na yi masa sanyi kamar ruwan randar ƙasa, taya Amna zata yi gaggawar yanke hukunci haka? Ko ba komai dai ta haƙura su yi nazari sannan su warware matsalar komai, amma yanzu kwatsam ta ce wai ta amince zata auri Yazeed? Sannan ta kallesa, hasalima idonsa cikin na ta ta furta maganar, bayan kalmar da ta faɗa na tana sonsa, har da wani babban ƙulli kuma zata haɗa? Taya zata auri Yazeed bayan yana nan?.
Yazeed ko da bai m'a lura da wani Shuraim ko shigowarsa ba, domin tun jin amsar da Amna ta bashi wanda dama abin da yake so kenan, ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi na shauƙi da samun cikar buri, haske yaji ya karaɗe ilahirin zuciyarsa, domin har ji yayi tamkar ta ma zama matarsa, idan har ba mafarki yake ba, sannan ba a wata duniyar ya ke ba, to fa shikenan burinsa ya cika, ji ya ke kamar babu wanda ya fisa farin ciki yau.
Ita ko Amna tana ganin Shuraim ya fice daga ɗakin ta sauke wata ajiyar zuciya mai cike da kasala, komawa tayi ta zauna tare da kallon zanin gadon da Yazeed yake akai, amma zuciyarta na wani fagen daban, ta ga rashin natsuwa haiƙan a kan ido da kuma fiskar Shuraim, to amma me yasa zai hana ta sanarwa Yazeed gaskiyar lamarin, duk da ta san hakan ka iya jawo wa su Shuraim ɗin matsala akan abin da suke yi, to amma ya fi so ta cigaba da wahalar da Yazeed akan abin da bai da masaniya akai? Ta so su sanarwa Yazeed gaskiya ne, sannan ita da Shuraim ɗin su kasance masoya a idon duniya, "in har kana so na, na san zaka sanar da Yazeed komai da kanka, saboda gudun kada ka rasa ni" ta tsinci kanta da furtawa cikin ranta tare da lumshe ido.
Sai kuma ta yi saurin buɗe ido haɗi da miƙewa sakamakon motsin Yazeed da ta ji yana sake ƙoƙarin tashi, da sauri ta kuma tsaida shi da cewa, "ka dai na ƙoƙarin tashi mana, duba jikinka ba ƙwari fa" hannunsa ya ɗaura akan bandejin da yake kansa, yana jin zugin da gurin ciwon ke masa, duk da cewa allurar bacci na ɗibansa amma shi kuma baya son yayi wani barci yanzu, don da ace yasan abin da Safna zata zo masa da shi kenan, da ya roƙi likita akan kada yayi masa allurar, ya fi son ya zauna tare da sanya Safnarsa à gaba yana kallonta ba tare da gajiyawa ba, cike da farin ciki mara misaltuwa da kawar da ciwon da kan na sa yake masa, idonsa kamar yana lumshewa ya ce.
"Don't worry my Safna, magan-ganunki sun riga da sun warkar da ni, a yanzu ba na jin ko wani zugi sai guda ɗaya, wanda kuma zai dawwama ne a cikin raina, ba tare da ya fice ba" ya faɗi yana gyara zaman da yayi bayan ya tattaro gaba ɗaya ƙarfinsa, saboda yadda yake jin jikinsa ya dawo kamar sabon jini, "wace ciwo ce wacche ta rage? Sabida bai kamata komai ya rage a zuciyarka ba, kowa so yake ya ganka cikin farin ciki da walwala, sannan ga su Hajiya da Dady da kuma 'yan uwanka kowa jiranka yake yi" sai da ya murmusa sanna ya bata amsa da cewa, "wannan ciwon shine soyayyarki, kuma na san duk rintsi ba zan warke daga shi ba,"
"Kana ganin ba ka yarda da maganar da na faɗi cewa ina sonka ba? Idan ba haka ba ya kamata a ce na warkar da ko wace irin cuta da ke ranka" cewar Amna tana kallonsa, wani ƙarin murmushin yayi wanda a yanzu Amna ta mara masa baya, "idan na warke da ciwon soyayyarki, hakan na nuna zan iya mantawa da ke wani lokaci, amma idan yana nan, kema kina raina har abada" ya faɗi yana jin tamkar ya zuba ruwa a ƙasa ya afka a baki, ko kuma ya tashi ya hau rawa da tsalle har sai ya faɗi, abin da ya jima yana so yau ya samu.
"Aahh ba shakka! Ashe kai ka warware mu muna can muna kwaranyar da hawayenmu akan ka?" Cewar Hajiya cikin buhun takaici da ɗarin haushi, akan Amna da ta gani, ƙarasowa tayi tana bin Amnan da kallon tsana, har ji ta ke kamar ta kamo wuyarta, tayi walagigi da shi makamancin yadda Amnan tayi mata rannan, sauran ne suka biyo bayan Hajiya, banda Shuraim da tun da ya fita barin wurin yayi m'a gaba ɗaya.
"My son ya warke masha Allah!" Cewar Dady cikin farin ciki da ganin ɗan na sa cikin ɗan warwarewa duk da cewa ba wai sosai ba ne, domin idon na sa har yanzu wani kala suke kamar wani wanda yayi shaye-shaye, Hajiya ce ta zo kusa da Amna ta ce, "to karere sai a bamu guri mu zauna ai ko? Tun da dai uwa ta fi gaban komai akan ɗanta" ta faɗi cikin haushi da ya mantar da ita kwakwar da ta fasa à baya, saboda yau Safna ta ƙona mata rai kamar wuta, miƙewa Amna tayi ba musu, ko ba komai ai gaskiya Hajiyar ta faɗa, dama uwa ce kan gaba, kuma masoyiya ga ɗanta.
Ganin tabbas ƙanin na sa jiki ya yi sauƙi, hakan yasa Marwan fara yin magana yana cewa, "to Dady tun da ya samu sauƙi ai shikenan, ya kamata mu koma gida a ci gaba da hidimar bikin da ake, saboda yanzu magriba ya kusa, kuma bayan sallar ne za a kai min amaryata" ya faɗi domin a kan Yazeed kawai ba zai hana shi angwancewa yau ba, duk da cewa ya ɗan tausaya masa kaɗan, amma yaji haushinsa da yayi sanadiyyar rugujewar wasu budget da yayi.
Dady ji yayi kamar an hankaɗo masa abin da yasa shi ɓacin rai ɗazu, zumbur ya miƙe daga kan mazaunin da ya ke, abin da ya faru awanni baya na dawo masa, maganar da mai ɗaurin auren ya faɗi bayan an ɗaura auren Marwan da kuma amaryarsa Sumee, kwatsam Dady ya ji abin da ko kusa ko tsammani ko tunani, ko kokwanto bai kawo masa ba, wato ji da yayi an ɗaura auren 'yar autarsa da wani wanda yaji sunan na sa kamar wani kafuri wai Jaiz, 'yarsa da yake da burin rayuwarta ya kasance tamkar sarauniya a gidan aurenta.
Bayan jin wannan kalmar da yayi sai da ya tsaya ƙam kamar wanda ya haɗiye taɓarya, domin tun bayan zuwan su ya ji ana za'a yi ɗaurin aure guda biyu, amma sai yayi tunanin ƙila ko akwai wani ɗaurin auren daban bayan na ɗansa, sai dai yanzu ji yayi kamar ba a tsaye ma yake ba, Marwan ne ya sake tambaya kan cewa ko dai sunyi kuskure ne, ƙila sun manta ne suka sanya Ruƙayya Jamilu a maimakon sunan baban yarinyar, amma aka sanar da su cewa ba kuskure ba ne, sunan ma'auratan kenan.
Sai à lokacin wasu daga cikin mutane da suka yi ikirarin su ne dangin Jaiz, suka zo suna gaishe da Dady da yi wa kansu duka barka da arziƙi Allah ya ba zuri'ar ta su zaman lafiya, can sai ga Jaiz cikin baƙar jomfa, wanda bai yi masa kyau ko kaɗan ba, sai ua fito kamar wata ƙabilar ba musulmi ba, ya zo in da Dady yake harda duƙar da kai kamar mutum mai kamala, sannan ya fara gaishe sa da gabatar da kansa cewa shine Jaiz, wato angon 'yarsa, wani irin cakuma Dady ya masa, kafin Dady ya sake yin wata yunƙuri Jaiz ya fara cewa, "Dady ni da yarinyarka muna son junanmu sosai, shiyasa muka amince da aure à tsakaninmu, kar ka damu domin komai da ya faru da saninta akayi ita da mahaifiyarta, ba wai kuskur.." kafin Jaiz ya kai ƙarshen magana Dady ya ɗauke fiskarsa da lafiyayyar mari.
"Kai ka isa!? Waye kai da zaka auran min 'ya ba tare da izini n'a ba!?" Dafe da kumatu Jaiz ke kallon Dady, ganin Dady ya shiga cikin ruɗani da kuma hasala ne yasa Shuraim dafa Dady tare da bashi haƙuri, akan ya bar maganar sai sun koma gida, ayi komai cikin nutsuwa kada ayi abun da za zama dana sani, a fisace Dady ya nufi inda motar su ya ke, don ya koma gida ya ji cewa maganar wannan Jaiz ɗin, n'a cewa suna ƙaunar junansu shi da Ruki, da kuma wai harda su Hajiya aka haɗa komai ƙarya ne?.
Kallonsu Hajiya da Ruki Dady yake yi kamar mai bitan kallo, fiskarsa ɗauke da tambayoyi bila adadin da yake son gabatar musu, zuciyar Hajiya ce ta razana, duk da cewa sun riga da sun shirya abin da zasu yi, Ruki kuwa ko ajikinta, kawai lokaci take jira su fara baza acting ita da Hajiya. Amna kuwa tunani take yi, wai shi Marwan wani irin ɗan uwa ne? Ace ɗan uwansa n'a asibiti amma yana maganar wani ɗauko amarya? Duk da cewa ƙanin na sa ya ɗan farfaɗo amma ya kamata a ce ya haƙura ko na yau ne ai.
"Waye Jaiz? Sannan kuma me dalilinku na shirya aure ba tare da sanina a matsayi na na uba ba?" Dady ya jefa musu tambayar tare da zama yana maida hankalinsa kan Hajiya da ke zaune kan kujera, da kuma Ruki da ke gefen gadon Yazeed zaune, cikin rashin fahimta Yazeed ya nemo muryarsa sannan ya ce, "Dady kamarya? Wani ɗaurin aure? Ina ce na Marwan kuka je?" Saleem da dama ya san komai shi da Marwan sai ba suyi mamakin maganar Dadyn ba, sai da Dady ya numfasa sannan ya labarta wa Yazeed komai da ya faru.
Bayan Dady ya gama yin maganar Amna da Yazeed suka zaro ido jin abin da Dady ya labarta musu, kamar abin da ya faru a labarin tatsuniyoyi, cigaba da magana Dady yayi yana kallon su Hajiya, magana yake yi cikin masifa, "ina tambayarku kunyi shiru, saboda baku ɗauki aure da daraja ba, baku ɗauki aure wani abun alfahari ba, akan me zaku aikata wannan al'amari ta wata bahaguwar hanya? Ina uba ga 'yata amma wai ji kawai nayi an ɗaura mata aure, ba tare da na san labari ko kuma wani magana a kai ba!, saboda gani an maida ni uba hotiho ko?".
Kuka Ruki ta fashe da shi kamar mai jira, cikin muryar kukan da ta ke yi tana cewa, "Dady ka ya fe min, na san mun tafka babban kuskure da muka aikata komai ba tare da sanin ka ba, amma ba wai munyi hakan don cin zarafinka ba ne, ko kuma mu nuna maka baka isa ba, na san da ace tuntuni n'a sanar da kai cewa ina da wanda nake so, nasan ko tantama ba nayi zaka aura min duk wanda nake so, sai dai komai ya zo mana ne baga-tatan, na san cewa idan har na sanar da kai ina son ayi min aure rana ɗaya da Marwan baza ka taɓa yarda ba, sanna kuma idan har na wuce wannan kwanakin zan rasa Jaiz, rashi na har abada Dady, ni kuma rasa Jaiz tamkar tsayuwar numfashi n'a ne, ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba, da ace na rasa wannan damar wato n'a zama matar Jaiz Dady! Da tabbas labarin soyayyarmu zai zama makamancen labarin soyayyar Lalila da kuma Majnun, sai dai mu rasa rayuwar mu lokaci ɗaya zamuyi, saɓanin Laila da aka aurar da ita ga wani namiji, sai dai ni lokaci ɗaya zan gangara mutuwata".
Last part.
___________________________________________________
Anan zamu tsaya 'yan uwa, shin ya kuke gani, wannan ƙaryar da su Hajiya suka haɗa zai yi tasiri a kan Dady ko kuwa? Ya maganar Amna da Yazeed? Da kuma Shuraim?
Me zai afku gaba?
Alƙamin✍🏼 {Mrs Umar} [Gimbiyar Fasaha]👸🏽
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣3️⃣1️⃣▶️1️⃣3️⃣2️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Tana gama wannan maganar ta kuma fashewa da kuka cikin makirci, ɗauke da damuwa da tausayawa Dady ya sanya hannunsa duka biyu ya taso da ita ganin tana shirin durƙushewa a ƙasa, Amna, Yazeed, Saleem, da Marwan sai kallon mamaki suke wa Ruki, gaba ɗayan suka saki baki, ganin ikirarin soyayyar da take har da kwatanta Laila da kuma Majnun, Hajiya kuwa ganin kamar fiskar Dady ya fara amsan wasan kwai-kwayon da Ruki ta ke yi ne, yasa itama ta ga ya kamata ta haɗa da na ta domin ƙarawa igiyar kauri, wato abun ya ƙara armashi.
Miƙewa tayi tana jan gelenta kamar mai share hawaye ta fara cewa, "Alhaji nima da fari ƙin yarda da maganarta ta nayi, sai dai bayan furucin da tayi min na cewa zata kashe kanta, idan har ba a aura mata wannan bawan Allahn mai kirki ba, hakan yasa ni kuma na tsorata, bisa ga yunƙurin da tayi bila adadin don ciki maganar da ta yi, sau biyu ina taro ta tana nufan bene don ta hau ta kuma faɗo, wai don na ce baza ta aureshi ba, hakan yasa na ji zuciyata ta bada ƙaras alamar karaya, shiyasa na bada gudunmawa don aiwatar da komai, gudun kada n'a rasa 'yar Autana, ita kaɗai ce mace a cikin ƴaƴana, gashi nasan haihuwa ya tsaya min, bare inyi runanin zan samu wacche zata maye min gurbinta, sannan ina tsoron ta sake biyowa ta wani fannin domin kashe kanta, kasan yaran zamani babu abin da baza su yi ba, shiyasa Alhaji, na so sanar da kai amma ban samu dama ba, kuma ina ganin kamar zaka tashi hankalinka sosai"
Hajiya ta ƙarashe maganar tare da sake share hawaye da gele, cikin wani munafurcin Ruki ta kuma cewa, "kuma har yanzu idan aka hana ni zama a gidansa sai na kashe kaina wallahi! Don Allah Dady ka ceci raina ka barni da Jaiz", sannan ta sake sakar wani kukan mai fitowa kamar muryar shaƙiyyiyar amarya, mai kuka kamar ƙarar mage. Yazeed ya tausayawa ƙanwar ta sa sosai, domin idan har gaskiya ta faɗi, to ba shakka so ya wuce hakan ma, domin shima ya ɗan-ɗana, duk da baya jin zai kashe kansa kamar yadda ita ta ce ɗin, amma alhamdulillah ma yanzu ya samu waraka, tun da ya samu abin da yake so daga Safna, don haka shima ba zai bari a sa lokacin da nisa ba zai wufce Safnarsa, suyi rayuwa cikin farin ciki.
Hajiya da Ruki babu abin da suke jira face suji amsar da Alhaji zai bada, duk da cewa sunga alamar amincewa a tare da shi. Dady kuwa yadda 'yarsa take ta faman kuka ba ƙaramin taɓa zuciyarsa yayi ba, duk da cewa ba hakan ya so ba, duk burin da ya ci a kan Ruki ta auri Shuraim domin cikar muradinsa, amma sai gashi komai ya rushe masa, da har ya fara sa rai da Hajiya ta taɓace masa ai ya kwantar da hankalinsa komai ya kusa zama dai dai, ashe dai ƙaryace, ko da ya ke haka Allah ya nufa, "Dad yarinyar nan fa tana da gaskiya, kawai à rabu da ita tun da komai ya riga da ya faru, an riga an ɗaura aure, tun da ita ta ce ta ji ta gani, nima har na ji haushi wallahi, ina ma ace na samu wata kyakykyawa an ɗaura mana aure da ita yau" cewar Saleem yana jin takaici a ransa, domin shima ya ci ace ya lula daga ciki.
"Rufa min baki, Ana magana ta hankali kana kawo wani shirme" cewar Dady yana mayar da kallonsa inda Rukin ta ke, sai ƙara sautin kuka take yi kamar da gaske, ajiyar zuciya na rashin mada fa Dady yayi, sannan ya fara yin magana cikin rarrashi da cewa, "shikenan ki dai na kuka autana, tun da kin faɗi kina sonsa shi Jaiz ɗin, to nima na amince, Allah ya sanya albarka a aurenku" ya faɗi ba tare da jin daɗi ba, sai dai tun da 'yar ta sa ta ce tana son yaron, to shi bai da ta cewa sai ya bata ƙwarin guiwa, ya kuma sanya mata albarka, ba ya jin zai hana 'yarsa Ruki wani abu idan ta nema, da ace tayi masa magana m'a da ya shirya mata komai na musamman.
Cike da farin ciki da jin daɗi Ruki da Hajiya suka fara washe baki, sai murna suke, murmushi Yazeed ya saki, Amna kuwa mamaki ne ya cika ta, taya Dady zai yarda da wannan maganar lokaci ɗaya haka? Shi ne fa uba, ya kamata a ce a ƙalla ya gudanar da bincike akan shi angon kafin aikata komai, amma sai gashi ya amince da 'yarsa, lallai hakan ya nuna yana son yaransa, so wanda uba ko uwa ke barin yaransu suke abin da suke so, kenan hakan ne yasa yaran suka zama sangartattu?.
Marwan ne ya buɗe ba ki yanzu ya ce, "to shikenan Dady sai mu koma gida yanzu ai" duk yadda Dady yayi da Marwan akan ya bari sai gobe su cigaba da hidimar bikin, amma Marwan ya ƙeƙashe ƙasa ya ce shifa bai san da labarin ba, babu abin da zai hana shi ƙarasa abin da ya fara yau, ai ko da Yazeed ɗin abin da zai yi kenan, Yazeed da maganin bacci ya ƙara sauya idanuwansa, har yake jin magana-ganun Marwan kamar à saman kansa, amma duk da haka ya ji haushin abin da Marwan ɗin ya faɗi, ko da yake dama ba abin mamaki ba ne.
Matsawa kusa da Hajiya Ruki tayi tana sanar da ita cewa, gwara ta sa baki Dady ya amince da komawa gida yau, don itama à samu à kaita na ta gidan, domin bata san kyautar da Jaiz zai yi mata a ranar farko a gidan sa ba, ya sanar da ita zai yi mata kyauta mai gigita tunani, ta faɗi wa Hajiya, domin kuwa ita ba zata so hakan ba, domin itama ya kamata a ce ta kwana a ɗakin da yake da suna n'a ta na har abada, kuma ta san ɗakin sai ya fi na gidan na su kyau sau ɗari
Ai da jin haka Hajiya ta fara taro Alhaji tun kan yayi ni sa, babu ɓata lokaci Dady ya amince, bayan doctor ya kuma yi wa Yazeed bincike tare da ba sa magun-guna, gaba ɗayansu suka kuɗunzuma komawa gida, duk da cewa kusan Isha'i suka koma gida, amma hakan bai hana komai kasancewa ba, suna isa Ruki ta fara shiri, domin ana gab zuwa ɗaukarta ita ma zuwa gidan Jaiz. Shi kuwa Marwan tuni an tafi ɗauko masa tasa Tauraruwar Sumee. Yazeed kuwa dama suna dawowa gida ya faɗa a gado, domin yadda bacci yake ɗibansa har baya gani.
Haka dai aka zo a ka ɗauki amarya Ruki a ka tafi da ita, ko wannan kukan na amare babu ita da Hajiya, sai cikin murna da ɗauki akan arziƙin da zasu kwasa, yadda kasan wasu talakawa tukuf da suke neman mafita ko ta yaya, shi kuwa Marwan aka kai masa amaryarsa gidan da Dady ya siya masa mai kyau da yake can wani unguwa.
Shuraim, tun bayan ya bar wannan ɗakin cike da ɓacin rai, wayarsa yayi ƙara, sai da ya bar asibitn sannan ya ɗaga wayar, ko da yaji akan wani bincike da suke yi ne, hakan yasa ya bar asibitin gaba ɗaya, don zuwa inda aka kira san.
Amna tun bayan da suka dawo gida bata ga gilmawar Shuraim ba, haka kawai sai ta ji ta damu, ita bata je kai Ruki ba bare ta je gidan Marwan. Tsaye ta ke a saman bene tana hango falo, a hankali ta ɗaura hannunta akan ƙarfe tana kallon ƙasan wato falo, ɗago wayarta tayi tana jin kamar ta kira Shuraim ta ji lafiya yake? Amma kuma ta kasa, domin abin da ya faru a tsakaninsu, sai kuma ta daure ta fara neman numbern na sa haɗi da saukowa daga upstair.
Kafin ta kai ga kiran numbern ta ga ya shigo, wani ajiyar zuciya ta sauke, aninsa babu abin da ya samesa, ganin yana neman juyo da idonsa inda take ne, yasa ta yin kamar bata ganshi ba, ta juya ta haye sama, da kallo ya bita da kuma mamakinta, domin yasan tabbas ta ganshi.
WASHE GARI.
Fitowa Amna tayi domin yau a kwai meeting ɗin da zata gabatar, hakan yasa ta shirya ta fito cikin shirin zuwa aiki, Shuraim ne biye da ita yana magana amma ko juyowa taƙi tayi masa, binta ya ke yana kiran sunanta amma kamar ko a jikinta, shigewa mota tayi tana wa driver da ke tsaye gefen motar magana akan ya shiga ya ja ta su tafi, kanta na kan jakar da ke hannunta kawai taji anyiwa motar key, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya glass don ta ga Shuraim ɗin da ke binta, amma me zata gani, driver ne ta gani tsaye ba Shuraim ba.
Goge idonta tayi wai ko dai gizo ne kawai, amma tabbas ba Shuraim ɗin ba ne, da sauri ta juyo don ta ga waye yake tuƙa ta to? Daidai fitarsu daga gidan, kafin tayi magana Shuraim ya ce, "Madam C.E.O ni ne fa ba wani ba, ni ne dai Shuraim masoyinki" haɗe fiska tayi tana cewa, "to me ruwanka da shiga motar nan? Ka shiga ta ka mana, ana dole ne?" "Ko ma dai me ni dai na shiga, kuma ba zan fita ba, ni zan kai sarauniyata gurin aiki da kaina, kuma ma ai dacewa yayi a bani haƙuri akan abubuwan da aka min, na rashin kyautawa, saboda anyi min abin da ba a san hakan zai iya haukatar da ni ba, to amma tun da akayi sa'a na kasance lafiya, ba sai a taushi zuciyata ba? Amma me makon hakan sai ana kuma min abun da ke sosa min rai kuma".
Saboda haushi ma bata iya tanka masa ba, me makon ya ce yanzu ya amince da sanarwa Yazeed gaskiya, amma wani magana daban yake faɗi, Shuraim bai ƙara yi mata magana ba ganin kamar ita ba son hakan take ba, amma cikin ransa sai tunanin abin da ya kamata yayi don ya ja ta da hira ya ke, saboda ba zai juri zama haka a tsakaninsu ba, haka har suka yi ni sa babu wanda ya ce uffan.
Wani tsoho ne ke tafe à kan hanya, saboda tsufan da yayi masa yawa har baya iya tafiya a miƙe, sai dogara sandarsa ya ke, da kuma wani ƙullalen buhu mai kaya à hannunsa, ya rataya a bayansa. Can gaba kuma, wasu matasa ne ke wasa a gefen hanya, da ka gansu ba mutanen arziƙi ba ne, domin yadda shigarsu ya ke da kuma askin da yake à kansu, dama duk wani mutum na gari, shigarsa ne abin da mutane ke fara gani, daga nan ne zasu zama masu yi masa kyakykyawa ko mummunan zato.
Abun da suke yi ne su ke ta ƙara himma a kai, wasan faɗa su keyi da kuma tsalle kamar sune kaɗai da filin, kamar ba su san akwai wa'yan da ke wucewa a hanyar ba, duk wanda ya zo wucewa ya gansu sai ya tsallake titi ya koma ɗayan gefen, amma Baba tsoho shi bai m'a yi tunanin hakan ba, domin kansa na kan hanyar da yake takawa, saboda kansa ba wai a ɗage yake ba, bai m'a san abin da wa'yan nan samarin suke ba, sai dai iyaka jin surutunsu da ya ke.
Suna cikin wannan wasan, suna gaba suna baya kawai mutane biyu daga cikin su, suka hankaɗa tsohon kusan a tare, faɗi yayi ƙasa saura kaɗan ya afka cikin lambatun da yake gefen hanyar, buhunsa ya faɗi gefe, haka sandarsa ma, "wai Allah na" cewar Tsohon, domin yadda ya ji zafin faɗin sosai, juyowa su kayi suna kallonsa tare da kwashewa da dariya, kamar ba zai iya tashi ba, bisa yadda yake yin komai a hankali, saboda jikin tsufa da kuma zafin buguwan da yayi akan faɗin.
"Haba yarana, yanzu kun kyauta kenan da kuka tureni? Amma kuma kuke dariya? Kun kyauta kenan?" tsohon ya faɗi cikin muryar da ke fita a hankali, bayan miƙe yana ƙoƙarin ɗago buhu da sandarsa, haɗi da ƙoƙarin maida buhun zuwa ƙafaɗarsa kamar yadda yake ɗazu, sai da suka dara domin basu ɗauki abin da su kayi da laifi ba, ɗaya daga cikinsu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 56