Share this page
a spoon ga baki, sai data haɗiye ta sake ɗebo ta biyu zata bata ta riƙe spoon ɗin tare da hannunta ta kaimata abaki tana faɗin, "Kici kema na san kina jin yunwa sosai" Kasancewar ko da suka fito Abba ya riga ya fita acan compound ɗin wajen gida yasa Janan cewa, "Na ci abinci fa a gidan grandma" "Ki ƙara to" bata yimata musu ba ta karɓi lomar itama ta ci, haka suka ci gaba da cin abincin idan ta bata ta ci sai itama taci... _Kuyi manage pls_ *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 33_ *TUKUICIN SO*💞 *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ Suna kammala cin abincin Abba ya shigo falon ransa a ɓace kamar zai tashi sama, kallo ɗaya Janan tayi masa ta sadda kanta ƙasa ganin yanda ya nufo wajen yana nuna ta da yatsa kamar zai daketa saboda tsananin ɓacin rai, "Dama ke shashashar yarinya ce ban sani ba?, Har yaushe kika zama marar kunya haka da bata san kima da darajar mutane ba da har kike da zimmar ɗaya hannu ki mari yaron mutane don kinga yana son ki?, To bari kiji in faɗa maki, ko kina so ko bakya so aure tsakanin ki da Asgar kamar anyi ma an gama ne, ya rage naki ki koyawa kanki son sa da kuma martaba sa ko kuma akasin hakan don na lura so kike yi ki wulaƙantani tare da maidani ba abakin komai ba a bainar jama'a, kuma wlh baki isa ba, baki isa ba kinji na faɗa maki, shashashar yarinya kawai" Sai alokacin ta ɗago idanuwanta da suka cika tafi da ƙwalla tana kallon mahaifin nata ta ce, "Abba don ALLAH kada kayi haka, kayi tunani wlh ba mutumen kirki bane.." kafin ta ƙarasa ya katse ta ta hanyar katsa mata tsawa tare da ɗaga mata hannu ya ce, "Rufe mun baki anan ko nazo na tattakaki a wurin, ke ɗin kirki ne dake da har kike da ƙwarin guiwar faɗar haka akansa, ina ke yanzu jayayya kike yi dani akan abunda na zaɓa maki, to taya 'yar kirki zatayi haka wa mahaifinta" cike da mamakin kalamin sa na ƙarshe take kallonsa kafin can cikin karyewar murya kamar za tayi kuka tana girgiza kai ta ce,5 "Abba ba haka bane wlh, a yanda naga ka dage akan zaɓin daka yimun da ace wani ne daban ba shi ba to dana haƙura da nawa zaɓin nabi naka, amma gaba ɗaya a mahangar hankali da tunani wlh akwai tangarɗa da ƙaramcin tarbiya ga wanda ka zaɓa mun, shiyasa ko mutuwa zanyi bazan taɓa yarda na auresa ba balle har na iya rayuwa da shi" Wata uwar tsawa ya daka mata data matuƙar tsoratata tare da kaɗa mata ƴan hanjin ciki kafin a hasale ya ce, "Enough Janan!, Ni kike maidawa magana saboda kina ganin kin isa da kanki yanzu? To ai kece keda ƙaramcin tarbiya ba Asgar ba, don haka tashi ki ɓace mun da gani, kafin na ɓuɗe idanuwa na" ya ƙare zancen yana nuna mata hanyar fita, "Abba.." "Ki fata nace" ya faɗa da ƙarfi kamar zai dake ta, cike da tashin hankali da tsoro ta miƙe ta bar ɗakin aguje tana wani irin kuka mai tsima zuciya, daidai lokacin grandma da isowar ta kenan ta zo duba Nihal kamar yanda ta alƙawarta ɗazu ta turo ƙofar falon ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, muryarta da Janan ta jiyo ta sata juyowa da ƙarfi daga upstairs ɗin da take ƙoƙarin hawa ta nufo wajenta aguje tare da faɗawa jikinta tana sake sakin wani kukan kamar ranta zai fita, "Subhanallahi, lafiya Janan?, Me yake faruwa ne?, Ina Nihal ɗin ne?" ta jefo mata tambayoyin a jere ba tare data bari ta bata amsa ko ɗaya ba saboda tsananin ruɗewar da tayi, ganin bata da niyar bata amsa sai faman kukanta takeyi yasa ta ƙara so shigowa cikin falon tana ƙwaƙwalwa Madam florence kira, da sauri Madam dake saye da kayan shiga kitchen tana gyara inda tayi aikin abinci ta iso haɗe da duƙawa har ƙasa tana gaishe da grandma, ba tare data amsata ba ta jefo mata tambaya cike da son jin bayani daga wajen ta, "Me yake faruwa ne agidan na tadda Janan tana kuka florence?" Ta kai ƙarshen zancen idanuwanta akanta tana ƙoƙarin fahimtar ko akwai wani abu daya faru, "Hajiya ina kitchen ina aiki ban san meke faruwa ba, na dai san a gabana Janan ta shiga part ɗin alhaji ta ce zata je dubo Nihal.." kafin ta rufe baki Hajiya tayi saurin katse tta ganin Abba na fitowa part ɗinsa riƙe da hannun Nihal, "Tashi ki tafi na samu amsar tambayata" ta faɗa tare da ɗaure fuska ta kauda kanta gefe tana ɗan bubbuga bayan Janan da har lokacin kuka take yi, da Farooq Hajiya tayi tsammanin wani abunne ya sami Nihal shiyasa Janan ke kuka, amma ganin yanda dady ya riƙo hannunta garas tgaras da ita ta samu sauƙi yana tabbatar mata da cewa mugun halin mahaifin nasu ne ya motsa, don ko shakka babu shine dalilin wannan kukan na Janan. "Barka da zuwa Hajiya" Abba ya faɗa bayan ya zauna a gefen daya zaunar da Nihal, "Barka" ta amsa masa ciki ciki tare da zaunar da Janan saman kujerar itama ta zauna, "Ya hanya Hajiya anzo lafiya?" "Lafiya" ta sake bashi amsar a daƙile ba tare data kalli ko gefen da suke ba, ganin haka yasa Abba ya kama bakin sa yayi shiru yana kallon yanda Janan ta shige a jikinta tana faman shesshekar kuka, ɗan ɗago kai Nihal tayi ta gaishe da Hajiya kamar bata so, itama ta amsa mata a daƙile tana faɗin, "ai da kin riƙe gaisuwar taki don ba ita nazo amsawa ba, ganin ki nazo yi kuma alhamdulillah naga kin samu sauƙi don haka riƙe gaisuwar ki bana so" kafin Nihal tace wani abun Abba ya marairaice murya haɗe da cewa, "Haba Hajiya, kin san bata da lafiya shiyasa kike ganin kamar tana gaisheki a dole, amma ba haka bane, duk da ta samu sauƙi akan ɗazu, amma har yanzu jikin nata ba ƙwari sosai" cike da mamaki Hajia ta bisa da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa, "To ALLAH ya kyauta ya kuma bata lafiya" "Amin Hajiya" shiru ne ya biyo bayan wasu mintota kafin Hajiya ta sake cewa, "To ita wannan baiwar ALLAHr dana isko tana kuka me akayi mata tunda dai ALLAH yasa ita ba ɗiyar so ce ba" Shafa kai ya shiga yi cike da rashin gaskiya don sam baya son Hajiya tasan da zancen haɗin auren Janan da Asgar har sai komai ya gama daidaita, ba tare data kawo komai aranta ba don ita a tsammanin ta halin nasa ne na banbanci daya saba nunawa tsakanin ta da ƴar uwar ta ko yanzun ya yi, hakan yasa ta sake yin wata ajiyar zuciya akaro na biyu haɗe da cewa, "Usman kenan, ina riƙon ka da kaji tsoron ALLAH, Katuna yaran nan duka ƴaƴanka ne, ka tuna cewa uwa ɗaya ce ta haifa maka su, katuna duka amana ne a wajenka kuma ALLAH zai tambayeka yanda ka kula dasu, a wasu lokutan mu muke haifar da ƙiyayya a tsakankanin ƴaƴayen mu ta hanyar nuna fifikon soyayyar wasu akan wasu, bayan mun san cewa yin hakan ba daidai bane kuma kuskure ne, bance zuciyar ka taƙi son Nihal akan Janan ba tunda ALLAH shike da ikon sarrafa zukata, amma ya kamata ace idan hakan ta faru ka ɓoyewa ranka domin kaucewa matsala, nayi imani da ALLAH cewa ba don yaran nan na son junan su ba da tuni ka dasa ƙiyayya mai tsanani tsakanin su, saboda haka na roƙeka ka gyara kafin lokaci ya ƙure maka, kafitar da abinda ke ranka akan Janan ka tubarwa ALLAH domin hakan shirme ne kuma aikin jahilci ne, babu mai ikon kashewa da kuma rayawa aduniya in ba ALLAH ba" "Amma Hajiya ai akwai sila ko?" "Sosai akwai, amma ai kai baka san ma me ake cewa suka ba, domin idan ka sani to bazaka taɓa cewa ƴarka itace silar rasa mahaifiyar su ba, ajali shine sila, sannan a halin da ake ciki yanzu har ma ada ta fika buƙatar mahaifiyarsu ta kasance araye, saboda haka ka fidda wannan aƙida a ranka don ba mai kyau bace" wani kukan Janan ta saka jin har yanzu mahaifinta be dena yimata kallon da yake yi mata a da ba, abunda tun tana ƙarama take kwana dashi kuma ta tashi dashi ace har yanzu yaƙi ficewa azuciyar mahaifinta, wannan wane irin ubane haka take dashi?, tsaki Abba ya ja, haɗe da miƙewa yana faɗin, "Hajiya wannan yarinyar ganin yanda kike biye mata yasa take neman maida mutane 'yan iska, amma da sannu zanyi maganin ta tunda bata san ana haƙurin da akeyi da ita ba" "Au! Usman, agaban nawa ma bazaka daga mata ba?, wato bata san haƙurin da akeyi da ita ba, shikenan tunda abun naka ya zamo haka taje ta tattaro inata inata mu tafi, kaga sai ta koma hannuna gaba ɗaya yanda zaka dena haƙurin da ita tunda baka son ta, amma ni bazan bari taci gaba da zama anan ba har kazo ka saka mata ciwon zuciya kamar yadda ƴar gwal ɗin taka ta ɗorawa kanta shi, ka ga shikenan ka huta da haƙurin da ita, ke maza tashi kije ki haɗo kayan ki muje kin ji ko, nace kiyi shiru hakan ki dena kukan kada kanki yayi ciwo" tana rufe baki Nihal ta saka kuka tana shusshura ƙafafuwa, "ALLAH ni bazan yar da ba, haka kurum kizo ki rabani da ƴar uwata, wlh ALLAH Abba bazan yarda ba sai dai mu koma tare" ta ƙare zancen tana sharɓar majina ita ala tilas babu inda za a je da Janany sister ɗinta, Mere baki Hajiya tayi kafin tace "Kya ji dashi in dai sakalci ne, gaki ga uban naki, ni kam babu inda zan je dake don bazai saɓuba na zauna da marar kunyar yarinya cikin mutanena na mutunci ta yar fani tunda baki san girman mutane ba, sai dai kiyita zama nan wajen wanda ya isa dake yayi ta biyewa sakalcin ki tunda bazai iya da shashancin ƴar uwar ki ba" ta ƙare zancen tare da taimakawa Janan ta tashi zaune tana sharar ƙwalla, suna haɗa idanuwa da Abba ya maka mata harara tayi saurin sadda kanta ƙasa, don kuwa ko shakka babu wannan karon tafiso tabi grandma ko don ta kuɓuta da takurar da Abba keyi mata akan masoyin ta, saɓanin da da itama sam bata son a rabata da ƴar uwar ta, ganin yanda Nihal ta ɓare baki da gaske da gaske tana kuka ya sata ɗago kai tana kallonta, sosai taji ba daɗi yanda take kuka saboda tasan irin tarin ƙaunar da take yimata ba kaɗan ba, amma ya zatayi? Mafita take nemarwa kanta don haka dole ta haƙura tabi grandma ɗin su koda hakan bazai wa ƴar uwar tata daɗi ba, Yanda take kukan ba ƙaramin tayarwa Abba da hankali yayi ba, don indai tashi ce bazai damu da komawar Janan hannun grandma ba, dama itace ta tilas tasa cewa lallai sai ta dawo hannunsa badon haka ba da babu yanda zai juri rayuwa da ita a inuwa ɗaya, sai kuma irin son da Nihal keyi mata da zancen aurenta da Asgar da baya buƙatar Hajiya ta sani yanzu, hakan kaɗai yasa zai dakatar da Hajiya akan tafiya da Janan, rarrashin Nihal ya shiga yi kafin ya samu daƙyar tayi shiru bayan yayi mata alƙawarin Hajiya baza ta tafi da Janan ba, lokacin har Janan ta haɗo kayan ta tana saukowa daga kan upstairs, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai tare da kallon mahaifiyar tasa ya ce, "Hajiya Don ALLAH da girmansa kiyi haƙuri kada ki raba yaran nan tunda Nihal bata so, nayi maki alƙawarin bazan sake aikata abunda bakya so ba" "Au saboda Nihal bata so kake roƙona, lallai Usman kayi nisa wlh sai addu'a? To ita fa waccan ɗin idan tana so? Sai ayi ƙaƙa?" Ta ƙare zancen tana nuna Janan ɗin dake tsaye da hannu. "Haba Hajiya, kefa kika gama faɗin dukan su abu ɗaya ne, don me zaki raba ɗaya biyu a yanzu?" "Kaga Usman, fita idanuwa na wlh kafin na saɓa maka, don na tafi da Janan zaka ce na raba ɗaya biyu? Ai bance zan hanasu ganin juna ko waya da juna ba idan suna buƙata, wannan zaman takurar ne dai bazan bari taci gaba dayi ba kaji na faɗa maka, sannan ko Nihal na so ko bata so ai dole wata rana zasu rabu tunda kowacen su aure za tayi ta tafi gidan mijin ta, shikenan sai ace an raba ɗaya biyu?" "Koma dai meye naji na yarda Hajiya, amma kiyi haƙuri don ALLAH, in Sha ALLAH bazan ƙara yin abunda bakya so tsakanin su bat, kin ga Nihal ba cikakkiyar lafiya ne da ita ba, hakan zai iya sake jefata cikin damuwa kuma kinga abun bazai yi daɗi ba" "Mtsss.." Hajiya ta ja tsaki tare da miƙewa ta je tariƙo hannun Janan dake tsaye suka fice daga falon tana cewa, "Ka ji dashi kai da Nihal ɗin, kai komai Nihal..Nihal, ko tsoron ALLAH ba ka ji tunda ba ita kaɗai ce ƴarka ba, ni wannan shashancin ya isheni haka" Suna kaiwa a compound ɗin gidan zasu shiga part ɗin Hajiya zee don su gaisa, Janan taji Nihal ta riƙo hannun ta tana kuka, "Janany sister kada ki tafi kibar ni don ALLAH, kin fa sani banda kowa sai ke sai Abbana, ke kaɗai ce abokiya ta kuma abokiyar shawara ta, wlh Janany bazan jurewa rabuwa dake ba" ta ƙare zancen tare da faɗawa akan kafaɗar ta, "Amma Adda kina fa jin abunda Abba ya faɗa, wlh kamar yanda kike jin baza ki iya rabuwa dani ba haka nake jin bazan iya rabuwa da mm ba, tafiya ta ba tana nufin mun rabu bane, kawai wata mafita ce a wurina kuma kema kin san haka!" "Na sani Janany, amma kiyar da dani, na rantse da sarkin daya jera mani a wazzu, zan tsaya maki da dukkanin iya ƙarfina kamar yanda uwa ke tsayawa ƴarta har sai naga kin mallaki farincikin ki, wannan alƙawarina ne kuma na tabbatar maki da zanyi hakan" ta ƙare zancen haɗe da miƙo mata hannun ta, duk yanda Janan taso ta kauda kai akan buƙatar ƴar uwar tata kasawa tayi, jefar da akwatin tayi haɗe da rungumeta tana kuka itama, "Bazan barki ba Adda ta, duk da nasan hakan bara zana ce a wajena na rasa abunda nake so" "Ki dena faɗa Janany, bazaki rasa abun da kike so ba kin ji, ina son ki sosai" ta ƙare zancen tana shafa kan Janan dake jikinta, sakwarkwatai Hajiya tayi tsaye tana kallon su, duk da kalamansa sun jefata cikin duhu dama tasan abune mai wahala iya rabasu don sau ɗaya hakan ta taɓa faruwa lokacin da Nihal ta je karatu waje, shima sai da aka kusan rasa Janan saboda yanda tayita fama da rashin lafiya, ita kanta Nihal saida akayi da gasken gaske aka samu ta natsu tayi karatun, tayi hakan ne dama ko ALLAH zai sa Abba ya sauko ya gane gaskiya. Shi kuwa Abba dake tsaye a can bakin ƙofar shiga falon yana kallon su, juyawa kawai ya yi ya koma ciki ganin Nihal ta shawo kan ƴar uwar tata yana mai saƙawa da warwarewa kala kala a zuciyar sa. Ranƙwashi Hajiya ta kaiwa Nihal akai haɗe da cewa, "Ai sai ki cikata haka, mai shegen bacin tsiya da daɗin baki, na ga yanda zakiyi duk ranar da aka ɗaura maku aure?" Cuno baki Nihal tayi tana shafa ƙeyar kanta kafin tace, "Na dai ji, ALLAH baki haƙuri" Nihal ta faɗa tare da ɗaukar akwatin Nihal ta ja hannun ta suka wuce ciki, ita kuma ta wuce part ɗin Hajiya zee tana jinjina shaƙuwa da soyayyar dake tsakanin su. *We back in Sha ALLAH, kuyi haƙuri, kuyi haƙuri👏🏻 nasan kun yimun uzuri and i really appreciate that, luv you all❤️🤍💞* *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 34_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI*💎 *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* _____________________________ Bata wani jima ba a part ɗin Hajiya Zee don suna gaisawa ta wuce gida abunta ba tare da ta bari ko sallama sun sakeyi da Abba ba kasancewar har lokacin drivern ta na nan a haraba yana jiran fitowar ta, A ɓangaren mm kuwa sosai Momy taji daɗin yanda ya labarta mata cewa Hajiya ta karɓe sa hannu biyu tare da yimasa fatan ALLAH ya tabbatar da alkhairi, bayan kwana biyu da mm ya shirya ya je gidan grandma kamar yanda ta buƙata, Tarba ta musamman Hajiya tayi masa inda tasa aka shirya masa abinci mai rai da kuma lafiya aka dama masu fura ta sha nono da madara aka saka masa fridge, lokacin da mm ya ƙara so gidan kai tsaye ta bawa baba mai gadi damar shigowa dashi har cikin falon nata, a lokacin tana zaune tana faman jan carbi, don bata jima da gama sallar walha data saba yi a koda yaushe ba, cikin girmamawa ya shigo ya zauna har ta kammala sannan ya ɗan rissinar da kansa ƙasa yana gaisheta, murmushi tayi sannan ta ce, "Ashe dai mijin nawa da gaske yake yi, ai nazata ma ka manta da zancen gaba ɗaya" "A'a Hajiya, ni dake neman farincikina taya zanyi in manta?" "Lallai kam, da kayiwa kanka sakkiyar da ba ruwa, don kan waigoni lokacin daka tuna zaka tadda har na ba wani ita" cike da tsokana irin ta kaka da jika mm ya ce, "Ai kuwa da kotu ta rabani dake da kuma kowaye kika bawa matata" dariya Hajiya tayi haɗe da ƙwalawa mai aikinta kira sannan ta ce, "Ya iyayen naka? In jin dai duk lafiya suke?" "Lafiya klw Hajiya, amma dukan su ALLAH yayi masu rasuwa" "Ayya.. Sannu Muhammadu, ubangiji ALLAH ya rahamshe su" "Amin" ya faɗa yana jin ɗacin rashin iyayen nasa a ƙasar zuciyar sa daidai lokacin, "Rabi akawo masa abinci ko?" Hajiyar ta faɗa lokcin da mai aikin nata ta ƙara so cikin falon tana tsane hannunta da zanen dake jikin ta, bata ce komai ba ta juya ta je ta haɗo masa abincin a ƙaton tray ta kawo ta ajiye masa agabansa sannan ta juya ta bar falon, "Muhammadu ga abinci nan ka taɓa da ƴan ruwa kafin na ɗan zaga, bari nazo?" ta faɗa tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗin ta, gorar ruwan dake kan tray ya fara ɗaukowa da zimmar tsiyayawa yasha sai kawai yaga an miƙo hannu an karɓa, ɗago kan da zai yi suka haɗa idanuwa da Janan cikin wata doguwar riga brown colour mai haske data kusa sadewa da jikin ta, sosai tayi masa masifar kyau saboda sun kwana biyu basu haɗu ba sai dai waya, a hankali ya lumshe idanuwan sa kafin ya sake buɗe su akan kyakkyawar fuskarta yana faɗar, "Subhanallahi khaliƙul azhim, fatabarakallahu ahsanil khaliƙin, nurul alb daga ina haka? Masha ALLAH gaskiya kinyi kyau sosai" Janan na dariya tare da zuba masa ruwan a cup ta miƙa masa tana faɗin, "kai hubbin ruh, karfa ka fasa mun kai, duk kyan da nayi na kaika?" Saida ya kurɓi ruwan idanuwansa na akanta tana ƙoƙarin zuba masa abincin sannan ya ce, "Ai kinma fini ranki shi daɗe, bar abincin nan kada ki zuba" kallonsa tayi cikin idanuwa haɗe da cewa, "Girkin ne na Hajiya yau baza ka ci ba?" "A ƙoshe nake shiyasa, musamman ma dana gaki sai naji na ƙara ƙoshi" Wani ƙayataccen murmushi ta sakar masa haɗe da ajiye plate ɗin a gefe sannan ta rufe warmer ɗin cikin jin daɗin kalaman sa ta ce, "To shikenan mijina, dama ina kishin kaci girkin ta ba nawa ba, ina kwana, ka tashi lafiya?" "Lafiya klw matata, ya kike?" "Alhamdulillah" "Ya karatun?, Kar dai ince yauma tserowa kika yi?" "Ai kuwa kamar ka sani" ta faɗa tana dariya tare da zaunawa akan kujerar dake kallon tasa, ɗaure fuska yayi tamkar ba shi ba haɗe da miƙewa tsaye yana faɗin, "Indai akaina zaki fara guduwa wajen lectures bara na tafi abina" "Nooo..mm wlh ba haka bane" ta faɗa kamar zatayi kuka, sallallamin da suka ji Hajiya na rafkawa da salati yasa mm komawa ya zauna tare da kafeta da idanuwa alamun zamu haɗu dake, sake marairaice fuska tayi haɗe da riƙo kunnuwanta alamun ban haƙuri ya kauda kansa ya maida inda Hajiya ke ƙoƙarin zaunawa tana faɗin, "Yau naga barbaɗa ni hafsatu, ke kuwa daga ina waya gayyato ki kika zomun gida bagatatan ba zato ba tsammani? Ina Muhammadu nace ya dawo yau ina nemansa ba ke ba?" Saida Janan ta kalli mm dake murmushi sannan ta maida kallonta ga grandma tana turo baki haɗe da cewa, "Yo tunda kika ce mijina ya dawo ai kamar kince nima na dawo, saboda duk inda kikaga wata dole zakiga Zarah awajen" "Tofah, kuji fi'ili, to wace Zarah" "Ga ni" "To naji, yanzu dai tashi ki bamu waje zamuyi magana" "To Hajiya, yanda duk kika ce, akwai fura?" Ta miƙe tare da nufar wajen fridge, tun kafin ta ƙara sa ta ce, "Ke..ke..ke, dakata, jeki can kitchen ki tambayi rabi baza a rasa wata ba, wacce kenan ta Muhammadu ce" "Kai Hajiya abun miji ai na mata ne ko hubbin ruh" ta ƙare zancen tare da buɗe fridge ɗin ta ɗauko furar tana kallon mm sannan ta kurɓa "Kai, wannan haɗin furar na musamman ne Hajiya, gaskiya tare zamu sha dashi" "Ai sai kiyi kwaɗayayyiyar banza, kawo masa nan ki ajiye kada na sake mantawa da ita" saida ta sake kurɓa kusan sau uku sannan ta rufe fridge ɗin ta zo ta kawo masa furar ta ajiye a gabansa sannan ta wuce can cikin gida inda rabi take, shi kuwa binta yayi da kallo tamkar zai haɗiye ta saboda yanda duk wani motsi nata ke sake tafiya da hankalin sa, Ƴar gyaran murya Hajiya tayi kafin takira sunan sa itama idanuwanta na akansa, cike da jin kunya ya shiga sosai kansa haɗe da amsa mata da, "Na'am Hajiya" "Ina so kayi haƙuri da tambayoyin da zanyi maka kuma kabani amsa tsakani da ALLAH, zanyi maka su ne saboda nasan yanda zan ɓullo wa lamarin mahaifin Janan bawai don na wulaƙanta kaba ko kuma wani abun, ko ɗaya bana nufin hakan" "Hajiya kada ki damu da duk wata tambaya da kike son yimun domin ko musulunci ya yadda da ayi bincike acikin sha'anin aure, kuma in Sha ALLAH zaki sameni mai faɗar gaskiya ga duka amsoshin tambayoyin ki" "Masha ALLAH, Nagode daka fahimceni" saida ta ɗan yi shiru sannan taci gaba da cewa "Muhammadu, ɗazu na tambayeka akan ya iyayen ka suke, sai kake shedamun cewa ALLAH yayi masu rasuwa, abun tambaya anan, dama can ku ƴan asalin wannan gari ne ko kuwa?, Ya sunan mahaifinka?, Meye sana'ar ka?, A ina kake zaune yanzu?, Wu ɗan nan sune kaɗai abunda nake son ji dangane dakai, daga su kuma babu wani abu da zan sake buƙatar sani akanka, suma ɗin na tambayeka ne saboda mahaifin Janan kamar yanda na faɗa maka tun farko, da kuma wata matsala da nake gudun sake faruwar makamanciyar ta acikin zuri'a ta, ina fatar kuma hakan bazai zame maka damuwa ba?" "In sha ALLAH Hajiya, farko dai sunana, Muhammad Muhriz, sunan mahaifina kuma Muhammad, iyayena ƴan asalin jahar nan ne, amma a ƙauyen caranci suke da zama su da mafiya yawan ƴan uwansu, noma da kuma kasuwanci sune sana'ar mahaifina kafin ALLAH yayi masa rasuwa a sanadiyar ɓarayi da suka afka ma ƙauyen namu, an haifeni a can kuma acan nafaro rayuwata ni da ƙanwata mai suna Razina, mutuwar mahaifina da mahaifiyata su suka zamo silar gudowar mu ni da ƙanwata muka dawo wannan garin da zama...." Nan yaci gaba da labartawa grandma ma yanda rayuwarsu ta kasance bayan zuwan su a wannan garin har zuwa yanzu daya mallaki hankalin sa ba tare daya ɓoye mata komai ba. *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU*👏😭 [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 36_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ Haka akayi kuwa, Janan na fita ta ɗauki hanyar gidan su Amira, bata wani ɗauki dogon lokaci ba ta isa anguwar, wayarta ta ciro ta lalabo lambar Amira ta kira, lokacin Amira na zaune tsakar gida tana latsar waya, ƙanwarta zarah kuma na can gefe kusa da mahaifiyar su dake kwance nan tsakar gida ba lafiya tana yimata fifita, tana kallon wayar Janan tayi mata har kusan kira uku bata ɗaga ba, sai a na huɗu shima har Janan tafidda rai saboda ya kusan katsewa sannan Amira ta

Chapter 19 of 40