nuna maka halin da zuciyarta ya ke a ciki ta ce, "Ba..Babana yana rayé? Bai mutu ba?" Tana ƙarasawa hawaye na sake ƙara gudu kan fiskarta, jikinta ya saki tayi ƙasa a durƙushe.
Ganin halin da ta shiga ba ƙaramin jefa Shuraim cikin tsananin damuwa ya yi ba, cike da tausayawa ya tsugunna a gabanta yana rarrashinta, kamar wacche ta tuna da wani abu, sai tayi saurin sa idonsa à kan na sa, tare da miƙewa, shima tashi yayi yana kallonta ganin yadda ta yi, "yana ina!? Ina Baba n'a ya ke?" Ta faɗi tana jiran amsarsa cikin ƙaguwa, sai da ya gimtse ido ya buɗe kana ya ce, "nima ban sani ba yanzu kam, amma ki dakata kaɗan, bari in kammala jin komai daga Ali" yana faɗi ya maida wayar kunnensa, tare da miƙewa, kasancewar daman Ali na kan layi bai katse ba, "ina jinka Ali".
Nan Ali ya gama yi masa bayani akan duk binciken da suka yi, bayan Shuraim ya gama jin komai, sannan ya ce, ya da Ali ya turo masa adireshin wurin, yana faɗi ya sauke wayar haɗi da kallon Amna da ta riga ta miƙe, jira take kawai ta ji abun da zaice, domin sanin inda mahaifinta ya ke, "me ya ce! A ina ya ce maka Babana ya ke?" Tayi masa tambayar a jere.
Kafin Shuraim ya bata amsa, wayar tayi ƙarar shigowar saƙo, ɗagawa yayi yana duba abin da Alin ya turo masa, take idanuwansa suka yi zuru, saboda ganin adireshin da aka turo masan, ganin yadda yayi ne yasa Amna sake tambayarsa, "menene? Ka gane inda Babana yake? Yana ina? Me yasa ka sauya fiska? Ka faɗamin inje in ɗauko shi!" ta faɗi jikinta n'a rawa, zuciyarta na ƙara, barin kallon wayar yayi ya maida kallonsa kanta ya furta, "ba zaiyu ba!" cikin rashin fahimta, da kuma tsoron kar dai wani abun aka turo masa game da Baban, kar dai wani abu ya sami mahaifinta, saboda jin wannan maganar na sa, tayi hanzarin cewa, "me kake nufi da bazaiyu ba? Kar ka ce mun wani abun aka ce ya same sa".
Sai da Shuraim ya jin-jina kai ya ce, "dama bamu da masaniya, a kan a wani hali mahaifinki ya ke, amma location ɗin da aka turo min, wuri ne mai matuƙar haɗari" kallonsa kawai Amna ta ke, ta kasa sake tambayarsa, domin bata gama gane abin da ya ke cewa ba, domin ita babu inda zai zame mata haɗari in dai akan ɗauko mahaifinta ne, cigaba da magana Shuraim ya yi da cewa, "wannan wurin hatsarinsa ya wuce tunani, ba wai guri ne kamar ko wanne ba, ya kasance kogo ne mai duhu, da kuma hatsari".
Cikin jin haushi da maganarsa Amna ta share hawayenta sannan ta ce, "har yanzu babu abun da na fahimta a mganarka sai hatsari, hatsari, me abun da ba zaiyu ba a kan ɗauko mahaifi na a kogo?" Numfashi Shuraim ya sauke sannan ya kuma maida hankalisa kanta, domin ya ga kamar bata gane abin da ya ce ɗin ba, "Amna! kin dai san duk abin da aka kira da kogo, zai yi wuya a ce bai da wani matsala ko? To wannan gurin yana da banbanci da ko wani irin kogo da kika sani, hatsarinsa ya wuce faɗa a baki, duk da cewa ban taɓa zuwa ba, amma akwai wa'yanda suka rayukansu a cikin sa da dama, kuma na sani, masihirta ne a cikinsa, kuma muna da kyakykyawan zaton cewa yana da haɗaka da Zabba-ba, saboda à baya na fara zurfafa tunani akan haka..."
"Toh sai me?!!" Amna ta katse bayanin da ya ke mata, da tsananin mamaki ya cigaba da kallonta, kafin ya samu damar yin magana ya sake jin maganarta, "idan kai baza ka iya zuwa ba, ni zanje! zanje in dawo da mahaifina ko ta yaya, ba zan sake barin wani abu ya same shi ba, a baya nayi tunanin cewa na rasa shi, tun da yanzu kuma na gane yana rayé, to ba zan sake jira ba, zan je in taho da shi da kaina, bana buƙatar haɗaka da kowa, kawai abin da nake so daga gareka, shine ka bani adireshin wurin" Ta yi maganar cikin nuna zata iya ko wani irin gwagwarmaya, don dawo da mahaifinta.
"Me kike faɗa ne Amna? Me yasa kika fiye jin kan ki da yawa haka? Me yasa idan ana nuna miki gabas ki ke yin yamma? Babu abin da kika sani game da wannan wuri, nima da ban kasance a cikin mutanen da suka yi dana sanin zuwa ba, na san illarshi, na san haɗarin wannan kogon, amma ke kuma kina yin wata magana daban" cewar Shuraim yana sake nusar da ita hatsarin da ke tattare da wannan wuri, amma Amna ta ƙi amincewa, ta dage ita dai ya bata adireshin kawai, duk yadda zai bi da ita ta ƙi amincewa.
"Shikenan na ji, kuma na amince a kan zamu je yanzu, amma kiyi haƙuri mu shirya kafin mu doshi wannan wuri" "Babu wani shiri da zan bari ayi, magana ake fa a kan Babana, Mahaifina! Wanda sanadiyyar shi na kasance a duniya, wai ko baka fahimta ba ne?" Ta faɗi cikin ɓacin rai,domin tana jin babu abin da zai dakatarda ita zuwa wannan wurin, ko da ma ace ya ƙi bata adireshin zatayi duk mai yuwa don ta je wannan wurin.
Ganin ta dage sosai hakan yasa shi amincewa kawai, domin ya san ƙaunar mahaifi dole ta dage, hakan ya sake nuna masa yadda ta ɗauki mahaifinta da mahimmanci, amma fa duk da haka yana fargaba sosai, saboda shi kaɗai ya san abunbuwan da ya sani, à binciken da yayi kan wannan wuri, jin ya amince yasa Amna saurin sake cewa, "shikenan to muje!" "A ah bai kamata muje haka direct ba, kin san kina da meeting ko? Sannan kuma ya kamata a ce mun fita ta yadda babu wanda zai ɗauka ba kya office, gudun matsala" shiru tayi tana sauraron kalamansa, sannan ta ce, "na gane, to amma ya za'ayi mu fita ba tare da mutane sun ankara ba?"
Shiru Shuraim yayi yana tunani, "akwai wata hanya" cewar Amna tana kallon Shuraim, bayan ta tuna da wani abu, Shuraim ya ce, "wacche kenan?" "Ranar da na fara zuwa wannan companyn, Dady ya nuna min ko ina da ke cikin office, sannan ya nuna min wata ƙofa, wacche ya ce min hanya ce da zata ɓulle zuwa fita waje ta baya, ba tare da kowa ya sani ba, ina ganin wannan zai yi amfani" ni sawa Shuraim yayi sannan ya ce, "tabbas wannan shawara ce mai kyau" "to amma maganar meeting fa?" Faɗin Amna cikin damuwa.
"Raheena, Raheena ƙawarku, zata taimaka mana ƙorai, abun da za'ayi yanzu, kije ki sameta daga ke sai ita, ki bi hanya mai sauƙi don yi mata bayani, ba tare da kowa ya ankara ba, sannan ba tare da itama ta san da wata matsala ba" Amna ta ce, "tabbas Raheena zata taimaka mana, kuma na tabbata ba zata bi diddigi ba" "yauwa to yanzu abin da za'ayi ke ki je, ki sanar da Raheena dabarar da zata yi, sannan kar ki damu, n'a san a hanyar ki ta fita ba zai kasance da wata matsala ba, tun da shi Dadyn da kansa ya nuna miki wurin, so ni kuma zan fita waje in jirayeki, in yaso bayan kin samu damar fita ta bayan, sai ki kira ni, ki sanar da ni inda kike".
Girgiza kai ta yi sannan ta ce, "ok to amma matsalar wayar ta fashe ai" ta faɗi tana kallon wayar da ke kwance a ƙasa raga-raga, ciro wata wayar da ke aljuhunsa yayi, sannan ya miƙa mata, amsa tayi sannan ta juya ta wuce da sauri. Koda ta koma, kiran Raheena tayi office ɗinta da hanzari, domin kuwa so take kawai ta ga ta bar company, bayan ta kammala sanar da Raheena, Raheenar ta ce, "ba damuwa, ki bar min komai, zanyi iya ƙoƙarina insha Allah" "yauwa na gode miki ƙawata, to yanzu bari ni inje".
Amna na gama maganar ta miƙe ta shige wannan ɗakin hutun, haɗi da gyara gelenta, itama Raheenar miƙewa ta yi ta fice, direct wannan ƙofar Amna ta nufa bayan shiganta, tana tuna maganar Dady na cewa amma sai akwai abu mai mahimmanci sannan zata bi ta wannan hanyar, sa numbobin da Dady ya ce ta sauya tayi, ai kuwa ƙofa ta buɗe babu ɓata lokaci, hannu ta sanya ta murɗa mariƙar ta janye, sannan ta fita ta kuma tura ƙofar ta rufeta, a hankali ta fara tafiya tana kallon wurin, da mamaki ta ke bin ko ina da kallo, ganin yadda wurin yake kamar ana gyara shi, babu wata yanar gizo ko kuma tashin wari, da ke nuna rashin zaman mutane a wurin.
Komai saf-tsaf hatta ƙasan da take takawa, hanya ɗaya kawai take bi, duk da bata da tabbacin hanyar da zai fitar da ita ne, kasancewar wurin na da girma, tafiyar kusan minti shidda ta yi, sannan ta fara bin wani step mai tsawo sosai, ta jima tana taka shi har ta sauka, mamaki bai bar fiskarta ba, sai tunani ta ke ta jerawa cikin zucinta, me alfanun barin wannan wurin haka? Da kuma ɓoye sa? Ko da tana jin cewa dole akwai masu shigowa ciki, idan ba haka ba taya zai kasance babu wata alamar datti, to idan ma mutanen suna shigowa ta ina? Sai dai duk wannan tambayar da ta ke, babu wanda ta samu amsarshi.
Bayan ɗan dogon tafiyar da tayi sai gashi ta iso wata ƙofa, tsayawa tayi tana bin ƙofar da kallo, da tayi zaton zata samu ƙofar da faɗi, amma sai gashi ta samesa tamkar wanda ta buɗe ta fito ɗazu, "to yanzu ya zanyi in buɗe ta?" Ta yi wa kanta tambayar, tun da dai babu mukulli à hannunta, taɓa ƙofar ta fara yi tana dubawa, ko zata samu wani hanyan don buɗe sa, zuciyarta cike da tunane-tunane, jingina jikin ƙofar tayi tare da ɗaga kanta tana kallon sararin samaniya, ta rasa me zata yi, kenan komawa yanzu za tayi?.
Sauke idonta tayi tana sake yin gefe da idonta, wani baƙin abu mai kama da penti ta gani, da sauri ta bar jikin ƙofar haɗi da sanya hannu tana gogewa, cikin sa'a kuwa ta ga ya n'a cirewa, ganin hakan yasa ta fara yin sauri don goge shi, cikin wani ƙarin mamakin ta ɗan buɗe ido, saboda ganin numbobi sun bayyana a wurin, ba tare da ta jira wani tunani ba ta fara sanya numbobin da ta buɗe wancan ƙofar, tana iyawa ƙofa tayi ƙara alamar ta buɗe, buɗesa ta yi ta fice waje sannan shima ta ja ta rufe, ba tare da ta yi tunanin in ta dawo ya zata yi ta koma ciki?,
Juyo da idonta ta yi kan gurin da ta fito, à wani babban unguwa ta ɓulla, shiru gurin ya ke duk da kuwa a kwai gidaje, ciro wayar da ke cikin aljuhunta ta yi don kiran Shuraim, sai dai babu network q inda ta ke, sai da ta juya ta ko ina tana kallon wurin, sannan ta fara bin hanyar da ya ke daga hagunta, network ta gani ya dawo, hakan yasa ta kira Shuraim, ɗagawa yayi ita kuma tana sanar da shi cewa ta fita daga cikin companyn, sannan ta sanar da shi inda ta ke, bayan ta kalli signboard, sannan kuma ta kusa zuwa kan hanya.
Bayan lokuta sai ga Shuraim ya zo, yana mamakin yadda hanyar ta kasance kamar ba kowa a cikinta don shi da kansa ma ta wayarta ne ya gane inda ta ke, bayan Amna ta shiga motar suka kama ɗamaran zuwa kogo, zuciyar Shuraim sam yaƙi natsuwa, domin so yayi sai sun shirya da kyau, sannan sun samu wata hanya wanda zasu aiwatar da abun cikin sauƙi, amma Amna taƙi yarda, ita tana jin kanta wata jaruma.
Tafiya sosai suka yi, har suka isa kan hanyar dajin, à gefe suka tsaida motar sannan suka fito, juyawa Shuraim yayi yana kallon Amna, itama juyawan tayi tana kallonsa, sannan suka juya da idanuwansu kan dajin, sai da suka ja dogon numfashi a tare sannan suka sanya ƙafa a ciki, bayan addu'ar da suka yi cikin ransu.
Tafiya suke yi suna ratsa cikin dajin, babu abin da yake tashi sai kuka kamar na tsuntsaye kamar ba tsuntsaye ba, duk da kasancewar rana baiyi ba amma ciyawun da suke takawa sai ƙara ya ke yi, bishiyoyisai kaɗawa suke yi, "ke madam C.E.O, ki bari muyi komai à hankali, ba wai kisa kanki kai tsaye ba, kar ki ga don kin yi faɗa da samarin nan na ɗazu, wannan lamarin yasha babban da wancan, ki dai na wani sa kai kamar ke ke da dajin" cewar Shuraim cikin saita muryarsa, gudun kada yayi amsa kuwa, ya faɗi hakan ne lura da yayi Amna kamar babu abin da take ji a zuciyarta mai sunan tsoro, sai wani tafiya ta ke kai tsaye kamar mai shirin shiga ɗakinsa.
Juyowa Amna tayi tana kallon Shuraim yayin da yake maganar, kamar zata yi banza da shi, sai kuma ta juyo ta dubeshi tana cewa, "da na ɗauka kai jarumi ne, ashe dai kuskuren fahimta ne? Rago kawai" Haɗe fiska yayi itama ta haɗe n'a ta, ya ce, "zaki ga rago nan gaba" sannan suka cigaba da kutsa kai a ciki, sai da suka share fage kafin suka samu isowa bakin kogon, kowa sai nishin gajiya da tafiya yake yi. Suna laɓe da bin bakin kogon da kallo, baƙi wuluk ne jikin gininnsa, sai wasu bashiyoyi masu ban tsoro, babu ganye ko kaɗan a jikinsu, rataye suke da wasu layoyi kala-kala a wurin, sai wasu rubutu wanda basu san na menene ba, sai kuma abu kamar zanen kan ƙorongol a jikin baƙin kogon, duk yadda zan suffanta muku ya wuce haka, saboda dole ka ji razana a zuciya, domin duk wanda ya kalli bakin kogon nan dole ya yi ribas, don bai bayyanar da akhairi ba daga ganinsa,
Duk jarumtar da Amna ta zo da shi, sai da taji zuciyarta ya razana da wannan wurin, domin yadda yake kewaye da surku kala daban-daban, juyawa tayi suka haɗa ido da Shuraim da shima tuni zuciyarsa ta cika da tsoro, a hankali Amna ta ce, "dole ne in shiga wannan wuri, koda à ce zai zama silar tsayuwar numfashi n'a, dole in shiga in fito da mahaifina" ta faɗi domin bazata ta taɓa sarewa a kan ɗauko mahaifinta ba, Shuraim kuwa kallon da dama ba barinsa yayi ba, ya cigaba da yi ganin taurin zuciyar Amna, amma ya kamata shi ya fita ma, tun da shine namiji.
Don haka ya furta, "Muje!" Juyo ido tayi ta dubesa, sannan suka kaɗawa juna kai, alamar eh zamu iya, sanna suka fara durfanar wannan kogo, shiruuu kamar an garƙame kunne haka suke ji, iskar da ke kaɗawa ta lafa ta tsaya cak, duk da jin haka bai sa sun tsaya ba, bayan sun kai gab ƙofar shiga suka ji wata irin jiri na ɗibarsu, wanda suka ji yana juyar musu a kai tamkar guguwa, hannu suka sanya duka a kansu tare, suna jin kamar suna juyawa gaba da baya, da wani ƙarfin zuciya Shuraim ya samu damar fito da wata addu'a a bakinsa, Amna ma ta amshe da ƙyar, kamar anyi ruwa an ɗauke haka su ka nemi wannan jirin suka rasa.
Idanuwansu ne ya fara kaɗawa, sai da suka sake haɗa idon juna, sannan suka doshi shiga gadan-gadan, nanma suna sanya ƙafa a ciki suka ji kamar wata iska mai ƙarfi ta kaɗa su, harda wani sauti iskar yayi, wuuuuuuuw, ba tare da sunyi tunanin komawa baya ba suka cigaba da shiga ciki, duk da cewa gaba ɗaya zuciyarsu tana harbawan fargaba da matsanancin gudu, amma sai suke bata ƙwarin guiwa, takawa suka cigaba da yi suna yin nisa, a inda suke suna hango can gabansu, duhu ne sosai babu alamar haske, babu abun da yake tashi sai ƙarar ƙafafuwansu da suke takawa, wanda suke jin sautin kamar ba nasu su kaɗai ba ne, ko da sunfi ɗauka ko ƙafafuwan n'a su ke amsakuwwa.
Wani irin ƙara suka ji mai ƙarfi ta bayansu, wanda ya girgiza kawunansu, à take suka juya cikin firgici da bugun zuciya, zaro ido sosai su ka yi, ƙirjin ko wannen su n'a sake harbawa da ƙarfi, sakamakon abun da suka gani a bayan su, sai kuma suka dawo kallon junansu a razane, har numfashinsu na sarƙewa jikin su ya fara wani irin harbawa kamar jannareto.
ABUJA.
HOSPITAL.
Uncle Musa ne ke tafiya cikin asibitin, shi ɗin babban mutum ne, domin da ganin fuskarsa ba ƙaramin mutum ba ne, wani ɗaki ya dosa yana tunani a ransa, yana isa ɗakin ya sanya hannusa ya murɗa hannun ƙofar, da sallama ya shige haɗi da ɗaura idonsa kan wata budurwa, da ke zaune a akan gadon jinya, isa gabanta yayi ya zauna kan kujerar da ke gefenta, haɗi da ƙura mata ido cikin tausayawa, itama ɗago fararen idonta ta yi zuwa kansa, ta kasance baƙa ce sosai, babu inda yake da haske à jikinta fa ce tafin hannu da ƙafarta, da kuma idanuwanta, in banda wannan wuri to ba inda ya fita da haske.
Saboda baƙa ce ta bugawa a jarida, sai dai à kirata da dark black ba ma black ɗin ba, kuma baƙin ma ba irin wanda ake kira black beauty ba, domin yananan kamar furtsa-furtsa, wato dai babu kyan gani, sai kasha ƙonewa tayi kuma wurin ya kasance babu farin ƙuna, idan ka zauna dap da ita, kuma ka ƙura mata ido irin na ƙurillan nan, to ba shakka sai kaji ka ƙyama ce ta, da ba don kusancin da yake da ita ba, da ƙila ba abin da zai sa ya kasence dap da ita, "yata" ya furta tare da sauke idonsa yana jawo takardun da ke gefensa, à hankali ta furta, "na'am uncle".
"Yau zamu bar wannan asibitin, da kuma garin m'a baki ɗaya, an riga da an sallame ki, tun da hakan ya faru kuma babu abun da ya kamata mu jira yanzu" rausayar da kai tayi tana jin wani abu ta cikin ranta, mai kama da ciwo, yadda rayuwa tayi da ita, amma ba komai, Allah na nan, kuma shi ne maganin duk wani mumini.
RUKI.
Ranar da aka kawota, bayan kowa ya wuce an barta, sauya kaya tayi zuwa rigar da ta sacewa Amna, wanda Yazeed yayi mata kyauta da shi, rigar yayi mata kyau, ta zaɓi ta sa ne domin ta faranta ran angonta, duk da cewa da Amna ce ta sanya rigar sai ya fi mata kyau, amma ita ɗin ma a haka ya ɗan haskata, tana zaune babu abin da take jira kuma take dako fa ce ta ga mijinta Jaiz, domin idan har ya cika duk wani abu da ya sanar da ita, to fa ya riga da ya ɗaga darajarta, wayyo daɗi cikin ranta.
Zata samu kuɗaɗe masu tarin yawa, saboda tun da Amna ta fara aiki a company, shikenan ta rage fantamawa, ta sha zuwa gurin Dady akan me yasa ya rage basu kuɗi, amma sai ya ce mata ai babu abin da ta ke da kuɗin sai albazaranci, shi kuma albazaranci bai da kyau, to ita kuma Hajiya dama tana da maƙon tsiya, domin kuwa hatta su dakansu 'ya'yan na ta ba wai ta ware su ba ne, indai harka ce ta kuɗi to fa tafi son ta ga an miƙo, ba wai ita ta miƙa ba, idan suka takura ta da roƙo kuma su kai mata magiya, da ƙyar ta ke basu, kuma kaɗan zata basu ba mai yawa ba, dama Dady ne mai ba su duk sanda suka buƙaci abu.
Tana zaune tana jiran zuwan Jaiz, kamar à sama ta ga anturi ƙofa, da sauri tasa hannu tana gyara zaman rigarta mai kyau, haɗi da gyara zama, sannan ta juyar da idonta zuwa gurin ƙofar don tozali da fiskar mijinta, mai ƙaunarta kamar yadda yake sanar mata ako da yaushe, sallama ya fara shigowa kafin ganin mutum, "Assala alaikul" zuciyarta ce ta bada wani irin rasss, ba wai don ba'ayi sallamar daidai ba, a ah, sai dai don muryar da taji yayi mata sallama, wani irin murya ce mai wani irin launi, wanda zata iya faɗin kunnuwanta basu taɓa sanin da wannan muryar ba.
Sai kuma ta tashi da saurin tashin hankali ta miƙe à tsakiyar gadon, gabanta yayi mugun faɗi, zaro madaidaitan idonta tayi tana kallonsa bayan ya shigo, zuciyarta na yi mata wani irin karar fargaba, take jikinta ya fara kyarma, tana jin tamkar fitsarin da bata san tana jinsa ba ya taso mata.
Last part.
___________________________________________________
Akwai magana?.
Amna da Shuraim gasu à cikin kogon masihirta, kogon matsafin Zabba-ba, wai à ciki Baba ya ke, shin zasu yi nasara a wannan kogon? Zasu samu damar fitowa da mahaifin Amna? Zasu tsira daga cikinsa? Me suka gani a bayansu, wanda ya haddasa musu tsoro? Hmmmm.
Waye ne wannan uncle musan? Me yasa ya shigo cikin labarin shida yarinyar da ya kira 'yarshi?
Ga amarya Ruki kuma, shin menene ya tada mata hankali haka da ganinsa? Waye ne ta gani? Waye Jaiz?
Ku biyo ni don jin komai. Alƙalamin ✍🏼
Aisha G Umar, {Mrs Umar} [Gimbiyar Fasaha]👸🏽
______________________________________________________________________________________________
Part1️⃣3️⃣7️⃣▶️1️⃣3️⃣8️⃣
📲 Writing✍🏼
Aisha G Umar {Mrs Umar}👸🏽
Ƙarasa shigowa yayi yana kallonta, sannan ya saki wani murmushi da ya bayyanar da karyayyun haƙoransa waje, tana tsaye à kan gadon fiskarta cike da tsoro, ta sauke idanuwanta kansa don ƙare masa kallo da kyau, daga ƙafafuwansa ta fara, sai dai tsawon wandon da ya saka ya hana ta gani gundulin ƙafarsa, yin sama ta fara yi da idanuwanta, gajere ne sosai, amma baza a kira shi da wada ba, don ya ɗan ɗara wadanni kaɗan, sanye ya ke da kaya baƙi sannan ga malum-malum a kai, wanda kalan kayan ya saje da baƙar launin fatarsa, idonsa ɗaya à kulle ɗayan kuma à buɗe, wanda zai iya tabbatar maka da cewa da alama ido ɗaya ya ke da, bakin nan wani wargajeje da shi kamar bakin randa, bai da fasali sam, yadda ka san jaririn aljani, yana riƙe da wata sanda da ya fisa tsawo.
Wani ihu ta saki bayan ta gama ƙare masa kallo, ihu ta ke yi sosai kamar zata tsaga gini, toshe kunnensa ya yi da hannun da bai riƙe sandar ba, ai kuwa ta ga hannun kamar kuturu, haba sai ta ƙara volum ɗin ihun da ta ke cikin tashin hankali sosai, "wayyo Allahna n'a shiga ukuna! wayyo Allah taimako a taimaka min, wayyo Hajiya ki kawo ɗauki, rayuwar autarki Ruki ya faɗa cikin masifa, ranar darena na farko a gidan miji na fara da tozali da aljani, wayyoo n'a shiga uku na lalace!".
Ruki na ƙarasa faɗi ta saki kuka mai cike da tsoron abin da ta gani, mannewa jikin bango ta yi kamar zata zama plestan da ke jikin bangon, wani dabara ne ta zo mata, na ta rufe idonta ta buɗe ƙila dai tunani ta ke yi kawai, ko kuma tana mafarki a baccin da bata san yaushe ya ɗauketa ba, don haka ta manne idonta na ɗan mintuna, shi kuma wannan mutumin sai kallonta yake yi, bayan ta ɗau minti kusan uku ta kuma buɗe idon, a tunaninta tana buɗewa zata ga babu shi, amma sai gashi ta kuma sa idonta à kansa, kuka ta sake yi tana haɗe hannuwanta duka biyu ta fara roƙonsa.
"Ranku ya daɗe dan Allah ku min rai, kar ku ɓata min wannan rana, don Allah na roƙe ku, idan laifi na yi muku ku yafe min, dama ku ke ganinmu ba mu muke ganin ku ba, ƙila ko na yi muku laifi ma ban sani ba" tana faɗi ta kuma rushewa da kuka, sai ƙara mannar ginin ta ke kamar wata kaɗangariya, da mamaki yake kallonta da wannan fiskar ta sa, buɗe bakinsa ya yi ya fara magana, yayin da harshensa ke wani lallauyewa, "haba atata, ni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 56