Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 1._ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free book* _Follow me on Wattpad@Billyfari9https://www.wattpad.com/story/310168898?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=WMb0QI%2F8tw%2FeCMe6tTqjkL9%2BJSTzXi4R0TeGKoTlDIO6AQJoOSzCfoSJAJXAprgtXUml1Wz9oTQW6GxRQxkJ2UqWCGOUTfCmcV3W3JfXc6hjdEkvOvANyT90h6stxTib_ _Bismillahirrahmanirrahim, wannan littafi bana kud'i bane(free book) ne don faranta zukatan masoyana, haqqin mallakata be, banyarda wani ko wata su saidamun dashi ba ko kuma su karanta mani abu ta YouTube har saida izinina!, na fad'a banyarda ba har saida izinina📵❌, don haka akula!😍_ *A* guje ta shigo cikin makarantar da mota kasancewar qarfe 8:00am na safe take da lectures, gashi kuma har takwas da rabi ta soma wucewa, sanin da tayi cewa babu jituwa tsakaninta da malamin da zai d'aukesu darasin yau da safe d'in saboda irin malaman nan ne masu muguwar matsala had'e da takurawa ga d'alibbai yasa ta sake take wutar motar ba tare da ta damu da dokar rashin yin gudu akan titunan makarantar da kewayenta gabanta na wani irin muguwar fad'uwa, ALLAH ALLAH kawai takeyi ta ganeta a cikin ajin duk da tasan zuwanta adaidai wannan lokacin baqaramar matsala zai iya haifarwa tsakaninta da malamin ba matuqar ta riskesa aciki, Tana wannan tunanin ne ba tare data ankara ba daidai lokacin da take qoqarin karya hannunta tashiga kwanar da zata sadata da b'angaren da suke daukar lectures d'in tayi saurin taka wani irin wawan burkin da yasa har seda kanta ya kusan buguwa da sitarin motar sanadiyar jin ta bugi wani abu da batasan ko meye ba agabanta, da sauri ta d'ago kanta cikin tashin hankali had'e da zaro idanuwa tasa hannayenta biyu ta safe kanta tana fad'ar "innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" cikin firgita da kid'imewa ganin aika aikar da tayi, Wani kyakkawan saurayine dake sana'ar saida kwakwa da dabino ta kad'e dake qoqarin fitowa jikin kwanar adaidai lokacin data kawo da ake kira MM MAIDABINO wato (Muhammad muhriz mai dabino), sai d'alibbai suka qire sunan suna kiransa da MM MAIDABINO saboda yayi masu sauqin fad'a, duk da irin tarin raunin da sana'arsa tasa ta nuna ajikinsa hakan bai hana tsala-tsalan 'yan matan dake makarantar bibiyarsa da kalmar so ba, saidai kash! Shi ba wannan bane agabansa, don kuwa yaqi basu dama ko sakar masu fuskar da zasu samu bayyana hakan agaresa, kawai shi dai abunda ya sani kuma ya saka a gabansa baiwuce sana'arsa ba, wacce a kullum yake d'auka a matsayin rufin asirinsa a idanuwan mutane, mutum ne shi miskili da bai fiye son duk wata harkar da zata sakashi doguwar magana ba har saida dalili, yanada tsatstsauran ra'ayi da kuma kwar jini sosai, shiyasa duk qwaqwar 'yan matan dake bibiyarsa basa iya tunkararsa kai tsaye su bayyana sirrin zukatansu, yanada sanyin hali sosai da sauqin kai wanda sune suka janyo masa tarin soyayya da kuma dad'in mu'amala acikin mutane, sosai yakan fahimci yarinyar da duk tazo wajensa da manufin soyayyar aranta saboda sauyin da dafin so ke saurin haifar mata alokacin ba tare da sanin taba, amma yana ganin hakan ko mutunci yake da yarinya zaiyi saurin sauya mata fuska ta yanda da kanta zata shiga taitayinta tare da had'iye abunda tázo dashi aranta, sau tari 'yan mata nashan yin fad'a akansa ba tare daya sanma sunayi ba sai dai in ya ji labari acikin makarantar, shima girgiza kai kawai zaiyi yace ALLAH ya kyauta, kyakkyawane naqin qari dake da hasken fata sosai tare da matsakaicin tsayi da kuma qiba, a yanda jikinsa ya nuna azahiri bazaka tab'a cewa shid'in mabuqaci bane har sai ka ankara da irin kayan da yake sakawa kala biyu da akoda yaushe suka zame masa tamkar wasu yunifom, doguwar riga jallabiya baqa da take had'awa da wani wando bula sai kuma wani yadi ruwan kalar ganye riga da wando irin d'unkin mutanen qauye da ake kira zauren d'ari, wanda yauma su d'inne ajikinsa, Fitowa tayi da sauri cikin motar tana yarfi da hannayenta had'e da nufar wajen data hango wani abokin sana'ar tasa da ake kira Jabir ya tallabosa, take ta sake kid'imewa tare da qarasawa wajen ganin yanda goshinsa da hancinsa ke fidda jini sai faman lumshe idanuwa yakeyi dake nuni da cewa ya bugu sosai ba kad'an ba, acan gefe kuma baronsa ne ya kife gaba d'aya a qasa komai dake ciki ya watse akan titin, dafe goshi tayi kamar zatayi kuka tare da kallon kayan dake qasa zube sannan ta juyo ta maido kallonta agaresa, "Subhanallahi! Don ALLAH kayi haquri, wlh ban lura da zuwanka ba, I thought babu kowa ne a gabana shiyasa na shigo aguje saboda in samu inyi attending lecture d'in wancan malamin...." kafin tarufe baki taji Jabir dake riqe dashi ya ce, "Dallah malama rufa mana baki, dama ku 'ya'yan masu kud'in nan haka kuke wlh, sam bakwa d'aukar talaka da wani mutunci ko kad'an, gani kukeyi ki kad'aine mutane su kuma kun maida su tamkar wasu dabbobi" "Nooo... Wlh ba haka bane!, kawai a tsorace nake, ina kaima kasan halin wasu malan nan tunda a cikin makarantar nan kake wuni kuma kana jin irin abubuwan da suke tafkawa, ALLAH yanzun nan ne akan abu kad'an zasu maido d'alibi baya ko kuma wata shekara saboda tsabar mugunta, musamman idan suka tasoshi agaba, pls don ALLAH kayi haquri MM ka ji?..." Sake watsamata wata uwar tsawar Jabir da yayi kutunkutun yana masifa yayi a hasale kafin taqarasa maganar da tasata saurin zabura har idanuwanta na kawo qwalla had'e da cewa, "Rufa mana baki dallah, wannan ai shirmene kikeyi, shikenan don malami nada tsanani sai akace kuyi gudu akan titi? Ko anfad'a maki cewa mu bamuyi bokon bane? irin wannan damuwar mu maza mu zamu fad'eta bawai ke mace da murmushi kawai zakiyiwa malami ya baki *A* ba!, 'yar rainin hankali kawai to babu inda zakije har sai kin kaisa asibiti ko yanzun nan naje nakai qararki ga hukumar makaranta, Ina kuma kinsan cewa dokar bata baku damar yin gudu hakan ba amma shine kikayi sai kace titin gidanku ne" "Ba haka bane wlh.." "Karki renawa kanki hankali da wayau, zaki wuce ne muje ko kuwa..?" Kafin yaqarasa yaji muryar MM da tunda ta qaraso wajen ya kafeta da idanuwa tamkar bashi bane ke neman agaji saboda tsananin azabar buguwar da yayi, amma da kallo d'aya sai yaji ya nemi duka ciwon dake jikinsa ya rasa duk dako har lokacin jinin dake zuba bai dena zubar masan ba, cike da qarfin hali ya ce "Ya isa haka Jabir mana, barta taje ai tsautsayine, ALLAH ya riga daya tsaro yau hakan zata faru dani ta sanadiyarta, jeki, ba komai kinji ko" ya qare zancen yana nuna mata hanya da hannu alamun zata iya tafiya, jikinta na rawa tanufi wajen motar had'e da cewa, "Nagode sosai MM" yayi mata murmushi had'e da kad'a mata kai ya lumshe idanuwa ya bud'e alamun tatafi ba damuwa, Har ta tada motar tata sai kuma ta kashe ta juya ta d'auki gorar ruwa had'e da ciro handkachif a jikkarta dake gefe ajiye tafito ta nufi wajen da suke tsaye Jabir da yayi mutuwar tsaye d'azu baki a bud'e yana zazzaga masa masifa akan don me zaice tatafi, cike da tausayinsa ganin yanda ya dafe goshinsa dake jini kamar zatayi kuka ta ce "Sannu, ga wannan ka gyara fuskarka kafin nafito lectures sai muje asibitin ko" taqare zancen tana miqo masa ruwa da handkachif d'in dake hannunta, rufe bakinta keda wuya taji Jabir ya ce, "Mtssss...ka gani ko MM!, wlh duk laifinka ne da kace yarinyar nan tatafi, dubi 'yar rainin hankali don tarena maka da wayau me take qoqarin yi, ka ce abarta taje saboda uzurin data bayar gashi don ta maida mu sakarkari ta sake dawowo, ALLAH kabarni na gyara mata zama tunda ta raina wayon mutane" Daga ita har MM d'in juyowa sukayi suna kallon Jabir dake ji tamkar ya kaima MM d'in naushi tsabar takaici, cikin marairaice murya tace, "Kayi haquri mana, ai na fad'a maka bada nufi nayi ba, sannan kuma meye laifi don na kawo masa abunda zai gyara fuskarsa?, ina dai shine wanda nayiwa laifin ba kai ba ko?, To don naroqeka kadena kada tinzirani" "Idan naqi fa?" Kallon MM tayi idanuwanta cike da qwallah, ta ce, "Ungo MM, zan nemeka idan nafito" wafce kayan Jabir yayi a hannun MM daya karb'a yana kallonta, ya sake damqa mata a hannu "Jeki da tsiyarki ba'a so, waya sani ma koda gangan kikayi 'yar rainin hankali" da sauri MM ya sake miqa mata hannu ya karb'i kayan yana fad'in, "Qyalesa kawo nagode sosai, jeki abunki kawai indai wannan ne bazai haqura ba yanzu ko kwana kikayi kina basa haquri, abokina me shi sosai baya iya jurewa duk wani abu da zai sameni" Jiki ba qwari ta sake miqawa MM kayan sannan tabar wajen ranta na suya ganin irin banzar kallon da Jabir keyi mata, dama shi haka halinsa yake sam baya shiri da 'ya'yan masu kud'i rayuwarsa, acewarsa sunfiye wulaqanci don haka yake saurin hasala da lamarinsu saboda gujewa wulaqancin irin nasu daya tsana, ita kuma ta tsani ayimata irin wannan kallon don ba haka take ba, nan da nan sai taji ta qara tsanar malamin da suke kira Ingaski, acewarta duk shine silar faruwar wannan abun data tsani ayi mata zargin tanayi kamar yanda Jabir ke tunani, abun haushi ma ko taje yanzu inba ALLAH ya sota ba daqyar zai barta tashiga don har qarfe tara da mintuna goma sha biyar tayi, d'an tsaki taja cike da takaici sannan tafad'a cikin motar tata ta tayar tayi gaba tanajin tamkar tafashe da kuka, MM kuwa saida yaga tabar wajen sannan yakoma gefe ya bud'e gorar ruwan data bashi ya wanke fuskarsa sosai sannan ya d'ago handkachif d'in da niyar sake goge fuskar yaji wani irin daddad'an qamshin turarenta dake jiki ya dakar masa hanci, lumshe idanuwa yayi ya bud'e had'e da rumqe handkachif d'in sosai da tafin hannunsa yana jin wani irin yanayi dabai tab'a tsintar kansa a ciki ba. Zaro idanuwa Jabir dake tsaye yana kallonsa yayi had'e da dukan kafad'arsa cikin jin haushi da takaicinsa ya ce, "Wai meye haka kakeyi Muhriz?, Janan ce fa ba wata ba?, Look! alqur'an ko katashi muje mu kwashe kayan can ko nayi tafiyata kaji na fad'a maka, don wannan iskancin daka d'au hanya ni bazan juri kallonsa ba" "ALLAH Janan ce Jabir?" "A'a ba ita bace kai ne" "Oh my God!, Kasan me kuwa?" "Bana son ji malan, kawai katashi mutafi kaji ko, anya ma kaine kuwa? Kaga yanda ka wani qura mata idanuwa sai kace wani sabon maye?, Sai kace ba Muhriz d'in dana sani ba mai shegen nuqufarci da miskilanci ga 'yan mata!" "Bari kawai Jabir, wlh nima ji na nakeyi tamkar bani bane yau, ji nake tamkar an sauyani daga asalin MM d'in daka sani akan Janan, wani irin yanayi na dinga ji da ban tab'a jiba akan wata 'ya mace lokacin data matso kusa dani na fizgata, gaba d'aya yanda kurar qarfe haka na dinga ji wani abu na fizgata zuwa gareta, shin me hakan ke nufi Jabir?" Jabir daya saki baki yana kallonsa cike da mamaki ya ce, "Hakan na nufin tabbas kasamu tab'in hankali Muhriz, wannan kad'ewar da tayi maka yasa kasamu sauyin tunani da manta kowaye kai da matsayin da kake dashi a makarantar nan, shin ko ka manta kai bakowa bane sai mai tallan dabino da batasan asalinka ba?, Ita kuma 'yar masu kud'ice dake ji da kanta ko ka manta alwashin daka d'auka?" "Ban manta ba Jabir, amma koma meye naji son Janan a zuciyata" "Tab! To ina shawartar ka da kayi gaggawar anfani da d'an sauran hankalin daya rage maka kafin ya ida gushewa ka tashi mubar wajen nan, kamanta da ita domin kuwa duk kanwar jaa ce babu kafi balle na d'ara, kana kallon idanuwanta zakasan biri zaiyi kama da mutum, in kuwa kace ba haka ba to Zan sakar maka gatari, amma kasani ita d'in bata dace da mafarkinka ba, ni kaga tafiyata kafin d'alibbai sufito sufara fahimtar alqiblarmu, amma dai kayi tunani akai" Jabir ya qarasa fad'ar hakan yana nuna gefen kansa da yatsa, "Sam baka fahimta ba Jabir, a gaskiya bana Janan tazama cikin bara gurbin dana tsana, kuma ni zuciyata tariga data kamu da sonta daga kallo d'aya" Cak Jabir ya tsaya daga tafiyar da yakeyi kafin can ya juyo cike da mamaki yace, "Me kace MM?, Mai maita banji kaba sosai, kardai ace zargin da zuciyata keyi kake son tabbatarmun? Noooo...am not supporting that, Janan bata dace dakai ba, idan zaka farka ka farka kawai kazo mukwashe wudancan kayan ko kuma natafi nabarsu a markanesu akan titin can kamar yanda aka tashi markaneka" Miqewa MM yayi cike da kuzari ya kakkab'e jikinsa tare da nufo wajen Jabir yad'an daki gefen kafad'arsa yana dariya, "Comoon...sonta nakeyi fa nace ko tun yanzu zaka soma takun saqa da uwar d'akin taka ne?" "Wa?... ALLAH ka tsari gatari da sarar masai, ai ko kai baka isa kazamo uban gidana ba balle ita, kawai ina tsoratar maka shan duka ne tunda kai raggo ne, amma tunda kace kana iya had'a gatari bari na sakar maka b'ota, idan gyad'a taji wuta da kanta zatayi d'wad'o, kad'ai san ita ko 'yar gidan waye da kuma abunda mahaifinta zai iya yimaka idan kaje masa a irin wannan siffar" Seda ya dafa kafad'ar Jabir had'e da d'an sosa gefen kunnensa tukuna ya ce, "Eh, ai cewa nayi ina sonta bawai nace zan fad'i mata ina sonta ba ko?, Ina son na auna halin Janan dana sauran mata tunda har zuciyata ta zab'eta, ban damu da kowaye mahaifinta ba da kuma mezai iya yimun, kawai nagartarta da qarfin mutuntakarta nake buqata, matuqar nasamesu awajenta a wannan yanayin data sanni, tofa shikenan haqata ta cimma ruwa" "Shikenan, munga bugun lamba, bara musa idanuwa muga yanda film d'in zai kaya, badai girin girin ba tayi mai" 'Daure fuska MM yayi tare da bud'e sauran ruwan dake cikin gorar ruwan ya watsa masa a fuska yana fad'in, "Kaifa d'an iska ne Jabir, bakinka baya fad'ar abu mai kyau, in sha ALLAH wannan zatayi mai har kuzo kuriqa lasa" Jabir dake dariya ya ce "ALLAH!" "Zaka gani ne" "To ai shikenan, nidai don ALLAH da girmansa kab'oye wannan son azuciyarka kuma kayiwa bakinka takunkumi wajen aikata kuskuren fad'arsa awajenta kamar yanda tsala-tsalan 'yan matan dake bibiyarka keyi har sai kaga kamun bakin ludayin daga wajenta, inba haka ba kuwa, tofa ka fad'a ruwan dafa kanka da kanka" "Angama matsoracin wofi, ka kwantar da hankalinka ai dole zanyi yanda kace tunda nasan ko waye mahaifinta duk da dai alamu sun nuna ita d'in ba halinsu d'aya ba" "Aifa, ni nasan tunda karoga ka saka alaqar zuci tsakaninku babu yanda za'ayi ka iya fahimtar duk wani aibinta yanzu, don haka ga filinan ga mai doki" "Ashe ko zaku sha sukuwa malan Jabir" ya amsa masa a miskilance yana murmushi tamkar bashi bane suka gama shaqiyanci dashi yanzu, Da haka suka je suka tattara dabinon da kwakwar suka kwashe waje d'aya suka saka cikin buhu, Jabir yakira aka sake kawo masu wasu suka koma gefe inda suka saba zama sukaci gaba da sana'arsu kafin d'alibbai sufara fitowa daga wajen lectures. _*WAYE MUHAMMAD MUHRIZ MAIDABINO?*_ *ALLAH KAJIQAN IYAYENMU 👏* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 2_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* _Wattpad@Billyfari9https://www.wattpad.com/1224710693?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=BTK2Vk0LL5HyZ7f8z6t5hJUXU2zgmsDfqOwA%2FHYKAXZqR35cPk3tmBsZcsQgSabPg%2F2ma3NiPJiyOw%2F8vbI%2FiCkTNduJzX1kysyIKbnFxScFE5Gu%2BWEUvIGcsAyRE3my_ *M* uhammad Muhriz, kyakkawan matashine kuma saurayi maiji da kansa da bazai haura shekaru 32 ba aduniya, hamshaqin mai kud'ine d'an kasuwa kuma d'an boko da yayi fice acikin garin na katsina, inda yafi bada qarfi ga kasuwanci gida da wajen qasar nan, iyayensa sun rasu tun yanada shekara goma sha biyar aduniya shi da qanwarsa Razina alokacin ita kuma tanada shekaru biyu kacal, sun rasu sanadiyar fashin da b'arayi suka kaimasu awani qauye da ake kira charanchi acan cikin jahar katsina, inda suka karkashe duka mazajen dake qauyen da kuma wasu matan da suka saka taurin kai wajen yunqurin tafiya da sukayi dasu, wanda alokacin mahaifiyar su Muhriz da Razina na mai suna Bilkisu na cikinsu, yayinda shi kuma mahaifinsa suka kashesa bayan d'auki ba dad'in da sukayi dashi wajen ceton rayuwarsa data iyalinsa da yayi, shi kansa Muhriz saida suka tafi dashi amma ALLAH yabashi ikon guduwa ya dawo ba tare da sun ganesa ba, koda yadawo gida ya tadda qanwarsa Razina a tsakar gidansu zaune cikin rana tanata faman kuka, da sauri yaje ya d'aukota had'e da fad'awa cikin d'akin mahaifinsa, inda ya taddasa kwance cikin jini anyi masa yankan rago, saurin saka tafin hannunsa yayi ya kwantar da kan Razina dake faman kuka a saman kafad'arsa ya durqushe agaban gawar ta mahaifin nasa ya saka wani irin kuka mai cike da ban tausayi wanda bayada mai rarrashinsa alokacin aduniya, babu babban tashin hankalinsa irin yanda kukan Razina ke ratsa kwakwalwarsa had'e da huda masa zuciya, yayi kuka irin kukan dake tabbatar da rashin gata da maraici da kuma hauhawar nauyi ga wanda keyinsa, yayi mintuna talatin awajen yana abu d'aya kafin yamiqe rungume da Razina data kasayin shiru har yanzu tamkar wacce tasan masifa da quncin da suka fad'a na rayuwa a yanzu, qarar bindigar daya jiyoce tasashi saurin fitowa daga gidan aguje cikin firgici da tashin hankali, yayinda itama ta sake fashewa da wani kukan, Ba tare daya san inda zai nufa ba yakama hanya domin neman ceton rayuwarsa da kuma ta qanwarsa, yana kaiwa bakin qofar fita qauyen yayi tuntub'e da wata gawa ya kife ya fad'i qasa dashi har Razina, yunqurawar da yayi yamiqe idanuwansa suka sauka kan gawar, tsananin tashin hankalin da yake ciki ko kad'an baiyi tasiri ba wajen mantawa da fuskar mahaifiyarsu, ko shakka babu ita d'in ce, shed'arsa ce tafara kaida komo tana neman kucce masa saboda firgicin daya sake shiga na ganin gawar jigo kuma ginshiqin rayuwarsu akaro na biyu agabansa, cikin sheshshekar kuka ya samu damar furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirrajiun da qarfi ya fad'a ajikin gawar ba tare daya damu da mutanen dake fitowa cikin qauyen aguje suna wucewa ba wasu har suna takinsu, rarrafowa Razina tayi wajen itama ta haye gawar mahaifiyar tasu gaba d'aya tana kuka ganin d'an uwan nata awajen, tamkar dai yanda suka kashe mahaifinshi itama sun kasheta tahanyar dab'a mata wuqa aciki, amma da yake rai mai alfarma ne bata ida qarasa mutuwa ba tana jin sautin kukan daya tabbatar mata na yaranta ne ta farfad'o tare da jan wata irin shed'a dake nuni da ran be ida fita ba da sauri ya d'aga daga jikinta yana fad'in, "Inna kada ki mutu, ki tashi Inna ga Razina na kuka, don ALLAH kada kimutu inna kibarmu kamar yanda baffanmu ya mutu ya barmu" yaqare zancen tare da jawo Razina daketa tsala kuka ya kara mata a fuska, riqo hannunsa tayi dake fuskarsa yana qoqarin goge hawaye ta sake zagaye jikin Razina dashi ma'ana ta d'ora saman wanda ya rungume Razina, cikin qarfin hali ta d'ago hannu tasa afuskarsa ta goge masa hawayen dake kwance akai tace, "Ku gudu sannan ka kula da qanwarka Muhriz..." Kafin tarufe baki hannunta dake saman fuskarsa ya fad'i qasa alamun rai yayi halinsa, nan take Muhriz yaji tamkar ana rura masa wata irin wuta acikin jinin dake yawo a jikinsa, duk wani tsoro, tashin hankali da kuma fargaba sai yaji ya gushe masa, gaba d'aya yaji zuciyarsa ta bushe ta yanda zai iya fuskantar kowane irin qalubalen rayuwa a halin yanzu, hannu yasa ya shafe idanuwan mahaifiyarsu da suka kakkafe tare da d'aukar Razina dake kuka yasa hannu ya goge mata hawaye yana fad'in. "Ya Isa haka Razina, kidena kuka ya zame mana dole mu fuskanci qaddararmu, a halin yanzu mune zamu tunkareta bazamu koma bari ta riskemu ba" Yana gama fad'ar hakan ya nufi hanyar komawa cikin qauyen babu tsoro ko misqala zarratin a zuciyarsa, acewarsa zai rayu acikinsa koda shi kad'aine da qanwarsa babu inda zasu je, Yana kaiwa a tsakiyar gari yaji muryar mahaifiyarsa nadawo masa akunnuwa, "ku gudu Muhriz sannan ka kula da qanwarka..." kallon Razina data fara bacci yayi sannan ya maida kallonsa ga gungun b'arayin dake tunkarosu zasu ficewa daga cikin garin suna ihu da shewa suna qarawa, sai kawai ya tsinci kansa da rugawa ya fad'a can wani dajin badon ya tsorata ba sai don kawai yacika wasiyar mahaifiyarsa akan qanwarsa, amma badon wannan ba a yanda yake jin zuciyarsa zai iyayin fito na fito dasu saidai su kashesa. (Hmmm Muhriz kenan, ai tunda manyanka da jami'an tsaro, gwamnati suka kasa da lamarin wud'an nan b'arayin kaima bazaka iya ba sedai kawai akai qararsu ga ALLAH shine zai iya yimana maganinsu, amma sam qarfin zuciya ko na jiki ko makamai bazai iya da lamurransu ba sai qarfin addua kawai) Gudu yayi sosai da bai tsinci kansa ako ina ba sai tsakiyar titi, tsabar gajiya baya iya yin komai gashi riqe da Razina wacce ga dukkan alamu babu fitar lumfashi ajikinta, da sauri wani mai motar haya ya fito daga qauyen qanqara daya tashi kadesu ya faka gefen titi, kasancewar marece yayi babu motoci da yawa yasa har ya d'aukikkesu daga kan titin babu abunda ya samesu, tambayar Muhriz yakeyi lafiya daga ina suke amma ya kasa bashi amsa sai nuna masa Razina yakeyi dake riqe a hannunsa gam, cikin tsoro mutumen ya dubi gefe da gefen titi da kuma hanyar daya hango sun fito yaga ba kowa ya d'aukesu su duka ya saka cikin motar sannan yaja sukabar wajen, dama garin katsina yayi sai kawai ya nufi can dasu, hannu Muhriz ya miqa ya jawo 'yar jarkar swan daya hango acan gefen driven da ruwa, mutumen be hanasa ba ya bud'e gorar ya tuttud'awa Razina a fuska da jiki, tafi mintuna biyu kafin can yaga taja shed'arta da qarfe ta maido had'e da fashewa da kuka alamun suma ne tayi ta farfad'o, murmushin qarfin hali yayi hawaye na zubo masa sannan ya d'auketa ya bata

Chapter 1 of 40