yi masa domin a yanzu idanuwanta ne kaɗai motsi sosai, "anty kyauta na kawowa Safna, bari in tafi karta ritsa ni, domin surprise ne" ya faɗi tare da barin Ammu ya wuce, Ammu kuwa da kallo kawai ta bisa har ya fita. Sai da Yazeed ya tsaya ya sake sakin murmushi, yana tuna yadda Safna zata ji idan ta kalli saƙon da ya rubuta mata, gobe ne zaiyi zaman jiranta, idan har ta karanta wasiƙar kuma ta bashi amsar da ya dace.
Ruki ce laɓe tana kallon Yazeed bayan ya wuce, domin tun tahowarsa riƙe da gift ta gansa, sai da ta fara waige-waige don tabbatar da babu alamar Amna ko wanda zai iya ganinta, sannan ta shige ɗakin, nufan kujerar da ya ijje gift ɗin tayi, tana zuwa ta ɗaukesa tana jujjuyawa tana kallo, sai da ta taɓe baki ka na ta ce, "immm irin wannan ƙaton kyauta haka? Na san abin da ke cikin sa zai kasance na musamman, zan so inga menene a cikinsa" ta faɗi tare da ɗaukar papern saƙon da ya faɗi lokacin da ta ɗaga kyautan, Buɗe shi tayi ta fara karantawa da ƙyar, domin ba wai katarun ta ke ganewa sosai ba, abun da ya rubuta cikin wannan saƙon shine.
___Na san zakiyi mamaki da wannan kyauta idan kika gansa, duk ba wai wani abu na daban ba ne, zanyi amfani da wannan damar in sanar da ke abin da na kasa faɗa miki lokuta da dama, i love you Safna! kalma ce da ta fito daga cikin zuciyata, soyayyarki a ko da yaushe ƙaruwa take a cikin ruhina, soyayyarki ta zama tamkar shan ruwa a gare ni, domin kuwa idan babu ruwa babu ran da zai rayu a duniya, na san cewa munyi zama na ɗan taƙi ni da ke a baya, wanda na ɗauki hakan kamar shekaru bila adadin ne daga cikin rayuwata, kyautar da na turo miki shi ne nazarin amsarki gare ni, ina fatan kalar da na zaɓa zai burgeki, ina son ki sanyashi gobe, yin hakan ne zai bani damar jin amsarki a gareni, idan kika sanya wannan rigar da na miki kyauta da ita, zai nuna min cewa kina sona kuma kin amince da ni, domin na san amsar ka iya yi miki wahala a faɗa, kasancewarki mai kunya da sanin ya kamata, idan kuma baki sanya shi ba hakan zai sa in karɓi amsar rashin amincewarki, wanda ni kuma zan so na samu amsar nan ba. Daga yayanki ɗan uwanki kuma masoyinki Yazeed___
Bayan Ruki ta gama karantawa ta saki murmushin mugunta tana faɗin, "ashe amsar tambayarka? Ai kuwa zaka rasa amsar, domin ni ɗin nan bazan bar hakan ya faru na, sanƙame kyautar zanyi, ba zan bari ka samu amsar tambayarka a wannan lokacin ba, sai dai gaba in kana da sa'a tun da zan tafi in bar gidan, inyi rayuwa a gidan Baby na cikin ƙasaaita da jin daɗi, Hmm ba ranar na faɗa maka ka ƙi yarda ba? To yau zaka gasgata akan wannan kyautar da kayi matan" ta juya zata fita riƙe da kyauta da kuma wasiƙa a hannunta idonta ya kai kan Ammu.
Takawa tayi zuwa in da Ammu ta ke tana cewa, "ohh jatumar Safna kina kallo na kenan? Ai ni da na ɗauka idon ki a rufe yake, tun da mutuwa ta ƙi ɗaukar ki tsawon lokaci, kina nan kamar gawa da rai. Gashi na ɗauke kyautar da ɗan uwa na yayi wa shegiyar 'yarki, idan ta zo sai ki faɗa mata ko? Uuu na fa manta, ashe tana da aljanu akanta, ƙila ma sun isar mata da saƙona" Tana faɗi ta barin Ammu bayan ta gama galla mata harara, domin tun tuni ta fara tantamar Safnar, wucewa tayi tana ci gaba da murmushin muguntarta.
Last part.
___________________________________________________
Tooo 'yan uwa na, kun dai ji Shuraim ya bayyanar da gaskiyar cewa yana son Amna, Amna har yanzu kuma bata yarda tana son shi ba, to ko zata yarda daga baya? Ko kuwa ba zata yarda ba saboda ta fara tausayin Yazeed?
Sannan ga Yazeed ya ijje mata gift Ruki ta ɗauka, sannan kuma shine amsar tambayar sa, shin ya kuke ganin zai kasance gaba?.
Sannan kuma gobe ranar ajren Marwan, shin kuna ganin za'a haɗa da na Rukin?
Akwai ƙaramin cakwakiya fa.
Ku kasance tare da alƙamin✍🏼 {Mrs Umar} [Gimbiyar Fasaha]👸🏽
Don ji da hasaso yadda zata kaya.
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣2️⃣3️⃣▶️1️⃣2️⃣4️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Yazeed. Bayan ya baro ɓangaren ɗakin su Amna, ya sauko daga upstair murmushi na cigaba da ƙayatuwa à light brown beautyn fiskarsa. Shuraim ma riƙe da jakar kaya a hannunsa shima yana murmushin, ko wanne a cikinsu na cikin wani irin shauƙi na daban, kawai suka bangaji juna ba tare da sun ankara ba, jakar da ke hannun Shuraim ya faɗi ƙasa, kayan da ke ciki na atamfa ya leƙo, kallon junansu su kayi kowa na cike da ɗan uwansa.
"Ba ka gani ne!?" Cewar Shuraim harda ɗaga hannu yana nuna Yazeed, shima ɗin ɗaga hannun yayi cikin tsana ya ce, "ni ban ce maka ba ka gani ba sai ni zaka cewa hakan?!" Ƙaramin tsaki Shuraim ya ja, domin ji ya ke da za a haɗa shi faɗa da Yazeed da yayi farin ciki, domin har yana ganin wata ragargaza da zai yi masa, tsugunnawa yayi don mayar da kayan da ya fito amma ba duka ba, da kallon mamaki Yazeed ya bisa har ya ɗago.
Shuraim na ɗagowa suka haɗa ido, kowa ya sake wa ɗan uwansa kallon banza sannan kowa ya juya yayi hanyar da dama nan yake don yi. Yazeed fita yayi, Shuraim kuma upstair ya hau don zuwa gurin Amna, ko da ya isa shima ya tarar da ba ta nan bata dawo ba, shiga ɗakin yayi da sallama har zuwaa gaban Ammu, murmushi ya sakar mata, itama kallon na sa ta ke, sai da ya ɗau minti ɗaya yana yi mata wannan murrmushin, har tunani ya fa ɗa lokacin baya, a asibiti sun kula dashi sosai ita da Mai daraja, ba ta bari ya zauna da kansa, ita take taimaka masa, ta sanya masa pillow ta baya yadda zaiji daɗin zaman, sannan ta ciyar da shi abinci a baki, ko da ya ƙoshi sai ta lallaɓa shi ya ci, ta bashi kulawa sosai.
Hawaye ne ya zubo daga idon na sa kamar bakinsa ba zai buɗe ba ya furta, "Ammmu!" Ya faɗi kamar yana son yin kuka, shine wanda ya sanya mata wannan suna (Ammu) hakan yasa tun da ta samu Safna ta ke sanya mata wannan sunan a baki, tun ba ta iyawa har ta tashi da shi. Ammu ma cikin ranta ambatan sunan na shi ta yi, itama ƙollah na ciko mata idanu, da sauri ya sanya hannunsa ya goge mata hawayen tare da girgiza mata kai alamar a ah, sannan shima ya share hawayensa, ba tare da ya sake wata magana ba ya nufa kujera ya ijje kyautar da yake a hannunsa.
Domin ya san idan har ya tsaya a wurin Ammu to hawaye ne zasu cigaba da cika masa ido, bayan ya juya daidai jin kamar takun takalmi ta wurin, wanda ya ke kyautata zaton na Amna ce, da sauri ya nufi bayan ƙofa ya ɓoye, tun da har ya zo bai ganta ba, to ya kamata ya tafi ba tare da ta gansa ba. Kai tsaye Amna ta nufo ɗakin, idonta ya gane mata takalma a ƙofar ɗakin amma hankalinta bai kai ba, da sallama ta shigo tana daddanna wayarta. Shi kuwa Shuraim Amna na shiga ya fara sanɗa don fita, sai à lokacin Amna ta bar kallon wayar na ta tana kallon ƙasan tayis, domin yadda zuciyarta yanzu ta sanar mata akwai wanda yake nan a bayanta.
Shuraim ya kusa fita Amna ta juyo, sai dai kafin ta gama juyowa har ya fice bata gansa ba, sauya fiska tayi ganin babu kowa ta bayan na ta, juyawa tayi gabanta sai kuma hankalinta ya kawo mata kamar ta ga takalmi à ƙofar ɗaki, hakan ya sata fita amma bata tarar da takalmin a wurin ba, ta koma ciki tare da ɗaga ƙafaɗu, alamar kawai hasashen zuciyarta ne, sai kuma ta sauya fiska zuwa mamaki yayin da idonta ya sauka akan jakar da yake kan kujerar ɗakin.
A mamakance ta taho wurin tare da ijje wayarta akan kujerar sannan ta sanya hannayenta ta ɗauki jakar, "Asnac tailor design" abin da ta karanta kenan a jikin jakar, ta sake cewa "to me a ciki? Kuma wa ya kawo?" Ta jefewa kanta tambayar ta na yi da kanta gefe kaɗan, sai kuma ta dawo da kallonta kan jakar haɗi da buɗewa, "tooo atamfa? Kuma ɗinkakku!?" Ta kuma furtawa da mamaki sannan ta sa hannu ɗaya ta fara cirowa.
Shuraim ko da ya bar ɗakin à falo ya tsaya, zama yayi à kan kujera yana sakin murmushi mai cike da farin ciki da yawa, tun ranar da ya ga ta sanya a tamfa, kuma ta yi masa kyau sosai, hakan yasa tun a ranar ya je ya siyo sannan ya bada ɗinki bayan ya zube zun-zurutun kuɗi don a fitar masa ɗinkin yadda ya kamata. "Ina jiranki my Amnah" ya furta tare da sake washe bakinsa cikin ƙarin farin cikin.
AMNA. Riga ta ciro kalar purple da ratsin baƙi da kuma milk, hakan yasa ta ijje jakar tana buɗe rigar daga naɗin da akayi masa, "wooooow" ta furta bayan ganin haɗuwar colour da kuma style ɗin da a kayi wa rigar, jujjuya shi ta fara yi tana kallon gaba da bayan sa, "to amma aikin waye wannan?" Ta sake yiwa kanta tambayar sannan ta ijje shi ta na ɗaukar jakar ta juye don ganin sauran kayan, ƙaramar paper ne ya faɗo a ƙarshe kan kayan, da mamaki ta sa hannu ta ɗauki papern tare da warwarewa, amma kaɗan ta warware, sai da ta zauna ka na ta fara karantawa.
"Atamfa na yi miki kyau!" Abun da ta fara karantawa kenan, ba tare da ta gama warware duka saƙon ta sauke hannunta ƙasa, tuna kwanaki da Shuraim ya sanar da ita atamfa na yi mata kyau ta yi, sannan ta sauke numfashi haɗi da murmushi à baki ta furta "Shuraim!" Ta faɗi tare da ijje papern kan kujerar ta miƙe, "shine na sani, kuma shiyasa naji ɗazu kamar mutum yana cikin ɗakin nan, kenan ya shigo ɗin?" ta kuma faɗin haka haɗi da tsintar kanta cikin duniyar farin ciki, sosai take murmushi har da bayyanar da haƙoranta.
"Murmushi? Murmushi fa nayi, yeee nayi murmushi!" Ta faɗi tana dariyar jin daɗi, sai kuma ta tsaya ta sake faɗin, "yes! Maganar Raheena haka ne, tabbas haka ne, nima, nima ina jin wani abu a kansa, kuma wannan abun SO ne, eh SO ne!" Ta kuma faɗi tana cigaba da dariya, taku tayi zuwa wurin Ammu ba tare da ta daina dariya mara sauti sosai ba, "Ammu wai ni ina son Shuraim, da gaske fa ina sonshi, wallahi kuwa!" Tayi maganar tare da riƙe hannun Ammu tana girgizawa, yayin da take jin zuciyarta tamkar anyi mata wani gagarumin albishir.
Sai dai ba ta yi mata wannan murmushin na ta ba, tun ranar da Ammun ta yi mata murmushi a asibiti bayan ta farka bata sake ganin wannan murmushin ba, sake hannunta tayi sannan ta koma inda kayan yake tana murmushi, ta ɗauka rigar tare da mannawa a jikinta tana zuwa gaban madubi, kallon kanta take tana cigaba da murmushi mai ƙara fitar da ainihin kyanta.
"Woow! Zanyi kyau sosai cikin kayan nan" ta faɗi tana karkatawa gefe tare cigaba da kallon kanta a cikin madubi, yayin da zuciyarta ya fara tafiya gurin wasu daga cikin maganar Shuraim da yayi mata ɗazu, "tabbas akwai alaƙa a tsakaninmu! kuma wannan alaƙar ita ce SO" "Amna a yanzu na riga da na amincewa kaina ina son ki" "na daɗe da gane ina son ki!" Ba ta san lokacin da ta rungume wannan rigar ba tare da lumshe ido, tana ji tamkar iska mai cike da sanyi da ni'ima na kaɗa mata, a take kalamansa suka kuma dawowa cikin kunnenta da kuma zuciyarta.
"Na daɗe da gane ina son ki" "tabbas akwai alaƙa a tsakaninmu! kuma wannan alaƙar ita ce SO" "Amna a yanzu na riga da na amincewa kaina ina son ki" "kuma wannan alaƙar ita ce SO, SO, SO". Buɗe idanunta tayi a hankali cikin wani yanayi mai wuyar fasaltuwa, ckin sanyin murya mai sanyi da kuma a hankali ta fara magana, tare da yin nuni da hannunta daga setin zuciyar ta zuwa kan madubi tamkar tana magana da shi a gabanta ta ce, "niima, a yannzu, na gane alaƙar da ke tsakani na da kai Shuraim!" Ta ƙarashe faɗin sunan nasa da sauri haɗi da ƙara fiddo da jerarrun haƙoranta waje.
SHURAIM.
Har yanzu yana nan zaune a falo, sai bin hanyar upstair ya ke da kallo lokaci zuwa lokaci, harda wani haɗa tafin hannayensa biyu guri guda yana mummurzawa, alamar ya ƙagu da kuma razana da fargaba akan amincewar Amna a kansa, domin bayan wannan saƙon da ya rubuta wanda Amna ta karanta, akwai wani rubutu a ƙasa, wanda ita kuma bata gama buɗe saƙon ba ta bar shi, abun da ya rubuta shine.
......"Kasa dauriya nayi shiyasa na faɗa miki abin da yake a zuciyata, saboda wani yanayi na rashin daɗi da ya ziyarce ni lokacin da kika ambaci Yazeed, amma sai dai na lura kamar hakan bai yi miki daɗi ba, dan Allah ki gafarce ni don Allah, mu cigaba da mu'amala kamar da,". Sai kuma ƙasa ya kuma rubuta, "idan har kin yafe min da wannan kuskuren da na yi, kuma atamfar tayi miki kyau, to ki sanya shi yanzu, ina jiranki a falo"......
Shiyasa yanzu yake kallon hanyar upstair don ganin ko zata fito. Sai dai bayan mintuna da yayi kuma bata fito ba ne ya sa shi tashi kawai don ya wuce ɗakinsa, guiwa a sanyaye ya fara tafiya, sai da ya tsaya a wurin yana kallon matattakalan ka na ya sa ƙafa don wucewa, sai dai takunta da yaji ne yasa shi dakatawa, yana ɗaga kai idonsa ya shige cikin na ta bayan ta dakata da saukowar, har ya buɗe baki yana murmushi sai kuma ya tsaya, gabansa na wani irin faɗuwa, saboda ganinta da yayi ba a sanye da kayan ba.
AMNA kuwa ƙin sakin masa fiska tayi, ta ƙara damƙe kofin ruwan da ke hannunta tare da barin kallonsa ta cigaba da saukowa, harta wuce bata ce masa ko sannu ba. Hakan kuwa ba ƙaramin sanya guiwansa sanyi sosai yayi ba, domin shi ɗauka yayi ta ga wasiƙar bata sanya kayan ba, sannan kuma gashi ta ƙi sakar masa fiska, hakan ya tabbatar masa da cewa kenan ba son shi ta ke ba, kawai dai yaudarar kansa yayi" kamar wanda babu jini a jikinsa haka ya fara tafiya zuwa ɗakinsa, yana jin yanayi na zafi da rashin daɗi a kan abun da ya faru da shi. Bai san cewa Amna kam ba ma ta ga saƙonsa na sa ba,
Ruki kuwa bayan ta koma ɗakinta da wannan saƙon, har da garkame ƙofa, ijje gift ɗin tayi a kan gado tare da hanzari don buɗewa, tun kafin ta gama buɗe wannan kyautar ta fara fiddo Ido sakamakon ɗaukar idon da colour ɗin kayan yayi mata, ƙarasa fiddo shi tayi tana ɗagawa, doguwan riga ce mai tsananin kyan launi da kuma ado, kalar pich kolliyan kuma launin maroon da fari, ya haska iya haɗewa. Sai da Ruki ta sake sakin baki sabi da yadda ta ga haɗuwan rigar.
"Yanzu dama wannan can-careɗiyar rigar ya sai mata, ko Hajiya ban taɓa ganin ya kawowa abu makamancin haka ba, amma da yake wannan tsinanniyar ce sai gashi ya siyo mata, gwara da na ɗauke shi ma, da gobe ina ji ina gani ni amarya amma zta fini kyau, dama ya take? Bere ta sa wannan kaya ai sai a dawo kallonta kawai, ijjeshi zanyi idan na je gidan Babyna in sanya masa ya gani" ta ƙarashe da dariya tana linked.
WASHE GARI. RANAR ƊAURIN AURE, MISALIN SHA ƊAYA NA SAFE.
Shuraim da tsananin damuwa ya kwana. yayin da a ɓangaren Yazeed kuma cikin farin ciki da kuma ɗauki, domin yana kyautata zaton yau zai samu gamsashshiyar amsarsa ga Safna. Ɓangaren Amna itama da farinciki ta kwana, domin tunanin Shuraim ya yi mata kamun kuku cikin zuciya, ta ƙi sakar masa fiska jiya ne don tayi masa ba zata, sai yau zata sanar da shi itama ta amince da shi, sannan kuma ta sa kayan da ya kawo mata, ta san wannan ba ƙaramin farin ciki zai sa shi ba.
Wa'yan nan mutane ukun kowa da yadda ya sauka daga gadonsa bayan ya farka, Amna da murmushi mai sauti da kuma shauƙi. Yazeed kuma da farin ciki da ƙaguwa. Shuraim kuwa da kasala da kuma yanayin rashin daɗi.
Taro yayi taro, mutane ne cike a gidan, kasancewar Dady ma da mutanensa, sannan Hajiya ma da na ta, ga kuma Marwan ma, sannan gefe ɗaya Hajja Ruki. Shiryawa Amna tayi tsaf cikin wannan atamfar, sannan tayi kwalliya mai ɗaukar hankali, kyan da tayi sai kun hasaso, domin ni idan na ce zan yi hakan to fa zan rage ne. Tsayawa tayi a gaban madubi yanzu ma kamar jiya, tana kallon kyawun da tayi yau sosai, ita da kanta ta shaida da hakan ko ba'a faɗa ba, murmushi ta saukar wa'yannan dimple ɗin suka bayyana, har ta riga da ta shirya yadda zatayi masa maganar cewa itama kogin son sa ya cika zuciyarta har ya fara zuba.
Barin wurin madubin tayi tare da ɗaukar mayafinta haɗi da zuwa inda Ammu take kan kujerar guragu bayan ta ci nasarar zaunar da ita kuma ta sauna dai dai ba tare da nuna alamar zata faɗi ba, "Ammu zamu iya tafiya?" Ta tambayi Ammu tana murmushi, sannan ta koma bayanta ta sanya fararen hannayenta da ke ɗauke da zobe da kuma agogo ta sa a kan gurin rikewar keken ta fara turawa suka fita daga cikin ɗaki. Tun ranar da Ammu ta dawo daga asibiti ba ta fito waje ba sai yanzu, domin Amna gani tayi ya kamata ayi komai na shagalin bikin nan da Ammu.
A hankali ta fara sauka da Ammun gurin upstair, ba tare da ta tambayi taimakon wani ko wata ba, turawa ta ke yi yayin da ta ke sarrafashi mai kyau ba tare da ya gangara ko ya ja ta gaba ba. Wasu taron mutane da suke a wurin suka ɗaga ido suna kallonta cike da mamaki, yadda take tura wannan keken tamkar a ƙasa, tayi musu kyau sosai shigarta da kuma haɗuwarta, Amna kuwa ko kallon inda suke baba yi ba har ta ƙarisa saukar da Ammun daga matattakalan, ɗaukar wayarta da ta ijje jikin Ammun ta yi sannan ta cigaba da turawa zuwa waje, domin ta san yanzu haka su Shuraim suna wajen.
A sannu a hankali take tura keken Ammu har suka kaiga fita daga falon. Yazeed ne tsaye yana kallon ƙofar falo cikin ƙaguwa sosai, sanye ya ke da riga da wando masu kyau, na manya masu tsada,
Ni fa ina ganin kamar zan katseku idan na yawaita faɗo muku kyan shigarsu, don haka yanzu ma na baku zaɓi da kan ku ku ɗaura musu duk kala da kayan da suke sanye da shi, daga Yazeed har Shuraim, amma fa sun haɗu ba magana😉.
Kamar da wasa, idonsa ya faɗa kan Amna da ta fito da Ammu sanye cikin wani kaya daban, ba wanda ya yi mata kyauta da shi ba, miƙewa yayi da hanzari yana kallonta, sai da yaji tamkar rugugin hadari ya fa ɗa masa daga tsakiyat kansa izuwa jijiyoyin dake riƙe da zuciyarsa.
Shuraim kuwa da kansa yake a ƙasa ya kasa sanin me ke yi masa daɗi a duniya, domin ko iskar da take kaɗawa ɗaukarta babu yayi, anya zai iya zuwa wannan ɗaurin auren kuwa? Ya tambayi kansa, domin yadda yake jin zuciyarsa a raunane kamar babu abin da zai iya yi cikin nutsuwa, lokaci ɗaya kawai ya miƙe ya na shirin komawa ɗakinsa, juyawar da zai yi idanuwansa kan Amna da ke tsaye idonta na kan sa, sai da yaji kamar guguwar hadari ta watso fiskar sa, sai da ya rufe ido ka na ya buɗe, cikin mamaki tsanani ne ya shiga, sannan kuma gashi sai wani sakar masa kyakykyawar murmushi take yi,
Wani kuɓutaccen murmushi ne ya kauce masa, ba tare da yayi izinin hakan ba, nan ya fara aika mata daga cikin ruhinsa, nan suka fara haɗa maganansu guri guda sunayi wa junansu yau kam direct kallon da kowa ka iya fassarawa da soyayya, domin yadda ko wanne a cikinsu zuciyarsa ke faman bugun bango mai amo da su kaɗai su ke jin hakan.
Yazeed. Wani irin rawa ƙafafuwansa suka hauyi ba ƙaƙƙautawa, zuciyarsa na yi masa wani lugude kamar ana matse kayan wanki, juwa na shirin yin awun gaba da shi, ƙyaƙyƙyafta ido ya fara yi da sauri-sauri yayin da ya fara kallon mutane kamar suna kasuwa izuwa kashi biyu, uku-uku.
Last part.
___________________________________________________
Hmmmm, mu haɗu à gaba kawai, yau n'a bar muku kuyi wa kan ku tambaya.
Alƙalamin ✍🏼........
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣2️⃣5️⃣▶️1️⃣2️⃣6️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Duk hakan ya sake kasance masa ne yayin da idonsa ya ke kan Amna da kuma Shuraim, tabbas kayan da Amna ta santa su ne wanda ya gansu jiya a wurin Shuraim, sannan gashi nan yanzu kuma suna aikawa junansu kallon da ya tabbata babu wani kwana-kwana kallon ƙauna ce, hakan ya nuna masa amsar da Safnar ta bashi, ba ta son shi kuma bata ƙaunar shi, Shuraim ne zaɓinta, don haka ta nuna masa komai a bayyane, ba tare da faɗi da baki ba.
Saurin zama kan kujera yayi bayan ji da yayi hajijiyar ya tsananta masa, sannan ga wani bugu da zuciyarsa yake tamkar zai bayyana a waje, take zufa ya fara tsatstsafo masa ɗaya bayan ɗaya hannun sa gaba ɗaya ya ɗaura a kai idonsa na fara canza launi. Shuraim kuwa taku ya farayi zuwa inda Amna ta ke, har yanzu wani irin shock ne ya ke ji à ransa, domin abin da ya cire rai akansa ne ya gansa. Mutanen da suke a wurin da dama tun fitowar Amna idon su yake a kanta, take suka cigaba da zura n'a muzurunsu akan Amna da Shuraim da sai yanzu suka ga ya isa inda take, wasu na yaba kyansu wasu kuma burgewar da suka yi.
Murmushi mai sauti Shuraim ya fara sakar mata kamar zautacche, itama bin ayari tayi tana washe masa baki, sai daga baya Shuraim ya buɗe baki yana furta, "kinyi kyau sosai, sosai, sosai fa!" dariya kaɗan tayi sannan ta ce, "na ji ai malam ɗan ƙasar London, ko ce maka akayi ina da matsalar kunne da kake nanata min?" Dariya suka yi a tare, kafin Shuraim ya kuma yin magana kira ya shigo wayar sa, "sorry 'yanmata, bari in amsa waya, amma gashi na ma ga ana fita ƙila lokacin tafiya ɗaurin auren yayi, so idan na dawo sai mu tattauna kinji kyakykyawa?".
Shuraim na faɗi ya bar in da ta ke cikin tsananin farin ciki da murmushi, ita kuwa tun da yayi mata wannan maganar ta tsinci kanta a duniyar gajimare, idonta ya rakashi da kallo, sai da ya juyo ya dubeta ya kuma sakar mata da murmushinsa da ya kuma shige mata uwaɗɗakan zuciya ka na ya juya, har sai da Amna ta daina hangosa sannan ta ɗauke idon tare da sakin a jiyar zuciya mai daɗi cikin annashuwa, sannan ta sa hannu don tura Ammu su koma falo, dama don ta ga Shuraim ɗin ne ta fito.
Da mamaki ta tsaya kanta ƙarisa bayan magananta sun gane mata Yazeed can zaune shi ɗaya, sannan ga shi riƙe da kai da hannayensa biyu akai alamar yana cikin damuwa, "to ko, ko dai bashi da lafiya ne? Dubi yanayinsa, idan ba don ba da sai ince kamar idona gani yake tamkar jikinsa na rawa" cewar Amna cikin zuciya tana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 56