acikin sa, domin na tabbatar maku da hakan nazo maku da kaɗan daga cikin wannan ƙayataccen littafi nata mai matuƙar ɗaukar hankali, ta bakin malam bahaushe dai, ya ce gani ya kori ji👇*
*Waminal Hoob*
_Asmy b Aliyu_
PAID BOOK##
Love#
Friendship#
Family#
NooryAli#moments
Tana ganin yarda jikinsa ke wani irin kadawa ,jawota yyi ta fado kansa Yana shakar kamshinta Yana sakin ajiyar xuciya ,kallon cikin kwayar idanunsa take .Wanda ya canja kala har kwallah take hangowa acikin su ,a hargitse ya shiga subbatar ta ta koina Yana tura kansa cikin Wuyanta,hawaye taji suna cika Mata ido tuno farhaan kurum,hade fuskarsa yyi da Tata fuskar Yana goga hancinsa da nata da wani irin Murya Yake fadin"I try Am very try Noory u belong to someone else,ya fada muryarsa na karyewa A hankali kafin ya hade bakinsa da nata.
Friendship#
Aliyu waxeer
Farhaan Shagari
"Da Alamar bakada hankali Farhaan ka Samu tabin kwakwalwa,ni kake tunanin naje na auri yarinyyar da kakeso har na tsawon shekara daya??''yyi maganar so pissed up ,farhaan ya kwantar da Kai Yana fadin nasan Nooriyyah Bata cikin kalar matan da kakeso ,nasan ba ajinka bace .Haka nasan baka sha'awar (BAKAR MACCE")bestT xakayiwa wannan Alfarma da xarar na kammala master's Dina xan dawo gareta muyi Aure!!"girgixa Kai Aliyu waxeer ya shigayi Yana fadin ka haukace Farhaan!!!"
Waminal Hoob#
Is out on the 31july..stay tuned and find out!!!!
Love is in the Air#
Team Noory-Ali#Forever❤️
FRIENSHIP##
Aliyu waxeer
Farhaan Shagari
Areefa Mansoor
Laylah waxeer
FAMILY#❤️
Wazeer Family
Shagari Family
Azeex Ali Family...
______________________________
Sun jima a cikin guiden ɗin ko wace na abunda ke gabanta har aka kira sallar azahar, Janan ce ta fara miƙewa ta nufi cikin gidan kafin itama Nihal tamiƙe tabi bayanta,
Suna kammala sallolin su suka dawo falo suka zauna suna kallon wani shiri a tashar zeeaflam da Nihal ke matuƙar so wanda sanadiyar hakan yasa itama Janan tafara kallonsa, wani saurayi aka nuno aciki Janan tayi saurin cewa, "Adda wannan gayen yana bala'in yanayi da mm ɗina, hadda shi yasa nake ƙara son kallan shirin nan don ba komai nake ganewa aciki ba" dariya ta aza mata har saida tayi mai isarta sannan ta ɗago tana yimata wani irin kallo haɗe da cewa,
"Lallai Janany sister yaron nan ba ƙaramin kamaki yayi ba, anya ma ba asiri yayi maki shiyasa kika ga yafara yi maki gizo a fuskokin mutane? Yanzu fisabilillahi taya za a yi wannan talakan baƙauye yayi kama da haɗaɗɗen ba Indiya nan?, Hmmm ni kam dai akwai wanda na sani ajin farko da gayen nan ke kama dashi amma ko waye na manta shi gaskiya" kutun-kutun Janan tayi da fuska tare da haɗe rai tana yiwa ƴar uwar tata wani irin kallo mai cike da ban mamaki da kuma takaici, badon tana ƴar uwar ta ba da yau ta mayar mata da maganar da har ta mutu bazata taɓa manta taɓa, ba tare da ta ce mata komai ba ta ajiye remote ɗin dake hannunta akan kujera tamiƙe tabar wajen gaba ɗaya, tana jin yadda take ƙwala mata kira tayi banza da ita tare da ficewa daga falon ranta aɓace,
"Mtsss...matsalata dake kenan Janany sister, wani lokacin ki fiye ɗaukar abunda ba wani abuba da zafi" ta sake sakin tsakin akaro na biyu tare da janyo remote ta gyara zamanta ta cigaba da kallon ta, ita kuwa Janan part ɗin Hajiya zee ta nufa tana mai sake jin ɗacin kalaman ƴar uwar tata akan masoyinta idan ta tuna, koda ta shiga kitchen ta samu Hajiya zee tana ɗauraye kayan data gama girki dasu yanzu, cikin girmamawa ta ƙara sa daga ciki tare da karɓar foodflaks ɗin da take wankewa tana faɗin,
"Barka da rana Aunty zee, ina wuni?"
"Lafiya klw, Janan ya kuke?" Ta amsata cikin sakin fuska da fara'a, saida ta ɗauraye foodflaks ɗin dake hannunta sannan ta juyo tana kallon ta, ta ce
"Lafiya lau nake"
"Adda ɗin ki fa, taji sauƙin?"
"Eh taji" ta bata amsa ataƙaice tare da cigaba da ɗauraye mata sauran kayan, kasancewar Hajiya zee macece ba mai yawan surutu ba yasa daga haka bata sake cewa da ita komai ba, haka itama bata ce komai ba har taƙarasa ɗauraye kayan gaba ɗaya, ta shiga goggoge mata ita kuma tana maida su inda ya kamata, bayan sun gama Hajiya zee ta kalleta tana murmushi haɗe da cewa,
"Sannu da ƙoƙari Hajiyar gida" don haka take kiranta wata ran idan tana jin tsokana, musamman idan ta ganeta ba daidai ba saboda sunan grand ma da take dashi, ɗan murmusawa Janan tayi haɗe da ficewa daga kitchen ɗin ta dawo falo ta zauna tana faɗin,
"Hmmm! kar muyi haka dake Aunty zee, ai kece Hajiyar gida, uwa maba ɗa nono sukutum da guda"
"Au! To ai shikenan kin rama, agaisheki ALLAH yayi maki albarka" ta faɗa tare da ajiya bowl ɗin data zubo cake da samosa aciki akan center table ta tura mata agaban ta, sannan taje ta buɗe fridgeyta ɗauko fresh yougurt da gorar ruwa ta ajiye mata itama ta zauna a ɗayar kujerar dake kallon ta, sunkuyar da kai Janan tayi haɗe da cewa,
"Nagode da addu'ar ki Aunty zee, Amin ALLAH ya karɓa"
"Ba komai, yau Auntyki kwaɗayi bata yi abincin kirki ba, gashinan ki taɓa"
"Kai Aunty, kullum bakya gajiya sai kiyi ta maidani tamkar wata baƙuwa"
"Ai kamar haka kike Janany, da yaushe da yaushe nake ganin ki in ba ALLAH ya kawo mani ke ba?"
"Kiyi haƙuri Aunty, kin san yanayin karatu ban fiye zan gida ba"
"Duk da haka dai"
"To ayi haƙuri zan gyara"
"ALLAH ya nufa" ganin ta kasa cin komai sai latsar waya takeyi yasa aunty zee jawo bowl ɗin ta ɗauki samosa ɗaya taci tare da ɗauki wani freshyourght ɗin ta shiga sha, don irin wannan halin kusan ɗabia ce da mahaifinsu ya nuna masu ta rashin yarda da ita shiyasa idan Janan tayi bata fiye jin haushi ba, a fannin Janan kuma gudun faruwar wata ƙaddara ko akasi bayan ta shigo part ɗin nata kesa take taka tsantsan don kar taja mata matsala tunda har mahaifin nasu baya buƙatar haka, sannan shi mutum ne da baisan ƙaddara ba koda ba abunda ya faru da ita data shigo part ɗin zai iya ɗora mata laifin da bata ji bata gani ba, ɗago kai tayi cikin son kawar ma da aunty zee tunanin ta ta ce,
"Aunty fa yau azumi nakeyi kar kufa ban taɓa komai ba"
"To shikenan ai" ta faɗa tare da jawo bowl ɗin agaban ta taci gaba ɗacin abunta, ita dai da zuciya ɗaya take da yaran ALLAH ma ya sani, batada wani buri ko manufa nason cutar dasu, ta faɗa a zuciyar ta tana mai jin ɗacin abun aranta, shekaru da shekaru abu yaƙi ci yaƙi canyewa balle tasa ran samun sauyi a rayuwa, kullum baƙar aƙida da taurin kan mahaifin nata sai ƙara tsanan ta yakeyi, wannan wace irin rayuwa ce haka?, Ta sake tambayar kanta a karo na biyu, Janan na kula da yanda yanayin ta ya canza don haka sai ta jefo mata wata tambayar don ta kautar mata da wancan tunanin,
"Aunty, Wai meyasa mutane suka fiye son kai da ɗaukar damuwarsu ita kaɗai ce damuwa?"
"Ga amsarki nan cikin tambayarki Janan, ai son kan da suke dashi shi yake jawo haka, sai kuma zallar zalunci don wani abun zalunci kawai kesa ana yinsa"
"Kamar ya?, Nifa a tunani na zalunci na ta'allaƙa ne a inda babu soyayya, taya wanda ke son ka zai iya zaluntar ka?"
"Janan kenan, ai duk son da mutum zaiyi maka bazai kai wanda yake yiwa kansa ba, duk yanda kake dashi kuwa, uwace kawai zan iya cewa zata so ɗan ta fiye da kanta aduniya amma bayan ita tabbas babu na biyunta a duniya, kuma duk hakan na cikin son kai"
"A tunani na duk duniya ba nida wanda ke sona sama ga Addata, amma meyasa take nuna rashin so ga abunda ni nake so, kuma take fifita damuwarta saman tawa, idan haka ne wannan ya nuna tafi son kanta akaina?"
"To bazan ce wani abuba anan, iya sanina dai ke ƴar uwarta ce da batada kamarki aduniya haka itama ƴar uwarki ce da bakida kamarta, tamkar idanuwa kuke, duk abunda ya samu ɗaya idon to ya samu ɗayan, alkhairi ne ko kuma akasin sa, ɗaya na so ko baya so, wannan shine kawai"
"Kin ƙi ki fahimta Aunty zee, shin idan har haka ne bayanin ki, ni meyasa Adda bata son wanda nake so"
"Kin jiki da wata magana Janan, ai shi so ALLAH ke sakashi a zuciya, ba hurumi ne na ɗan adam ba, kuma idan har haka ne abunda kika faɗa to ki haƙora da abunda bata so mana, ko kuma ita ta thaƙura dashi sai azauna lafiya"
"Zancen haƙura dashi hurumin a ne ba nata ba, kuma ni bazan iya hakan ba koda duniya duka zata juyamun baya"
"Tirƙashi, to abunda zaifi dacewa anan shine kibi lamarin da addu'a, sai kiga ALLAH ya daidaita ra'ayin naku, amma dai ko meye kada ki kuskura ya zamo dalilin haɗaki da ƴar uwarki don ba kida kamarta aduniya"
"To aunty nagode sosai" ta faɗa tare dayin murmushi sannan ta maida hankalin ta ga wayar ta, har aka kira sallar asar Janan bata koma part ɗin su ba tayi zamanin ta anan, haka ma sallar magrib anan tayi abutta, kasancewar ta cewa aunty zee azumi takeyi yasa tana gama magrib ta shiga kitchen da kanta ta dafa masu indomie ƙwaya uku da seiden, sai kuma ƙwai guda biyu da ruwan tea saboda jin da tayi ta ce bata dafa abinci ba, sai da ta kawowa Aunty zee nata sannan ta ɗauki nata itama ta zauna tana ci,
"Sannu da ƙoƙari, keda ke azumi shine zaki wani wahalshe da kanki haka?, ALLAH yayi maki albarka"
"Amin Aunty, ba komai"
Ganin har bayan magrib Janan bata dawo ba yasa Nihal fitowa tanufi wajen guiden da niyar dubota, amma ga mamakin ta sai ta isko wayam bata ciki, lungu da saƙo ta ta koma cikin gidan tana dubata har ɗakin ta bata ganeta ba gashi Madam florence bata nan duk sai taji ta tsargu da zama ita kaɗai, waje ta sake fitowa ta sake duddubata a harabar gidan da can wajen parking space nan ma bata nan, har wajen motarta ta sake zuwa ta dubata amma bata ganeta ba hakan ya tabbatar mata da cewa tana part ɗin Hajiya zee, ɗan tsaki ta saki haɗe dayin tsaye tana tunanin ya zatayi ne, shin taje ne ko kuwa ta komawarta part ɗin su, ta saki tsaki yafi a ƙirga kafin tayi ƙarfin halin fuskantar part ɗin Hajiya zee ɗin, ba kunya ta kutsa kai ta shiga har cikin falon, kallo ɗaya Hajiya zee tayi mata cike da mamakin abunda ya kawota sannan ta ɗauke kai, Janan kuwa ƙin ɗagowa ma tayi balle tanuna tasan da zuwanta wajen,
"Janany sister ke nake son gani" ba tare da Janan ta ɗago kai ta kalle ta ba ta ce,
"Gani"
"Ki taso mana"
"Abinci nake ci, idan na gama zan zo"
"Please.." ta faɗa cikin marairaice murya don ta lura har yanzu haushin ta take ji, ɗan rolling ɗin idanuwa Janan tayi kafin tace,
"Amma dai Adda ai kinga ba ni kaɗai ce awajen ba, kiyi magana da ita idan ta amince haka musulunci yace" babu yanda Nihal ta iya don tana da buƙatar Janan tare da ita, don haka cike da takaici ta ce,
"Sannu, ina son ganin ƴar uwata" ba tare dako kallon gefen da Hajiya zee take tayi ba, ɗan murmushi Hajiya zee ta saki haɗe da cewa,
"Sannu Nihal, ya jikin naki?" ta amsa mata a daƙile haɗe dayin ɗan siriri tsaki sannan tabar wajen, Janan bata tashi ba har sai data ƙara sa cin abincinta takai plate ɗin kitchen ta wanke sannan ta fito tayiwa Hajiya zee saida safe ta wuce, ga mamakin ta har lokacin ashe Nihal na nan waje tana jiranta, ko ta kanta bata bi ba tawuce part ɗin su, bayan ta tabi tana kiran sunan ta tayi banza da ita har suka isa tsakiyar falon,
"Haba Janany, nifa yayarki ce amma inayi maki magana kinyi banza dani" tsaye cak Janan tayi daidai lokacin data riƙe ƙarfen upstairs ɗin tana ƙoƙarin hawa sama, saida Nihal ta sake kwantar da murya haɗe da cewa,
"Koma meye kiyi haƙuri tunda haushi na kike ji" sannan ta juyo tare da folding hannayenta akan ƙirji tana kallon ta, ta ce
"Upcouse dole naji haushi tunda kin kushe mani masoyi kuma kin aibantashi agaban idanuwa na, hakan kuma ya nuna cewa nima zaki iyayi mani tunda har kika yimasa"
"Oh my God, Janan kidena haɗa kanki dashi, ke daban shi daban, don ina son ki ba lallene dole saina so shi ba, kece ƴar uwata kuma damuwata"
"Wannan ƙwarya ne Adda, idan har ni kina so na to dole ki soshi tunda ina son sa, haka kuma dole ki damu dashi in har kin damu dani, idan kuma bazaki iya ba so let respect each other, kidena aibata shi agabana ko bayana, bana son hakan, kuma wannan kalmar da kika jefesa da ita karki manta shi ALLAH jujjuya lamarinsa yakeyi, za a iya wayuwar gari kina mai neman wata buƙata a ƙarƙashin sa asanadiyar ɗaukaka shi da ALLAH zai iya yi"
"What ever dai yanzu kiyi haƙuri, in sha ALLAH wannan ranar ma bazata zo ba, ai magana yayi gaba..." Girgiza kai Janan kawai tayi tare da hayewa sama tana mamakin yanda take faman lurar da Nihal amma tana sake faɗar maganganun da basu kamata ba, ALLAH ya ganar damu ta fada a zuciyar ta tare da shigewa ɗakinta ta rufo ƙofa, shiru Nihal tayi cike da mamaki, anya kuwa ba waccan matar ta sake zuge ta ba har tayi fushi haka? Ta tambayi kanta ciki zuciya haɗe da cije baki ta girgiza kai tana faɗin,
"Bari Abban ya dawo"
***. ***. ***
Mm kuwa yanayin aikin da yakeyi ya dakatar da zancen tafiyarsa ƙauyen iyayensa daya tashi yi jibi, don kuwa sun kirasa akan lallai gobe gobe ya dawo bakin aikinsa, hakan yasa ya bar tafiyar har sai nan da wani wata idan ya dawo.
Washe gari ya shirya tsaf misalin ƙarfe takwas na safe ya kira Janan ya ce yana son su haɗu gidan grandma zasu zo tare da Jabir, sosai hakan yayi mata daɗi ta shirya cikin koriyar atamfarta mai ratsin baƙi riga da sket ta yafa mayafi shima ɓaki da takalma baƙaƙe, ta feshe jikinta da turarukka masu matuƙar ƙamshi, tayi kyau sosai ta ɗauki jikkarta itama baƙa da makullan motar ta ta nufi gidan grandma tana sauraren suratul baƙara aciki har ta isa.
Tana isa su mm na isowa, lumshe idanuwa tayi ta buɗe ganin irin shigar da yake cikin ta, badon ko idanuwanta sun kasa gane mm ba zuciya da kuma ƙwaƙwalwar ta baza su taɓa mance fuskar sa ba da ta ce sam bata ganesa ba saboda kyan da yayi mata, yana murmushi ya ƙaraso wajen motar ta lokacin da tayi parking tare dasa hannu ya buɗe mata,
"Barka da isowa tauraruwar matan duk duniya" ya ƙare zancen yana mai rissinar da kansa haɗe da dafe saiti ƙirjinsa.....
*ALLAH KAJIƘAN IYAYENMU👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 40_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
______________________________
Murmushi tayi cike dajin daɗi ta miƙo masa hannu, ƴar hararar ta yayi irin ta masoya ɗin nan kafin ya miƙa hannu yana ƙoƙarin riƙo hannun nata tayi saurin janyewa tana dariya,
"Sorry mr.man, har yanzu da sauran lokaci, yi ƙoƙarin jajircewa akan wannan tayin dana yimaka, don kuwa farashin nasa tsadaddene" saida ya shafo haɓarsa yana ƙare ma kyakkyawar halittar ta kallo sannan ya ce,
"Duk girman tsadar sa a shirye nake dana siya koda kuwa komai nawa zai ƙare, ciki har da rayuwata amma bayan na aureki" ya ƙare zancen yana nuna ta da ɗan yatsa haɗe da kashe mata ido ɗaya, murmushi ta saki tare da sakin marfin motar da take riƙe dashi ta juya ta rufe sannan ta juyo tana kallon sa,
"Ka yanka kuwa?"
"Me ya faru?"
"Kayi masifar kyau, kamar na saka maka niƙab" buɗe baki yayi haɗe da zaro idanuwa yana tafa hannuwa kafin ya riƙe haɓar bakin sa,
"Liƙabi kuma ni Muhammadu?, Don ALLAH rufan asiri tunda dai ba macce nake ba" Janan na dariya ta shiga takawa a hankali ta nufi inda ta hango Jabir tsaye yana dannar waya,
"Ina kwana?" Ta gaida mm kafin su ƙarasa wajen,
"Lpy klw my princess, kin ganki kuwa?" ta ɗago kai tana murmushi ta kallesa haɗe da cewa,
"Za ka rama kenan!"
"Ko ɗaya, kinfi kyau kyaune nagani shiyasa nayi magana"
"Na kai ka?"
"Wake zancena ranki shi daɗe, ai kyan ma kin fisa kyau nake faɗa maki, badon kar na takuraki ba da nace ke yakamata ki riƙa saka niƙabi kina ɓoyemun kyakkyawar fuskar nan taki ni kaɗai"
"ALLAH hubbin ruh"
"Sosai ma kuwa"
"Ya Adda Nihal?"
"Tana gida na baro, lafiya klw"
"Ta huta abunta, ita sam bata gajiya da zaman gida"
"Haka rayuwar ta take, bata son mutane shiyasa bata fiye son mu'amala dasu ba, har aiki Abba ya nema mata amma ta ce bata so, kuma ya ƙyaleta"
"Tab, ai kuwa mutum rahama ne, kuma data daure tayi amfani da damar ta tun yanzu, nidai a nawa fannin banga laifi ba don macce tayi aiki, at least kodta zata zama dependant kaɗan ne ko ba haka ba?"
"Haka ne kam, amma rayuwar tace, kuma tunda haka ta zaɓa babu yanda zamuyi da ita"
Daidai lokacin suka iso inda Jabir ke tsaye ya ɗago kai ya kallesu, sannan ya ce,
"Ai nazata ma bazaku ƙaraso ba, kuna wata tafiya a hankali sai kace wuɗanda basa son taka ƙasa" ya ɗan ja tsaki haɗe daci gaba da cewa,
"Ni nafara gajiya da wannan tsayin malam idan ku bakwa buƙatar zama" kallon Janan dake kallon Jabir cike da tsantsar so irin na ƴan uwantaka mm yayi haɗe da cewa,
"Kin ga halin mutumen naki ko?"
"Ai da gaskiyar sa, tuba muke ya Jabir ayi haƙuri"
"Ƙyalesa Janan, ai nasan duk laifin nasa ne, ya kike?"
"Lpy klw, ina kwana"
"An tashi lafiya mrs.mm" ya faɗa cikin sigar tsokana yana gyara tsayuwar sa, Janan dake ji tamkar ta bayyana masa matsayinta awajensa don suyi shearing farincikin ta ce,
"Lafiya klw ya Jabir, wai meye sirrin naga kai da mutumen duk kun sauya tamkar ba ku ba, kodai akwai abunda kuke ɓoye mun don ban fahimci wannan gayun naku haka ba?" Gaban mm ne yayi wata irin muguwar faɗuwa, don gaba ɗaya yama manta da plan ɗin su shiyasa bai sauya shiga ba saboda yanda yake so yana barin wajen zai wuce filin jirgi zuwa Abuja, cikin daburcewa ya kalli Jabir yana sosa gefen kansa haɗe da cewa,
"Ai a..." Kafin ya ƙarasa Jabir yayi saurin katsesa ta hanyar cewa,
"Ba kya son sauyin ne?"
"No..ba haka nake nufi ba, na san dai ba haka nasan ku ada ba, shiyasa kaji nayi magana"
"To kiyita addu'a, in sha ALLAH zaki ci gaba da ganin mu haka, bai faɗa maki cewa na samu aiki ba a wani shagon abokina na saida kayan sawa?"
Saida ta kalli mm da taji yayi wata irin ajiyar zuciya sannan ta ce,
"Ya manta ƙilan shiyasa be faɗamun ba" tana ƙare kallon nata ga Jabir, ƴar gyaran murya mm yayi kafin yace,
"Oh my God, kiyi haƙuri na manta gaskiya, ai shiyasa kika dena ganinsa kwana biyu, wani abokin mu ne ya buɗe shagunan saida suturu, kusan tare muka tashi dashi to shine fa ya bawa Jabir tsaron ɗaya daga ciki, kuma alhamdulillah yana taimaka mana sosai don waɗan nan kayan ma shiya ɗunka mana tare"
"Wow..gaskiya ya kyauta, ALLAH ya saka masa da alkhairi kuma ya hore maku naku nakan ku da zaku taimaki wasu"
"Amin ya rabbi, shiyasa nake matuƙar son ki, kina da uzuri da kuma sauƙin fahimta, kiyi haƙuri na shafa'a ne"
"Ba komai ya wuce" Janan ta faɗa haɗe dayin murmushi, duk da har yanzu jikin ta bai gama yarda da abunda ya faɗa ba, excuse ta nema a wajen su ta shiga cikin gida ta gaisa da grandma tare da faɗa mata cewa mm ne yazo shi da abokinsa suna waje, saida grandma tagama tsokanar ta irin ta jika da kaka sannan ta ce,
"Jeki ki shigo dasu to"
"A'a, yau a waje zamuyi firar mu don kar ki takura mu, in zasu tafi sa shigo ku gaisa"
"Kedai kika sani, nima ai na sha wankan nawa na saka jambaki sai na fito ayi firar dani"
"Ai kuwa zaki sa na rufeki ta baya har sai mun gama, kun jimun tsohuwa na son yimun snatching" ta ƙare maganar tana dariya tare da ƙwalawa mai aikin Hajiya kira ta zo ta riƙa mata wasu jaijayen kujeru na roba suka fidda a can wajen rumfar motar da ake fita da Hajiya anguwa suka aje, sannan ta ce ta kawo masu ruwa da ɗan abun taɓawa ita kuma ta je ta zo dasu suka Zazzauna,
Kasancewar akujerar dake fuskantar gate ɗin shigowa Jabir ya zauna sai ya fara ganin kamar yasan gidan, dama tunda ya shigo yake ƙarewa harabar gidan kallo duk da ƴan sauye sauyen da aka yi tyana ji tamkar ya taɓa zuwan sa, isowar mai aiki wajen dake gaishe su ta katse masa tunani tare da kallon gefen da take ya amsa mata da lafiya lau itama yana ji tamkar ya taɓa ganinta a wani wajen, ɗan bubbuga gefen kansa yayi mm dake kallon sa tun ɗazu ya ce,
"Jabir lafiya?"
"Lafiya klw, gidan nan gani nake kamar na taɓa zuwan sa" sai da mm ya kalli Janan sannan ya maido kallon sa garesa, ya ce
"Anya? Yaushe kenan?"
"Bazan iya tunawa ba, amma tabbas kamar na taɓa zuwa, waccan matar ma itama kamar na santa"
"Ikon ALLAH, to kodai kasan masu gidan ne?"
"Bana ce ba gaskiya, amma ba kace gidan grandma ɗin Janan ce ba"
"Eh, haka ne"
"To taya zan sansu, duka duka yaushe muka haɗu da Janan ɗin balle nasan wasu ƴan uwan ta, ai ko kai bana tunanin kasan su in badon ta kawo ka ba"
"Gaskiya ne, to kayi tunani mana"
"A'a, bari dai nasha ruwa ko tunanin Razy baby ne ke neman sauya ni" ya ƙare zancen tare da ɗaukar gorar ruwa ya fara sha yana mai ƙoƙarin saita tunanin sa daidai, mm kuwa ɗan tsaki yayi haɗe da kallon Janan data gwalo idanuwa jin abun da Jabir ya faɗa, ya ce
"Ke kuma fa?, Ko kema tunanin zaki faɗa bacin gani kusa dake" ƴar dariya ta saki kafin ta maido kallonta garesa,
"Ka ji abinda ya Jabir ke faɗa?, Wai dama he's in Razina sister..?"
Kafin tarufe baki Jabir daya sauke gorar ruwan daya sha fiye da rabi yana ɗaure bakin, ya ce
"Au! Wai dama bai faɗa maki ba?, Ummm! Gaskiya da gyara a wannan soyayya taku, ai ni bana ɓoyewa Razina komai, ta zama ni na zama ita, ke ALLAH ko yayan ta yayi wani abun ba ruwana sai na faɗa mata, wether is good or bad, don haka karki yar da wlh" ya ƙare zancen haɗe da miƙewa yabar wajen yana dariya ganin yanda mm ya sako masa idanuwa yana kallo jin wutar da yake neman hasa masa, hannayen ta tasa ta tafa a fuskar sa haɗe da cewa,
"Juyo nan muyi magana" hannayensa ya haɗe waje ɗaya tare da cewa
"Pls karki yadda dashi, zai haɗa mu ne"
"Ba wani, ai gaskiya yafaɗa" ta ɗaure fuska tare da naɗe hannayenta a kan ƙirji ta kauda kai gefe,
"Haba Janany ta, nifa ne naki"
"Yau mun raba jaha dakai, kowa yayi ta kansa tunda har yanzu baka ɗauka mun zama ɗaya ba"
"Bazan iya jura ba, na yarda nayi laifi amma kiyi haƙuri, akwai abubuwa da dama dako bakiga na faɗa maki su a yanzu ba nan gaba kaɗan dole na faɗa maki tunda banda abokiyar fira da shawara sama dake"
"Daɗin baki ko?" Ta faɗa tare da ɗan juyowa kaɗan ta gefen ido tana kallon sa, murmushi yayi sannan ya miƙe akan kujerar da yake zaune ya je ta gefen data maida fuskarta ya yi niledown agabanta yana faɗin,
"Am so sorry Noor alb, wannan fushin naki bazan iya jura ba saboda azabtar dani zaiyi fiye da tunaninki" kallon gefe da gefen harabar gidan tayi don kar wani ya hangosa sannan ta ce
"Pls ka tashi kada a hango ka"
"Ba zan tashi ba har sai kince kin haƙura ko da duka duniyar nan zasu taru" sinne kai ƙasa tayi tana murmushi hango yanda Jabir dake can wajen baba mai gadi ke kwasar masa dariya, ta ce
"Shikenan na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 40