Share this page
ni dai kar azo a isheni da salo aje a haye mun gado kuma ace za'a tashi abar mani shi haka bayan an sauke masa gajiya akai tunda ba uban mutum ke gyarawa ba, koda yake na tuna ba kece ke da wannan baƙin halin ba waccan mai baƙin faɗin ran tsiyar ce" "Ehm, ALLAH ya baki haƙuri ni toilet ma zan shiga ba wajen gadon ki nayi ba, kuma mun gode da zagi ni da Addata" "Tunda kun gode ku kawo tukuici mana, indai Nihal ce baki yi Addar ƙwarai ba tunda take da baƙin hali, ALLAH dai ya shirya mana ita" "Amin Hajiya, bari nafito" ta faɗa tare da shigewa toilet ta rago cikin ta sannan ta fito, Zaune ta isko Hajiya ta rabka uban tagumi tamkar ba ita ce yanzu ta gama yiwa Nihal tsiya ba, da alama ta faɗa wani tunanin ne, "Hajiya, Hajiya, Hajiya..." Janan ta faɗa har sau uku bata amsa ba har sai ga na huɗun tayi saurin fitowa duniyar tunanin data faɗa haɗe da zaro idanuwa tana kallon ta, "Haba Hajiya, wai har sai yaushe ne zaki dena irin wannan dogon tunani ka?, tun ina ƙarama nake lura da irin wannan ɗabi'ar da kike yi har na girma, kuma tsab kin san irin illar da hakan ke iya jawowa lafiyar ki, amma ke kasa denawa, sai dai kina ganin mutum ya fara ɗaukar ɗabi'ar zaki fara masifa dashi, don ALLAH kema kidena kada wani abu yazo ya sameki" "Hmmm Janan kenan, ai in kika ga na dena wannan tunanin kuma sai in mutuwa nayi, abubuwa da dama ke cunkushe azuciyar nan tawa da ban san iya adadin su ba, ALLAH dai ya kyauta kuma yayi mana magani" "Amin Hajiya, amma duk da haka haƙuri za kiyi ki fiddasu aranki ko don sama kanki lafiya, saboda wasu abubuwan sai an fitar dasu ake samun sassauci a zuciya, wannan shawara ce dako likitoci sukan bada ita don samawa zuciya lafiya da kuma kwanciyar hankali da waraka, don haka don ALLAH kirage ko kuma muci ta tsane ba tare da kin ankara ba" takai zancen cike da zolaya har tana tuntsirewa da dariya, "Ke dai kika sani, tashi jeki ga mai gadi can naji yana sallama ko aikosa akayi..." Kafin tarufe baki mai yi mata aiki ta shigo falon tana faɗin, "Sannu Hajiya, wai wani mutum ne ke sallama da 'yar gidan Alhaji inji baba mai gadi" "To jeki kice masa ya faɗa masa gata nan tafe" Ɗan turo baki Janan tayi duk da tasan ko waye haɗe da cewa, "Kai Hajiya, shine zaki ce ace gani nan zuwa bacin baki san kowaye ba" "Ikon ALLAH, idan ke kika je ɗin baza ki ganowa idanun naki ko waye ba?, yau ni naga rashin arziƙi, ko kema halin yayar taki kika ɗauko?" "To Hajiya baki fasan ko waye ba" "Ikon ALLAH, zaki tashi ki tafi ɗin ne ko kuwa?" Da ƴar shagwaɓa ta miƙe ta fice daga falon tana ɗan bubbuga ƙafafuwa, mere baki Hajia tayi don ta gano ta kar tare da ɗan gincirawa akan kujera tana mai fatar ALLAH ya zaɓi masu mazaje na gari.... #COMMENT PLS *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 31_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ Tsaye ta hango mm a bakin gate ɗin ya yimata kyau tamkar bashi ba saboda kayan daya ɗan sauya ba irin wuɗan da ta saba ganin sa dasu ba, murmushi ta saki haɗe da takawa a hankali ta nufi wajensa fuskarta na ɗauke da tsantsar farincikin dake cikin zuciyar ta na ganin sa da tayi, "Barka da isowa ya kai ma'abocin hasken fuska da annurin zuciya, a gaskiya ba ƙaramin ƙoƙari kayi ba wajen gane gidan nan, sannu da zuwa yallaɓai na" "Yawwa ranki shi daɗe, amma dai bakiyi lecture ɗin yau ba ko?" "Eh banyi ba" ta faɗa tana haɗiye yatsun hannayenta cikin junan su haɗe da turo masa idanuwa da baki, dariya ta basa don haka sai ya ce, "Sannu baby doll, to meya sa?" "Dogon turanci ne, don haka murnar zancen, ya kake ka iso lafiya?" "Lafiya klw, kefa?" "Nima haka" Shiru ne ya biyo na bayan ɗan wani lokaci kafin tace "to shigo daga ciki ko?" "A'a, je dai kine mo mani izinin yin hakan a wajen grandma" "Laa..ai ba wata matsala kawai kazo mu shiga daga ciki, amma gaskiya nifa ina kishin ta ganemun kai" "Kishi kuma? Na meye? keda nake da tabbacin in sha ALLAH ubangiji bazai halitto wata da zata iya shiga rayuwar hubbin ki ba balle har kiyi kishi da ita" "Ehm...to ba ga Hajiya nan ba, wato don zaka zo wajen ta shine hadda saka kaya masu kyau haka, amma ni baka sakamun na gani" "To ko na koma gida na cire ne?" ya faɗa idanuwansa akanta, ba kunya ta ɗaga masa kai alamun eh tana 'yar dariya, dariyar shima yayi tare da nuna ta da yatsa ya ce, "Ke ko?" Sannan ya haɗiye hannuwansa waje ɗaya yaci gaba da cewa, "Adai yimun afuwa yallaɓiyata, ina komawa yanzu mai kayan zai karɓe abunsa kuma kinga kamun ƙafar auren ki nazo nema dole na naɗan zo da haibata ko grandma zata yaba itama" "To ai shikenan bara na faɗo mata ɗin" "Yawwa nurul alb, ko kefa" Batafi mintuna biyu ba da tafiya ta dawo suka shiga tare gabansa sai faman faɗuwa yakeyi akan yanda hajia zata karɓesa, kansa ƙasa ya ƙarasa shiga daga ciki Hajiya na zaune kan kujera ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta cike da girmama wa, cikin sakin fuska ta amsa masa tana ƙare masa kallo haɗe da nuna masa kujera ta ce ya zauna, kasa zama yayi sai dai yayi zaman sa a ƙasan yana sauraren me zata ce tare da ƙare mata kallon itama tana ƙasan idanuwa, kyakkyawar dattijuwa ce mai kaurin jiki, ba tada wani haske sosai don zai iya cewa kusan kalar fatar ta ce daga Janan har Jabir suka ɗauko, amma gaba ɗayan su babu wanda ya ɗauko tsantsar kyawon ta daidai, dama dama ma mahaifin Janan, yana da yanayi da ita sosai don shima kyakkyawa ne sosai, Muryar ta ya jiyo tana faɗin, "Ɗan saurayi ya sunan ka ne?" "Sunana Muhriz Hajiya" ya faɗa yana sake duƙar da kai ƙasa, "Murhuz" murmushi yayi sannan ya sake cewa "A'a Hajiya, Muhriz" Janan ce ta turo baki tana faɗin, "Kai Hajiya dena ɓata masa suna ba haka yake ba, Muhammad Muhriz zaki ce, shine ainahin sunan sa" "Ke dallah ja can, wani murhiz can bayan ga sunan shi nan mai ma'ana Muhammadu zaku wani canza don kuna ƴaƴan zamani" dariya mm yayi don har ga ALLAH yana kallon matar ya ji ta kwanta masa arai, "Ke ni tashi kije ki kawo masa ruwa kin zauna sai kace wata baƙauya, yau ko ƴan matan ƙauye sun san tarbar saurayi da ruwa balle kuma na birni" turo baki Janan tayi haɗe da miƙewa tana faɗin "Ai dai suma ƴan matan ƙauye mutane ne, sannan su samarin su ne ni kuma shi ɗin mijina ne, don shi kaɗai nake so na aura ko mm?" Sinne kai yayi ƙasa Hajia ta shiga yin sallallami tana tafi da hannuwa cike da mamakin wai yau Janan ce dako magana bata dameta ba ke faɗar haka ko kunyar ta ba ta ji, "Eh lallai Muhammad kaciri tuta kuma da gaske takeyi tana yi dakai" ta ƙare maganar tana kallon sa, murmushi yayi haɗe da ɗago kai yana kallon Hajiya ya ce, "Wannan dalilin ne yasa nace bari nazo na gaishe ki na kuma sake kamun ƙafa awajen ki don har ga ALLAH nima da gaske nake son Janan kuma da zuciya ɗaya ba don wani abuba, duk da dai banda irin tarin arziƙin da zan iya mallakarta har na kula maku da ita yanda kuka saba, amma na tabbata zan yi iya ƙarfi a wajen kula da ita sosai" "Muhammadu kenan, ai shi arziƙi na ALLAH ne,, sannan matar mutum kabarin sa, nasan halin Janan tun tana ƙaramar yarinya tana da wani irin hali na mahaifinta data ɗebo na kafuwa, tunda har ta amsa cewa da bakin ta tana son ka, to fa ko ba kada komai zata iya zama dakai, badon tana jika taba, tana da matuƙar hankali da sanin ya kamata sosai, matsalar ɗaya ce dai, shine mahaifinta, mutumne dake da tsattsauran ra'ayi, a wasu lokutan ko ni ban isa na saukar dashi ba idan ya hau kan bakar sa, amma wannan karon zan ƙoƙarta a matsayina na mahaifiyar sa tunda har kuna son junan ku naga ya aura maka ita, bazan bari son kansa ba yasa ya cutar da ƴar marainiyar yarinyar nan ta hanyar hana mata abunda zuciyar ta ke so, arziƙi kuma ba hauka bane balle na ci gaba da zura masa idanuwa yana aikata kuskuren dani kaina nasan ba akan daidai yake yi ba, kuma matuƙar ya ce zai aikata wani abunda dabai kamata ba a wannan karon zan jajir ce wajen nuna masa kuskurensa tunda nice na haifesa kuma...." sai kuma ta kasa ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka, irin kukan da kana ji zaka fahimci akwai wani ɓoyayyen al'amari a zuciyar ta dake damun ta, bai samu cewa komai ba har Janan ta shigo, mai aiki na biye da ita ɗauke da tray da abinci da abun sha akai, da sauri Janan ta ƙara sa tare da dafa kafaɗar ta tana faɗin, "Hajiya lafiya kike kuka? Me ya faru ne ko ya faɗa maki wani abun ne?, Hajia don ALLAH ki faɗamun ko bakya son sa ne na haƙura" Ganin taƙi magana sai faman sharɓar majina take yi ya sa Janan juyowa tana kallon mm haɗe da cewa "Ya Muhriz don ALLAH kayi haƙuri ka tashi ka tafi, wataƙil Hajiya ba tada buƙatar ka shi yasa ta zubar da ƙwalla, nasan cewa zan matuƙar shan wahala idan nace zan rabu dakai, amma saboda farincikin ta zan iya haƙura" "A'a Janan, kada kice zaki haƙora da farincikinki don kin ga na shiga cikin wannan yana yin, kuma kuka na baya da alaƙa da zaɓinki k kaɗan, indai zaki samu farinciki dashi ni ina goyon bayan ɗari bisa ɗari, a zahiran ce kinyi zaɓi mai kyau kuma na yaba dashi, fatana kawai yayi mun alƙawarin zai riƙe ki amana ko don maraicin ki, idan yayi mun hakan shikenan ya gama mani komai, kuma zai sa naji sassaucin raɗaɗin da nake ji ta wani ɓangare na zuciyata" daɗi ne ya rufe Janan da har taso tayi mata tambayar wane irin raɗaɗi take ji azuciyar ta ɗaya sakata kuma, amma da yake burin ta ya gama cika sai ta jefa mata tambaya akan Abban na ta, ta ce "Hajiya Abba fa, wlh zai iya hanani aurensa" kallon ta hajia tayi kafin tace, "Ai ni na haifi ɗana bashi ya haifeni ba, don haka kibar ni dashi, kai kuma Muhammadu idan kasami da ma jibi ka dawo ina son ganin ka" tana gama faɗar haka ta miƙe Janan ta riƙata ta wuce bedroom ɗin ta ta basu waje, mm na faɗin, "Nagode Hajiya ALLAH ya ƙara lafiya" ta amsa da "Amin" haɗe da ƙara sa shigewar ta, Kusa dashi Janan ta dawo ta zauna tare da tsiyayo lemu a cup ta miƙa masa tana faɗin "to ya kaga dabarar tawa?" Sai daya amshi cup ɗin ya ɗan kurɓa yana kallon ta sannan ya ce, "Ai kin faɗo ƙasa warwas malama, ke da kika ce idan grandma bata so zaki iya haƙura dani" "Laaa..wlh haka nace ba, cewa fa nayi zan haƙura" "To zaki haƙura dame in ba ni ba" ɗan kwaɓe fuska tayi cike da shagwaɓa sannan ta ce, "Kai hubby, zan haƙura da rayuwa fa nake nufi" dariya ya yi tare dakai cup ɗin a bakin sa ya ƙara kurɓar lemun yana cewa "Kin kuru, da na ce ni nama ga matar aure don Hajiya tayi mun ɗari bisa ɗari.." bai ƙarasa rufe baki ba ta janyo throw pillow dake saman kujera ta shiga maka masa akai tana faɗin, "Cheater, cheater..." Dariya yake yi sosai ya samu daƙyar ya riƙe pillow ɗin yana faɗin, "Am sorry, am not a cheater ranki shi daɗe, kin manta da alƙawarina agareki ne? Ai in ina ganin ki ba abunda zanyi da waccan 'yar tsohuwar, yi haƙuri nurul alb, na tuba bazan ƙara ba kin ji ko?" ya samu da wayo ya amshe pillown dake hannunta y maidasa inda yake yana kallon yanda ta turo leɓen ta na ƙasa cike da shagwaɓa kamar za tayi kuka, "Ayya sorry matata ni kaɗai, mm ne ko?" ta ɗaga masa kai tamkar wata samna, ya yi ɗan murmushi haɗe dasa yatsa ya zun gure goshin sa yana cewa, "Baka jin magana kada ka ƙara ɓatawa gimbiya rai kaji ko?" ya wani haɗe fuska tamkar yana faɗa da wani, ba tare data ankare ba ta saki wata irin dariya haɗe da cewa, "You always drive me like crazy hubbynah, thank you so much, ina matuƙar son ka da ƙaunar ka da yawa" ta ƙare maganar tare da langaɓar da kanta gefe tana aika masa da wani irin kallo mai cike da tarin ma'anoni daban daban, ƙasa yayi da muryar sa shima haɗe da saita bakinsa a daidai kunnen ta ya ce, "Nima ina sonki, ina ƙaunar ki fiye da ƙarfin tunanin ki da nawa kai harma dana grandma gaba ɗaya" hannuwanta tasa a fuska tana dariya tare da cewa, "har da na kaka?" "Sosai kuwa" "Tab..lallai wannan so naka da yawa yake, tunanin kaka fa ba nan kusa ba kuma ba kaɗan ba" "To anfaɗa maki shi son da nake yi maki ɗin kaɗan ne, ai badon ni ɗin mai ƙarfin zuciya bane a dare ɗaya zai iya yin wuff da rayuwata" "Ahh..bana son yayi haka gaskiya, ya bar ni nayi wuff dakai da kaina" suka sa dariya tare, abincin ta buɗe ta zuba masa da kanta ta tura masa agabansa haɗe da cewa "bisimillah" tamkar wanda ya saba da gidan haka ya saki jiki sosai yaci abincin sa kuma suka sha soyayyar su sannan yayi sallama da Hajiya ya tafi bayan ya ajiye mata dubu biyu ya ce taci goro tayi ta sa masa albarka tana mai jin daɗin kyautar duk dako tafi ƙarfin ta, Sai da Janan ta rakosa har titi ya hau abun hawa ya tafi sannan ta dawo tana cewa Hajiya, "Hajiya ni na wuce" "Au tun yanzu? Ai na zata wuni zakiyi mun" "A'a makaranta zan koma, mota ta na can na baro" "Ke dai kika sani da kicihin ki, a dama kar nake kallonki, kuma ina sane da salon ki, wato kun haɗa baki zai zo shine kika zo zaki yimun boko ko?" "Kai Hajiya, to ina laifi na ma tunda gaisuwa muka zo kawo maki" "To kun kyauta ai, ALLAH yayi maku albarka" "Amin Hajiya, ni na tafi" "ALLAH ya kiyaye, anjima ai zan shigo wajen naku da duba waccan uwar tsiwar" "Ehm..ka dai ji Hajiya, a haka ɗin dai kike son ta tunda har zaki je dubata" jefota da carbin dake hannunta tayi haɗe da cewa "Ke dallah ni tafi kin zo kin isheni da surutu tun ɗazu, Muhammadu kam zai sha fama da wannan surutu naki" Da sauri Janan ta fice tana dariya abin ta, tana son grandma sosai saboda halinta, yanzu ne zaku yi daɗi da ita kuma yanzu ne zaku koma faɗa, wanda hakan ne yasa Nihal ta kasa fahimtar ta, har ya zamana basa shan inuwa ɗaya, Ta gate ɗin data fito ta sake komawa cikin makarantar, tsaitsaye ta isko su wajen motar wasu kuma suna faman zagayen classes ɗin nasu haɗe da leƙa windows suna neman ta, dariya ta kwashe da ita sannan ta ɗaure fuska tayi kamar daga Masallaci ta fito ta nufi wajen motar ta fuskar ta ɗaure ba alamun wasa aciki, tana sake danne dariyar dake ƙoƙarin zo mata ganin yanda suka yo kan motar gaba ɗayan su, su wajen tara, ba tare data kula ta kansu ba ta buɗe motar don basu da lecture ɗin marece ta shige, agogon hannun ta ta duba ƙarfe kusan biyu har da rabi kawai ta tada motar ta ta ja tabar wajen, aguje suka riƙa bin motar har takai bakin gate ta saukar da glass ɗin motar haɗe da yiwa mai gadin godiya sannan ya buɗe mata gate ta wuce, koda ta fita har sun shige motocin su ita kaɗai suke jira, tana wucewa suma suka bi bayan ta aguje kamar yanda suka ga itama taba motar wuta. #COMMENT PLS *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 32_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ Cike da shaƙiyanci Janan ta riƙa shiga lungu da saƙo da motar tana gudu don kawai ta wahal da su, gaba ɗaya ta kasa tsayawa tayi tuƙin hankali ganin yanda suke biye da ita gashi kan titin ma sauka tayi don ta rena masu da wayau tana yi tana dariya abunta har suka isa gida, Tana gama daidaita parking ɗin motar ta Asgar dake can zaune cikin tashi motar ya fito ya nufo inda take murtuƙe da fuska ya tsaya a gefen da zata fito yana jiran fitowarta, Janan da gaba ɗaya bata lura da zuwan sa wajen ba ta fito tana yiwa su Jazz dariya, tana ganin Asgar tayi saurin ɗaure fuska tamkar ba itace ke dariyar ba, ko kallon sa bata yi ba ta raɓa ta gefensa zata wuce yayi saurin shan gaban ta, sinne kai tayi ba tare data bari sun haɗa idanuwa ba haɗe da cewa, "Malam bani wuri na wuce!" Cikin ɓacin rai dajin tamkar ya rufeta da duka ya ce, "Waya baki izinin fita ba tare da kin jira na zo ba?, Ko shi Abban bai faɗa maki cewa yanzu a ƙarƙashi na kike ba?, Haƙƙin fitar ki gaba ɗaya ya komo a kaina, kama daga makaranta har zuwa inda duk kike son zuwa nine zan riƙa kaiki." A hankali ta ɗago kai tana watsa masa wani irin mugun kallo tun daga sama har ƙasa sannan ta saki tsaki tare da sake ra ɓawa ta gefensa zata wuce kawai taji ya riƙon hannun ta, bata tsaya yin wata wata ba tana juyowa ta ɗaukesa mari tare da nuna sa da yatsa cikin ɓacin rai tana zaro masa idanuwa ta ce, "Wannan ya zamo na ƙarshe a wajen ka! Idan ba haka ba ka dinga shan marukka kenan a wajena, kuma ina tabbatar maka daga ƙarshe wuta ce zata cinye wannan tsinannen hannun naka daya saba da taɓa jikin mata yana neman lalata su sai kace bunsuru" ta ƙare zancen tana nuna hannun nasa da yatsa, kallon ta yakeyi cike mamaki kafin yace, "Janan ni kika mara?" "Ko kana tantama ne ka sake maimata abinda kayi ni kuma na shere maka ita?" "To sai me idan ma kinyi hakan?, Na lura da ƙarfi kike son musguna wa rayuwata don kawai na rabu dake, kuma wlh tallahi kinji na faɗa maki komai zakiyi mun bazan rabu dake ba har sai na mallaki wannan kyakkyawar surar taki" ya ƙare zancen yana nuna ta da hannu tun daga sama har ƙasa tare da gyara tsayuwar sa yana murmushi sannan ya ci gaba da cewa, "Don haka ki ci gaba da duk abunda kika iya lokacin ki ne 'yan mata" ya yi salutin nata a daidai gefen idonsa ya jefa mata sannan yabar wajen yana faɗin "ki kula mani da kanki, anjima zan dawo" Takaici ne ya rufe Janan hannayen ta na naɗe akan ƙirji ta bisa da kallo tana hurar hanta tare da cije baki tana girgiza kai sannan ta nuna sa da yatsa ta ce, "Zamu haɗu ne dakai, ko ni ko kai shege ka fasa" sannan ta wuce cikin gida, Da ɗan gudu gudu take hawan upstairs ɗin har ta ƙarasa ta nufi wajen ɗakin ta, tana kaiwa zata shiga ta tuna da cewa ai Nihal ba tada lafiya sai ta nufi ɗakin ta ta tura ƙofar ta shiga bakin ta ɗauke da sallama, saman gadon da ta kai buban ta akai bata hango kowa ba yasa ta maida hankalin ta akan kujerar dake cikin ɗakin daga can gefe, amma ga mamakin ta itama babu kowa akai, don haka kawai sai ta fito ta sauko ƙasa tana ƙwalawa Madam florence kira, Da sauri ta fito daga can backyard ɗin dake bayan kitchen ɗin tana zaune tana ɗan hutawa taji kiran nata, "Good afternoon madam" Janan ta faɗa fuskar ta a sake, "Afternoon my dota, how was the study?" "Fine mah, where's my sister?" "Oh! She's their" ta ƙare zancen tana nuna mata ɗakin mahaifin nasu, "Ok, ya jikin nata?" "To, i don no my dear, but i hope she will be ok by now" ajiyar zuciya Janan ta sauke haɗe da cewa, "ALLAH ya ƙara sauƙi, bari naje na duba ta" ta wuce kai tsaye ɗakin mahaifin nasu ba tare data jira me madam ɗin zata sake cewa ba, Sallama tayi har kusan sau biyu bata ji an amsa ta ba hakan yasa tayi knocking ɗin ƙofar da ɗan ƙarfi yanda za'a iya jiyo ta tare da gyara tsayuwar ta, "Yes" Abba dake zaune tsare da Nihal tun ɗazu ya kasa matsawa ko nan da can ta ji ya faɗa, hakan yasa ta tura ƙofar ta shiga idanuwan ta suka sauka akan 'yar uwar tata dake kwance ruwa na shiga jikin ta a hankali ta ƙara sa daga ciki haɗe da maido kallon ta ga mahaifin nata dake latsar waya ta ce, "Abba barka da rana, ya jikin Adda ɗin" kamar bazai amsa ta ba sai kuma ya ce, "She's fine now, hop bakiyi wani kuskuren ba" "Bana tunanin haka Abba" ta faɗa cikin ko in kula tare da zuwa kusa ga kan Nihal ta zauna ta ɗago kan nata ta ɗora saman cinyar ta tana shafawa a hankali haɗe da cewa, "Sannu Adda Nihal ya jikin?" Nihal ta buɗe idanuwanta a hankali ta saukar akan fuskar ta tare da sakin murmushin ƙarfin hali ta ce, "Da sauƙi Janany har kin dawo?" "Eh, wajen grandma nake ji ashe bayan fitata kuma rashin lafiya ta kama ki" "To ita waya faɗa mata?" Kallon Abba Janan tayi haɗe da rufe baki kafin ta ɗan duƙo saiti kunnen Nihal tace, "Naje wajen ta ne ni da mm, inaga madam Florence ce takirata" Ƴar dariya Nihal tayi tare da raɗa mata a kunne "Lover girl, ya akayi su Jazz suka barki?" Janan na dariya sosai tunawa da yanda har ta tafi ta dawo basu sani ba ta ce, "Manta dasu kawai Adda ta kin ci abinci?" Kafin ta bata amsa taji muryar mahaifin nasu na faɗin, "Idan zaki dameta ne zaifi kyau ki tafi har zuwa anjima, bana son yawan surutu kinji ko?" Yana latsar wayar ya faɗi hakan fuskarsa a ɗaure tamkar ba shi ya faɗa ba, don ko ɗago kansa bai yi ba balle kasa ran shi ɗin ne, Duk da abun yayiwa Janan ciwo haka tayi murmushi haɗe da miƙewa ta ce, "An sorry Abba" sannan ta fice, kai tsaye kitchen ta nufa ta bubbuɗa warmers ɗin da Madam ta zuzzube abincin data gama akai ta ɗauko plate ta ɗiba aciki ta ɗora akan ɗan madaidaicin tray tare da ruwa da lemu ta koma ɗakin, har lokacin Abba na zaune ta jawo center table ta ɗora akai haɗe da kallon gorar ruwan da kaɗan ya rage su ƙare ta ce, "Abba ruwan ya kusa ƙare wa" bai tanka taba ya ɗago kai ya kalli gorar ruwan tare da ajiye wayarsa a gefe yasa hannu ya cire mata calula ɗin, yana faɗin, "Sorry my dota" Jin ta ɗan saki ƙara tare da saka kaɗa ya danne mata wajen, ganin tana ƙoƙarin tashi yasa Janan matsowa da sauri ta riƙa ta, "Janany sister zan shiga bayi" "Ok, to sauko a hankali" ta faɗa tana ƙara riƙo ta sosai ta miƙe, hanyar waje ta nufa da ita da biyar kaita toilet ɗin dake ƙasa a can main falon Abba ya ce, "Ki shiga bedroom mana, ko baki ga jikin nata ba ƙwari ba zata iya wahala kafin ku ƙara sa" ba musu Janan ta rakata har cikin toilet ɗin ta tara mata ruwa sannan ta fito ta jirata abakin ƙofa, sai da Nihal ta rage cikin ta sannan tayi tsarki ta wanko bakinta haɗe da fuskarta ta fito, "Sannu Adda nah" Janan ta faɗa tare da sake riƙo ta suka dawo falon ta zaunar da ita kan ɗayar kujerar sannan ta jawo Centre table ɗin data ɗora abincin akai ta buɗe ta ɗauko tana faɗin, "Sannu Adda, ki daure kici abinci ko ɗan jikin naki zai yi ƙarfi" "Ke kinci ne?" Ta jefo mata tambayar tana kallon cikin idanuwan ta, "No, idan kin ci, ni naci nawa abaya" ta ƙare zancen tare da miƙa mata lomar abincin data ɗebo

Chapter 18 of 40