yazeed magana ba, sai ma kawar da kansa gefe da ya yi, duk da cewa abin da Yazeed ya faɗi ɗin ya daki zuciyarsa, saboda yana matuƙar son 'ya'yan na sa sosai fiye da kansa, "Yazeed kai me yasa ba ka da hankali ne" cewar Marwan yana kallon Yazeed ɗin cikin ɓacin rai, Hajiya ce ta ce, "rabu da, ƙyale shi ya yi duk abin da ya ke ganin daidai ne a rayuwarsa" Yazeed bai kuma cewa komai ba, sai kallon Dady da ya yi ya juya ya bar wurin.
RUKI, wata 'yar aiki ce ta kirata da sanar da ita ana magana da ita a waje, sai da ta saki tsaki tukunna ta fara saukowa daga kan upstair tana cewa "waye ne ya ke son takurawa rayuwata ne wai? Haba dan Allah, baccin da na ke son yin ma ba za a barni inyi ba?" Bayan ta fita wajen gate ta kuma cewa, "wai ina mai kiran na wa ne? Haba!" Ta faɗi tana waige-waige, "Atata uki" kamar da ga sama ta ji muryar Jaizu Alhaji mammaƙo ya kirata.
Zaro ido ta yi tare da yin baya ta jingina jikin gate ɗin numfashinta na sama da ƙasa, "me me me ya kawoka gurina?" Baki na rawa ta faɗi tana kuma kallonsa, domin sai ta ga kamar ya ƙara muni ne ma. Sauke sandarsa ya yi ya kunno ido ɗayan nan na sa ya fara yi mata magana, duk da yanayin maganar ta sa amma ta fahimci wasu, domin dagewa ya yi yana maganar, ji ta yi ya ce.
"Ai na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 52 Chapter of 56