e fa ankwanki, ya ike min wannan magana aka? Ba ajjani ba ne fa" zaro ido ta yi jin maganar sa, duk da a wani iri ya yi maganar kamar bébé, amma ta ɗan fahimci abin da ya ce.
Sai kuma ta cigaba da kukan sannan ta fara magana cikin muryar kuka, "ya za'ayi ku ce ku ne miji na, don Allah ni dai ku yafe min, idan ma na muku wani laifi" matsowa kusa da gadon sosai ya yi, ita kuma sai ƙara damƙe gini ta ke yi, tana ɗadɗaga ƙafa kamar zata haye sa, tana kallonsa ya samu wuri ya zauna a kan gado, sannan ya kuma juyowa yana dubanta, fiskar nan baza ma ka gane haɗe fiska yayi ko murmushi ba ya ce, "aukko, ki aukko" kallonsa kawai ta ke tana cigaba da kukanta, "ki aukko ki jauna an ga'onnan a ce!"
Ya faɗi da ƙarfi, ai kuwa muryarsa ba ƙaramin ƙara razanar da Ruki ya yi ba, sai a lokacin ma ta gane ashe wai cewa ya ke ta sauko, da sauri jiki na ɓari ta zauna can gefen gadon nesa da shi, idanuwan nan sun fara kumburan kuka, kwalliyar da ke fiska ta chaɓe ta dawo iya an yi damun kunun koko, gyara zama wannan mutumin ya yi don yi mata baya ni, ganin sai wani kiranshi da aljani ta ke, ko da ba a wurinta kaɗai ya ke jin hakan ba, amma an fi yi masa bayan idonsa.
"Ni unana J'ai..Jai..." ya fara faɗa masa sunansa amma ƙarshen ya ƙi fitowa saboda yanayin harshensa, amma duk da haka ya dage don sanar mata da ko da sunan ne daidai, "unana Jaizu, amma na kila na da Alaji mammaƙo, kuma nine ijinki da ki ka aula, alak malak mallakinki, kuma asoyinki" firgigit Ruki ta dire à ƙasan tayis, jin bazzar maganar da yayi, domin sarai ta fahimcesa, "wannan wani irin bazzar magana ne!? Yau ni Ruki na shiga ukuna, ko dai turo ka a kayi ka kashe ni kafin angon na wa ya ganni? Jaiiiz! Angona ka zo ka ceci amaryarka, masoyiyarka, anzo raba tsakani na da kai, an turo min aljan....".
Kan Ruki ta kaiga ƙarisa kururuwar da ta ke, ya daka tsawa, ɗib tayi kamar an tsaida duniya, buɗe wannan ƙwallin idon na sa ya yi, haɗi da miƙewa ya tashi, sannan ya nuna ta da sandar shi da ke hannu, "auuna!" Da sauri da zauna a ƙasa kamar yadda ya ce tana kallonsa, kamar wacche ta zo gidan ɗan bori, magana ya fara yi mata na duk abin da ya faru baya.
KOGO.
Kallon junansu suke cike da fargaba, har numfashinsu na sarƙewa jikin su ya fara wani irin harbawa kamar jannareto, sake maida kallonsu su kayi kan hanyar da suka biyo, ƙofar kogon da suka shigo ta wurin ta ɓace babu ita, a hankali duhu ya fara mamaye gaba ɗaya wurin, ya zamana hatta junansu basa gani, cikin tsoro Amna ta fara yin magana, "Shuraim Shuraim ina ka ke? Kana ina? Bana ganinka, bana ganin komai, kana ina?" "Gani nan Amna, nima ba na ganin komai, bari na kunna waya" cewar Shuraim yana sanya hannunsa à aljuhu don ciro wayarsa ya kunnan tochi.
Sai dai yana ciro wayar ta faɗi ƙasa, da sauri ya durƙusa yana laluben ta, amma Sam bai ji ta ba, "ka kunna mana, ya har yanzu baka kunna ba" Amna ta faɗi tana juye juye kamar makauniya, domin babu abin da ta ke gani, "wayar ta faɗi nemanta na ke" ya bata amsa yana cigaba da lalube, a hankali hannusa ya taɓa wayar, da sauri ya ɗauka haɗi da miƙa hannunsa neman inda Amna ta ke, saboda ya ji kamar ƙararta ta wani gefe, "kina ina Amna?" Ba tare da ya ji amsar ta ba ya ji an damƙi hannunsa, sai dai ko da ya kuma kiran sunan Amnan shiru ba ta amsa ba yanzu ma, kawai riƙe hannun da ya damƙesa Shuraim ya yi da kyau.
Amna da ta kira sunansa ta ji ya amsa mata, sannan ta ji Shuraim ya ce, "ki tako ki biyo ni, saitin da ki ken nan ba sai kin juya ba, na gano mana wata hanya" cikin fargaba ta fara tafiya kamar yadda ta ji Shuraim ɗin ya ce da ita, sai haɗiye nyawun tsoro ta ke yi.
Shuraim kuwa bai kunna hasken wayar ba, sai ya fara murza hannun da ya ke a cikin na san, saboda yadda bai ganewa abun da ya riƙe ɗin ba, shi à tunaninsa hannuya riƙe, amma kumayanzuya farajin bambanci, wani irin zaro ido ya yi jin kamar ƙashi hannunsa ke murzawa, ta ke jikinsa ya fara karkarwar tsoro, ya ɗaga wayar da ke ɗayar hannun sa, da sauri ya ke ƙoƙarin kunnawa har wayar na rawa kamar zata faɗi, da ƙyar ya yi nasarar kunna tochi.
Idonsa cikin tsoro ya fara juyawa inda ake riƙe masa da hannu, haɗi da ɗaga wayar don ya haske abun da ya riƙe sa, sake fiddo ido yayi bayan ya kai hasken inda hannunsa ya ke a razane, amma da mamaki bai ga wani abu da ya riƙe masa hannu ba, da sauri ya ɗaga hannunsa yana kallo da mamaki, tabbas akwai abin da ya riƙe masa hannu, amma yana ina?.
Cikin razani ya fara waigawa tare da haske tochi, can idonsa ya gane masa Amna na yin wani wuri daban, sannan can gabanta wani baƙin cycle ne mai kama da bakin rami, cikin tashin hankali yafara cewa "Amna! Amna ki dakata! Ki daina wannan tafiyar nan, Amnaa!" Amma ina Amna ko kaɗan ba ta jin maganarsa, ko hasken tochin ma ba ta gani, domin har yanzu idonta duhu ya ke gane mata, cikin wani ƙarin tashin hankali Shuraim ya doshi inda ta ke da gudu, ganin kamar ma ba ta sauraron abin da ya ke cewa, sannan kuma gashi saura dap ta faɗa cikin ramin.
Ita kuwa Amna sai ma ƙara sauri da ta yi, saboda sake jin muryar Shuraim ya ce mata ta ƙara sauri sosai, sanya ƙafar damarta ta yi gurin ramin, saura kaɗan ta afka ciki Shuraim ya yi tashin zaki ya janyota da ƙarfi, suka yi bayan suka faɗi a ƙasa, wayar da ke hannun Shuraim ya kuma faɗi, sai dai hasken bai mutu ba, gaba ɗayansu zuciyarsu sai sama da ƙasa yake yi, a hankali suka miƙe Shuraim ya ɗauke wayar yana haska ta, rintse ido Amna ta yi saboda yadda tochin ya kashe mata ido, "ke baki da hankali ne? Akan me zaki doshi rami? Ina kiranki amma kika yi shiru".
Hannu ta sa ta sauke hasken wayar da ke hannunsa ƙasa, sannan ta dubesa ta ce, "kamar ya? Bayan kai ne ka ce in bika ka samun mana hanya, akan me zaka ce min ban da hankali, ni bance baka da hankali da kaso sanya ni a rami ba, amma kai kake wata magana?" Cewar Amna cikin jin haushi, da mamaki ya ce, "ni kuma?! Ni fa tun ɗazu kiran sunanki na ke kuma banji kin amsa ba" itama Amna cikin mamakin ta ce, "me!?" Shiru suka yi suna nazarin wani abu, kawai suka ji sautin dariya a kunnuwansu, juyawa suke Shuraim na haskawa Amna ma ta ciro wayar da ke aljihunta ta kunna haske.
Suka taru suna haskawa amma basu ga mai dariyar ba, sai ƙarar dariyar da yake amsakuwa a kunnuwansu, daga can nesa suka fara ganin duhu na tunkarosu, hasken wayoyinsu da ya haske wurin yana disashewa, baƙin na ƙara kusantowa sannan duk wurin da tochinsu ke haskawa duhun na lulluɓesa, cikin tashin hankali da tsoro suka fara ja da baya, amma ina wannan duhun na cigaba da tahowa, idon Shuraim ne ya samu daman ganin wata hanya daga can gefe, cikin muryar a hankali ya dubi gefen Amna ya ce, "Amna duba can", barin kallon duhun da ke ƙarato musu ta yi, ta dawo da idonta kan Shuraim, duk da ba kallonsa da kyau ta ke yi ba, domin rashin haske sosai da bai bayyana a wurin ba,
"Duba can kamar hanya, mu yi saurin zuwa wurin, ƙila mu tsira" Shuraim ya kuma faɗi, amma Amna ɗauka ta yi da ko ƙila muryar da yayi mata magana ɗazu ne, wato wanda ta ɗauka Shuraim ne, don haka ta ce, "Wace hanya? Yanzu ma so ka ke na kuma dosan rami? To bazan je ba!" Girgiza kai cikin takaici ya yi, ganin yadda ta dake cewa ba zata ɗin ba, juyawa yayi yana kallon duhun a yanzu saura kaɗan ya taddosu, cikin tsoro sosai ya maida kallonsa gun Amna, da itama gaba ɗaya fiskarta ya gama bayyanar da fargaba.
Sannan ya kuma maida kallonsa gun hanyar da ya gani, haske na ɗan walwalawa a wurin, Amna kuwa zuciyarta ya tsaya cak, ta rasa wani dabarar zata yi? Amna kuma juyar da kanta ta yi zuwa inda Shuraim ya ce ta gani, sai dai ita har yanzu bata ɗauka da gaske hanyar ba ce, zuciyarta na cikin zullumi da bugawa da sauri, da kuma tsoro mai tsanani, domin wannan duhun ya riga da ya cinye gaba ɗaya hasken toshin na su yanzu, saura kaɗan ya shafeta, har ta rufe idanuwanta kawai ta ji Shuraim ya kamo hannunta da ƙarfi ya ja ta, wayar da ke hannunta ya faɗi ƙasa.
Gudu suke yi zuwa wannan wurin, duhun nan kuma na biyo su a baya, ƙara gudu su kayi cikin tsananin tsoro, inda suke son zuwa ma sai suka ga ya yi musu nisa, ya kusa cin musu suka samu nasarar tsallake wani dutse da ke kan hanyar, suka dira a wannan wurin da ya bayyanar da haske kaɗan, yayin diran wayar da ke hannun Shuraim ya zame ƙasa, juyawa suka yi da sauri suna kallon duhun nan daidai lokacin da ya ɓace ɓat, nishi suka fara saukewa mai ƙarfi, saboda yadda suke ji daga cikin zuciyarsu, kallon Shuraim Amna ta yi shima sai sauke numfarfashi ya ke.
Ya juyo ya dubeta cikin muryar fitar numfashi ya ce, "kin gani ko? Kinga abun da na ke faɗa miki ko? Dama na san babu alkhairi a zuwanmu, gashi kin gani" itama cikin fitar numfashin ta ce, "ni har yanzu ban sare ba, kuma zan nemo mahaifina" "yanzu wace hanya kike ganin zaki bi, inda da kike da tabbas nan ne mahaifinki ya ke? Tun farko na ce ki barimu shirya amma ke ki ka ƙi" Bata amsa masa ba, ta juya ta fara nufar shiga siririyar hanyar, wanda ya ke ɗan bayyanar da haske ja kamar wuta, "ke, ke ya zaki tafi haka kai tsaye?" Cewar Shuraim amma ganin bata juya masa ba , yasa shi sauke nannauyar numfashi sannan ya bi bayanta suka jera.
Tafiya suke yi amma har yanzu basu ga inda wannan hasken ya ke ba, sai wuce layoyi suke, da ƙorongol ɗin mutane kwance, sai jajayen rubutu da ke bayyane a jikin bangon gefen-gefensu, bin komai da kallo suke yi, amma zuciyarsu na cigaba da ɗarsa musu tsoro mara adadi, hatta tafiyar da suke a hankali suke yi, tafiya suka yi sosai! Har sai da suka fara dafa bangon don gajiya da ko wannensu ya yi, da ƙyar suka samu damar isowa gurin hasken wutar, wutane ya ke ci a jikin wata ƙatuwar itache, wacche suffanta ya ke a lanƙwashe, kallon wurin suke yi, yadda wutar da ke ci sai wani jujjuyawa ta ke yi.
Sai dai fa duk abin da ake ɗin nan gaba ɗayansu ƙwaƙwalwarsu ya kulle daga tunanin yin addu'a, ko tunanin ma basu yi ba, ƙara suka fara ji daga cikin wutan nan kamar ana dariya, kamar ana kiran sunansu, matsawa dap juna Amna da Shuraim suka yi, ba tare da sun haɗe jikinsu ba, ko wanne sai kallon wutar nan ya ke da matuƙar tsoro, nan ma suka sanya hannuwansu a kan kunnuwansu, saboda ƙarar da ke tashin yayi yawa fiye da wanda suka ji ɗazu, domin har yana shirin fin ƙarfin ƙwaƙwalwarsu, wannan wutar ce ta tashi kamar iska ya yo kansu, suna kallon yadda ta ke zuwa kansu suka zare ido sosai.
Sai da kafin suyi wata tunani suka ji kamar wutar ya shige jikinsu, ƙara Amna da Shuraim suka sake à tare, cike da azaba da kuma raɗaɗi, ba su gama fama daga wannan ƙarar da ke cikin ƙwaƙwalwarsu ba sai kuma suka ji jikinsu ya fara wani irin tururin zafi, wanda ya wuce tunani, suka fara jin jikinsu na wani irin suka kamar ana fiɗansu da wuƙa.
Last part.
___________________________________________________
Ko ya zata ƙarewa su Amna? Ko zasu samu abun da suka zo nema? Ga dai sunan suna fama.
Ruki amarya à gidan alaji mammaƙo😂 ko ya akayi wannan juyin mulkin? Wannan shine kwaɗayi mabuɗin wahala, dama duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba, to fa zai godewa azabarsa.
Mu kasance a next part, don jin yadda zata kaya.
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣3️⃣9️⃣▶️1️⃣4️⃣0️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Azaba suke ji ta ko ina, nishi suke fitarwa mai shegen zafi, sakin jiki suka yi suka durƙushe a ƙasan da ƙarfi suna neman kwanciya, sannan suka sake ji kamar macizai na kai musu dafi, ƙara suke sakewa sosai, ba tare da sun kuma tunanin yin wata addu'a ba, tun suna ƙarar da iya ƙarfinsu har suka fara yi da hankali, take wannan dariyar na cigaba da tashi cikin kwanyarsu, idanuwansu ya dawo na wahala kamar wanda masifaffen barci ke shirin ɗaukar shi, jikinsu rawa ke ƙara yi kamar an jona musu shocking mai matuƙar ƙarfi.
Idanuwansu na neman kullewa sai lumshesu suke, numfashinsu na neman kaucewa, numfashi suke saukewa cike da raɗaɗi, kallon Amna Shuraim yayi a galabaice, yayin da itama ta ɗago tana dubansa, wani hawayen zafi ya fara zubo mata, shima ɗin Shuraim hakan ta ke a nasa idon, da ƙarfi ya ke ƙoƙarin zuwa inda ta ke, amma da ya yunƙura sai ya zube, itama Amna abin da ta ke yi kenan, amma gaba ɗaya jikinta ya ƙi bata haɗin kai, buɗe baki take son yi domin yin magana amma bakin ya ƙi buɗuwa.
Ta tabbatar da maganar da Shuraim ya faɗa mata a yanzu, sai dai lokaci ya riga da ya ƙure, me yakamata ta yi? Babu abin da zata iya, sannan ga Shuraim ma da kansa yana jin jiki, cikin firgita zuciyarta ya bada bugu, ganin yadda fatar jikin Shuraim ya fara rikiɗewa izuwa ja, zaro idanuwanta da suka zama jawur ta yi, sai dai bakinta ya ƙi motsawa har yanzu, ɓangaren Shuraim ma zaro idanuwansa da suka canza launi ya yi, shima sakamakon fiskar Amna da ya gani ya fara rikiɗewa zuwa jan launi.
Shima bakinsa matuƙar nauyi yai masa gurin buɗuwa, cikin tashin hankalin da ke ta sintiri cikin zuƙatansu, suka fahimci ashe gaba ɗayansu ne jikin nasu ke dawowa red, juyi suke ta yi, abubuwan da suke ji a jikin su na ƙara tsananta, tururin wuta ƙari kamar yaji, dariya mai kulle ƙwaƙwalwa, suka kamar dafin maciji, da kuma yanka kamar ana yanka fatarsu, duk haka suke cigaba da ji, ƙarfi Amna ta fara ji a jikinta, hakan ya sa ta fara yunƙurin tashi, yayin da ƙwayar idon ta ya fara zama kamar hasken garwashi kaɗan.
Idon Shuraim na kanta a galabaice, haɗe fiska ta keyi tare da nemo jarumta a jikinta, sai dai tana samun damar tsayuwa azaba ya kuma shiganta da ƙarfi, wannan kalar garwashin ya ɓace ya dawo baƙin, komawa baya ta yi ta zube à ƙasa rufda ciki, kallon junansu suke ita da Shuraim, kowa sai tausayawa ɗan uwansa ya ke ta ido da kuma fiska, domin baki ya ƙi buɗuwa, hawayen ciwo sai zubar musu ya ke, ƙirjinsu ya dawo bugawa a hankali, jikinsu tuni ya gama zagayewa da jan launi, kamar wata cuta ce ta kama su.
Tsawon mintuna suna à wannan hali na azaba mara misaltuwa, numfashinsu na barazanar ɗaukewa, jikinsu ya riga da ya daina motsi hatta yatsa sun kasa ɗagawa, sun fita daga gaba ɗaya hankalinsu, sun gama sadaukar da cewa mutuwa zasu yi, domin ba makawa ba su da hanyar da zasu fita daga wannan wuri, ciwon da suke ji a jikinsu bai rage ba, sai ma ƙaruwa da yayi. Idanuwan Amna kam ya daɗe da rufewa, Shuraim ne idonsa na kan Amna cike da tashin hankali da kuma tausayinta da na kansa, hawaye na ta sauka a idonsa domin ganin yadda idanuwanta suka rufe.
Babu abin da ya ke zuwa a ransa sai, da lokacin da ta yi ta takura masa akan sai sun taho wannan masifar, da ya ƙi amince mata da babu abin da zai same ta yanzu, domin shi yafi damuwa da ita akan kansa, so ya ke ya kira sunanta ko zata buɗe idonta amma ina ya kasa, sai rintse ido yake yana buɗewa saboda yadda yake cigaba da ji a jikinsa, da kuma wannan dariyar da ke cigaba da ratsa masa kunne, ashe duk yadda ya ke ganin wannan wuri abun ya ma wuce tunani.
Lokaci ɗaya dariyar nan ta tsaya cak, gurin ya gauraye da shiru na ɗan mintuna, ka na daga baya ya fara jin wani irin sauti na ban tsoro na tashi a wurin, wasu mutane ya fara gani suna tsayawa a kansu, amma daidai nan shima idonsa ya rufe, kamar dai suma yayi, ba tare da ya gama gane su waye mutanen ba, ko kuma me suka zo yi musu..
Mutanen kuwa ɗaure suke da fararen yadi ƙal a ƙugunsu, sai wani zane-zane da yake a fiskokinsu da kuma jikinsu, sai kuma layoyin tsafi da suka sanya ta ko ina a jikin na su, manyan mutane ne ti ƙa-ti ƙa, babu ɓata lokaci suka sanya hannu suka kwashi Amna da Shuraim suka fara tafiya da su wani ɓangaren daban, babu abin da ya ke tashi sai dim-dim ƙarar tafiyarsu.
RAHEENA.
Shiru-shiru su Amna ba su dawo ba, duk ta riga da tayi yadda zata yi an fasa meeting ba tare da an san takamemmen silar fasawan ba, duk da kuwa meeting ne mai mahimmanci, amma sai gashi anɗau lokaci har bayan la'asar ba tare da Amna ta dawo ba, tayi ƙarya har ta gaji da masu saƙo da kuma neman magana da C.E.O, ta kira numbern Amna karo na babu adadi amma ba ya shiga, domin bata san da cewa wayar Amna ta samu matsala ba.
Hankalinta gaba ɗaya ya tashi, ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai tunani ta ke Allah dai yasa ba wani abun ya samu Amnar ba, kar wani abu ya sami sabuwar ƙawarta Amna kamar yadda ya sami Safna, tagumi ta yi cikin zullumi da fargaba, "ya Allah ka kare min ƙawata Amna, ya Allah ka kareta daga duk waga matsala ko tashin hankali, ya Allah ka sa tana cikin aminci yanzu haka" ta yi addu'ar daga zuciyarta tana jin hanayin fargaban cikin ranta.
KOGO.
Hasken wutar icche ne ke tashi à wurin, a hankali Shuraim ya samu damar buɗe idanuwansa, duk da cewa har yanzu yana jin ciwo a jikinsa, amma ya ragu kaɗan, ɗaga idon yayi don ganin à inda ya ke, saboda bai gama fiskartar komai ba, kawai idonuwansa ya fara gane masa mutane suna tsaye can gefe jere kamar sojoji, jin kamar jikinsa a ɗaure ne yasa shi sauke idonsa zuwa ga jikin na sa, ganinsa ya yi an cire masa riga, wannan kalar da fatarsa ta canza ɗin nan yana nan raɗau bai ɓace ba, ɗaure yake da igiyoyi an rataye hannayensa sama hatta ƙafafuwansa an ɗaure su, da sauri ya kuma ɗaga idanuwansa cikin tashin hankali yana neman inda Amna ta ke amma bai ganta ba, can sai idonsa ya gane masa wani gajeren mutum zaune kan wata mummunar kujera, kujerar da ke kewaye da abubuwan tsafi.
Cikin lumshashshun idanuwansa ya ga mutumin na tashi daga kan kujerar na sa, wato matsafi shugaban mutanen nan, yana tashi ya kwashe da dariya mai amo mara daɗin sauraro, sauran mutanen nan ma suka amshe da nasu amon, Shuraim bai gama fita daga tsoron muryoyin dariyar na su ba, ya ga mutumin nan ya isa gurin wata baƙar tukunya, sannan ya sanya hannunsa ya fito riƙe da wani baƙin ƙaho guda ɗaya murɗaɗɗen babba da ke cikin wani abu mai kama da tangaran mai haske, baza ka taɓa gane wannan ƙahon na menene ba, domin yadda suffan ya ke daban da irin dabbobi da mutum ya saba gani.
Ijje wannan tangaran ɗin shugaban matsafan ya yi, wanda sai a yanzu Shuraim ya lura da kalar da ya ke fatar ta sa, blue ne sosai sai abubuwan tsafi da ya ke kewaye da jikinsa, Shuraim na cigaba da kallonsa ya ga ya ɗauki wata kafurar wuƙa ƙatuwa daga gefen dutsen da ya ijje wannan ƙahon, ɗaga wuƙar yayi yana sake sheƙewa da dariya sai kuma ya sauke wuƙar yana taku izuwa wurin wasu igiyoyi da suke ɗaure, da ido Shuraim ya cigaba da bin ko wani taku da ya ke yi, yana kallonsa ya sanya hannunsa wanda babu wuƙa ya kama wata igiya ɗaya.
A galabaice Shuraim ya samu damar ɗaga idonsa saman igiyoyin da yaga wanna mutumin ya riƙe, amma me zai gani? Amna ce ɗaure jikin igiyar a sama tana reto kamar babu rai a jikinta. Ganin ta ɗaure a sama ya girgiza masa ƙwaƙwalwa, kamar an ciro masa zuciya ana matse ta, bai san yaushe bakinsa ya buɗe ba cikin fitar hayyace ya furta, "Amnaaaaaa!!!!" Juyowa sauran suka yi suna kallonsa domin dama ba su san da shi ya buɗe ido ba, ai kuwa suna kallonsa suka sa wannan razananniyar dariyar ta su, "Amnaaa!! Ki.. ki tashi, babu abin da zai same ki.. ya..." ya faɗi da ƙara yana fashewa da kuka mai tsuma zuciya, don à tunaninsa mutuwa Amna ta yi, bisa yadda ya ga take reto a sama.
Ba tare da wannan matsafin ya ce komai ba, ya juya da idonsa kan igiyar da ke hannunsa, sannan ya ɗaga wannan wuƙar ya yanke ta, yana yankewa igiyar tayi sama da sauri wasu daga cikin sauran igiyoyin ma suna warwarewa, kawai Amna ta fara faɗowa ƙasa, yayin faɗuwarta zoben da ke cikin aljuhunta ya faɗo sai ta faɗi a kansa, ƙara Shuraim ya kuma saki haɗi da kiran sunanta cike da tsoron abun da ya same ta.
Zaro idanuwan nan na sa mai kama da 'yan china marasa kyan gani matsafi ya yi, da sauri ya juyo da kansa zuwan kan Shuraim da ke faman kuka, takowa ya fara yi dumm-dumm zuwa gaban Shuraim da idonsa akan Amna kawai ya ke, yana faɗin, "ki tashi Amna, ki tashi, ya zaki tafi haka?" Faɗi ya ke yi da sanyin murya cikin raɗaɗi a zuciyarsa.
Matsafi ya ɗaga wannan lahanannen wuƙar sama, haɗi da sanya ta gefen wuyar Shuraim, sai da ya kwashe da wani mahaukacin dariya na ban tsoro sannan cikin muryarsa mai kama da gurnanin zaki ya fara magana daki-daki da cewa, "kafin na fara, saudaukar da ita, ya kamata in fara ta kanka, musamman yau n'a ƙi ba, kowa umarni, ni da kaina na ke son, sadaukar da ku ga ƙahon tsafi, kun kawo mana kanku, da kanku, kunyi babban garaje, da ya kasance kuka bari ƙwaƙwalwarku, ta yi muku tunanin shigowa wannan kogo! Amma kun taimaka mana, kun rage mana wahalar zuwa ɗaukarku, sai ku ka zo da kanku, mun riga da mun san da zamanku, tun kafin ku bayyana garemu, wai ku jarumai ko? Kun zo taimakon wani, ku ɗauke sa daga cikin wannan kogon, lallai kun tafka babban kuskure, baku san me za ku tawar à cikin duniyarmu ba, shiyasa kuka taho".
Yana karshe maganar ya Rufa da dariyar nan, ajiyar zuciya Shuraim ya yi, ko ba komai ya ji cewa basu kashe Amna ba har yanzu tana rayé, hawaye na ta gangarowa a fiskarsa, yana kallon matsafi yayin da zuciyarsa ba ta tsaya daga bugun da take ba, hannuwansa da jikinsa na cigaba da amsan raɗaɗin da ke cigaba da shiga jikinsa yanzu, lumshe ido ya yi ya buɗe, yana shirin yin magana matsafin nan ya kuma manna masa wannan wuƙar sosai jikin fatar wuyansa,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 42 Chapter of 56