Share this page
haƙura and i love you so much" Dariya yayi tare da riƙe kunnuwan sa yana faɗin, "ko dai naƙara da tsallen kwoɗo don ki sake faɗan haka?" "Me kenan?" "Abun da kika faɗa yanzu" rufe fuskarta tayi da tafin hannuwa cikin jin kunya ta ce "Ka rufan asiri, ai ko bakayi hakan ba zan iya cigaba da faɗa har sai kace ka gaji da saura" "To sake faɗa naji idan da gaske kike yi" ya tsura mata idanuwa yana kallo tamkar zai haɗiyeta, "To shikenan nafaɗa i love you, i love you so much hubbin Raina" "Wowww..Love you too Noor albina, ALLAH yayi maki albarka" ya ce tare da miƙewa ya koma wajen zaman sa yana dariya, tsintar kanta tayi da kasa buɗe fuska balle su haɗa idanuwa har sai da taji yana huro mata iskan bakinsa a bayan hannunta data rufe fuskar dasu, "Janan kenan, daga faɗa i love you shikenan har kinji kunya?, ni dake cewa ba ruwana ALLAH ya hutasshe ni da kallon finafinan soyayya ina da kajol a gidana idan munyi aure" dariya ta saki tare da ɗan ɗago kai tana jifansa da wani irin sanyayyen kallo, ta ce "Kai kuma shahruk khan ko?" "Tab..ai ni nafi shahruk khan, irin soyayyar dana tanadar maki na tabbata ko Majnun ɗin Laila bai yi mata irin ta ba, haka ma ko makamanciyar ta Romeo bai gwadawa Juliet ba, ki sha kuruminki nayi maki tanadi mai kyau acikin zuciyata, gidana da kuma rayuwata, in sha ALLAH zan baki kulawar dake kanki sai kinyi mamaki, nakuma so ki mafi ƙololuwar soyayya a aduniya, na ƙaunace ki irin ƙauna wacce uwa ke yiwa ɗan ta, tsawon rai da kuma lokaci kawai nake jira don tabbatar maki da hakan" "Kabar ni haka mm kada kasa na aza rigima nace lallai lallai yau sai an kaini gidan ka, Ni Janan ina da tabbaci da kuma yaƙin akan duka maganganun daka faɗa, amma kasani koda bazaka yimani dukan waɗan can abubuwan ba, zan sadaukar da rayuwata duka na rayu dakai kuma na mutu dakai a haka, domin soyayyar gaskiya nakeyi maka da bata jiran wani sakamako akai" "Na yarda da dake da kuma kalamanki ranki shi daɗe, amma tsabtatacciyar soyayya irin taki dole ayi mata babban TUKUICI da SO, hakan shine zai zamo mata ban ruwan dazai sake bata damar yaɗuwa har ta saki ƴaƴan da za a tsinka a amfana dasu" "To shikenan yallaɓai, ALLAH kacika mana burin mu" "Amin ya rabbi Noor alb, haka nake son jin kin faɗa" Sun jima suna faranta wa junansu da daɗaɗan kalamai, anan yake sanar da ita zancen tafiyarsa Abuja, acewarsa aiki zai je nema kamar yanda ya faɗa mata, don ita a tsammanin ta zancen tafiyarsa garin su ne da suka yi sai gashi taji akasin hakan, ita kam sam ta nuna masa rashin amincewarta akan tafiyar wai ai duk aikin da yake nema zai iya tsayawa a nan garin ba sai yayi nesa da ita ba, sai da yayi da gaske da ban magana da ban rarrashi sannan ta amince shima ɗin har dasu ƙwallanta don kuka ta so aza masa, ganin abun nasu yaƙi ci yaƙi canyewa yasa Jabir isowa wajen yana faɗin, "To shahrukhan, in kun gama ya kamata mutafi rana keyi" murmushi mm da gaba ɗaya kukanta ya soma dagula masa lissafi yayi haɗe da cewa "Sunan da madam kenan ta bani yau" ya ƙare zancen haɗe da kallonta yana nuna ta da yatsa, kallonta yayi shima yaga ƙwalla a idanuwan ta, ya ce "Kai kai kai...waya taɓa mana Mrs mm haka take zudda tsadaddin hawayen nan nata da mm ke ji har cikin ransa" wasu hawayen ne suka sake zubo mata a fuska tayi saurin sinne kai ƙasa, ta ce "Ya Jabir don ALLAH kace masa kada ya tafi, wlh bana iya jurewa rashin ganin sa har na tsawon wasu kwanaki balle kuma ace satikka" a lokacin Jabir ya fahimci inda kukan nata ya dosa, cikin sigar ban magana yana ƙoƙarin taushe dariyar dake ƙoƙarin zo masa, ya ce "A'a, bazan ce kada ya tafi ba Janan, idan ya zauna to dame zaiyi ƙoƙarin ganin ya mallakeki?, kinga, kiyi haƙuri nasan ba wani jimawa zai yi ba zai dawo, shin wata uku ne kacal zakayi ko mm" ya ƙare maganar cike da zolaya yana kallon sa, "Mts..ba kada kirki fa Jabir, so kake yi taƙara rikice mun ne? Ƙyalesa in sha ALLAH bazan wuce sati biyu da kwana uku ba kamar yanda na faɗa maki kin ji ko?" "To shi Jabir ɗin yaje mana, kai saika tsare shagon da yake kula dashi kafin ya dawo" Ɗaure fuske Jabir yayi tamkar wanda akayiwa albishir ɗin mutuwa yana ɗan hararar Janan irin ta ɓata masa rai ɗin nan. "Ashe haka kike da muguwar fata ban sani ba?, To ai naki wasa ne, don duk baby ta ƙyalla idanuwa taga bana cikin gidan nan har na tsawon sati biyu, to fa ba Momy kaɗai ba hatta maƙwabtanta sai sun gaji da sauraren rigimar da zata saka mata, shiyasa ko da wasa bazan yarda nabar garin nan ba indai bada ita ba, shima ɗin idan munyi aure" "Ka ji ko?, ALLAH ya Jabir ya fika wayau, amma shikenan ba komai na haƙura ALLAH yasa kayi tafiyar sa a kuma ya kaika lafiya kadawo lafiya" "Amin ya rabbi Mrs mm ke kaɗai bada kowa ba" "ALLAH?" "Wannan ai DAƊAƊƊEN ALƘAWARI na ne" cike da jin daɗi ta rufe fuska tana mai addu'ar ALLAH ya tabbatar da hakan har iya ƙarshen rayuwar su, Ganin ya miƙe ya sata buɗe fuskar haɗe da miƙewa itama ta buɗe jikkarta ta ciro wayar ta, yana kallo ta buɗe gidan layi ta ciro sim card ɗinta ta miƙa masa wayar, idanuwa ya zubo mata cike da ayar tambaya, ta ce "Ka karɓa mana zanyi maka bayani" ba musu ya karɓa, "Ka saka layinka aciki, ina so muriƙa chart da vedio call, don na tabbata kiran waya kaɗai bazai hanani kewar ka ba" "What? Don ALLAH ki rufamun asiri, i phone 11pro ce fa?" "Eh mana, ai ka fita daraja awajena" dariya ya yi yana jujjuya wayar kafin yace, "Duk da haka dai, ai sai kisa nakasa samun aikin idan aka ganeni da ita, ungo abunki in Sha ALLAH zan samu aron waya da zamu iyayin chart ko da baza tayi vedio call ba, sai muriƙa gaisawa ina turo maki hotuna na, ina wannan shine damuwarki ko?" "Eh amma kariƙe" "ALLAH bazan karɓar ba" ya ƙare maganar tare da jawo handbag ɗin tata dake rataye a kafaɗarta ya jefa wayar aciki, "To shikenan" ta faɗa tare da ciro atm card ɗin ta ta saka masa agaban aljihu tana faɗin, "ALLAH NI kuma sai ka karɓi wannan, ƙarshen lambarka sune pin ɗinsa, a maimakon ka ari waya, to kayi amfani da kuɗin dake cikin sa kasiyi wata tare dayin ƴan buƙatocin da ba a rasa ba kafin kadawo" Miƙa hannu yayi da zimmar ciro atm card ɗin tayi saurin cewa, "Wlh bazan karɓa ba" "Me yasa kikayi haka?" "Saboda kafi ƙarfin hakan" "Yanzu ke idan buƙata ta taso maki, ya zakiyi?" "Bama zata taso ba in sha ALLAH" "Amma dai kinsan baki kyauta ba ko?" "Kai kake ganin haka, ehm kaga, don ALLAH mubar ma wannan zancen, ku shigo ku gaisa da Hajiya naga ya Jabir sai faman hararar mu yakeyi, da alama har yanzu haushi na yake ji" ta ƙare zancen tare da wucewa gaba tana dariya, har takusan shigewa mm na tsaye yana kallon ta cike da mamaki, abubuwan daya kamata ace shi keyi mata amma ita take yimasa, wannan wane irin so ne da yarda ta bashi? Ya tambayi kansa yana mai jinjinawa girman soyayyar ta, matsowa Jabir yayi ya ɗan taɓa kafaɗar sa haɗe da cewa "Kaga, wlh nagaji da tsayuwa cikin gidan nan, ina son ganin matata, in zaka shiga agaisa mu tafi, idan kuma bazaka shiga ba don ALLAH mu wuce" yayi zancen cike da ƙosawa zaman gidan, A bakin ƙofa suka cire takalman su haɗe dayin sallama suka shigo ciki bayan an basu izini, lokacin Hajiya na zaune tana karatun alƙur'ani, gabanta ne taji yayi wata irin muguwar faɗuwa jin murya sak irin ta ɗanta Jamal, wanda a iya sanin ta yabar duniya da daɗewa, shin me hakan ke nufi, fatalwarsa ce ta dawo gareta ko kuma itace ke shirin riskar sa ta hanyar zuwa inda ya je?, ta tambayi kanta tare da ɗago kai don ganin ko waye..... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 41_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ______________________________ Wata irin muguwar faɗuwa gabanta ya sakeyi lokacin da suka haɗa idanuwa da Jabir dake ƙoƙarin ƙarasuwa daga ciki, tsaye yayi cak yana ƙare mata kallo, tabbas itace, matar da har ya mutu baya mance wulaƙancin da akayi masu sanadiyar zuwa gidan ta, duk da alokacin bai fi shekaru goma sha huɗu ba aduniya ba, zai iya tuna yanda komai ya faru a wannan ranar, bai sake gasgata ita ɗin ce ba sai da yaga tanufato wajensa jikin ta na rawa, magana take son yi amma ta kasa cewa uffan sai hawaye dake silalo a fuska, duk da baya da hasken fata irin ta mahaifinsa kuma bai ɗauko kamar shi sak ba, ta tabbatarwa kanta cewa wannan jininta ne saboda abubuwa guda uku, muryarsa, yanayin tsayuwarsa da kuma satar kamannin mahaifinsa da yakeyi, a hankali Jabir ya fara ƙoƙarin ja da baya ita kuma tana matso shi, "Jabir wai meye haka?" Mm ya faɗa tare da ƙoƙarin matsowa kusa dashi, fashewa da kuka grandma tayi haɗe da cewa, "Tabbas shi ne, Jabir ne jika na ɗan ɗan Jamal" wani irin mugun kallo Jabir ya watsa mata tare da juyawa zai bar falon tayi saurin kamo hannun sa, "Don ALLAH kada katafi Jabir, ina mahaifiyar ka?, Na roƙeka kadawo nayi nadamar abunda aka aikata maku" Fizge hannunsa yayi tare da juyowa yana kallonta da idanuwansa da sukayi jajir, ya ce "Na dawo?, Wai acikin gidannan ake roƙon nadawo na zauna, ban san ko waye keba ban kuma san wace alaƙa ce tsakanin mahaifiyata daku ba, kamar hakane a waccan ranar mahaifiyata tadinga roƙonku kina kallo aka wulaƙantata aka koreta, ko sau ɗaya kinyi tunanin tsaida mu ko dakatar da wanda ya koremu, ko kuma hanamu tafiya? Bakiyi ba, don me yanzu zaki dakatar dani kuma har kiyi tunanin zan tsaya?, Wlh da nasan wannan gidan ne Muhriz zai kawo ni da ban yarda nazo ba, don tun a waccan ranar na kashe gidannan da duk wanda ke cikin sa acikin rayuwata" "Kada kayi haka Jabir, kai jikan ne kuma ina tsananin ƙaunar ka, waccan ranar fin ƙarfi a akayi amma duk tsawon shekarun nan zuciyata bata taɓa hutawa daidai da rana ɗaya ba akan tunanin ka da mahaifiyarka, nayi kukan safe nayi na rana nayi na dare duka akan nadamar abubuwan da akayi maku, na nemeku a inda nayi tsammanin samun ku amma hakan ya gagara, don ALLAH kasamaman gurbin komai ƙanƙantar sa azuciyarka da zaka ji tausayi na kayafe mun" "Idan har ni jinin ki ne to tabbas bazaki taɓa samun wannan gurbinba a zuciyata, saboda jininki basada imani ko tausayin iya yafe kuskure komai ƙanƙantar sa, na tabbatar da haka ne a waccan ranar da aka wofantar dani da mahaifiyata a gabanki ba tare da ke ko shi wanda ya aikata kunji tausayin mu ba" yana gama faɗa haka yafice daga falon yana jin ɗari da ɓaƙin cikin takowa gidan da yayi alƙawarin bashi baya har duniya ta naɗe, da sauri mm ya biyo bayansa yana faɗin, "Haba Jabir, meye haka ka aikata, ALLAH ma fa munayiwa kuskure ya yafe balle ɗan adam, sannan a waccan ranar da kake magana bafa ita ta aikata laifin ba" Cikin ɓaci rai ya juyo yana kallonsa da rinannin idanuwansa kafin yace, "A'ina aka aikata laifin?, da sanin ta ko bada sanin taɓa?, Shin tanada ikon hanawa ko batada?, A gaban idanuwanta ne ko ba agaban idanuwanta ba?" "Jabir..." "Look kaje idan kasamo amsar tambayoyin dana yi maka sai kazo kayi ƙoƙarin tabbatar mun da cewa batada laifin kamar yanda kake iƙirari yanzu, kuma wlh da nasan Janan nada alaƙa da waɗan nan mutanen da ban taɓa bari ka faɗa soyayya da ita ba, don basu san meye so ba? Kuma basu san darajar sa ba" yana gama faɗar haka ya juya yabar gidan ba tare daya koma saurarar mm daketa faman kiransa ba, "Ya Salam!" Mm ya furta haɗe da girgiza kai sannan ya koma cikin gidan, dama yasan haka zata faru indai Jabir ne, yana da matuƙar zuciya da baisan inda ya samota ba saboda ba haka Momy take ba haka ma ga yanda yake jin labarin mahaifinsa shima yanada sanyin hali. (Ah to, nikam nace ina zai samota in ba wajen baffansa ba mahaifin Janan wato Alhaji usman😅😜). Koda ya shiga ya tadda Hajiya dirshan tana kuka Janan na faman rarrashinta, kasa sanin ta ina zai fara yayi don kuwa Hajiya nada hujjar yin kuka duk da ita yakawo hakan, sai da tayi mai isarta ta gama Janan ta riƙata ta je ta wanko fuskar ta ta dawo, kallon mm tayi da idanuwanta da suka kumbura yayi saurin sinne kai ƙasa saboda ba kaɗan ta bashi tausayi ba, "Muhammadu a ina ka haɗu da jikan?" "Amm... Hajiya dama sune mutanen da nake baki labari da suka riƙemu ni da ƙanwata, naso tun awaccan ranar na sanar dake sai nayi tunanin bari inyi maki bazata, kiyi haƙuri ban zata hakan zai faru ba" "Aa Muhammadu, ai bakayi kuskure ba kuma naji daɗin wannan bazatar taka, na kuma yi farincikin jin cewa tare kake dasu, saidai na fara jin tsoro a raina, anya zasu iya yafemun wannan kuskuren dana aikata?" Ta sake saka wani kukan har tana sharɓar majina, "Kiyi haƙuri Hajiya, in sha ALLAH zasu yafe maki, na sani Momy ma yafe maki tun kafin ki roƙeta, tayi farinciki sosai ranar dana bata labarin yanda mukayi dake, don banzo nan bama alokacin saida yardar ta, itace tayita ƙarfafamun zuwa kuma nasan shima Jabir idan ya sauko zai haƙura ya saurareki" "ALLAH sarki, don ALLAH ka kaini wajenta, ina so na haɗu da ita in roƙeta yafiya" "Kiyi haƙuri Hajiya, ba yanzu ba, in sha ALLAH jikanki zai ɗaukeki da kansa ya kaiki wajen ta" haka mm yayita lallaɓata yana bata magana tare da sake jan hankalin ta akan kuskuren da iyaye ke aikatawa da kansu sanadiyar ƴaƴan su don sunada tarin arziƙi ko kuma wani muƙami ko mulki, sai su koma sune ƴaƴan su kuma ƴaƴan sune iyayen, wanda sau da dama haka ke janyo lalacewar zumunci ko kuma kuskuren dahar a mutu ana nadamar aikatawa saboda an kasa gyarawa, sosai Hajiya taji kunyar abunda ta aikata da kuma nadamar yinsa, ta kuma ɗauki alwashin bazata koma barin haka tafaru ba acikin sauran rayuwar da take da ita nan gaba, Duk da mm sai yi yake yana duba agogo saboda lokaci dake ƙare masa saida suka jima suna fira sannan ya wuce, Janan kuwa gaba ɗaya jikinta sanyi yayi don bata taɓa tsammanin zafin rana Jabir zai iya aikatawa grandma haka ba, ta zata kawai ga ƴan mata ne kamar yanda yayi mata awaccan ranar da suka fara haɗuwa, Duk da mm yasan Jabir nada damar yin abunda yayi hakan bai hana shi ɗaura aniyar yaƙar zuciyar sa ba kamar yanda sukeyi akoda yaushe, yana isa gida bai zame ko ina ba sai part ɗin Momy don dama acan yafi tsammanin ganin sa saboda Razina, yana shiga kuwa ya isko zaune saman kujera ya jingina kansa a jikin kujerar idanuwansa a rufe, Razina na gefensa sai faman tambayar me ya samesa takeyi ya kasa yimata magana, kallo ɗaya mm yayi mata tabar wajen, cikin ɓaci rai da ɗan ɗaga murya ya fara magana, "Ni zaka wulaƙanta Jabir, ninzaka tozarta a gaban idanuwana?, Ashe dama haka ƴan uwan taka da abota take, dama a haka taren mu zata kasance babu sadaukarwa aciki? Ka bani mamaki wlh, kuma bari kaji, ko ina so ko baka so Hajiya kakar kace, Janan da Nihal ƴan uwane kuma ƙannen ka ne, haka ma mahaifinsu baffan ka n..." Kafin ya ƙarasa Jabir ya mike cikin zafin rai ya ce, "Enough, enough Muhriz ya isa haka, ni ba abun daya dameni dasu, ban sansu ba basu sanni ba, banda wata alaƙa dasu ka yarda ko karka yarda, kai kaɗai ne ɗan uwa kuma mahaifi da nake dashi, Momy kuma mahaifiyata uwata, Razina ƙanwata matata, kune duniya ta kuma ƴan uwana, bayan ku bana buƙatar kowa a tare dani, wata kaka, ƙanne, baffa da kake faɗa to hell with them ba abunda ya dame ni dasu..." Kafin ya rufe baki ya ji an ɗauke sa da zazzafan marin da sai daya ga wasu taurari, juyowar da zaiyi yaga Momy tsaye tana jifarsa da wani irin kallo da bai taɓa ganin tayi masa ba kafin ta shiga nuna sa da hannu tana cewa, "Dama shashasha na haifa ban sani ba?, Kai waye da zaka faɗi irin wannan mummunar maganar ga kakar ka, baffan ka da kuma ƴan uwan ka?, Ka manta sune silar ka da kuma asalin ka? Ka manta girman zumunta da sakamakon dake cikin wanda ya girmamawa? Na rantse da sarkin daya halitta mana Annabi Muhammadu duk ka sake faɗar irin wannan kalmar ba nice mahaifiyar ka ba, stupid boy an faɗa maka kai kaɗai ne mai zuciya, waɗan da suka fika sunyi wane amfani tayi masu da har zaka zomun cikin gida kana wannan shirmen" "But Momy they insult..." "Shut up! Idan sunyi insulting namu then what? Bai wuce bane ko an rubutasa ne a goshin ka, be side a wancan lokacin kai wane pain ne ka ji? Duk muninsa ko girmansa yakai wanda ni na ji a raina?" Yanda taga yana kuka hawaye na zubar masa a fuska yasa tayi lowering voice ɗin ta haɗe daci gaba da cewa, "My son let bygones be gone, babu amfanin riƙe abunda ALLAH ya ƙaddartowa bawa acikin rayuwa, mu zamo masu tuna alkhairi akoda yaushe, masu kuma mantawa da baƙin ciki har abada, katuna a sanadiyar su muka haifo ka a duniya, kaga kuwa sun bamu Alkhairin daya fi wancan baƙin cikin ɗaci, kuskuren da suka aikata mana bai kai wanda ƴan uwan annabi Yusuf suka aikata masa ba, amma daga ƙarshe da suka gane kuskurensu suka nemi gafara kasan me yace dasu?, *_'laa tasriba alaikumul yaum, yagfirullahu lakum, wa huwa arhamurrahimiyn'_ ma'ana _'Babu zargi akanku a yau, kuma ALLAH yana gafarta maku, kuma shi ne mafi rahamar masu rahama'_* anan nuni yakeyi masu da cewa bai rikesu azuciya ba kuma ya yafe masu, babu wani sauran zargi tsakani nai dasu, don haka kaima kayi koyi dasu sai Ubangiji yayi maka sakayya da babban rabo" Ganin kamar yaƙi haƙura har lokacin yasa Momy kallon mm dake tsaye yana kallonta cike da sha'awa, yana ji tamkar ina ma ace mahaifiyarsa zata dawo duniya shima ta riƙa lurar dashi da tausasan kalamai irin waɗannan tana tunasar dashi, ta ce, "Muriz jeka abunka ƙyalesa, wannan baƙar zuciyar tasa bazata sauka yanzu ba, ALLAH yasa mata sanyi ya kuma shiryaku duka" "Amin Momy" mm ya faɗa tare da komawa part ɗin su ya ɗauko jikkar sa da zai tafi, sai daya dawo ɗakin har lokacin Jabir na nan zaune inda yake ko motsawa beyi ba sukayi sallama da Momy sannan ya ajiye mata kuɗi koda zata buƙaci wani abun, dama tuni yayi booking ticket don cewa yayi bazai iya tafiya da mota ba saboda matsalar tsaro, don haka sai Momy ta sako mayafinta tana saka masa albarka haɗe da cewa, "Muje na kaika sai nadawo da motar, shi wannan da alama yau ya zama shuka tsirowa kawai muke jira yayi mu cira" abun ya ba mm dariya amma sai ya fuske tare da riƙo hannunsa sukayi musabaha ya ce, "Kayi haƙuri, in sha ALLAH komai zai daidaita yanzu ba yanda kake tunani ba, sai munyi waya" yayi hugging nasa sannan ya wuce, Har mm ya fidda ran zai rakasa sai gashi ya fito, hakan yasa Momy cilla masa makullin ya caɓe ba tare daya ce komai ba ya buɗe wajen zaman driver ya shiga ya tayar da motar, murmushi mm ya yiwa Momy ta shafa kansa tare dayi masa addu'a sannan ya zagaya ya shiga, lokacin Razina tafito itama da sauri ta shiga ɗaga masu hannu har suka tafi, haka kurum ta tsinci kanta da fashewa da kuka tare da faɗawa jikin Momy,..... *ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭* [8/17, 7:45 PM] ƳAR FARA KYAKKYAWA💎: _Page 42_ *TUKUICIN SO💞* *NA* *BILLY S FARI💎* *HASKE WRITTER'S ASS..💡* *Free Book* ****** *Ina masoya littattafan ASMY B ALIYU?, Kumar matso kusa yazo maku da wani shahararren littafin ta mai suna WAMINAL HOOB!, Hmm tirƙashi dajin sunan wannan littafin kinsan zaku gwangwaje da soyayya da kuma chakwakiyar ƙauna acikin sa, domin na tabbatar maku da hakan nazo maku da kaɗan daga cikin wannan ƙayataccen littafi nata mai matuƙar ɗaukar hankali, ta bakin malam bahaushe dai, ya ce gani ya kori ji👇* *Waminal Hoob* _Asmy b Aliyu_ PAID BOOK## Love# Friendship# Family# NooryAli#moments Tana ganin yarda jikinsa ke wani irin kadawa ,jawota yyi ta fado kansa Yana shakar kamshinta Yana sakin ajiyar xuciya ,kallon cikin kwayar idanunsa take .Wanda ya canja kala har kwallah take hangowa acikin su ,a hargitse ya shiga subbatar ta ta koina Yana tura kansa cikin Wuyanta,hawaye taji suna cika Mata ido tuno farhaan kurum,hade fuskarsa yyi da Tata fuskar Yana goga hancinsa da nata da wani irin Murya Yake fadin"I try Am very try Noory u belong tot someone else,ya fada muryarsa na karyewa A hankali kafin ya hade bakinsa da nata. T Friendship# Aliyu waxeer Farhaan Shagari "Da Alamar bakada hankali Farhaan ka Samu tabin kwakwalwa,ni kake tunanin naje na auri yarinyyar da kakeso har na tsawon shekara daya??''yyi maganar so pissed up ,farhaan ya kwantar da Kai Yana fadin nasan Nooriyyah Bata cikin kalar matan da kakeso ,nasan ba ajinka bace .Haka nasan baka sha'awar (BAKAR MACCE")bestyn ka xakayiwa wannanr Alfarma da xarar na kammala master's Dina xan dawo gareta muyi Aure!!"girgixa Kai Aliyu waxeer ya shigayi Yana fadin ka haukace Farhaan!!!" Waminal Hoob# Is out on the 31july..stay tuned and find out!!!! Love is in the Air# Team Noory-Ali#Forever❤️ FRIENSHIP## Aliyu waxeer Farhaan Shagari Areefa Mansoor Laylah waxeer FAMILY#❤️ Wazeer Family Shagari Family Azeex Ali Family.. ______________________________ Ɗora hannunta Momy tayi akan Razina dake saman kafaɗar tata tana kuka, ta ce "Aah autan Momy meye abun kuka anan kuma?, Ai ba jimawa sosai zaiyi ba" "Momy suna yin faɗa da ya Jabir, bana son haka sam" "Commooon, ai haka sukeyi akoda yaushe, matuƙar abu ya faru tsakanin su tofa sai sun hau sama sun faɗo suke daidaita, yayan naki ne zuciya tayi masa yiwa, pls kiyi ƙoƙari ki sauya mun shi kinji ƴatah?" Ta ƙare zancen tare da ɗago fuskar Razina dake saman kafaɗarta, tayi saurin maida kan ƙasa tana wasa da yatsun hannunta haɗe da cewa, "Bazan iya ba Momy, wlh nima tsoronsa nake ji aduk lokacin daya sauya irin haka" "Don't worry kinji ko ƴatah, ina yimasa addu'a sosai na tabbata kuma da taimakonki zai sauya da izinin ALLAH" "I wish that Momy" ta faɗa tare da ɗago kai tana kallonta, ta sakar mata murmushi alamun ƙarfafa guiwa da kuma sa ran da take dashi akanta wajen sauyawar yaron nata sannan ta shige cikin gida, ƙarasawa bakin gate dake buɗe ita kuma tayi ta rufe sannan ta wuce part ɗin su ta gyara kafin Jabir ɗin ya dawo, don dama wasu lokutan ita ke gyara masu idan mm bai samu gyarawa ba, don shi mutum ne mai tsananin tsabta da baya son zama da datti, shiyasa duk lokacin da wani uzuri ya hanasa gyarawa sai ya kira Razina bayan sun fita yace ta shiga ta gyara masu, hakan yasa abun ya zame mata jiki ko makaranta taje ta dawo zata shiga part ɗin ta duba, idan ba a gyara ba sai ta gyaro tayi masu turare sannan ta jawo ƙofar ta rufe masu, Ganin har sun kusa isa airport ɗin Jabir baice komai ba yasa mm ɗago kai yana kallon sa, ba tare daya damu da kallon da yakeyi masa ba ya ja wani iska ya furzar ta baki haɗe da ɗage hannunsa ɗaya daga sitarin motar yana dubin agogon hannunsa, murmushi mm yayi haɗe da cewa, "Alhamdulillah, zuciyar ƴan mazan ta kwanta kenan, wannan irin iska daka furzar haka ai sai kasa ya ɗage motocin dake gaban mu" murmushi ya saki ba tare daya auna ba haɗe da kauda kansa ta gefen glass ɗin motar yana ƙoƙarin danne dariyar dake son zo

Chapter 23 of 40