WANNAN LAMBAR๐๐ผ_
+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.
MUN GODE.
*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*
_Wannan garabasar tamai rabo ce๐๐ป๐๐ป sa kud'i kad'an ki debi hani'an๐๐_ ____________________
" *T* saya daga waje!" Janan taji malamin nasu dr. Ingaski ya fad'a ba tare da ya juyo ba adaidai lokacin da take qoqarin aza qafarta ta shiga cikin aji, runtse idanuwanta tayi tare da komawa baya batare data aza qafar tata ba tana jin wani irin qunci da kuma sululi acikin zuciyarta, dama tasan za'a rina, mutumen daya takura rayuwarta ba tare da tayi masa komai ba balle yanzu data aikata laifin da tasan ko bashi bane hakan zata iya faruwa, ALLAH dai ya kyauta ta furta cikin zuciyarta had'e rolling idanuwanta tana furzar da iska abaki sannan takoma a gefen qofar ta tsaya,
"Sorry sir, I got an accident on my way coming that's way"
Ba tare daya damu da juyowa ya kalleta ba balle har ya saueari uzurin da take qoqarin kawo masa yaci gaba da yiwa d'alibbai lecture d'insu hankali kwance, saida ya kammala lecture d'insa tsaf sannan ya juyo yana qare mata kallo tun daga sama har qasa, hannayenta tasa ta jawo mayafin abayar dake jikinta tarufe qirjinta daya qurawa idanuwa tana turo baki, murmushin gefen baki ya sakar mata had'e da d'aukar teaching materials d'in daya shigo dasu yana fad'in, "meet me in my office Janan" sannan ya fice fuskarsa d'aure tamkar bashi bane yagama yimata kallon qurulla don kar d'alibbai suga damarsa, murgud'a baki tayi bayan ya wuce tare da qarasawarta cikin aji hankali kwance ba tare da tadamu da binsa baya ba kamar yanda ya buqata,
D'aure fuska tayi ganin yanda 'yan uwanta d'alibbai ke binta da kallo bakunansu d'auke da alamar tambaya akan qin bin bayan Dr ingaski da tayi,
"What?" Tafad'a tana zaro idanuwa tare da ware hannuwanta gefe gefe, alokacin d'aya daga cikin qawayenta da suke zama tare Amira ta samu damar yin ajiyar zuciya had'e da cewa,
"Janan bakiji me dr. Ingaski yace ne ba?"
"Naji man, sai akaye me?" Tafad'a had'e da zaunawa,
"Sai akayi me ma kike tambaya Janan, halama kin manta ko waye shi?
"ALLAH ne shi?"
"Ko d'aya, mutum dai ne mai tsananin iko akan karatunku, don girman ALLAH kirufa mana asiri ki tashi kije kada kishafa mana kashin kaji awurinsa"
"Tab! Wlh bazani ba, me zanje nayi masa bayan 'yar lecture d'in tasa da nake kwad'ayin samu da attendance don gudun matsalarsa ya hanani?, Kawai ki qyalesa na manta ne shiyasa banje ba, dt's zit"
"Hmm! Gamu ga ALLAH" Amira tafad'a tana zabga wani uban tagumi,
Dariya janan tayi had'e da dukan bayanta, "Amira kenan, dama ke a hannun Ingaski kike ba'a hannun ALLAH ba?"
"Mts...kidena don ALLAH, wlh gaba d'aya a tsorace nake, ban cika son kina shiga 18 d'in malamin nan ba" taqare maganar tare da cire hannun janan d'in daga bayanta.
"Matsoraciya kawai" Janan tafad'a tana jawo takardun dake gaban Amira da tayi jotting.
"Naji dai koma meye zakice, tsoro ai gaskiya ne, musamman na irin wud'annan malaman da basa fatan gamawa lafiya da dalibbansu"
"Kyaji dashi nidai, dame dame yayi maku ne?, pls help me and explain it for me"
"Bazan iya ba, jeki keda ba matsoraciya ba yayi maki, bama wannan ba, meya sakaki latti Janan keda bakya son abunda zai had'aki dashi?
"Bari kawai, ai daga yau angama don bansan meye amfanin da tsoron nasa ke haifarmun ba, kinafa ji nake fad'a masa accident nayi kafin naqaraso amma yayi banza dani, shiyasa nima nayi banza dashi saboda duk abunda yafaru yau shine silar dana aikata hakan, don haka wlh munsa qafar wando d'aya dashi kenan Amira"
"Tofah! meya farune? Kuma kina ganin ke zaki iya dashi a matsayinki na d'aliba shi kuma malami?, Kinga ajiye duk wani mafarki ka kikayo da yasa kike neman maidashi gaskiya ki shafawa kanki lafiya"
Kallon gefen idanuwa Janan tayi mata had'e da harara kafin race,
"Naji, sai kuma meye?"
"Kitashi kije kiji meyake kira gareki saiki dawo nayi maki bayanin"
"ALLAH bazan je ba Amira kinji ma na fad'a maki, in zakiyimun bayanin nan kawai kiyimun in kuma bazakiyi ba naje pro (wani student a ajin) yayi mun"
"ALLAH ya baki haquri."
Amira ta fad'a tare da gyara zamanta ta shiga koyar da ita had'e da yimata bayanin abunda Dr. Ingaski ya gama yimasu, har goma da rabi tayi bata gama mata ba kasancewar lecture da suke da ita gaba ta 10-12 malamin bai zo ba, basu suka gama ba sai 11 saura mintuna goma Janan ta kalleta had'e da cewa,
"Thanks qawata, gaskiya kanki na ja, wlh dama an had'a ki aure da Ingaski kinga shikenan ku kakarku ta yanke saqa, bakida wata matsala indai akan karatune hakama 'ya'yanku"
Tattare littafan Amira tayi kamar wacce ke shirin tafiya, aikuwa Janan bata sarar ba ta d'ima mata su abaya tana fad'in,
"Aniyar mod'a dai tabi randa Janan, ALLAH ya tsareni aurn sa'ar ubana tunda ba baki akayimun ba, sa'arsa ma d'in kuma ace wai Ingaski, godforbide wlh, in sha ALLAH over my died body bazakiga hakan ba Janan, wannan ai shi ake kira mugun tare tsakaninmu tunda kike yimun irin wannan muguwar fatan"
Taqare zancen in a serious tone kamar zatayi kuka, dariya Janan ta saka mata har tana riqe ciki saboda qeta kafin can tariqo hannunta ganin tana shirin tafiyarta tabar wajen,
"Sorry qawaliya romon jab'a, ai nima da wasa nakeyi bazan so hakan tafaru ba, muje ki rakani wajen MM tunda sai 12 zamu shiga"
"Kinga nifa yau tsoron ma tafiya nakeyi dake kar wancan bawan ALLAHn ya ganemu tare, me zakiyi awajen MM keda ba abun makarantar nan kike ci ba"
"Wlh shine kad'e da zan shigo kwanar department d'in nan da kikaji ina zancen nayi accident"
Kusan fad'uwa littafan hannun Amira sukayi jin me take fad'a da sauri ta tarosu tana fad'in,
"MM d'in kika kad'e Janan? Garin Yaya?" Har idanuwanta na kawo qwalla,
"Tofah! Meye haka Amira?, daga magana sai kiwani bi ki koma kalar tausayi, kodai kema kina cikin masu son nasa"
Kauda fuska Amira tayi ta goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata agefen ido had'e da cewa,
"Tashi muje, hop dai baki jimasa ba ko?"
Mere baki Janan tayi don tana kallon abunda tayi had'e da cewa,
"Gaskiya ya d'an jimu a fuska, kuma duka kayansa sun zube"
"Kuma shine kika iya zuwa lecture Janan don rashin tausayi?, Kada fa kisa nafara zarginki da wulaqanta mutane don kin ganesa talaka" Amira da tajuyo rungume da littafanta fuska a d'aure ta fad'a tana nunata da yatsa, baki bud'e Janan ke kallonta kafin tace,
"To ke wai meye naki Amira?, mai qaya ya daure sai mai cira ke kuka?, Kinga, watch ur tongue, ni bana son kina jifata da irin wud'annan nan maganganun kuma kinfi kowa sani tunda ba haka bane"
"Ada ba, yanzu kam ai banada wannan tabbacin tunda kika aikata hakan"
Nan fa suka rikice da fad'a, ta fad'i itama ta fad'i sukayi baran baran da ita kowa ya kama gabansa, Kai tsaye Amira wajen dasu mm ke sana'a ta nufa acan nesa kad'an dasu inda zata iya hangosa a bayan wani iccen beji ta b'uya tana kallonsa, ganin babu wani serious enjury d'aya samesa sosai yasata juyawa ta jingina ajikin iccen tana sauke ajiyar zuciya tare runtse idanuwa ta furta, "Alhamdulillah" a hankali tana mai qara jin wata irin qaunarsa na zagaye lungu da saqo na zuciyarta,
Janan kuwa kai tsaye wajen motarta ta nufa ta fad'a ciki had'e da kife kanta ga jikin sitarin motar, "me yake faruwa da ita ne hakan da take faman cin karo da kalaman da tafi tsana arayuwarta yau?, meyasa abunda bata tab'a yiba yau take aikatasu, accident, fad'a da kuma kafiyar da tayiwa dr Ingaski ita sake matuqar tsoronsa, duka hakan fa ba halinta bane, meke faruwa ne da ita" ta shiga tambayar kanta cike dajin haushin fad'an da sukayi ita da qawarta Amira,
Janan kyakkyawa ce sosai dake da matsakaicin shekarun da bazasu wuce gama sha tara ba, tana da tsayi daidai gwargwado tare da kyakkyawar sigar data fidda shape din jikinta, farace sosai irin farin nan mai madara dake da 'ya fad'in fuska kad'an tare da tsawon hab'a, tanada idanuwa da dogon hanci irin mai d'an tsayi kad'an ba sosai ba, duk da bakinta ba d'an qarami bane haka bazaka kirasa da babba ba saboda yanda ALLAH ya tsaga labban da yake d'auke dasu daidai misali, tanada son wasa da tsokana amma fa duk da hakan bata son reni da kalaman aibatawa, ba kasafai take nuna gazawarta a lamurranta ba har sai abu yakai maqura saboda haaurinta, ataqaice dai zaka iya cewa tako ina tayi sai inda baka rasa ba, koshi d'in don d'an adam tara yake bai cika goma ba.
Bata tafa fad'a da wani ko wata ba koda na fatar bakine tun tasowarta sai yau saboda kauda kanta ga abubuwan da basu fiye shafarta ba, sai gashi yau bata san meyasa ba tayi da qawarta, d'an tsaki tayi tare dasa key d'in motar ta tayar tabar wajen don taji gaba d'aya lectures d'in sun fice mata akai kawai bari taje gida, kamar ance ta d'ago kanta lokacin da take tafiya kan titin makarantar a hankali zata je gida idanuwanta suka sauka akan mm dake wajen sana'arsa da har ta soma mantawa da abunda ya faru tsakaninsu d'atsu, parking tayi a gefen titi tare da fitowa cikin motar ta nufi wajensu,
Kallo d'aya mm yayi mata ya kauda Kai saboda wani irin Abu da yakeji na tsirgo masa tun daga tsakiyar qafafuwansa har zuwa qwaqwalwarsa,
"Assalamu alaikum, sannu ko Mm, Ina kwana?" Yaji ta fad'a lokacin data qaraso wajen, kallon Jabir yayi daya murtuqe fuska ya juyar da kansa gefe ganinta sannan ya maido kallonsa gunta had'e da cewa,
"Lafiya klw Janan, har kin gama lectures d'in"
"A'ah, gida dai Zan je am not in the mood, don haka bazan iya sakawa kaina komai ba, ya jikin?" Tafad'a tana kallon goshinsa d'aya d'an kumburo kuma ya fad'a kad'an yayi ja, Saida yasa hannu ya shafo gurin ganin tana kallonsa sannan yace,
"Ai naji sauqi, kawai dai d'an ciwon kaine kad'an nake ji"
"Ayya sorry, kayi haquri don ALLAH, banji dad'in faruwar hakan ba ko kad'an"
"Karki damu, in sha ALLAH Zan koma normal zuwa anjima"
Tsakin da Jabir ne yayi ya d'an kauda murmushin data qaqaro a fuskarta tare da kallon Jabir tace,
"Jabir kadena jin haushi na, ita fa qaddara tana faruwane akan kowa kuma a sanadiyar kowa, saboda haka kayi haquri kaima don ALLAH bani ba"
Ganin bai amsata ba yasa mm yad'an taka qafarsa da sauri ya d'ago kai yace
"Shikenan"
"Nagode Jabir sosai, mm ko zakazo muje clinic d'in school tunda nafito da katina na clinic saina karb'a maka magani tunda kace kanka na ciwo ko kuwa Jabir?"
"A'a kibarshi angode" Jabir yafad'a a daqile had'e da miqawa wata student dabino data siya, d'an gyara tsayuwarta tayi tare da juyawa tana kallon yanda d'alibbai 'yan uwan nata ke kaida kawo acikin makarantar kafin ta maido kallonta garesa,
"Jabir kenan! Har yanzu dai baka haqura da abunda nayiwa abokinka ba?, Fad'amun! me kake so nayi da zaisa kaima ka haqura, bana son kana yimun kallon tunanin da qwaqwalwarka keyi akaina"
Kallon mm yayi daya saki baki galala yana kallonta duk wani motsi nata burgesa yakeyi musamman yanda gefen chicks d'inta ke motsawa idan tana magana, yanda yayi masa d'azu ya taka masa qafa shima yayi masa had'e da cewa,
"Kuje mana idan kana buqatar hakan tunda kace kanka na ciwo, amma gaskiya yakamata kiriqa kulawa kema ko ba'a cikin makarantar nan ba, Rai fa d'aya ne daga shi ba wani, idan yafita kuma shikenan" yakai qarshen zancen yana kallonta, murmushi ta d'an saki had'e da cewa,
"To shikenan angama, kuma in sha ALLAH zan kula, mm zamuje clinic d'in ne ko kuwa?"
Sai alokacin hankalinsa ya dawo gangar jikinsa da sauri yasa yatsa ya sosa gefen idonsa cike da kunya don tabbas ko shakka babu ta lura da irin kallon da yakeyi mata, ita kuwa bata kawo komai aranta ba na rashin maganar da yakeyi sosai saboda ta saba jin irin miskilancin da yake dashi a bakin student, wataqil hakan ALLAH yayisa shiyasa ya samu aboki mai shegen surutu da tsiwa atare dashi.
Ganin yayi shiru baice komai ba ya sata juyawa ta wuce gaba, kallon Jabir yayi suka had'a idanuwa yayi murmushi shi kuma ya mere masa baki had'e da cewa,
"ALLAH dai yafidda a'i ga rogo....wannan rawar qafar taka daqyar in zata tabari ka iya tafiyar da plan d'inka yanda ya kamata"
Juyowar da Janan tayi ganin har tana qoqarin tsallaka titin bai qaroso ba yasa mm rufe bakinsa ba tare daya tankasa ba yabi bayanta,
Kusan tare suka tsallaka titin da ita inda motarta take ta nuna masa can gefen motar da key d'in dake hannunta alamun ya zagaya ya shiga itama tana qoqarin bud'e gaban tashiga, murd'a marfin ya riqayi da qarfi kamar mai shirin kokuwa yana fizgarsa, ala tilas bai iya ba, dariya tayi had'e da miqa hannu bayan ta shiga ta bud'e masa gefen nasa ya shigo,
"Mm stop pretending, a yanda kake d'in nan babu ta yanda za'ace baka iya bud'e marfin motar ba, saidai ko kawai kace qilan baka tab'a shiga irinta ba" taqare zancen tare da murd'a sitarin motar tana dariya tabar wajen, gabansa ne ya fad'i kodai Janan ta sanshi tasan plan d'in da sukeyi? Amma duk da hakan sai ya sake matsewa tare dasa hannayensa agefen kafad'unsa ya zagaye jiki dasu yana fad'in,
"Kai, ya akayi naji sanyi? Gaskiya yayi yawa zan iyayin zazzab'i, ajeni nafita sai muhad'u acan, juyowa tayi ta kallesa sannan tasa hannu ta rage qarfin sanyin a.c daya mamaye motar don tasan a kanshi yake maganar ba tare da tasake cewa komai ba har suka isa bakin clinic d'in, yanayin parking ya fara qoqarin tura marfin motar da qarfin tuwo wai zai fita, dariya tayi ta sake cire lock d'in da tasawa motar gaba d'aya sannan tamiqa hannu ta sake bud'e masa,
Har zai fita tace, "mm, kai kuwa d'an wane gari ne don ALLAH"
"Ni?, Anan nake charanchi qauyen katsina"
"Anya mm, Aiko 'yan caranci baza suce basu iya bud'e mota ba, saidai ko kakumi ko?" ta qare zancen cike da zolaya tana dariya, dariyar yayi shima sannan yafita itama tafito ta kulle motar suka nufi cikin clininc d'in tare,
Suna kaiwa bakin qofar ya ja ya tsaya ta juyo had'e da cewa,
"Shigo man ka zauna anan reception bari nazo" tawuce kai tsaye office d'in consultant dr da aka tanada, ba'a jima ba tafito riqe da ledar magani har lokacin yana tsaye bakin qofa ya nad'e hannayensa a saman qirjinsa, yana ganinta yayi saurin sakin hannayen ta miqo masa leda tana fad'in,
"Au! Wai dama baka nemi wajen zaman ba tsaye kayi abinka?"
"Eh naga mutane sunyi yawa ne shiyasa"
"Kai kuma tsoronsu kakeyi ko?" Tafad'a cikin zolaya tare da wucewa abinta tamkar ba ita tayi maganar ba, bayanta yabi yana kallonta har ta tada motar ta juya tana qoqarin tafiya yayi kamar bai gani ba seda tayi masa horn sannan ya tako yazo ta gefen da zai shiga yayi tsaye, ganin yaqi shigowa yasa ta sauke glass d'in gefen nasa had'e da duqo kanta yanda zata ganshi tace,
"Muje ko mm?"
'Dan duqowar yayi shima tare da cewa
"A'a kitafi abunki ni sai naqarasa qasa"
"Haba! Ai ba'ayi haka ba, indai baso kakeyi Jabir ya tatamun rashin mutunci ba, ai hannun ansa hannun mayarwa" taqare zancen tana bud'e masa marfin motar kamar d'azu, ba yanda ya iya dole ya bud'e ya shigo yana murmushi, tabbas Janan ta dace da rayuwarsa saboda yanayin halayyarta, akwaita da son barkwanci idan ta tashi duk da dai alamu sun nuna kamar tana yine saboda tsarguwar kanta da tayi akan abunda tayi masa, koma dai meye shi tayi masa haka kuma sai yaga abunda ya turewa buzu nad'i akanta.
Da wannan nan tunanin da yakeyi suka qaraso wajen sana'arsa ta sake rakasa har wajen tana fad'in,
"To malan Jabir, ga amininka nan na dawo maka dashi sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, ALLAH yaqara sauqi"
"Amin ya rabbi, sai anjima mungode" Jabir ya bata amsa cikin d'an sakin fuska kad'an don shi har yanzu bata wani burgesa ba balle har yafidda ita sahun daya sakata, don ba'a yabon d'an kuturu sai ya shekara arba'in da yatsunsa.
"Mm, sai gobe ALLAH yaqara sauqi"
"Amin Janan, ngd sosai" yafad'a cikin sanyin murya yana kallonta, har taqarasa gaban motar ta bud'e ta shiga ta tayar idanuwansa na akanta saida yaji Jabir ya kece da dariya tukuna ya maido kallonsa akansa,
"Alqur'an Mm yarinyar nan na nema ta maida mana dakai wani tsohon maye, wai kaga yanda ka tsareta da idanuwa?, Tab kuma yasin ba qaramin kyau zakayi ba da zama mijin hajia ba"
"Mtsss..Kai fa d'an air ne Jabir, waya fad'a maka cewa har muyi aure ina nan a matsayin MAIDABINO, wuce nan guy" yaqare zancen yana cilla masa ledar maganin.
A b'angaren Janan kuwa tana kaiwa bakin gate d'in fita dr Ingaski na wajen zai fita, har zai taka wutar motarsa ya hangota ta madubi yayi saurin taka burki, wani irin ribas taja don kad'an ya rage ya bugi motarta da sauri itama ta taka nata birkin ta tsaya, murmushi yayi had'e da ficewa cike da takaici taja tata motar itama ta fice, tana fitowa taga har yayi parking d'in motarsa yana jiran fitowarta, tana kawowa saiti dashi ya maza ya fito tare da shan gabanta, wani wawan burki taja had'e da d'auke kanta gefe ganin yana tunkarota,
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" tafad'a cikin zuciyarta har ya qaraso wajen had'e da qwanqwasa mata glass d'in motar da take gefe, yi tayi kamar zata qyalesa can kuma ko me tatuna ta d'aure fuska tare da sauke glass d'in motar a hankali ba tare data kalli inda yake ba.
*Coment
*Like
*Share pls
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU ๐๐ญ*
[8/17, 7:39 PM] ฦณAR FARA KYAKKYAWA๐: _Page 5_
*TUKUICIN SO*๐
*NA*
*BILLY S FARI*๐
*HASKE WRITTER'S ASS..๐ก*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1228556252?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=mYrSfXopi0y3oPiu7GUqySjbsXBMVJX43kBOg04%2B5L0d0SbkVf0XnIXAWORHibq7vq5BIwk0Z%2FpKeoPXn9rPR8dsgzC65JLBGFgYtXScDzKTCbinX%2BGfHEnzWXNXigiJ_
*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*๐ช
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO ๐ฃ๏ธ
SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
1- *KAUNA CE*
NA UMM ASGHAR
2- *RUKUQI*
NA FEEDHOM
3- *WANI SO*
NA ZEE YABOUR
4- *SO DA ALAKA*
NA UMMI AISHA
5- *MUGUN GANI*
NA SADIYA NASIR DAN
6- *ABDUL_HAMEED*
NA NANA DISO
7- *MUKULLIN ZUCIYA*
NA MAMAN KHADY
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL
KAI KA KAI....!
TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU...
1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA๐
*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*
2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA
*DAGA AYUSHER MUH'D*
3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI
*DAGA HAJJA CE ๐*
MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN
_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT๐๐ผ_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS
*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR๐๐ผ*
+447894142004
IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR๐๐ผ*
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki
_GA MUTANENMU NA QASAR NIGER๐ณ๐ช ZAKU IYA TURA KUDINKU 550F TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR๐๐ผ_
+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.
MUN GODE.
*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*
_Wannan garabasar tamai rabo ce๐๐ป๐๐ป sa kud'i kad'an ki debi hani'an๐๐_
*B* atare daya damu da yanda ta d'auke masa kai ba yayi gyaran murya had'e da cewa, "Janan, wai meyasa bakyason kulani ne aduk lokacin dana buqaci hakan daga gareki, kin kuwa san yanda kike azabtar da zuciyata?, Kin..."
Tayi saurin dakatar dashi ta hanyar juyowa had'e da rolling d'in idanuwanta tana fad'in, "oh my God!, malan karka manta nifa d'alibarka ce, all these words bai kamata suna fitowa daga bakinka ba, zasu iya sawa nadena ganin girmanka kuma..."
"Ya isa haka Janan!, Sai akace maki shi malami baya da zuciya? Bayada hurumin yaso duk abunda zuciyarsa ke so ki akan waye?" Ya katseta shima yana yimata wani irin kallon shaqiyanci, sake kauda kanta tayi had'e da cewa,
"Ok, I understand malan kayi haquri am not interested of you, karatu nazoyi ba soyayya ba don haka let me be plsss malan" taqare maganar tare da had'e hannayenta waje d'aya tana baging d'insa, d'an sosa hanacinsa yayi had'e da miqewa daga duqowar da yayi ta jikin tagar motar tata tare da kallonta yace,
"Ok, as you wish, saidai ina so kisani kamar yanda karatu ba zai tab'a yuyu ba har seda cikakkiyar kulawar malami haka shima malami bazai tab'a samun natsuwa ba saida cikakkiyar kulawar abincin zuciyarsa, kece abincin zuciyata Janan, haqqin ciyar da ita yana kanki, idan kin so ki kula da ita nima na kula da sha'anin karatunki idan kuma kink'i kinsan me zai iya biyowa baya" Yana gama fad'ar hakan yasa glass d'in idanuwansa da tunda ya hangota ya cire had'e da juyawa yabar wajen.
Kota kan maganganunsa bata tsaya biba ta ja motarta tabar wajen aguje, batasan meyasa malamin nan ke bibiyar rayuwarta ba duk daba ita kad'aice d'aliba ba acikin makarantar, ba kuma ita kad'aice keda kyauba balle yabi ya uzzurata, da ire_iren wannan tunanin ta isa gida, tun kafin taqaraso makeken gate d'in dake jikin gidan nasu daya kasance mai sensors ne yayi saurin zugewa gefe ta shige mai gadi ya d'aga hannu had'e da russunawa yana gaisheta cike da girmamawa, horn kad'ai tayi masa alamun amsawa tare da zagaye katafaren roundabout d'in dake tsakiyar harabar gidan sannan ta nufi inda aka ajiye don motoci tayi parking motarta tafito riqe da makullin motar da jikkarta a hannu, daidai lokacin mahaifinta shima yafito bodyguard d'insa na biye dashi sun take masa baya zai fita, tsaye tayi tana kallonsa ganin waya yakeyi har saida taga ya qarasa yana qoqarin shiga motar da d'aya daga cikin guard d'in ya bud'e masa tayi saurin zuwa wajen.
"Abba.."
Da sauri ya juyo fuskarsa d'aure ba walwala had'e da cewa,
"What Janan? Har kin dawo daga school d'inne?"
"Eh Abba, barka da fitowa antashi lafiya?"
"Lafiya Lau"
Har zatayi magana sai kuma tayi shiru don akwai maganar da take so tayi dashi ga kuma bodyguard awajen, kallo d'aya yayiwa guards d'in gaba d'aya suka bar wajen don sun fahimci me yake nufi kamar yanda shima ya fahimci dalilin daya hana 'yar tasa maganar da take son yi.
"Ina saurarenki Janan akwai wani abune?"
"Eh Abba, Ina so ne muje wajen grandma idan ka amince"
"Kinyi marmarin tacimun mutunci kenan!"
"Noo.. Abba kawai dai naga mun kwana biyu ne bamu je ba, and i know tana buqatar ganinmu"
"Tana buqatar ganinki dai, ai kinsa ba ragawa 'yar uwarki takeyi ba duk kuka je, don haka you can go but mind you! Duk NIHAL ta dawo rai ab'ace kema saina sab'a maki"
Yana rufe baki wata kyakkyawar budurwa tafito da gudu gudu daga cikin gidan saye da riga da wando irin na zuwa support kanta ko d'an kwali babu hannunta riqe da agogo tana fad'in,
"Abba ga agogonka ka manta dashi a falo baka saka ba" taqare zancen had'e da qarasowa idanuwanta na akan Janan da tasa key d'in mota tana sosa gefen wuyanta dashi,
Miqa mata hannu Abban nasu yayi cikin sakin fuska yana murmushi ta saka masa agogon had'e da dafa kanta yana cewa,
"Thank you my dota, God blesses you"
"Amin Abba God blesses us dai me and my sister, Janan fa? Ko ka manta da itane?"
"Am sorry dear, tace zakuje wajen grandma d'inku anjima, kina son zuwa?"
"Yeah! Upcouse Abba tunda Janan na buqatar hakan ko lil sis"
Kad'a mata kai kawai Janan ta iya tana murmushi, aranta kuwa mamaki takeyi yanda mahaifin nasu ke nuna fifiko tsakaninta da 'yar uwarta Nihal duk da kasancewarsu abu d'aya, don uwa d'aya uba d'aya suka haifesu, gaba d'ayansu duka yana sonsu sosai baya qaunar abunda zai samesu, amma farincikinsa da walwalarsa na bayyana ne kad'ai aduk lokacin da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 40