san ko waye mm da kuma matsayin sa, mutane ire-iren ku su suka sakasa ɓoyayyiyar baiwar sa kasa bayyana, amma ni dana san abuna na kuma san ko shi waye ina son sa a haka" dariya Nihal ta kece da ita har tana riƙe ciki kafin tace,
"Ɓoyayyiyar baiwa? Ta me kenan?, Saida dabino ko kuma talaucin da yake fama dashi? Look Janany, ki buɗe idanuwanki ki fuskanci arziƙin ki, tun farko na faɗa maki bazan taɓa goyon bayan zuwa ki jefa kanki cikin ƙangin bauta ba"
"Alƙawarin ki fa?"
"Nayi ne don faranta zuciyar ki a lokacin amma taya zakiyi tunanin zan bari ki faɗa wa rayuwar talauci bayan babu abunda nafi tsana aduniya sama da ita?"
"Tabbas kuwa kin cutar dani kuma kin yaudarar ni yaudara mafi girma a rayuwa, a yau na ƙara yarda cewa kama da wane bata taɓa zama wane, a kullum safiya ina yimaki kallon mahaifiya ta dana rasa, a wani ɓangaren kuma ƴar uwa rabin jiki da zata riƙa share mun hawaye aduk lokacin da sukayi kwaranya, ashe ba haka bane kuskure nake ta tafkawa acikin duhun dana rasa mai haskamun gabana balle na gano daidai, a yanzu kam na yarda cewa kowa zai iya cutar dakai aduniya ciki har da jinin jikin ka, wani ɓangare ɗaya ne acikin mutane da bazai iya aikata hakan ba wato mahaifiya, gashi ni narasa wannan ɓangaren tun kafin nasan ko waye ni, na roƙeki don ALLAH ki tashi ki tafi bana son ganin ki gaba ɗaya" ta haɗe hannayen ta waje ɗaya tana riƙon ta,
"Zan tafi Janan amma idan hankalinki ya gushe ne kiyi ƙoƙarin dawo dashi a jikin ki, sauke kayan ka bai taɓa zama sauke mu raba ba, tunanin kuma da kikeyi akaina ki janyesa domin ni gaskiya na faɗa maki, mm ba right man ɗinki bane wether you like or not.." cikin kukan data kasa dakatar da kanta tun ɗazu ta daka mata wata irin tsawar da ita kanta bata san ma tayi ba tana faɗin,
"Ki fice mun nace bana son ganin ki Adda" ɗage kafaɗu tayi haɗe da miƙewa tana faɗin,
"Anyway, kidai sawa ran ki salama kidena wannan kukan haka don Abba bazai taɓa sauya magana ba"
"Saboda ba halittar sa akayi ba kuma baida zuciya a ƙirjin sa?"
"Ko ɗaya, saboda dai haihuwar ki yayi bake kika haifesa ba, don haka kima ɗauka aure ya ɗauru"
"Ta ALLAH ba taki ba domin dashi ne na dogara"
Irin ko oho ɗin nan ke kika sani Nihal tayi da hannuwa tare da ficewa abunta daga ɗakin, jin tayi hawayen idanuwanta sun ƙafe ta bita da wani irin kallo cike da mamakin wai anya Adda ɗin tace dake nuna mata tafi sonta fiye da kuwa, take nuna ta damu da ita fiye da kowa aduniya?, Anya itace yau ke nuna mata ko oho da lamarin ta saboda abun duniya, lallai rayuwar duniya ba tada amana, kai dai kawai ka kalli mutum ko waye shi,
Abba kuwa har aka kwana biyu ya rasa ta yanda zai tun kari ambassador Hussain da maganar gashi kwana ɗaya ya rage Hajiya ta sake waiwayo sa da maganar, cike da damuwa ya kira Nihal a waya ya ce ta samesa a ɗakinsa, bayan ta shiga ta zauna ya kalleta haɗe da cewa,
"Duk duniya in kuka cire Hajiya ba nida wasu sama daku Nihal, gaba ɗaya na ƙare rayuwata wa neman abunda zai inganta maku rayuwa, amma ki dubi yanda ƴar uwarki ke naman tozarta ni a idanuwan duniya, fasa auren nan daidai yake da tonuwar asirina, gashi ta saka Hajiya a wannan maganar kuma na tabbata bazata taɓa bari ayi wannan auren ba indai ba ita tace ta hanƙura ta amince ba, wlh narasa yanda zanyi" ya ƙare zancen tare da fashewa da kuka, shiru Nihal tayi tana jin zafin kukan mahaifin nata har cikin ranta, ta rasa meke damun Janan data kasa banbance arziƙi da kuma rashi da har ta nace wa mm, sai da tayi ajiyar zuciya sannan ta kalli mahaifin nata haɗe da cewa,
"To yanzu menene mafita Abba?" Kamo hannuwanta yayi da sauri ya riƙe cikin nasa tare da ɗorawa akan goshin sa,
"Nihal so nake ki fiddani wannan abun kunyar ki amince ki auri Asgar a maimakon Janan.."
Kafin yarufe baki ta kwace hannunta haɗe da matse fuska, ta ce
"Kamar ya Abba? Ban gane ba?"
"Ina nufin ke ki auri Asgar...."
"Ya isa haka Abba, wannan wane irin sabbatu ne kakeyi haka?, Ina kasan wanda nake so kuma nake burin rayuwa dashi, ka kuma san alƙawarin da kayi mani akan sa, taya yanzu kuma zaka bijiro mani da wani zance haka?, Noo...bazan iya ba domin ni Asgar baya ɗaya daga cikin irin mazajen da nake so, kawai a nemi wata mafitar amma wannan batayi ba"
"Haba Nihal, kada ki bari a goranta mani, koda tuna Asgar nada kuɗi haka ma mahaifin sa, aurensa ba ƙaramar daraja da kima zai jawo maki ba har ma dani kaina, ke kaɗai ce last hope ɗina da zan iya kuɓutar da kaina daga tozarci da wulaƙanta a fuskokin mutane"
"But Abba ba fa ni yake so ba, taya zan yarda in auresa, be side kamar ni bazan taɓa amincewa da auren musaya ko kuma huce haushi ba"
"Wani zakiyi Nihal don ALLAH don annabi, nayi maki alƙawarin duk randa muka samo wanda kike so da kaina zan warware auren kamar yanda na ɗaura shi"
Shiru tayi tana wani nazari aranta kafin tace,
"Shikenan Abba, ka tabbata zaka cika alƙawarin warware auren aduk lokacin dana samo zaɓi na?" Da sauri ya riƙe hannun ta haɗe da cewa "Na tabbata sweetheart, ke kin sani ban taɓa alƙawari na saɓa ba, shiyasa ma nake son ke ki amince da auren Asgar tunda na riga da nayi masa alƙawarin bashi ƴata ya aura"
"To amma fa a bisa sharaɗi ɗaya abba"
"Ki faɗa ko meye sharaɗin ki na amince"
"Zan aure sa ne kaɗai idan har za a ɗaura auren mu rana ɗaya da Janan, idan kuma ba haka ba tofa sai dai a ɗaura auren da ita ba ni ba, zaka iya faɗa mata wannan sharaɗin idan har ta amince shikenan nima na amince"
"Ban fahimceki ba Nihal"
"Abunda nake nufi Abba tunda Janan taƙi amincewa da zaɓin ka to kaima ka nuna mata cewa baza ka amince da nata ba sai bisa sharaɗi ɗaya, sharaɗin kuwa shine ta tura wanda take so a ɗaura auren mu rana ɗaya idan ba haka ba kuma dole auren ya kasance da ita za a ɗaura bani ba"
"Nihal kenan, to menene hikimar yin hakan?"
"Yawwa Abba, kai kasan hidimar aure ba abu bane mai sauƙi, kuma kasan wanda take so ba yada halin yin aure don ko lalurar kansa ta ishesa, bai aje ba bai kuma bawa wani ajiya ba, a sali ma dabino yake talla, kaga kuwa abune mai wahala ba garesa ba ko wuɗan da suka ɗan fisa rufin asiri ace su fito lokaci ɗaya a ɗaura aure, wlh ko ana saura sati biyu ne aka ce ya turo bazai iya ba saboda lokaci ya ƙaru balle kuma ace kwanaki biyar, idan har ya kasa turowa cikin kwanakin da akace to dole Janan zata haƙura ta auri zaɓin ka kaga shikenan an huta dayin musanya"
"Wow, wow...gaskiya kin kawo shawara mai kyau Nihal, dama kina da wannan tunani akan ki naje ina ta wahalda kaina?, Indai wannan shine sharaɗin naki na amince kar ki wani samu damuwa, kuma zan tabbatar nayi duk yanda ya dace wajen ganin na yanda muke so ya tabbata, God bless you"
"Amin Abba" ta faɗa tana murmushin mugunta don tayi hakan ne saboda a tunanin ta ko ana ha maza ha mata mm bazai iya auren Janan adaidai wannan gaɓar ba don bayada halin yin hakan, a ta wata fuskar kuma ta amince zata auri Asgar ne badon ta damu da auren ba sai don tayi amfani da wannan damar itama ta tara nata abun duniya kamar yanda akoda yaushe take mafarki na mallakar manyan gidaje, motoci da kuma manyan shaguna da zata dinga business aciki, ta yanda itama zata shiga sahun jerin manyan mata da aka sani kuma ya zamana sunan da za tayi sai ya shallake na mahaifin ta ba anan ƙasar ba har ma a ƙasashen duniya baki ɗaya, so take yi taci arziƙi ta kuma juya arziƙi yanda ranta ke so, alokacin ne zata bazama uwa duniya ta nemo farincikin ta da take mafarkin mallaka akoda yaushe, don haka duk wanda ya faru cikin biyun nan a shirye take kuma tana maraba dashi,
Washe gari tun misalin ƙarfe tara Hajiya tasa driven ta ya kawo ta gidan, fuskar nan tata babu alamun walwala ko farinciki a tattare da ita don karma yaga damarta, part ɗin Hajiya zee ta fara sauka suka gaisa bayan sun ɗan taɓa fira har tana tambayar ta yaushe yaron ta dake karatu India zai dawo ta ce, ai da ya ce nan da watanni biyu zai dawo amma saboda akwai wani course da yayi yake jiran karɓar certificate ɗin sa sai ya ƙara wata ɗaya tukuna, addu'a Hajiya tayita yi masa tare da fatan ALLAH ya dawo dashi lafiya sannan ta miƙe ta nufi part ɗin su dady, tana shiga yana ƙoƙarin fitawo don bai yi tsammanin zata zo gidan ba adaidai wannan lokacin, a tsammanin sa ma kiransa za tayi tace ya sameta acan gida, hankalin sa kwance ya tarbeta don ya gama amincewa da shawarar Nihal, bayan ta zauna ya gaisheta cikin girmamawa tare da cewa,
"Hajiya kika ƙi kirana, ai da sai nazo da kaina na sameki acan"
"Ba wannan nake son ji ba, ka kira su sun karɓi kayan su ko kuwa?"
"A a Hajiya, amma dai na janye batun aura mata shi matuƙar shi wanda take son zai fito a ɗaura dashi a lokacin dana tsara, wannan shine sharaɗina, idan ta amince shikenan sai ta faɗa masa ya turo iyayen sa"
"Kaga Usman karka maida ni ƙaramar yarinya, a ina aka taɓa yin hakan lokaci ɗaya ace yaro ya fito za a ɗaura masa aure?, Ai ko yanada hali baza a rasa ƴan shire shiren da yake buƙatar shima yayi ba, wannan irin abu sai kace ka gaji da yarinyar nan, to ni ban amince ba kuma dole ko kana so ko baka so ta aure sa tunda shi take so.."
"Hajiya na amince, zance ya turo ɗin ko da a kango ne zai kaini ya ajiye idan an ɗaura auren" suka jiyo Muryar Janan dake saukowa daga upstairs zata tafi makaranta wajen jarabawa ta faɗa, juyowa sukayi atare suna kallonta cike da mamaki har ta ƙaraso wajen, cikin girmamawa ta duƙa ta gaida mahaifin nata daya ɗauke kai ya juyar gefe, sannan ta juyo tana ɗauke guntayen hawayen da suka sauko mata da yatsa ta gaida Hajiya dake sake ƙare mata kallo cike da tausayin yanda taga duk ta fa ɗa, dafa kanta Hajiya tayi tamkar wacce zatayi kuka haɗe da cewa,
"Lafiya klw Janan, kiyi haƙuri da wannan jarabawar in sha ALLAH sai kin bada labari, amma gani nakeyi tamkar anƙure Muhammadu idan akace za a ɗaura wannan aure yanzu, duk da ba laifi naga ALLAH ya wadata ba kamar da ba"
"Ba komai Hajiya, nasan zai amince, aure kuma ai ALLAH ke lalura shi zai rufa asiri"
"Haka ne, yau she zaku ƙare jarabawar?"
"Jibi in sha ALLAH"
"Hakan na nufin wani sati kenan fa"
"Eh Hajiya na amince" ta faɗa tana kallon mahaifin nata daya tsuke fuska,
"To shikenan tashi ki tafi ALLAH ya bada sa'a ya kuma yi maki albarka"
"Amin Hajiya" ta ƙare zancen tana faɗin "Abba na tafi" banza yayi da ita har saida Hajia ta ce,
"Tana magana ko baka ji ne"
"Hajiya me zan ce mata tunda ni dai ban isa gareta ba"
Ita dai Janan dama tuni tayi gaba hawaye na sauko mata, Hajia kuwa rufesa tayi da faɗa saboda yanda ranta yaɓaci haɗe da cewa,
"Wallahi Usman idan baka gyara tsakanin ka da yarinyar nan ba haƙƙinta bazai taɓa barin ka ka zauna lafiya ba, wannan tsana da ƙiyayya haka har ina, sai kace tsintota kayi ba haihuwar taba, to da wannan masifar ai ƙara tayi auren taje ta samu sauyin rayuwa ga wanda ke sonta kuma yake ƙaunar ta ko ta samu farincikin da ka kasa bata a matsayinka na mahaifinta"
Janan kuwa kasa tada motar tayi saboda yanda kuka yaci ƙarfin ta, sai da tayi mai isar ta gama sannan ta share hawaye haɗe da tada motar tabar gidan, tana fitowa taga mm tsaye a bakin gate ɗin yana ƙoƙarin kiranta a waya, saboda tun da asuba yake kiran wayarta bata shiga saboda gaba ɗaya ta manta jiya bata saka caji ba, to shine fa hankalinsa ya tashi ya biyo sawun ta saboda ta sanar dashi duk abunda ke faru, na yau kaɗai ne ya rage mata ta sanar masa, a hankali ta taka burki tayi parking a gefe tare da saukar da glass ɗin motar tana mai ƙaƙaro murmushin ƙarfin hali ta sakar masa....
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 53_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
***********
_https://www.wattpad.com/1259629415?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=erYTLedawma3HhdUzjI4OdwNdsDmvItB9CI8RbPJeo%2B2AhQk%2BNG8vfm4qu2EJ3I9pG3fA%2BsCkiqf6TlxAOMsMl9tUHiWNfNAgV%2FFvdPxe%2Bm5em8vtAua1NNvDeb870VU_
______________________________
Cike da damuwa yake kallon cikin idanuwan ta yana ƙare mata kallo ganin yanda ta zabge cikin kwanaki uku, ganin hawaye na ƙoƙarin zubo mata tunawa da abubuwan da suka faru ya sata saurin sadda kai ƙasa,
"Me nene?" Ya faɗa cikin taushin murya har lokacin idanuwansa na kanta,
"Kayi haƙuri mm na yanke hukuncin da ban sani ba ko zai yi maka daɗi arai saboda samawa kaina mafita"
"Janan kowane irin hukunci zaki yanke tsakanin ni dake bazan taɓa jin kinyi ba daidai ba balle har kiyi tunanin zaki bani haƙuri saboda raina ya ɓaci, koma meye ni yanzu ba shine damuwata ba, wannan yanayin da nake kallon tki aciki shine babbar damuwata da kuma tashin hankalina, ki faɗamun me yake faruwa kuma?"
"Abba ya samani sharaɗi akan cewa bazai janye zancen ɗaura mani aure ba har sai ka turo iyayen ka anyi magana dasu, ba tare da naji ta bakinka ba na amince da hakan kuma nasan..." wata irin dariya ya kwashe da ita kafin tarufe baki haɗe da cewa,
"Sabida wannan zaki zubar mani da waɗan nan tsadaddin hawayen nan naki? Common...ba ke kaɗai ba har ni na amince da wannan sharaɗin, sai me kuma?" ya kafeta da idanuwa yana kallo ganin yanda ta saki ido itama tana kallonsa cike da mamaki, matso da fuskar sa yayi saiti da tata haɗe da hura mata iskan bakinsa ta wani lumshe idanuwa ta buɗe su akansa, sai da ya yi murmushi haɗe dasa yatsa ya ɗauke mata hawayen dake kwance akan fuskar tata yana cewa,
"Kin ga, taimaka ki tada motar nan mu tafi kafin lokaci ya ƙare, ba kince sha biyu zaku shiga exam ba?"
"Eh"
"To duba agogon motar ki ki gani kwata to 12, ki kwantar da hankalin ki, indai zancen turowa ne ki ɗauka anyi angama"
Cikin jin daɗi tayi murmushi haɗe da tada motar tabar wajen, tafe suke mm na tunanin ta wace fuska zai je ga mahaifinta, zai je a irin fuskar da yake buƙata ne ko kuma zai je ne da fuskar daya alƙawarta cewa zai auri Janan da ita tun farko, ƴar gyaran murya Janan tayi ganin ya faɗa duniyar tunani haɗe da cewa,
"Dama nasan abun zai zamo ma damuwa saboda ba lallene ka shiryawa aurena yanzu ba, amma ina so ka sani ni kai nake so don haka ban damu dako ina zaka ajiye ni ba, a ɗakin da kake kwana ne ko agidan haya duka bai dameni ba, sadaki ma idan baka da hali zan iya biya make da kaina ko na yafe maka gaba ɗaya idan kana buƙata, muradi na kawai ka tura saboda hakan kaɗai zai dakatar da wancan zancen, sauran lamarin kuma sai mu barwa ALLAH domin shika lalura" duk wannan maganar da takeyi a natse hankalinta na akan titi har takai aya tare da juyowa tana kallon fuskarsa, suna haɗa idanuwa ta ɗaga masa hira alamar tambaya, girgiza kai kawai yayi tare da maida hankalin sa akan titi shima kafin can yace, "Ajiye ni anan" ganin sun ƙara so bakin gate ɗin makarantar,
"Ai nazata zaka rakani ne ka jira har mu ƙare sai mutafi gidan grandma"
"Saboda gani mijin Hajiya ko?"
"Laaa..ba haka nake nufi ba, 12 zamu shiga, kuma na tabbata zuwa 1, ko 1:30 na gama, kaga kenan ba wani jimawa zamuyi ba tunda paper ɗaya ce shiyasa kaji na faɗi haka"
"Tab..to ni ai awar nan ɗaya ko ɗaya da rabi da kike zacen na zauna jiranki a tsammanina lokacin ai na kai caranci ko kuma na kusa kaiwa"
"Ban fahimta ba?"
"Janan kenan, ai yau ɗin nan dole naje na sanar da Baffa Ali halin da ake ciki, ina barin nan gida kaɗai zan shiga na sanar da Momy sai na ɗau hanya in sha ALLAH, Ai bazan yi wasa da wannan damar da zata saka ki zamowa mallakina ba" sinne kai tayi ba tare da ta ce komai ba tana mai jin wani irin farinciki da kunya lokaci ɗaya sun rufeta,
"Ki kula mani da kanki kafin na dawo" ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe motar ya fita don kar ya tsaya ɓata wani lokacin gashi itama sun kusa shiga exam, ɗago kai tayi haɗe da cewa
"Shikenan hubbin raina, ALLAH ya kaika lafiya kuma yasa ka dawo lafiya"
"Amin yallaɓiyata" ya faɗa yana murmushi haɗe da buɗe ƙofar ya fita, ji tayi tmkr ta dakatar dashi daga zuwan saboda tana buƙatar kasantuwa atare dashi a ƴan kwanakin nan, amma saboda tafiyar tasa itace samun kwanciyar hankalinta da natsuwa dole ta haƙura ta bar sa ya tafi, bata bar wajen ba har sai da taga ya tari mai mashin ya hau ya wuce sannan itama ta tayar da motar tata ta shige cikin makarantar tasu,
Abba kuwa duk inda ransa yake in yayi dubu ya gama ɓaci, bai taɓa tsammanin cewa Janan zata amince da sharaɗin sa ba sai gashi tun kafin a tambayeta ta amince, wani irin ɗaci da tuƙuƙi ya riƙa ji azuciyar sa har Hajiya ta gama faɗanta ta wuce ba tare daya koma cewa uffan ba,
Wayar sa ya ciro daga cikin aljihu ya kira lambar ambassador Hussain, bayan ya ɗaga sun gaisa ya shiga yimasa bayanin halin da ake ciki cikin marairaice murya tare da ƙasƙantar da kai, inda ya nuna masa cewa Hajiya ce bata son auren gaba ɗaya, sosai ran ambassador Hussain ya ɓaci ya dinga masifa a waya, inda yake shiga ba nan yake fita ba akan Abba bai isa ya walaƙanta sa ba don shi gaba ɗaya ma ya gama raba invitation a can ƙasar tare da gayyatar manya manyan baƙin sa da mutanen arziƙi, yanzu haka anfara sanarwar auren a gidajen yaɗa labarai na talabijin da redio, shine don ya maida shi ƙaramin mutum zai ce wai yarinya bata so mahaifiyar sa ta hana, to ya yake so yayi da mutanen daya gayyata, shi dai Abba banda haƙuri babu abunda yake basa, wani irin tsaki ya ja tare da cewa ya kunna tv yanzun nan ya kamo tashar nagarta dake can ƙasar Ethiopia, ba musu Abba ya kira Madam florence ya ce ta miƙo masa remote kuma ta kunna masa tv, yana kamo channel ɗin ya ga ana hasko katin sanarwar auren, kamar jira ambassador Hussaina keyi yagama kallon sanarwar ya sake kiransa a waya haɗe da cewa,
"Ya kake so muyi da wannan kuma me kake so na faɗawa mutanen dana gayyata?"
Nan Abba ya shiga yimasa bayanin cewa idan har sun amince Nihal ta yarda zata maye gurbin ƴar uwar tata, shiyasa ma ya kirasa saboda a sanar da Asgar da wuri idan ya amince, ambassador Hussain mutum ne dake da son harkar girma, duk abunda zai jawo zube war mutuncin sa sam baya so, wanda jin ya sa sai da Abba yayi da gaske ya amince da hakan, a tunanin sa da afasa auren gaba ɗaya yaji kunya ƙara ya amince da musayar, duk da yasan ba lallai ne Asgar ya amince ba amma dole hakan shi za a yi don tseratar dakai daga abun kunya, ya kuma yanke shawarar bazai sbari Asgar yasan da wannan zancen ba har sai bayan an ɗaura auren don gudun kada ya jawo wata matsalar shima, zai sa a turasa wani aiki mai muhimmanci a wannan ranar da zata hanasa zuwa ɗaurin auren balle ma yasan da wa aka ɗaura auren, shiru ya yi yana sake nazarin abubuwan da zuciyar tasa ke kitsa masa akan wannan sabon al'amarin da aminin nasa ya bijiro masa dashi, yayin da shi kuma Abba sai faman ma giya yake yimasa haɗe da basa haƙuri, a tunanin sa fushi ne ya yi shiyasa ya yi masa shiru,g
"Is ok, na amince, amma kada ka sanarwa da Asgar halin da ake ciki, ni zan sanar dashi da kaina, sannan ina so aci gaba da shirye shiryen yanda muka tsara ba tare da an sauya komai ba saboda bana so ya fahimci komai shima"
"In sha ALLAH ambassador haka za a yi"
Da hak duk katse wayar Abba bakin wani sanyi a gefen zuciyar sa da ALLAH yasa ambassador ya amince da zancen yayin daya ɗauki alwashin sai ya nunawa Janan kuskuren ta matuƙar yana raye,
*** *** ***
Cike da farinciki mm ya samu Momy ya sanar da ita halin da ake ciki haɗe da faɗa mata cewa yanzu haka kan hanya yake don so yake yau ɗin nan yaje ya sanar da Baffa Ali komai, addu'a Momy tayi masa don hakan ba ƙaramin daɗi itama yayi mata ba tare da fatar yaje lafiya ya dawo lafiya, Razina na jin zancen tafiyar ta aza rigima itama babu inda zai je ya barta, ya so hanata amma Momy ta ce ya tafi da ita ba komai ALLAH ya kaisu lafiya, kafin su gama haɗa ƴan kayan su su shirya tuni Jabir shima ya gama haɗa nasa ya je ya fiddo mota ya goge ya tsaya jiran fitowar su, zaro idanuwa mm ya yi ganinsa cikin shiri shima, kafin yace wani abu Jabir ya shige gidan driver yana faɗin,
"Dallah malam ka shigo in zakaga shigo lokaci na ƙurewa, in kuma bazaka shigo ba kawai baby na ta shigo kai kuma ka zauna a baya"
"Wait, ban fahimta ba ina zaka je?"
"Inda ƙafa ke zuwa" ya bashi amsa tare da jan marfin gefen sa ya rufe, juyowa ya yi ya kalli Momy haɗe da cewa,
"Momy dubesa, ki faɗa masa ya fito so nake mu wuce lokaci na tafiya"
Saukar da glass ɗin motar ya yi tare da cewa,
"Na rantse babu inda zan fito malam, shikenan kai ba kada aiki sai ɗauke mani mata ka tsiri tafiye-tafiye da ita don ka raina Mani da wayo, to wannan karon ƙafata ƙafarta, nima zan je gaida dangi tare da neman iri"
"Mtsss..ka fiye wasa JB, idan muka tafi duka awajen wa za mubar Momy"
"A wajen ALLAH mana, da can mu muke tsare ta ne ba shi ba, malam kawai ka shigo mutafi ba abunda Momy zata ce"
"Momy..." Mm ya faɗa yana kallonta kamr zai yi kuka tayi masa murmushi haɗe da lumshe idanuwanta ta buɗe alamun yaje su tafi, tunɓuke fuska yayi kamar zai yi kuka haɗe da cewa,
"But Momy bana son dukan mu mutafi mu barki" tana dariya ta kalli Jabir sannan ta maido kallonta ga mm ta ce,
"To ya kake so nayi, kafi kowa sanin halin rigimar abokin naka, tunda kaji ya rantse babu indai zai je kawai ka haƙura ku tafi, ALLAH ya tsare hanya yasa ku dawo lafiya, duk ina gishe da su Baffa sosai da sosai"
"Zasu ji in sha ALLAH Momy tunda kin ɗaure masa" ya ƙare zancen tare da ma ka masa harara, dariya Jabir yayi haɗe da tada motar, hakan yasa Razina dake tsaye gefen Momy itama tana dariyar ƴan uwan nata ta rungume ta tana faɗin,
"Bye mom, gonna miss you"
"Me too my dear, wish you safe trip"
"Prayerd so" ta faɗa sannan ta sake ta haɗe da jan ɗan ƙaramin akwatin data shirya kayan ta aciki ta wuce ta shiga motar shi kuma ya ja suka fice yana ɗagawa Momy hannu, girgiza kai kawai tayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 40