ɗara ta tsawo kaɗan. Shima kyakykyawa ne, Kusan 30 minute suke tsaye a gurin ga layin mutanen da ta tara a bayanta, akan takalma ɗaya da ta keson zaɓa tsakanin baƙi da ja.
Kallonta saurayin yayi cike da takaici yace "ke nifa nagaji haba, da yanzu ina gida ina cin daddaɗan girkin Ummee, amma kin jawoni nan tin ɗazu kina abu ɗaya, dan Allah kisai takalmin nan mu wuce, duba bayan ki fa mutane ne ke jira"
hararansa tayi, sannan ta juya ta dubi mutanen da suma cike suke da ita, taƙara juyowa ta dubeshi ta ce, "dama ba ce maka nayi kawuce ka ƙyaleni ba, harda cewa ƙafa ta-ƙafar ki, to ma mutum da kuɗinsa bazai zaɓa ya darje ba, ha'a" ta ƙarasa faɗi tana tattaɓe baƙin takalmin, Inta ɗaga jan sai ta girgiza kai, "a'a kamar wancan yafi kyau" sai ta ɗaga baƙi kuma.
"To ki zaɓa ɗin mana, kuma da kike cewa nace ƙafa ta-ƙafar ki ai kinsan wannan tsohuwar, dana koma ba tare da keba zata hanani sukuni", tafara faɗin, "kai Mubaraka ina kabaro min jika ta Aminatu, saboda Allah kataho kabar yarinyar da babu ruwan ta, in wani abu yasa meta fa, haka zatai ta min sababi, Mubarak ɗin ma bata iya faɗi in tana masifa sai ta kirani da sunan mace wai Mubaraka".
Bata tanka masa ba sai ma cigaba da abinda take tayi, gyaran murya yayi da alama ma shi ake biyan kuɗin a wurinsa, ɗago idanun ta dake cikin glashi tayi tana duban sa, shima kallonta yayi sannan yace "biwar Allah me kike nema ne anan, akan takalma biyu kike wasting time ɗin mutane, inba siya zakiyi ba kiba mutane wuri".
Kamar zata cire glass ɗin sai kuma ta fasa sannan ta ce, "kaga malam kuɗi zan bada fa, ko so kake in siya takalmin da bai da lasting, toma tinda bason ciniki kukeyi ba nafasa siya, ku sayar a wani" ta ajiye takalmin, tayi fitowar ta, take mutanen wurin suka hau surutu, haƙuri Mubarak ya basu, sannan ya biyota yana faɗin.
"Amma ke Amna ko, yanzu duk wasting time ɗin da mukayi ba ki siya komi ba". "Dama ce maka akayi siya zanyi?" ta furta hakan tana kwashewa da dariya. Yace "what me kike nufi, ba cemin kikayi kintara wasu kuɗi ba?" Amina ta ce, "ba wani kuɗin da natara, ƙure ƙaryan me ƙarya nayi, Zubi ce ke cewa "ai Haleem shoprite na manyan masu kuɗi ne, waini takewa bagu, shine nace yau zanzo in ƙure ƙarya"
Yace "wato shiyasa ta biyoki kenan?" "eh mana ba kaga tana ganin abin bana ƙare bane ta ware" ta kuma kwashewa da dariya. dariya yayi shima yace "kuma wai a haka mamma take cewa ba ruwanki, duk abinda zan faɗa mata sai taki yarda", Amina ta ce "kai kuma gashi baƙin ciki kakeji in ta faɗi hakan ba mai gulma" tafaɗi tana ɗan sa gudu-gudu, shima bin bayan ta yayi yana faɗin "nine magulmaci?"
______________________________________________________________________________________________
Part 0️⃣5️⃣▶️0️⃣6️⃣
Tsayawa napep ɗin yayi a daidai kofar gidansu. Amna ta fara sauka "kefa zaki biya kuɗin" mubarak Yafaɗi hakan, tace "bazan biya ba, ai nina biya jiya" takarashe faɗi tana buɗe gate ɗin gidan ta shige da sauri, ƙofa yayi sannan ya ciro kuɗi yana miƙawa me napep ɗin.
Jikin tsufa sai a hankali hakan yasa ta ɗan kishin gida, dan tasamu damar hutawa, jin an faɗi akanta yasa ta ƙoƙarin tashi a hankali, "ke Aminatu karyani kikeson yi?, ina ganin sai kin karyani murƙuƙus tukunna zaki huta ko?" Tsohuwar ta faɗi haka, cikin shogoɓa Amna tace, "haba dai Mamma, ni ɗin nawa nake da zan karyaki, kuma ma ai ke Tsohuwa ce mai ran ƙarfe" Mamma tace "bawani mai ran ƙarfe, yadda kike ƙashi ɗayan nan"
"Kaii Mamma!, Aminatun kice fah" "Aminatun nawa fa, yadda kike ƙaƙƙarfiyan nan, ya akayi yau kuka Daɗe, baku dawo da wuriba, ina Mubarak ɗin?" Amna tace"Tare dashi muke, kuma wahalar abun hawa akayi a cikin gari fa yau, shiyasa bamu dawo da wuriba"
Shigowa Mubarak yayi yana cewa "sannu Zubaida wato" miƙewa Amna tayi ta katseshi da faɗin, "wato kai inba ka haɗa ni da tsohuwa taba bakajin Daɗi ko?, to muje dama bacci take son yi" ta ƙarashe faɗi haɗi da kama hannun sa ta jashi waje.
"Wai ke Amna in tambaye ki mana?, meyasa bakya tsoron yin ƙarya ne?" Mubarak ya faɗi mata, bayan sun fito daga ɗakin, sai da tayi masa kallon tara saura kwata, sannan tace, "menene matsalarka dani?, ƙaryar tawa cutar da wani zatayi ne?"
"Akan me kuke magana, wace ƙaryar?" Matashiyar matar ta furta hakan yayinda ta fito daga ɗakin ta, da sauri dukkansu biyu suka dawo da dubansu gareta Amna ta ɗan zaro ido kaɗan, "ummee dama, daman Amna" "Ummee magana nake akan abinci, kada yunwa ya cutar damu saboda da yunwa muka dawo" tayi saurin faɗin haka saboda tasan Mubarak yanzun nan sai ya konce mata zani a kasuwa, kuma tasan Ummee bason shashanci take ba.
"Toh me yakawo cutarwa ta yunwa kuma tunda kun iso gida, sai kuje ku watsa ruwa kuzo kuci ai" taƙarashe maganar tana juyawa. Ƙaramar ajiyan zuciya Amna ta sauke tana mai kallon Mubarak, "maƙaryaciya!" "Magulmaci!" Suka furtawa junansu. Suka juyawa kowa yayi hanyar dakinsu.
SALLAHR MAGRIBA
Bayan sallahr magriba, gaba ɗayan su suna zaune a gefen tsakar gida kan babban tabarma, yayin da iska me tattare da ni'ima ke kaɗawa, baƙaramin jin daɗin yanayin suke ba, jin ƙarar motan mahaifin su yasa Mubarak miƙewa dan buɗe masa gate, fitowa yayi daga motar bayan shigowan sa ciki, amsan jakar dake hannun Baba Mubarak ɗin yayi haɗi da yi masa barka da dawowa.
Nufo wurin su yayi fiskarsa da murmushi me haɗe da gajiya, zama yayi akan tabarma, sannu da dawowa Ummee tayi masa, Amna ma tayi masa.
Juyowa yayi gurin Mamma.
"Mamma kin wuni lafiya ya jiki jikin?" "Lafiya ƙalau alhmdllh Baba ya aikin da alama yau ba ƙaramin gajiya kayi ba daga ganin fiskar" murmushi yayi sanna yace "Mammata kenan harkin gane ina tattare da gajiya" dukkan su sukayi murmushi, yacigaba da faɗin, "wani aiki ne ke ƙoƙarin bani wahala, aikine me ɗauke da sarƙaƙiya, narasa gano ta inda zan fahimci lamarin"
"Baba nima ka sani a cikin aikin, zan taimaka muku please" ta ƙarashe faɗi tana haɗe hannu alamar roƙo, dariya Mubarak yayi yana nunata da yatsa yace "sannu akaran bana mai karan bani" haɗe fiska tayi tana hararan sa. Mamma tace "kai banason iskanci fa, kasan dai Aminatu na jaruma ce shiyasa takejin zata iya komi"
"yauwa Mammata" Amna ta faɗi tana murmushi. Haɗi da yimasa gwalo, Ummee tace "Mamma kullum abayan Amna kike" shikuwa Baba kallo kawai yake binsu da shi yana murmushi, musamman ma Amina yana matuƙar mamakin yarinyar,
tunba yauba indai za taji labarin da akace akoi wahala to sai tace itama zatayi,Tun tasowar ta yarinya ce meson kasada, ko labari ake bata indai bana gwagwar maya ba, bata tsayawa jinsa, kuma ita bawani abu bane a wurinta, tayi faɗa da yaro namiji, har Mubarak ita take tare masa faɗa, dukda kuwa namijine shi.
tafison wasan maza, har mamaki sukeyi a inda take koyon faɗa, don yasha kamata tana faɗa da wa'enda suka fita, kuma tayi galaba akansu bata neman tsokana ammafa in aka taɓo ta, batasan yafiya ba saita rama, dan bata barin kota kwana, dan ma a haka yana taka mata birki.
gashi kwayar idon ta launin toka, ganin bakin mutane nason yawa a kanta yasa ta sa glass, indai zata fita waje sai ta saka kafin ta fita, ganin babu abinda yake mata yasa su barinta ta cigaba da sawa, basa zaman 10 minute da Mubarak batare da sun yi faɗa ba, ammafa bakaramin ƙaunar junan su a matsayinsu na en uwa suke ba.
shigar ta kuwa, atamfa baya daga cikin abunda takeso, sai dai tasa dan wani shagali, barta da kayan kanti, dogon riga ko riga da wando, musamman ma riga da wandon, shine 80% ɗin kayanta, dukda kuwa bata taɓa sa rigar da bata wuce gwuiwa ba, kuma hannunsa mai tsawo. Sannan ba matsatstse ba.
Idan ya tam bayeta, "What do you want to be?" Sai ta bashi amsa da "Soldier" sai yace mata lawyer yakeson ta zama, idan Yafaɗi haka kuwa, bata ƙara ce masa komi, sannan bata manta da matsayinta na Ƴa mace ba, gurin kare mutuncin ta da Ƴan uwanta, da kuma riƙe addinin ta. Amna yarinyace da kowasu irin ahali zasu so zama tare dasu.
"Baba Baba!" Mamma ta furta ganin yadda yayi shiru yana nazari, shima dawowa yayi daga duniyar nazarin da yake wa Amna, "na'am Mamma, kutayani da addu'a akan wannan aikin da nasa gaba" "kullum cikib addu'a muke daman, amma zamu ƙara bi iznil lahi" Mamma ta faɗi hakan bayan jin maganar sa.Suma sauran da addu'ar samun nasara suka bishi daga bisani ya wuce ciki.
WASHE GARI
Gurin ƙarfe 07:00am, tana shirin zuwa makaranta, yauma sanye take da riga da wando, saidai design da colour sun ban banta dana jiya ashcolor, haɗe baƙin dogon gashinta tayi da rimbom, sannan tayi rolling ɗin ƙaramin gelen ta, sallama tayi wa Mamma.binta da adawo lfy tayi,
ɗaukar madai daicin bag ɗin ta tayi, da kuma, glass ɗin ta, sannan ta fito, nufar ƙofan ɗakin Mubarak tayi, saida ta duba agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannunta tukunna ta fara magana cikin ɗan ɓacin rai.
"Matsala na da kai kenan, baka daraja lokaci ko kaɗan, kuma fa na faɗa maka yau wannan malamin me kunnuwa kamar na jaki shi zai yi mana lecture 08:00am, yakamata in rigashi zuwa amma kai" tsayarda maganar tayi ganin fitowan Baba.
Cikin shigarsa dake nuna tabbacin shi ɗin babban ɗan jarida ne, "cigaba da faɗa mana, wato malaminki kike cewa kunnuwa kamar na jaki ko?" Yakarashe faɗi yana ƙureta da idanu fiskarsa a haɗe, ƙasa da kai tayi a tinanin ta yariga da yafita, "a ah Baba daman sonake yafito muje kar mu makara."
Alokacin Mubarak ya fito shima cikin shigarsa ta riga dark blue da wando black, harda hula black facing cap, riƙe da wasu takardu a hannun sa, "to sai ku wuce ai" baba Yafaɗi hakan dai dai fitowan Ummee da Mamma, Amna tace "Baba tare zamu?, zaka ijjemu a makaranta ne?".
"A a kuyi tafiyarku ni sai anjima zan wuce, kuyi karatu da kyau, kunga yanzu ana kan gaɓan hutu" ya miƙa musu kuɗi,Ummee ma fatan alkhairi tayi musu daga bisani suka fito, Mubarak ya sa littafansa cikin jakan Amna, amma da masifa tabarshi yasa, haka yake mata kullum, sai lokacin da yakeso yazo ya amsa, wani lokaci tace ita bazata riƙe jakan ba saidai ya riƙe, baza tarinƙa yi masa dakoba kullum, hakan kuma bazai hana gobe ma yasa ba.
Shiga cikin S K U university jamian nasu sukayi, amsan littafi da biro ɗaya yayi, yana yin ɓangaren su yayin da itama tasu ɓangaren tayi, tana shiga ajin ya kwashe da tafi, suna yi mata kirarin, "barka dai barka dai, wanke hannu kataɓa, barka da shigowa, Ƴar baba zakanya"
Taku tafara yi cikin isa, har izuwa mazaunin ta, tana mai jin farinciki à ranta, "yakuke friends" ta faɗi tana mai kai dubanta ta ko ina a ajin, tana ganin masu ƙaunar ta da masu yi mata kishi, amsa mata sukayi "lafiya sanyi ƙalau zakanya" ɗaya daga cikin mutanen da tsakanin su ba nisa yace "ya kika gano mana Haleem shoprite?" Shu'umin murmushi tayi. Tana kai duban ta inda zubi take tareda abokan tafiyar ta, sannan tace,
"I'm telling you Wali, jiya na ƙure ƙaryan me ƙarya, wato yadda naji labarin wannan shoprite ɗin, bahaka na sameshi ba" Wali "kice Zubi ta samu a buhu kenan" dariya Amina tayi tana kuma cewa, "buhun masara ma kuwa" gaba ɗayan su suka maida kallonsu kan Zubi. Suna faɗin "ooo anji kunya masu bagun banza" Zubi kuwa ji tayi kamar ta shaƙo wuyan Amna saboda baƙin ciki, zama kowa yayi a mazauninsa ganin malami yashigo."
KADUNA
Sai da ta tabbatar ta kula da farin cikin ta wato Ammun ta, sannan ta shirya cikin Atamfa riga da skirt da kuma himar iya gwuiwa, tukunnan ta fito riƙe da jakar ta, sallama tayiwa Ammu tukunna tafito, da maganar Hajiya ta kwana, cikin tafiyar ta ta nutsuwa tafara taka falon, saidai tatsaya yayinda ta ga Ruki a gabanta.
budurwace ta ba Safna shekara uku, kuma tafi Safna jiki da tsawo, tanada 'yar kyanta daidai, baƙar riga da wando na bacci ne a jikin ta, Ga tsinanniyar gashin atach ɗin da ta ƙara à ƙoiƙoi-don gashinta, daka ga idon ta kaga hamshakiyar mara kunya.
Safna kuwa jira take kawai taji dame Ruki tazo kuma, saida ta ƙarewa Safna kallo uku saura kota, sannan tace "dady yace kije room ɗin sa" kawai ta furta, sannan ta nufi hanyar fita daga falon. Simi simi Safna ta fara tafiya zuciyar ta cike da tsoro, ko me yafaru yau kuma.
Bayan sallamar da tayi yabata izinin shiga haɗaɗɗiyar ɗakin, ganin inda yake zaune gefe kan kujera, yasa ta nufan wurin haɗi da durƙusawa, saida ta gaishesa bayan ya amsa yace, "my daughter menene yasa kikace kinason barin school, keda nasanki da jajircewa a makaranta".
Saurin ɗago kai tayi, tana kai dubanta gareshi cike da mamakin tambayar tasa, daidai shigowar Hajiya ɗakin riƙe da plate ɗin shayi, mai mai ta tambayar yayi à karo na biyu, kan Safna tayi yunƙurin magana Hajiyar tace "Alhaji kenan" ta faɗi haɗi da miƙa masa cup ɗin shayin tana cigaba da cewa,
"Alhaji kenan to tunda har tagaji da makarantar kawai ka rabu da ita, tunda ita tafaɗi da bakin ta" zuciyar Safna ne yafara zillo kenan abunda Hajiya ke shirin yi mata kenan.
#EN UWA NA, HAR YANZU BAMU SHIGA LABARIN KA'IN DA NA'IN BA FA, INA FATAN KUNA FAHIMTAR LABARIN.
LABARI NE ME CIKE DA SARƘAƘIYA, SAI KUN CIGABA DA FOLLOWING ƊINA SANNAN ZAN WARWARE MUKU KOMAI.
ALKALAMIN TAAKU
Aisha G Umar ✌🏽
______________________________________________________________________________________________
Part 0️⃣7️⃣▶️0️⃣8️⃣
Sai da ya kurɓi tea ɗin sannan yaƙara faɗin "hakan kikeso Safna?" Kanta yunƙura dan yin magana, ya shigo ko sallama babu, tun kan yayi magana idonsa ya faɗa kan Safna, "what are you doing here?" Ya furta haɗi da haɗe fiska, "hee Yazeed, she's my daughter, zata iya shigowa lokacin da takeso kamar dai kai" Dady yabasa amsa. "Amma ba a ƙasa take yin magana dakai ba?, yau meya kawo ta?" Ya ƙara tambaya.
"So take ta bar school, shine na keson naji masalar" "barin school kuma?, to tayi me a gida? rabu da ita dad ba tinani mai kyau bane" Yafaɗi yana hararar inda take, kanta na ƙasa yayin da zucuyar ta ke motsawa haɗi da tsoron abunda dady zai ce.
Ƙara faɗin "baza kibar zuwa school ɗin ba, maza kije ki shirya ki wuce" Yazeed ya faɗa, saurin tashi daga inda take tayi, ta fice, ranta fal farin ciki, koba komai taji daɗin zuwan sa, zata cigaba da zuwa school ɗin ta, Yazeed yafi raga mata akan sauran yaran, hakan yasa koda wasa bata son shiga harkar sa.
"Dad ai da baka saurare ta bama" Dady yace "well dama so nake naji dalilin ta, amma ni kaina ai nafison taci gaba da karatun" Yafaɗi yana miƙewa yayi musu sallama zuwa company.
Bayan yafita, cikin takaici da haushin ɗan nata, tace "kai Yazeed!, wai menene matsalar ka da yin Makarantar Safna ko rashin sa ee?" "No momy she's a little girl shiya sa zatayi tinanin hakan, taya za'abar ta tabar school ta zauna tayi me a Gida?, file ɗin dana baki ajjiya nazo amsa, jirana ma ake"
Cike da haushin maganar sa ta ɗauko mishi file ɗin, batare da sake yin magana ba ya fita.
Binsa tayi da kallon takaici, yadda ya rusa mata ƙaramar plan ɗin ta, ita tama rasa gane kan Yazeed, tsana ya ke nunawa ƙasƙas-tacciyar yarinyar nan kokuwa kula da ita yake?,
Bayan isar ta ƙayataccen makarantar irin wanda ake kira sai ɗan wane da wane, nufan ajinsu tayi, tun kan ta ƙara sa ciki Aminiyar ta ɗaya tilo Raheena ta taho haɗi da yimata oyoyo, ta kama hannun ta har izuwa mazaunin su suka zauna, Raheena tace "ya akayi kikayi latti besty? najira ki, har nayi tinanin tahowa kikayi" ciro littafin ta tayi ba tare da tace mata komai ba.
AMNA
Bayan me kunnuwan jaki ya gama lecture suka fito shan iska waje, zaune suke kusa da wata bishiyar Limis, a kan wasu daga cikin bencin makarantar, suna cin gurguru, su na hira, su huɗu, Amna, Zara, Nabila, da kuma Walid. Zuby ce tazo wucewa itama da ƙawayen ta, Jamila, zaliha.Tsayawa tayi tafara binsu da kallon tsana, wanda bakowa bane ya haddasa wannan tsanar face Amna.
Zuby yarinya ce mai matuƙar ƙoƙari, saidai tauraron ta ya dishe ne sanadiyyar zuwan Amna ajin su, saboda Amna ta take ta ƙoƙari matuƙa, bata taɓa zuwa na ƙarshe aduk abu na karatu, itace ta dawo ɗaliba mafi hazaƙa a jin su, duk da kuwa bata ɗaukar raini ko kaɗan, itafa Amna bataƙi su daku da kowaye ba, indai yashiga harkar ta,
su karan kansu samarin makarantar basa gigin zuwa mata da maganar banza, bare ayi maganar SO, ai basu samu wannanr fiskar ba, saboda daidai take da uban kowa, Hakan kuwa baƙaramin tsana ya haddasa mata, a cikin wasu daga cikin ɗaliban makarantar ba, musamman Zuby da ƙawayen ta, da kuma wasu maza biyar da ba a ajin nasu suke ba.
sunyi matuƙar sa mata ido akan glass ɗin da take sawa, har wasu na tunanin ko tana da matsalar ido ne, so suke kawai wata rana suga idon da take rufewa,Amna ba tada girman kai fannin karatu, wasu da dama sukanzo wurinta tayi musu bayani akan Subject ɗin da basu gane ba.
"Keh Amna duba yadda Zuby ke mana wani irin kallo" Zarah ta faɗi tana taɓo kafaɗar Amna, ahankali ta kai idon ta izuwa inda su Zubyn suke, sai da ta taɓe baki kana tace, "rabu da ita babu abinda zata iya sai kallon ai" kasan cewar babu tazara a tsakanin su yasa maganar ta shiga kunnen Zuby.
Takowa Zuby tayi izuwa gaban su ta dubi inda Amna take sannan tace "ke Makauniya! ki kiya yeni niba kalarki bace, don haka kishiga taita yinki bafa tsoronki muke ba!" "Lallai Zubi, ke har zaki cewa Wanke hannu ka taɓa Makauniya, to kishiga taitayin ki, da alama baki san me ake kira da Danger ba ko?" Wali ya faɗi hakan,
Murmushin gefen baki Amna tayi, Jamila kuwa cewa tayi, "don Allah rufa mana baki, dubeka ko kunya ba kaji namiji ɗaya cikin mata" kwashewa da dariya su Zubi suka yi, a hasale ya miƙe, dakatawa yayi yayinda Amna ta daga mai hannu, ta miƙe ta fara takawa izuwa gaban Jamila, ta fara magana.
"Jamila kike ko Jumla?, inace ke kin taɓa ɗanɗana jan layin kinsan yadda yake, toh zaifi miki salama ki sawa bakinki kwaɗo" riƙe kumatu Jamila tayi yayin da ta tuna marin da Amna ta taɓa yi mata, komawa gun Zuby tayi, ta cigaba da faɗin "ke kuma!, ni nafi ƙarfin in kiyaye ki sai dai in ƙyamace ki, saboda baki fara wanka ba bare har kifita inga abun kiyaya a tattare da ke" tafaɗi tare da juyawa.
Zuby bata iya cewa komi saboda ba ƙaramin gamawa da ita Amna tayi ba, sukuwa abokan Amna dariya suka farayi har da ƙyalƙyalewa, da kyar suka tsaya da dariyar suka furta, "da kyau!". Nabila tace, "wow Amna kinyi wallahi" murmusawa kawai Amna tayi ta furta, "let's go" suka wuce su kabar Zubi da tawagarta.
Kiran Mubarak ne ya tsaidasu, yana faɗin "ashe ta nan kuke" "Aboki na ya akayi yau kun daɗe a class" "bari kawai wali yau dogon karatu mukayi" murmushi dukan su sukayi, Zarah tace "Mubarak anyi abu baka nan" "wani abu?" "gani ya kori ji naso ace kagani" Nabila ta faɗi hakan, Mubarak yakuma faɗin "hmm nasan bai wuce Amna ce ta buga game ba, saboda nasan ta" dariya sukayi.
Wali yace "Kasan sistern ka she doesn't take affence" "it's ok" Amna ta furta ta sa hannu a jakan ta fito da gurgurun da yake daure a leda yaji madara, tana ƙara faɗin "ga naka dan na kusa cinyewa ma" "aiko da kinbiya" Yafaɗi bayan ya ansa, shima ya fito mata da chocolate yace,
"kinga chocolate ɗin da na siya miki, amma bazan baki ba" kwacewa tayi "basai ka bani ba na ƙwata" gaba ɗayan su suka sa dariya. Mubarak bai da Abokai, hakan yasa Abokan Amna ne nasa.
YAU ASABAR RANAR HUTU,
Gari ya waye tangararan, zaune gaba ɗayan su suke akan tabarmar Ummee suna karin kumallo, Amna tace "Ummee me zaki dafa mana da rana" "ko gama cin na Safe bakiyi ba amma kina tambayar na rana" "eh ɗin ina ruwan ka" mubarak yakuma cewa "akoi ruwana ai Ummee na kika tambaya" dakatar dasu Mamma tayi da Fadin
"kai kai so kuke ku ƙware ne?, to bari kuji bamai kawo muku ruwa in ku ka ƙware kuna abu kamar ƙananun yara" dariya Ummee da Baba sukayi, Amna ce ta dubi Mubarak tace, "laah Mubarak da kai fa Mamma take" "a ah dake dai, dan Mamma ɗaukar ki take ƙarama"
Bugu ta kai masa a cinya, tare da hararar sa, "wai Allahna wannan hannun ƙarfen naki kika samin?" Darawa su Mamma suka yi, mamma tace "Ƴan rigima" "yakamata ace Amnata ta fara girki tunda batason akira ta da ƙarama ko?" Baba Yafaɗi hakan yana kallon Amna, Ummee tace
"aikuwa dai gata ta tsani ko zuwa kitchen bere girki itafa kawai a dafa abata" "cab Ummee to ai in mutum yaci Abincin Amna wllh sintirin bayan gida zaiyi ranar, kofa riƙe ludayi bata iya ba" turo baki tayi tana faɗin "Mamma kin ganshi ko!" Dariyar suka ƙara yi, Ummee tace, "yaran nan in ka biye su, baza kaci abinci ba har yayi sanyi,
KADUNA Safna
Ba ƙaramin ruwa akayi ba jiya da dare gari ya ɗau sanyi sosai, hakan yasa bacci yazama mai Daɗi a wurin masu gata, amma Safna kuwa, kasan cewar yau Asabar babu Makaranta, hakan ya zame mata dole da ta tashi tayi dukkanin aikin cikin gida, koda kuwa saukan ƙanƙara ake. Sanin hakan yasa tunda suka tashi asuba sukayi sallah su kayi karatun Alqur'ani, batayi gigin komawa bacci ba.
Lulluɓe Ammu tayi da lallausan bargo, ido suka haɗa da Ammu, ganin yadda ta keyi mata kallon tausayawa yasata tsayawa, ta shapa kan Ammu tana ƙirƙiro murmushi a fiskarta cikin sassanyar muryar ta tace, "my Ammu na kinsan mene ne?, yau tashi nayi da karsashi a jikina sosai, koda ace duk gidan nan akace na gyara zan iya"
Ganin yadda tayi maganar sai itama ta maida mata murmushi, acikin ranta kuwa, tasan Ƴarta so take kawai ta cire ta a damuwa, domin tasan wahalar dake tattare da aikin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 56