inda take zaune,
"Ban fahimceki ba Amira, taya kike tunanin zan zamo silar faɗawarki cikin irin wannan mummunan yanayin, kin ga tashi muje class koma meye mayi magana acan" ta ƙare zancen tare da miƙa hannu da nufin riƙota, tasa hannu bibbiyu ta tureta da ƙarfi har sai da ta faɗi ƙasa kanta ya bugi wani dutsi dake wajen ta saki wata irin azaba biyar ƙara saboda azabar buguwar da tayi, da gudu mm ya rugo haɗe da ɗurƙusawa a daidai saiti kan Janan daya fara zubar da jini, cikin ɓaci rai ya ɗari kai yana kallon Amira dake tsaye tana murmushin jin daɗin yanayin da Janan ke ciki, ba tare data ankara ba taji an ɗauke ta wasu irin zafafan maruka guda biyu da har sai da suka kusa sa ta dena gani, cike da mamaki ta dafe kunci tana kallon mm da idanuwan sa gaba ɗaya suka sauya sukayi jajir saboda tsananin ɓacin rai,
"Ke wace iri yar dabba ce da ba ta da hankali kuma bata san abunda ya dace ba" ya faɗa yana nuna ta da hannu,
"Koma me zaka kirani mm ka kira ni ba kada laifi, amma ina so ka sani ita ya kamata ka kira da dabba wacce bata san me abunda ya dace ba ba ni ba, kuma ina so ka sani wlh in akwai abunda yafi hakan ma zan iya yiwa Janan saboda mafiya amana ce da bata san me ake kira tare ba, ba kuma tasan cewa ana barin halas don kunya ba"
"Amma meye nayi maki da na cancanci ki wulaƙantani haka agaban mutane, har kina kirana da maciyiya amana, amanar me naci maki Amira da bazaki iya faɗa mun daga ni sai ke ba har sai kin yi hakan a bainar jama'a" Janan dake ƙoƙarin miƙewa ta daɗi hakan cikin ƙarfin hali tare da dafe saiti inda ta bugu akai, tangal tangal tayi kamar zata daɗi da sauri mm ya miƙa hannu zai riƙota tayi saurin ɗaya masa nata hannun haɗe da cewa,
"Is ok mm, nagode"
Cikin zafin rai Amira taja wani irin dogon tsaki haɗe da cewa,
"Ba dai mm ba? Gaki nan ga shi, na rantse maki da ALLAH yanda kika rabani dashi kema sai na rabaki dashi har lahira, ba zaki taɓa samun farinciki ba dake har shi tunda har ya iya ɗaga hannu ya mare ni akan ki, banza kawai shashasha wacce bata ramen kanta sai na wani" sannan ta juyo tana kallon mm da mamaki ya gama kashesa ta ci gaba da cewa, "kai kuma ka sani ko kana so ko baka so kai ɗin mallaki na ne ni kaɗai, idan ma mafarki kakeyi to ka farka, Amira itace masoyiyar ka kuma wacce ta dace da rayuwar ka, tun da kafara zuwa makarantar nan zuciyata taji babu wanda take so sai kai kaɗai, babu hanyar da ban bi ba wajen nuna maka soyayya tare da tura saƙwanni kai tsaye daga zuciyata zuwa taka amma kayi kamar baka san ina yi ba, kawai don cin amana sai kuka zagaya kai da ƙawata kuka ƙalla soyayya, to wlh baka isa kaso wata macce aduniya bayan ni ba, kaji ma na faɗa maka don haka mu zuba mu gani ni da kai" takai zancen tana nuna idanuwan ta da yatsu biyu tare da nashi, kafin ma ta ƙara sa ake hannun taji an shaƙo wuyanta haɗe da danganeta a jikin iccen dake bayanta, cikin kakarin mutuwa take kallon idanuwansa da sukayi jajir tamkar an watsa masu barkono yana faɗin,
"Uban waye kikewa gargaɗi haka?, Na taɓa cewa ina sonki ko wata magana makamanciyar haka ta taɓa haɗani dake da zaki ce anci amanarki?, To bari kiji, yanzu zuciyata ta fara son Janan, kuma har na mutu bazan dena ba, itace rayuwata, farinciki na, zaɓi na kuma uwar ƴaƴana, Idan kin fasa rabani da ita baki haihu acikin uwar ki ba" yakai zancen yana ƙara shaƙureta yanda ko motsi ta kasa ci gaba dayi sai kakarin mutuwa kawai da idanuwanta da suka turikke, da ƙyar Jabir da tunda aka fara case ɗin ya koma gefe yana kallon chakwakiya yazo ya ɓanɓaresa gudun kar ya jamasu wata fitina suna zaman-zaman su, don tsaf Amira zata iya mutuwa a hannunsa ba tare daya sani ba saboda tsananin ɓacin rai, wani irin yarfi yayi da ita gefe sai ji kakeyi tim tamkar an jefar da kayan wanki.
Daidai lokacin Amira ta farka daga nannauyan baccin da takeyi a cikin class sanadiyar yawun da suka sarƙeta acikin mafarkin da takeyi sai abun yazo mata a zahiran ce tana ta faman tari tare da haɗa zufa, gashi dama ba kowa a cikin ajin kasancewar malamin da zai yi masu lecture ta gaba ya ce bai samun zuwa shine fa duk suka watse tana bacci ba tare data sani ba, su kuma suka tafiyarsu ba wanda ya tada ta saboda kowa harkar gabansa yakeyi.
Ta jima tana tari mai tsananin wahala kafin ta samu ya tsaya mata, da sauri ta fito class tare da kiran wani mai sai da ruwan leda data hango ta ɗauki ƙwayar ɗaya ta fashe ta shanye tas, ta sake ɗaukar wasu ƙwayar ɗaya ta fasa suma ta shanye sannan ta koma class ta ɓuɗe jikkar ta ta ɗauko naira hamsin ta bawa mai sayar da ruwan ta ɗauki wasu ƙwaya ɗaya ta wanke fuskar ta zuwa wuyan ta data haɗa wani irin gumi da har tsiyayar mata yakeyi, shi kuma ya miƙa mata canjin ta naira ashirin ya wuce yana kallon ta cike da mamakin abunda ya haddasa mata yin gumi haka sai kace wacce taci ƙari,
Jiki ba ƙwari Amira ta ɗauko jikkarta ta sagale a kafaɗa ta nufi bakin gate, tafe take tana faman tunane tunanen abubuwan da suka faru acikin mafarkin ta, babu abunda ya ɗauke mata kai kamar irin yanda taga mm ya sauya acikin mafarkin tamkar wani mafaɗacin zaki, anya kuwa zai iya yin hakan a zahiri? Ta tambayi kanta haɗe da shafo wuyanta, da alama shaƙurar da yayi mata a mafarkin ce ta zo mata arai, kamar ance ta juya gefen dasu mm ke zama, ai kuwa ta hango sa tafe shi da Janan zasu tsallako titi ta gefen da take suna dare, wani irin ƙululu taji ya tokare mata zuciya tayi saurin komawa gefe jikin i.c.t block tana kallon su cike da takaici har suka tsallako zuwa jikin motar ta, sai da tasa makulli ta ɓude marfin motar tukuna ta juyo bayan ta jingina ajikin motar tare da naɗe hannayenta ta ɗora a ƙirji tana kallon mm.
"To yallaɓai zan tafi"
"ALLAH ya kaiki lafiya ranki shi daɗi, ki kula mani da kanki"
"Bakada damuwa akan hakan, nidai ke tunanin anya zaka kula mani da kanka kuwa?"
"Me yasa kika ce haka?"
"Baka ji me Jabir yace ba da zamu taho, baka samun isasshen bacci haka ma baka gajiya da aiki, to taya zan sa ran zaka kular mani da kanka, wataƙilma ko abinci baka kulawa da ci yanda ya kamata"
"Ƙyalesa sharri kawai ne yake yimun, amma maganar gaskiya ba haka nake ba sai da na haɗu da cutar son ki"
Sinne kai tayi tana dariya cike da jin daɗi kafin tace,
"In kuwa haka ne na sha godiya sosai, sai dai ya kamata cutar son nawa, ta sake ka haka tunda ka samu magani saboda ka kula mani da kanka"
"Eh..amma ai shi magani a hankali yake aiki ajiki, sannan yuyuwar samun waraka ya ta'allaƙa ne da irin inganci da ƙarfin da maganin yake dashi, don haka tabbacin samun waraka ta daga cutar son ki shine samun kulawarki da kuma soyayyarki koda kaso tamanin ne cikin ɗari"
"To shikenan kasa a ranka ma ka samu"
"ALLAH kuwa Janany tawan"
"Sosai kuwa, sai ka tuna mani da Addah ta Nihal, ita kaɗai ke kirana da wannan sunan saboda ƙaunar da take yimun, sai gashi kaima ka faɗa, inaga sunan na fitowa ne daga bakin mutane na musamman dake yimun soyayyar gaske"
"ALLAH sarki, Nihal? Sunan yayar tamu kenan?"
"Eh, bari na hanzarta naje gida gaba ɗaya soyayyar ka ta sa na manta dana na baro ta bata jin daɗi"
"Subhanallahi, da sauƙin ko?"
Dariya Janan tayi sosai don tun jiya take faman yinta idan ta tuna da dukan da ruwa suka yiwa Nihal garin neman the charming ɗin ta saboda matar ta data tsaya mata a hanya, shine fa bazata iya jira ba ta hau mashin ruwa yayi mata duka, yanzu haka tana can kwance cikin duvet in ba ALLAH ya sa jikin ya yi mata sauƙin ba,
"Kai Janany, wannan irin dariya haka fa" mm ya faɗa yana dariyar shima,
"Ba komai, wlh Adda Nihal nake tunawa, ALLAH dai ya cika mata burin ta"
"Amiin my luv, ki gaishemun da ita idan kin je"
"Zataji in sha ALLAH" ta faɗa tana buɗe marfin motar sannan ta shiga ta zauna tare da sauke glass ɗin tana kallonsa"
"Ya dai ranki shi daɗi?"
"Bana son na tafi na barka ne, zanyi matuƙar kewarka kafin wayewar safiyar gobe" ta ƙare zancen tare da ɗora haɓarta saman jikin tagar motar data sauke glass,
"Ko ɗaya bazan bari hakan ta faru ba tunda ga lambar wayar ki a tare dani" ya ɗago 'yar nokia dake hannunsa da sukayi musayar lambobi, murmushi tayi haɗe da tada motar sannan ta ɗago kai ta ce,
"Byee luv" tana ɗaga masa hannu, shima hannun ya ɗaga mata haɗe da cewa,
"Bye sweet.." tare da ɗora wayar a bakinsa yana ji kamar kar ta tafi ta barshi, ganin ta tsaida motar bayan ta ɗan yi nisa ya sashi nufo wajen sanadiyar Amira data hango a laɓe tana ƙoƙarin fitowa ta sadda kai ƙasa da alama kuka ma takeyi, bata yi niyar tsayawa ba amma ganin yanda makarantar tayi tsit don ƙarfe biyar har ta wuce yasa ta taka burki lokacin da ta kawo wajen da take tare da sauke glass tana faɗin,
"Ah!.. Amira, dama baki wuce ba?"
"Eh Janan, yanzu dai zan tafi" ta faɗa ba tare data bari sun haɗa idanuwa ba,
"Ok, to shigo muje ko! Nima na tsaya wajen su mm ne, shiyasa ban tafi ba, saboda tun 3, pro...ya kirani ya ce ba lectures Wai malqn ya ce bazai samu damar zuwa ba"
"Ok, hakane" ta faɗa tana ƙoƙarin tafiya,
"Shigo mana muje sai na saukeki"
"No ki barshi na gode"
Daidai lokacin mm ya ƙara so wajen haɗe da cewa,
"Ranki shi daɗe lafiya kuwa?"
"Lafiya ƙlw yallaɓai" ta faɗa tare da juyowa tana kallonsa tana murmushi,
"Amira na gani shiyasa na tsaya" sai alokacin mm ya ɗago kai yana kallon gefen da Amirar take haɗe da cewa, "sannu Malama Amira ya karatu" karaf idanuwan su suka haɗu sanadiyar kallon data tsare sa dashi tun daya iso wajen, da sauri ta sadda kanta ƙasa ba tare da tace dashi uffan ba gabanta sai dukan uku-uku yakeyi saboda wani irin kwarjini da ya yi mata,
"Shigo mana" Muryar Janan da ta ji yasa tayi saurin faɗawa cikin motar don ba taso su ƙara haɗa idanuwa dashi, ɗan ranƙofowa yayi ta jikin tagar haɗe da cewa,
"To Madam, ALLAH ya kiyaye ko" ta sakar masa murmushi haɗe da rolling idanuwanta sannan ta ce,
"Godiya nake" haɗe da tada motar ta bar wajen,
Wata irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa ya koma wajen sana'ar sa yana jin yau burinsa ya gama cika saboda ya samu soyayyar masoyiyar sa,
Amira kuwa suna fita bakin gate ta kalli Janan ta ce,
"Ajiye ni nan Janan"
Janan dake kallon gefe-gefen titi tana ƙoƙarin tsallaka wa ta ce,
"Me yasa?" Ta faɗa ba tare da ta kalli gefen taba,
"Akwai inda zan je"
"Bara na saukeki acan"
"Na haɗa ku da ALLAH ki ajiye i man, wai meye hakan?" Amira ta faɗa cikin fushi da ɓaci rai tare da haɗa hannayenta waje ɗaya alamar roƙonta, cak Janan ta taka burki haɗe da juyowa tana kallon Amira cike da mamaki, wai meye haka takeyi ne, meyasa bata fahimtar ta akoda yaushe ita kullum faɗa ko gajiya bata yi? ta shiga tambayar kanta, kafin ta ankare tuni Amirka ta ɓalle marfin motar ta fice daga motar, sai dai Janan ta hangota tana tare mai mahin zata hau.
"ALLAH ya kyauta" ta faɗa a fili tare da tada motar ta tabar wajen.
*ALLAH KAJIƘAN IYAYENMU 👏😭*
[8/24, 9:13 AM] Beey Sai dake: _Page 19_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1237455446?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=PYGQ%2BdOO8e%2BCwsNwn9fb5e1%2BzLxKjUxQ96n8c%2FLnmLxdmMcOcGqbBGiAMZKGkI91RPQWQMCjqhSn7rSSvPO8Db%2BTYr74tNLrPYhmznvY9Z1ZkJLEu5JQu27aPuIJ7ZQs_
*KIN SAYI SHIRINMU NA TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B?, IDAN BAKI SAYA BA MAZA KI HANZARTA KI MALLAKI NAKI TA HANYAR WUƊANNAN LAMBOBIN DOMIN SAMUN ƘARIN BAYANI
+447894142004, 07065283730, LITTAFAI BAKWAI DA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU MASU MATUƘAR ƘAYATARWA AKAN NAIRA DUBU ƊAYA (1000) KACAL, ƳAR UWA GWADA KI GANI IDAN KINA CIKIN WUƊAN DA SUKAYI RASHIN BATCH A ƊIN MU, NA TABBATA BAZA KIYI NADAMA BA😍*
______________________________
Cike da farin ciki ta ƙarasa gida, yau ma sai da ta fara biyawa party ɗin Hajiya zee tayi mata ya jiki suka taɓa 'yar fira wacce hakan ba ƙaramin farin ciki ya saka Hajiya zee tayi ta saka mata albarka sannan ta wuce party ɗin su, tana shiga ta tadda madame florence a kitchen ita da Nihal suna girka abun da za a ci da daddaren,
"Wow! Adda Nihal kice kinji sauƙi" Janan ta faɗa tana yiwa Nihal wani kallo mai cike da burgewa saboda yanda taga tayi kyau, support wears ne a jikin ta pink colour and white, wanda da riga masu dogon hannu sai p-cap data saka, tasowar ta kenan tana tambayar Madam florence ko Janan ɗin ta dawo, shine fa ta shiga tana ɗan rirriƙa mata aikin sai gata ta dawo, murmushi kawai Nihal tayi ba tare data juyo ba don fushi takeyi da ita, haka yasa Janan lallaɓowa ta bayanta ta rungumeta haɗe da ɗora kanta saman bayanta,
"So much missed you Adda Nihal, pls kada kiyi fushi da Janany sister ɗin ki bazata jura ba?" ta ƙare zancen tare da saƙalo hannayenta a wuyanta ta turo fuskarta tana kallonta, ɗan juyo da fuska Nihal tayi itama har suna shaƙar numfashi juna haɗe da cewa,
"Ba wani can, ni cikani tunda kin manta dani"
"Laaa..inji waye? Ai in zan manta ki Adda zan manta da kai na, kawai wani abun ne mai matuƙar muhimmanci a school ya sakani zama busy, but i'm sorry pls..."
Ta faɗa haɗe da sakinta ta haye cabinet ɗin dake cikin kitchen ɗin tana gaida Madam florence dake faman kallon damar su tana murmushi, hannu ta saka ta ɗauki samosa ƙwaya ɗaya da take soyawa ta saka a baki tana ci tare da kallon Nihal dake faɗar,
"Ehmm!, Janany sister ashe har akwai abunda ya fini muhimmanci a school ɗin taku!" Ta ƙare zancen tana wanke hannayenta a jikin fanfon dake cikin kitchen ɗin haɗe da jawo ƙaramin towel dake sagale ta goge tana ƙoƙarin ficewa, don dama ita ke naɗawa Madam florence samosa ɗin,
Saukowa Janan tayi daga kan cabinet ɗin ta ɗauki wata samosar ƙwaya ɗaya tabi bayanta tana faɗin,
"No Adda Nihal ba haka bane, kawai dai abun nada muhimmanci ne shiyasa ma kika ga nakai wannan lokacin ban dawo ba, ya ƙarfin jikin naki?"
"Am just little fine dear, ya karatun?"
"Alhamdulillah Adda ALLAH ya ƙara sauƙi"
"Amin ya rabbi"
"Adda gaskiya wannan yayan nawa da zan ganesa yanzu saina makashi a kotu kafin ayi komai na wahalarmun da yaya da ya yi"
Murmushi Nihal tayi suna yi suna taka matattakalar hawa saman zuwa ɗakunan su haɗe da cewa,
"U'uhm Janany Sister, kibar nono yayi bacci, ai ba dukan ruwa zan sha ba ko dukan 'yan sanda zan sha saboda shi bazai yuyu a ma kashi kotu ba, wanda kuma yayi hakan ko waye zamuyi baraa'a dashi, ko kuwa dai kin manta da irin girman soyayyar da nakeyi masa ne shi yasa kika daɗi hakan"
"Ko ɗaya Adda, amma ai ya wahalar mani dake, dubi yanda zazzaɓi ya rufeki jiya.."
"Duk yana cikin TUKUICIN da SO ya haifar mani, yanzu ma kinga muyi Sallah muje ki rakani a can ko zanyi game da katar..." Ta ƙare zancen tana dariya tare da shigewa ɗakin ta,
Zaro idanuwa Janan tayi tana mamakin wai duk wahalar nan da Adda ɗin ta tasha jiya tana nufin yau ma komowa zatayi? Tirqashi! Lallai mai so ba ya gajiya kuma ba ya ganin wahalar dake cikin sa komai girmanta ta faɗa a zuciyar ta haɗe da shigewa ɗakinta itama, a gurguje ta cire kayan ta ta faɗa toilet ganin magrib ta kusa ƙarasowa, tana shiga wayar dake kan gado ta ta hau ru ri, dai dai lokacin Nihal ta shigo ɗaukar wani lifaya a cikin kayan Janan da take son sakawa yanzu, kusan kira huɗu ya yi tana tsinke wa sai a na biyar Nihal da har zata fita ta zo ta ɗauki wayar cikin jin haushin kiran da ake tayi tun ɗazun, ba tare data tsaya duba ko waye ba ta ja dogon tsaki haɗe da cewa,
"Wannan wane irin abune haka? Tunda aka ga ba'a ɗaya ba ai ya kama asan wacce keda wayar ba ta kusa sai a ɗan jira, irin wannan kiran ai ba wayewa da burgewa a cikinsa" ta sake jan tsaki a karo na biyu sannan ta kashe had'e da jefa wayar a kan gado, dai dai lokacin Janan ta fito ɗaure da towel iya cinyarta sai wani ɗan ƙarami kuma a hannunta tana goggoge jikinta dashi,
"Ke da waye Adda?" Ta faɗa tana kallon Nihal dake ƙoƙarin ficewa a ɗakin ranta a ɓace, ta tsani disturbing a rayuwar ta musamman ma na waya, shiyasa tayi blocking mutane da dama a wayarta dake damun ta,
"Oho, ki duba wayarki ki gani man" ta bata amsa a taƙaice tare da ficewa daga ɗakin, da sauri Janan ta jawo wayarta tana dubawa don har ga ALLAH ta zata Nihal a wayarta take wannan lukutar masifar, zaro idanuwa tayi ganin missed call har guda huɗu na mm ɗin ta da kuma recieving call ɗaya nasa wanda ko shakka babu shine Nihal ta ɗaga, kenan wai duk baƙaƙen maganganun da Adda tata tayi duka wa mm ɗin ta tayi su?, Dafe goshi tayi da tafin hannun ta haɗe da sake kiran lambar tana ji tamkar taje ta kaiwa yayar tata duka don takaici, ringing ɗaya tayi a na biyu ya ɗaga, kusan tare sukayi wata irin ajiyar zuciya kafin ta zauna gefen gado tana makawa ƙofar fita ɗakin harara tamkar ita ce tayi mata laifin haɗe cewa.
"Yallaɓai barka da marece"
"Barka dai ranki shi daɗe" mm ya faɗa haɗe da sakin wani murmushin jin daɗin muryar ta da yayi, dama can ko ɗaya bai damu da maganganun da aka faɗa masa ba ɗazu, don ya tabbata ba Janan ɗin sa ba ce sai dai ko wace, tana da alaƙa da ita shi yasa bai maida kalma ko ɗaya ba, don yanayin sautin muryar daya ji iri ɗaya ce da tata, ɗan kaushi ne kawai ta waccan tafi shima ɗin wata ƙil don ta kausasa tata ne tana faɗa,
"Hello hubbin ruh (masoyin raina), kana jina kuwa?"
"Eh Janany, ya kike kin isa lafiya"
"Lpy klw, tunanin me kakeyi, ina ta magana baka ji ba"
"Tunanin ki mana, me kika ce?"
"Hmmm, haƙuri fa nake baka akan abun da Adda tayi ma, don ALLAH kayi haƙuri ka ji?"
"Ai ba komai, ni hakan ma da tayi ya yi mun, saboda hankali na ya soma tashi dana kira har sau huɗu baki ɗaga ba"
"Na san ka faɗa ne kawai hubbirruh, amma ko ni dana fito naji abunda take faɗa ban ji daɗi ba, pls kayi haƙuri ka ji" ta ƙare cikin shagwaɓe murya da har sai da ta sashi sakin 'yar dariya haɗe da cewa,
"To shikenan, tunda baki yarda ba, na ji kuma na haƙura"
"Yawwa yallaɓai na, ina godiya"
"To kawo TUKUICI"
"Ai tuni na baka"
"Ni ɗin? To TUKUICIN me kika bani bada sani na ba?"
"TUKUICIN SO mana" ta faɗa tana dariya tare da faɗa wa kan gadon fuskarta na kallon rufin ɗakin, cikin jin daɗi ya ce,
"Ina son ki Janan"
"Ni ma ina son ka muhriz"
"ALLAH ya bani kuɗi na mallakeki ki zamo asusun sirrin zuciyata da kuma gangar jikina"
"Kasa a ranka ko babu kuɗin Janan zata zamo asusun sirrin dukkanin rayuwarka domin kai nake so ba kuɗi ba, saboda haka shirye nake da na zamo mallakin ka kai kaɗai" wani irin murmushi ya saki da har sai da sautin sa ya dakar mata zuciya ta mirgina daga kwancen da take tana kallon sama haɗe da cewa
"Kabi a hankali yallaɓai zaka iya kasheni da wannan murmushin naka fa"
"Kema haka, domin kuwa kalamanki gaf suke dasu sa na kife acikin baron dabinon nan nawa" sosai ya bata dariyar da har sai da tasa dimples ɗin ta lotsawa tare da saka haƙoranta gaba ɗaya suka bayyana saboda jin daɗin zancen haɗe da cewa
"Ka rufa mana asiri kada ka karya mana jari, in dai kalamai na ne sun tsaya anan don ga kiran sallar magrib can na jiyo, sai aje ayi Sallah ko?"
"To shikenan nurul alb (hasken zuciya), bari mu hanzarta muje gida muma, ki kula mani da kanki"
"Zanyi hakan wakai yallaɓai" sannan ya kashe wayar yana kallon Jabir daya tsura masa idanuwa cike da mamaki, koda yake ba abun mamaki bane indai mm ne, kana ganin idanuwansa kasan mayen soyayya ne,
"Au! Duk zamana mayen soyayya na kaika? Ɗan sa ido kawai" Mm ya faɗa tare da tura baron dabinon sa yayi gaba, ashe zancen da Jabir keyi a zuci har ya fito fili shi yasa ya bashi wannan amsar, don haka Jabir ya kwashe da dariya tare da tura baron nasa yabi bayan sa shima yana faɗin,
"Yasin duk zama na mayen soyayya baka taɓa kamani ina cewa zan faɗa a baron dabino na ba"
"Jeka dai, na ji don kanka"
Haka dai suka ƙarasa bakin gate suka karɓi motar kamar yanda suka saba suka wuce gida, ita kuma ta ɗora wayar a ƙirji tare da rufe idanuwa tana tuna kyakkyawar fuskarsa haɗe jin soyayyar sa na sake shiga lungu da saƙo na zuciyar ta, ta jima a haka kafin tamiƙe ta fara gyara kanta, kasancewar ruwan da aka sheƙa jiya sun sa garin ya yi sanyi sosai ya sa ta ciro dogon wando blue da t.shet fara ta saka, dogon hijabi ta ɗauko ta ɗora akai ta tada sallar magrib don dama ta riga da tayo arwalar ta wajen wanka, tana gamawa ta ɗauko wata doguwar riga da zata kai mata guiwa iirin mai kabrin nan ta sanyi ta saka tare da rolling kanta da white vail, sosai ta kalli kanta cikin madubi taga tayi kyau duk da mai kawai ta mutsitsikawa jikin ta sai powder da lips tick data sakawa fuskarta kaɗan, turaren oud Saudi ta ɗauko ta shashshafawa bayan hannayen ta sai kuma wani lovely upon mai matuƙar sanyayayyen ƙamshi na fesawa ta feshe jikinta dashi, tana tsaya a gaban madubin Nihal ta turo ƙofa cikin shirinta na lifaya tayi kyau sosai tana faɗin,
"Muje ko?" Murmushi tayi mata tare da bin bayanta suka sauko suna ɗan taɓa fira bin gwanin ban sha'awa, suna kawowa tsakiyar falon Madam florence na ƙoƙarin hawa ta kirasu,
"Ah weldone my doters, you look very beautiful today"
"Thanks Madam" suka amsa a tare suna ƙoƙarin fita, kallonsu Madam florence ta ƙara yi haɗe da cewa,
"My doughters, what about the food?, It's ready there for you"
"Till we be back mam" Nihal ta bata amsa a taƙaice tare da ɗaga mata hannu,
"Ok, safe journey and drive safe you hear?"
"Yes Madam, thank you"
Har bakin ƙofa ta raka su suka shiga wata baƙar parado dake ajiye daga cikin jerin motocin dake a parking space ɗin gidan jere, Nihal ce ta shiga wajen tuƙawa yayin da Janan ta shiga gefe ta zauna tana latsar wayarta, key ta bawa motar sannan ta ja suka fice daga gidan, tafiya mai nisa sukayi kafin Janan dake latsar wayarta ta ɗago kai,
"Wai ina muka nufa ne Adda?"
"Neman the charming ɗina mana"
"Da haka me zai hana muje can inda kuka haɗu ki kwatanta wa ma'aikatan wajen shi ko ALLAH zai sa akwai wanda ya san shi, wannan wahalar banza ce kawai zamuyi tunda shi ba zaman yawon bin titi zai riƙa yi ba"
"Babu wahala aciki Janan, bakiji me malam bahaushe ya ce ba?, Indai jere na yawo zabo ma yana yi tofa watarana sai sun haɗu"
"Haka kike gani?"
"Sosai kuwa" ta faɗa tare da murɗa staring motar ta shiga round ɗin da zaka ɗauke hanyar da zata kai ka bebeji plaza, tana faɗin "Amma bazan ƙi shawarar ki ba, bari muje can ɗin" tana rufe baki motar su mm na wucewa ta ɗaya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 40