lafiyayyun marukka masu zafi har sau biyu haɗe da zafi, hakan ya tun zura grandma itama ta rufeta da masifa tayi mata tas kuma ta sakata dole ta bawa mai aikin haƙuri, shikenan fa ta fara baƙin rai tana kumbura fuska har suka iso gida, babu kalar rarrashi da irin haƙurin da Janan bata bata ba gudun kar mahaifin nasu yaci mata mutunci amma taƙi haƙura saboda tuƙuƙi da zafin da zuciyarta keyi mata nasa tabawa talaka kuma mai aiki a ƙarƙashin mahaifinta haƙuri, daga ƙarshe ma rufe kanta tayi cikin ɗakinta taci kuka ta mai isarta, Janan kuwa ji tayi tamkar tabar gidan saboda sanin abinda zai iya biyowa bayanta idan mahaifinsu ya ji wannan maganar, gabanta ne ya daɗi jin ƙarar tsayawar motocinsa don sai lokacin yadawo shima, tafin hannayenta tasa ta rufe baki da hancinta haɗe da kulle idanuwanta tana addu'a,
Sautin dukan ƙofar ɗakin nata data kiyo da qarfi ya sata faɗuwar gaba haɗe da buɗe idanuwanta cike da tsoro ta nufi wajen ƙofar jiki na rawa ta buɗe, cikin girmamawa kanta na sinne a ƙasa ta fito tana qoqarin gaida mahaifin nasu dake tsaye wajen cikin ɓacin rai, hannu ya ɗaga da zimmar wanketa mari tayi saurin rufe idanuwa, Muryar Nihal dake tsaye bakin ƙofar d'akinta ce tayi saurin dakatar dashi jin ta ce,
"Ni Abba, me Janan tayi kuma da zaka doketa?, I think hakan ba daidai bane, i zuwa yanzu yakamata ace ka dena dukanta akan wasu abubuwan, musamman wuɗanda basu shafeta ba" ta ƙare maganar tare da ƙarasowa wajen ta rungumo Janan a jikinta, kallonta yayi yaga yanda idanuwanta suka kumbura suka yi jaa saboda kukan da tayi ya ce,
"Ki ƙyaleni da ita sweetheart, ai tasan yanda muka yi da ita kafin kutafi, duk laifin nata ne don da baku je ba ai hajiya bazata sa a wulaƙan taki ba"
"No Abba, she's our grandma, dole ko Janan bata ce muje ba ace mun tafi, but nakasa sanin dalilin da yasa take fifita wasu bare akai na ba, ban san me yasa bata sona ba Abba tafi don Janan" da sauri Janan ta d'ago idanuwanta da suka cika da ƙwalla tab tana kallonta, ta ce
"Ba haka bane Adda Nihal, dukkanmu grandma na son mu, kawai wasu daga cikin d'abi'u ne da halayyar da kikeyi bata so.." ai kuwa bata ƙarasa rufe baki ba Abba yayo kanta,
"Kin gani ko Nihal, ai duk wannan abun ita Janan ɗin ke had'ashi, ina ruwanta da halayya da kuma ɗabiun ki?" yakai zancen yana nuna Janan da Nihal ta ɓoye a bayanta, juyo da ita Nihal tayi a gabanta ta ɗora hannayenta akan kafaɗun Janan tana kallon fuskarta ta ce,
"Look Janan, rayuwar nan da kike gani mai sauƙice, ke da grandma halayenku daban nawa daban haka na Abban mu daban, so banga dalilin da zai sa grandma tace dole saina sauya daga halayyata da d'abiuna na koma irin naki ko nata, ni haka ALLAH ya yini, sam bana son talaka saboda basu san halacci ba, zaka ɗaukesu ne daga rana ka saka su a innuwa su kuma idan sun samu dama sai su sakaka a rana, ko ba haka ba Abba"
"Haka ne mana, amma ita da hajiya sun kasa fahimtar hakan, ban san dalilin su ba na cewa lallai lallai sai sun ja talaka aikinsu ba ko sun so shi, babban takaicin ma shine yanda suke iya fifitasa akanki"
"Abba ba haka bane, Ni da grandma ba muda wani dalili face mu da talaka duka ALLAH yayi mu, kuma badon baya don su ba yayisu a yanda suke, zancen fifiko kuwa duk duniya ba nida wanda nake so sama da Adda Nihal, itama tasan hakan, sai kuma kai da grandma ko ba haka ba Adda?" Ta ƙare zancen tare da fashewa da kukan da tun ɗazu take ko kuwa da fitowarsa.
Jawota ajiki Nihal tayi ta rungume tana rarrashi haɗe da cewa,
"Sorry darling, i know bakida kamata kuma nima banda kamarki, saboda haka kiyi shiru, grandma kuwa zanyi magana da ita, tabarni nayi rayuwata kuma kuyi taku yanda kuke buƙata ba tare da mun takurawa juna ba, wannan shine kawai"
"A'a Addah.."
"Ya isa haka Janan" Nihal ta faɗa haɗe da ƙoƙarin hanata ƙarasa maganar data tashi yi.
Wani irin tsaki Abba ya jaa tare da barin wajen yana faɗin,
"I will make sure that wannan mai aikin tabar gidan an samo wata don bazan d'auki wannan shashancin ba, Janan matsala Hajiya damuwa, how i wish Nihal kaɗai nake da ita, da yanzu ina nan tare da matata, gashi garin haifomun waccan matsalar na rasa farin ciki na" haka yayita sabbatunsa har ya sauka ƙasan ya wuce sashensa zuciyarsa cike da damuwar mahaifiyarsu daya tuna wacce ako yaushe yake ɗora alhakin mutuwar ta akan Janan,
Kusan dai ranar Janan batayi bacci ba, babu abinda take tunani irin yanda zata sauya tunani da halayyar 'yar uwarta da mahaifinsu ya ƙaƙaba mata da sunan soyayya, mm ne ya daɗi mata arai lokacin da yake faɗin tsautsayine ya haifar da kaɗewar data yimasu kuma dama can ALLAH ya tsaro hakan yau zata faru, murmushi tayi ta juya kwanciyarta haɗe da cewa a zuciyarta,
" To meye abun ƙi ga talakka in har ya san komai tsari ne da kuma nufi daga ALLAH, ya kuma iya yarda da qaddarar da ALLAH ya rubuto zata same sa, ai shine mutumen daya kamata a so bawai a wofantar dashi ba don baida dukiya, yanzu dai ga mahaifinta babu abunda ya nema aduniya ya rasa amma ya kasa gane cewa duk abinda zai sami bawa daga ALLAH ne kuma shine ya tsaro masa haka, shi dai akullum tunaninsa, itace ta kashe mahaifiyarta tunda garin haihuwarta ta ya rasata, wannan wane irin tunani ne na marasa ilimi yake yi?, Kullum baida aiki sai kuka da ita akn rashin mahaifiyarsu, wlh ta tabbata tafishi buƙatar mahaifiyarta aduniya, amma tayi haƙuri da maraicin data taso cikinsa na rashinta, domin ALLAH shi yasan dalilin haka ya kuma tsaro mata haka a rayuwa, ta kuma tabbata yafita son kanta da kanta ya kuma fi kowa son mahaifiyarta daya karb'a, ciki kuwa har da shi mahaifin nata dake tunanin yafi kowa sonta" da wannan tunanin bacci ya soma d'aukarta, ba'a jima ba ta tsinci kanta a duniyar mafarkai kuma abun mamaki wai ita da mm, tana wannan mafarkin taji ana yaɗata acikin barci, zumut ta miƙe tana fad'in,
"Mm meya kawo ka anan?"
Nihal ta gani bakin gadon a tsaye da sauri ta murza idanuwanta,
"Adda lafiya?" Tana duba agogon dake gefen gadonta ƙarfe biyu saura, d'an yatsina fuska Nihal tayi ba tare data bi takan taba ta ce,
"Janany sister nakasa bacci, zan iya kwantawa a d'akinki?"
"Eh Adda, amma me yasa?" Ta ƙare zancen tana matsawa gefe haɗe da janye mata duvet, bata ce da ita komai ba har saida ta kwanta ta rufa mata duvet ɗin sannan ta ce,
"Janany sister"
"Na'am Adda ta" ta faɗa tare da matsa kusa da ita ta ɗora kanta a saman kafad'arta,
"Kin ji haushi na d'azu ko?"
"Ko d'aya Adda t, amma pls..."
"No..ya isa haka tunda dai baki jiba, mu kwanta muyi bacci kin san kina da school gobe" Nihal ta katseta tare da gyara kwanciyarta, turo baki Janan tayi irin bata ji daɗin hanata faɗar abunda tayi niya ba ta koma ta kwanta fuskarta na kallon rufin p.o.p dake saman ɗakin tare da ɗora hannayenta a saman ƙirjinta, da haka bacci mai nauyi ya zo yayi awon gaba da ita,
Daga ita har Nihal basu farka ba sai kusan qarfe takwas saura don kuwa ko sallar asuba basu samu ba saboda nannauyan baccin da yayi awon gaba dasu, a gurguje suka tashi sukayo arwala sukayi sallah yayin da Janan ta had'o gaba ɗaya har da wanka lokacin da tayo arwalar, hakan yasa tana shafa addu'a ta miƙe ta sauya kayanta, dama ita bar fiye yin kwalliya ba don haka mai kawai ta muttsikawa jikinta ta dauki jikka da littafan ta da makullan mota tana sauri ta fice d'akin, dama tuni Nihal ta fita ta yadda har Madam florence ta kammala masu bin kari ta shiga haɗawa Janan nata, tana fitowa daga ɗaki sukayi karo da ita,
"Janany sister, ga breakfast ɗinki na haɗo maki kada kije da yunwa"
"Noo.. Adda nayi latti, zan tsaya a capteria idan mun fito lectures nayi.." bata ƙarasa rufe baki ba Nihal ta naɗo gasasshen biredi (sandwitch) da soyayyen ƙwai ta tura mata abaki saka makon buɗe baki da tayi tana magana, haka ta yita bata abaki har suka kai wajen motar ta, seda ta buɗe marfin motar ta saka jikka da littafanta tukuna ta juyo ta karɓi cup ɗin ruwan kakkauran tea ɗin data miqo mata ta sha fiye da rabi sannan ta miƙa mata cup ɗin ta rungumeta haɗe da cewa,
"Thanks Adda Nihal, bye bye"
"Bye Janany sister, sai kin dawo"
Ta ƙare maganar tana ɗaga mata hannu ganin har ta shige motar ta tayar tana ƙoƙarin fita...
*This page is dedicated to all sister's in the world, no matter how life it change, luv your sister's, care for them d always be by their side👩❤️👩, i luv my sister's and if you luv your #comment #vote, #share, and #like.*
_Srry guyz in sha ALLAH mun dawo kenan, aimun afuwa, masu zagi da masu kyakkyawan fata duka Nagode, sai dai har wayau banyi alƙawarin update kullum ba saboda ina da abubuwa agabana, but i assure you zan ƙoƙarta da yardar ALLAH_
*ALLAH KAJIƘAN IYAYENMU👏😭*
[8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 7_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfar9https://www.wattpad.com/1231887990?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=y3hZPXsR3hFuYm5xsZGdA7ie%2Bxtl6Je1fSdRjxdLY%2BRRYi%2FIiEGinlbsNrmL6MNpxDxsUoIbJ95KSwc9nFtd%2FQZBru%2B0vmFUYEe3iJQabmq5fLoickCYt6guQHzAZi96_
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN
👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
---777778
______________________________
*S* aida ta ga ficewarta tukuna ta koma cikin gida itama ta nemi waje ta zauna ta ƙarasa sauran abin karin data ɗibama Janan, bayan ta gama ta koma cikin ɗakinta ta haye kan gadonta ta jawo system ɗinta ta shiga vedio call da ƙawayen ta dake ƙasar uganda da sukayi karatu tare, wanda mafi aksarinsu har yanzu suna can ƙasar a dalilin aiki daya kai iyayensu suke zama acan.
Janan kuwa da gudu ta fice daga cikin gidan rana ba motar wuta har ta kai bakin gate ɗin makarantar, a hankali ta soma rage wutar motar lokacin data isa kafin nan ta shiga ciki don gudun kar abun daya faru jiya ya sake faruwa, cikin yardar ALLAH har ta ƙarasa department ɗin nasu ta daidaita tsayuwar motarta haɗe da fitowa ta shiga cikin ajin malamin bai zo ba, lokacin har ƙarfe takwas da mintuna biyar tayi, ajiyar zuciya ta sauke haɗe da samun waje ta zauna tana kallon Amira da tayi tuƙun-tuƙun da fuska ta d'auke kai, saida ta jima da shiga sannan malamin nasu dake ɗaukarsu course ɗin (chemical-Ako-Carbony/compound) a fannin Chemistry/computer da take karanta ya shiga, cikin natsuwa da kwanciyar hankali ta fara sauraren bayanan da yake yi, kasancewar tanada tsananin kaifin basira yasa cikin ƙanƙanin lokaci ta gama fahimtar dukkanin abinda yake koyarwa, don indai ƙoƙari ne to Janan ba baya ba, irin ɗaliban nan ne da ake kira da intellegent, ba kowa ne zai fahimci hakan a tattare da ita ba sai wanda suka zauna tare, sai kuma su kansu malaman kasancewar ita ɗin tana ɗaya daga cikin sahun ɗaliban da ake kira introvert acikin aji, duk da tanada basira sosai basa fahimtar hakan har sai idan anyi mata tambaya ta amsa ko kuma idan anzo wajen test ko jarabawa a nan ne take baje dukkanin basirarta da kuma baiwar da ALLAH yayi mata har suka gane irin talent ɗin da take dashi.
Bayan sun gama ta ɗago ido tana kallon Amira data ɗaure fuska ta kauda kai gefe tana ƙoƙarin miƙewa, da alama har lokacin bata daina fushin da takeyi da ita ba akan abunda ya faru, murmushi tayi tare da riƙo hannunta, ta ce
"Amira barka da safiya, kin tashi lafiya"
Ba tare data juyo ta kalleta ba ta ce "lafiya" can ciki ciki, murmushi Janan ta sakeyi karo na biyu tare da miƙewa tsaye ta dawo gabanta suna fuskantar juna, ta ce
"Amira kenan! Wai har yanzu fushi kike dani akan abunda ya faru jiya? To kiyi haƙuri don kuwa ni har na manta da hakan, kuma nasan ai duk wannan abun da kikeyi akan na kaɗe mm ne na kasa tsayawa na kula dashi ko? To kiyi haƙuri shima jiya na je na bashi haƙuri har ma na ɗaukesa a mota muka je clinic aka bashi magani, ina shikenan ai ko?"
Da wani irin ƙarfi Amira ta juyo jin abunda Janan ta faɗa tana jifar ta da wani irin kallo mai cike da tuhuma,
"Kika ce kin ɗauke sa Janan? Kuma a motarki?" Ta ƙare maganar cike da tsantsar kishi daya tirniƙe mata zuciya,
Lumshe idanuwa Janan tayi tare da jinjina kai alamun tabbatar mata da hakan fuskarta ɗauke da murmushi, kasa jurewa Amira tayi har saida ta bayyanar da jin haushinta ƙarara ta hanyar fizge hannunta daga riƙon da tayi mata ba tare da tasan tayi hakan ba, wani irin da nasani take ji aranta na zamowa silar da har mm zai shiga motarta daga shi sai ita, da tasan hakan zai faru ko ɗaya da bata nuna mata ɓacin ran ta jiya, atunaninta faɗan da sukayi yasa Janan fahimtar kuskurenta ta je gyarawa, tambayar kanta ta shiga yi wai ma taya ta samu wannan damar har hakan ta faru awajen mm, mm ɗin dako kallo macce bata ishesa ba balle akai ga yayi mata magana ko kuma ya kulata, amma shine har ita tasamu fuskar da zai shiga motarta, how?, Ta sake tambayar kanta a karo na ba adadi, "mtssss..." Ta ɗan ja tsaki cike dajin haushi ba tare data sani ba.
Zaro idanuwa Janan tayi cike da mamaki ta ce,
"Meye kuma Amira?, Ko shima wannan d'in baiyi ba har yanzu ina da sauran laifi?"
Sai alokacin Amira ta ankare da abubuwan da takeyi da sauri ta saki fuska haɗe dayin yaƙen da baikai zuci ba ta ce,
"Noo...ba haka bane, babu wani sauran laifi da kike dashi, dama dai kin san shi ɗan adam daraja ne dashi a duk yanda ka gansa, shiyasa na nuna maki rashin jin daɗi na akan halin ko in kula da kika nuna masa kika shigikke lectures abinki, amma yanzu tunda kin gyara shikenan komai ya wuce"
"Kin tabbata?"
"Sosai ma, muje muyi break kafin sir Victor ya shigo" wanda ke ɗaukarsu course na gaba da zasu shiga wato chemical kinetic.
"Muje dai na rakaki don ni kam alhamdulillah a ƙoshe nake"
"To muje, daga nan ma sai mu biya wajensu mm na siyo dabino"
"To shikenan" Janan ta bata amsa ataƙai ce tana sagala jikkarta a kafaɗa, basu wani jima ba acan wajen cin abincin don indomie kaɗai da soyayyen ƙwai tasa aka dafa mata taci Janan ta biya kuɗin sannan suka fito suka nufi wajensu mm, duk wanda yasan yanda dafin so ke harbawa a zuciya to yana kallon Amira zai fahimci hakan saboda yanda ta shagala da kallon mm tun kafin su ƙarasa, tsabar kallonsa kad'an ya rage ta fad'i sanadiyar wani irin tuntuɓe da tayi har saida Janan tayi saurin riƙota,
"Subhanallahi sannu, me kike kallo haka Amira kike neman faɗuwa ki ja mana abun dariya"
"Ba komai Janan, wani abun dai nake tunani"
"Tunani kuma? ALLAH ya kyauta, amma kiyi ƙoƙarin ajiyesa gefe don kar ki kai kanki ki baro"
Mm kuwa tuni dama ya ci alwashin danne duk wani abu da yake ji azuciyarsa akan Janan har sai lokacin daya kamata ya bayyana mata hakan yayi, ma'ana har sai ya gama sanin ko waye ita, hakan yasa kyakkyawan kallo ɗaya yayi mata lokacin daya hangosu tafe ya kauda kai haɗe da ci gaba da gyaggyara dabinon sa, duk da ba kallonta yakeyi ba yakan ji bugun zuciyarsa na tsananta a kowane taku ɗaya nata dake kusanto da ita agaresa, ɗan runtse idanuwa yayi lokacin da suka ƙaraso ƙamshin turarenta ya daki hancinsa ya sauke wata irin sanyayyar ajiyar zuciya a hankali,
Yana ji suna gaisawa da Jabir tana tambayarsa ya mai jiki amma yaƙi koda kallon gefen da take balle tasa ran zaiyi magana, hakan kuwa ba kaɗan ya yiwa Amira daɗi ba data fara tunanin ko akwai wani abu da mm ya fara ji akan Janan da har ya kulata tare da bata damar da zai iya shiga motarta, yanda tayi tsaye ta ƙura masa idanuwa yasa Jabir da suka gama gaisawa da Janan juyowa ya ce da ita, "ke lafiya? Me za'a baki"
"Amm.. zan sayi dabino ne amma wannan nake so" ta ƙare zancen tana nuna dabinon mm dake gabansa, sai alokacin ya ɗago haɗe da miƙa hannu ya karɓi kuɗin da take miƙo masa fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ce,
"Na nawa?"
"Na duka zaka bani" ta faɗa tana wani gyara tsayinta haɗe da sakin wani irin ƙayataccin murmushi, yana ganin hakan ya ɗaure fuska tare da ɗauke kansa ya ciro leda ya zuba mata dabinon daidai na kuɗinta ya miƙo mata,
"Na gode" ta faɗa haɗe da karye murya tana wani fari da idanuwa, yi yayi kamar bai ganta ba tare da ɗauke kansa gefe ya miƙa hannu yana ƙoƙarin ɗauko sinƙin leda a baron Jabir dake faman fira abunsa da Janan tana dariya don tashi ledar ta ƙare, kamar ance ya ɗago idanuwa karaf suka haɗe dana Janan data ɗago itama a lokacin,
"Barka da safiya mm, Ina kwana an tashi lpy?" Ta faɗa tana ƙarewa yanayinsa kallo tamkar ba shine mm ɗin jiya data kaɗe da mota.
"Lafiya lau" ya amsa mata shima cikin basarwa duk da wani irin yanayi da yake ji na fizgarsa, sautin muryarta ya jiyo ta sake cewa,
"Ya jikin?, Hop kan ya dena ciwo ko?"
"Eh, alhamdulillah, naji sauki" ya sake bata amsa, daga haka bai ƙara cewa komai ba, don haka sai itama ta ƙyalesa tare da ciro naira dubu ta miƙawa Jabir,
"Gashi nima ka bani na ɗari biyu tunda Amira ta siya a wajensa"
"To shikenan" Jabir ya faɗa tare da ciro leda ya zuba mata fin na naira ɗari biyun da ta ce har da ƙarin kwakwa aciki ya miƙo mata haɗe da canjinta yana faɗin,
"Yawwa, gashi ko, mun gode da cinaki"
"A'a riƙe canjin ko ruwa kwa ƙara ku siya"
"A'a ba'ayi hakan ba, kedai karɓi canjin ki"
"Laaa..wlh bazan karɓar ba, dubi fa har da ƙarin kwakwa kayimun aciki, kaidai ALLAH ya ƙaro kasuwa mu munyi aji, mm ALLAH yaƙara sauƙi" ta faɗa tana kallonsa lokacin data gama duba ledar dabinon tare da juyawa suka bar wajen ba tare da ta jira me mm ɗin zai faɗa ba.
Amira kuwa sai wani iyayi takeyi da kwarkwasa tana go and come kafin Janan tagama magana da Jabir har suka bar wajen, a haukanta hakan zaisa ta burge mm, abunda bata sani ba shi gaba ɗaya ma hankalinsa ko a gangar jikinsa baya nan balle kuma gareta, aa salima tuni ya shagala wajen sauraren zazzaƙar muryar masoyiyarsa da yake ji tamkar ya fizgota a jikinsa ya rungume saboda wani irin magana ɗisu dake ɗibarsa.
Janan kuwa ko kaɗan hankalinta bai kai ga abubuwan da Amira keyi ba balle har tasan inda ta nufa, kawai dai ita a tunaninta Amira na cikin irin mutanen nan ne da basa son ana walaƙanta mutane, kallon ta tayi ganin yanda walwalarta da farin cikinta suka ƙaru ta ce,
"Ni kam dai Amira wannan farinciki da kikeyi duk na meye?"
"Abun sirrine ƙawata, bazan faɗa maki yanzu ba sai nan gaba idan ta gama wari ta fashe" da yake Janan bata fiye son matsawa mutane ba sai kawai ta amsa mata da to,
Haka suka ci gaba da shiga lectures ɗin ranar har suka gama, amma abu ɗaya ya ɗaurewa Janan kai shine yanda mm ya sauya, gaba ɗaya ba mm ɗin jiya bane data sani take hangowa acikin idanuwanta! Me yasa? Ko ya fara jin haushin abunda tayi mashi ne jiya? Haka ta rinƙa saƙawa da warwarewa ba tare data ankara ba har suka tashi gaba ɗaya, ajiyar zuciya tayi tana tambayar kanta to wai ma meye damuwarta don ya sauya?, Shi ya sani, rayuwarsa ce ba tata ba, kuma tunda haka yake buƙatar tafiyar da ita ai sai ta ƙyalesa meye na damar da kanta, ba tare da ɓata lokaci ba kawai ta tattarasa gaba ɗaya ta watsar itama,
Amma ga mamakinta har ta isa gida lokacin ƙarfe shida daidai na marece tunaninsa bai gushe mata ba a zuciya, gaba ɗaya sai ji take abun duk ya dameta, shin me hakan ke nufi ne? Ta tambayi kanta da kanta.
Ganin ba tada amsar tambayar yasa ta tuɓe kayan jikin ta ta faɗa toilet tayo wanka ta fito, tana fitowa Nihal na turo ƙofar ɗakin cikin shirinta dake nuna alamun fita zatayi, tayi matuƙar kyau sosai tamkar ba ita ba, ta ce
"Janany sister kin dawo?"
"Eh Adda Nihal, fita zakiyi ne?"
"Eh, ko zaki zo muje ki rakani"
"Nooo..bazan iya zuwa ko ina ba gaskiya na gaji"
"Ok bye, pls kici abincinki kinji ko?"
"Ok i will in Sha Allah, adawo lafiya"
Daga haka Nihal bata sake cewa komai ba ta fice ta ɗauki motar ta nufi wani irin katafaren supermarket, dama sayayyar kayan sha fa zata yi masu ita da Janan don sun ƙare,
Kiraye kirayen sallar magrib da taji anayi yasa ta fara ɗaukewa ta hanyar gidan wata ƙawarta dake kusa da wajen tayo sallah sannan ta dawo ta shige supermarket ɗin, sai da tayi sayayyar duk abubuwan da take buƙata ta gama sannan ta shiga zaɓawa Janan abubuwan da tasan itama tana so ta je ta biya kuɗin aka saka mata a leda ta d'auko, tana kawowa bakin ƙofar fitowa su kayi karo da Razina dake ƙoƙarin shigowa ita da Momy da mm dake biye dasu a baya, faɗuwa ledar dake hannunta tayi gaba d'aya kayan suka zube suka ƙ'asa haɗe da watsewa, cikin ɓ'acin rai ta ɗago fuskar nan a ɗaure babu alamun mutunci ta d'aga hannu da niyar wanke Razina da mari mm dake saye cikin wata irin gizna mai masifar kyau kalar ruwan ƙwai tasha anyi mata ɗinkin nan da ake kira zauren ɗari amma irin na zamani fuskarsa saye da gilashi yayi saurin riƙe mata hannu haɗe da cewa..
*ALLAH KAJIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 8_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9https://www.wattpad.com/1232233680?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=UZ6w6%2B3P4SM9m%2B8oYMWOxC2OyAGths4uDQxLM3q6nPRYMbCLxiH1RNJcVgzJpQYUxW%2B5O%2BxuVk%2FFa7s%2Fxg8lt6kLSy9JyW7RbiViaLpuS7WywxghkDQgIFmxcG58ppYg_
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN
👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
---777778
______________________________
"A'a 'yan mata, ai ba'ayi hakan ba tunda karo ne kukayi da juna, abunda kawai zan iya cewa shine kiyi haƙuri bisa zubewar da kayanki sukayi amma ba sai an kai ga duka ba" ya ƙare maganar tare da sakin hannun nata sannan ya ja Razina dake watsa mata wani irin mugun kallo cike da tsana ya maida gefensa, itama Momy haƙuri ta shiga bawa Nihal ganin yanda ranta ya ɓaci sosai, ga mamakin ta sai taga Nihal data kafe mm da idanuwa tana kallo tayi murmushi haɗe da cewa "ba komai mama" har lokacin idanuwanta na akansa har da wani kar kace kai tana ƙare masa kallo
Mm kuwa da bai masan abunda take yi ba duƙawa yayi da kansa ya kwashe mata duka kayan ya mayar mata a ledar da suke ciki sannan ya miƙa tsaye ya miƙa mata haɗe da kallon Razina ya ce,
"Kibata haƙuri"
Sai da Razina ta fara cuno baki kafin can ciki-ciki tace wa Nihal,
"Kiyi haƙuri"
Nihal da har lokacin idanuwan ta na akan mm ta d'agawa Razina hannu kawai haɗe da karɓar ledar da yake miƙo mata ta ce "Na gode" fuskarta a sake ɗauke da murmushi.
Murmushin shima yayi mata haɗe da jan hannun Razina suka ƙarasa shigewa daga ciki tana faman gunguni ita ala tilas taji haushi, a zahiri kuwa cewa takeyi, "ALLAH shiyasa bana son fita dakai ya Muhriz, da ya Jabir ne da yanzu ya koyawa matar can hankali musamman idan ta sake ta mare ni, kiji fa Momy ai gaba ɗaya mukayi karo da juna amma shine zata wani d'aga hannu tace zata maran"
"To
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 40