ai dai bata mare kin ba tun da ALLAH ya taimakeki kyakkyawan yaron nan nawa ya tafi da hankalinta, badon hakan ba yau da sai dai a baki haƙuri a maimakon haƙurin da ke kika bata"
Sake cuno baki tayi cike da jin haushi abunda Momyn ta faɗa,
"Ai dama nasan haka zaki faɗa Momy, amma bari nakoma gida saina faɗawa ya Jabir, yanda gobe bazai bari muzo mu kaɗai ba idan zamu fita, don na gano indai yana tare damu shike maganin duk ire-iren wannan iskancin da yarinyar nan ta nemi yimana"
"Yi maki sai malama, kuma bari kiji dake har yayan naki sai kun sha duka wata rana garin wannan tsiwa da rashin jin naku, in banda abunki meye na jinini dakai ƙara tunda gashi cikin sauƙi an magance komai, koda yake dake har yayan naki duk halinku ɗaya, ALLAH kasa kada ku janyo mana duka wata rana" mm ya fad'a haɗe dayin gaba don ya fara gajiya da shegen jinini irin nata,
Dariya Momy ta saka haɗe da cewa,
"To kin ji dai, don ALLAH don Annabi kurufa mana asiri kar kusa da tsufana naci duka ba gaira ba dalili"
Dariya itama Razina tayi haɗe da rungumota ajiki ta ɗora kanta saman kafad'arta tana fad'in,
"Wa mutun inji mutuwa, ai babu wanda ya isa ya taɓa mana Momy da sunan duka bai kwana prizin ba, sha kuruminki ina gama karatun nan soja zan je, kinga kuwa taɓa uwar soja ba qaramin tashin hankali bane aka taddo"
Da wannan surutun nata har mm yaje ya fara d'aukar wasu abubuwan da yasan suna buƙata na rayuwar yau da kullum, koda suka ƙaraso har ya kusa gamawa sai kawai suka ƙarasa ɗaukar sauran suka saka ya kai inda ake biya aka yimasa bil ɗin kuɗin ya biya sannan aka saka masu a ledoji ya d'auka suka nufi wajen motar su, kai tsaye gida suka nufa don dama wannan sayayyar kaɗai ce ta fiddosu, itama babu yanda baiyi dasu su bari idan anyi sallar isha'i ya huta tunda dawowarsu kenan daga wajen tallar dabinon amma Razina taƙi ta aza rigima ita lallai sai dai yanzu zuwa bayan isha'i bacci za tayi, wannan dalilin yasa bayan ya gama sallar magrib tunda Momy tasa baki ya gyara ya ɗ'aukosu suka zo wajen sayayyar, Jabir kuwa dama cewa yayi babu inda zai je don ya gaji da yawa sosai, ashe rabon haɗuwar su da Nihal ne ya jawo hakan, don kuwa gaba ɗaya ganin mm yasa Nihal duk tabi ta susuce, tuƙin kawai takeyi amma babu wani ƙwari a jikinta har ta isa gida, ba abunda take tunan in banda fuskar mutumen da bata san ko waye shi ba, sunansa da kuma inda ya fito duka bata sani ba, amma ya bala'in shiga ranta fiye da tunani, kyansa, surarsa da kuma yanayin halittar sa sak irin ta mijin da ta daɗe tana yiwa kanta mafarki ne, murmushi tayi lokacin data ƙarasa shigowa cikin ɗakinta ta zauna bakin gado tana kallon hannunta daya riƙe, a hankali tayi kissing hannun haɗe da cewa,
"Mr.man!, son ka ya shigeni ba tare da nasan kai ko waye ba, amma jikina na faɗamun kai ɗin kana da duk wani abu da nake buƙata awajen ɗa namiji, kyau, arziqi, wayewa da kuma kyakkyawar sura, saboda haka zan nemoka aduk inda kake tunda son ka ya riga daya taɓani ya kuma shiga zuciyata yayi ginin da hannu bazai taɓa iya tureshi ba"
Ta bayanta Janan data shigo ɗakin tun d'azu ba tare data lura ba taje ta rungumota had'e da turo kanta ta gefen wuyanta tana dariya ta ce,
"Who's this lucky man da yayi wuff da zuciyar addatah daga fita har ya soma sakata sabbatu haka?"
Dariya Nihal tayi tare da juyawa ta gyara zamanta akan gadon daidai tana kallon Janan data dawo gabanta itama ta zauna ta tanƙwashe ƙafafuwa tana kallonta kamar mai shirin ɗaukar karatu ko cin abinci tace,
"He's quit handsome, very wealthy and classy, kallo ɗaya zakiyi masa kisan cewa shi ɗin cikakken namiji ne abun son kowace macce, to be Frank sister I'm in luv with him"
Dariya Janan ta kwashe da ita har tana tuntsirawa kan gadon jin yanda auntyn tata ke expressing irin haɗuwar wannan mutumen tare da fallashe sirrin zuciyarta wa ita, sai kace ba Nihal ɗin data sani ba mai yaƙuna samari da wulaƙanci, ciki kuwa hadda wuɗanda keda tarin dukiya saboda ɗai basu cika qualities ɗin da take son namiji dasu ba,
Ganin haka yasa Nihal jin haushi tare da janyo pillow tayo kanta, da sauri ta miƙe tana ci gaba da dariya ta bita suka fara zagayen ɗakin da gudu tana son maka mata shi....
_Hmmm tirƙashi, ƙara-ƙara-ƙaƙa, yanzu fa za'a soma littafin, ga dai Janan masoyiyar Muhriz wacce ga alama itama ta fara sonsa, ga kuma Amira ƙawarta dake masifar sonsa, sannan ga Nihal yayar Janan itama ta ɓullo da tata salon soyayyar agaresa, shin ko waye a cikinsu zata lashe kambun TUKUICIN SO daga wajensa?, Ku biyo ni sannu a hankali domin samun amsarku ta hanyar zafafan #comment #like #share da kuma #voting, it's just the beginning 😁💃💃_
*ALLAH KAJIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 9_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1232646048?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=CvU1L4Ri7P2MwK59Vhcm%2F2QRIHE7SJOZdQXGBegtDJBU1zEcYmdVN%2FRFMn3QqHHj40EHjCBfnM6fwoHbj2CeF4Tz3beDd12SEQ6LRjk34HAiBtmHcKeNe7hIGsnLDe%2Bj_
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_
👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
______________________________
*A* Kan gadon Janan ta sake faɗawa har lokacin tana dariya ta dinga doka mata pillow ɗ'in ajiki tana faɗin,
"Wai meye abun dariya anan Janan?, ba zaki dena ba?" Nihal ta faɗa haɗe dayin jifa da pillow ɗin fuska a ɗauke ta koma bakin gadon ta zauna tana hararar ta,
Sai alokacin Janan ta tsaida dariyar da take yi tare da tasowa ta zauna kusa da ita,
"I'm sorry Adda na dena" harararta ta sake yi ta kauda kanta gefe, Janan ta riƙe kunnuwanta haɗe da sa ke cewa
"Pls... Adda" juyowa tayi tare da ɗaga hannu kamar zata mareta da sauri ta rufe idanuwa haɗe da faɗawa jikin ta,
"Am sorry Adda bazan sa ke ba"
"Matsoraciya kawai, ga tsokana ga tsoro ko?" Nihal ta faɗa tana dariya, don ta riga da ta san halin Janan, in dai ta fannin tsoro ne akan duk abun da zai taɓa mata jiki, tofa tabbas zata ɗauki lamba ta ɗaya,
"Ai na dena bazan sake ba, abun ne ya bani mamaki fa, wai ke da kanki ke faɗar kin kamu da son saurayi da ƙaunarsa har kina cewa zaki nemo a duk inda yake, lallai duniya juyi juyi, yau so yayiwa Adda ta mugun ƙulli"
"Hmm ba zaki gane ba Janan, gayen ya haɗu ne tako ina, bari nayi maki na Umar m Sharif, daga kallo ɗaya zuciyata ta kamu da son sa, kuma bana tunanin zan rayu idan ba dashi ba"
"Tirƙashi, kice zancen nayi ne Adda, hala ma ya sunan gayen ne?"
"Ban sani ba"
"To a ina kuka haɗu dashi?"
"Bebeji supermarket, bari na baki labarin abun da ya haɗa mu dashi..." Daga nan ta kwashe labarin duk abun da ya faru ta faɗa mata.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama saurarar yayar tata haɗe da cewa,
"Wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa Adda, ai kinyi ragon azanci da baki yi ƙoƙarin samun abun da zai sake haɗa ku ba ko da kuwa da sunan ƙawance ne"
"Kamar ya kenan Janan"
"Ai kamata yayi lokacin daya miƙo maki ledar kayan kika yimasa godiya kiyi introducing sunan ki garesa saboda ki samu ko da sunan shi ne shi ma ya baki tunda ba a san kuma ina za a ƙara haɗuwa ba, yanzu ke ta ina kike tunanin zaki fara nemosa bacin ko sunan sa baki sani ba?"
Shiru tayi kamar mai wani nazari kafin can yace,
"Koma ina ne sister zan nemosa"
"To idan kika samu yana da wacce yake so fa?"
"Sai ta haƙura ta barmun shi"
"Son kai ne fa wannan Adda, to idan ma yana da mata fa gaba ɗaya, ai kin ga ita bakyace ta haƙura ba ko?"
"Bana fatan haka Janan, amma idan ma hakan ta kasance sai nace ya rabu da ita ya aure ni"
"Taya?, Mutum da matar sa za kice ya rabu da ita ya aure ki? Ke dai ALLAH yasa cikinsu ko ɗaya ba ya da ita"
"Amin kam, don ko ana ruwa ana iska haɗe da kiɗa da bushe bushe wlh saina mallake sa, wai kuwa kin san yanda nake jin son sa kuwa?, Na rantse maki zan iya mutuwa idan ban samesa ba"
Zaro idanuwa Janan tayi haɗe da cewa,
"Subhanallahi Adda, ki dena faɗar hakan, ai rasa wata rayuwar acikin rayuwar mu bazai hana ci gaba da wanzuwar wata rayuwa ba, da kuwa yana hana wa ni dake da muka rasa mahaifiyar mu da bamu rayu ba, saboda haka kisa a ranki kamar yanda kike rayuwar ki a can da babu shi, haka ma yanzu koda baki samesa ba za kici gaba da rayuwar ki da yardar ALLAH, kiyi addu'a sosai akan ALLAH ya ƙaddara sake haɗuwar ku dashi cikin sauƙin kuma yasa yanda kike son sa shima yana sonki haka, nima kuma zan taya ki addu'a in sha ALLAH"
"Shikenan Janany sister na gode, muje muyi taking dinner na fara jin yunwa"
"Au! Ai na zata soyayyar unknown ɗin nan naki tasa kin ji kin ƙoshi?"
"Ke ko!" Nihal ta faɗa haɗe da sa hannu ta maƙalo wuyanta suka sa dariya tare, sai da sukayi sallar isham sannan suka sauko ƙasa suka ci abinci, suna ƙarewa Abba na dawowa duk suka miƙe a tare suka nufo wajen sa, hannu Janan ta fara miƙawa ta karɓi jikkarsa dake hannun ɗaya daga cikin guard ɗ'in sa dake biye dashi a baya sannan ta ɗan rissina tana yi masa sannu da zuwa, fuskarsa a sake ya amsa haɗe da buɗe mata hannu ta je ya rungumota kamar yanda ya yiwa Nihal tun iso warsu,
"My doter's how are you?"
"We're fine Abba i have a little gist for you" Nihal ta bashi amsa tana dariya har da ɗan tsallenta, dariya Janan itama tayi tana mamakin yanda Nihal bata iya ɓoyewa mahaifin nasu komai wanda ya shafi rayuwar ta, ba shi kaɗai ba hatta ita kanta Nihal bata iya ɓoye mata komai wanda ya dangance ta.
"Wow! Am happy, don da alama ko labarin meye ya saki farin ciki sosai, can't wait to hear it darling" sannan ya juyo ga Janan ya ce,
"What of you my dear, any gist?"
"No.. Abba" ta faɗa tana sunkuyar da kai.
"Ok bara naje na dubo auntyn ku bata jin daɗi sai na dawo abani labarin nasha, Janan kai mun jikkar a ɗaki ina zuwa kun ji"
"Ok Abba, ka gaisheta kafin muzo duba ta, ALLAH ya ƙara sauƙin" Janan ta faɗa, Nihal kuwa ɓata rai tayi haɗe da hayewa sama abin ta ba tare da ta ce komai ba,
Hakan yasa a gurguje Abban nasu ya fito ya nufi wani katafaren part acan gefe, inda ba kowa bace aciki face matarsa wacce mahaifiyar sa tasa ya aura bayan rasuwar mahaifiyar su Janan da shekara biyar wato hajia zainab, bazawara ce da yaranta biyu ALLAH yayiwa mijinta rasuwa, haƙuri da kaifin hankali irin nata yasa mahaifiyar Abba ta nema masa aurenta saboda ta kula masa da ƴaƴansa da ALLAH ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa sai aka ci rashin sa a da Abba baya son ta saboda 'yar gidan talakawa ce, ganin da yayi mahaifiyar sa ta kafe kai da fata har tana cewa yazo ya kwashe yaran sa bazata cigaba da riƙe masa su ba tunda yaƙi yin aure ya sa ya haƙura ya aure ta ba don ransa ya so ba, itama mutuncin da iyayenta keyi da hajiyar yasa tayi biyayya ta aure da da zuciya ɗaya badon wani abu nasa ba, tun da aka kai ta sam bata gaban sa, da ita da babu duka ɗaya awurin sa saboda part ɗin da aka kaita daban ba wanda yake ciki ba ya ajiyeta sai dai babu abun da ta nema ta rasa kama daga ci sha da kuma sutura, kulawar miji kaɗai ce ba ta samu, yaran sa kuma ya ajesu anan part ɗin farko da yake inda ya zauna da mahaifiyarsu ya kuma nemo mai aikin da zata riƙa kula masa da su wato madam florence, sannan ya yiwa hajia Zainab ƙwaƙƙwaran jan kunne akan babu ruwanta da yaransa, don baya son abunda zai haɗa ta dasu balle har ta cutar masa dasu, wannan dalilin yasa iya karta dasu idan sun haɗu a compound ɗin gidan ko kuma idan su da kansu sun shiga part ɗinta, duk da dai ba wani kasa fai suke shiga ba musamman Nihal, Janan ce kawai tun tana ƙarama take da ƙulahucin shiga, wanda kusan mafi aksarin ɗabi'un da take dasu za a iya cewa daga wajenta ta koya, Kasancewar hajia zainab mace mai haƙuri yasa har tayi shekaru kusan uku agidan babu wanda yasan halin da take ciki da mijin ta har sai da Madam florence ta je ta sanarwa da hajiar Abba, don matar akwai kirki da mutunci duk da ko zamanta ba musulmai ba kuma ya re, saboda tana ganin Abba kullum tare yake da yaran sa, hatta da daddare wani lokacin wajensa suke kwana in dai yana gari, bata taɓa ganin yabar part ɗin ba da sunan zuwa na hajia zainab shiyasa ta faɗa wa hajiar saboda kirkin ta, ran hajiarsa ya ɓaci sosai ta kirasa ta zazzage sa tare da yimasa faɗa da nasiha sosai akan abunda yayi bai kyauta ba, ta kuma ce tabbas idan bai gyara ba bata yafe masa haihuwar data yimasa ba sanin taurin kan da yake dashi, don kuwa itama tana da zafi sosai shi yasa ma ta iya magance wasu matsalolin na sa,
Wannan dalilin yasa ya fara kulata tare da sauke haƙƙinta na aure dake kansa, amma duk da haka babu abun da ya ɗauka na shi ya kai part ɗin ta, haka kuma matuƙar ba yana da buƙata da ita ba to fa bazaya taɓa zuwa part ɗin ta ba, yana inda yaran sa suke akoda yaushe kuma acan yake komai, ciki kuwa hadda kwana acan sashensa, zai iya shafe sati ko sati biyu bata saka shi a idanuwa ba, bai neme ta ba ita kuma bata neme sa ba, sau da dama takan ɗaya waya ta lalibi lambar wayar sa takira don gaishesa amma yaƙi ɗagawa, sai dai koma meye ta haƙura har sai lokacin daya buƙaci ganin ta ko ya je part ɗin don kan sa, haka take ta haƙurin zama dashi har aka kawo wannan lokacin, kuma sanin halinsa da tayi yasa wannan karon ma da bata jin daɗi bata bi ta kansa ba sai da hajiya ta kirata taji muryar ta ba dai dai ba sannan take sanar da ita bata jin daɗi, ita kuma ta kirasa ta faɗa masa halin da matarsa ke ciki tare da yi masa faɗa sosai akan halin ko inkula da yake yiwa iyalinsa, shine dalilin da yasa yana dawowa ya je dubota,
Nihal kuwa dama basa shiri da ita ko ɗaya, tun data tashi ta buɗe idonuwa ta ganta agidan ta tsaneta, musamman data tambayi grandma wace ce ita lokacin suna da shekara goma sha uku, ta ce mata matar ubansu ce kuma itace matsayin uwar su, sai ta ji ta ƙara tsanar ta, rashin son da take yi mata ya sa ko maganar ta bata so ayi tana kusa, ba kuma ta shiga duk wani abun da ya shafeta, sauƙin ta ɗaya bata fiye damuwa da duk wani abun da baya gaban ta ba, da tuni ta hana Janan zuwa part ɗin gaba ɗaya ko kuma shiga shirginta, rayuwar ta takeyi yanda take so haka kuma ba ruwanta da hana wani yayi tasa yanda yake so.
Koda Abba ya isa part ɗin kwance ya iskota tana fidda lumfashi ɗaya bayan ɗaya, ba tare daya zauna ba daga tsaye ya kalleta haɗe da cewa,
"Meke damun ki ne?" Kasa amsa masa tayi sai dai hawaye dake zarya a gefen idanuwanta, ɗan tsaki ya ja haɗe da ciro wayarsa a aljihu ya kira family doctor d'in su ya ce yazo yanzu yanzu yana nemansa gida, yana gama wayar ya kashe had'e da cewa,
"ALLAH ya sawaƙe, bari naje na watsa ruwa kafin Dr yazo" kai kawai ta iya ɗaga masa ba tare da ta samu cewa komai ba ya fice saboda yanda yaga Nihal ta ɓata rai dazai fito...
Pls #comment
#vote
#share
*ALLAH YA JIƘAN IYAYENMU👏😭*
[8/17, 7:39 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 10_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1232646055?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=v1lidYDTadGvF424bpMWoylSjWajIz1akGv7hQF4Tz%2F0wtkrLZXqXE9af1RdHS5AKzKWoPRtcUPS%2BriQifsEyJBoyKoTjuHKWnwRJa%2BHn3GLqQKt8jrr3WRzDEEc3Fl8_
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_
👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
______________________________
*K* oda ya koma bai shiga wankan ba har sai da ya kira Nihal ya ce ta sanar dashi abun da take son faɗa masa tare da cewa Madam florence ta kawo masa abinci,
Ba kunya Nihal ta kwashe duka labarin haɗuwar su da mm da irin son da take yi masa ta faɗa masa yana cin abincin yana dariya har ta gama, sai da ya kai spoon ɗin ƙarshe ya ture plate ɗin gefe tare da ciro tissue ya goge bakin sa sannan ya ce,
"Aaaa..lallai Nihal ɗita ta girma aure take so tunda har ta fara tunanin kawo mun mijin aure, to ya sunan shi surukin nawa sai naje naga mahaifinsa muyi magana don nasan bazaki taɓa kawo mun abunda ba na ƙwarai ba"
Da sauri Janan dake gefe zaune tana latsar wayarta tasa hannu ta toshe bakinta haɗe da gumtse dariyar dake son zo mata,
"Ka ganta ko Abba?, haka fa ɗazu ma ta azamun dariya daga bata labari" Nihal ta faɗa cike da shagwaɓa tana nunata kamar za tayi kuka, ita kuwa Janan abu ɗaya ne ya bata dariya shine da Abban su ke cewa wai zai je yaga mahaifinsa, abu sai kace garin indiyawa da dangin macce ke zuwa nemawa ƴaƴan su mata aure.
Ɗaure fuska Abba yayi haɗe da juyowa yana kallon Janan, irin kallon nan na ina wasa dake? Da sauri ta sadda kai ƙasa tana faɗin,
"Am sorry Abba" har zaiyi magana wayar sa dake gefen kujera ajiye ta hau ruri, Dr ne ya ƙaraso don haka yana ɗagawa ya ce,
"Kawuce part ɗin hajia Zainab ka duba ta, idan ka gama sai ka kirani" ɗagowo Janan tayi jin abunda mahaifin nata ke faɗa haɗe da girgiza kai ta miƙe cike da mamakin sa tana faɗin,
"Abba bari naje na duba aunty"
"To sekin dawo" kallon Nihal tayi da niyar cewa ta taso suje ta balla mata harara, hakan yasa kawai sai ta wuce ta biya ta kitchen madam Florence na tsaye tana wanke-wanke ta ce,
"Pls madam, ko zaki rakani na dubo aunty, she's not feeling well"
"Yeah! upcouse my dota, what happend with her?" ta fad'a tana tsantsame hannunta acikin ruwan wanke wanke tare da ciro towel ta goge,
"I don't no madam"
"Ayya lez go" ta faɗa tare da fitowa suka nufi part ɗin hajia Zainab,
Shi kuwa Abba tambayoyi ya shiga jehowa Nihal akan masoyin nata da tayi tozali dashi yau tana bashi amsa ba tare data ɓoye masa komai ba. Jinjina kai yayi haɗe da ɗago kai yana kallon ta ya ce,
"To shikenan, idan har kin sa mosa to ki sanar dani, kama daga kan single kobo har zuwa trillion naira zan kashe wajen ganin na aura maki shi matuƙar hakan zai saki farinciki"
Ta sowa tayi daga wajen zaman nata ta rungume sa haɗe da cewa,
"Thank you so much Abba, shiyasa kullum nake alfahari dakai"
"Me too am proud of you" ya faɗa tare da miƙewa ya wuce sashensa ita kuma ta koma ɗakin ta sama abin ta,
Har kusan ƙarfe sha ɗaya likita na gidan yana duba Hajiya zainab, inda yayi mata gwaje gwaje da allurai ya haƙa mata drip ɗin ruwa, da ƙyar ta samu ALLAH ya taimaka tayi bacci sannan ya haɗa kayansa yana ƙoƙarin tafiya zuciyarsa cike da tausayin ta, ko ba a faɗa wa mutum ba yana kallon Hajiya Zainab yasan tana da damuwa duk da duban tarin arziƙin da take ciki, wayarsa ya kira yana ƙoƙarin kiran Abba sai gashi ya shigo saye da jallabiya alamun har yayi wanka ya huta,
Hannu ya miƙa masa suka fara gaisawa kafin nan ya tambayesa meke damun ta, sai da Dr Bilal ya cire glasses ɗin idonsa sannan ya kallesa ya ce,
"A gaskiya jinin ta ne ke son hawa, ga kuma ciwon zuciya a gefe, matuƙar ana son dakatar da faruwar hakan dole a bincike ta aji ko meye ke damunta, aji wace irin damuwa ce haka ta saka a zuciyarta dake neman illata ta a kuma yi magani ta"
Shiru Abba ɗaya zuba gaba ɗaya hannayensa cikin aljihu yayi kafin ya ce,
"Wannan kaɗai ne matsalar?"
"Eh kusan haka dai, ga wannan takardar magani ce da zata riƙa sha, matuƙar an kiyaye sha shi cikin lokaci da kuma tsari shima zai taimaka in sha ALLAH"
Karɓar takardar yayi haɗe da bashi hannu ya ce,
"Na gode likita, zaka ga saƙona in sha ALLAH"
"Ok sai da safe"
Yana fita Abba ya jawo waya ya rubuce maganukkan ya tura inda yake karɓar magani yace akawo masa yanzu sannan ya fita ya zauna akan block ɗin dake zagaye da round about ɗin dake tsakiyar harabar gidan yana jiran isowar mai kawo sauƙin maganin, ba a fi mintuna goma ba sai gashi ya iso aka buɗe masa gare ɗin ya shigo ya gaisheshi tare da bashi ledar maganin sannan ya wuce,
Abba bai tashi ba sai daya turawa Dr kuɗin sa da kuma na maganin da aka kawo masa yanzu sannan ya miƙe ya koma part ɗin, har lokacin Janan da Madam florence na ciki zaune, tashi suka yi da zimmar fita ya tsaida Madam florence haɗe da miƙa mata ledar maganin ya ce ta zauna ta kwana tare da ita har zuwa gobe sannan ta tabbatar idan ta farka tasha maganukkan, ta russuna ta karɓa haɗe da cewa,
"Ok sir, by God i will"
"Thank you"
"Thank you sir God night" ta faɗa cike da mamaki gal azuciyarta, sam batayi tsammanin irin condition ɗin da aka ce hajia Zainab na ciki ba Alhaji zai iya komawa part ɗinsa ya kwana, a zahiri kuwa bayan ya fice cewa tayi,
"Ha'a! alaji this is not Good fa, she's you wife, you have to show some mercy and care to her, why naa.." ta ƙare maganar hannayenta na saman cikinta tare da juyawa tan kallon Hajiya Zainab dake kwance tana bacci.
Ita kanta Janan bata ji daɗin baro part ɗin da mahaifinta yayi ba, ko ba komai ita ɗin matar sa ce kuma tana da tarin mabanbanta haƙƙoƙinta akansa, ALLAH ya kyauta ta faɗa acikin zuciyar ta tare da hayewa sama, don ta soma jin bacci.
***. ***. ***.
A ɓangaren su mm kuwa suna isa gida tun daga bakin ƙofa da Razina ta hango Jabir ta fara labarta masa abun da ya faru a supermarket, daga Momy har Jabir babu wanda ya tsaya bin takan su kasancewar an fara kiraye-kirayen sallah suka wuce ciki abinsu, sai da tagama faɗa masa komai yayi gyaran murya haɗe da cewa,
"Manta da ita tunda ba tayi gangancin taɓa mana 'yar ƙanwa ba, da yau ina tabbatar maki da sai ta san ɗan jaki dukiya ne, yanzu kije ki watsa ruwa, shi kuma yaya Muhriz ɗin banni dashi"
Wani irin ƙayataccen murmushi ta saki da saida ya dakar masa zuciya tabar wajen cike da farin ciki tana tsallen jin daɗi, girgiza kai yayi haɗe da furzar da wani irin fuska a baki yana gwalo idanuwa, murmushi ne ya kucce masa yayi saurin dukan gefen kansa yana faɗin,
"Meye haka yaya, dawo a gayyaci ka mana"
Yana zaune a ƙofar gidan mm ya fito yana gyara hannun rigar sa da alama arwala ya yo, kallo ɗaya yayi masa ya ɗauke kai haɗe da cewa,
"Muje masallaci ko?"
Tare suka tafi suka dawo lokacin Momy ta gama sallah ta sa Razina ta shirya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 40