ɗaga,
"Yawwa Amira Ina kika shiga inata kiran wayarki baki ɗaya ba, hop dai lafiya ko?" Sai da Amira ta yatsine fuska sannan ta ce,
"Klw, ina ɗan wani aiki ne shiyasa" ta faɗa muryarta a adaƙile tamkar wacce aka tilasta ma wayar, murmushi Janan tayi daga can gefen ta haɗe da cewa,
"Lafiya klw Amira kuma naga baki shigo school ba, kin fa san last semester muke kuma final year sai munyi da gaske mun jajir ce"
"Matsalata dake kenan wlh, kin maida boko tamkar wata ibada, ko ibada ce ai akwai lokutan da ake hutawa ba a yi"
"Ehm! hakane, yanzu dai fito gani anguwarku inda muka tsaya a ranar"
"Wai da gaske kikeyi, me kika zo yi?"
"Amira kenan! Wajenki nazo mana"
"To gani fitowa ina zuwa" ta kashe wayar haɗe da kallon Zarah ta ce,
"Ke tashi ki gyara wajen nan zanyi baƙuwa"
"Ni kuwa meye illar gidan nan da zaki wani ce a gyara?, Ki kira Al-amin sai yayi ya gyara shi don dai bazan iya tashi daga wajen nan ba" Zarah ta faɗa tana ƙare wa gidan nasu kallo dake gyare tsaf, kunnuwan ganyen iccen umbrella ne kawai da suka faɗo suma ɗai-ɗai ku ba wani can da yawa ba, harara Amira ta banka mata haɗe da cewa,
"Ni kike faɗa wa haka?, na rantse saina faffasa maki wannan bakin baki mai rashin kunya kwanan nan" ta ƙare zancen haɗe da kaɗa kai sannan ta wuce ɗaki ta ɗauko mayafinta ta fice daga gidan, umma dake kwance tana jin jiki ta kalli Zarah ta ce,
"Jeki ki tsittince ganyen can kafin tadawo, kinsan halin ta ba daɗi ne da ita ba, yanzu ne zata birkice kuyita masifa agidan na har ku ƙaramun damuwa akan wacce nake da ita"
"Amma umma..."
"Tashi mana Zarah kiyi yanda na ce, ko ba komai ai yayar ki ce, ya kamata kidin ga fita batun ta kina bata girmanta da ALLAH yayi mata akan ki"
Ba don Zarah taso ba ta miƙe ta je ta sa tsintsiya da paker ta kwashe dattin ta je ta zuba a dusbin sannan ta dawo ta zauna tana faman kumbura fuska, "ALLAH ya shiryeku" umma ta faɗa tana kallon Zarah, bata daɗe da zaunawa ba Amira ta shigo Janan na biye da ita a baya,
"Umma tashi ga Janan ta zo duba ki" Amira ta faɗa tare da ɗora mayafin data cire akan igiyar dake tsakar gidan, gefen barandar da suke ciki Janan ta zauna tana kallon umma da tunda ta shigo idanuwanta suka sauka akanta taji gabanta ya faɗi, haka kurum taji matar tayi mata wani irin kwarjini da bata san dalilin saba, cikin sakin fuska ta amsa gaisuwar da Zarah keyi mata haɗe da kallon Momy ta ce,
"Sannu umma, ina wuni?"
"Lafiya klw, dama kece Janan?"
"Eh Umma, ya jikin?"
"Alhamdulillah da sauƙi"
"ALLAH yaƙara sauƙi umma, dama kwana biyu Amira bata je school ba shine nazo naga ko lafiya, sai take faɗa mun ashe kece bakya jin daɗi"
"Wlh kuwa, kiyita dai haƙuri da ita, ko ba komai nasan zaki ɗarata hankali nagode ƙwarai ALLAH yayi maki albarka"
"Amin umma, kunje asibiti?"
"Eh mun je, dama matsalar hawan jinin nan ne da kullum bata ci bata ƙarewa ta tasoni agaba, shiyasa yau da taga jikin nawa ya ɗan yi nauyi bata tafi ba, amma alhamdulillah yanzu na samu sauƙi saidai fatan ALLAH kasa mucika da imani"
"Amin umma, amma ai indai za a tsare shan magani kuma a riƙa fidda damuwa da matsalolin yau da gobe a zuciya to komai zaizo da sauƙi, ALLAH dai ya ƙara lafiya" ta ƙare zancen tana kallon Amira data ɗaure fuska jin abunda ummanta ta faɗa, wato ma har faɗi takeyi Janan tayi haƙuri da ita har tana cewa ta fita hankali, bayan duk tana sane da abunda Janan ɗin tayi mata na ƙwace mata masoyi, tana wannan tunanin taji Muryar Janan na faɗin,
"Amira umma nashan magani yanda ya kamata kuwa?"
"Eh" ta faɗa a tsiwace tana kauda kai gefe, da sauri Zarah ta ce,
"Ai maganin ma ya ƙare aunty Janan.." kafin tarufe baki Amira ta kaimata duka tana faɗin,
"Wa yasaki? Shugabar ƴan surutu?"
Cuno baki Zarah tayi da niyar yimata tsiwa umma tayi saurin cewa,
"ALLAH dai ya shiryeki zarah, tashi je ki kawo mata ruwa"
Yanda Zarah tamiƙe tana tunzurar baki ya bala'in bata dariya, sai taga ta bala'in yimata yanayi da mm ɗin ta idan yana yanayin fushi, murmushi tayi haɗe da kallon amirayta ce,
"Ahhh...gaskiya ki dena takurawa Zarah, daga faɗan gaskiya shikenan har dasu duka, zo Zarah ki karɓa" Janan ta ƙare zancen tare da zuge jikkarta ta ciro chocculate da waffer ta miƙa ma Zarah, haka kurum taji yarinyar ta shiga ranta"
Murmushi Zarah tayi bayan ta ajiye mata ruwan haɗe da miƙa hannu takarɓi chocculate ɗin tayi godiya, mere baki Amira dake kallonsu tayi kafin tace,
"Oho, indai Zarah ce bakiyi komai ba, kina tashi zata zageki don ba kirki ne da ita ba"
"Anya ƙawas, kodai kishi kikeyi da ita saboda tafiki kyau"
Miƙewa gaba ɗaya Amira tayi tabar wajen haɗe da cewa,
"Ai kuwa da na dena fita" duk suka sa dariya har da umma dake kwance tana jin wani irin yanayi da ita kaɗai tasan yanda take ji, Janan ta jima agidan sosai kafin tayi sallama da umma tare da ajiye mata dubu biyar na dubiya duk da bata san da rashin lafiyar tata ba, dama su kaɗai ne acikin jikkar don haka sai ta ajiye mata tare da addu'ar ALLAH ya bata lafiya,
Saida Amira ta rakata har wajen mota sannan ta dawo gida lokacin ana kiraye kirayen sallar magrib, Zarah ta kalleta haɗe da cewa,
"Aunty Atmira amma wannan ƙawar taki nada kirki ba kamar ke ba" dariya Amira tayi kamar da gaske haɗe da laƙƙamo Zarah dake ƙoƙarin tashi ta sakar mata wata irin duduniya a baya data sata sakin wata uwar ƙara,
"Don ƙaniyar ki tunda tafini mutunci sai ki koma gidansu ta zama yayarki"
"Hasbunallahu wani'imal wakeel, wai ke bakya gajiya da cin zalin ƴan ƙannen nan naki?, Idan basu ji sanyi a wajenki ba to a ina kike so suji?"
"Umma fa kina jin me tace"
"To ƙaryat tafaɗa ne? Ai koni yarinyar ta burgeni wlh, gata da natsuwa da hankali, dubi yanda take jan ƴar uwarki ajiki amma ke banda hantarar ta babu abunda kika iya" cikin ƙunƙuni Amira da taji tamkar ta fashe da kuka saboda yabon da umma keyiwa Janan ta ce,
"Ai itama ashibanci ne tunda ba tada ƙanne"
"Oh! ALLAH dai ya rabaki da sakarci Amira, koma dai meye ni ta biyani tunda ALLAH yasa ba tada hali irin naki"
Ƙunƙuni taci gaba dayi cike dajin haushin Janan, shikenan duk inda ta je sai anfi sonta akanta, yanzu ma ana nufin mahaifiyar ta da ƴar uwarta fifita soyayyar ta zasuyi akan tata?, Ta tambayi kanta tare da komawa gefe ta kumbura fuska aka tilas fushi takeyi,
Dariya Zarah tayi haɗe dayi mata gwalo irin ke ji haushi ɗin nan, banza tayi da ita kamar bata ganeta ba tana mai rayawa a zuciyar ta sai ta ɓata Janan a idanuwan kowa ta yanda babu wanda zai koma yabonta fiye da ita,
Bayan sallar magrib umma na zaune tagama tana lazumi ta ciro dubu uku acikin kuɗin da Janan ta bata ta miƙawa Zarah tana faɗin,
"Kuje keda Al-amin chemest ɗin bayanaka kuce ya haɗo mani magungunan daya saba haɗa mun na samu nasha, yanzu haka kwana biyun nan da ban sha ba ji nake tamkar ana hasa mani wuta acikin jiki"
"To umma" Zarah ta faɗa haɗe da karɓar kuɗin ta saka hijabin ta suka fice ita da Al-amin, bayan sun fita Amira ta kalleta cikin ƴar damuwa jin halin data ce tana ciki, ta ce
"Umma don ALLAH kidena wannan tunane_tunanen hakan, kin san bamu da kowa aduniyar nan sai ke kuma muna tsananin buƙatar ki"
"Amira kenan! Ke yarinya ce, bazaki taɓa iya fahimtar yanayin da uwa ke kasancewa aciki ba alokacin data rasa wani ɓangare daga cikin rayuwar ta, musamman idan ta rasa tabbacin shin ta rasa shine na har abada ko zai iya dawowa gareta"
"Kamar ya umma?" Murmushi tayi haɗe da cewa,
"Shiyasa nace bazaki iya ganewa ba Amira, addu'a ta kawai ALLAH kasa na cika da imani, amma har na mutu wannan mijin na azuciya ta.." ta ƙare zancen tare da fashewa da wani irin kuka mai cike da ban tausayi da tarin ma'anoni daban daban, tagumi Amira tayi tana jin ɗacin kukan mahaifiyar tata a zuciyar ta, ita kanta takan tsinci kanta cikin damuwa aduk lokutan da irin wannan yanayin ya bijirewa mahaifiyar ta wanda shi ɗin ne ke haifar mata da tashin hawan jinin da take fama dashi tun suna ƙanana, don koda suka tashi sun taddata tana fama dashi tun mahaifin su na raye, jin motsin dawowar su Zarah yasa tayi saurin tsaida kukan ta tare da share hawaye don bata so su risketa cikin yanayin, ko Amira ta riga da tasan wannan matsalar shiyasa har take barin hawayen ta su rinjaye ta agaban ta, Kar ɓar maganin Amira tayi ta ɓaɓɓalla mata yanda take sha tasa Zarah ta ɗebo mata ruwa ta bata ta sha, cikin sanyin murya umma ta kallesu haɗe da cewa,
"ALLAH yayi maku albarka ya kareku da dukkanin sharrin maƙiya da azzalumai, ya baku yawancin ran da zanga ƴaƴa da kuma jikokin ku"
Duk suka amsa da amin tayi murmushi haɗe da jinginawa ajikin ginin ɗakin tana mai tunano abubuwa da dama da suka shuɗe a shekarun baya acikin zuciyar ta da kuma ƙwaƙwalwar ta.....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏🏻😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 35_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
______________________________
Sosai grandma ma ta tausayawa irin halin rayuwar da mm suka tsinci kansu lokacin da suka rasa iyayen su duk data wani ɓangaren ta jinjinawa matar data riƙe su sosai, don ba kowa yake da wannan zuciyar ba yanzu, a hankali tayi ajiyar zuciya haɗe da kallon mm da idanuwansa sukayi jajir saboda ɗacin da yaji na tunawa da irin kisan wulaƙancin da aka yiwa iyayensa a gabansa, ji yake gaba ɗaya komai ya koma masa sabo tamkar yanzu abun ya faru, cikin tausayawa ta ce,
"Kayi haƙuri Muhammadu, dukkanin mai rai mamaci ne, su kuma wuɗan nan bayin ALLAH dake faman zalintar mutane suna rabasu da rayuwar su da duniyoyin su ALLAH ka shiryesu in masu rabon shiryuwa ne in kuma basu da rabon shiryuwa ALLAH kayi mana maganin su"
"Amin Hajiya" ya bata amsa yana ƙoƙarin danne abunda yake ji na taso masa a zuciya,
"To, duk da dai na ce bazan sake yimaka wata tambayar ba, zan so in san ko wace baiwar ALLAH ce wannan data taimaki rayuwar ku haka, sannan kamar yanda ka ce ɗazun ka kammala karatu yanzu haka kana aiki, to meya kaika makarantar su Janan har kuka haɗu, kuma meyasa baka sake waiwayar ƙauyen ku ba ko ALLAH zai sa ka riski wasu daga cikin ƴan uwan mahaifinka ko na mahaifiyar ka?"
"To Hajiya bari nafara amsa maki tambayar ki ta biyu, dalilin ɗaya kaini makarantar su Janan shine neman wani abu da nakeyi don kaucewa abinda zai jawo damuwa cikin rayuwar mu ni da ƴan uwana sai nake sana'ar dabino saboda na samu na cimma nasara akan wannan abun, sai kuma zancen rashin komawata ƙauye mu, a gaskiya ƙwaƙwalwa ta bata taɓa kawomun wannan tunanin ba saboda ganin agabana aka kashe iyayenmu gaba ɗaya, sai nake ganin idan ma na koma hakan bazai amfane mu ba tunda koda muka baro ƙauye gaba ɗaya ya watse, babban dalilina kuma shine babu abunda muka nema muka rasa awajen baiwar ALLAHr da muke tare da ita, sai wannan tunanin bai zo mun a ƙwaƙwalwa ba gaba ɗaya, Momy wata irin uwace da tsayuwar ta agaremu ya kauda dukkanin rashin jigo na rayuwa, macece mai matuƙar karamci da haƙuri, imanin ta da kuma yaƙinin ta akan ALLAH ke ƙaddarta komai na rayuwa yasa bata da baƙinciki da kuma ƙyashin taimakon kowa, ta riƙemu irin riƙon data yiwa ɗan ta ƙwaya ɗaya tilo duk dako mahaifinsa baya raye ba tare da tayi duba da irin rashin karamci da kulawar da ita akayi mata da ɗan ta ba, fatana shine ALLAH ya faranta zuciyarta kuma ya yar mata damuwar fili data bayyane" cike da damuwa Hajiya da idanuwanta suka fara cika taf da ƙwalla tunawa da abunda suka yiwa matar ɗanta da jikan ta saboda son zuciya ta ce,
"Amin ya ALLAH Muhammadu, duk inda ake karamci wannan baiwar ALLAH tayi maku kuma ubangiji kaɗai ne zai iya biyan ta wannan taimako data yi ba tare da dubi rashin alaƙar dake tsakanin ku da ita ba, abun da mu muka kasa yiwa matar ɗan mu da yaron ta saboda kawai banbancin yare da addini duk dako ɗan mu ya musuluntar da ita, amma..." Sai kuma ta kasa ƙara sawa saboda kukan da yaci ƙarfin ta, abune wanda ya daɗi yana ci mata zuciya ta rasa wanda zata faɗawa taji sanyi, sai gashi sanadiyar labarinsa yau tafara fitar dashi, kuka takeyi sosai cike da nadamar abunda ya faru ba tare daya hanata ba har sai da tayi mai isarta tayi shiru don kanta, gyaran murya yayi haɗe da gyara zamansa kafin yace,
"Kamar dai yanda akoda yaushe Momy ke faɗa, ko wane abu na tafiya ne bisa tsarin ƙundin ƙaddarar rayuwar da ALLAH ya tsarowa bawa, taimako abune mai kyau ga duk wanda ALLAH ya bawa ikon yi, ba sai ga wanda ka sani ba hatta wanda baka sani ba zaka iya yi masa, ALLAH ya tsaro hakan zata faru, don haka haƙuri ya kamata kiyi Hajiya sai kuma atuba a nemi hanyar gyara kuskuren da aka aikata"
"Muhammadu tuni na tubarwa ALLAH akan wannan kuskure da muka aikata, sai dai taya zan gyara bayan na yakuce su daga jikina da kuma ahalina, inda nake tsammanin zan samesu na kasa samun su awajen, su kuma gaba ɗaya sunyi fushin zuciya sun kasa dawowa garemu, kuma na tabbata ba kowa ya jawo hakan ba sai Usman" hajiya takai zancen tare da sake fashewa da wani kukan, sosai mm yaso bayyana mata cewa yana tare dasu ganin irin tarin nadamar da tayi acikin idanuwan ta, amma sai yabar hakan a zuciyar sa har sai zuwa nan gaba sai yayi mata bazata, baki ya shiga bata tare da addu'ar ALLAH ya bayyana su, ya kuma bata shawara akan tafi gaba da addu'a in Sha ALLAH nan kusa bada jimawa ba zasu dawo gareta, kuma hakan ya matuƙar kwantar mata da hankali sosai, inda ta sake jin ya shigar mata rai fiye da tunani, ɗago kanta tayi tana kallonsa haɗe da cewa,
"Kaima Muhammadu ya kamata ka sake waiwayar ƙauyenku ko ALLAH zaisa ka riski ƴan uwan ka, tunda har yanzu akwai sauran mutane aciki"
"Shikenan Hajiya, in Sha ALLAH zanyi hakan ko don nasamawa soyayyata notukkan da zasu ɗaureta kuma su tsayar mata, saboda ba kowane ahali ne zai yarda ya aurar maka da jinin sa ba ba tare daya san kai naka ahalin ba" murmushi irin na manya masu saurin fahimtar abu Hajiya tayi haɗe da cewa,
"Muhammadu kenan! Kana tunanin cewa trashin sanin ahalin ka na iya dakatar da ƙudurina wajen ganin an aura maka Janan? Wlh ko ɗaya, domin na yarda da tarbiyar ka nagartar ka da kuma ko waye kai, ko da ace bakada kowa aduniya kuma ba kada komai, to ni zan tsaya maka ka auri Janan a matsayina na mahaifiyar mahaifin ta, don haka kada ka kawo wannan a zuciyar ka, kaje kawai ka nemi ƴan uwan ka domin na tabbata suma suna da buƙatar ka" tana rufe baki Janan ta shigo falon cike da shagwaɓa tana faɗin " ALLAH Hajiya nima inada buƙatar zantawa da mijina ba ke kaɗai ba, kinga ƙarfe ɗaya tayi makaranta zan koma muna da lectures zuwa ƙarfe biyu"
"Oh Janan, wai yaushe kika koma hakan ne?, Gaba ɗaya kin feɗare kin koma mani marasa kunya, anya kuwa wannan Hafsatu na ce ta asali" sai alokacin kunya ta kama Janan ganin yanda Hajiya tayi maganar cikin sanyin murya tana kallon ta, hannu tasa ta rufe fuskarta haɗe da cewa,
"Wayyo ALLAH kakus na dena"
Shi dai mm idanuwansa na akan fuskar Janan har Hajiya ta miƙa ta nufi bedroom ɗin ta tana faɗin, "A'a yi abunki ja ira, ai kin bi sahun tantiriyar yayar can taki kun maida ni abokiyar wasar ku"
Murmushi ya saki haɗe da cewa "ƙyaleta Hajiya, ai sai na fasa yi da ita na ce in ba keba sai rijiya"
Hajiyar na dariya ta ƙara sa daga ciki haɗe da cewa, "ba ruwana da daɗin baki, kadai sha furar ka kafin katafi kar wannan kwaɗayayyiyar yarinya ta shanye"
"Ba komai ai abun husband na matar sane ko hubby?" Janan ta bata amsa tana kallon fuskar mm,
"To madam yanzu sai ki tashi mutafi kiwuce makaranta ko?"
"Amma ai da sauran lokaci, sai 2 fa"
"Au Hajiya kike son kora shiyasa Kika azalzaleta"
"Ya zanyi, so nake naji muryan ka kuma nayita kallon fuskarta kafin na tafi"
Turo fuskar tasa gaba ɗaya yayi suna kallon juna ya ce, "to gata kiyita kalla har sai kin gaji" tana dariya haɗe da wasa da hannunta akan throw pillow ɗin dake kan cinyarta ta sunkuyar dakai ƙasa saboda wani irin kallo da yake aika mata dashi daya sa gaba ɗaya jikin ta mutuwa ta ce,
"Ai bazan gaji da kallon wannan kyakkyawar fuskar taka mai cike da zati ba"
"Ko?" Ta kaɗa masa kai tana dariya,
Sun jima sosai suna sanyaya zukatan junan su kafin mm ya miƙe ganin har ƙarfe biyu saura kwata tayi yana faɗin,
"Zumar zuciyata tashi mu tafi kada ki makara a hanaki shiga, cema Hajiya zan tafi"
"Angama yallaɓai" ta faɗa tare da ajiye throw pillow ɗin a gefe ta nufi ɗakin Hajiya, bata wani jima ba suka fito tare yayi mata godiya tare da sallama ya ce zai tafi, ta ce
"To ka gaida Momyn taka da kuma Razina"
"Za su ji in Sha ALLAH, ɗan uwa na fa? Ko so kike yi idan kuka haɗu yace bai auren?" Ya faɗa yana gyara tsayuwarsa, Hajiya na dariya ta ce,
"To a gaida shi shima, don da alama gunsa zan koma tunda wannan ja irar ta kasa ta tsare tayi kane-kane da kai" duk suka sa dariya su da ita, anan ma sun ɗauki sakanni suna wasar jika da kaka kafin ya sake yimata sallama ya wuce, itama Janan sallamar tayi mata sannan tabi bayansa suka fita tare har lokacin yana dariyar dramar grandma,
Kasancewar da motarta ta zo yasa bai fara wucewa ba har sai daya ga tafiyar ta sannan shima ya je ya hau mashin yabar wajen, yana isa gida ya tadda Momy nayiwa Razina tsira kai, ɗan ma gare nata kai yayi haɗe da cewa,
"Razina wai ke sai yaushe zaki girma kidena wahalar mana da momy haka?" Razina da tasa kukan shagwaɓa Momy na dariya ta ce,
"Sai ranar da yayana da mijina suka dena shagwaɓa ni" takai zancen haɗe da rufe fuskar ta da rafin hannuwa, girgiza kai kawai mm yayi haɗe da faɗawa kan kujera, don ya lura soyayyar ɗan uwan nasa tasa ƙanwar tasa tafara fetsare masa,
"Ya naji kayi shiru my son" Momy ta faɗa tana yimasa dariya, murmushi yayi shima haɗe da cewa,
"To me zance Momy, yarinyar nan ta girma kawai ki aurar da ita a huta"
"Ba yanzu ba sai ta ƙara wayau don kar naje na kaita ku haɗe mata kai kaida abokinka ku takurata ko my dota" ta faɗa tare da ɗago fuskarta yana kallonta, ba kunya kuwa Razina ta ɗaga kai tana dariya, mere baki mm dake kallon ta yayi kafin yace,
"Tab, ai indai Razina ce Momy wannan baƙin nata dani har ɗan uwan nawa tana saida mu saboda shegen wayau" yana rufe baki Jabir na fitowa da plate ɗin indomie daga kitchen ya zo ya ajiyewa Razina agabanta yana faɗin, "pls momy cika ta taci abinci kada yunwa ta kama mun ita" haka kuwa akayi Momy ta sakawa Razina ɗan kwali akan ta sannan tabar falon tana dariyar yanda mm ya saki baki yana kallon ikon ALLAH haɗe da cewa, "my son ALLAH dai yasa girkin yayi daɗi ƴah ta zata iya ci, Razina ma miƙe tana faɗin "ai kuwa Momy idan baiyi ba, bar masa abunsa zanyi ya cinye" tare da wucewa ta je ta wanko hannun ta sannan ta dawo ta jawo plate ɗin indomien ta fara ci, murmushi kawai Jabir yayi haɗe da juyowa wajen mm ya miƙa masa hannu ba tare daya damu da irin kallon da yake aika masu dashi ba daga shi har masoyiyarsa ya ce,
"Welcome back man, har ka dawo?" wani kallon mm ya sake jefa masa dashi da hannun nasa daya miƙo masa yana faɗin,
"Wa? Ni? ALLAH ya tsare na gaisa da ɗan daudu, yanzu kai ko kunya ba ka ji gotai gotai ka shiga kitchen dafawa yarinya abinci"
"So what?, Yunwa fa take ji, gashi ta dawo school a gajiye, shine fa nace ta zauna ko noodles ce na dafa mata, to meye aciki?"
"Any way ni kaga tafiya ta, ka riga ka faɗa kwata tun yanzu, don haka ko aure kukayi chif cooker zaka komawa" ya ƙare zancen tare da miƙewa yabar falon shima yana dariyar sa azuciya, Jabir dako ruwan zafi baya iya dafawa lokacin da suna school sai dai ya dafa masu wai yau shine har da dahuwar indomie, lallai soyayya ba abunda bata sawa,
Jabir kuwa cikin ɗaya murya yanda mm zai iya jiyosa don har ya kusa fita ya ce,
"Yasin ni nawa da sauƙi, daga gani kai ɗan wankin da gugan ta zaka koma" dariya Razina ta saka har tana sarƙewa da sauri Jabir ya je ya buɗe fridge a kitchen ya ɗauko gorar ruwa da cup ya tsiyaya mata haɗe da miƙa mata a baki yana hura mata iskan bakinsa akai, ya ce
"Sorry princess, kiyi a hankali pls "
"ALLAH dear kai da ya mm kun bani dariya sosai"
"Ai hakan ɗai zan yimasa in rama kuma na kashe masa baki, in ba haka ba ya dinga tsokana ta kenan, gashi ke ko yabawa girkin ma kin kasa yi" ya ƙare zancen yana maka mata harara,
"Kai dear, ai baka jira na ƙare ba, ALLAH the noodle was so delicious, amma dai in munyi aure dear kai zaka riƙa dafa mana abinci ko" ɗaure fuska yayi tare da ɗaga hannu zai kai mata ranƙwashi tayi saurin saka hannuwa akai haɗe da runtse idanuwa ta saki ƴar ƙara, dariya yayi yana lasar leɓensa na ƙasa ya ce,
"Matsoraciya, ai ni ba namijin duka bane balle na dake ki, amma dai duk kika kuskura na dinga shiga kitchen ina girka mana abinci to ya zama dole ki bani kulawa ta musamman tare da haifo mani kyawawan yara masu kyau kamar ki, wannan shine ai kin ki idan kin amince"
Cike da jin kunya ta rufe fuskar ta ba tare da ta ce komai ba har yabar wajen yana dariya,
Da daddare bayan kammala dinner mm ya labartawa Momy yanda sukayi da Hajiya ɗazun, tsabar farinciki har da ƙwalla Momy tayi haɗe da cewa gobe zata je gunta, dariya mm yayi kafin yace,
"No Momy, ban faɗa mata komai ba fa, don haka ki bari lokaci ne zai tabbatar maki da nadamar da Hajiya tayi don na tabbata da kanta zata zo neman ku aduk lokacin data samu labarin cewa kune ahalin nawa da nake dasu a yanzu"
"My son, am very eager to see her again" yanda take farinciki yasa mm kallonta cike da mamaki ya ce,
"Momy, yanzu duka abunda suka yimaki baisa kika ji haushin su ba"
"Naji mana, but to me komai ya wuce, duk abunda ka gani aduniya yana faruwa to yana tafiya ne bisa tsarin ƙaddarar da ALLAH ya ƙadarowa mutum"
"Haka ne, ALLAH ya bamu irin zuciyar ki Momy" tayi murmushi haɗe da ɗaya hannayenta sama tana yaren daya tabbatar addu'a ce takeyi cike da farinciki,
Jabir da Razina kuwa dama suna can tsakiyar falo suna shan soyayyar su hankali kwance,
A ɓangaren Janan kuwa cikin kwana biyun nan ta samu sauƙin takura da tsangwama daga wajen Abba, don guard ɗin daya sa mata ma duka ya janye su kamar yanda Nihal ta buƙata yayi, haka ma tun daga wacce ranar da suka haɗu da Asgar bata sake ji ko ganin sa ba, rayuwarta takeyi hankali kwance, ba tada wani buri yanzu bayan ta kammala karatun nan lafiya ɗaya rage mata wata biyu da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 40