Share this page
masu abinci akan dining table suka ci suka ɗan taɓa fira mm na zolayar Jabir wai ya zama matsoraci yanzu daga ɗai an ɗan sha shi sau ɗaya duk yabi ya wani maida kansa matsoraci mata, shikenan yanzu ko kallo macce baya iya wa balle ya tunkareta da kalmar so, Razina dake gefen Momy zaune ta dinga tintsirar dariya haɗe da cewa, "wai ya Jabir ɗin ne ke tsoron mata yanzu?" Karaf ya amshe yana hararar mm haɗe da cewa, "Ƙyalesa Razina ba gaskiya ya faɗa ba, kawai dai yanzu bana da lokacin kowace macce ne" "Yawwa ni nasan hakan, amma har dani da momyn mu?" "Aiku na musamman ne, tamkar rayuwa da kuma farinciki kuke agare ni, anyi ni ne aduniya waku kaɗai, don haka kisha kuruminki" "Tab!..yau ni naji ikon ALLAH, wai Jabir kai ne ke faɗin anyi ka wa Momy da Razina kaɗai ne, ka manta lokacin idan nayi maka zance akan Hanan cewa kake yi na barka anyi ka ne don ka bautu wa ita" Ɓata Jabir yayi yana nuna sa da yatsa haɗe da cewa, "Bana son haka fa mm, kadena tuna mun irin wuɗan nan magana ganun ko mu samu matsala" Tuntsirewa da dariya mm yayi har yana riƙe ciki, "Ikon ALLAH, shin ƙarya nayi man, ba a yi hakan ba?" "To idan ma anyi ai a mankas nake alokacin, kaga kuwa ai ba a riƙa yimun hukunci da shi ba" "Ehm..lallai wannan biyar dai da alama ta illa taka da yawa shiyasa ka tuba da shanta, mukam yanzu zamu fara sha miji yanda take, da daɗi ko kuwa?" "Kaji dashi, kwanan nan zan baka mamaki yaro, don tatil zanyi da wata mai ɗan karen daɗi ko ƙanwata?" Jabir ya ƙare maganar yana jifar Razina da wani irin kallo, don kuwa kwanakin nan wani irin yanayi yake ji a kanta da bai taɓa ji ba, hakan ne ma yasa mm daya lura da hakan ya bada ƙaimi wajen yin duk abunda zai jawo hankalin su wa juna, yanzu ma mere baki yayi haɗe da kallon Razina ya ce "To ƙanwarsa sai ki dage da addu'a ALLAH yasa kar ya koma kai hajar sa a in da baza a siya ba" ya ƙarƙare maganar haɗe da miƙewa yabar wajen, sai da ya leƙa ya yiwa Momy sai da safe sannan yabar falon yana faɗin, "Jabir mai dabino sai ka shigo ko" "Wannan kuma sunan kane malam ba nawa ba" Miƙewa yayi ganin Razina na hamma da alamun bacci take ji itama haɗe da cewa, "Bari naje nima na kwanta ƙanwata naga kema bacci kike ji ko?" "Eh wlh, gashi akwai assignment da aka bamu banyi ba kuma gobe ne za muyi submitting, kuma ALLAH bacci nake ji sosai, ko zaka yimun ya Jabir" ta ƙare maganar cike da shagwaɓa tana lumsar idanuwa, murmushi yayi yana ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo don ba ƙaramin kyau takeyi musamman tana irin wannan shagwaɓar, gyara tsayuwar sa yayi haɗe da folding hannayensa ya jingina ajikin ƙofar fita daga falon ya ce, "To nawa zaki biyani idan nayi maki?" Shiru Razina tayi kamar mai son tuno wani abu kafin can tace, "Kawo kunne ka kaji" Kunnensa ya miƙo mata a hankali ta raɗa masa wata maganar data sa shi shan toka haɗe da nuna ta da yatsa tabar wajen aguje ta shige ɗakin ta tana dariya, dariyar yayi shima kafin yabar ɗakin yana jin wani irin nishaɗi na musamman a tattare dashi... pls #comment #vote #share *ALLAH KAJIƘAN IYAYENMU 👏😭* _Page 11_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1233037125?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=3hlpWL61IPamNe8YA2X8b6FEZOUI1IBk3K%2BO63HoUXQxvuO5rXf9NwdIhJYYosceurjgxtRwlaxe696cshdtC28umXpLZLbnh0TsaA%2FZNZ0ob77qpPo7L2Y7MT5FSVaB_ *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B* INA KUKE MAKARANTA?? INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️ TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI. DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA (1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_ 👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 +447894142004 07065283730 ______________________________ *K* oda ya shigo sashen nasu kwance ya tadda mm a nan falo saman doguwar kujera yayi rigingine fuskarsa na kallon rufin saman falon ya ɗora hannayen sa akan ƙirji idanuwan sa a rufe, a zahiri za kace bacci yakeyi amma kuma idanuwansa biyu, zallar soyayya ce ta sashi faɗa wa duniyar tunanin da bai ma san da shigowar Jabir ba, kallo ɗaya Jabir yayi masa ya ɗauke kai tare da shigewa uwar ɗakin ya faɗa a kan makeken gadon dake tsakiyar ɗakin tare dayin wata irin ajiyar zuciya shima yana ƙoƙarin afkawa duniyar tunanin ta shi masoyiyar, Ganin haka ya sashi miƙewa ya ciro wayar sa dake jone tana caji haɗe da kamo jerin lambobin dake cikin wayar sa ya dannawa lambar da aka rubuta wa *Sister Razy* kira, kasancewar har ta fara bacci yasa har kiran ya taimake bata ji ba har sai da ya sake kira a karo na biyu sannan ta miƙa hannun ta ta jawo wayar ta saka a kunne ba tare data tsaya duba ko waye ba har lokacin idanuwan ta na a rufe, cikin muryar bacci ta ce, "Hel..lo, assalamu alaikum" "Wa'alaikissalam, ba dai har kin fara bacci ba?" "Eh Ya Jabir, ai na faɗa maka bacci nake ji sosai" "Assignment ɗin da?" "Zan yi koda da asuba ne" "Noo..tashi kije ki wanke fuskarki kizo muyi kin ji ko" "Pls..Yaya .." "Ya isa haka, je ki wanke fuskar ki nace muyi bana son gardama." Babu yan da ta iya dole ta tashi ta je toilet tana faman turo baki ta wanko fuskarta, har lokacin yana kan layi ba tare daya tsinke ba, murmushi yayi kamar yasan tutar baki take yi haɗe da cewa, "ALLAH ya baki haƙuri, duk wannan dai bazai sa na fasa abinda nayi niya ba, hop kin wanko fuskar?" A shagwaɓe ta amsa masa da eh tare da jawo jikkar tata ta makaranta ta fiddo littafin, "Hello.." "Ina jinki Mrs j" wani irin dimmm.. ta ji jin abunda ya faɗa haɗe da buɗe idanuwanta ta wartsake daga baccin ba tare da ta sani ba, "Mrs j?" ta nanata a zuciyar ta kafin ta saki murmushi haɗe da basarwa ta ce, "Ya Jabir gashi na ɗauki" "Ok faɗomun question ɗin farko?" "Write a Java program that execute 2 binary number.." "Ok ciro biron ki da takarda" "Wai yaya a waya zamuyi assignment ɗin? Kodai nayo maka snap ɗin assignment ɗin na turo maka?, ko kuma na turo maka ta watsApp?" "Ban faɗa ba, hakan dai nake so nayi ta jin muryar 'yar ƙanwata ko kuwa?" Sake sakin wani murmushin tayi da har sai da ya jiyo sautin sa sannan ta ce, "Shikenan, duk yanda kake so haka za a yi Yaya j" wani irin daɗi ya ji a ransa ganin duk sauƙin da yake isar mata tana saurin ɗauka, wanda hakan ya tabbatar masa da bazai wani sha wahala ba wajen isar mata da sauƙin zuciyarsa kai tsaye da kuma shawo kanta, A hankali ya fara karanto mata amsar question ɗin farko data faɗa masa step by step tana rubucewa har ya gama, sannan ta sake karanto masa na biyun shima ya faɗo mata amsa ta rubuta haka ma na ukun har zuwa na huɗu, bayan ta gama rubuce amsar tsab tayi gyaran murya haɗe da cewa, "Na gode ya Jabir, ALLAH ya saka maka da alkhairi ya baka mata ta ƙwarai da zata kula mana dakai da Momy da kuma ni" "Amin, duk da dai addu'ar ki ta riga da ta karɓu tunda ya riga ya bani, zan so dai ki bani tukuici, shi zaisa naji daɗi sosai a raina" "Hmm! Yaya Jabir kenan, Ni kuwa wane irin tukuici zan baka da yafi wannan addu'ar da nayi maka? Ba na so ne ya Muhriz ya riga ka aure shi yasa, don nasan tabbas zaka sha gori da tsangwama a wajen sa sosai" "Ai hakan ma bazai faru ba sai dai idan ni ɗin ba mai nasara bane yarinyar ta ce bata so na" "Tab, wace yarinyar ce zata kalli wannan santalelen kyakkyawan yayan nawa tace ba ta so?, ai ina tabbatar maka cewa sai dai in ba ta da rabo ne kawai zai sa tayi hakan" "Wai da gaske kikeyi?" "Sosai ma kuwa, baka kallon kanka a madubi ne?" "Ina tare da wancan yayan naki taya za a yi naga kyau na ko wani ya gane mun, kema ina tsammanin mafarki ne kawai kikeyi shiyasa kika daɗi haka, ko kin manta abunda kika ce ɗazu, wai ni zaki je ki bada haƙuri ayi welcome back ɗina" Tuntsirewa tayi da dariya haɗe da cewa, "Laaa.. kai yaya! Ai da wasa nake yi, Hanan sam ba ta da sa'a a rayuwa shiyasa ta barka, yanzu kuwa ai kafi ƙarfin ta, ba tada wata sauran daraja da kimar da za a daɗi a gabanta nemawa mutum mai girma da daraja irin ka soyayyar ta, manta da wannan shaci fad'in nawa ka fuskanci tan tagaryar gaskiyar dake fitowa daga ƙasan zuciya ta" "Ƙanwa ta kenan! Naji kuma na yarda da zancen ki, amma idan duk wannan gaskiya ne, me zai hana ki bawa yayanki tukuicin daya nema a wajen ki don naga dare nayi, ya kamata ace kin kwanta, ko kuwa dai bakya son bani ne shi yasa kike so ki shashantar da zancen?" "Ko ɗaya, ai kai mutum ne mai karamci, don haka ka faɗawa ƙanwar ka ko wane irin tukuici kake so, in sha ALLAH zan baka" "Kin tabbata?" "Sosai kuwa" "Idan na nemi ƙanwata data yi mani TUKUICI da SO anya banyi abun kunya ba?" Shiru Razina tayi don bata zaci da yayan nata zai iya faɗa abunda ke zuciyar sa da sauri hakan ba, wani irin faɗuwar gaba taji haɗe da nauyin sa lokaci ɗaya sun rufeta, jin ya ya sake maimai ta mata tambayar daya gama yi mata yasa cikin wata iri yar kasalalliyar murya mai haɗe da jin kunya ta ce, "Kana nufin ni Razina na baka TUKUICIN SO? to ya zanyi hakan bayan wata ta rigani samun muhalli a zuciyar ya'yan nawa? Nasan a koda yaushe zai riƙa kallon sa a ta ce silar faɗuwar masoyiyar sa" Murmushi Jabir yayi da tun ɗazu gaban sa sai faɗuwa yake yi jin shirun da tayi masa haɗe da cewa, "Ki manta da gurbin da wata ta taɓa samu a zuciya ta, kiji tausayin rayuwar yayan ki da zuciyar sa ke mamaye da duhu sanadiyar raunin azanci da yayi na saka wancan lalataccen gurbin a zuciyar sa, ki shigo duniya ta da kuma rayuwa ta don ki musanya wancan duhun da hasken ki, don ALLAH Razina kada kisa rauni na ya bayyana a idanuwan duniya ta hanyar rashin nasara a waje da kuma faɗuwa cikin gida, ina son ki kuma ina ƙaunar ki sosai, irin ƙauna da soyayyar da ban taɓa jin yanayin ta a zuciya ta ba, amma duk da hakan bazan takura ki ba kasancewar ni ɗan uwa ne kuma yaya a wajenki, na baki dama kije kiyi tunani kuma ki bawa ALLAH zaɓi akaina, duk abunda na gani ko naji zanyi haƙuri dashi kuma nima zanyi hakan in sha ALLAH? Yanzu kije ki kwanta dare ya yi, sai da safe kinji ko?" Ya ƙare maganar cikin marairaice murya haɗe da jin wasu zafafan hawaye na zubo masa, sosai jikinta ya yi sanyi jin kalaman sa na ƙarshe, ko da ba ta son Yaya Jabir bazata taɓa nuna wa ba saboda karamci da halacci irin na mahaifiyarsa ko ma tace mahaifiyar su, balle ma ita kanta tana jinsa a ranta saboda yanda tun tana ƙarama yake bata kulawa da kuma kyautata mata, bai taɓa bari tayi kuka ba matuƙar yana a waje, don haka ko yanzu ta tabbata bazai taɓa bari tayi kuka ba, zata amshe sa hannu biyu kuma ta haskaka duhun dake zuciyar sa ta riƙe sa a matsayin jigon rayuwa matuƙar yayan ta ya amince da hakan, Miƙewa ta yi tana jin wani irin sabon yanayi a tattare da ita ta shige toilet tayo arwalar bacci sannan ta haɗa littattafan ta data watse ta maida cikin jikka ta haye gadon ta tana mai karanto addu'o'in bacci tare da fatar ALLAH ya tasheta lafiya, shima dai kusan haka a ɓangaren sa, don har ya kwanta mm bai dawo ɗauki ba yana can falo a kwance yana faman saƙawa da warwarewa akan soyayyar sa, don ya san tabbas in akaci gaba da tafiya hakan tofa zazzafar ƙaunar Janan dake zuciyarsa zata iya kaishi kwance... ***. ***. ***. Yau ma kamar kullum tun da safe Janan ta tashi tayi shirin zuwa makaranta cike da ɗokin son ganin mm daya cika duniyar mafarkan ta a daren jiya, haka ma ta ɓangaren Nihal bata taɓa jin daɗin bacci ba aduniya irin jiya, duk wani juyi da zatayi cikin baccin ta fuskar mm take hangowa lokacin daya miƙo mata ledar kayan ta yana yiwwa Razina magana akan ta bata haƙuri, hakan yasa yau ta tashi zuciyarta cike da nishaɗi da farinciki, Da sauri da sauri take saukowa saman upstairs ɗin hango Janan na ƙoƙarin fita riƙe da gorar ruwa a hannunta, "Hi Janany sister, good morning" ta faɗa lokacin data ƙaraso ƙasa kusa da ita, murmushi Janan tayi haɗe da rungumeta tana jin soyayyar ƴar uwar ta ta har cikin ranta, musamman yau da ta hango zallar farin ciki kwance a fuskar ta, itama ta ce "Morning Adda Nihal, kin tashi lafiya?" "Lafiya klw, kar dai kice har zaki fita haka da wuri yau" "Eh, ina son nafara biyawa na dubo aunty ne, pls Adda kema don ALLAH..." "E'ehm Janan ya isa haka bana so, jeki ALLAH ya kiyaye sai kin dawo" ta ƙara sa maganar tare da ɗaga mata hannu sannan ta bar wajen tana kaɗa kai saboda waƙar da take sha ta Umar m. Sharif mai taken (SO YA SHIGENI), girgiza kai kawai Janan tayi tare da juyawa ta bar falon, ta rasa me yasa Nihal ta tsani aunty haka dako maganar ta bata so, koma meye ALLAH ya ganar da ita kuma ya daidaita tsakanin ta da ita, Kai tsaye sashen Hajiya zee ta nufa ta tadda Madam Florence ta gyare ko ina sai ƙamshi yake yi, haka ma aunty zee ta samu sauƙi sosai don har ta samu ta watso ruwa tana karya wa, murmushi ɗauke a fuskar Janan tayi sallama a bakin ƙofar falon tare da cire ta kalman ta ta shiga, "Aah.., alhamdulillah sauƙi ya samu, ina kwana aunty?" "Lafiya klw Nihal, kin tashi lafiya?" "Lafiya klw aunty ya ƙarfin jiki" "Alhamdulillah, ina samun sauƙi sosai, ina Nihal duk lafiya kuke?" "Lafiya klw, tana gaisheki" "Ina amsawa, har za a tafi makarantar ne?" "Eh aunty" Shiru ne ya biyo bayan gaisawar tasu kafin can Janan tace, "Aunty" sai kuma ta yi shiru ta kasa magana saboda rashin sanin ta ko ina zata fara yin zancen, murmushi Hajiya zee ta yi haɗe da kallon ta ta ce, "Na'am Janan, ko akwai wani abu?" "Eh aunty, dama cewa nayi don ALLAH idan akwai wani abu a ranki dake damun ki kiyi hakuri ki fidda shi tare da barwa ALLAH komai, ko kuma kisamu wani da kika yarda dashi kiriƙa faɗa masa zaki samu sassauci sosai a zuciyar ki, rayuwar nan aunty duk wanda lafiya zata yiwa daɗi baran mai ita ce, idan wani ciwo ya shige ka babu wanda zai sha wahala sama da kai, ko da mutane sun nuna damuwar su akan hakan tofa na banza ne tunda bazai yi maka maganin abun da kake ji ba, babbar mafita shine addu'a, domin ita waraka ce ga dukkanin matsaloli" "God bless you my dear, that's exactly what i'm telling her now" Madam Florence da shigowar ta kenan riƙe da ledar magungunan ta data ɗauki daga bedroom ta faɗa, "Look Hajiya, what ever is going to happen to you ALLAH has on ready plan it for you since before you were giving birth, so let continue to be patience, everything will be okay" "Shi kenan Janan, in sha ALLAH zan kula, tashi kije kada ki makara lokaci na wucewa kinji ko" "Pls..aunty.." "Na faɗa maki zan kula, jeki ALLAH ya kiyaye kuma yi maki albarka" "Amin na gode, sai na dawo, Madam akula da shan maganin ta pls" "Ok my dear, i will do that for you" ta faɗa haɗe da rakata har bakin mota, Sai da taga ta fita sannan ta dawo lokacin Hajiya zee ta gama karya wa ta ɓallo mata magungunan tasha haɗe da kallon ta ta ce, "I like Janan Hajiya, yarinyar ba ta da wata matsala, tana da hankali sosai, jiya da daddare muna tare da ita sai da Alhaji yazo sannan ta tafi, You see all this thing data faɗa maki, is true Hajiya, so let continue to be patient again and again" "Zanyi hakan Madam na gode, zuciyar ce ke gazawa a duk lokacin da abubuwa suka tunkushewa ƙwaƙwalwa, sai kiga duk iya jarunta da ƙoƙarin mutum ya kasa jurewa, amma ko don Janan da kuma ke da kuka nuna damuwar ku a kaina zan sake fidda komai kuma na ƙaurace wa tunanukkan da ba sa da wani amfanin yi, Ubangiji ALLAH yayi mana mafita ya kuma shige mana gaba ga dukkanin lamurran mu" "Eme" Sai da Madam Florence ta tabbatar babu wani abu ɗaya rage sannan ta yiwa Hajiya Zee sallama saboda taje ta ɗora abunda za a ci kafin Nihal da Alhaji su tashi, tana shiga ta tadda Nihal a kitchen har ta gama shirya komai na breakfast, dama indai wajen girki ne bata fiye matsala ba, sau tari takan shiga kitchen ta taya madam florence idan tana yi ko kuma tace yanar mata taje tayi wani aikin daban, Cikin girmamawa Madam florence tayi mata sannu itama ta gaisheta tana faɗin, "Today i have a special delicious breakfast for you madam" "Wow!, I like that my dota, it's always good for you to try it, lemme taste and hear this yummy" ta ƙare zancen tare da gutsirar garlic bread ɗin data haɗa da kuma zuma tea a gefe, sai farfeaun kayan ciki with arish patotoe, wanda duka Nihal ta koye su ne a online classes na ƙwararriyar mai koyar da abincin nan wato *chief Deejerh berver*, _(idan kina son ki koyi kalolin abinci, snacks, different birthday cake da kuma yanda ake haɗa khumras da turarukkan wuta masu d'an karen daɗi da tsuma zuciya, just give her a call or contact her in WhatsApp with this number👉+234 907 927 4454, Zata koya maki komai dalla-dallah and i know you will thanks me later, so just try it💃)_. Ƴar rawa Madam florence ta kama yi saboda daɗin girkin tare da yaba mata ita kuwa tana ta dariya, don babu abinda take so a duniya irin a yaba mata idan tayi abu mai kyau musamman ta fannin girki da take matuƙar ƙauna, wanda hatta karatun da tayi a fannin catering tayi specializing, ɗibar nata tayi sannan ta haye sama tana dariyar Madam florence da sai faman zuba sanyi take yi. Janan kuwa ko da ta isa makaranta kai tsaye wajen dasu mm ke zama ta nufa, basu fito ba don haka saita wuce class cike da shauƙin son ganin sa, haka shima mm da suka shigo kasa haƙura yayi da har sai sun fito lectures sannan ya ganta, don haka ya ja baron sa yayi wajajen classes ɗin su, kamar ance ta ɗago kai ta hangosa tafe, ai ko da sauri ta ɗauki ɗari biyar cikin jikkarta tare da ɗaukar excuse wajen lecturer ɗin ta fito har da ɗan haɗawa da gudun ta ganin yana ƙoƙarin wucewa don bai san class ɗin da take ba kawai dai yasan a nan biology department take shiga saboda haɗe suke da 'yan Chemistry, "Mm" ta faɗa cikin wata kasalalliyar murya dake nuna jin daɗin ganin sa da tayi, murmushi ɗauke akan fuskar sa ya juyo saboda ya gane muryar ita ce, juyo kan baron yayi ya dawo baya inda take haɗe da cewa, "A'ah Janan ashe kin shigo?" "Eh wlh, ina kwana" "Lafiya klw, kin tashi lafiya" "Alhamdulillah, ai dana shigo har inda kuke na tsaya sai na samu ashe baku fito ba" "Ayya, eh wlh, ya gida ya karatu, in Jin dai lafiya ko?" Ya ƙare maganar yana ƙara gyaggyarawa dabino sa zama, sai da tayi murmushi tana ƙare wa kyakkyawar fuskarsa kallo sannan ta ce, "Komai lafiya klw, kawai ina so ne na ƙara ganin ka da jiki" "ALLAH sarki, shi wannan jikin ba'a gajiya da tambayar sa?, Kidena damuwa ai na samu sauƙi sosai" "Alhamdulillah, haka nake son ji, ina ya Jabir ne ban gaku tare ba yau?" "Eh.. yana can wajen zaman mu, Ni na gaji da zaman ne shiyasa nace bari naɗan zazzagaya ko za a samu kasuwar kafin a fito" "Ok, to ga kuɗi na ka ajiye in ba damuwa zan zo na karɓa idan muka tashi kaga ko yanzu excuse ne na ɗauka na fito kada yaga na daɗe " "To shikenan na nawa?" "Ko na nawa ka saka" ta faɗa haɗe da miƙa masa kud'in, "Ko na duka ne?" ya ƙare maganar yana kallon fuskarta da sai faman tashin annuri da hasken farin ciki takeyi, Dariyar da sai da ya kusa mutuwa ya dawo yaga ta saki haɗe da juyawa ta bar wajen tana fad'in, "Zaka iya mana" Da sauri ya dafe sauti zuciyar sa yana ji tamkar zata ɓalle ta fito haɗe da jan baron sa ya koma wajen zaman su jiki ba ƙwari, Kallon sa Jabir yayi tare da cewa, "lafiya kuwa?" "Yarinyar nan zata sa na mutu Jabir, anya zan iya haƙura har lokacin da plan ɗin nan zaizo ƙarshe, wlh sake jiƙuwa nakeyi shataf akan ƙaunar ta, kaga wata irin zuƙeƙiyar dariya mai ɗan karen kyau data sakar mun?" "Ahh..ina zan gani kai dai ka gani kai data yiwa, ai ni dariya ɗaya nake hangowa yanzu malan, don haka rabani da wannan zancen, kasan ALLAH ma? Gab nake da ajiye wannan aiki na gaji, jira kawai nake a saka mani hannu a upper ta kuma a buga mani stamp, ɓat zaka nemeni ka rasa" "Ha don ALLAH?, Yau she kuma kafara neman wani aiki ban sani ba" "Oho, sa ido ka gani, ni bazan ƙare a kallon wannan lalacin soyayyar ba, mai rai da lafiya zan je na ji na kuma gani, wata ƙilma na aikata ta a zahiran ce na more" "Ohh! Kace kayi welcome back kenan!, To ɗan bani nasha mana, ita kuma wannan wace ce?" "Mai rabo, mai kuma Sa'a" "Hmmm! To ai shikenan idan tayi wari ma ji" Dariya Jabir yayi tare da kwanɗara dabino ɗaya ya jefa a baki, don yasan daga randa mm yasan zan cen sa da Razina tofa ta kaɗe masa, kodai yasha tsarguwa ko kuma yace ala tilas dole ya ba shi wani girman na daban. Pls #comment #vote #share *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭* [8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 12_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1233389769?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=VR3qhUPjb7B8CFuwKDn6FFZb7Np28u4fmDdh8%2FnE0AV5arKj1uPuGzbzcf2H1ofraDYYuEBZJkggMvqQ5Of0e7nKNbhJa5Q7dj5iN5CEB3Zz0JKvuSBbBvM%2F9ltKEYHb_ *TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B* INA KUKE MAKARANTA?? INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️ TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI. DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA (1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_ 👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 +447894142004 07065283730 ______________________________ *S* ai da aka share kusan awa ɗaya kafin su Janan su fito wajen lectures, cike da farin ciki Janan ta ɗauki jikkar ta ta sagala a kafaɗa ta ce wa Amira bara taje ta amso dabino wajen mm data siya ɗazu ta ce ya ajiye mata kafin su fito, wani irin kallo ta bita dashi cike da tuhuma kafin tace, "Oh! ke ba zaki je practical ɗin bane?" "Zan je mana, amma sai na samu abunda na sakawa ciki na a capteria tukuna, kin ga idan zaki je taso muje kada ki ƙara ɓata mun lokaci" Duk da akwai abunda Amira keyi haka kurum taji bazata iya bari Janan taje inda mm ba ita kaɗai, bazata juri ko kallonta yayi ba saboda kayan da ALLAH yayi mata ba duk namiji zai kalleta ba bai ji wani abu ya burgesa a tattare da ita ba, ko dai kyanta, ko ɗabi'unta ko kuma surar jikin ta, dole wani abu ya iya ɗauke maka hankali tattare da ita, kuma bata buƙatar hakan ta faru ga mm ɗin ta, don haka sai ta miƙe ta ɗauki jikkar ta itama ta sagala a kafaɗa, haɗe da cewa, "Muje ko?" Ba haka Janan ta so ba, amma nuni yanda ta iya sai kawai ta haƙura suka fita tare suna kaiwa bakin acadamic staff sai ga Ingaski shi da wani lecturer sun ci karo dasu, da sauri Janan ta ɗauke kai tayi kamar bata gane su ba, cike da mutunta Amira ta shiga rissinar da kai tana gaisheshi don yasan ko Amira ba ta so itama dole ta gaishe sun, shi kuwa Ingaski babu yanda za a yi

Chapter 7 of 40