Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zata yi ta kuma fasawa, akan me ya ke yi mata dariya? Kenan ba ya jin kunyar, tsagaita dariyar ya yi da cewa, "madam C.E.O kenan, to ke ba kya jin kunyar tafiya babu mayafi ne? Ina ce ba ni na cire rigar ba?" Taɓa kanta ta yi don tabbatar da gaskiya fa ya ke, "kar ki damu" ya faɗi yana zagayawa zuwa bayan mota, buɗewa ya yi ya fito da wani riga wanda ya ke akwai t-shirt à ciki da kuma na sama, cire na saman ya yi ya sanya, sannan ya taho gabanta, rintse ido ta yi ganin yana shirin zuwa gabanta, sai da ya saki murmushi mai sauti sannan ya ce, "yammata kar ki damu, zaki iya buɗe idonki yanzu" ido ɗaya ta fara buɗewa, ganin ya suturta ne ya sa ta buɗe ɗayan ma. Shuraim ya miƙa mata rigar ciki mai laushi ya ce, "ga wannan ki rufe gashinki" da mamaki ta kalli rigar ta ce, "duk a ina ka sami wa'yannan?" "Zaki saka ne ko kuwa za ki tsaya tambaya?" Hannu ta sa ta ansa, sai da ta yage shi da ƙarfinta tukunna ta yafa kamar mayafi, "to muje ko? Ya kamata mu koma don mu tsarkake jikinmu muyi ibadar da muka rasa". Kallon hanya suke gaba ɗayansu suna sauke numfashi, a hankali kuma Amna ta fara magana kamar mai shirin kuka, "Shuraim kana ganin Babana ya mutu?" Juyowa ya yi cikin tausayawa yana kallonta, cikin rarrashi ya ce, "ki kwantar da hankalinki, tun da har ki ka ji wannan matsafin ya faɗi cewa bai mutu ba yana hannun Zabba-ba, to ina da tabbacin haka ne" yana faɗi ya maida kallonsa ga tuƙin da yake, a razane kamar ta ji abun tsoro ta juyo tana kallonsa. "Idan da gaske ne, kenan gobe shugaban ƙungiyar Pospa zai gudanar da shirinsa kan Baba!? Zai kashe shi?" Shima Shuraim sai a lokacin ya ankara da wasu daga cikin maganganun da matsafin ya yi, "ya ce gobe Zabba-ba zai yi amfani da ruwan iko, kenan zan rasa shi?" Amna ta faɗi hawaye masu zafi na sauko mata, sai da ya danne zafin da gefen wuyar nan na sa ke masa sannan cikin tausayawa da jin raɗaɗin hawayenta ya ce, "ki daina zubar da hawayen nan, bana jin daɗinsu, na yi miki alƙawari muna komawa zan fara bincike akan inda ya ke, kuma insha Allah babu abin da zai same shi, ki daina kuka please". Kallonsa ta yi ta sauke ajiyar zuciya, domin wannan maganar na sa ya faranta ranta, ya sanya jin sanyi da ga tsoron da ke ranta, ta ce, "ina zoben nan ya ke?" Ya ma manta da ya zuba zoben a ljuhunsa tun fitowarsu. Zaro ido suka yi bayan ya fito da zoben riƙe à hannusa, ba shiri Shuraim ya tsaida motar, mamaki ne ya cika su da kuma wani tsoro, domin ganin zoben haske ya dawo duhu, wannan farin diamond ɗin ya zama baƙi ƙirin abin sa, har ya ma fara farfashewa, kafin su yi magana suka ga ya cigaba da murmushewa, yana dawowa kamar ƙasa, tsoro na cigaba da wanzuwa cikin zuciyarsu, suka ga zoben nan ya dawo kamar ƙasa shima, ya zama saura ƙarfen kawai. Haɗa ido da junansu suka yi, sannan suka sauke numfashi, "ina ganin amfaninsa ya ƙare ne" cewar Shuraim, Amna ta ce, "amma ni na yi mamakin wannan zoben sosai, kenan ba ƙaramin abu wannan tsohon ya ba mu ba, kuma wannan matsafin sai ambatan zoben haske ya ke, amma da ba don wannan zoben ba da Allah kaɗai ya san abin da zai faru" "wannan haka ya ke, to amma ina da kokwanto akan wannan tsohon, sannan akwai maganar da ban fahimta ba cikin maganar wannan matsafin" Shuraim ya faɗi yana tuna lokacin da matsafi ke cewa, "tun baya, ni ne, na hana à kashe ki ke Amna, ni ni na hana, eh hakane". Sauke numfashi dukkansu suka yi a karo na sosai, domin ba su da amsoshin tambayarsu yanzu, tun da dai matsafi ya riga da ya tafi, idan suka tuno da abubuwan da ya faru sai suga kamar almara. Shuraim ya tada mota suka cigaba da tafiya. COMPANY. YAZEED. "Ke wai me haka? Akan me zan zauna tun ɗazu kina sanar da ni wani shirme? Kin hana ni shiga cikin office ɗin nan, sai wasu zantuka kike hankaɗo min" Yazeed da ke tsaye kan Raheena ya ke wannan masifar, don da ba don ya san tsakaninta da Safna ba, da wani batun ake daban, saboda ya shafe awanni a wurin yana son ganin Safna amma Raheena sai yi masa inda-inda take, ta hana shi shiga, sai ta shiga office ɗin Safna ta fito ta kuma yi masa wata ƙaryar, gashi magriba n'a ƙaratowa, __ko da ya fito da safe aka sanar da shi cewa Amna ta riga ta tafi company, tun lokacin yaso ya bita, amma Dady ya hana shi, saboda kasancewar jikinsa bai gama warwarewa ba, sannan ga kansa da ke ɗaure da bandeji, kan ciwo yake yi masa har yanzu, da ƙyar ya yarda ya fasa binta, amma koda ya ɗauki numbernta à wayan Dady ya yi ta gwada kira amma baya shiga, ya shiga damuwa sosai, har ya gwada kira da wayar Dadyn m'a shiru numbern baya shiga, nan hakalinsa ya tashi sosai, hakan yasa ya kuma tashi yana ƙoƙarin tafiya company don ya duba lafiya Safna ta ke kuwa?, Hajiya ta kuma jan shi ta hana shi, ta ce wai "to me zai cinye Safnar? Ai ta riga da ta mallaki hankalin kanta, yarinyar da take jagorantar kamfani babba haka" sai daga ƙarshe ne ya fita a ɓoye ba tare da ya bari su Hajiyar sun gansa ba, shine fa ya zo kuma sai ga shi bai ganewa Raheena ba__ Hannunsa yasa à saman kansa da ke ɗaure da bandeji, yana ɗan masa zugi sanadiyyar maganar da yake da ƙara, amma duk da haka ya kuma ɗaga murya ya ce, "ke ya ishe ni! Ni da kaina zan shiga office ɗin yanzu, n'a gaji da maganganu marasa ma'ana da kike faɗa min! Me ma yasa na tsaya tura ki neman izinin shiga?" Yana faɗa ya nufi office ɗin Amna, da sauri Raheena ta miƙe zuciyarta na bugun fargaba, yanzu idan Yazeed ya shiga kuma bai ga Amna ba kuma fa? Shikenan ta san ba zai barta ba, saboda ta yi tayi masa ƙarya, to kuma gashi Amna ta ce mata bata son kowa ya san bata nan, kallonsa ta ke har ya buɗe ƙofar ya shiga da sallama. Yazeed yana shiga ya fara ambatan sunanta, amma bai ganta à kan teburin kamar yadda Raheena ta sanar da shi cewa, tana tura wani abu mai mahimmanci ne a computer tana aiki, kuma idan har ta tashi komai zai dawo mata baya, sannan kuma idan ana yi mata magana ana sata yin kuskure. Fiskar Yazeed cike da tambaya yana kiran sunan Safna, amma shiru, da sauri ya fice daga office ɗin yana komawa gun Raheena. Yana isa inda Raheena take ya fara cewa, "kin ce tana office amma banganta ba, me ki ke ɓoyewa ne? Ban yarda da maganganun da ki ke yi min ba, idan na gane kina ɓoye wani abu to zaki gamu da fushina!" Zuciyar Raheena babu abin da ta ke yi sai harbawan fargaba, da ƙyar ta samu ta saki murmushi tana cewa, "da gaske nake yaya Yazeed, tana ciki, ina ga ko ta gaji da takura mata da nake yi na zuwa ne yasa ta shiga ɗakin hutawa" ta kira shi da sunan yaya ne saboda haka itama Safna ke ce masa. Juyowa ya yi yana mata wani kallo na rashin yarda, sannan ya juya ya kuma nufan ƙofar office ɗin, da sauri Raheena ta bar inda take ta nufo sa haɗi da shan gabansa, kallonta ya ke yi cikin ɓacin rai da tunanin me yasa take yin hakan ne? Wai to ko bata sanarwa Safna cewa shi ne yazo ba, ya san dai Safna ba za ta yi masa wulaƙanci ba, idan har aka ce shine ya ke son ganinta, ko da babu soyayya a stakaninsu, bare yadda yanzu komai ya ke da dama. Yazeed ya ce, "ke me haka? Wai ko dai baki sanar da Safnan ni ne na zo ba?" Shiru Raheena ta yi tana haɗiye nyawun rashin gaskiya, da tunanin amsar da zata bashi, kar ta ce Amna ba ta san da zuwanshi ta haifar da matsala, ya ga cewa Safna ta wulaƙanta shi, kada kuma ta ce masa bata faɗa wa Amna ba ya ce ta raina shi. Kallon sa take shi kuma ya kuma jefa mata tambayar, haɗi da ƙureta da ido, wanda yasa da sauri ta sauke na ta idon ƙasa. "Yazeed!" Da sauri ya ɗaga idonsa don ganin wacche ta ambaci sunansa, wanda ya ke ji da zai yu ta dawwama tana furta sunan daga bakinta, itama Raheenar firgigit ta juya tana kallon gurin ƙofar office da jin muryar da ta kira Yazeed, murmushi Amna ta sakar musu duka biyu tana yowa inda suke sanye da kaya daban, wata ƙaƙƙarfan numfashin na tsira Raheena ta sauke, sannan ta saki murmushin na gode Allah, Yazeed kam dama tuni fiskarsa yake ta bayyanar da murmushi cike da jin daɗi. Isowa gabansu Amna ta yi tana kallonsu sai ta furta "lafiya?" Domin yadda ta ga Yazeed ɗin n'a kallon Raheena ɗazu, "ba komai, dama ce masa na ke ƙila kin koma cikin ɗakin hutu don ki ƙarasa aikin computern da ki ke, domin ba kya son takura kar ki yi kuskure" Raheena ta yi saurin faɗin haka haɗi da yin alama da ido, don ta nunawa Amna ƙarya ta yi masa, Amna ta gane hakan yasa ta ɗage kai, suka sanya Yazeed cikin duhu ba tare da ya sani ba, Yazeed ya ce da Amna, "wai ko bata sanar da ke nine na zo ba?". Sai da Amna ta kalli Raheena sannan ta saki murmushin iya kan baki ta ce, "eh da zata faɗa min, sai na dakatar da ita, na ce ta tafi in ba haka ba za'a samu matsala, a aikin da nake ɗin, amma ai da na san kai ne ka zo da na taso, ko da kuwa zanyi asarar abin da nake ɗin ne" washe baki Yazeed ya ƙara yi cikin farin ciki da abun da ta ce, ya kuma cewa, "ba komai na gane yanzu, to mu koma gida ko? Lokacin tashi ya wuce, mutanen companyn ma wasu sun tafi, saura kaɗan à kira sallan magriba" da toh ta amsa masa sannan ta ce da Raheena su tafi. Barin wurinsu Raheenar ta yi, ita kuma Amna ta juya office don ɗauko jakarta, tana fitowa suka fita Raheena ma ta shige na ta motar da driver ya zo ɗaukarta, Amna da Yazeed kuma suka shige daban. Lokacin fitar na su Amna ta ga Shuraim na ƙoƙarin shigewa da mota cikin kamfanin, shima ya canza kaya, yanayi ta ji zuciyarta ya yi, domin ta san zuwa yayi don ya ɗauketa su ta fi, ta haɗa ido da shi, amma da kallo kawai ya bita fiska babu murmushi, kuma ta san ba komai ba ne yasa shi ba sai ganinta da Yazeed. Yazeed kam bai m'a gansa ba, hanakalinsa n'a kan tuƙa mota, jingina kai kan kujera ta yi cikin damuwa ta furta, "ko ya yake jin ciwon na sa yanzu?" Ta faɗi tana tunanin Shuraim, Yazeed kuwa jin maganarta yasa ya juyo ya dubeta ya ce, "what did you say?" Da sauri ta ɗaga kanta dake jikin kujere jin maganar da ta zata à zuciya ta faɗa ya fito fili, ta ce, "am oh wai abin da na ce? Ai dama cewa na yi ko ya kake ji a wurin ciwonka da ke kai, ina fatan ya daina damunka ko?". Murmushi mai sauti Yazeed ya yi jin Safnarsa ta damu da shi, sannan ya ce, "dont worry my Queen, babu abin da ya ke damuna yanzu, sai dai ke na lura kamar fiskarki ya canza, lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau kawai gajiyan ayyuka ne, saboda yanzu aikin n'a yi min yawa" Yazeed ya ce, "ohh dear sorry, zan rinƙa taimaka miki daga yanzu kin ji?" murmushi kawai ta yi masa haɗi da mayar da bayanta jikin kujerar tana sake tuna wahalhalin da suka sha ita da Shuraim. Na san zaku yi mamakin yadda ta dawo kwatsam ko? __wani wuri Shuraim ya kaita, inda sauran ma'aikatansa suke, à kwai mata da kuma maza, duk da Amna tayi mamakin inda ya kaita, domin kuwa aiki suke yi tamkar wani office, computoci bila à dadin à wurin, a can suka shirya sannan suka gabatar da sallolin da suka rasa, duk da cewa magriba n'a ƙaratowa, domin da ba don gudun da Shuraim ya rafka à mota ba, da har yanzu suna hanya, suna gamawa à gurguje suka fito don Shuraim ya maida Amna company, dama wannan wurin aikin na sa ba nesa da ƙofar bayan companyn, ko da ta yi masa tambaya bayan sun koma mota, a game da wannan bai bata amsa ba, ya dai ce mata an fara binciken neman inda Zabba-ba ya kai mahaifinta, bayan ya ijjeta sai a lokacin ta tuna da ya za'ayi ta shiga? Amma bayan sun duba suka ga ashe a kwai gurin sa pin ɗin ta baya ma, haka dai ta rinƙa sauri harda gudu-gudu ta iso cikin office ɗinta__ DARE. Amna ce ke ƙoƙarin buɗe idanuwanta à galabaice, jikinta duk ciwuka sun bayyana, faɗawa idonta ya yi kan wani mutum, tana ƙarasa buɗe ido taga ashe matsafin nan ne, juyowa ya yi ya kalleta sannan ya sheƙe da wani razananniyar dariya, haɗi da ɗaga ƙatuwar wuƙar da ke hannunsa sama, a hankali ta kai idonta ƙasa, ai kuwa sai ta ga Baba kwance akan wani ƙatoton teburi baya motsi, cikin tashin hankali ta maida kallonta kan wannan matsafin, aikuwa taga kallonta ya ke cigaba da yi yana dariya, bata gama tantance komai ba, ta ga ya sauke wuƙar da ƙarfi kan Babanta, a gigice ta ce "Baaaabaaaaa!!!!" Last part. ___________________________________________________ Hmm mu kasance da ku a next part insha Allah!! ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣4️⃣5️⃣▶️1️⃣4️⃣6️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 "Aaaaa aaaaa!!" Ta kuma faɗi cikin firgita tana farkawa daga mummunar mafarkin da ta yi, sai sauke numfashi take zuciyarta na bugu da ƙarfi, "A‘ūzu billāhi minash-shaitānir-rajīm wa min sharri hādhihi ru’yā." Ta yi addu'ar tana kallon ɗakin cikin figici, bayan minti biyar ta ɗan samu natsuwa, amma dai barci ya fita daga idonta baki ɗaya, don haka ta tashi ta ɗoro alwala don gabatar da nafila. WASHE GARI. Shuraim ne ya tada mota yana shirin fita wayar da ya canza sabo ya fara ruri, wannan yankan wuƙar da ke gefen wuyarsa an ɗinke masa shi, sannan aka rufe sa da abun asibiti, bai yi mamakin ganin sabon number à wayarsa ba, tun da dama canzawa ya yi, kawai ya ɗaga haɗi da sanyawa à kunnesa, "hello hello, MR kana ji na? Hello" fiddo ido ya yi saboda jin muryar da ke yi masa magana ta waya, baki na rawa ya ce, "Su su Sulaiman?" Daga can gefen ma baki na rawa mutumin ya ce, "eh eh ni ne MR" "Sulaiman dama kana rayé? Ba ance ka mutu ba?" Cewar Shuraim cikin ruɗewa. Sulaiman ya yi saurin cewa, "MR ban mutu ba, ni kaɗai ne na tsira sauran duk an kashe su, ni ɗin ma Allah ne ya nufa ina da tsawon kwana a gaba, ina ta nemanka tun jiya a wancan layinka ban same ka, yanzu ma na samu damar zuwa wurin aikinmu ne Ali ya ban sabon number, amma MR yanzu wani mahimmin magana na ke son sanar da kai, shiyasa tun jiya nake ta nemanka tun kan lokaci ya ƙure", Shuraim da kansa ya ke cikin kullewa, amma sai ya zare key daga jikin motar ya kashe, haɗi da maida hankalinsa kan Sulaiman saboda jin abin da ya ce. __Sulaiman ɗaya ne daga cikin ma'aikatan su Shuraim à baya ne, yana ɗaya daga cikin wa'yan da aka tura leƙen asiri a ƙungiyar Pospa, amma sai dai bayan sun tafi ba daɗewa su Shuraim suka samu labarin Zabba-ba ya kashe su, bayan ya gano abin da suka zo yi a wurinsu, duk da cewa ba wai Zabba-ban da kansa ne ya aikata ba, don baya barin ya bayyana a idon kowa sai wanda ya so, sai dai yanzu idan har ya samu wannan sinadari ya yi aiki to baya buƙatar ɓoyewa. Tun daga lokacin da Shuraim suka ji cewa an kashe musu ma'aikata suka daina tura kowa wannan wurin, to sai ga shi yau kuma Sulaiman ya kira shi ashe shi ya samu tsira__ "Ina ina jinka Sulaiman, wani abu kake son faɗa min?" "Na san inda Zabba-ba ya ke yanzu haka, kuma yana wannan wurin ne don cikar muradinsa akan wata sinadari, na faɗa maka ne ko zaku yi gaggawar dakatar da shi kan ya kammala, saboda na tabbata wannan hatsari ne mai matuƙar gaske" yarfe zufan da ya taho masa ya yi jin maganar da Sulaiman ya faɗi, da hanzari ya ce, "ka tabbata abin da kake faɗa?" Sai da Sulaimanya sauke numfashin zugi sannan ya ce, "ƙwarai na tabbata MR", nan ya sanar da Shuraim sunan wurin da yi masa kwatance. Sulaiman na gama yi wa Shuraim maganar ya sauke wayar daga kunnensa, haɗi da zama kasancewar ciwon da ya ke daɓe a ƙafarsa sai zafi ya ke yi masa, Ali ne ya hau yi masa sannu yana faɗin, "to tun da ka gama sanar da shi ya kamata mu tafi asibiti, domin wannan ciwon na ka ba ƙarami ba ne" ɗaga masa kai ya yi sannan Ali ya fara taimaka masa don ya kaisa asibiti, sai dai kan su kaiga isa ƙofa wasu mutane suka shigo cikin office ɗin. A take suka fara kame duk wanda ya ke cikin wannan office ɗin maza da mata, suna tambayar mutanen nan suwaye su? Me yasa suka zo suke kamasu amma ko ihin basu ce da su ba, saima jibgarsu da suka hau yi kan su fitar da su, à motocinsu da suka yi parking à waje suka jefa ma'aikatan Shuraim haɗi da ɗaura musu bindigu a kai, na cewa idan ba su yi gum da bakinsu ba zasu kashe su, haka suka ja motar suka bar office ɗin babu kowa a ciki. A ɓangaren Shuraim kuwa da sauri ya fito daga cikin motar ƙirjinsa na bugu sosai, komawa ciki ya yi ya nufi ɗakin su Amna, sallama ya yi Amna da ke zaune kan kujera ta amsa da sauri haɗi da miƙewa. Yana shiga ta zuba masa ido jin abin da ya kawo shi, duk da zata so ya zamana magana akan mahaifinta ne, domin kuwa mafarkin jiya har yanzu giftawa ya ke a cikin zuciyarta. "Shuraim ka samu wani bayani ne" ta katse shi tun kafin ya kai ga furta komai, sai da ya matso kusa da ita sannan ya ɗaga mata kai alamar eh, Ammu na kwance kan gado idonta na a kansu, "da gaske!?" Amna ta kuma faɗi cikin ƙaguwa, Shuraim ya ce, "eh dama na zo sanar da ke ne saboda ki kwantar da hankalinki, ni zan tafi yanzu" kafin ya kai ƙofa tasha gabansa tana jin bugu sosai cikin ranta ta ce, "taya zaka ce zaka tafi? Babu inda za ka je kai kaɗai, tare zamu je, Mahaifina ne kuma haƙƙi n'a ne in je in taho da shi, amma kayi haƙuri ba zan iya zama anan ba". Ji ya yi dama bai zo sanar da ita ba, "yau ma taurin kai zaki yi?" "Ka yi haƙuri mu tafi tare, wallahi ko da na zauna ba zan taɓa samun sukuni ba, zuciyata zata yi ta saƙa min abubuwa da dama, please kar ka ha ni yau ma" ta faɗi hawaye na sauka daga kumatunta, ijje numfashi Shuraim ya yi sannan ya dubeta ya ce, "it's ok, kawai dai bana son ki kuma jefa rayuwarki cikin wata matsala ne, amma shikenan zamu iya tafiya" ya faɗi yana shafo wurin ciwon wuyarsa, "sannu kayi haƙuri ban tambaye ka ya wuyanka ba" murmushi ya sakar mata ya ce, "dama ina binki bashi ai" itama murmushin ta yi sannan ta cire murmushin ta kuma cewa, "to mu hanzarta tun kafin su cutar min da Babana, idan hakan ya faru ban san ya zanyi ba" ta faɗi tana matso wasu hawayen. "Ni dai bana son ganin wannan hawayen gaskiya, don haka ki daina ba na so, amma maganar ki hakane, ya kamata muyi gaggawan zuwa, so amma bari in kira uncle Musa tukunna" cewar Shuraim yana ɗaga wayarsa, sai da ta share hawaye sannan ta yi masa tambaya, "waye kuma uncle Musa?" "Abokin Abba Mai-daraja ne, wanda na sanar da ke shi ne ya sanar da ni kashe Mai-daraja aka yi, jiya ma sai da ya yi min faɗa akan ya za'ayi mu doshi kogon da muka san yana da hatsari ba tare sa mun sanar da shi ba, don haka ya kamata na sanar da shi yanzu" jin jina kai Amna ta yi, shi kuma Shuraim ya fara kiran number uncle Musa, sai dai kiran ya yanke ba tare da an ɗaga ba, don haka ya sake gwadawa. Ringing biyu wayar ya yi aka ɗaga, "uncle barka da wannan lokaci, na kira ka ne dama in sanar da kai mun samu adreshin inda Zabba-ba shugaban ƙungiyar Pospa ya ke, don haka yanzu gamu za mu nufi wurin, zan turo maka da adress ɗin wurin na gode" Shuraim na yin maganar ya sauke wayar daga kunnesa, sannan ya juya ya ga Amna har ta yi rolling gelenta tana jiransa, nan suka fice daga cikin ɗakin da sauri. Ammu da ta gama jin duk abubuwan da suke cewa, ta ke zuciyarta ya fara wani irin ƙara, jikinta ya hau kyarma, hannu da ƙafanta ya fara wani motsawa da ƙarfi, bakinta ya fara ƙoƙarin buɗuwa, sannan ko wani gaɓa na jikinta ya fara motsawa, girgiza ta ke yi a wannan gadon sosai, nan bakinta ya fara ƙoƙarin yin magana, lokaci ɗaya ta dakata da wannan girgizan, kallon slim take yi tana zazzare idonta, kamar wasa kanta ya juya gefe, hannunta ya ɗaga, zaro ido ta yi ganin ta ɗaga hannunta, ai kuwa sai ɗayar hannun ma ya ɗagu, nan ma juya kai gurin damanta ta yi ganin shima wannan hannu na ɓangaren ya ɗaga. Hajiya ce ke fitowa daga ɗakinta ita da ƙawarta Ladingo, suna nufar upstair, kawai suka ga Amna da Shuraim sun fito da sauri-sauri suna sauka a upstair, juyowa Ladingo ta yi ta dubi Hajiya, Hajiya ta taɓe baki sannan ta juyo inda Ladingo take. Yazeed da ya kusa zuwa falo ne shima ya ga Amna da Shuraim sun fito, kafin ya gama wani tunani ya ga sun shige motar Shuraim ya ta da, wani irin abu ya ji ya bugi zuciyarsa, da sauri ya nufi ta sa motar ya shiga haɗi da yi wa motar key, "ya ishe ni! Akan me wannan guy ɗin zai rinƙa zamar mini matsala? Tun ɗazu n'a ce da Safna ta zo in kaita company, amma ta ce min yau Jumma'a zata huta, so yanzu kuma me zai fitar da ita kuma da shi? Dole na bisu inga ina zasu je! Sannan dole in yi maganinsa, I'm tired!" Yazeed ya yi maganar wa kansa cikin ɓacin rai. Suna ficewa daga cikin gidan Yazeed ya mara musu baya kafin a rufe gate. Ammu ji ta yi kamar duk ƙarfinta da ta rasa tsawon shekaru yana shirin dawowa jikinta yanzu, gaba ɗaya gaɓɓanta motsi suke yi, hatta jinin jikinta gudunsa ya daidaita, kamar à mafarki Ammu ta tashi ta zauna, bata gama gane da gaske

Chapter 44 of 56