Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ammu kamar a mafarki, a hankali ya iso gabanta ya durƙusa, sunan Ammu ya ambata cike da mamaki, hakan yasa Ammu da Safna ɗagowa suna kallonsa da idanuwansu mai cigaba da amayar da ruwa. "Na'am ɗana Shuraim, ya ya..." Ammu ta kasa ƙarisawa saida ta miƙe tsaye ta kuma cewa, "Shuraim ɗana ka ji sauƙi? Kana lafiya ɗana? Babu abin da ya ke maka ciwo ko?" Ƙwallan da ya cika a idon Shuraim ya fidda, sannan ya amsa wa Ammu tambayarta da faɗin, "na warke Ammu, na na yi farin ciki da ganin ki haka". Ammu ta ce, "Shuraim Amna.." "me ya samu Amnan Ammu me ya ke faruwa?" ya katseta da faɗin hakan tare da waigawa yana dubawa amma bai ga Amna a ɗakin ba, "Ashe dama ita ɗin 'yata ce?" Cewar Ammu idonta kan Shuraim, juyawa ya yi yana kallon Safna, shima ta giɗa masa kai alamar eh ta sanar da Ammu, Ammu ta kuma cewa, "Amna 'yata ce, ban taɓa sani ba, amma bai kamata wani abu ya sameta yau ba bayan na san da cewa ita ɗin daughter na ce, muje inda aka kaita, inga ya jikin na ta yanzu?". Sai à lokacin Shuraim ya gane cewa Amna na cikin wani hali, hankalinsa shima ba ƙaramin tashi ya kuma yi ba. Sun yunƙura zasu fice a ɗakin dukkansu, kafin su fice Baba tsoho ya dakatar da su bayan ya tsaya a ƙofar, da mamaki Shuraim ya bisa da kallo, domin bai manta da fiskarsa ba, ƙarasa shigowa ya yi sannan ya umurcesu da su kwantar da hankalinsu, insha Allah babu abin da zai faru da Amna, kawai abin da ya ke so da su, su yawaita yin addu'oi sosai. Yadda ya yi musu maganar ne ya sanya su kwantar da hankalinsu amma ba sosai ba. Uncle Musa ne ya ba da saƙon à je a sanar wa da Hajiya ɗanta na asibitin, domin ya kamata su san da hakan. Saboda shima Yazeed ɗin bai farka ba, haka shima Baba. Su kuma su Dady wani asibitin aka kaisu ƙarƙashin kulawar hukuma. Ba ƙaramin tashin hanakli Hajiya ta shiga ba da jin labarin ɗanta mafi soyuwa ba lafiya, dama tun ɗazu ta ke gwada layinsa amma babu labari, dama bata san yaushe ya fita daga gidan ba, gashi har dare na neman yi, sai kuma ga mummunar labarin da ya risketa lodi-lodi, da fari Ruki yanzu kuma Yazeed. Ba ta da labarin Dady saboda dama shi ya sanar da cewa ya yi tafiya ne. ONE WEEK. Zaune su ke cikin falon dukkansu, kama daga su Mamma, da Shuraim ya kawo su gidan yau, sai su Ammu, Safna, Amna, sai Baba, Mamma, Ummee, Mubarak, sai Hajiya, Yazeed, Marwan, Saleem, Ruki, da kuma Shuraim, uncle Musa, Baba tsoho, gaba ɗayansu jiran jin abin da Baba zai ce su ke. Sai da Baba ya numfasa cikin raɗaɗin yau zai bada labarin cewa ba shi ya haifi Amna ba. _shekaru ashirin da kusan huɗu da su ka Shuɗe a baya, an ba ni takardar canjin aiki daga Kaduna zuwa Gombe, hakan yasa ni da matata Habiba da kuma ɗanmu da bai wuce wata goma da haihuwa ba, mu ka kama hanya don zuwa ƙauyen Takori sanar da mahaifiyata Mamma, da kuma neman amincewarta don mu koma Gombe tare, motarmu ta samu matsalar ɗaukar zafi sosai, hakan ya sanya muka sauka daga cikin motar don mu samu ruwan da zamu yi amfani da shi, cikin sa'a muka haɗu da wani mai tura ruwa, na sayi ruwan sannan na zuba, bayan na miƙa wa mai ruwa jarkansa sannan na yi wa Habiba magana da mu shiga cikin motar yanzu zan ta da shi, kafin mu kai ga shiga cikin motar na ji andafa ƙafaɗata, ko da na juyo na kalli wani bawan Allah riƙe da jaririya ɗanya a hannunsa tana ta faman kuka, kallonsa na yi da mamakin abin da yasa ya tsaidani ga shi gumi sai tsiyaya ya ke a fiskarsa, "barkanku dai bayin Allah, ni sunana doctor Salis, ina da buƙatar taimakonku" abin da ya faɗi kenan wanda daga ni har Habiba mu ka cigaba da sanya masa ido, na ce da shi, "bawan Allah wani irin taimako ka ke nema daga gareni? Ga yarinya à hannunka sai faman kuka ta ke yi, ya kamata ka miƙawa mahaifiyarta ita" doctor Salis ya ce, "yau ne zuwanta duniya, sannan a yanzu haka komawarta gurin mahaifiyarta babban hatsarine a gareta, domin yadda ka ke gani yanzu kasheta aka sa ni inyi, amma ba zan iya ba, saboda ban taɓa kashe mutum ba, amma an tilasta min idan ban aikata ba za'a kashe tawa matar, wacche kuma a yanzu haka tana ɗauke da ciki wata bakwai" ya faɗi idonsa cike da ƙwallah, ba ƙaramin razana da batunsa mu ka yi ba, ya ƙara da cewa, "na zo ina shirin aikata abin da aka sani yarinyar nan ta fara kuka, wanda wannan kukan na ta ya sanya ni na kasa aikatawa, sai gashi Allah ya bayyana ku a wurin nan, na ji cewa ku ne wa'yan da zasu yi silar taimakon wannan jaririyar da kuma matata da ɗana, don Allah ina roƙonku ku amshi yarinyar nan, ku zame mata iyaye na gaskiya, sannan don Allah ku nisanci wannan garin da ita na roƙe ku da girman Allah!" Doctor Salis ya faɗi cike da magiya, ƙwarai abin da ya faɗa ya razana mu, ban yi masa magana ba na juya na kalli Habiba, ita ta fara amincewa da mu amshi wannan yarinyar, domin ba mu san abin da ubangiji ya ke nufi da haɗa mu da ita ba, wannan dalili ya ƙara ƙarfafa min guiwa hakan yasa muka amshi jaririyar da ga hannunsa, duk da har lokacin bata daina kuka ba. Bayan mun isa gida Mamma ta yi mamaki sosai da abin da ta gani, ba ita kaɗai ba hatta da wasu mutanen ƙauyen, ko da mu ka yiwa Mamma bayanin komai sai ta amince da mu, kuma ta bamu goyon baya. Kasancewar Habiba dama tana kan shayar da Mubarak, hakan yasa ta cigaba da shayar da jaririyar aka yaye Mubarak, daga baya kuma aka raɗa mata sunan mahaifiyar Habiba ni kuma na laƙabta mata Amna, tun da muka bar ƙauyen na ƙi bari mu kusanci garin gaba ɗaya, don kawai kada hakan ya kasance matsala ga rayuwar Amna, saboda ina ganin za'a ganeta a duk lokacin da muka kasance a garin. Saboda gudun faruwar matsala ga rayuwarta hakan yasa ko da wasa ba na amincewa da yin nisa da gida, domin ina ganin a duk lokacin da na yi nisa da Amna za'a cutar da ita, na rusa duk wani cigaba da aka kawo min don zuwa wata ƙasa saboda jajircewana na ɗan jarida, na fi son na kasance da iya ƙaramin abin da na ke samu a kan na yi nisa da iyalaina, abin da yasa na zo garin Kadunan ma don ta'asan da Ƙungiyar Pospa ta ke yi ya yi yawa, na ji ba zan iya sallamar da binciken da na fara a kansu ba, hakan yasa na zo. wannan shine abun da ya faru_ Baba ya ƙarashe maganar da muryar ciwo, yana kallon inda su Ammu su ke. Duka sauran mutanen da ke zaune a falon ma duk idonsu na kan Ammu da 'ya'yanta Amna da Safna da su ke ta faman rusa kuka bayan da Baba ya gama ba su labarin. Gyara zama Baba tsoho ya yi shima ya fara magana da cewa, "Alhamdulillahi, to kamar yadda na sanar da ku cewa ku kwantar da hankalinku zan kuma warware muku komai. Babu buƙatar ku san ni wane ne? Amma zaku iya duk tunanin da ku ke so game da ni, walau ku ce ni aljani ne, walau ku ce ni masihirci ne, walau kuma ku ce ni ɗin malami ne, sai dai ku sani ni ɗin musulmi ne kamar ku, ranar da na bayyana filin wasu marasa kunyar samarin nan, har su ka yi min rashin ɗa'a Amna ta yi faɗa da su don kareni, ranar ne fara ganinta da na yi na farko, sai dai da ganinta na ga wasu al'amura a kewaye da ita, ga ni na yi suna daf da faɗawa cikin wata masifa wanda zai iya yin sanadiyyar rasa rayukansu, wannan dalili ne ya sanya na ɗau zoben haske na ba su, wanda wannan zoben nima gadansa na yi, zobe ne da ya shiga idon mugaye su ke son samunsaa don su salwantar da shi, domin kuwa ya yi sanadiyyar kashe matsafa da dama, kuma aikinsa sau ɗaya ne kaɗai ya rage, daga nan zai tarwatse. Cikin ikon Allah Amna da Shuraim su ka samu nasara. Sannan kuma game da wasu abubuwa da ya ke bayyana ga Amna, ƙarfi da kuma sauran sauyi, tun suna ciki sihirin da ke kasancewa tsakanin tagwaye ya rinjaya a kan Amna, sai dai shi ba kalar na ko wasu irin 'yan biyu ba, na sun ya kasance ubangiji ya ba su na musamman, a duk lokacin da ranta ya yi mugun ɓaci kuwa idonta zai kasance jazir, amma ranar da gaskiyar komai ya bayyana daga bakin mugun da ya tarwatsa rayuwarsu, Amna da Safna ransu ya ɓaci sosai, wannan dalili ya sanya duk wani abu da ya rage a jikin Safna ya koma kan Amna, su ka haɗu don ramuwar abun da aka yi musu. Duk wannan ƙarin bayanin ne ya sanya na ƙi tafiya tun tuni, amma yau zan tafi, sauran abubuwan da ya rage ku zaku kammala shi, nagode". Baba tsoho na ida jawabinsa ya tashi ya kuma yi musu sallama, bayan su uncle Musa sun gama yi masa godiya ya fice. Hajiya ko ƙwaƙwaran motsi ba ta iya yi, domin tun fari da zaman su aka riga aka sanar da abin da Alhaji ya yi, ba ita kaɗai ba hatta sauran 'ya'anta da ba su san da alamarin ba. Su Ammu hawaye su ke sosai, da su Mamma. Sauran 'yan cikin falon sai alhini su ke da abubuwan da ya faru, tabbas babu abin da ya gagari Allah!. Babu abin da ke tashi a cikin falon sai tashin kukansu Ammu, sauran ma masu rarraunar zuciya tuni hawaye ke ta aikinsa à gare su, musamman Ummee da kuma Mamma, Ammu sai godewa Allah ta ke da wannan ni'imar da ya ba ta, ashe dai 'ya'yanta biyu ba ta sani ba, juyawa ta yi tana kallon su Mamma tare da cewa, "ban san ta ya zan fara yi muku godiya ba, ban san da wani kalma zan fara ba" sai da Mamma ta share hawaye sannan ta ce, "duk abin da mu ka aikata shine abin da ya dace da duk mutum na ƙwarai, ya taimaki mutum ba sai na sa ba, don haka kada ki damu da yin wata godiya, Aminatu ba za ta taɓa barin sunan 'yarmu ba, za ta kasance a haka har abada a cikin zuciyarmu". Baki cikin kuka Amna ta ce, "ko da wasa, ko à mafarki ban taɓa sanin cewa ba ku ba ne ahalina, kuma don na san haka daga baya ba zai sa na cireku a raina ba, har kullum ku ɗin familyna ne, dangina kuma farin cikina" maganar da Amna ta yi ba ƙaramin sa ke sosa musu zuciya ya yi ba, ba su so gaskiyar cewa ita ba 'yarsu ba ce ya bayyana, sun so su cigaba da kasancewa ahalinta na gaskiya, amma ya su ka iya, dole gaskiya ta yi halinta. Hambali ne ya shigo da sallama, su ka amsa masa, nan ya sanar da su akwai 'yan sandan da su ke da buƙatar yin magana da su, uncle Musa ya ce ya je ya ce su shigo. Bayan 'yan sanda sun shigo ɗaya daga ciki wanda shine babba a ciki ya fara cewa, "mun zo ne mu sanar da ku, nan da kwana uku za'a fara gudanar da shari'ar Jamilu kamar yadda aka bamu tabbaci daga kotu, ku shirya duk abin da ya kamata kama daga lauya da kuma shedu, zuwa jibi zamu jira ku ku gabatar mana da sauran bayanan" zaro ido Hajiya da Marwan, Ruki su ka yi, shi kuwa Yazeed kauda kai kawai ya yi yana kuma jin zafi a ransa. Amna da Safna kuwa haɗe fiska su ka yi a take da jin an anbaci sunan Dady, ko da ya ke dama ya kamata a kammala komai a hukunta shi daidai da abin da ya shuka. Last part. ___________________________________________________ Toh fah, kun dai ji duk abin da ya wakana a cikin wannan part ɗin. Ko ya shari'ar Dady zai kasance? Mu haɗu da ku a next part idan Allah ya kaimu. React, comment and share fisabilillah🙏🏻🙏🏻 _🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_ ______________________________________________________________________________________________ Part1️⃣6️⃣5️⃣▶️1️⃣6️⃣6️⃣ 📲 Writing✍🏼 Aisha G Umar _🌹Zahra-tul-Qalam🖋️_ Bayan 'yan sanda sun gama jawabin abin da ya kawo su, su ka tafi. Babu wanda ya ta da maganar, ko ba komai su Hajiya suna kusa abin ba zai yi musu daɗi ba. Hira ake yi tsakanin ɓangarori, Mamma ce ta dubi Baba sannan ta ce, "ɗana ban taɓa tunanin zan sake sanya ka cikin idona ba, ashe dai ina da rabon sake ganinka à kusa da ni" ta faɗi tana share ido, sauran ma cikin yanayin alhini su ke zaune a wurin, duk da cewa alhinin ya na haɗe da farin ciki ne, amma ya sanya tausayi cikin zucinsu, Baba ya dubi Mamman ya ce, "ƙwarai Mammata ni ma ban taɓa tunanin hakan ba, domin na riga da na sadaukar da na riga da na bar duniya, domin tun bayan da su ka kamani, suka kai ni cikin wani ƙaramin kogo, sun bani azaba sosai da shocking ɗin da suka haɗa jikina da shi, tun a lokacin na ɗauka zasu gama da ni, amma sai ga shi daga baya sun kuma ɗaukana su ka kaini wani ƙaton kogon mai tattare da abubuwa kala-kala, tun ranar da aka kaini ban ƙara sanin inda na ke ba, sai ranar da na buɗe ido na na ganni cikin wannan hall ɗin, Allah mai ikonsa yadda ya so, haƙiƙa babu wanda ya isa ya yi maka abin da Allahu subhanahu wata'ala bai nufa ba". Jinjina kai su ka yi da ƙara godewa buwayi gagara misali, sannan su ka ɗaura cikin hira gwanin sha'awa gaba ɗayansu, Hajiya bata iya jurewa ganinsu ba, hakan yasa ta miƙe zuwa dakinta, shi kuwa Yazeed kunyar haɗa ido da su ma ya ke yi, don haka shima ya yi na sa ɗakin. BAYAN KWANA UKU. Amna da Safna ne su ke cikin ɗaki suna shiryawan fita zuwa kotu, jikinsu ya ɗan yi sauƙi, saboda an cire musu bandejin da ke a ko wani ciwo, "Amna?" Safna ta kira sunan Amna, hakan yasa Amna ta dakata da abin da ta ke yi ta ɗago tana dubanta, kallonta Safna ta ke sosai ya yin da cikin idonta ke ƙoƙarin fitar da ƙwallah, à yanzu Amna ba ta da buƙatar kayan basaja, don haka babu abin da ta sanya a fiskarta, tana a asalin kamanninta. Tahowa ta yi a hankali ta ƙaraso gaban Safna, tana ƙarasowa Safna ta rungumeta haɗi da fashewa kuka, itama Amna ƙwallan ne ya cika mata ido amma saboda ba ta son kukan 'yar uwarta ta, hakan yasa ta yi saurin share na ta hawayen sannan ta ɗago Safna daga jikinta tana dubanta cikin raha, "ohhhh 'yan matana wai me yasa ki kuka ne? Faɗa min ko mene ne zan yi maganinshi" yadda ta yi maganar yasa Safna dakatawa da kukan tana duban Amna. Ɗaga mata gira Amna ta yi alamar eh faɗa min, ganin har yanzu hawaye na fitowa daga idon Safna, ya kuma sa Amna sake cewa, "amma 'yan matana wai in tambaye ki mana?" Ɗagawa Amna kai Safna ta yi itama alamar ina jinki, a hankali Amna ta matso da bakinta setin kunnen Safna ta ce, "na ce wai ke wacece? Amna ki ke ko Safna?" murmushin da ba ta shirya ba ya kufce mata har da matsawa baya. Itama Amnan murmushin ta yi ta ƙara cewa, "sanar da ni mana, ke Amna ce ko Safna? "Ni Amna ce" Safna ta ba Amna amsa, sai da Amna ta juya sannan ta kuma waiwayowa kan Safna ta ce, "iiimmmm, to idan har ke Amna kuwa, to kuka fa ba na ki ba ne, sai dai ki bar min" cewar Amna tare da sharewa Safna hawaye, juywa Amna ta ƙara yi tare da ɗaura hannu a kwankwaso tana tafiya, in ta ɗaga ƙafa ɗaya a sannu sai ta ɗaga ɗayar ƙafar, cikin ƙaton murya ta kuma cewa. "Tun da kin kasance Amna haka zaki rinƙa tafiya, sannan muryarki ta canza zuwa yadda na ke magana yanzu, sannan ki rinƙa haɗe fiska a duk lokacin da aka yi miki abin da ba ki so ba" ta faɗi tare da juyowa tana kallon Safna haɗi da sake irin tafiyar tana tahowa gaban Safnan, har da ɗage kai ta ke yi, "à duk lokacin da aka nuna miki yatsa! To kisa na ki yatsan ki kare-raye wa mutum yatsa, idan aka ce ke wacece, sai ki ce ni ne Amna Zakanya!". Amna ta ƙarashe maganar daidai isowa gaban Safna. Dariyar da Safna ta ke riƙewa ne ta saki, sosai Amna ta ba ta dariya don haka itama ta zage tana dariyar, wanda dariyar nan zata iya cewa ba ta san ko ta taɓa yin irinsa ba, itama Amnan taimakonta ta yi gurin dariyar su ka haɗe su biyu sai darawa su ke yi abunsu. Dakatawa da dariyar Safna ta yi, hakan yasa Amna ma yin hakan. Sake rungumarta Safna ta kuma yi a karo na biyu, cikin sanyin muryarta ta ce, "ƙwarai haka zan rinƙa yi, tun da ni Amna ce, amma fa kukan farin ciki, dole ne a gareni" ta ƙarashe maganar da ɗagawa daga jikin Amna murmushi na sake wanzuwa a fisakarta. Amna ma kamar Safnan fiskarta abin da ya ke yi kenan, "ban san ta yadda zan sanar miki ba Amna, amma na ji daɗi da ya kasance, ina da 'yar uwa kamarki, a ƙalla dai ba zan sake kasancewa, ni kaɗai ba, nima ina da 'yar uwa, uwa ɗaya uba ɗaya, kin san me? Akwai lokacin da na taɓa yin mafarki wata tana kusa da Ammu tana yin magana da ita, sannan muryarta irin nawa, haka yanayinta. Amma sai yanzu ne, na san amsar mafarkin na wa, mafarkin ya nuna min cewa, ina da 'yar uwa kamar ni ba tare da na sani ba". Kallonta Amna ta ke yi cikin tsantsan farin ciki sosai, kafin ta kai ga yi mata magana wayarta ya hau ruri, ɗauka ta yi ta ga numbern Raheena, murmushi ta saki tana kallon Safna ta ce, "bestynki ce fa ta ke kira, kin san dama na ce miki ban sanar da ita kin dawo ba, kuma na hanata zuwa, so na ke na ga shock ɗinta idan ta ganki, saboda zai yi wuya in zauna da ita ba ta kawo min maganarki ba" murmushi mai sauti Safna ta yi sannan ta ce, "Allah sarki Raheena, wallahi nima tana raina, she's the best friend in the world". "Nima na shaida. Tom mu yi sauri mu fita, don na san ƙila kowa ma jiranmu ya ke yanzu" faɗin Amna tana yafa gele saman doguwan rigarta, ita ma Safnan doguwan rigar ta sa, don Amna ce ta zaɓan mata. Amna lanƙwasa hannunta ta yi tana kallon Safna ta ce, saƙala hannunki muje 'yan matana" sanya hannun Safna ta yi itama tan cewa, "tom 'yan matana zamu iya tafiya?" Murmushi lokaci ɗaya suka saki, hannunsu cikin na juna suka fice daga ɗakin. Suna saukowa daga step mutanen da ke falon idonsu ya koma kan Amna da Safna, domin dama yanzu ake shirin zuwa kiransu. Ammu da su Ummee cikin farin ciki su ke kallonsu Amna, yayin da Shuraim da shima ya ɗan samu sauƙi da kuma Yazeed kuma su ke sake murmushin shauƙi da ƙauna, Hajiya da sauran 'ya'yanta kuwa, na ciki na ciki kawai, saboda har da harara su ke haɗawa a kallon su Safna. Sumee ce ta ɗan tsungule Marwan, hakan yasa ya yi saurin dafe inda ta tsungulesan tare da juyowa yana kallonta, "ke me haka?" Cewar Marwan a hankali yana wurga mata harara, Sumee ta ce, "dalla ni tambayarka zan yi, wai wa ce Safna wa ce kuma Amna à cikinsu? Ka ga dai wancan ita idonta yana da kala, ita kuma ɗayan babu, to ko me kalar idon ne Safna? " "Ban sani ba! Je ki tambaye su mana, ai ga ki ga su" Marwan ya faɗi kamar zai rufe ta da duka ya kauda kansa, tsaki sumee ta ja tare da jefawa Marwan ɗin harara. Fitowa dukkansu su ka yi kowa ya shiga motocin da ke jere a harabar gida, bayan masu gadi sun hangame gate ɗin su ka fice zuwa babban kotun jihar Kaduna. KOTU. Gaba ɗaya mutane sun hallara a cikin ƙaton kotun, kama da ga wa'yan da abun ya shafa, da kuma masu kallo. Alƙali na zaune a mazauninsa, sauran masu gabatarwa su ma suna zaune a ta su kujerar da ke ƙasan gaban kujerar Alƙali, sun ba Alƙali baya, sai sauran lawyer su ma su na zaune a ta su kujerun. Mai gabatarwa ne ya miƙe ya gabatar da shari'ar da su ke da shi, da kuma abin da ake zargin Jamilu Ibrahim, wato Dady da kashe mutane har ma da wa'yanda ba a sani ba, sannan da batun ɓoyayyiyar ƙungiyar Pospa, har da ta'asan da ta yi na kashe mutane bila'adadin a Nijeriya watannin da su ka gabata. Byana gama wannan jawabin ya miƙawa Alƙali takardun da ke hannunsa. Kallon takardun Alƙali ya ke yi tare da buɗewa ya na nazarinsu, daga bisani ya ɗago kansa yana faɗin, "shin akwai lauyoyin da ke ɓangaren masu ƙara da kuma wanda ake ƙara?" Ɗaya daga cikin lauyoyi ya miƙe ya gabatar da kansa da cewa shine lauyan masu ƙara, jim kaɗan wani lauya ya kuma miƙewa shima ya gabatar da kansa kan cewa shine lauyan wanda ake ƙara. Su Amna sun yi mamaki sosai, taya Dady zai samu lauya? Shin yana da ƙwarin guiwar kare kansa kenan bayan duk abin da ya faru?. Dady ne ke shigowa cikin kotun hannayensa ɗaure da ankwa, wasu police huɗu na bayansa, Hajiya da 'ya'yanta ne su ka yi saurin miƙewa su na kallonsa, Ruki da Hajiya su ka fara kuka, Ruki na kiran Dady. Juyowa Dady ya yi yana kallonsu, fiskarsa duk a kumbure, tafiya ma da ƙyar ya ke yi, domin har yanzu jikinsa na yi masa zafi, saboda dukan da ya sha à wurin Amna ba na wasa ba ne. Su Amna da sauran kuwa da kallon tsana su ka bi sa. Zuwa ya yi ya tsaya a gurin gurfana, fiskarsa babu alamar tsoro ko da na sani. Bayan lauyan ɓangaren su Safna ya gama magan-ganunsa, sai lauyan da ke kare Dady ya miƙe ya fara magana kamar haka, "ya mai girma mai shari'a ina da ja akan abin da lauyan masu ƙara ya ce, domin kuwa su karan kansu ba su da tabbacin zargin da su ke yi masa, wannan bawan Allahn babban mutum ne, mutane da dama sun sanshi, kuma sun san da cewa ko kusa ba zai taɓa aikata laifin da ake tuhumarsa ba, kawai wata ƙulla-ƙulla aka haɗa masa, sharri kawai aka yi masa ta yadda bai zata ba. Ya mai girma mai shari'a Wanda na ke karewa ba shi da wata alaƙa da ƙungiyar Pospa, ina da shaidun da zai sa a gasgata abin da na ke faɗa". Su Hajiya murmushi su ka fara yi domin kuwa dama sun san ƙarya ake yiwa Dady. Su kuma Amna da sauran zaro ido su ka yi da jin maganar lauyan Dady, bayan sun riga da sun bayyana hujjojinsu wannan kuma wace iriyar magana ce?. Miƙa takardun da ke hannunsa lauyan Dady ya yi ga Alƙali, Alƙali ya amsa yana dubawa. Bayan doguwan lokaci da aka shafe ana muhawara a cikin kotu, rashin gamsashshiyar shaida daga ɓangaren

Chapter 51 of 56