Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar mai shirin barin wurin, domin ya rikice sosai, saboda jin halin da ɗansa yake a ciki, gaba ɗaya sauran ma zuciyarsu cike da fargaba akan abin da doctor ya faɗi. Wucewa kawai Dady yayi don nufar inda doctor ya ke, ya sake yi masa bayani da kyau, don ba zai juri jin mummunar abu ya faru da ɗan na sa ba, shima abokin Dadyn bin bayansa yayi yana basa haƙuri. Amna taimakawa Hajiya tayi ta zaunar da ita a kan kujera daman a tsaye suke tun bayan ganin fitowar doctor, tausayin Hajiya ta fara yi sannan ga Ruki da tuni ta fara rero kuka, Hajiyar m'a hawaye na bidiri a kan fiskarta yanzu, Shuraim kallon Amna ya ke sosai yadda take cikin damuwa dumu-dumu, suma Saleem da Marwan sun shiga damuwa da abin da ya faru ɗan uwan na su. BAYAN AWANNI BIYAR. Wasu zaune wasu tsaye cirko-cirko. Yazeed ya n'a a cikin wannan yanayj bayan awannin da ya ɗauka, à hankali hannunsa ya fara motsawa yayin da zuciyarsa take cigaba da bugawa sosai, nurse ɗin da take ɗakin tana sanya ruwan allura a cikin drip ta ji motsinsa da ƙarfi, domin mugun girgiza da yake yi, da sauri tayi waje tana ambatan doctor, doctor. Cikin tashin hankali su Amna suka bita da kallo, ganin ta fito daga ɗakin da Yazeed ya ke kuma tana kiran sunan doctor, wa'yan da ke zaune ma tuni suka miƙe, jikin su Hajiya sai rawa yake na tsoron abin da ya faru da Yazeed. Da sauri suka nufi ƙofar ɗakin don su shiga, lokacin doctor yazo, basu haƙuri yayi a kan su bari yayi aikinsa, sannan cikin gaggawa ya shige ya bar su tsaye à ƙofa, take Hajiya ta fara sintiri tana safa da marwa, Dady kuma haɗe hannusa yayi guri ɗaya ya matse ƙam, zuciyar na bugawan tashin hankali, sauran ma haka, Amna kuwa komawa gurin zama tayi ta zauna, tare da haɗe hannuwanta tana ɗaurawa a fiskarta cikin rashin nutsuwa, shima Shuraim biyota yayi cikin ta shi damuwar, ganin ta kasa natsuwa ko kaɗan. Ya zauna à gefenta yana kallonta ya ce, "ki kwantar da hankalinki Amna" "Taya kake ganin zan kwantar da hankalina bayan duk ni ce silar kasancewarsa haka?!" Ta faɗi tare da matse ƙwallah hawaye na gangarowa, wani irin shock Shuraim ya ji ya ziyarce shi jin furucinta, da kuma yadda ya fita da ga harshenta, cikin nuna tsqnanin damuwa akan Yazeed, ya ce, "kamar ya ya ke ce silar kasancewarsa haka?" Juyowa tayi tana kallonsa kamar me nazarin tambayarsa, kafin tayi magana suka tsinci maganar doctor yana cewa, "Wacece Safna?". Zunbur Amna ta miƙe tana kallonsu lokacin da doctor ya kuma jefe musu tambayar, "eh wacece Safna? Tana nan ne?" Su Hajiya kallon doctor kawai suke yi cikin tsantsar mamaki, kamar ba su fahimci abin da doctor ya ce ba, Dady ne ya yi saurin cewa, "Safna kuma? Me ya faru?". Amna kuwa da sauri tayo wurin don jin me yasa suke nemanta, shima Shuraim bin bayanta yayi yana zuwa wurin don jin me yasa doctor ya ambaci sunan Safna?. Doctor ya amsawa Dady da cewa, "majinyacin ne ya ke kiran sunanta, kuma kamar nemanta yake," "kamar ya yana nemanta? Me zatai masa?" Cewar Hajiya da ɗagun murya cikin wani yanayi da ta kasa gane na haushi ko na menene? Shuraim kuwa sai da yaji wani irin abu ya bugan masa zuciya, akan me Yazeed zai ne mi Amna? Sai dai kafin wata tunanin ya kuma zuwar masa Amna tayi saurin cewa, "ne ce Amna doctor" ta faɗi tana yin gaba doctor ya buɗe mata ƙofa ta shige, bushewa Shuraim yayi yana kallon abin da yake faruwa, me nufin Amna da cewa ga ta nan? Kuma ta shige?. Hajiya kuwa da sauran cikin takaici suka juya, banda Dady da ya rufe ido yana addu'ar Allah dai yasa ba bu abin da zai sami Yazeed ɗin sa. Bayan Amna ta shiga cikin ɗakin da Yazeed ya ke, tsayawa tayi tana kallon inda ya ke a kwance ba tare da ta ƙarasa ba. Ɗaukar wata paper doctor yayi sannan ya fice waje, ya bar ta a ciki. Har Shuraim ya yunƙura zai shiga, sai doctor ya ce da shi, "a ah ranka ya daɗe, suna buƙatar à bar su su kaɗai" bin doctor da kallo Shuraim yayi kamar ya faɗi wata mummunar magana, shi kuwa doctor juyawa gurin su Dady da suma jiran su ji ya ɗansu ya ke kaɗai su ke yi, doctor ya ce, "har yanzu zuciyar ta sa tana bugu, amma ya ɗan samu hankalinsa kaɗan, na yi mamaki da ya buƙaci yarinyar nan, amma ina fatan hakan ya zame masa sauƙi a zuciyarsa, saboda..." "Dacta ya yaro na yake? Shi nake son ji yanzu" cewar Hajiya cikin hashin da ya cikata maƙil, tana jiran amsar da zai fito daga bakin doctor cikin damuwa, doctor ya amsa mata da cewa, "idan munyi sa'a komai zai zama daidai nan da ɗan lokaci, domin na lura ƙila cutar masoya ce babban matsalar, shiyasa ya nemi da Safna ta je wurinsa ba wani ba" sai da Shuraim yayi saurin juyawa cike da baƙin cikin furucin doctor, "kamar ya ciwon so kuma?" Sake yunƙurawa yayi don shiga doctor ya sake taran sa da cewa, "yi haƙuri ka bari na ɗan lokaci sai ku shiga duka". Dady ma ya ce, "eh ɗana, mu haƙuri kaɗan ka ga muma bamu shiga ba" barin wurin kawai yayi cikin jin haushi da kishi à tare, ba tare da sun fahimci dalilnsa na yin kan ba suka rakashi da ido, Hajiya da dama cikin haushi take ta saki wata tsaki mara sauti, wai ace duk yadda hankalinta yake a tashe akan halin da Yazeed ya ke a ciki, amma wai ace Safna ce ta shiga don ganin lafiyarsa? Wai wannan wace irin masifa ce? Suma sauran su Ruki kowa da haushin da yake ji cikin ransa. Amna. Tafiya take yi kamar mai tsoron ganin abin da take son zuwa gani, bayan ta isa wurinsa ta tsaya tana ƙare masa kallo tausayinsa na sake shiganta, ga farin bandeji da aka zagaye masa kai da shi, har jini ya sake ɓata shi ta gefen kansa, idanuwansa da suka yi masa nauyi kamar ba zai iya buɗe su, a sannu ya buɗe ya ɗaura su cikin idon Amna, gani tayi idon na sa ya rame sosai, kamar wanda ya jima a kwance, ga kumburin da su kayi nai saɓe ba, numfashi yake fitarwa da ƙyar, zuciyarsa na ci gaba da yi masa zafi sosai. Sai da Yazeed ya ɗaga idon nan na sa masu nauyi sama, yana kallon slim kamar mai nemo abin da zai faɗi, sannan ya fara magana cikin sanyin muryar wanda yake cikin jinya, da ƙyar yana cewa, "Safna kiyi haƙuri kinji?" Cikin tausayawa tayi ƙasa da kai ka na ta ɗago ta ce, "me kake cewa? Babu abin da ka min". Dawo da kallonsa gareta yayi sannan ya sqke juriyar cewa, "A ah, ni na san nayi miki laifi, amma ki tausaya min ki soni don Allah, idan ba haka ba ban san halin da zan shiga ba" sai da ta ji gabanta ya faɗi da abin da ya ce, da sauri ta ce, "don Allah Yazeed ka dai na faɗin wannan maganar ka ji?" Yunƙurawa yayi zai tashi, tayi saurin sanya hannunta a ƙafaɗarsa tana komar da shi kan gadon, shi kuma sai da ya ja numfashi sosai, sannan ya ce, "to ki ce kina so na, ki sanar da ni duk mafarki ne, abin da ya faru da ni a baya, ki nuna min, zahiriyyar gaskiyar yanzu kinji?". Ya ƙarashe faɗi hawaye na sake biyo baya, daina kallon fiskarsa tayi, saboda wani yanayi da yake son dawar ma kamar ɗazu, "ka daina magana, kana da buƙatar samun nutsuwa" cewar Amna ba tare da ta dawo da idonta kansa ba, "abin da zaki faɗa min daga bakinki, shine kaɗai abin da zai, sa ni in natsu" ya faɗi yana sake kallonta vikin raunana. "To me kake son in faɗa maka don ka kasance cikin nutsuwa?" faɗin Amna tana kallonsa, ya bata amsa, "ki ce, ina sonka Yazeed!" ya faɗi tare da yin mata alama da fiskarsa cikin roƙo da magiya, ɗauke kanta ta sake yi tana jujjuyawa cikin rashin mafita sannan ta ce, "Yazeed wannan ba abu mai yu..." "kar ki ƙarasa, don Allah kar ki ƙarasa" ya faɗi ta ré da sanya hannunsa kan ƙirjinsa yana sake jin zuciyar na bugawan da ƙarfi, wanda ke son fin na ɗazu bugawa, rintse ido yayi hawaye na sake fitowa babu jira, sannan jikinsa ya fara girgiza makamancin na ɗazu. Cikin tashin hankalin Amna ta fara ambatan sunansa tana faɗin, "Yazeed ka tashi, na shiga uku na" tana faɗi ta fice da gudu itama yanzu tana kiran doctor, a tsorace Hajiya suka sake tashi, doctor da dama ba barin wurin yayi ba ya taho. "magana, kawai dai..." Amna ta kasa ƙarisa saboda tashin hankalin da take a ciki, babu ɓata lokaci doctor ya kuma shigewa ciki, juyowa ta yi tana kallonsu Hajiya amma ta ga bata kalli Shuraim ba. "Ina yake? Ya kamata inyi magana da Shuraim, eh!" Ta yi maganar daga zuciyarta, domin ya kamata tayi gaggawan yin magana da shi, cikin rashin nutsuwa tayi musu tambayar ina Shuraim ya ke? sai dai babu wanda yakula ta, domin kowa yana cikin damuwa sosai, bere ma haushi dama take basu, sai dai tunanin kada wani abun ya biyo baya ne yasa Marwan saurin cewa, "ya fita waje" ba tare da ta yi magana ba da sauri ta juya ta bar wurin, sai zuba sauri take har ƙafarta na harɗewa, bare dama skirt ne ta sa. Duddubasa ta fara yi domin halin da Yazeed ya kuma shiga ba ƙaramin sake razanar da ita yayi ba, me yasa ta kuma sake sa shi cikin damuwa? Shi da a yanzu kulawa ya ke nema. Can ta ga Shuraim na tsaye kansa na kallon sama, kamar mai nazarin gajimare, da hanzari ta isa inda ya ke, Shuraim da ya lula duniyar tunane-tunane ya tsinkayi muryar Amna ta ambaci sunansa, fitar nishi ya biyo baya kamar gudu tayi. Kallonta yake yi, idonsa faɗaɗe da mamaki, "ina son yin magana da kai!" Ta faɗi tana kallonsa fiskarta cike da damuwa, shi kuwa cikin haushin kishin abin da tayi ɗazu, ya juyo jefe kamar bai damu da abin da take son ce masa ba ya ce, 'ina jinki" ba tare da ta ɗauki komai ba ta ce, "ka ga yadda jikin Yazeed ya ke kuwa? Yana shan wuya" ta faɗi idonta na son kawo hawaye, cikin takaici ya juyo ya dube ta har da canza fiska, "kamar dama ai ke kaɗai rashin lafiyar na sa ya shafa ko? Shiyasa kika fi kowa shiga damuwa, nayi gaskiya?". Cikin kawar da maganarsa ta sake cewa, "ba wannan ba, duk ni ce sanadiyyar shigarsa cikin wannan halin, shi Yazeed dama ɗaukata yake a matsayin Safna, shine ya ke sanar da ni cewa yana sona, har da kuka sosai yake yi, na rasa amsar da zan bashi, shine na tafi n'a barshi, hakan yasa shi kasancewa a halin da yake ciki yanzu" ta faɗi cikin sauya fiska cikin damuwa, wani murmushi Shuraim ya saki cikin jin rashin daɗi, sannan ya furta, "wato sabida ya ce yana sonki kuma baki ba shi amsa ba, shine yasa shi faɗi har ya fasa kai?" Ya faɗi domin shi bai ɗauki maganar da gaske ba. "Eh haka ne, ni dai kawai dama so nake na sanar da kai zan faɗa masa gaskiya" da sauri Shuraim ya ce, "kamar ya gaskiya?" Sai da ta ni sa kaɗan ka na ta bashi amsa da cewa, "gaskiyar cewa ni ba Safnarsa ba ce, ban ma taɓa ganinta ba" "me kike shirin yi Amna? Kina nufin zaki faɗa masa cewa ke ba Safna ba ce ke? Amma kin san idan kika faɗa masa haka dole zai so ya ji ya akayi kika zo gidan, da ma wasu bayanai ko?" Cezar Shuraim cikin nuna abin da take shirin yi babban kuskure ne. "Eh zan faɗa masa idan ya nema, zan sanar da shi komai da komai, ba zan ɓoye masa komai ba, ƙila idan nayi hakan zai barni in huta, zai rabu da kallo na akan Safna, daga nan kuma sai ya gane ba wai Safna ta ƙi sa ba ne" saurin taran numfashinta yayi cikin tashin hankalin abun da take son aikata musu ya ce, "baki da hankali ne?! Kin san asarar da zaki ja mana idan kika yi hakan kuwa? Zaki rusa mana gaba ɗaya plan ɗin mu, komai na mu zai lalace, domin da ƙyar ya bar maganar" ya faɗi yana ƙureta da ido. Cikin dakewa da ainahin Amnarta ta juya kamar zata wuce, sai kuma ta juyo gabansa ta ɗaga ido ta kallesa sannan ta fara magana cikin nuna ba zai hana ba ta ce,, "ba ka son na sanar da Yazeed gaskiya?" "Eh don Allah kada ki sanar da shi, idan ba haka ba..." "Ba zan sanar da shi ba kamar yadda ka nema, amma ina son ka sani, ba zan taɓa yarda na ci gaba da zama sanadiyyar kasancewarsa cikin damuwa ba, domin ni ba na son kowa ya kasance cikin matsala saboda ni, ya ce idan har bai same ni ba wani abu zai iya samunsa, kuma ni na ga alamar hakan zai iya kasancewa, don haka ba zan bari ba". Sai da Shuraim ya matso kusa da ita kaɗan ransa cikin fargaba ya sake ƙura mata ido bayan maganar da ta faɗa ya ce, "me kike nufi da maganar baza ki bari ba? Me zaki yi?!" Ɗaga idonta tayi ta kallesa sai da ta danne zugin da maganar zai sanya mata sannan ta ce, "zan amince da shi inso shi" ta faɗi tare da juyawa kamar zata wuce, ta cigaba da cewa, "sannan idan ya kama na aure ne m'a, zan aure shi!" sai da ta runtse ido kafin ta ƙare maganar, wanda shima Shuraim hakan yayi, domin ba ƙaramin bugan zuciyarsa ta yi ba da wannan zancen. Ba tare da ya samu da mar magana ba, Amna ta buɗe idonta da wani dauriyar ta kuma cewa, "saboda ni ba zanyi silar mutuwar zuciyar wani ba" tana faɗi ta sanya hannu ta share hawayen da ya gangaro mata sannan ta wuce ba tare da ta sake juyowa inda ya ke ba, sai a lokacin ya buɗe idon na sa tare da ƙanƙance su yana bin ta da kallo kamar mai gasgata abin da yaji a kunnuwansa, domin yadda ya ji a ransa ya wuce misaltuwa, "da gaske ne abin da na ji?" Yayi tambayar kamar yana jiran a basa amsa, sannan ya juya da idanunsa yana kewaya wurin, kamar wanda bai san a inda yake ba. Last part. ___________________________________________________ Huuummm, ko ya zata kaya gaba? Amna zata so Yazeed kamar yadda ta faɗa saboda gudun abin da ka.iya faruwa da shi? Ko kuma dai Shuraim zai amince da faɗin gaskiya don gudun kada ya rasa ta? Idan za a faɗi gaskiyar ya kuke ganin yadda Yazeed zai yi? Ku biyo ni a kashi na gaba din jin abubuwan da zasu faru. Alƙalamin✍🏼 Aisha G Umar. ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣2️⃣9️⃣▶️1️⃣3️⃣0️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽 Ko da Amna ta bar wurin Shuraim, gurin da su Hajiya suke ta koma, jikinta sai rawa yake yi ta rasa abin yi, sai da aka ɗau dogon lokaci daga bisa ni doctor suka fito, sai da Amna ta riga su zuwa gabansa ta na jerowa doctor tambayoyi akan halin da Yazeed yake ciki. Nan doctor ya sanar da su cewa "gaskiya zuciyarsa ta hau sosai, domin kaɗan ya ra ge hawan jini yayi masa kamu mai girma, tabbas akwai abin da yake damunsa sosai, ƙila ransa na son abu amma ya gaza samunsa, ko dai wani abun daban". "Yanzu dai ya samu nutsuwa? Ko da kaɗan ne? Ko kuwa a wani hali yake yanzu?" Cewar Amna cikin hanzari kamar mai jiran sakamako, saboda tsabar damuwar da take da kuma tsoro, sai da gaba ɗaya 'yan wurin suka ƙura mata ido, ganin abin da take nuna wa na son wuce tunani, banda abokin Dady da dama tun ɗazu ya bar wurin, "eh bacci ya samu damar ɗaukarsa, domin allurar da aka yi masa." Amna bata bari doctor ya ƙarasa ba ta nufi ɗakin da Yazeed ɗin ya ke tare da shigewa, à idon Shuraim hakan ya faru, da sauri shima ya nufa dakin, da ido su Dady suka rakasa, mamaki na faɗaɗe a fiskarsu, har sun fara tantamar wani abu a tsakanin Amna da Shuraim ɗin. Hajiya ce ta ce, "doctor na ga baka ce komai ba yaran nan sun shiga? Kenan komai ya dawo daidai?" Kallonta doctor yayi ba tare da ya ce komai ba. Amna bayan shigarta ɗakin da sauri ta isa gaban Yazeed tare da zama kan kujerar gefen gadon, kamar ɗazu zagaya idanuwanta take yi kan fiskarsa kamar mai neman wani abu, sai da ta ja numfashi tare da haɗe wani irin nyawu da ta rasa na me sannan ta fara magana, "yanzu ni ce na zo baka haƙuri Yazeed, ka yafe min duk abin da nayi maka, ka buɗe idonuwanka, ina son na gansu, sannan ka buɗe kunnuwanka, ka ji abin da zai fito daga baki na, na san zaka ji daɗin magan-ganun da zan faɗa maka". Ta faɗi ƙwalla n'a cika mata gefen ido suna rawar fitowa, Yazeed da yaji maganar na ta kamar a mafarki ne ya fara buɗe idanuwansa a hankali cike da dauriya, domin jin idanuwan na sa yake kamar an watsa masa ƙasa a ciki, allurar da akayi masa bai gama shigewa jikinsa ba, bayan ya buɗe idanun ya samu damar kai fiskarsa gefen da take haɗi da sauke jajayen idonsa cikin na ta, murmushi mai ƙayatarwa yayi ƙoƙarin sakar mata kamar wanda aka sa dole, itama Amna murmushin tayi cike da farin ciki na ganin ya buɗe idonsa, "yauwa Yazeed ka buɗe ido? Tom da ma so nake na nemi yafiyarka akan abun da nayi maka, na san na cutar da kai, ni ce silar duk abin da ya faru da kai". Baki Yazeed ya buɗe kamar mai son yin magana, amma kuma ya kasa furta komai, ganin yana son yin magana kuma bakin na sa ya ƙi ba shi ƙwarin guiwa ne yasa Amna gyara zama haɗi da matsowa kusa da shi sannan ta ce, "ba sai kayi magana ba, kawai ka saurari abin da zan sanar da kai, dama kawai gwada ka ne nake son yi, domin in tabbatar da soyayyarka à gareni, domin ni ma..." sai dai nauyi maganar da zata faɗi yayi mata, hakan yasa ta dakata haɗe da rinste idonta, "ke, m'a me?" Ta ji maganar ta sa, bayan furta wa da ƙyar da yayi, buɗe idon tayi sannan ta ƙarisa kamar wacche aka tirsasa, "domin nima ina sonka Yazeed!!". Charab wannan kalmar ta shige kunnen Shuraim, daidai buɗe ƙofar da yayi ya shigo, yayin da yaji wannan shigewar da kalmar ta yi cikin kunnensa tamkar ya haɗe da tafiyar masa da dodon kunne, sai da ya kusa faɗi daga tsayen da yake yayi saurin dafa jikin ƙofar, Yazeed kuwa kallonta kawai yake kamar bai ji mai ta ce ba, lura da yadda yake kallonta kamar bai yarda da abin da ta ce da shi ba ne yasa ta sake cewa cikin tabbatar masa da hakan, "haka ne ina sonka! kamar yadda na ce kawai gwada ka na ke yi, domin kuwa nima na kasance a makamancin halin da ka shiga bayan ba ka nan". Sai da ta ji rashin daɗi a ranta domin kuwa ta san ƙarya kawai take yi masa, to amma ya zata yi, dole ta kasance kamar maƙaryaciya a wurinsa, cikin wata murya mai kama da babu, wato sai wanda yasa hankali sannan zai fahimci magana Yazeed yake, ya buɗe bakinsa da yake ji kamar garwashi ya ce, "da gaske ne? Da gaske ne abin da kika faɗa min? Don Allah kar ki faɗa min don inji sauƙi a zuciyata, kar ki sanar da ni abin da ba shi ne ba" ya faɗi ba tare da idonsa ya fita daga gareta ba, sai ma hawayenda ya gangaro daga cikin idanun, domin ji yake a ransa kamar so take kawai ta kwantar masa da hankali, saboda ganin halin da yake ciki, shi kuwa ba zai so hakan ba, duk da cewa ko da ƙarya ce tayi masa zai yi farin ciki, amma zai fi so ya zamana har cikin zuciyarta ta ke faɗa. "Ka kwantar da hankalinka Yazeed, da gaske nake maka, saboda à yanzu har jin tsanar kaina na ke yi da ya zamana ni ce wacche ta jefa ka a halin da ke ciki, na tsani kai na!" "Noh, no Safna don't say that, baki da laifi ko kaɗan, ko da ma ace laifin ki ka yi, to ni ba na gani" Yazeed yayi maganar yana son tashi daga kwancen da yake da ƙarfi, "ya ka ke ƙoƙarin tashi kuma?" Amna ta katse shi da faɗin haka, dakatawa yayi da zamar da yake son yi ya saki wani irin murmushi, da ya fito tun daga ƙasar ransa, "amma don Allah, da gaske kina so na?" Sakin murmushi Amna tayi cikin nuna masa farinciki da kuma zolaya ta ce, "ka yi min wannan tambayar a baya, kuma na faɗa maka da gaske na ke yi" Murmushi yayi sannan ya kuma cewa, "to Amma me yasa nake yawan ganinki tare da Shuraim?" "Am im, wai Shuraim? Shi ɗin kawai ya kasance, kawai just my friend only!" Ta yi maganar cikin dabur cewa, Shuraim da ya kasa kunne yana jiran matsayinsa da zata faɗawa Yazeed ɗin, sai gashi ta faɗi abun da ya rusa masa jerin ƙwaƙwalwarsa, ya girgiza masa zuciya, wai to ko dai dama Amna ta na son Yazeed ne? Yayi wa kansa tambayar da babu kai bare amsa. Sai da Yazeed ya saki murmushi mai cike da sautin nishaɗi da jin daɗi, akan abin da yake buri kuma yana gab da samu, sannan ya ce, "Safna zaki aure ni?!". Duk da cewa har yanzu ba wai dai na jin abun da yake a jikinsa yayi ba, amma kaso tamanin ya ragu, idan kuwa har Safna ta tabbatar masa da amsar da ya ke so, to ko shakka babu kaso ɗarin ma cika zaiyi dam. Jin maganar ta sa Amna tayi kamar wani bugun ƙaton dutse cikin zuciya, shiru tayi tana kallonsa ba tare da ta bashi amsa ba, "please tell me Safna, idan da gaske kina so na, to zaki aure ni?" Ya kuma sakar mata da tambayan cikin wanna muryar ta sa mai sanyi a hankali, miƙewa ta yi tare da juyawa, turus ta yi ganin Shuraim da idanunta suka ci karo da shi, wanda ba su san yaushe ya shigo ba, domin hatta Yazeed ɗin ba lura da shi yayi ba, wani irin faɗuwa gaban ta yayi, sai dai tunawa da ƙin amincewar da Shuraim yayi akan ta sanarwa Yazeed abin da yake faruwa, hakan yasa ta ba Yazeed amsa da cewa. "Yes Yazeed, I will marry you!" Ta faɗi idonta na cikin na Shuraim ɗin, don tabbatar masa da abin da ta ce ɗazu, duk da ta ji ba daɗi kuwa, idon Shuraim ne ya sake sauyawa sosai, kallonta ya ke kamar wanda yake kallon abin tsoron da yake ratsa masa zuciya, nanata maganar da ta faɗi yayi à ransa, ya juya ransa na yi masa wani irin suya mai cike da kishi da kuma takaicin abin da Amna tayi masa, ya fice waje jikin

Chapter 38 of 56