Share this page
sati ɗaya, wannan yasa kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci irin kwanciyar hankalin da take ciki yanzu, shiyasa har ta samu damar baro school yau yazo gidan Hajiya don tasan babu wanda zai takurata ko kuma hanata, Ko data koma ta tadda har anyi nisa da lecture ɗin, kuma cikin taimakon ALLAH lecturer ya barta ta wuce ba tare daya hanata shiga ba, tun data shiga take raba idanuwa inda zata hango Amira don gaba ɗaya yau ko da safe bata gane ta ta shigo ba, har suka kammala lecture ɗin zuwa ƙarfe huɗu ko mai kama da ita bata gani ba, hakan yasa ta shiga tambayar ƴan class ɗin nasu ko lafiya yau Amira bata shigo school ba?, Anan fa ake faɗa mata cewa ba tada lafiya, sosai ta ji ba daɗi duk da ƴar tsanar dake tsakanin ta da ita tare da ƙudur tawa aranta cewa daga nan tana fita gidan su zata je ta dubota, duk da ba lallai ne ta iya ganewa ba saboda sau ɗaya ta taɓa zuwa ta sauke ta da suka tashi school, shima ɗin akan kwana ne ta nuna mata gidan nasu dake can gaba idan anshiga cikin kwanar da yatsa.... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 37_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ Janan kuwa ko data isa gida anyi sallar magrib, don haka bata tsaya bi takan kowa ba tawuce ɗakinta kai tsaye, jikkar ta tafara ajiyewa kan gado sannan ta faɗa toilet tayo arwala, tana fitowa ta tada sallah, bayan ta kammala tayi azkar ɗin marece sannan ta jawo alƙur'anin ta dake kan bedside ta shiga karantawa, bata kammala ba sai da taji ankira sallar isha sannan ta rufe ƙur'anin ta tashi ta kabbarta sallah, tana gamawa ta tuɓe kayan jikinta ta faɗa toilet tayo wanka, fitowarta keda wuya wayarta ta hau ruri, murmushi tayi saboda ringing ɗin da tayi mutum ɗaya ne dashi wato masoyinta mm, bata tsaya wani saka kaya ba ta ɗauki wayar tare da ɗaya kiran daya shigo a karo na biyu ta kara akunnuwa, "Ran yallaɓiyata ya daɗe" mm ya faɗa yana duba wasu takardu daya je ɗaukowa cikin mota, saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Tare dakai yallaɓai, ina wuni?" "Lafiya klw, ya kike?" "Alhamdulillah, kai fa?" "Nima hakan, in jin ɗazu kin samu lecture ɗin?" "Sosai ma kuwa, ko ka manta kayimun addu'a?" "Ehmm, kinci abinci?" "A'a hubby" ɗan zaro idanuwa yayi daidai lokacin daya ciro wani file daga cikin mota yana ƙoƙarin rufe marfinta, "Me yasa?, So kikeyi yunwa ta kama mani ke ne?, Kin san na faɗa maki cewa dena wasa dacin abinci akan lokaci ko?" "Kayi haƙuri, ban jima da dawowa ba, sai na tsaya gabatar da salloli, amma yanzun nan zan sauka naci in sha ALLAH" "Okay shikenan, amma ina kika tsaya ne haka da har kika jima awaje baki dawo gida ba?" "Naje gidan su Amira dubata ne?" "What...?" Ya faɗa da ƙarfi har wayar ta suɓuce a hannun ta, cikin mamaki ya ci gaba da cewa, "Janan kin kuwa san ko waye Amira?, Kin san yanda ita ta ɗauki tarenku kuwa?" "Na sani mm" "Noo..baki sani ba, idan kuma har kin sani to wani ɓangaren kika sani ba duka ba" "Hmm, hubbin ruh kenan! Nasan kaso tis'in da tara bisa ɗari na daga cikin halayen Amira, na kuma san yanda na ɗauke ta ba haka ta ɗauke ni ba, amma ni har ga ALLAH ƙaunar ta nakeyi da zuciya ɗaya, ban taɓa jin abubuwan da take yimun ba zasu iya sa na sauya mata duk da ita ɗin ta sauya mun sosai ba kamar yanda muke ada ba, na kuma ɗauki wannan a matsayin ajizancin ɗan adam da ake cewa ɗan tara ne bai cika goma ba" "Tirƙashi! Lallai zuciyarki mai kyau ce Janan, amma duk da haka kiyi takatsantsan da ita, ba ina nufin ki rabu da ita ba, amma ki kula dakyau a taren ku, kin san halin rayuwa da kuma halin ɗan adam" "To shikenan yallaɓai zanyi hakan, ya Momy da Razina?" "Duk suna nan lafiya klw, ina da kyakkyawan albishir agareki" "Wow! Are you serious?" "Sosai kuwa, amma kafin nan ki fara sauka kici abincin, anjima sai muci gaba da maganar mu ko?" "No hubby bari na saka kayana na suka naci abincin, go ahead ina saurarenka" ta ƙare zancen haɗe da miƙewa ta nufi wardrobe ɗin kayanta ta ciro wando iya guiwa da ves mai faɗitn hannu ta saka saboda yana yin garin da zafi da alama hadari ne ke haɗuwa, sannan ta ciro mayafi ɗan siriri ta ɗora akan ta tafice daga ɗakin tana faɗin, "Hello hubbin ruh ina jinka" "Kin gama sa kayan?" Cike dajin kunya tana saukowa akan upstairs ɗin don tama manta data ce masa hakan ta ce, "Eh" can ciki alamun kunya ta rufeta, murmushi ya yi haɗe da cewa, "Okey, he kici abincin, i will call you later" duk daba haka taso ba batada wani zaɓin daya wuce ta amsa masa da to, don haka cikin kwantar da murya ta ce, "Ok, bye" "Bye, i luv you" sannan ya kashe wayar bayan itama ta ce, " I love you too hubbynah" tana dariya, Cilla wayar tayi sama tana faɗin "Mm kenan!, Fillah bazan iya son ka kaɗan ba koda zan rasa komai nawa" taƙare zancen tana ƙoƙarin tara hannu ta caɓe wayar data cilla sai kawai taga Nihal da tun ɗazu ke bayanta ta caɓe tana cewa, "Wannan Man ɗin naki ya kusa susuta mun ke sai sabbatut kike faman yi ke ka kaɗai, yaushe kika dawo ne?" ta cilla wayar itama Janan tayi saurin caɓewa tana dariya haɗe da cewa, "Ana gama kiran magrib na dawo" "Kuna tare kenan?" Nihal ta faɗa tare da jawo mata kujera ɗaya daga cikin kujerun dake jera wajen dining table ta zauna, ɗago kai tayi tana kallon yayar tata kafin tace, "Ko ɗaya Adda, na dai biya gidan su Amira ne dubota" "Wai ke har yanzu kina nan tare da yarinyar nan?, Nifa na tsaneta sam bana son ta" "Tofah, data yi maki me Adda" "Kawai dai, baki ganta wata iri ba?" "No..daidai ƙawata take, kedai kice dai halin ne naki shiyasa bata yimaki ba" "What ever dai, can ita ta sani" ta turo mata plate a gabanta data zuzzuba masu abincin, girgiza kai Janan tayi haɗe da ɗaukar cokali ta fara ci suna ɗan taɓa fira jefi-jefi har suka kammala, bayan Janan ta ciro tissue ta goge bakin ta haɗe dayin hamdala sannan ta kalli Nihal ta ce, "Adda wai Abba na garin nan kuwa?" "Me kika gani?" "Emmm, guard ɗin sa naga sun dena bina, sannan wannan ɗan iskan gayen ma ya dena bina" "Kin yi farinciki ne?" "Sosai kuwa Adda, ai shiyasa kikaga nayi maki zancen, don nasan indai Abba na nan tofa bazai ƙyaleni ba" "Kar ki damu, ai na faɗa maki everything will be right in sha ALLAH, Abba kuma ya wuce Ethiopia tare da gayen naki" ta faɗa cikin tsokana tana kashe mata ido ɗaya, dariya Janan tayi haɗe da cewa, "Wai! Nikam na sani, ai da wannan ɗan namamajon na nan mai ƙirar samudawa da halin bunsuraye ALLAH bazai taɓa bari na shaƙi iska mai kyau ba" "Janan kenan, ni kuwa banga illar gayen nan ba, kawai dai kin riga da kin folama wa yake da suna?" "Mm.." ta bata amsa tana dariya, "Yawwa shi fa, shi yasa bakya ganin haɗuwar gayen" "To Adda ko za a baki shine?" "Haba dai, shifa the charming ɗin nawa da nake jira?, Ai bana tunanin zan iya rayuwar aure indai bada gayen nan ba, i luv him, I luv him more than my life, zan kuma iya jurewa rasa kowa da komai akansa" "Haddani Adda?" "Ban faɗa ba, amma yanda kika ji na faɗa hakan ne" "Emmm, lallai Adda, kice ƴaƴan Abba bakin rai suke akan gayun nan nasu, die hard kenan!" Janan ta faɗa tana cigaba da dariya, itama Nihal dariyar tayi kafin ta miƙe tana faɗin, "Wuce gado wasa ne?, Ko bakiga yanda Abba ke son Umman mu ba duk data mutu, rayuwa yakeyi da wata amma tamkar ba a tare suke ba, kuma duka wannan aikin so ne, ko kina musu?" "Ko ɗaya, nice sheda akan hakan, amma ai shi nashi bana tunanin yana da inganci tunda har zai iya wofantar da wani sashe na soyayyar sa, kuma hakan kuskure ne ko a muhallin so, ni sam bana fatar nayi gado irin nasa indai ta wannan ɓangaren ne" Itama tamiƙe haɗe da tattara kayan ta nufi kitchen dasu, ita kuma ta komawarta falo tana latsar wayarta hankali kwance ba tare da tasamu da maganar data faɗa ba, Duk da maganar data faɗa duka gaskiya ne amma sai Janan ta ji ba daɗi a ranta, musamman inda take cewa, rayuwa yakeyi da wata amma tamkar ba atare suke ba, sosai abun yayi mata zafi ta kuma ji haushin maganar a ranta, don haka sai kawai ta koma sama abun ta ba tare data koma bi takan ta ba, shirin kwanciya tayi tare da hayewa kan gadon ta sai ga kiran mm ya shigo, yanda ya ji muryarta data ɗaga ya sashi cewa, "Matata meya faru?" Murmushi ta saki kafin tagyara kwanciyar ta haɗe da cewa, "Adda ce tayi wata magana da batayi mun daɗi ba, shiyasa kaji ni a haka" "Ayya Adda ɗin mu bata kyauta ba, bata san ba a ɓatawa gimbiyar mata rai ba?, To ayi wa Adda haƙuri bazata ƙara ba kinji noor albi na?" "Shikenan tunda mai girma mm ya bada haƙuri a matsayin Adda ɗin sa, ya wuce" "Kin tabbata?" "Sosai kuwa, ya zancen kyakkyawan albishir ɗin da za a yimun?" cike da zolaya ya ce, "eh, dare yayi mu barshi sai gobe" cikin shagwaɓa ta samasa kuka tana faɗin, "Kai hubby, ALLAH naƙi wayon, kaifa kace na bari sai yanzu" "Yanzu kuma nace kibari sai gobe, between me and you who is the boss" "Kai ne mana, amma ai kasan ba kyau saɓa alƙawari ko?" "To naji Malama Janan, dama da wasa nakeyi" "Kai ko.." ta faɗa kamr zatayi kuka, like irin ma tana kusa dashi takai masa soƙo akai, dariya ya samata har sai da ya yi mai isarsa sannan ya ce, "Sorry wifey, yanzu dai kunnenki nawa?" "Biyu" ta bashi amsa tana dariya, ya ce "To ƙara takwas su cike goma kisha labari" harara ta aika masa da ita tamkar yana agabanta haɗe da turo baki ta ce, "To a ina kake so na aza sauran idan na ƙara" "Kisa ɗaya a goshin ki" "Ehim" "Biyu kuma a chicks ɗin ki" "Sai kuma a ina?" "Eh sai ki ɗora ɗaya a ƙasan bakin ki" tana dariya ta ce, "sauran huɗun kuma sai kai ma ka aza a inda kace na aza nawa ko?" Suka sake sa dariya gaba ɗayan su har sai da sukayi mai isar su suka gama tare da sauke ajiyar zuciya atare sannan ya shiga labarta mata yanda sukayi da Hajiya da kuma labarin data bashi akan matar yayan mahaifin nata, kasancewar Janan tasan wani ɓangare daga cikin labarin yasa ta faɗawa mm cewa, tabbas tasan Abban ta nada yaya kuma yanada mata har da yaro ɗaya kamar yanda Hajiya ta faɗa masu, amma ALLAH yayi masa rasuwa kuma bata taɓa faɗa masu cewa ga abunda ya faru tsakanin su ba, wanda yasa tun yaron na ƙarami data tafi dashi bata koma dawowa garesu ba, kuma shine dalilin da yasa har yanzu basu san ma inda yaron yake ba dashi har mahaifiyar tasa, sai da mm ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "To ni na sani Janan" a yanda taji ya ambaci sunan ta kai tsaye ya tabbatar mata da gaskiyar abunda ya faɗa, tayi saurin tashi daga kwancen da take ta zauna haɗe da cewa, "Hubby ka sani da kace?, Suna ina yanzu?, Ka faɗawa grandma kuwa?" "A'a ban faɗa ba, amma yanzu haka ina tare dasu" "Pls hubby don ALLAH kayimun bayani, wlh har naji jikina ya fara tsima ina son na gansu" "Kwantar da hankalinki zaki gansu in sha ALLAH, Jabir da Momy sune mutanen da Hajiya ke nema ruwa a jallo kamar yanda ta faɗa mun" "Taya akayi kasan sune to?" "Ranar da Abba ya kawo maki wanda zaki aura kika kirani kika sanar dani, to aranar Momy ta faɗa mun da bakinta cewa indai Abba shine mahaifinki to na haƙura dake saboda shine ƙanen mahaifin Jabir, shine ya raba zumuncin dake tsakanin ta dasu bayan rasuwar mahaifin Jabir saboda kawai ita musulunta tayi kuma ba yaren su ɗaya ba...." Nan ya labartawa Janan komai dangane da abunda ya sani akan Momy da Jabir, wasu hawaye ne suka riƙa korarowa akan fuskar Janan cike da tausayin halin da rayuwar Momy da Jabir suka tsinci kansu, cikin muryar kuka ta ce, "Haƙiƙa Abba da grandma sunyi kuskure, sun raba zumuncin da ALLAH da manzon sa sukayi umurni da a sa dashi, wlh hubby tun ranar dana fara ɗora idanuwana akan Jabir jikina ke bani da kamar akwai wata sanayya tsakanina dashi, shiyasa duk hantara da cin kashin da kaga yayimun a waccan ranar na kasa yin komai, na kasa ce masa komai bayan ina da damar yin hakan tunda ba shi nayiwa laifin ba, ashe ƙarfin jini ne dake gudana tsakanin ni dashi" "Haka ne, dama shi ALLAH haka yake tsara lamarinsa Asad da yaso da kuma lokacin daya so, shiyasa duk wanda baiyi imani dashi ba yayi aikin banza" "Tabbas kuwa, can't wait safiya ta waye hubby na bawa Adda da grandma labari" "A'ah kada kiyi hakan, ki bari da sannu suma zasu san komai kinji ko" "Hubby why?" "Kina ganin idan Abba yasan da wannan zancen bazai ƙara ɗamarar hanani auren ki ba?, Ki bari mu warware komai cikin natsuwa, nima in sha ALLAH jibi zanyi tafiya" "Kuma?" Ta faɗa kamar zata sake saka wani kukan, ɗan murmushi yayi haɗe da cewa "Eh mana, zan je inda ya kamata ace tun tuni naje na dubo sauran ƴan uwana da suka rage idan har ALLAH yasa suna raye sai ban je ba" "To amma zamu haɗu kafin ranar ko hubby?" "In Sha ALLAH my cry cry baby, ke komai nakir sai kin saka shagwaɓa da kuka aciki, hakan baki san yanda kike rikita ni bane, kisa duka lissafi kwancewa?" Ta rufe fuskarta cike da jin kunya tamkar tana agabansa, haka suka ci gaba da firar su cike da so da ƙauna kowanen su naji tamkar ya jawo ɗan uwan sa ya tsaga jikinsa ya saka aciki... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 38_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ***** *Ina masoya littafan ASMY B ALIYU?, Kumar matso kusa yazo maku da wani shahararren littafin ta mai suna WAMINAL HUB!, Hmm tirƙashi dajin sunan wannan littafin kinsan zaku gwangwaje da soyayya da kuma chakwakiyar ƙauna acikin sa, domin na tabbatar maku da hakan nazo maku da kaɗan daga cikin wannan ƙayataccen littafi nata mai matuƙar ɗaukar hankali, ta bakin malam bahaushe dai, ya ce gani ya kori ji👇* *Waminal Hoob* _Asmy b Aliyu_ PAID BOOK## Love# Friendship# Family# NooryAli#moments Tana ganin yarda jikinsa ke wani irin kadawa ,jawota yyi ta fado kansa Yana shakar kamshinta Yana sakin ajiyar xuciya ,kallon cikin kwayar idanunsa take .Wanda ya canja kala har kwallah take hangowa acikin su ,a hargitse ya shiga subbatar ta ta koina Yana tura kansa cikin Wuyanta,hawaye taji suna cika Mata ido tuno farhaan kurum,hade fuskarsa yyi da Tata fuskar Yana goga hancinsa da nata da wani irin Murya Yake fadin"I try Am very try Noory u belong to someone else,ya fada muryarsa na karyewa A hankali kafin ya hade bakinsa da nata. Friendship# Aliyu waxeer Farhaan Shagari "Da Alamar bakada hankali Farhaan ka Samu tabin kwakwalwa,ni kake tunanin naje na auri yarinyyar da kakeso har na tsawon shekara daya??''yyi maganar so pissed up ,farhaan ya kwantar da Kai Yana fadin nasan Nooriyyah Bata cikin kalar matan da kakeso ,nasan ba ajinka bace .Haka nasan baka sha'awar (BAKAR MACCE")bestyn ka xakayiwa wannan Alfarma da xarar na kammala master's Dina xan dawo gareta muyi Aure!!"girgixa Kai Aliyu waxeer ya shigayi Yana fadin ka haukace Farhaan!!!" Waminal Hoob# Is out on the 31july..stay tuned and find out!!!! Love is in the Air# Team Noory-Ali#Forever❤️ FRIENSHIP## Aliyu waxeer Farhaan Shagari Areefa Mansoor Laylah waxeer FAMILY#❤️ Wazeer Family Shagari Family Azeex Ali Family.. ______________________________ Basu bar juna ba sai kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare, shima yanayin muryar Janan da mm ya soma jin sauyawar ta izuwa ta bacci ya sashi yin sallama da ita badon ya so hakan ba, don kuwa in ta tashi ce baiƙi su kwana yana jin zazzaƙar musayar ta dake matuƙar tafiya da dukkanin tunanin sa, ya jima zaune yana ƙiyasta yanda yake son abubuwa su kasance tsakanin shi da ita idan ALLAH ya yarda su mallaki junan su kafin bacci mai nauyi shima yayi awon gaba dashi, Washe gari Janan ta tashi cike da farinciki a zuciyar ta bayan tarin mafarkai da tayi masu matuƙar daɗi da take fata su zame mata gaskiya, kasancewar yau weekend ne babu school yasa ko da ta gama sallar asuba haɗe da azkar ɗinta na safiya rana na fitowa ta haye kan gado abunta ta kwanta ta ci gaba da baccin ta hankali kwance, bata farka ba sai kusan ƙarfe sha biyu, da alama shima yunwa ce ta tashe ta, toilet ta fara shiga ta wanko bakin ta agurguje ba tare data tsaya watso ruwa ba ta sauko ƙasa riƙe da wayar ta tana ƙoƙarin kiran Amira don taji ya mahaifiyar tata da jiki, saboda a cikin mafarkan da tayi jiya hadda nata sai da bata fahimci inda mafarkin ya dosa ba, haka kuma bata maida hankali akan sa ba saboda ta ta'allaƙa hakan ƙilan da zuwa dubata da take yi da kuma yanayin da ta ganeta aciki, sau kusan huɗu wayar na ringing amma Amira na kallo taƙi ɗagawa saboda haushin abunda ya faru jiya akanta da take ji har sai da umma dake kwance ta juyo tana kallon ta, ta ce "ALLAH ya shiryeki Amira ya rabaki da mugun hali, waye haka ke faman kiranki kika ƙi ɗagawa?" "Wani ne umma ƙyaleshi damuna zaiyi da ɓaƙin iyayi da surutu.." kafin ta rufe baki Al-amin dake kusa da ita zaune ya miƙa wuya ya ga mai kiran nata, ya ce "Laaa..umma wlh ba wani bane, Janan naga an rubuta" ce ki da takaici ta yunƙuro da niyar kai masa duka Zarah ta janye sa tana dariya, "Jimun aunty Amirar nan, daga faɗan gaskiya sai duka?, ALLAH shiyasa nace aunty Janan tafiki kirki, da alama fa umma kiranta tayi ta tambayeta ya jikin ki amma take yimata haka, ALLAH ba kyau ki dena, don wlh da nice ita da tuni na barki" "Ƙyaleta zarah, miƙomun wayar anan" Turo baki tayi tana makawa Zarah harara haɗe da cewa umma, "Kiran fa ya tsinke, kuma bana da kati awaya" ta ƙare zancen tare da miƙa ma Umma wayar, girgiza kai umma tayi haɗe da cewa, "Zarah jeki ɗauko ɗari biyu na nan kan madubi ki siyo kafin na Naira ɗari, ina laifin yarinyar nan wlh ki sauya hali in kina sauyawa, inba haka ba wannan halin da kikeyi mata wata rana shi zai kaiki dajin kunya da kuma nadama" ƙafafuwa Amira tashiga shurawa tana faɗin, "Kai umma, kai Umma, yanzu fisabilillahi baki kike mun akan ta?, Kenan tafini awajen ki" "Ko ɗaya, Ni ba haka nake nufi ba, yarinyar nan ba kida aiki sai aibanta ta da musguna mata bacin tana biye dake da alkhairi akoda yaushe, ina guje maki kada wuɗan nan abubuwan da kike yi mata su janyo maki faɗuwa ita kuma ɗaukaka, kinga alokacin dole kiji kunya kuma kiyi nadama" "Amma umma wanda nake so fa taje ta rabani dashi, kuma don munafunci zata riƙa shiga jikina da sunan tana so na, to a ina aka taɓa so haka?" "Banda abunki ai ba ita tahana ya soki ba, shi ya zaɓe ta ya barki sai kiyi haƙuri har kema ALLAH yakawo maki wanda zai so ki kema" "Ni umma bazan taɓa haƙura da mm ba, yanda take son shi haka nima nake son shi, don haka zanci gaba da addu'a ALLAH ya mallaka mani shi koda ya aureta nima ya soni fiye da yanda yake son ta" "To alhamdulillah, indai addu'a zakiyi ai ba laifi, nima sai in tayaki ALLAH ya zaɓa maki mafi ƙololuwar alkhairi" "Umma kenan! Ai mm alkhairi ne gareni, kawai ki roƙamun ALLAH ya mallaka mani shi, zanyi farinciki sosai" da mamaki umma take kallon ta, don ko a mafarki akace mata Amira zatayi irin wannan shirmen bazata taɓa yadda ba, amma sai gashi agabanta takeyi ba tare da ta ji kunyar taba, gaba ɗaya tarasa wane irin so ne haka take wa yaron nan, sallamar Zarah ta dawo da umma hankalinta dake faɗin, "Umma Sa'idu mai shagon baya nan, sai dai in can bakin titi Al-amin zai je ya karɓo" "Bashi yaje, ka siyo duka na ɗari biyun, inyaso ta bani naira ta ɗari inta samu" "A'a Umma, ni ba ruwana da kati in dai ba sos zanyi ba, duk wanda ya damu da son waya dani ya kirani kawai" "Eyyeeee, to sannu ƴar gwal, koda yake wazai kiraki in ba Janan ba tunda itace mai iya haƙuri da halin ki?" Turo baki tayi tana ƙoƙarin sake magana sai ga Janan ta sake kira, "ungo Zarah miƙa mata wayar ta" Zarah na karɓa taga Janan ce ta sake kira da sauri ta ɗaga haɗe da karawa a kunne, "Hello aunty Janan, Ina wuni?" Cike da fara'a Janan dake zaune a ɗaya daga cikin farare kujerun dake cikin guiden ɗin dake can bayan ɗakunan su ta ce, "Ahhh...Zarahty kina lafiya?" "Lafiya lau aunty Janan, ya gida ya gajiyar jiya?" "Alhamdulillah, ya jikin Umma?" "Ta samu sauƙi sosai" "Masha ALLAH, ina Auntyn taki? Na kira sau barkatai bata ɗaga ba" saida Zarah ta kalli gefen da Amira take zaune sannan tayi dariya haɗe da cewa, "Tana tsakar gida tana wankin bayi (toilet) shiyasa..." Kafin tarufe baki ba Amira data zaro idanuwa tana sauraren ƙaryar da take sheƙa mata tayo kanta, aikuwa da sauri ta miƙe tare da miƙawa Umma wayar tana faɗin, "Wayyoo...., Aunty Janan ga Umman" ta kwasa aguje tana zagayar falon Amira na biye da ita tana cewa, "Yau sai kin faɗa mun uban waye ya sani wankin bayi" Haka ta riƙa binta aguje suna ta gudu har tsakar gida tana ƙoƙarin kamata, sai da Zarah ta gaji don kanta sannan ta tsaya haɗe da duƙewa ƙasa ta tura fuskarta cikin cinainanta tare da ɗago hannayen ta tana faɗin, "Wayyo Aunty Amira don ALLAH kiyi haƙuri bazan ƙara ba" "Badai kin rena ni ba, ALLAH yau zanyi maganinki" ta ɗaga hannu tare dakai mata dundu a baya, har zata sake kai mata dundun a karo na biyu Umma ta ce, "Karki kuskura ki sake dakar mun yarinya, zo ki karɓi wayar ki Janan na akan layi, babbar banza babbar wofi" duk da haka saida takai mata ranƙwashi akai haɗe da cewa, "Zamu haɗu ne yarinya" girgiza kai kawai Umma tayi tana mai addu'ar ALLAH ya rabata da zafin rai, da biyema ƴan ƙannen nata da takeyi akoda yaushe. Tana karɓa Janan dake faman dariya jin abunda Umma tafaɗa ƙarshe, ta ce "Kai Aunty Amira, in angirma asan angirma fa, ya kina takurawa yaran umma haka?, zafa mu saidaki mu huta" cikin ɓaci rai Amira ta ce, "To ku saida ni tunda akuya nake ko shanuwa" tayi tsaki sannan ta kashe wayar cike dajin haushin ta, dariya Janan ta riƙa yi sosai har saida tayi hawaye, ire-iren wannan saurin fushin na Amira wani zubin akan abunda baikai ya kawo ba kan bata dariya wani lokaci kuma ya bata mamaki, shiyasa sam bata ji haushin abunda tayi mata ba yanzu sai ma dariya da abun ya bata, wai tunda ita shanuwa ce ko akuya, ta sake saka wata dariyar, tana a haka Nihal ta iskota, Ɗan turo idanuwa tayi haɗe da cewa, "Tofah! Janany sister yau soyayyar ta dariya ce?, Tun fa a falo nake jiyo wannan dariyar taki" "Bari Adda, Ni da ƙawata ce Amira" "Au na zata ma da mm ne daɗin soyayya ya sa kike wannan ƙyaƙyatawa haka?, Mtssss...da alama kuwa in kika ci gaba da biye mata zata mai sheki mahaukaciya" ta ƙare zancen cikin ko in kula tare da wucewa ta haye kujera ɗaya itama tana latsar wayarta...... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 39_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ****** Ina masoya littattafan ASMY B ALIYU?, Kumar matso kusa yazo maku da wani shahararren littafin ta mai suna WAMINAL HOOB!, Hmm tirƙashi dajin sunan wannan littafin kinsan zaku gwangwaje da soyayya da kuma chakwakiyar ƙauna

Chapter 21 of 40